Category: Waminal Hoob Hausa Novel

  • Waminal Hoob 16

    Waminal Hoob 16

    Waminal Hoob_* 16

    PAID BOOK
    _Asmy b Aliyu_

    Kallon Aliyu tayi tana fadin muje kar dare yyi ,Yyi murmushi Yana fadin”ga saurayinki Nan shi xai saukeki,hade Rai tayi tana fadin”Idan baxa kaje ba kabani car key din peter ya saukeni .
    Mika mata car key din yyi tana gabda ficewa daga parlorn farhaan ya wani irin fixgota Yana kallon fuskarta ,
    Kokarin fisge kanta take ya riketa sosae Yana girgixata a tsawace yake fadin”Kara ki fito fili ki fadamin kin tsaneni kin daina yina yanxu sai na San matsayina a wajenki da wannan munafurcin da kike min,fisge kanta tayi tana fadin”kaje ka fara tambayarka Farhaan
    Kaje ka tambayi kanka meyasa alakarmu ta canja.”ka sauya gaba daya tamkar ba farhaan din da Yake sona a baya ba wannan daban ne ,,da wanda na sani,wata irin Daria farhaan din yyi wacce Bata tattare da nishadi acikinta,
    Ta gefen sa tabi xata wuce ya Kara fisgota Yana fadin,Ina kike tunanin xakije da wani kato……”!komawa tayi parlorn tana kallon Aliyu waxeer dake kallonsu tun daxu tamkar ya samu Tv.,Yanxu Kai nake Aure ba farhaan Shagari ba,kayi min ixini fita Dan Allah naje gyaran Kai…….”Tayi Maganar da rawar Murya,kalllonta kurum Yake Yana karantar yanayinta nishadin da takeyi xuwan farhaan ya kawarda shi kije kawai Allah ya kiyaye.”Ya fada Yana kallonta fisgota farhaan yyi ya xabga Mata Mari akan fuskarta Yana huci Yake fadin”ni xaki rainawa hankali ,Aliyu waxeer ya daka masa tsawa Yana fadin”Ka fara shaye-shaye ne??”Kai waye da xaka mareta ??”’ka fitar min a gida tun kafin rayukka su baci,ya kalli Nooriyah da hawaye sun gama wanke Mata fuska tana kallon farhaan din,wuce daki.”da gudu ta nufi dakin barcinta tana barin parlorn farhaan ya karaso gabansa Yana kallonsa a xafafe Yake fadin”Ae ni ne dai silar wannan Auren kou.”To ka saketa ynxu kabani takardar sakinta ,,ni da Kai ae kasan mun San hakan,kawai ka saketa ni xanji da sauran nagode da dukkan Karamci ,duk da wata xuciyar tana fadin ka fara cin Amanata shiyasa Nooriyah ta tsaneni, murmushi Aliyu waxeer keyi Wanda ya tsaya iyakarsa labbansa,xuciyarsa ta girgixa akan kalaman da suka fito daga bakin farhaan Shagari sai dai Bai nuna hakan a fili ba,Auren shekara daya kabani ba Auren wata daya ba,macce ce xata shiga tsakanin mu Besty Kuma ka yarda da hakan???”Abokantar shekara talatin tana neman ta rugeje sabida macce.”Ba Kai bane Besty wannan ya canja,Kai kana tunanin xan iya son Abunda kake so.”wani murmushi Mai ciwo yyi Yana fadin” hakan kakeso?? sakin Nooriyah inhar hakan xai sakaka farin ciki kabani wata daya xan fara shawo kan Ammah.”kasan ciwon da take dauke dashi ,xan iya rasa komai Banda mahaifiyata ,Idan wani Abu ya sameta baxan taba yafewa ba.”farhaan yyi murmushi xuciyarsa na tafasa Yake fadin”meyasa baka fada Mata contract marriage bane,akan me xata damu da Nooriyah har haka.”batareda Aliyu ya Kara kula sa ba ya dauki laptop dinsa ya nufi dakin barcinsa da sassarfa ,dauriya kawai yake agaban farhaan da ya ambaci kalmar sakin da ta Kusan tarwatsa xuciyar Aliyu waxeer a wannan lokacin,da ya runtse idonsa maganganun farhaan Shagari ke dawo masa cikin kunnuwan sa,hannu biyu yasa ya dafe kunnuwan sa Yana sauke wani irin numfashi……..A bangaren farhaan kuwa dakyar ya Kai masaukin sa,fridge ya bude dake gefen bed dinsa kwalaben beer ne masu tsadar gaske aciki ya fito da kwalba daya,ya cire marfin ya kafa a bakinsa sai da yaji bbu komai ya sauke haka ya tada kwalbar beer guda ukku da alamar ya Saba Sha sosai ,Amma har ynxu fuskar Nooriyah Yake gani agabansa.watsi da komai na Room din ya shigayi kafin ya xube Akan bed ya shiga surattai.”wlhi tallahi baki Isa ba bbu Namijin da kika Isa ki so sai farhaan Shagari,ni kadai xaki so da ni kadai xaki rayu,bbu namijin da ya Isa ya soki bayan ni!””…….Sai ga hawaye na xuba akan fuskarsa……..saloon din da ba samu xuwa kenan ba har washe gari basu sake haduwa da Junan su ba,kowa da abunda ke cin xuciyarsa .A bangaren Aliyu ya xabi akan ya rage mu’amala da Nooriyah hakan ne kadai xai samu ya rage Jin Abunda Yake ji akanta,duk da xuciyarsa ba karamin axabtuwa take da hakan ba,baisan shi so ba ruwansa da wannan ba .”sabida xuciya an halicce tane da soyayyar Mai kyautata mata ,Yana daukarka minti daya kacal kaji kana ra’ayin mutum,xai iya daukarka kwana daya kaji ka kamu da xaxxafar soyayya Amma Kuma xai daukeka tsayin Rayuwa kafin ka manta wannan soyayyar,cikin sati daya ba karamin axabtuwa Aliyu waxeer yyi ba yarda ya kauracewa nooriya ko abincinta ya daina ci ya daina xama a duk inda take xama,ko gaisuwarta ba ya amsawa cikin kwanakki kalilan nooriyah tayi wani irin Rama ta ban mamaki,
    Kasar London gaba daya ta fice Mata arai,
    Ko gaisuwarta Aliyu ya daina amsawa,Wanda Linda ta lura da haka, Abubuwan da take ko yamata ta rage fahimtar ta,akwai ranar da ta tsareta da tambayar meke damunta.”Hawaye kawai ke xuba a idonta ta kasa baiwa Linda Amsa,ganin haka yasa Linda ta fada Mata bara ta Bata hutu na sati daya kafin ta dawo natsuwarta,godia tayiwa Linda.tana kwance a dakinta kamar yarda ta Saba,
    Wayarta ta fara ring kurawa wayar ido tayi
    Har tagama ta katse sai ga wani Kiran ya Kara shigowa tasan shi da mugun naci a Kusan karo na biyar ya sake Kiran ta daga Amma batayi magana ba,ina kiranki a waya baxaki daga ba Wai mena maki Noor kinbi kin tsaneni??”Farhaan Shagari yyi Maganar cikin kwantar dakai,
    Hawaye na xubar Mata take fadin bakai na tsana ba Farhaan halinka ne na tsana duk kabi ka canja,ka juyamin baya haka ma Aliyu tun ranar da abun Nan ya faru na nemi farin cikin da nakeyi a gidan sa na rasa ,sai da nace kar ayi wannan Auren gashi yanxu tun baaje koina ba Kai da kanka kakeso ka lalata komai……….”ni na fada maka da bakina ina son Aliyu waxeer ne??”da xakayi min irin wannan mummunan fahimtar ,shuru yyi Yana sauke ajiyar xuciya maganganun ta kurum sun kwashe Rabin damuwar da Yake ciki. Haka Kuma yayi nadamar abunda yyiwa bestyn shi.ina sonki baxan iya rasaki ba wlhi.”Shuru Nooriyah tayi xuciyarta na bugawa da wani irin yanayi.ka kula da kanka ina son na kwanta kaina na ciwo.”Ta fada hawaye na xubar Mata tana mamakin Hawayen da basa gajia da xuba a idanunta tausayin farhaan takeji,Ashe da can baya haukan banxa takeyi akan son da take yiwa farhaan yanxu take ganin banbancin hakan da son da takeyi wa Aliyu waxeer.tana Jin lokacin da Farhaan ya fada Mata Kalmar ina sonki fiye da son da nake yiwa kaina……”Batace komai ba har ya kashe wayar,tana ta kwanciyarta a daki har Kusan karfe 2 na Rana kasancewar week End ne,a hankali ta Mike tsaye tana Jin jirin da takeji tun safe ,tana alakanta hakan da Rashin cin Abinci da baxata iya tuna Yaushene na karshe da taci Abincin ba,lemu da ruwa da bescuit sune Abun shanta Idan suka kare xata koma store ta kwaso wasu,fitowa tayi a falo tayi ido biyu dashi cikin kananun Kaya na Shan iska,
    Da mug a hannunsa batasan menene aciki ba.wani irin faduwa gabanta yyi shima dauke kansa yyi xuciyarsa na wani irin Rawa,tana dawo masa da sabon ciwon da ya kwana biyu da mantasa ,duk da xuciyarsa ta kasa cire Nooriyah daga ransa,
    Har aransa Yana Jin da gaske ba son Nooriyah yake ba kyawawan halayenta kawai ne yakeso ba ya Mata soyayyar Aure Yana sonta kamar yarda yakeson Batool waxeer.saurin mikewa tsaye yyi gamida daukar car key da alamar fita xaiyi tayi saurin shan gabansa hawaye na xubar Mata da rawar Murya take fadin”me nayi maka kabi ka tsane ni??”Kamo hannunsa tayi tana fadin ka manta Amintakar mu??”meyasa xaka biyewa shirmen farhaan ka yarda da maganganun sa kenan,ganinta kurum Yana ruguxa masa duk wani shiri da yyi axuciyarsa musamman da yaji tattausan hannunta cikin nasa,Xare hannunsa yyi cikin nata idanunsa na juyewa da wani irin yanayi,xamuyi magana wani lokacin inason xama ni kadai.”Ya fada da wata irin murya,ki shirya Mana Abincin dare ya fada Yana barinta tsaye a wajen Dan sanyi taji aranta ,ya fara saukowa kenan har xaice ta hada masu Abincin dare.
    Ranar farhaan ya kirasa yafi sau goma Amma Bai daga ba,
    Suna da exam’s baxai iya barin Cyprus ba da yaxo har kasar London ya basa hakuri ,shima abubuwa sunyi masa yawa ,Mami ta kirasa an Kai kudin Aurensa da ya ruguxa sauran hope dinsa,da ba Mami ce maihaifiyarsa ba waya Isa yyi masa wannan Karen tsaye da shisshigi acikin Rayuwarsa , sunyi waya da Aunty Nafisa wato yayarsa ita ta tabbatar masa da hakan,haka tace yakira xahra a waya tana ta korafi baya kiranta haka itama Idan ta Kira Bata samun sa,su basu sani ba ya dde da yin blocking dinta,Koda rantsuwa nawa xaiyiwa Mami akan xahra azeex Ali Yar hannuce baxata taba yarda ba,xata iya cewa sharri yayi Mata dama ya nuna bayason Auren tun farko
    Bbu Abunda Bata Sha na kayan maye ,,haka tasan maxa kala-kala a rayuwarta shi baxai iya Aurenta ba wlhi ,yadai gama karatun Ya dawo gida ya fuskanci Mami.Shima exam’s kawai Yake Amma hankalinsa gaba daya yayi gida Nigeria……..da murnarta ta shiga kitchen Bayan la’asar har sai da peter yyi mmkin hakan,Tuwon shinkafa Mai Rai da lafia tayi masa,Wanda kafin ta gama kamshi ya cika koina ,tana gamawa ta hada masa coconut juice Dan tasan Yana sonsa,Wanda ta lura Aliyu ya fison juice din gargajia fiyeda na kanti,Ana gabda sallar magrib ta jere komai a dinning Area,Koda ta koma dakinta Kusan 5 miss call ta gani duk daga farhaan,wanka ta shige .tana fitowa mayukkan ta kawai ta shafa masu sanyayyen kamshi ta nemi riga marar nauyi ta saka ta tada sallar magrib tana cikin sallar taji rurin motar Aliyu da alamar ya dawo.kusan bakwai da rabi ta fito daga room dinta cikin shigar doguwar rigar Abaya kalar maroon Mai ratsin Baki ajikinta sai veil din da tayi Rolling kanta dashi,Bata samesa a parlor ba tasan Yana bukatar wanka da gabatar da sallah,xamanta tayi a parlor gamida kunna tv.tana kallon program din da suke na tashar larabawa,sosai ta maida hankali suna fada cikin harshen turanci Wanda ta fahimta tana rubutawa a takarda ,Wanda Bata fahimta ba xata nunawa Linda tayi Mata bayani,tana cikin rubutun sai Gaya ya fito,yyi wanka har ya sauya kayan jikinsa.
    Wani irin sanyi nooryn taji lokacin da taci karo da kyakkyawar fuskarsa,shima a wurinsa hakan ne sai dai dukan su bbu Wanda ya nuna hakan a fili Kai tsaye dinning Area ya nufa,ita tayi serving dinsa da yarda ta lura ya natsu Yana cin Abinci tasan yamasa ddi,ke baxaki ci Abincin ba.”Yyi Maganar da sauti marar Amo.,,sai lokacin yyi Mata magana tun xamansa ,Bata kallesa ba take fadin sai xuwa anjima.sabida saurayinki na fushi dake shine xaki kashe kanki da yunwa.”wannan karon da Dan daga Murya yyi Maganar Kuma akwai wani yanayi na kishi acikin muryar tasa Wanda baisan Yana dashi ba,ta girgixa Kai tana fadin ba Saboda shi bane bana son naci Abinci banyi sallar ishaai ba ,farhaan yanata Kiran ka a waya kaki ka dauka “.dan Allah kayi hakuri cikin fushi yyi hakan.”kallonta kurum Yake da wani sabon bacin Rai acikin fuskarsa,tambayar kansa Yake Yaushe suka shirya suka Jone kansu wuri daya.”kenan shine mahaukaci sun ware kansu gefe suna faranta ran Junan su ,Jin yyi Abincin ya fice masa arai sabida kishi mikewa tsaye yyi
    Ta kallesa da mamaki
    Tana kallon Abincin da iyaka Rabi yaci ko coconut juice dinsa Bai shaba,bar Mata wurin yyi batareda ya Kara kallon inda take ba ,xuciyarta na bugawa take binsa da kallo.tayi tunani iya tunani Bata hango Kalmar da xa fada Dan ta Bata masa Rai ba,kodan tace sai tayi sallar ishaai xata ci Abinci shine yyi fushi??”har aranta Bata Jin Maganar farhaan xata Bata ransa lokaci daya…..Kusan 9 tayi fito wanka kenan Dan tana so ta kwanta da wuri yau ,taji ana knocking kofarta da sauri ta xura hijab tana basa umurnin ya shigo ,Kai tsaye ya sanyo kansa cikin room din da sallama a bakinsa cikin Italyn suite bakake da sukayi mugun karbarsa.yyi kyau har ya gaji kallonta yyi daga dama har kasa ,
    “Ki shirya yanxu xaki rakani wani wajen.”da haka ya juya Yabar kofar batareda ya Kara kallonta ba, murmushi ta shigayi ita daya Aliyu waxeer Yana da wani irin good personality da ba duk maxa suke dashi ba,
    Tukish gown ce a jikinta kalar mint green Wanda tayi Mata kyau sosai,itama kallon kanta ta shigayi a madubi turarrukan da take amfani dasu ta saka da Wanda Aunty Ramla waxeer ta Bata tace ta rika using dashi duk lokacin da xata kasance tareda Aliyu waxeer,tana fada Mata turaren Kusan 50k ta sayeshi Yana mallake xuciyar maxa,baa fi sati da sukayi waya ba ta Kara tambayarta turaren da tabata tana amfani dashi kuwa Yana da kyau.”kunya yasa ta fada Mata Yana da kyau,Alhalin Bata taba amfani dashi ba,tasan ba Auren gaske bane.”Amma kasancewar xata fita da Aliyu waxeer yasa taji tana son amfani da turaren ko kadan ne,maybe yace Yana son turaren ko ya yaba kwaliyyarta,Babu wani tunani ta bude Yar karamar kwalbar tana jujjuya sa a hannunta Wai wannan shine dubu hamsin?”kadan ta xuba a hannunta tabi koina ajikinta dashi har akan dogon wuyanta.cover shoe ta xura a kafanta Wanda sukayi shige da gown din jikinta,A hankali ta tako cikin parlorn Yana xaune cikin soofa yyi crossing leg’s dinsa Yana danna waya,kamshin turarenta yasa yaji tsikar jikinsa na wani irin tashi catching breath dinsa ya shigayi tamkar Mai Asmaa,wani irin tari ya shigayi da sauri Nooriyah ta nufi kitchen Dan dauko masa Bottle water,Mika masa tayi ya amsa sai da yyi rabi ya Mika Mata sauran dawowa tayi gabansa tana jera masa Sannu ,mikewa yyi ya nufi kofa turarenta na Kara saka sa cikin wani yanayi Bai taba Jin irin wannan kamshin ba rabonsa da Jin haka,tun ranar da aka daura Auren su.”meyasa yanxu xata saka,Jin yyi tamkar ya fasa fitar Amma yasan xaisha korafi wajen Khaleel waxeer,yau Yake birthday a gidan sa laylah waxeer ta hada masa Party,Abokan business dinsu duka ta gayyacesu.Haka Ammah ta matsa masa Akan laillai yaje da Nooriyah,A mota ya dubeta da idanunsa da suka fara canja kala,Yake fadin meyasa kika saka wannan turaren bana Jin ddin sa.da sauri ta kallesa gabanta na faduwa,,Amma Kuma Aunty Ramlah ta fada Mata turaren Yana da kyau,meyasa shi baiji ddin sa ba.”shuru kurum tayi masa tana ganin yarda Yake tukin motar duk baya cikin yanayi Mai ddi sai Tasha jinin jikinta tana da na sanin sakawa…….

    Waminal Hoob na kudi ne#500
    Account Details
    0004157137
    Jaiz Bank
    Asma’u Buhari Aliyu
    Katin Wayar MTN.ta wannan lambar #
    09060259200
    Shidar Biya ta wannan lambar
    08086207764#

    _Duk barauniyar da ta karanta min book Bata Biya ba ban yafeba.”_??
    [9/15, 6:11 PM] Asmy Mom Aydah??: *

  • Waminal Hoob 15

    Waminal Hoob 15

    _*Waminal Hoob*_ 15

    PAID BOOK
    _Asmy b Aliyu_

    Doguwar rigace a jikinta ta less kalar milk da ratsin lemon green ajikin less din sai mayafin kayan ,ko powder bbu akan kyakkyawar fuskarta dama Kuma haka Allah yyi ta bamai yawan son kyale-kyale bace.
    Sai mayukkan da take amfani dasu Wanda basu da surkin karawa fata haske ko kadan sai dai suna gyaran fata.kallonta kurum Yake har ta karaso cikin parlorn da murmushi a fuskarsa shima yyi kyau har ya gaji,salute yyi agabanta Yana fadin”Anya irin wannan kwaliyyah haka xan iya tuki kuwa.”Tayi murmushin da ya tsaya iya fatar bakinta ,tana Dan bude ido take fadin”ko mu fasa fitar,shima murmushin yyi Yana fadin mutafi kawai ganinki kurum Yana sakani nishadi,
    Kitchen ta nufa tana fadawa peter yau Linda baxata xo ba,sabida bakon da suke dashi ta fada masa ko Mai xaiyi masu na lunch …….peter ya bita da ido Yana mmkin kwaliyyar da tayi Kuma da Abokin ogansa xasu fita,sai yaji Yana Jin haushin kwaliyyar haka ta dayan bangare Yana taya ogan nasa kishi,
    Kallo ya bita dashi har ta fice daga kitchen din,dama Aliyu Yabar masa car key ko Yana bukatar fita wani wajen,tunda ya kanxo kasar ba bakon wajen sa bane ,sai da suka hau titi ya Kira Aliyu wanda ya fice tun safe daga gidan ,
    Tun jia da dare rabon Nooriyah dashi.mun fita yawo munata jiranka kaki dawowa…….”Kaida wa??”taji Aliyu ya fada ta cikin wayar,Farhaan ya bude ido Yana fadin nida Nooriyah mana.”Allah ya taimaka ya fada Yana kashe wayarsa ,acan bangaren Aliyu waxeer Jin yyi xuciyarsa na tafasa tamkar xata kone duka saboda kishi da tashin Hankali ,Idan shi farhaan baida hankali ita Nooriyah fa??”daukar Laifin duka yyi ya Dora akanta ,meya fada maka A wayar?”Nooriyah ta fada tana kallon farhaan dake tuki cike da nishadi,kin San halinsa miskili ne mefa xaice .Shuru Nooriyah tayi gabanta na faduwa,ta fara sanin Halayen Aliyu Dan xaman da sukayi ,ta tabbata Yana can Yana fushi.
    Amma ya xatayi bashi ya bada kofar hakan ba,kawar da tunaninsa tayi daga ranta karma yaxo ya hanata sukuni…….sai Bayan sallar la’asar suka dawo dauke da manyyan ledoji Wanda peter ne ya daukosu , xuwa cikin parlorn, farhaan ya juya kan motar Yana fada Mata sai magrib xai dawo,da yake Yana da family friends Wanda suke makaranta acikin London din,wata irin faduwa taji gabanta yyi da suka hada ido da Aliyu waxeer dake xaune cikin parlorn ya daura kafa daya kan daya yyi mugun hade Rai,ko sallamar ta Bai amsa ba shima peter Yana ganin yanayin ogansa yyi ta kansa,Jin tayi jikinta yyi mugun sanyi dakinta xata wuce taji ya daka mata wata irin tsawa gamida fixgota ,,daga gidan ubanwa kike??”tana ganin yarda idanunsa suka koma jaa hawaye suka wanke fuskarta cikin rawar Murya take fadin”Tare da farhaan muka fita.”Wannan karon turata yyi ya shiga ball da ledojin da peter ya dire a tsakiyyar parlorn dafe kansa yyi dake neman tarwatsewa sabida kishi da xafin xuciya,wani irin numfashi ya shiga ja Yana dafe da kirjinsa tamkar xai shede Mata a wurin cike da tashin Hankali ta karaso gabansa tana rikosa wani irin turata yyi da karfi yana fadin”don’t touch me.”
    Yana gargadinta da babbar Murya Bata taba ganin tashin Hankali irin wannan ba,da wani irin yanayi ya nufi dakin barcinsa Yana bugo kofar,itama da gudu ta nufi nata dakin.kan bed ta fada tana Fashewa da wani irin kuka……….”Shin Yaya Aliyu yakeso tayi ne,duka sun sakata a tsaka idan ta kaurace ma wannan ,wannan ya nuna ba haka ba
    Gaba daya taji duniar ta Mata xafi,ko Bayan magrib da farhaan ya dawo kiranta yyi a waya ta fada masa kanta na ciwo.da haka ta kashe wayar duka Bata Kara saka su a ido ba sai washe gari,
    Ta fito xataje Kitchen da safe ta samesu a parlorn suna break fast suna Hira dukan su ,su biyu din suka bita da ido cike da kulawa farhaan ke fadin”ciwon kan ne har yanxu ko sai munga likita,tana nufar kitchen take basa amsar ta samu sauqi,acikin kitchen ta tsaya tayi break fast dinta,sai ga farhaan din ya sameta a kitchen din,Hannu ya Kai xai taba goshinta tayi saurin janyewa tana hade Rai .ya wara ido Yana fadin xanji ya yanayin jikin naki Yake.”Nagode na samu sauqi tana gama Abunda take ta kallesa tana fadin bbu Abunda kake so xan koma daki,ya langabar da Kai Yana kallonta Yake fadin.”ke kurum nakeso ,xanje nayi wanka ta fita tana nufar kofa,Koda ta fito parlorn still Aliyu na xaune a parlorn ta kallesa ta dauke Kai da sassarfa ta nufi dakinta yabita da wani irin kallo.tana shiga dakin shima ya shigo dakin ya saka key jikin kofar xaro ido tayi tana kallonsa da mmki jingina Bayan sa yyi jikin kofar fuskarsa har ta Dan fada,shi yyi breaking silent din da fadin”Saboda saurayinki ya kawo maki xiyara ko Yar gaisuwar da nake samu kin watsar,na lura kin ma rainani da yawa ,yyi Maganar cikin kwantar da Murya Yana kallon fuskarta,tamkar jira take hawaye suka fara sauka kan fuskarta A hankali har lokacin Taki cewa komai .Juyawa yyi ya fice daga dakin,Kusan tare suka yini a gida da farhaan ,sosai farhaan din ya damu da Rashin fitowar Nooriyah a daki,
    Ya kalli Aliyu Yana fadin”Wai meke damun Nooriyah ne.??”Aliyu yyi tamkar bai jisa ba ,sai da farhaan ya Kara maimaitawa Yana kokarin danne bacin ransa,ni yaronta ne da xan Rika kula da yarda take” .ba kana da kafafuwa ba,kaje ka dubata Mana.”Yyi Maganar cikin Rashin walwala a fuskarsa,
    Tamkar jira farhaan yake a basa umurni ya nufi dakin nata da sassarfa da wani irin kallo Aliyu ke binsa dashi xuciyarsa na bugawa,tsaye yyi a kofar dakin sai da ya fara yin knocking kafin ya tura kofar dakin,
    Xaune ya sameta da waya a hannunta tana dannawa ,mamaki ya Kusan kasheta da ta gansa tsaye a tsakiyyar dakin daga ita sai Yar shimi da wani shegen skirt da Yake tsage har kan cinyoyinta rarumar hijab tayi ta saka,
    Da mamaki Yake kallonta a fusace ya fisge hijab din gamida jefar dashi kasa,da mugun shock take kallonsa ya fisgota ya matseta a bango Yana wani irin jifarta da mayen kallo ,xatayi magana ya Dora yatsan sa akan dan kyakkyawan bakinta da Yake mafarki a kullum,kokarin turesa take ya riketa jikinta har rawa Yake tamkar ba farhaan din da ta sani acan shekararun baya ba,Mai sonta Mai tausayinta haka Mai girmama soyayyar ta,
    “Meyasa Noor meyasa kika canja meyasa kike guduna.”meyasa kike xama da hijab aduk lokacin da muka hadu,shi Aliyun haka kike masa.”Ya fada da tsawa cike da matsanacin kishi a muryarsa,sai ga hawaye sun fara ambaliya akan fuskarta cikin rawar Murya take fadin”Farhaan ina da Aure kana so tsinuwar Allah ta hau kaina,, na tambayeka jikina kakeso koni kakeso.”Wata Daria farhaan yyi Yana fadin duka komai naki ina so Noor kina bani haushi .Aduk lokocin da muka hadu saiki xurma hijab,tamkar kinga mugun Abu.”Auren da kike magana Kuma ai contract ne kin manta.”bbu Aure contract a Rayuwar mu ,ko contract ne ya kamata mu kiyaye dokokin dake cikin sa,kirjinta ya kafe da ido Wanda yyi balain daukar hankalinsa dama haka take da manyyan na Fulani,gaskiyya xaya more…turasa tayi da karfi ta saka hijab dinta tabar masa room din duka tana Fashewa da kukan bakin ciki duk taji ta tsani kanta ta tsani wannan Auren tantamar ma soyayyar da farhaan ya Rika nuna Mata a baya take ,wannan sabon farhaan ne Mai kokarin karya dokar Allah Yana kokarin Kai hannunsa jikinta,
    Bbu kowa a parlorn acikin garding ta wuce ta hada Kai da gwiwa tana shessheka Jin tayi ta fara tsanar farhaan,ganin irin kallon da Yake bin jikinta dashi da kalar idanun da Bata taba gani ya kalleta dasu ba,ta window din dakinsa yake hangota .Kura Mata ido kurum yyi tamkar Mai son gano wani Abu acikin fuskarta,
    Ya lura tunda farhaan yaxo farin cikin ta ya ragu,wata xuciyar tayi saurin kwabarsa da fadin Kai Kuma ina ruwanka.”ae sunfi kusa,karar bude kofa yaji ya kalli farhaan da ya fara hada kayansa da mamaki Yake fadin”ina Kuma xaka tafi??”hotel xanje na kama na lura gaba daya Nooriyah ta canja min koma dai menene xan shawo kan matsalar Yana gama hada kayansa ,
    Ya kalli Aliyu waxeer Yana fadin xan tafi da motarka,muyi waya da haka Yabar dakin da sassarfa.xuciyarsa da Yake Jin tayi nauyi tun xuwan farhaan yaji ta fara sauka tamkar an axa masa wani katon dutse,sai da yaga fitar motar farhaan ya nufi cikin garding din.”Yau a matsayin Aboki naxo maki ba matsayin miji ba ,shin meye damuwarki Yar baka.?””kina tareda Wanda ke maki soyayyar tsakani da Allah sai Kuma rikici da damuwa.”Wannan karon ya fada da rauni a muryarsa,ta dago da jajjayen idanunta tana kallonsa,cikin Murya Mai rauni take fadin”ina so nayi maka tambaya Dan Allah.”Idan kana son mutum tsakani da Allah xaka so shine.”ko Dan wani Abu nasa,juya tambayarta ya shigayi aransa Jin yyi tamkar akan shi tayi tambayar,Farin Areefa Mansoor da kasancewar ta kyakkyawa shine Abunda ya fara fisgarsa akanta,daga wannan baxai iya cewa komai. Ba”meyasa xakiyi min wannan tambayar,ka Amsani Dan Allah.”Yana girgixa Kai Yana fadin”Ban San komai ba a wannan fannin gaskiyya,na dauka Idan kana son wani Abu da Allah ya halicce mutum dashi ajikinsa shine soyayyar kawai.”kallonsa take da mugun mamaki,
    Kenan ko xaa Dora masa wuka Bai masan meye so ba.”Sai dai wata xuciyar tana fada Mata karya Aliyu yyi Mata, murmushi kurum tayi masa xatayi magana wayarsa ta fara ring,barin wurin yyi ya tsaya can gefe Yana Amsa wayar……….Saukarta kenan a filin jirgi shiya je daukarta bbu wani Bata lokaci suka nufi hotel din da ya kama masu,suna shiga room din da ya kama masu ta wani rungumesa tana fadin”I miss you,wanka Tayi taci Abinci ta saka wasu tsinannun nyt wears Wanda su da bbu duka daya ,ta kalli farhaan dake kwance kan bed yyi xurfi cikin tunaninsa,ta fada kansa tana shafa gashin kirjinsa take fadin”Besty Wai lafiar ka kalau kuwa ,tunda ka daukoni a Air port Naga baka cikin farin ciki.ko kunyi fada da mutunen ka ne??”Bai Bata damar magana ba ya jawota jikinsa ya hade bakinsa da nata,
    A daren sun faranta ran Junan su ,haka yasa ya Dan manta da bacin ran da Nooriyah ta dasa masa ,Tun da safe wayar Aliyu waxeer ta tashe sa barci,cikin barci ya daga wayar
    “A wane hotel ka sauka ??”jin yyi barcin dake cikin idanunsa na rugujewa a hankali,
    Jin tambayar da Aliyu ya jefo masa kallon Areefa yyi wacce ke kwance cikin jikinsa tana sharar barci.kaga ni barci nakeyi kabari xuwa anjima Idan na tashi xan kiraka.”da mamaki Aliyu ke fadin
    Barcin da kakeyi shi xai Hana ka fadamin masaukin da ka sauka.”muyi magana xuwa anjima plz Besty.”kashe wayar Aliyu yyi Yana mamakin sabbin Halayen farhaan Wanda Bai yarda dasu ba,shima sharesa yyi ya cigaba da sabgoginsa ,itama Nooriyah tun daga ranar Bata Kara ganin farhaan ba. Haka bbu wayarsa bbu dalilinsa ,itama Bata ga Abunda xai saka ta Kara kiransa ba.haka Linda ta cigaba da xuwa wajenta tana maida hankali sosai ,
    Mu’amalarta da Aliyu Kuma girmamasa take sosai da wata irin soyayyar sa dake cin xuciyarta a hankali sai da tana kokarin kwatanta boye hakan agabansa,Saboda kare mutuncin ta da martabarta na Diya macce.sai da Areefa Mansoor ta kwana ukku kasar London suna faranta ran Junan su, itada farhaan sa’anan tayi Shirin komawa Nigeria dama ba Egypt xata koma ba,sun samu hutu.Ranar da ta tafi sai ga farhaan ya Kai masu xiyara a yammacin da ya cika kwana 4 da barin gidan,peter ne ya bude masa kofa,Aliyu Yana cikin soofa din dake xagaye da parlorn Yana turawa Baffa waxeer sako ta email dinsa na cigaban da companyn waxeer ya samu Bayan dawowarsa,Haka kudaden da suka Bata yabi diddigi ya gane ta hanyar da suka salwanta,Laylah waxeer ta account dinta kudin ke shiga Wanda ko Khalil waxeer baida labarin hakan,da Yake duk a karkashin wannan company suke aeki itada mijinta wato (Waxeer motors)duk da ba company daya bane,akwai na kayan sakawa ,,company da ake sarrafa abincin Nigeria , Ana sarrafa wasu ana shigowa da wasu ….. Khalil waxeer shima acikin London din Yake Rayuwarsa sabida company waxeer dake Nan,A tsakanin gidan Khalil da gidan Aliyu ba wani nisa ne dashi ba ko a kafa kana iya takawa ka tafi….sanye take cikin riga da skirt na atamfa tayi Rolling kanta da veill Wanda yyi shige da kayan fitowarta kenan daga kitchen rike da cup glass Mai dauke da sanyayyen lemun inibi acikin sa.dai-dai lokacin da Farhaan ya sanyo Kai cikin parlorn suka hada ido nooriyah tayi saurin dauke nata idon ,ta nufi Aliyu waxeer .dama Kuma Shirin fita suke xai sauketa a wajen saloon,ta ajey masa Akan Dan madaidaicin center table gamida jansa gabansa,dakinta ta nufa da sassarfa batareda tasan Allah yayi halittar farhaan Shagari a wajen ba,Aliyu ya daga Kai ya kallesa
    Ya maida kansa kan aikinsa Yana fadin Ashe kana cikin kasar Nan har yanxu.”Farhaan ya xauna Yana kallonsa ya hade Rai Yana fadin,wannan wane irin tambayace tun ranar ka Kara nemana,da mutuwa nayi ae baxa ku sani ba,
    Ayi tattaki akawowa mutum xiyara Amma sai wulakancin Yake fuskanta,sosai farhaan ke fada Yana hura hanci Aliyu waxeer ya tabe Baki Yana fadin”Ae bani ka kawowa xiyarar ba da xaka cikamin kunne da ihu matsalarka ce wannan,yanxu ma Shirin fita muke da baxaka samemu ba,
    “Xuwa ina kenan?””
    Saloon xan kaita ,tunda ka doramin nauyi.Ae tun da gani na hutar dakai ni xan kaita na daukota,wani irin faduwa gaban Aliyu waxeer yyi ya kallesa da sauri Yana fadin”ka kaita ina??Da mamaki farhaan ke fadin saloon din mana,
    Shuru Aliyu yyi Yana kallon farhaan din,
    Dai-dai lokacin da Nooriyah ta fito dauke da karamar handbag a hannunta.

    Littafin waminal Hoob na kudi ne#500
    Account Details
    0004157137
    Jaiz Bank
    Asma’u Buhari Aliyu
    Katin wayar MTN.ta wannan lambar#
    09060259200
    Shaidar Biya ta wannan lambar
    08086207764#

    Thank yhu#
    [9/15, 6:11 PM] Asmy Mom Aydah??: _

  • Waminal Hoob 8

    Waminal Hoob 8

    Asmy Mom Aydah❤️: *_Waminal Hoob_* 8….

     

    PAID BOOK

    Free page.

     

    _Asmy b Aliyu_

     

    Yau laraba ta kasan ce yauce Ranar da xaa saka Nooriyah lalle itada Aliyu a kaidar xuri’ar waxeer amarya da Ango xasu saka fararen kayan,A  samu fili babba ayi decorating din wajen,a rubuta sunan Amarya da Ango,dangi amarya da na Ango xasu xo daya Bayan daya su shafawa Amarya lalle hakama Ango a hannuwa da kafafuwa ,hadin lallen xaayi na musamman xaa xuba turarruka aciki.idan angama familyn Ango xasu xaunar da Amarya ta buda babban mayafinta su rika xuba mata kyauttukka,da xarar an gama xaa kawo Abinci Wanda uwar Ango xata dafa da hannunta Ango ya ciyar da Amaryarsa,ana daukarsu pics ana yimasu vedio ,da angama wannan daya daga cikin dangin Amarya xasu tsaya tsakkiyar fili da Amarya,shima Ango yaxo ya tsaya sai ta hada hannayensu wuri daya tace ga amanar Yar uwarta nan tabasa ,yay mata Alkawarin sai mutuwa xata rabasu .shima mahaifiyarsa ko Yar uwar mahaifinsa ,

    Xatace sun dau Alkwarin bbu Abunda xai rabasu sai mutuwa….idan Angama wannan kanwar mahaifin Ango xata dauki amarya na kwana daya,tayi mata wanka da Ruwan lalle,

    Ta Kara fahimtar halinta shin yaronsu ya dace da mata ko akasin haka,sauran Abunda xai biyo baya event’s ne idan kana da Ra’ayi xaka iyayi….sai Kuma Ranar daurin Aure da an daura aure wakilin Ango xaa kawo masa Amarya ya fiddo da sarkar xinari ya baiwa Ango ya sakawa Amaryarsa  ,shi kenan ta xama daya daga cikin xuri’ar waxeer ,Wanda in har aka auri macce acikin xuri’ar waxeer xaa ganta da wannan sarkar ta xinari ,duk hidimar da xaayi baa canja sarka itace dai xaa gani a wuyanta,

    Sai idan acikin gidanta tayi ra’ayin canja wata Dan yiwa mijinta kwaliyya,amma in har xaa yi wani taro acikin xuri’ar waxeer dole ta saka sarkar xuri’ar waxeer ta Aure….

    A gidan yayan mahaifinsa xaayi event din saka lalle,wato gidan kabeer waxeer ,Wanda shi kadai ya rage masu namiji sauran matane su biyu ,hajia Ramla waxeer sai Fatima waxeer wacce itace auta Kuma dukan su suna da Aure da ya’yah Ramla a sokoto take Auren wani hamshakin Mai kudi,sai Fatima dake Aure a zamfara gusau itama dai babban Dan siyasa ne take Aure,Wanda idan suka xo basa sauka gidan yayunsu maxa,gidan iyayensu suke  budewa su shige suda Yayansu,sai dai kawai suje su  gaisa da yayunsu. Wanda kusan iri dayane da na Yaran,Babu Abunda bbu ciki na Rayuwa….

    “Ya kamata yanxu ace Amarya ta iso hajia Amina ta fada wacce itace matar kabeer waxeer  ,itama tana da manyyan ya’ya maxa da mata Wanda matan sunfi yawa.”ummi toh ki Kira Ammah a waya Mana.”daya daga cikin yaranta ta fada Mai suna Fauxiyya itama baa dde da aurenta ba har ga albarkar ciki,

    Hajia Amina tayi dialling lambar Ammah,bugu daya ta dauka,na jiku shiru ne Ammah lafia kuwa??”gamu nan xuwa kin San halin yaronki shiya Bata Mana lokaci,acan bangaren Ammah kuwa wata kawarta ta Kira agefe hajia saudah tace mata taje a matsayin yayar uwar Amarya ,da mamaki hajia sauda ke fadin ita Amaryar Bata da dangine??”cikin sanyi murya Ammah ke fadin marainiyya ce saudah xan warware maki komai idan aka gama,sauke ajiyar xuciya hajia sauda tayi ita ta fita da Amarya har xuwa compound din gidan  katuwar jeep dake fake a wajen  ,ita ta budewa Amarya ta xauna itama ta xagaya ta xauna driver ya jasu,Kusan gidajen manne suke da juna,

    Mutane har sun fara taruwa sai kade-kade akeyi ,ganin mota na shigowa Yammatan gidan suka nufi motar da gudu suna shewa kowa so Yake yaga matar Aliyu waxeer……Ummi ce ta bude bangaren da Amaryar take ta fito daita Ahankali ,nan suka gaisa da hajia saudah wacce ummi ba kowa ta sani ba ko acikin  kawayen Ammah ,Dan haka Bata shaidata ba.Su suka rika Amarya har xuwa maxauninta,Bata Dade da xama ba saiga Aunty’s din Aliyu waxeer shima sun rakosa,wato kannen mahaifinsa.shima yana sanye cikin shadda fara Kal ,Amma kallo daya xakayi masa kasan baya farin ciki da wannan Auren sai yanxu yake da ya sanin  biyewa Besty yasan Yarda Auren gidan waxeer yake.Aunty Ramla ce ta bude fuskar Amarya sai fadin take “Masha Allah  Allahumma barik Alaekhi” .Aliyu ka iya xaben macce har taso tafi matar Khalil kyau fari kawai xata gwada mata.daria akasa Banda Aliyu da ya wani  dakune fuska,

    Nan akaxo daya Bayan  daya ana shafa masu lalle,

    Laylah waxeer ce karshe,Aliyu yana kallon yarda take wani babbata rai da alamar tana taya kawarta kishi,murmushi kurum yyi yana ganin irin kallon da take bin Nooriyah dashi,Bayan Angama saka lalle ta xauna ta buda mayafinta aka rika saka mata kyauttuka harda kyautar mota,Nasir waxeer ya Bata Wanda shine babban da awajen kabeer waxeer.laylah bakin ciki tamkar xai kasheta ,itama A aurenta kyautar mota yayi mata,russunawa Aliyu yayi dai-dai kunnenta Yake fadin”karma ki fara Jin ddi duka amshe gifts din nan xanyi,ae fake marriage ne.murmushi Nooriyah tayi tana fadin ,Nima basa gabana Mr.Aliyu waxeer inhar xan rayu tare da Farhaan Dina acikin Aminci.”na yafe wannan kyalkyalin”.daure fuska yyi yana fadin xan Aure ki Kuma kike fadin wani naki. A gabana “Ya fada da wata irin murya da mamaki take kallonsa,sai ya dauke kansa,haka aka cigaba da hidimar saka lalle har akaxo Wurin da Ango xai baiwa Amaryarsa Abinci abaki.dakyar ta yarda yabata sabida kunya,haka aka rika daukarsu pics,wasu suna ganin kunyarta ta burgesu ,wasu Kuma akasin haka.suna ganin Rashin wayewa ce kurum sai Kusan 2 Aunty Ramlat ta tafi daita bangaren da suka sauka,Ruwan wanka ta hada mata masu hadin turarruka na musamman,da Ruwan lalle aciki tayi wanka ,tana fitowa daga wanka tana tsane jikinta da towel sai ga Aunty Ramlat ta shigo dauke da katon tray ta aje a tsakiyyar carpet ,wata irin kunya ta rufe Nooriyah ganin yarda Aunty Ramlat ke kallonta tana sakin wani irin blushing ita har ga Allah taji tana kaunar Nooriyah tun farkon ganinta,Bata San meyasa take Jin kaunar yarinyyar kamar Aliyu waxeer ba.tana son macce Mai natsuwa da kunya ,sabanin matar Khalil waxeer Wanda idonta ya gama budewa da wayewa.tana ji ajikinta Aliyu yyi dacen macce ta gari a wannan bangaren,wasu irin mayyuka Aunty Ramlat ta turawa Nooriyah agabanta tace ta shafa ,bbu musu ta rika dibar mayukkan tana shafawa ,sukan su  wani irin sirrukkan kamshine acikin su.Bayan tagama Aunty Ramlat ta Mika mata wata plain gown kalar sararin samaniya ,juyawa tayi ta nufi toilet da sauri Aunty Ramlat ta dakatar daita.ki saka abunki Anan Nooriyah Sam -sam ban yarda ki daukeni matsayin suruka ba.kin ji kou.”daga yau ni kawarki ce kuma Auntyn ki ,xaki iya fada min dukkan damuwarki karki ji komai keda Aliyu duka ya’yana ne ,ko acikin ya’yan Yan uwana Aliyu shine Fav Dina …..Kaunar da nake masa Mai girmace plz kibasa dukkan farin cikin da Yake nema,kinyi dace sosai da samun miji irin Aliyu watarana da bakin ki xaki rika yaba kyawawan Halayen Aliyu believe me noory.”Aunty Ramlat ta fada tana kallonta da murmushi a fuskarta,

    Jikin Nooriyah lokaci daya yayi sanyi ,ta rasa mexata fara tunani akai tana ganin yarda mutanen nan suka dauki Auren Aliyu waxeer da muhimmanci fiye da komai ,Ranar da Kuma Auren su da Aliyu waxeer ya kare batasan ya xasuji ba”.kenan xasu rusa dukkan farin cikin su,musamman mahaifiyarsa xasu koma gefe Kuma su cigaba da Rayuwa.juyawa tayi ta koma toilet Aunty Ramlat na kwala mata Kira Bata saurareta ba,

    Kiran Aliyu waxeer ne ya shigo a wayar Aunty Ramlat,juyawa tayi tabar room din tana daga wayar lokaci daya tana fadin my fav….”

     

    ASMY#❤️

    Team#NooryAli forever#

  • Waminal Hoob 6

    Waminal Hoob 6

    Waminal Hoob_* 6…..

    PAID BOOK
    Free page.

    _Asmy b Aliyu_

    Murja ta hada mata ruwan wanka ta fito ta samu Nooriyah duk ta takure kanta waje daya,murmushi murja tayi tana fadin ki saki jikin ki Dan Allah.”daga kai kurum Nooriyah tayi ,na tayaki wanke kanki ko xaki iya??murja ta fada tana kallon Nooriyah, kitayani bana iya wanke kaina ni daya yana dayawa……tare suka nufi toilet dakyar Nooriyah ta rage kayan jikinta murja ta fiddo mata da sabon towel ta daura ,ganin yawan kan Nooriyah sai da yaso ya firgita murja tana mmki tana karawa duk wannan tulin gashin na mutum dayane,ba laifi bayada wani datti sosai sabida duk Karshen wata farhaan na bata kudin saloon tana shiga wajen wata makociyarsu inya mura tana wanke mata.rabi kawai suka kai murja taji ta gaji ,dakyar suka samu aka gama.murja na xufa tana fadin”kibarsa haka xanyiwa Hajia magana kawai akaiki kiyi saloon.
    Wanka murja tabarta tanayi,tana fita batool ta shigo dauke da kaya cikin leda.”Aunty murja Ammah bakuwa tayine??”mekika gani Autar Ammah.”nagan Ku Anan dakin inhar Ammah ta sa aka kawo bako anan wajen to nasan special ne,ina bakuwar batool ta fada tana bin dakin da kallo.Amsar kayan Murja tayi tana fadin”tana wanka ko xaki jirata.noo xamu fita tareda Aysha waxeer idan na dawo anjima ma gaisa da haka batool tabar dakin da sauri,Alwallah Nooriyah ta dauro Dan ta lura ana gabda sallar xuhur,da taimakon Murja Nooriyah ta busar da kanta da drayer……ga kayanan ki saka inji Hajia bara naje na hado maki Abinci,da haka murja ta nufi kofa.Dan ajiyar xuciya Nooriyah ta sauke farhaan ya sasu a matsala,dakin ta shiga karewa kallo komai na cikin dakin blue black ne har pentin dakin.bbu komai acikin room din sai ltalyn bed da mirror dressing dinsa,sai kuma wardrob dinsa mai gida biyu,da kuma doguwar soofa itama kalar blue black…..dakin yyi matukar yin kyau,ledar da Murja ta ajey mata ta jawo xuwa gabanta tun Kafin ta buda ledar taji tana wani kamshi na musamman,buda ledar tayi ta fidda Turkish Abaya kalar brown,masu wasu irin duwatsu gaban rigar sai Dan karamin mayafin abayar.sai bran da pant suma sabbi dal da kuma ,agurguje ta shiga saka kayan.tana cikin saka kayan aka wani bugu kofar ,ido biyu tayi dashi wani irin ihu ta saki gamida xubewa akasa tana wani kare kirjinta ,shima da sauri ya juya har yana buga kansa ga kofa.wani irin bacin rai ya saukarwa Nooriyah shi wannan mutunen bayada hankali xaya shigowa mutane a haka.”kuma ai lokacin haduwarsu baiyi ba,da sauri ta rarumi hijab dinta ta saka.juyawa yyi yana wani hade rai,gamida shigowa cikin dakin duka.karki bada hanyar da Ammah xata gano bbu auren soyayya acikin auren mu,haka karki fadawa kowa yarda Auren nan yake.”kibarsa mu ukku kurum yarda muka tsarasa ,juyawa yyi ya nufi kofa batareda ya kara kallon inda taketa ba…….da kallo tabisa ,
    Tsaki tayi ta cire hijab din gamida saka doguwar rigar tamkar Dan jikinta akayi rigar tayi kyau sosai acikin kayan.da sallama murja ta shigo dakin dauke da katon tray,mai dauke da cima kala-kala da sauri Nooriyyah ta karbi tray din tana yimata sannu.kallon ta Murja tayi tana fadin”kinga shigowar babana kuwa?da ido Nooriyah tabita Dan bata fahimci xancenta ba,Dan murmushi murja tayi tana fadin Aliyu nake nufi ya shigo .”Ya fadamin Bayaso Hajia tasan ya shigo,,ya shigo har ya tafi.Nooriyah ta fada tana komawa gefen gado ta xauna,ya kuma kin xauna sauko kici abinci.bara na baki waje ,xan dawo anjima murja ta fada tana barin dakin.samun kanta tayi da fadin”nagode Aunty……….murmushi kurum murja tayi gamida ficewa daga dakin duka,
    Farar shinkafa ce da stew ,sai dayar cooler mai daukeda farfeson naman Rago,sai katon kwalin five alive.kadan taci abincin kasancewar ba mutum CE mai cin abinci sosai ba,tana idar da sallar axxahar barci ya dauketa akan carpet ba ita ta tashi farkawa ba sai kusan 5….Ahankali ta fara mika ta soma bude idonta tana karanto Addu’ar barci,ido biyu tayi dashi wani irin faduwar gaba ta tsinci kanta dashi,shima kusan hakane awajensa.baisan meyasa duk lokacin da suka hadu daita ba,xuciyarsa xata fara bugawa .baxata daina ba har sai lokacin da yabar wurinta,wani irin irritating look yake watsa mata fuska a daure yake fadin kin watse baki kina barci ,kinji sanyi A/c an samu banxa na baki minti biyar ki shirya farhaan na nemanki .”Ya fada yana bar mata dakin cikin takunsa na kasaita haushi da takaici suka cika xuciyarta lokaci daya,tambayar kanta take tsawon Mintuna nawa yayi yana kallonta ,tsaki tayi ta tsani ganin wannan fuskar tashi mai kama da kosai,haka kurum taji jikinta duka na kamshin turarensa,da dakin ma gaba daya.toilet ta shige ta dauro alwallar la’asar ,
    Sai da tayi sallarta cikin natsuwa,tana linka sallayar murja ta turo kofar da sallama.Babana yana ta jirafa .”hijab dinta take kokarin sakawa kalar Ash colour Wanda ya Dan fara tsufa ,da sauri Murja ta karaso gabanta tana fadin”ki Dora mayafin Asama mana,ina ganin xaifi kyau………..wani iri Nooriyah taji aranta karo na farko da xata tsaya a haka gaban mutane ,ko acikin gidan kawu kullum tana sanye da hijab ko barci xatayi.
    Da sauri tabi bayan murja,ta godewa Allah da ya kawota da batasan hanyar da xatabi ta koma wurin Ammah ba.
    A falon Ammah suka samu Aliyu tsaye yana kaida kawo ,Ammah na xaune cikin soofas.da sauri Aliyu ya karaso gabanta yana fadin”kin kyauta shine kika shanya Aliyu waxeer har haka???”Ya fada sounding so cwt yana yimata wani irin kallo,dauke kai tayi ta isa gaban Ammah ta durkusa tana gaisheda Ammah.da murmushi Ammah ke fadin kin tashi barci jewel?”sannu da tashi ,cike da jin kunya Nooriyah ta daga kai.
    Aliyu yana son magana dake kina da lokaci ko sai gobe.”cike da takaici Aliyu waxeer ke kallon Ammah.jira yake yaji me Nooriyah din xata fada sai yaji tayi shuru tana wasa da yatsun hannunta,Aliyu kuje karka wahalar daita da yawa.Rabin awa na baka ka dawomin da ya’ta .”Ammah ta fada tana barin su A falo.wani bacin rai ya sauka a xuciyar Aliyu waxeer me Ammah ke nufi??”me ma xai kaisa yawo da wannan bakar Yarinyyar………tare suka jera suka fice daga cikin parlon suna fita ya nufi part dinsa ita kawai binsa take xuciyarta na bugawa ,batasan meyasa duk lokacin da ta hadu da Aliyu waxeer ba ,xuciyanta tana hanata hutawa daga bugawa.aduk lokacin da suka hadu itada Aliyu waxeer ,batasan meyasa ba.ko farhaan da suke soyayyah batajin bugawar xuciyarta idan suka hadu,sauran kadan tasha kasa wajen kallon haduwar parlon Aliyu waxeer ,idan baxatayi karyaba wannan parlon har yafi na mahaifiyarsa kyau da tsaruwa sai kace akasar turai Dan kyau ,komai na cikin parlon Fari ne Sol”har ta da fentin parlon Fari ne wato Fari shi daine Fav din Aliyu waxeer. Farhaan ne yayi saurin tarota a hannunsa,wara ido tayi tana kallon farhaan shagari cikin kananun kayan da sukayi matuqar karbarsa,
    Da sauri Aliyu ya juya xuciyarsa na tsananin bugawa bai kara koda second 1 a wurin ba ya nufi hanyar stair’s da ido farhaan yabisa yana sakin murmushi……Da sauri Nooriyah ta kwace kanta a hannun farhaan ,harde hannunsa yyi akan kirji yana binta da wani sanyayen kallo.
    Shigen ba karamin kyau yyi mata ba,lumshe ido yyi ya kara budewa akanta.ta Dan turo baki tana fadin baka fadamin xaka xoba.ko awaya.”nima Ramawa nayi na shanyaka ,meyasa xaka aikosa kasan bayada kirki.”ta karasa maganar tana wani hade rai ,hade hannu yyi alamar yana Neman Afuwa xama sukayi acikin fararen soofas din da suka kayata parlon na Aliyu,ya dafe kansa dake yimasa ciwo tun Daren jia sabida maminsa tayi Rantsuwa ayau xaibar kasar nan .”Ba haka yaso ba sai yaga Auren Noory dinsa da Aliyu ya tabbata ,jirgin karfe 6 xanbi xuwa cyprus……. Wani mummunan faduwa gabanta yyi har hawaye sun cika idonta cikin rawar murya take fadin”Baxa ka bari sai an daura auren ba??”ta fada hawaye na sauka a fuskarta ,kuka kuma noory??”bafa mutuwa zanyi ba,xan dawo nan da watanni shidda Kafin mu idar da gamawa gabaki daya,ina jin tsoron duniar nan Farhaan .shigowarka cikin Rayuwata Alkhairi ne Farhaan ina addu’a Allah yasa wannan Auren kar yaxamo silar tarwatsa farin cikin mu,ina sonka farhaan!!”Dan Allah karka manta dani ko na sakan dayane cikin rayuwarka,
    “Waye kika taba ganin ya manta da xuciyarsa kin manta ke xuciya ta CE gabaki dayanta ,ki kwantar da hankalin ki bbu abunda xai faru ,kuma ae xamu rika waya wannan karon harda vedio Call .xaki rika ganina nima na ganki…….”haka Farhaan yyi xaune sunata hira,
    Ga Aliyu yaki fitowa shi xai saukesa a airport ,
    Acan kuma bangaren Aliyu waxeer wanka ya shige yana sakarwa kansa shower,wani irin numfashi yake saukewa xuciyarsa na bugawa da karfi tamkar xatabar kirjinsa ,da ya runtse idonsa Nooriyah yake hangowa tana sakarwa farhaan sanyayyen murmushi baisan meyasa hakan ke hurting dinsa ba,meke damunka ne da lamarin Yarinyyar nan Aliyu waxeer??? Xuciyarsa ta fada masa tsaki yaja a karo na farko yana basar da tunanin Nooriyah aransa,koda ya gama wanka ransa a bace yake,agurguje ya shirya cikin blue din jeans,da farar shirt mai dogon hannu sosai yyi kyau acikin shigen ,turarukkansa ya saka masu tsadar gaske,
    Agaban mirror dressing ya tsaya yana gyara sumar kansa tamkar ta macce wadda ta taru sosai akansa,wani irin faduwa gabanta ya shigayi da sauri da sauri kamshin turarensa ya sanar mata da xuwansa,Kafin takunsa ya fara ansa amo acikin kunnuwanta,Runtse ido tayi gagam tamkar mai Asmaa ta rika Jan numfashi tana dafe da xuciyarta dake tsananin bugawa ,da sauri farhaan ke tambayarta lfy???dai-dai isowar Aliyu waxeer cikin parlon bude ido tayi suka sauka cikin nasa,
    Da sauri ya jaye nasa idon ya wani hade rai.
    Ya maida idonsa cikin na farhaan yake fadin”baka duba tym ne besty.?mikewa yyi hannunsa xube cikin aljihun wandonsa ,yana bin Nooriyah da wani irin kallo itama kallonsa take idonta na cika da hawaye.mika mata hannun sa na dama yyi Ahankali ta samu kanta da Dora hannunta cikin nasa,lokaci daya Aliyu yabi hannayen da kallo xuciyarsa na bugawa.,,mikar daita yyi tsaye gamida jawota jikinsa duka abunda baitaba yiba,tun haduwarsu.suna hada ido da Aliyu gabanta yyi wani irin faduwa ganin yarda idonsa ya koma mata kalar red,dauke kanta tayi ta mayar kan farhaan .Hannayensa yasa ya rike kugunta ,cikin tsawa Aliyu waxeer ke fadin”meye Haka farhaan???”shi kansa baisan meyake fada ba ,baisan lokacin da maganar ya fito ba.da sauri farhaan ya saki Nooriyah yana shafa kansa yake kallon Aliyu da wani irin yanayi………….Idan Ammah ko wani ya gani fa??shirin mu xai wargaje duka.Ka sallameta pls mutafi,Aliyu ya fada yana barin wajen.dafe da kirjinsa dake Neman tarwatsewa ,Ahankali farhaan ya rika daga mata hannu .hawaye taji suna cika idonta, xubewa tayi daya daga cikin soofas din parlon Aliyu.sosai hawaye ke gudu akan fuskarta,A mota ma Aliyu kin kula farhaan yyi baisan meyasa yake jin haushinsa ba.murmushi Farhaan yyi yana riko hannunsa yake fadin fushi kayi ne besty?”
    Nan ma Aliyu yaki kulasa har lokacin yaki saukowa,koda suka isa a air port akwai sauran mintuna xaman su sukayi a mota farhaan na Dan Jan Aliyu da hira kafin a fara kiran sunaye,,
    Da an daura aure wani satin xan koma London ,,da sauri farhaan Ya kallesa yana fadin da wuri har haka???toh ya xakayi da nooriyah wani kallo Aliyu yayiwa farhaan yana fadin”tare aka haifemu da xata riqa bina duk inda na shiga bakin aikina xan koma ,ga kuma wasu kudi da suka bata a companyn waxeer dake kasar London ga kuma aikina.”Yana aiki da airport din (LHR)London Heathrow airport, duk da yanzu wani Dan siyasa dake kasar ta London ,ya dauki Aliyu waxeer aiki a karka shin sa.abunda yasa ya Dan kwana biyu a Nigeria shima baya kasar Yana kasar Indian,
    Ajiyar zuciya farhaan ya sauke ,xaiyi magana Aliyu ya daga masa hannu yana fadin”xamuyi magana besty,kusan tare suka fito daga motar side hug farhaan yabasa,
    Daga kai Aliyu yyi yana fadin”ka kula da kanka……..sai da yaga shigar Farhaan acikin jirgi shima ya juya ya nufi motarsa.cikin gari ya shiga bai dawo gida ba sai bayan magrib ,da mmki yake kallon compaund dinsu ganin motar mum dinsu farhaan,mmki yake Mai ya kawota gidan su a irin wannan tym din.”Jin yyi xuciyarsa na tsalle bai gama dawowa normal ba ,sai ga Kiran Ammah ya shigo a wayarsa.dagawa yyi batareda yayi magana ba ,kana ina??”Yaji Ammah ta fada tamkar yace mata baya gida sai yaji baxai iyaba.ka shigo ga hajia Maryam ta shigo da haka Ammah ta kashe wayar ,cikin takunsa na kasaita ya shiga parlorn Ammah dauke da sallama a bakinsa,da fara’a Mami ta amsa tana fadin”Aliyu yaushe ka xama surikina ban sani ba.”Dan sosa Kai yyi ya xube agaban Mami yana gaisheta da ladabi Mami ta amsa tana fadin”nayi fushi Aliyu wannan satin ake daura maka Aure ko ka sanar Dani,ko a bakin farhaan banji xancen Auren kaba…….
    Mami ta karasa xancen tana kallonsa,Dan shafa kansa yyi gabansa na faduwa yake fadin”Am sowiee mami Auren ne yaxo a haka,da mamaki Mami ke fadin”Amma wacece wannan Mai sa’ar haka ??Ammah ta fadamin bada Areefa Mansoor ba.dan shafa sumar kansa yyi yana murmushi batareda yace komai ba,wayarsa ce ta fara ring wani irin ajiyar xuciya ya sauke ko wanene ya cecesa daga tambayoyin Mami,da sauri ya Mike ya nufi hanyar barin parlorn nan Mami ta juya suna magana da Ammah akan yarda xaa gudanar da bikin Aliyu,kasancewar Mami da Ammah kawayene tun su Aliyu na kanana ,Wanda sanadiyar yaransu Allah ya hada jinin su.
    Shifa yace baxaayi wani taro ba kawai a daura aure akawo masa Amaryarsa.”da mamaki Mami ke. fadin shine Kuma xaki biyewa shirmen Aliyu.”shi yaji xai iya Ammah ta fada tana basar da hirar gamida dauko wata hirar,
    Washe gari Khaleel waxeer ya iso shida Mai dakinsa laylah waxeer part din Ammah aka tarbesu ,cike da damuwa Ammah ke bin laylah din da ido ,ganin shekara kusan 3 har yanxu Layla din Koda batan wata Bata tabayi ba,sosai Ammah ta damu akan hakan,Haka Yan uwanta suna Maganar rashin haihuwar matar Khalil din,Bayan sun kammala cin Abincin.Ammah ta Kira murja tana fadin taje ta sauko da Nooriyah xata gaisa dasu Khalil da mamaki Laylah ke fadin har iyayen nata sun kawota kenan Ammah.”da murmushi Ammah take fadin Nina bukaci hakan me yayi saura jibi xaa su shiga lalle,kusan minti goma sai ga Nooriyyah tana saukowa akan stairs itada murja wacce ke take mata baya,tana cikin shigar doguwar rigar atamfa kalar red and yellow wacce tayi matukar dacewa da kalar fatan jikinta,sai wani irin sheki take acikin kayan sai babban mayafi Wanda ta axa akan kafadarta,
    Babu kwaliyya a fuskarta ,duka xuba mata ido sukayi daga Khalil waxeer har matarsa Laylah baki bude duka suke kallonta,ganinta bakar fata dukansu tunani daya suke yaushe Aliyu waxeer ya sauya tunaninsa akan bakar fata.?””xubewa tayi akan carpet tana gaishesu cikin sanyi muryarta, Layla ce ta amsa cike da tambayoyi a bakinta ,
    Da murmushi Ammah ke fadin tashi ki xauna cikin su Nooriyah Yan uwanki ne……..da murmushi Laylah ke fadin Amaryar mu gaskiyya kina da sa’a da kika samu Aliyu waxeer a matsayin mijin Aure ina maki fatan Alkhairi acikin Rayuwar Aurenku.”murmushi kurum Nooriyah tayi batareda tace komai ba, Khalil ne ya Mike yana fadawa Ammah xasu wuce part dinsu suyi wanka.a fito lafia
    Abinci dare na jiranku karfe takwas na dare”.mun gode Ammah Allah ya kara nisan kwana ya fada yana kallon laylah ,kusan tare suka fice daga part din na Ammah,tamkar jira laylah keyi su fito ta kalli Khalil da sauri tana fadin”Wai da gaske leel Aliyu ne xai auri wannan Yar kauyen??”ko kadan Bata dace da taxama matar Aliyu waxeer ba wlhi.”Laylah ta fada tana dakune fuska,Wai taya ma xaayi Aliyu yaso bakar macce??”Khalil ya dage kafada yana ware mata ido yake fadin”Waike me ya dameki kiyi Abunda ya dameki plz ya fada cikin Dan daga murya,shuru Layla tayi tana bin Khalil din da ido…..kamar yarda Ammah ta fada bayan ishai sai ga Khalil waxeer shida Aliyu sai Kuma Layla dake bayan su taci ado cikin wani tsadadden less Wanda yayi mugun karbarta ,dama laylah badai gayu ba.tayi simple make up Wanda ya Kara fitowa da Asalin farinta dama farace sosai,da fara’a Ammah ta tarbesu,.wannan karon Ammah Bata tura murja xuwa ta taho mata da Nooriyah ba Aliyu ta kalla ta fada masa yaje yaxo da Nooriyah xasuci Abincin dare tare ,shaye da toka Aliyu ke fadin Ammah plz…wani kallo da Ammah tayi masa yasa ya Mike da sauri ya nufi part din da Nooriyah din take,da ido laylah tabisa.tsaye yyi ajikin kofar yana sauke ajiyar xuciya baisan meyasa duk lokacin da xai kusanceta ba yake jin bugun xuciyarsa na karuwa,yafi minti biyu tsaye a kofar dakin kafin yayi knocking ,gamida tura kofar .gefen bed ya sameta ta buga uban ta gumi sanye take da hijab,tsaki yaja aransa .tana cikin daki Kuma sai ta saka hijab sabida kauyanci,gyaran murya yyi ta dago dara-daran idanunta ta xuba cikin nasa,yana wani daure fuska yake fadin,kixo Ammah na nemanki.”Ya fada yana nufar kofa har yakai kofa ya juyo da sauri yana fadin Kuma ki cire wannan hijab din,Yar kauye kawai…..”Ya karasa maganar fuska bbu walwala da mamaki take kallonsa,saka hijab din shine kauyanci,ki fito yanxu malama kina Bata mana lokaci ya fada da Dan daga murya.mikewa tayi tsaye ta nufi kofa sanye da hijab dinta baki ya bude yana kallonta…..

     

  • Waminal Hoob 13

    Waminal Hoob 13

    Waminal Hoob_* 13

    PAID BOOK
    _Asmy b Aliyu_

    Xagaye hannayen sa yyi akan kugunta dago kanta tayi tana fadin “Da gaske Kaine.”wani sly smile yyi Yana dage gira Yake fadin”nine Mana,Dan rage tsawon sa yyi ya subbaci bakinta tareda fadin I miss you my luv.”Kara kankame sa tayi tana Jin tamkar ta maida sa ciki,sakin sa tayi da sauri ta nufi Kitchen lemu ta dauko masa da cup glass ta tsiyaya ta Mika masa tana kallonsa da murmushi a fuskarta,
    Hira suka Dan taba ya tambayeta ya karatun ta,Dan juya ido tayi tana fadin bbu ddi.kumatun ta yaja Yana sakin murmushi,Yana tare daita Amma mind dinsa gaba daya Yana kan Nooriyah Kusan 9 yyi Shirin tafia Yana fadin xai tafi.”da mamaki take fadin ba kwana xakayi ba ,Yana shafa kansa yake fadin bani kadai naxo ba Areefa.”Nan take mood dinta ya canja ,
    Kaida waye??”girl friend din Farhaan ,toh meye Kuma na daga hankali badai ka sauketa masauki ba.”ta karasa Maganar da bacin Rai A muryarta ,sai Kuma nabar Yar mutane a bakon wuri.”yyi Maganar Yana kallon cikin idanunta kin cewa komai tayi ta juya xa tabar masa parlorn ya fisgota lokaci daya,Bai Bata damar magana ba ya hade bakin su wuri daya.Ya dde Yana tsotsar bakin ta sai da yaji jikinta ya saki duka sa’annan ya saketa,gobe xan fito mu fita jibi xan wuce…….”da haka ya subbaci goshinta ya juya da sassarfa Yabar parlorn gamida ja mata kofar…….sanye take cikin sleeping dress riga da wando da hula akanta tana xaune a parlor wayarta a hannunta tana famar juyata taji ana saka key a kofar,kallo daya tayi masa ta dauke Kai,shima kasa hada ido yyi daita wucewar sa yyi acikin bedroom ,kwanciyar ta tayi akan soofa batareda ta koma cikin room din ba.shima Koda ya fito wanka Shirin barci yyi,
    Ya tuna baiyi waya da Ammah ba,shi Kuma Bai shirya yimata karyar suna London ba,Idan Kuma yace Yana Egypt xaya Sha tambayar meya kaisa Egypt Kuma.washe gari kamar yarda yayiwa Areefa Mansoor Alkwari suna tare har Bayan magrib shopping yayi Mata na fitar hankali,sai Kusan 10 Yabar gidanta ,haka ya samu Nooriyah a parlor a karo na biyu wannan shurun nata Yana saka sa Jin wani iri,
    Shima girman Kai ya Hana yayi Mata magana.washe gari jirgin safe sukabi xuwa kasar London…..dukan su barcin gajia sukayi acikin kyakkyawan gidan Aliyu waxeer,da yamma ya tashi peter ma’aikaci Mai masa gyaran gida da girki har ya shirya masu teburin cin Abinci,xama yyi ya cika cikin sa Yana yi Yana kallon kofa yaga ta inda Yar baka xata fito sai Kuma gata cikin takunta Mai natsuwa tana cikin shigar (Allura maxi dress)kalar yellow,
    Wani irin yawu Aliyu waxeer ya hade haka ya kasa dauke kansa daga gareta,kayan ba karamin kyau sukayi Mata ba,har ta karaso agabansa Bai sani ba.
    “Xanyi waya da Ammah wayarta Bata xuwa ko kasan wani layi nata bayan wannan.”nima ban sani ba ,ki bari sai kin gama miskilancin ki sai ki tambaya kwana nawa bakya min magana bakya gaisheni.”Ya fada yana wani hade Rai,Baki ta bude tana kallonsa sai dai Bata ce komai ba ta juya ta koma cikin parlorn ta xauna,da ido yabita tana barin kamshinta a wajen,tana xaune taji an wani fisge wayar ya hade Rai sosai ya shiga xuba Mata lambobi a wayar,
    Yana gamawa ya Mika Mata wayar .nagode ta fada cikin rawar Murya baice komai ba ya nufi master bedroom dinsa dama tunda suka iso ya nuna Mata dayan dakin da xata sauka,
    Baa jima ba ya fito cikin bakin yadin filtex sai kamshi yake xubawa ya kafa hula akansa Wanda ta dace da kalan shigen nasa,
    Kallonsa kawai take xuciyarta na bugawa ,Bata taba ganin Wanda traditional kaya keyiwa kyau ba irin Aliyu waxeer,kina bukatar wani Abune??”da sauri ta girgixa kai Kofa ya nufa Yana Amsa waya da sanyayyen turancin sa,haka ta saki Baki tana kallonsa har ya fice daga falon.cikin sa’a Wayar ta Ammah ta shiga ,mutanen uk na sameku lfy??”cike da ladabi ta gaisheda Ammah , Ammah ta amsa cike da Jin ddi tana tambayarta ya bakunta garin Yana Mata ddi kuwa.”Ita dai murmushi kurum tayi Wanda Ammah na Jin sautin murmushin ta cikin wayar,Ammah Batool fa??”Batool ta koma Kano sunyi resuming school ki kirata.”Hira sukayi da Ammah kafin Ammah tayi Mata Alkawarin tana Nan tana bincika Mata wacce xata koya Mata turanci da harkar Business har ma da harkar passion godia tayiwa Ammah sun dde suna waya kafin suyi sallama.Farhaan ta Kira suka taba yar Hira har Yana fada mata Koda wane lokaci xai iya xuwa ya kawo Mata xiyara,yyi missing dinta sosai……..washe gari da farin ciki ta tashi kurum farhaan ya fada Mata xai kawo Mata xiyara tana sanye cikin Jallabiyya kirar oman,
    Karar Buda kofa taji da sauri ta kalli kofar
    Yana cikin Asalin uniform dinsa na tukin jirgin Sama wannan karon harda hular tana ajey bisa kansa,ya fito captain dinsa,wata xuciyar tana fadawa Nooriyah karki yaba kyawun da yyi ina ruwanki da kyawunsa,
    Kasa dauke idonta tayi har ya karaso wajenta,xanyi tafiar kwana biyu xuwa kasar somalis, duk Abunda kike bukata kiyi magana da peter xai kawo maki.”ta girgixa kai Cikin muryar tausayi take fadin bana gane turancin sa,ba karamin Daria ta basa ba sai dai baiyi dariar ba,Yana hararta Yana fadin”kin ga Amfanin ilimi ae yanxu xaki biyewa Ammah.”kiyi tunani kafin ki hau kan Abunda Ammah xata doraki……….”Idan xakuyi vedio call da farhaan ki tabbata kin saka hijab ba haka xaki tsaya agabansa ba,karki manta matsayinki Yanxu.”yyi Maganar Yana wani hade Rai,kallo ta bisa dashi har Yabar parlorn aranta take fadin “Allah ya kiyaye hanya masifaffe kawai.”A yinin ranar ta wuni cikin kadaici ,haka wani sashen na xuciyarta tana ta kewarsa.har dare Aliyu waxeer na makale a xuciyarta ,tana tsaye a tsakiyyar master bedroom dinsa tana karewa hadadden bed dinsa kallo kalar fari kall ,sai doguwar soofa itama fara da 1 seater guda biyu duk acikin room din sai katon hoton sa Wanda ke kallon bangon gabas,Yana sanye da kayan pilot da murmushin kasaita a kyakkayawar farar fuskarsa,shagala tayi da kallon hoton xuciyarta na amsar wani bakon yanayi ,wani irin kamshi room din keyi
    Kamshin da Aliyu keyi…hayewa tayi akan bed dinsa gamida daukar favourite pillow dinsa ta manna akan kirjinta,al’amari Mai girma take ji Akan Aliyu waxeer Wanda ko farhaan shagari da take soyayya dashi Baa ta Jin haka ,Ahankali taji xuciyarta bbu burbushin son farhaan aciki sai dai akwai girmamawa Mai girma da xuciyarta keyi masa.
    Kenan hauka takeyi ,ba soyayyar Aure take yiwa farhaan Shagari ba.”tana yimasa so sabida kyautatawar sa agareta ,da sauri xuciyarta take fadin”da kin cika butulu Noor ki farka da wannan mafarkin da kikeyi,tabi shawarar xuciyarta ta soma yaki da sabbin kibiyoyin da xuciyarta kebin ta dasu akan Aliyu waxeer,kwana tayi tana Addu’a Allah yasa kar xuciyarta ta kunyatata ta wulakanta ta,babban wulakanci kuwa na son Aminin farhaan Shagari Dan Bai cancanci irin wannan sakayyar ba,amma sai dai Kash xuciyarta ta riga da ta makaro kwana tayi da mafarkan Aliyu waxeer masu wuyar misiltawa na haihuwar kyawawan Yara tare dashi ,suna acikin babban lambu suna guje-guje da ya’yan su…..da tayi sallar Asubah acikin sujadar ta ta karshe tana Rokon Allah sassauci akan lamarin Aliyu waxeer maimakon ta samu sauki saima soyayyar Aliyu din ta Kara mamaye sako da kowane lungu na xuciyarta,hawaye takaici take xubarwa akan me xuciyarta xata xo mata da wannan mummunan kaddarar.”Har karfe 12 na Rana Nooriyah Bata fito daga dakin Aliyu waxeer ba tana can dunkule cikin tattausan bargonsa jikinta ya dau xafi sai kakkarwar sanyi takeyi,haka peter ya shiga xarya a parlor da kitchen Kiran da Aliyu yayi masa yakai goma,
    Yana fada masa madam Bata fito daga dakinta na barci ba,
    A Kiran karshe Aliyu ya umurcesa yaje ya kwankwasa kofar kusa ga dakinsa na barci ,peter yabi umurnin Mai gidansa ya nufi wurin da sassarfa ya shiga bugu kofar shuru yakeji,bugun ya tada Nooriyah daga barcin wahalar da ya kwasheta dakyar takai kofa ,da hijab ajikinta idanunta sunyi sukutum,har Peter xai juya sai gata ta bude kofar .xaro ido peter yyi Yana kallon yanayin nooriyah wacce ta fara layi ,tana dafa bango sannu madam??”ya fada cikin harshen turanci,meke damunki??”dakyar ta karaso parlorn.”dakyar ta iya hado kalmar turanci nacewar Bata da lfy.”da sauri Peter ya Kira Aliyu a wayar tamkar jira Yake ya dauka,cikin harshen turanci yake masa bayanin tamkar Bata Jin ddi Bata wayar Aliyu ya fada masa,
    Muryarsa kawai ta Kara sakata cikin wani yanayi……”meke damunki??”tambayar da ya soma jefo Mata kenan,cikin rawar Murya take fada masa ciwon Kai da xaxxabi,
    Ba peter wayar.mika masa wayar tayi,sun dde suna magana,
    Kafin ya kashe wayar.
    “Sai can Aliyu ya Kara Kira lokacin peter na a kitchen Yana kokarin hadawa Nooriyah din Tea,Bata wayar yyi
    “Kiyi wanka ki Sha tea doctor xaixo gida ya dubaki ,ki tabbata da Hijab ajikin ki .”da haka ya kashe wayar,
    Duk da tana cikin ciwo sai da tayi murmushi komai nasa daban ne…samun kanta tayi da bin umurnin sa wanka tayi riga ta saka marar nauyi taje parlor peter ya hada Mata wani tea,Dan wancan ya Dade da sandarewa,mintuna Kusan Ashirin sai ga kararrawar buga kofa da alamar dr.da xai dubata ya iso kyakkyawan bature,sai sannu yake Mata cikin harshen turancin haka sunyi waya da captain Aliyu waxeer ya fada masa meke damunta ,
    Magani kawai yabata dama ya riga da yaxo dashi ,Yana fita tabi umurnin Dr.tasha maganin Kusan 2 ta samu barcin Rana ,Koda ta tashi Kusan 5 ciwon kan ya sauka haka xaxxabin ya rage sai dai ko kadan jikinta bayada karfi wanka ta karayi,
    Ko lunch din da peter ya hada Mata kadan taci har yau Bata Saba da cimar kasar ba,sai a hankali……..Sai da dare Aliyu ya kirata ya Mata ya jiki ta fada masa ta samu sauki,
    Sai da safe yayi Mata gamida kashe wayar.
    Yau ko kadan Bata da sha’awar Kiran farhaan shima sai akayi sa’a Bai kiraba.a gida Nigeria Kuma ta Kira kawunta tana tambayarsa labarin Kabir fa.”Ya fada Mata Yana cikin koshin lfy Kabir ya fara samun natsuwa Aliyu na kula da lamarinsa,haka ya fada masa idan ya natsu xai tsaya masa tsayin daka yaga ya samu ilimin boko,murna tayi sosai yau a dakin ta tayi kwanciyarta.yau tun da safe da kanta ta shiga gyara gida ,ta canjawa Aliyu bedshirt ta wanke masa toilet,tana tsaye da peter acikin kitchen suna hada dinner dama peter ya fada Mata,oga mafi yawancin tafiarsa yafi dawowa da dare .suna gamawa ta shige wanka gamida dauro Alwallah.Amma har Kusan 10 bbu Aliyu bbu Alamarsa har ta gaji da duba agogo,
    Haka peter ya sameta a parlorn ,Yana fada Mata oga Ba xai samu shigowa ba sai gobe da safe,ta fahimci haka acikin turancinsa.nan take fuskarta ta canja ,sai da safe yayi mata ,ya Rufo Mata kofar haushin xuciyarta taji akan me xata ma damu da dawowar mutunen da Bai wani dauketa da muhimmanci cikin Rayuwarsa ba.Har tayi Shirin barci tana Jin haushin xuciyarta sosai akan damuwa da lamarin Aliyu waxeer…..

    Littafin waminal Hoob na kudine#500
    Account Details
    0004157137
    Jaiz Bank
    Asma’u Buhari Aliyu
    Katin wayar MTN.ta wannan Lambar#
    09060259200
    Shaidar Biya ta wannan lambar
    08086207764#

    ASMY#??
    WM#??
    Team#NooryAli forever??
    [9/15, 6:11 PM] Asmy Mom Aydah?

  • Waminal Hoob 23

    Waminal Hoob 23

    M] Asmy Mom Aydah??: _*Waminal Hoob*_ 23

    _Asmy b Aliyu_

    Wacece matar Captain??”Tambayar da Dr .Arhaam ya jefo kenan,da sauri Ammah ke nuna Noory,tana fadin”Dr .Ya farka ne?”Yeah ya farka Kuma Alhmdullh numfashin sa ya dawo dai-dai har ancire masa oxgyen,ajiyar xuciya Ammah ta sauke.dr.Arhaam ya kalli Ammah a karo na biyu Yana fadin”Ina son Naga matarsa Hajia…….yyi Maganar cike da girmamawa ,Ammah ta kalli Noory tana fadin”taje taga doctor gabanta na faduwa tabi bayan doctor kowa yabita da kallo tareda tambayoyi aransa,Idonsa na akanta har suka karaso cikin room din,
    Wanda ya dau sanyi saboda AC.doctor Arhaam yaja Mata kujera ta xauna Taki yarda ta kalli Aliyu,lokaci daya yayi gyaran Murya ya maida kallonsa kan Aliyu Yana fadin”meya faru Aliyu??”me yayi xafi haka.”meya Kai ka shiga damuwa har haka??”da xuciyarka ta buga ka mutu fa.”tambayoyin da doctor ya jero Masa kenan Yana bin Aliyu da ido ,lumshe idonsa yyi lokaci daya kafin ya budesu Akan Doctor Arhaam din,
    Ya dakune Fuska lokaci daya Yana fadin”meya faru??”murmushi doctor yyi Yana fadin”meya jawo maka doguwar suma.”Shuru Aliyu yayi Yana tuna Abunda ya faru,lokaci daya ya hade Rai baya Mason tunawa,pls mubar wannan Maganar,Dr.Arhaam ya girgixa Kai Yana maida kallonsa kan Noory da tun daxu kanta ke sauke a kasa,
    Ya riga da yasan halin Aliyu ba tun yau Yake aeki acikin Asibitin waxeer ba ,ko xasu kwana Aliyu waxeer baxai fada masa damuwarsa ba.”mijinki bakya basa hakkinsa na Aure ne sparm ya tarar masa a mara sosae,Wanda Idan bakuyi wasa ba xai iya haifar masa da matsala.”Idan kinyi Masa kadan yayi Aure mana.”Dr.Arhaam yyi Maganar sounding so very serious.!”da sauri Noory ta dago tana kallon doctor xuciyarta na wani irin bugawa da Kalmar Aliyu ya Kara Aure,
    Shawarwari doctor ya shiga Basu dukan su kafin ya rubutawa Aliyu maganun nuka,Haka ya fadawa nooryn tayi kokari ta rika kaucewa Abunda baya so,bacin Rai ne ya haifar masa da doguwar suma.magana na karshe Akwai Abunda ke damun mijinki Akwai Abunda ya saka sosae aransa kiyi kokari ki gano koma menene damuwa tayi Masa yawa,gaf Yake da kamuwa da ciwon xuciya.”da wani irin shock Nooriyah ke kallon doctor,tattaro dukkan jarumtar tayi tana fadin”pls doctor karka fadawa Familyn waxeer insha Allahu xamuyi kokarin gyara matsalar mu, doctor Arhaam ya girgixa Kai Yana fadin”shiyasa ma na bukaci ganinki,godia tayi Masa Yana fita sai gasu Ammah sun shigo ,Ammah ta nufi gadonsa tana yimasa sannu.sai Kara wani narkewa Yake,A hada maka tea.??”,Ammah ta fada masa ,girgixa Kai yyi Yana fadin”muje gida Ammah wanka nake son nayi.”Baki bude Ammah ke fadin”wane irin gida kayi wankan Anan Mana,ko likita ya sallameka ne.ya kalli Ammah Yana fadin”baxan iya komai cikin Asibitin Nan ba,
    Khaleel waxeer ya girgixa Kai Yana fadin”kin manta halin Aliyu ne Ammah ,bara naje Naga doctor Arhaam Idan da bukatar a basa sallama sai mu wuce gida,kallon kowa laylah keyi cike da bacin Rai ganin yarda kowa ya rude akan ciwon Aliyu waxeer, Khaleel ko gida Bai kwana ba a Asibiti ya kwana tareda su Ammah sai da safe ya koma gida,Har wurin doctor Khaleel yaje ya karbo takardar sallamar Aliyu saboda sanin rikicinsa, Khaleel ya jasu su duka cikin motar ferari,Layla sai cika takeyi tana batsewa,
    Ammah aka fara saukewa da Ummah,
    Sa’anan Aliyu da Nooriyah Yana saukesu Khaleel waxeer ya mikawa Noory din maganinsa dake cikin Leda,Yana kallonta Yana fadin”Allah ya Kara sauki xamu shigo xuwa Anjima,Amsa tayi tana masa godia cike da ladabi wani kallo laylah keyi Mata na tsana,motar Khaleel na wucewa tana kokarin kamo hannunsa ya fisge gamida nufar entrances din shiga gidan,kallo tabisa da shi lokaci daya taji jikinta yyi sanyi haka xuciyarta na bugawa.
    Bayansa tabi ko a parlorn Bai tsaya ba upstairs ya nufa ya shigewarsa dakin barcinsa,aje ledar maganin tayi Akan center table ta nufi Kitchen tsaye tayi acikin kitchen din tana tunanin Mai bakinsa xaaya iya dauka , Fruits salad ta hada Masa da Madara cikin fridge ta saka ya danyi sanyi ta fitar tasan Bai cika son Abu Mai sanyi ba hakama Mai xafi sama-sama dae
    Karshe ta hada Masa black tea irin Wanda Ammah ke hada Masa,ta xuba masa kayan kamshi tana gamawa ta gasa bread tareda kayan hadinsa,cikin minti Ashirin ta Gama jera komai akan madaidaicin tray ta nufi master bedroom dinsa xuciyarta na bugawa,da sallama ta shiga cikin Room din
    Baya ciki da alamar Yana toilet ,Dan center table dake gefe ta jawo ta Dora tray din akae,fitowa yyi daure da farin towel a kugunsa sai Kuma karami da Yake goge Ruwan dake xuba acikin sumar kansa Mai kama da ta larabawa,kallo daya yayi Mata ya dauke kae duk lokacin da ya tuna Rungumar da farhaan yyi Mata sae yaji ransa yyi balain baci,xama tayi acikin doguwar soofa tana kallonsa,Bai San ta karaso gabansa ba sai yaji ta karbi towel din hannunsa tana tayasa goge Ruwan dake diga a hankali wasu Kuma sun manne da gashin dake manne da kirjinsa,fisge towel din yayi Yana fadin”ta fita!!”Yyi Maganar sounding so very Angry ,rungumesa tayi ta baya ta kwantar da kanta acikin bayansa tana shakar kamshin jikinsa haka hawaye lokaci daya suna cika idonta,cikin wata irin Murya take fadin”Are you upset with me??”kayi min fada pls fadan ka nake bukata ,ka fadamin ba dai-dai nakeyin komai ba,da Aurena Ina kula wani,Yana Kai hannunsa jikina..”pls kayi min fada fadanka nake bukata shurunka na azabtar da xuciyata Ali.”Hawayenta yaji suna sauka a gadon bayansa,A hankali ya cireta daga jikinsa .Kayan da ta fidda Masa na Shan iska Wanda Basu da nauyi ya dauka ya nufi toilet,acikin toilet ya saka kayan .ga mamakin sa Koda ya fito tana dakin,black tea ta shiga hada Masa ya xauna gefen bed Yana Danna wayarsa ,Jan center Table din tayi xuwa gabansa .ta Mika masa cup din Hannunta,karba yyi Yana kallonta sai yaji ya mutu da wani irin tausayinta,sai sharar hawaye take.kin San babban xunubin da kike kwasa na Rungumar wani da Aurenki Noory??”Yayi Maganar cikin Murya marar Amo.”dagowa tayi tana kallonsa da fararen idanunta da suka fara canja kala,
    “Ba Wai Ina rabaki da Farhaan bane,ko daya kawai dai ki San yarda xakiyi mu’amala dashi,
    Wani sabon sonsa taji Yana bude Mata xuciyata Wanda batasan ta inda ya fara ba,ko Maganar tasa cikin natsuwa yake yin ta.”xanyi kokari cikin satin Nan na raba Auren Nan,Farhaan yana bukatar Hakan.”da wani irin shock take kallonsa,kallonsa takeyi da sabon tashin hankalin da Yake hangowa cikin fuskarta,Hawaye da gudu suke mirginowa Akan fuskarta tamkar an Buda famfo ,wara ido yyi da sauri Yana ajey mug din hannunsa,Ya Jawota gaba daya jikinsa,cikin kwantar da Murya yake fadin”kuka Kuma meyayi xafi pls ki daina karki karya min xuciya Shima yayi Maganar xuciyarsa na bugawa,dauriya kurum yake a gabanta .Ranar da ya raba Aurensa da nooriyah ya tabbata farin ciki ya ruguje masa,Noor din ta xama wani babban bango acikin Rayuwarsa,sai yanxu yaji maganganun Ammah na dawo Masa hankali.”Aliyu ko Mai Rintsi karka taba yarda Nooriyah tabar Rayuwarka,Noory Alkhairi ce acikin Rayuwarka ,Rayuwarmu ma duka .shigowar Nooriyah cikin rayuwarsa ya fara samun canji a dukkan al’amuran sa,A hankali ci gabansa da daukakarsa ke budewa,dukiar su Kuma sai Kara daukaka take da wata irin habakar Mai ban mamaki,sanadiyar nooryn,ya daina shanshanci da Areefa Mansoor Wanda yasan har a wurin Allah xunubi ne Kuma Mai girma,har bbu Kaya Yana kwana shida Areefa mansoor ,sai dai Bai taba Kusantarta ba yasan Yana rage xafi ne kurum daita ,ko anan Allah yabarsa Yyi Masa babbar niIma Wanda ba kowa xai samu hakan ba,da yaje yyi xina ya haifawa Ammah jikoki shegu fa?”da baxai taba yafewa kansa ba…….lokaci daya ta xare jikinsa cikin nasa batareda ta kallesa ba ta juya taba room din,
    da wani irin Kallo ya bita ,Bata dde ba ta dawo dauke da ledar magungunan sa,ta nuna masa yarda xai Sha kowane,tamkar yarda khaleel waxeer ya fada mata,so Yake su hada ido Amma Taki basa damar haka,lokaci daya taji ya Jawota ta daga ido da sauri tana kallonsa xuciyarsa na bugawa,
    Kokarin sauka take Akan cinyarsa ya hade Rai tea ya shiga hada Mata,Kai cup din yyi a bakinta ya hade Rai sosai karma tayi masa gardama.buda bakin tayi tana sha sai taji wani iri jinta akan cinyarsa ,kusan rabi tasha tareda bread din da ta gasa.ta kallesa tana fada masa ta koshi,ya ware mata ido yana fadin”meyayi saura ,ki idar da ladarki shanyewa tayi ta matsu ta daga daga bisa kafunsa jinta take wani iri haka tun safe take fama da ciwon mara,sai dai bata fadama Aliyu ba gashi maganin da take sha tabaro sa a London,tana ta so ta fadawa Aliyu musamman yarda take shan wahala idan xatayi period tamkar mai Aljannu take komawa sabida ciwon mara,haka Aliyu xaiyi ta fama daita yinin ranar daga shi har ita A wahalce xasu yini,
    Shima maganinsa ya sha ya dan kwanta dan yana jin barci,
    Itama dakinta ta wuce tayi wanka. kwanciyarta tayi tana jin ciwon marar dake kokarin hanata kwanciyar,tasan period dinta ne xaixo,
    Tareda Batool suka shirya lunch a gidan ta,suka xubawa Ammah nata …..Ammah na ganin Abinci ta hau fada sosai tana fadin karta kara shiga kitchen wane irin Rashin hankali ne wannan,tana tunanin abinda ke cikinta kuwa??Hakuri Aliyu ya hau bata a waya yana fadin”insha Allahu xaa kiyaye nan Ammah ke fada masa xata samo yar aekin da xata rika taya nooryn kula da gida,Bayan la’asar bayan Batool ta wuce gida ita daya a daki sai juye-juye take akan marbles haka ta fara fita hankalinta,Aliyu yana turo kofar dakinta yaci karo daita tana mirgina gabansa yayi mugun bugawa , Addu’a yake Allah yasa ba period dinta bane,da sauri ya karaso yana dagota yake fadin”lafia?Are You ok.”Kusan lokaci daya ya jero mata tambayoyin hankalinsa a mugun tashe, cikinta ta fara nuna masa tana jujjuya masa ido,ina maganin ki.”da azaba take fadin”ta barosa,
    Ya girgiza kai cike da tashin hankali yake fadin,kin san yarda kike wahala meyasa xaki barosa.mikar daita yyi tsaye dole subar gidan nan yanxun nan,Yasan Ammah xata xo ganinsa bayan magrib haka ma Batool na iya dawowa kowane lokaci dan ya lura yanzu wani shiri take da noory ……..Hijab ya saka mata kayan su ya ha?a na kwana ?aya acikin karamar trolley ya Kai mota ya dawo da sauri ya ganta durkushe tamkar mai nakuda ya girgiza kai rakin Nooriyah na basa mmki dagota yyi ya rikata suka bar gidan,
    Tun a mota ta fara yi masa ihu tana dafe bayanta da takeji tamkar ba nata ba,koda suka isa can gidan nasa.shiya fito daita daga motar har ta fara ficewa daga hayacinta kan lafiyayyen bed dinsa ya kwantar daita ya cire Hijab din jikinta,
    Waya yyi a waxeer pharmacy ya tura masu sunan maganin,
    Baifi minti biyar ba aka kirasa akan bbu shi .kashe wayar yyi ya zauna gefen bed ya cire doguwar rigar jikinta daga ita sai farar vest da dan short shima fari sol.”hannunsa ya axa kan cikinta yana shafa mata a hankali hawaye take tana jujjuya kanta,haka ta shiga wullah kafafunta ihu ta shiga xubawa abun daria abun tausayi,ihu take tamkar xata tada gidan,Hade bakinsa yayi da nata a hankali yake tsosar bakin still hannunsa na kan mararta yana shafawa shiru tayi tana karbar sakonsa gefe kuma ga azaba,Wani irin abu yakeji dauriya kawai yake,vest din dake jikinta ya idar da cirewa,ya kafe na shanunta da ido wanda sun dde suna cika masa ido,yana son macce mai halittar manyyan na shanu,sabanin Areefa mansoor da bata fiye manyyan na shanu ba,
    Hannu yasa yana murxasu a hankali yana jin wani irin yanayi da bai taba tsintar kansa aciki ba,
    Jin wani irin dadi na xiyarta noory yasa ta shiga bankare masa ddin takeji tunda ga cikin kunnuwanta har cikin tafin kafarta sae kara danna kan Aliyu waxeer take a wajen,
    Wanda shima gaf yake da rasa control dinsa,bakinsa ya kafa ya fara sha batareda tunanin komai ba,ihu noory ta fara yimasa tana juya kanta side by side wani irin fitsari takeji wanda ya hade mata da wani irin ciwon mara,Yana jin yarda bbc dinsa tayi wani irin mikewa tunda yake a rayuwarsa bai taba jin dadin na shanu ba kamar yarda yake jin na noory yanxu,yarda take juye-juye yana kara saka sa cikin wani irin yanayi ,wani irin barcin wahala ya dauke nooryn lokaci daya,idonsa ya bude da suka dde da canja kala yana kallon kyakkyawar fuskarta ,
    Tuno farhaan Shagari yasa gabansa yyi mummunan bugawa ,
    Da sauri ya mirgina gefe yana dafe kansa da ya damesa da ciwo,haka yana jin marar sa na wani irin ciwo tamkar xata fice .
    Wani irin numfashi ya shiga ja dakyar yaja kafafunsa xuwa toilet still bbc dinsa bai kwanta ba,Ruwa ya sakarma kansa Yana sauke wani irin numfashi ,yanxu haka Farhaan xai kasance da Nooriyah idan sukayi Aure???”wani irin kishi mai zafi yaji yana lullube masa xuciya .Idan wani ya kasance tareda noory bashi ba xae iya mutuwa.yafi karfin minti talatin a toilet kafin yyi wanka ya fito,
    Kallonta yake tana barci cike da kwanciyar hankali,
    Wani irin sonta yaji yana kara shigarsa,
    Haske yaga wayarsa nayi dama ya riga ya sakata a silent ganin Mai Kiran yasa gabansa ya fadi dakyar ya saita kansa ya daga.Kira nawa nayi maka Aliyu??”kuma a ina kuka je mun tarar da gidan babu kowa,
    Ya langabe kai gamida kwantar da murya yake fadin”Amma bana son hayaniya muna a guest house dina.”Yana Jin sautin murmushin Ammah ta wayar kafin tace muke yi maku hayaniyar kenan .”da sauri ya katse Ammah yana fadin”Ba haka bane,
    “Ka bani Nooriyah itama wayarta kashe,
    Ya dan sosa kai tuno ddin da ya gama sha yanxu yake fadawa Ammah tana barci,
    Ammah ta girgiza kai tana fadin “Idan ta tashi ka kira,kuma xan turo mata Batool koda tana bukatar wani abu,da sauri yace karki turota Ammah ,
    Ni xanyi mata idan tana bukata.”xaro ido yyi bai ma san a fili ya fadi kalmar ba,da sauri ya kashe wayar,
    A daren ma basuyi barci ba sabida ciwon marar noory din,sata yyi duka acikin jikinsa yana karanto mata duk addu’ar da taxo bakin sa,sai kusan Asubah duka suka samu barci ,wanda yasa ya rasa jam’i….
    Wajajen karfe 8 na safe noory har tayi gyaran gidan,tayi wanka koda ta tashi period dinta yaxo sai dai tana dan jin ciwon baya,haka ta daure tayi gyaran gida ,Ammah ta riga ta kirasu A waya akan nooryn karta kuskura tayi wani girki xata turo driver da abincin karin su,tana ta zama a parlorn kasa taki komawa sama,duk lokacin da ta tuno abunda ya faru itada Aliyu a daren jiya sai taji wani iri,haka wani irin kunyarsa taxo ta tsaya mata a rai,tana jin karar fitowarsa da turarensa da ya fara xiyartar hancinta tayi saurin dunkulewa acikin soofa,gamida lumshe idonta tamkar mai barci,a hankali ya daga kafafunta ya xauna gamida dora kafafun nata kan kafafunsa yana jan kyawawan dogayen yatsun kafafunta,da sauri ta bude ido tana kallonsa, eye’s dinsa yyi Rolling Yana fadin”dama nasan ba barci kike ba,Runtse idonta tayi kafin ta budesu a hankali lokaci daya kuma ta mike xaune ,good morning Yar baka.”hope you slept well in d whole nyt.”I’m feeling much better,
    Ta fada cike da jin kunyarsa haka ta kasa kallonsa,hannunsa taji akan shoulder dinta kafin tayi magana ,ya Jawota zuwa jikinsa duka,bai bata damar magana ba in a second Ali yyi merging lips dinsu wuri ?aya,bata san mai yasa ta fara mayar masa da martani ba tamkar yay mata asiri,
    Jin tayi hannunsa na yawo ajikinta,wani irin tsoro ya shigeta lokaci daya,tuno farhaan Shagari kurum yasa tayi saurin cire bakinta cikin nasa,samun kanta tayi da dora kanta kan chest dinsa,Ta fashe da wani irin kuka mai cin rai,idan ta rabu da Auren Aliyu waxeer mutuwa xatayi ,wani irin xaxxafan so takeyi masa. Bai hanata kuka ba hugging dinta yyi slowly ,Yana Dan shafa bayanta shima zuciyarsa na bugawa.

    _Gareku masu karanta min book yan bati wlhi tallahi har dunia ta nade baxan yafe hakkina na dari biyar ba kin ciwa Kanki wuta dake nake wacce karnuka suka gama lashewa xuciya!ku cigaba da karantawa for free Ni kuma baxan fasa Allah ya isa ba.!”_

    Littafin waminal Hoob na kudi ne #500
    Account Details
    0004157137
    Jaiz bank
    Asma’u Buhari Aliyu
    Katin wayar MTN.ta wannan lambar#09060259200
    Shaidar biya ta wannan lambar#08086207764

  • Waminal Hoob 9

    Waminal Hoob 9

    Waminal Hoob*_ 9..

    PAID BOOK
    Free page.

    _Asmy b Aliyu_

    Ajiyar xuciya ya sauke ya gaishe da Auntyn nasa da ladabi yana fadin “.taimako xakiyi min Aunty nasan a kaf familyn waxeer ke kadaice kika fi kaunata ,ni nasan da hakan…”Yayi Maganar cikin sanyi murya,murmushi Aunty Ramlah tayi tana fadin fadamin me kake so.”shuru yyi na Kusan sakan biyar kafin ya buda bakin sa cike da Jin kunya yake fadin ina son ganin ta Aunty.”wara ido Aunty Ramlah tayi tana murmushi take fadin”wacece kakeso ka gani,tana so ya fada mata da bakin sa Amaryar sa yake so ya gani,cikin kwantar da murya yake fadin ance tana side dinki,kayi min hausar da xan fahimta Aliyu wacece take a wajena.”cike da Jin haushin farhaan yake fadin Noory,ya fadi sunan tamkar yarda yaji su Batool na kiranta ,Dan shi har ga Allah bai wani rike sunan ta ba.daria Aunty tayi tana fadin”Yeaah Yarona ya girma duka-duka yaushe kuka rabu da har xaka fara tunanin kara ganin ta.”cike da gajia yake fadin sako xan Bata.”toh naji ka kawo min sakon na Bata Mana,ya dakune fuska Yana fadin”noo kibarsa kawai cike da Jin haushi a muryarsa ,kowa Yana tunanin da gaske soyayya Yake daita har Yana mugun son ya ganta.kayi fushi kenan?”Aunty Ramlah ta fada tana murmushi,shaye da toka yake fadin”kema ae kin San dole nayi fushi Kuna tayi min yanga kunki hadani da Amarya ta kwana Kuma Nawa ya rage.”Ya fada batare da yasan maganar
    ta fito ba ,Aunty Ramlah ta kama baki tana fadin ni dai karkayi min Rashin kunya na baka dama kaxo kaga amaryar ka a minti Ashirin yayi maka.”Yana dakune Fuska yake fadin ni yayi min ma Yawa ,toh naxo yanxu…..”A’ah sai xuwa Bayan magrib tana hutawa yanxu barci xatayi gaba daya ta gaji Kuma baa son Amarya ta rika aikin wahala.”lallai ma ta samu banxa kenan .wato hutawa ma.”Ya fada can kasan Ransa ,kwafa yayi ya fada mata da magrib xai shigo da haka sukayi sallama,
    Aunty Ramlah ta koma wajen kanwar ta Fatima dake sakawa Yarta Pampers tana Bata labarin Maganar da sukayi a waya,Fatima waxeer tayi Daria tana fadin”dama kece baki yarda da Aliyu bbu Ruwan sa ba ,jeki gidan sa ki Mike kafa Kisha kallon yarda xai rika tarairayar matarsa ,maybe harda gudowa xakiyi sabida Jin kunya.”waya sani ko da daren xuwa xaya yi ya Dan shafa Amaryar sa,Aunty Ramlah ta girgixa Kai tana fadin toh Banda sharri gaskiyya Yarona ba haka Yake ba.”Fatima waxeer tayi Daria tana gyada Kai,
    Kibar samarin yanxu kurum Maman Airah sunfi ma masu Auren sanin wasu Abubuwan,mikewa Ramlah waxeer tayi tana fadin bari ta koma wajen Nooriyah taga taci Abinci ,ta samu Nooriyah nacin Abinci .Yawwa Yar gidana ki saki jikin ki kici Abinci Dan Allah ,idan kin gama ki kwanta ki huta .godia tayiwa Aunty Ramlah ta juya gamida rufo mata kofar…haka ana gafda sallar magrib Aunty Ramlah ta sakata yin wani wanka,sai wani kamshi ke fita ajikinta fatarta sai wani irin glowing take tamkar ba Nooriyah Yar gidan kawu balele ba.bata taba saka ran Rayuwa xata kawota Anan wurin ba,tana xaune a daki har aka Kira sallar magrib .wannan karon Atamfa Aunty Ramlah ta kawo mata ta saka dinki riga da skirt kayan sun Dan kamata sabida ta Dan yi kiba jikinta ya canja,
    Atamfar da kalar mayafinta.Aunty Ramlah tajata agaban mirror dressing tace ta Dan shafa powder ,ta Dan goga man baki a saman lebunan ta.bbu musu tayi yarda Aunty ta fada mata ta taimaka mata ta saka turarruka…….masu sanyi kamshi,muje kina da bako a parlorn baki .gaban Nooriyah ya fadi to ita Kuma wane bakone Yaxo ko dai farhaan dinta ya dawo.”haka tabi Aunty Ramlah har xuwa babban parlorn baki.jin kamshin turarensa kawai sai da gabanta ya fadi,ta daga Kai ta kallesa wannan karon kananun kayane ajikinsa,hannayen sa xube cikin Aljihun wandon sa.Ya karaso Yana yiwa Aunty murmushi minti Ashirin kayi sauri lokacin ka na tafia fa??shafa sumar kansa yyi ,Aunty ta juya tabar parlon gamida Rufo masu kofar.da sauri ya xauna Yana fiddo wayarsa batare da Ya kalli Nooriyah ba ita kuma ta kasa xama cikin parlorn tayi tsaye ,ya dago da wani irin yanayi a fuskarsa yake fadin Dan xaku gaisa dashi a waya xakici uban wannan kwaliyya haka .”Ya fada fuska bbu walwala ,toh jeki toilet ki wanke wannan fuskar .”Kana kaini karshe Aliyu kanka na koyi fada da masifa harma da Rashin kunya duka Kuma kaine ka koyamin , .Kuma waye ne xamu gaisa dashi a waya kake masifar nayi kwaliyya inhar farhaan ne ae kaima kasan ya cancan ci fiye da haka,Babu ruwanka da kwaliyyar da nayi masa.”,maganganun ta sunyi masa xafi sosai baisan lokacin da ya fisgota ba ta fado kansa gabanta ya shiga faduwa ganin yarda idanunsa suka koma Red tana Jin yarda xuciyarsa ke bugawa.A tsorace take kokarin kwatar kanta Amma yayi mata rikon da baxata iyaba.baxato taga ya matse bakin da karfi sai da ta saki karar axaba.ya turata da karfi Yana huci yake fadin” gobe ma ki kara yimin Rashin kunya ,ya daka mata tsawar da ta gigita ta Yana fadin ta tashi taje ta wanke fuskarta duka inhar tana so tayi waya da farhaan.”mikewa tayi hawaye suka shiga Rolling akan face dinta ,tayi missing din farhaan sosai tana so suyi waya akan wannan dalilin shiyasa baxata ki karbar wayar Aliyu waxeer ba.nuna mata toilet yyi dake cikin parlorn nan ta shiga tana wanke face dinta hawaye na xubar mata tana tsinewa Aliyu waxeer ,samun kansa yyi da Jin haushin kansa to shi ina ruwansa idan tayiwa Farhaan kwaliyya “Aliyu meke damun kanka akan yarinyyar nan.”da sauri Ya shiga girgixa Kai Yana fadin ,kawai na tsaneta ne ina kishin yarda besty ke tsananin kaunarta,
    Kallon fuskarta yyi ya wani daure fuska yace karaso ki xauna xan hadaku vedio call ,idan kikayi min rawar Kai wlhi xan fasa.”Ya karasa maganar shaye da toka.xama tayi Dan nesa dashi ya watsa mata harara Yana fadin ni xan sameki na Mika maki wayar,Kara matsowa tayi kusa dashi Amma sai da ta tabbatar akwai space tsakanin su,bugu daya farhaan ya daga ,Aliyu ya hararesa Yana fadin ka xama namiji Mana kan macce kana wani Rawar Kai ,marar aji kawai.”Aliyu waxeer yyi maganar Yana hararar farhaan din ya wani hade Rai,minti goma na baku da ya cika xan karbe wayana inada Abubuwan yi a daren Nan tunda ka hadani da wahala”…….Ya karasa maganar Yana mikawa Nooriyah wayar batare da ya kalleta ba ,mikewa yyi hannun sa xube cikin Aljihun wandonsa ya koma can kusa ga window yyi crossing hand’s din shi akan kirjinsa gamida kurawa window din ido tamkar Mai son ya gano wani Abu acikin window din,sai da ta saci kallonsa in a second taga hankalin sa baya kansu. sa’annan ta maida hankalin ta kan farhaan…Sallama tayi masa tana boye dukkan damuwarta ,duk da haka sai da yaga hawaye akan fuskarta .farhaan ya ware ido Yana fadin ”ya Kuma da haka??ta shagwabe fuska cikin muryar son tayi kuka take fadin kawai ina kewarka farhaan ko nemana bakayi ,plz ni ka sayamin waya mana murika waya da tawa wayar kadaina hadani da wannan mutunen Mai fadin rai.”ta fada cikin muryar tausayi,
    Murmushi Farhaan yyi
    Yana fadin”kece kuwa my love kin ga yarda Fuskarki ke wani irin sheki ,gaskiyya Aliyu yana kular min dake .
    Tasha toka tana fadin ni baya wani kula Dani Ammah kurum ce ke kula Dani,Aliyu duka hirar da suke Yana jinta.ba xato taga ya fisge wayar gamida kasheta duka,Fashewa tayi da kuka tana yarfi da hannayenta da mamaki yake kallonta yarda ta bude baki tana kuka tamkar wata baby doll.”Toh ni ka siyamin wayana Mana sai na rika wayar dashi ,ta fada tana Kara volume kukanta…..”kukanta yaji Yana dagula masa lissafi da sauri ya durkusa agabanta Murya kasa-kasa yake fadin “baki da Hankali ne sai kin Sa anji kukanki an xargi ko ina maki wani Abu.”
    To kabani nayi waya da Farhaan Dina shi kawai ne ke Sona shi kawai ke sani farin ciki Kuma baya min ihu kamar yarda kake yimin……..”xai riko hannunta yayi saurin janyewa a tsorace mikewa yyi tsaye Yana fadin”ki bari idan kika tare a gidana xan siya maki waya ,sai ku cigaba da wayar bbu takura Amma Banda kwanakkin Nan.wani xai iya suspecting wani Abu,ni Kuma duk Abunda xai taba xuriata bana maraba dashi. Kofar baya ya nufa da sassarfa Yana barin parlorn da ido tabisa har ya bace.
    Washe gari bata tashi ba sai Kusan 11 wanka ta farayi sa’annan tayi break fast da axxahar Aunty Ramlah da Fatima waxeer suka yi Shirin maidata wajen Ammah.sosai Nooriyah taji tana kaunarsu ganin yarda suke sonta suke Bata wata irin kulawa tamkar ta fito daga cikin su,da fara’a Ammah ta tarbi su Ramlah waxeer tana masu sannu da xuwa ,
    Yan aikin Ammah ne suka fara cika gabansu da kayan motsa baki.da murmushi Ammah ke fadin yanxu nake xancen ku araina,Yan uwan Nooriyah suna so su karbeta .”sai Kuma Ranar da aka daura aure muda sake haduwa daita ,tunda Aliyu ya kafe baya wani event’s .”Da sauri Ramlat waxeer ta tari numfashin Ammah tana fadin shi Aliyu ne ya fada baya son wani Event sai kace marar gata.”Aunty Ramlah ta fada cikin fuskar damuwa.Ammah ta tabe baki tana fadin toh ina Maganar wane event lokaci ya riga ya kure jibine daurin Aure,baxai yuyuba gaskiyya xamu shirya ko mother’s day ne da waleema……Idan baayi ba xai iya xama wani magana.,,Aunty Ramlah ta Kira Aliyu a waya ta fada masa komai yake yaxo Yanxu tana son ganinsa.basu jima wajen Ammah ba suka koma part dinsu ,Bayan tafiar su Ammah ta samu Nooriyah a daki ta xauna gefen bed tana fadin”murja ta riga ta shirya maki kayan da xakiyi amfani dasu a gidan hajia saudah ,na turaki ne sabida gudun surutun mutane.”musamman wannan familyn xasu fara tunanin ina dangin ki da xaki tare anan??”shiyasa nayiwa su Ramlah karya da an daura Aure ni da kaina xanje na dauko ki,baxan bar kowa yaje dauko Amarya ba sabida kananun maganganu………kinga Yarda Rayuwa ta juya maki Nooriyah na yarda dake a koina xaki shiga ki kama kanki.”hawaye taji sun cika idonta batasan dame xata sakawa Ammah ba irin kaunar da ta nuna mata.,har fargabar take Ranar da Auren su na karya xai kare da Aliyu waxeer……daga lokacin kuma Ammah xataji ta tsaneta,Tare da driver da Ammah suka nufi gidan Hajia saudah,da hannu biyu Hajia saudah ta tarbesu dama Ammah ta fada mata ko wacece Nooriyah itama hajia saudah ba karamin tausayin Nooriyah din taji ba,
    Ammah Bata jima ba tayi masu sallama har bakin mota hajia saudah ta rakata Ammah na Kara yimata tuni akan Nooriyah ta rika shan tsumin da ta taho mata dashi kafin Ranar daurin Aure ,
    Hajia saudah tace insha Allahu…..Ammah tayi mata godia driver yaja motar..

    Thank you.

  • Waminal Hoob 7

    Waminal Hoob 7

    Waminal Hoob_* 7…

    PAID BOOK
    Free page.

    _Asmy b Aliyu_

    Baki jin hausa ne??”Ya fada sounding so very harsh,malam meye matsalarka da hijab Dina.”itama tayi Maganar cike da gajia da al’amarin Aliyun,
    Fisgota yyi yana huci yake fadin ni kike fadawa magana..”Kallonsa take a tsorace ganin yarda ya rikota ,kokarin kwatar kanta take Amma ta kasa shaye da toka yake fadin”kin san cikin Rules dinmu bbu gardama karki yimin Rashin kunya ya fada yana saka hannunsa yana cire hijab din jikinta duka,wannan karon riga da skirt ne na material ajikinta kalar pink ,kallo daya yayiwa kayan yasan na batool waxeer ne .Dan ita kadai ke saka ire-iren waya’nnan dinkunan,tsaki yaja sosai kayan gaba daya basuyi masa ba duka sun fito mata da halittar jikinta,ki canja kaya gani a bakin kofa ina jira…….”Ya fada yana barin dakin,da kallo tabisa cike da mugun Jin haushinsa,wasu kayan ta shiga dubawa black Abaya ta fidda ta saka gamida Rolling din mayafin akanta samun kanta tayi da fesa turare tana fita sukayi ido biyu dashi,
    daure fuska tayi shima Fuska bbu walwala yayi gaba tana binsa a baya.gaba dayan su kallo ya dawo kansu,
    Wara ido batool waxeer tayi tana kallon yayan nata ,ina ya samo wannan black beauty din.”laylah sai bin Nooriyah take da kallo,har suka karaso cikin dinning Area din.da sauri batool ta karaso gabansu ta kama hannu Nooriyah ,tana murmushi take fadin Yaya ina kasamo wannan kyakkyawar.”Yaya itace wacce xaka aura??”Gaskiyya tana da kyau ,batool waxeer ta fada tana wani rungume Nooriyah ,toh saketa haka mana jamata kujuera ta xauna.”Ammah ta fada tana kallon Batool din,
    Murmushi batool tayi tana jawa Nooriyah seat ta kusa ga Aliyu waxeer,ta russuna cikin girmamawa tana fadin barkar ki da xuwa cikin familyn waxeer.”Batool waxeer ta fada sounding so very happy,wani irin Abu ya tsayawa Layla a wuya.sai murmushi take kwakwalowa ,bata san meyasa tun farkon ganinta da Nooriyah taji Bata sonta,har ga Allah tasan tafi Nooriyah komai sai kamar tana ganin kamar ba haka bane,tana son wani ya fada mata Nooriyah tafita komai .kayi serving din matarka ka tambayeta mexa taci.”da ido yake bin Ammah da kallo tamkar da wani yare ta fada masa hakan,
    dan russunawa yayi murya can kasa yake fadin”tell me mexaki ci??”Kur idon laylah akan su ,sai taga sunyi mata wani irin kyau.har sai taga Aliyun yafi Khalil waxeer iya kula da macce.”Abunda xaka ci shi xanci ta fada tana kallonsa,daure fuska yyi ganin ta gama Raina sa.ganin ido akansu yasa baice komai ba ya shiga serving dinsu plate daya yayi masu,sakin baki da ido batool waxeer tayi tana sakin wani irin blushing.bata taba ganin yayanta yana tarairayar macce ba irin yau,ko Areefa Mansoor da yake fadar yana so bai Bata irin wannan kulawar,
    Da ido kurum Nooriyah ke binsa me Aliyu waxeer ke nufi??”Yana nufin agaban Ammah xataci Abinci tare dashi,muryar Ammah taji akanta tana fadin”kici Abinci Mana Nooriyah ,ta Yaya xataci Abinci plate daya da Aliyu waxeer”.suna hada ido ya wani ware mata ido gamida bude mata hannuwa,duk Abunda suke a idon laylah sai taji gaba daya ta tsani Abincin,wani irin kishin Nooriyah yaxo ya tsaya mata a xuciya ,idan batayi da gaske ba Nooriyyah xata xama best daughter in-law a wajen Ammah ,taga yarda Ammah ke wani rawar kafa akanta….A hankali ta Mike tsaye ,ta subbaci Khalil waxeer gefen kuncinsa tana fada masa ta wuce sashensu kanta nayi mata ciwo,nan ta juya tana yiwa Ammah sai da safe.ita dai Ammah binta kurum take da ido ganin yarda yanayinta ya canja lokaci daya,gefen Nooriyah mamaki take taya Layla xata subbaci Khalil waxeer agaban surukarta?”
    Nan laylah ta juya tabar parlon da sassarfa ,shi dae Aliyu cin abincinsa kurum Yake,hakama Khalil waxeer sunaci suna hirar business dinsu,
    Ammah itama ta Mike ta koma parlor har lokacin Nooriyyah takicin komai, Khalil ya kalleta yana fadin kici Abinci plz kibar biyewa Aliyu shegen cin tsiyane dashi ,xakiyi aiki sosai a wannan bangaren.”da sauri Aliyu ya kalli Khalil waxeer yana dakune fuska.dage gira Khalil yayi yana fadin”na fadi karya ne.”Kusan lokaci daya Aliyu da Khalil suka Mike suka bar dinning area din,ya rage daga ita sai batool dama batool ta matsu subar dinning din,ta dawo kusa ga Nooriyah tana murmushi take fadin”Aunty noory taya kika sace xuciyar Yah Aliyu haka?”murmushi kurum Nooriyah tayi taki cewa komai,Haka batool ta shiga janta da labari sama-sama take Bata Amsa,bbu laifi ta Dan sake da batool,sai kusan 10 sukayi sallama da batool kowa ya nufi makwancin sa,washe gari Mai gyaran jiki taxo ta fara yiwa Nooriyah gyara ,kusan kwana 4 Aliyu baisa ta a ido ba gata bangaren farhaan ya damesa ya hadasa vedio call da Nooriyah.Ammah taki basa damar hakan,
    Tace baxasu hadu ba sai ranar da xasu hadu wajen sakasa lalle.haka Aliyu yyi xuciya ko parlon Ammah ya daina shigowa,bangaren kayan da Nooriyah xatayi amfani dasu na hidimar biki tayi magana da laylah ta damka komai a hannunta,cike da kosawa da xance laylah ke fadin”Ammah ki samu wani ki basa banda lokaci Kuma duka masu yimin dinkuna basa da Alkawari kar axo asamu matsala.”tayi Maganar in I don’t care manner.murmushi kurum Ammah tayi tana fadin bbu komai xata samu wani,karshe batool ta damkawa komai ita duka ta xabarwa Nooriyah din kalar dress din da xatayi Amfani dasu,da aka kawo kayan Ammah ta yaba sosai da hakan,acan bangaren laylah kuwa bincike takeyi sosai taya Aliyu waxeer ya yarda xai auri wannan Yar kauye marar wayewa wacce,da alamar batada ilimin boko ko kadan.”tasan wannan bashi ne mafarkin Auren Aliyu waxeer ba,tayi ta Kiran lambar Areefa Mansoor a kashe ko xata samu karin bayani akan hakan ,Areefa Mansoor kawarta ce ta sanadiyarta suka hadu da Aliyu waxeer.Yarda tasan Areefa Mansoor haka kawai baxata barwa wata Aliyu waxeer ba.yarda take mafarkin samun sa,tasan akwai dalilin wannan Auren dalilin takeso taji ko Ammah xata daina wannan Rawar kafar Akan Nooriyah…..

    ASMY#??

    Haske Writer’s Association#
    [9/15, 6:11 PM] Asmy Mom Aydah??: *

    _Waminal Hoob_* 8….

    PAID BOOK
    Free page.

    _Asmy b Aliyu_

    Yau laraba ta kasan ce yauce Ranar da xaa saka Nooriyah lalle itada Aliyu a kaidar xuri’ar waxeer amarya da Ango xasu saka fararen kayan,A samu fili babba ayi decorating din wajen,a rubuta sunan Amarya da Ango,dangi amarya da na Ango xasu xo daya Bayan daya su shafawa Amarya lalle hakama Ango a hannuwa da kafafuwa ,hadin lallen xaayi na musamman xaa xuba turarruka aciki.idan angama familyn Ango xasu xaunar da Amarya ta buda babban mayafinta su rika xuba mata kyauttukka,da xarar an gama xaa kawo Abinci Wanda uwar Ango xata dafa da hannunta Ango ya ciyar da Amaryarsa,ana daukarsu pics ana yimasu vedio ,da angama wannan daya daga cikin dangin Amarya xasu tsaya tsakkiyar fili da Amarya,shima Ango yaxo ya tsaya sai ta hada hannayensu wuri daya tace ga amanar Yar uwarta nan tabasa ,yay mata Alkawarin sai mutuwa xata rabasu .shima mahaifiyarsa ko Yar uwar mahaifinsa ,
    Xatace sun dau Alkwarin bbu Abunda xai rabasu sai mutuwa….idan Angama wannan kanwar mahaifin Ango xata dauki amarya na kwana daya,tayi mata wanka da Ruwan lalle,
    Ta Kara fahimtar halinta shin yaronsu ya dace da mata ko akasin haka,sauran Abunda xai biyo baya event’s ne idan kana da Ra’ayi xaka iyayi….sai Kuma Ranar daurin Aure da an daura aure wakilin Ango xaa kawo masa Amarya ya fiddo da sarkar xinari ya baiwa Ango ya sakawa Amaryarsa ,shi kenan ta xama daya daga cikin xuri’ar waxeer ,Wanda in har aka auri macce acikin xuri’ar waxeer xaa ganta da wannan sarkar ta xinari ,duk hidimar da xaayi baa canja sarka itace dai xaa gani a wuyanta,
    Sai idan acikin gidanta tayi ra’ayin canja wata Dan yiwa mijinta kwaliyya,amma in har xaa yi wani taro acikin xuri’ar waxeer dole ta saka sarkar xuri’ar waxeer ta Aure….
    A gidan yayan mahaifinsa xaayi event din saka lalle,wato gidan kabeer waxeer ,Wanda shi kadai ya rage masu namiji sauran matane su biyu ,hajia Ramla waxeer sai Fatima waxeer wacce itace auta Kuma dukan su suna da Aure da ya’yah Ramla a sokoto take Auren wani hamshakin Mai kudi,sai Fatima dake Aure a zamfara gusau itama dai babban Dan siyasa ne take Aure,Wanda idan suka xo basa sauka gidan yayunsu maxa,gidan iyayensu suke budewa su shige suda Yayansu,sai dai kawai suje su gaisa da yayunsu. Wanda kusan iri dayane da na Yaran,Babu Abunda bbu ciki na Rayuwa….
    “Ya kamata yanxu ace Amarya ta iso hajia Amina ta fada wacce itace matar kabeer waxeer ,itama tana da manyyan ya’ya maxa da mata Wanda matan sunfi yawa.”ummi toh ki Kira Ammah a waya Mana.”daya daga cikin yaranta ta fada Mai suna Fauxiyya itama baa dde da aurenta ba har ga albarkar ciki,
    Hajia Amina tayi dialling lambar Ammah,bugu daya ta dauka,na jiku shiru ne Ammah lafia kuwa??”gamu nan xuwa kin San halin yaronki shiya Bata Mana lokaci,acan bangaren Ammah kuwa wata kawarta ta Kira agefe hajia saudah tace mata taje a matsayin yayar uwar Amarya ,da mamaki hajia sauda ke fadin ita Amaryar Bata da dangine??”cikin sanyi murya Ammah ke fadin marainiyya ce saudah xan warware maki komai idan aka gama,sauke ajiyar xuciya hajia sauda tayi ita ta fita da Amarya har xuwa compound din gidan katuwar jeep dake fake a wajen ,ita ta budewa Amarya ta xauna itama ta xagaya ta xauna driver ya jasu,Kusan gidajen manne suke da juna,
    Mutane har sun fara taruwa sai kade-kade akeyi ,ganin mota na shigowa Yammatan gidan suka nufi motar da gudu suna shewa kowa so Yake yaga matar Aliyu waxeer……Ummi ce ta bude bangaren da Amaryar take ta fito daita Ahankali ,nan suka gaisa da hajia saudah wacce ummi ba kowa ta sani ba ko acikin kawayen Ammah ,Dan haka Bata shaidata ba.Su suka rika Amarya har xuwa maxauninta,Bata Dade da xama ba saiga Aunty’s din Aliyu waxeer shima sun rakosa,wato kannen mahaifinsa.shima yana sanye cikin shadda fara Kal ,Amma kallo daya xakayi masa kasan baya farin ciki da wannan Auren sai yanxu yake da ya sanin biyewa Besty yasan Yarda Auren gidan waxeer yake.Aunty Ramla ce ta bude fuskar Amarya sai fadin take “Masha Allah Allahumma barik Alaekhi” .Aliyu ka iya xaben macce har taso tafi matar Khalil kyau fari kawai xata gwada mata.daria akasa Banda Aliyu da ya wani dakune fuska,
    Nan akaxo daya Bayan daya ana shafa masu lalle,
    Laylah waxeer ce karshe,Aliyu yana kallon yarda take wani babbata rai da alamar tana taya kawarta kishi,murmushi kurum yyi yana ganin irin kallon da take bin Nooriyah dashi,Bayan Angama saka lalle ta xauna ta buda mayafinta aka rika saka mata kyauttuka harda kyautar mota,Nasir waxeer ya Bata Wanda shine babban da awajen kabeer waxeer.laylah bakin ciki tamkar xai kasheta ,itama A aurenta kyautar mota yayi mata,russunawa Aliyu yayi dai-dai kunnenta Yake fadin”karma ki fara Jin ddi duka amshe gifts din nan xanyi,ae fake marriage ne.murmushi Nooriyah tayi tana fadin ,Nima basa gabana Mr.Aliyu waxeer inhar xan rayu tare da Farhaan Dina acikin Aminci.”na yafe wannan kyalkyalin”.daure fuska yyi yana fadin xan Aure ki Kuma kike fadin wani naki. A gabana “Ya fada da wata irin murya da mamaki take kallonsa,sai ya dauke kansa,haka aka cigaba da hidimar saka lalle har akaxo Wurin da Ango xai baiwa Amaryarsa Abinci abaki.dakyar ta yarda yabata sabida kunya,haka aka rika daukarsu pics,wasu suna ganin kunyarta ta burgesu ,wasu Kuma akasin haka.suna ganin Rashin wayewa ce kurum sai Kusan 2 Aunty Ramlat ta tafi daita bangaren da suka sauka,Ruwan wanka ta hada mata masu hadin turarruka na musamman,da Ruwan lalle aciki tayi wanka ,tana fitowa daga wanka tana tsane jikinta da towel sai ga Aunty Ramlat ta shigo dauke da katon tray ta aje a tsakiyyar carpet ,wata irin kunya ta rufe Nooriyah ganin yarda Aunty Ramlat ke kallonta tana sakin wani irin blushing ita har ga Allah taji tana kaunar Nooriyah tun farkon ganinta,Bata San meyasa take Jin kaunar yarinyyar kamar Aliyu waxeer ba.tana son macce Mai natsuwa da kunya ,sabanin matar Khalil waxeer Wanda idonta ya gama budewa da wayewa.tana ji ajikinta Aliyu yyi dacen macce ta gari a wannan bangaren,wasu irin mayyuka Aunty Ramlat ta turawa Nooriyah agabanta tace ta shafa ,bbu musu ta rika dibar mayukkan tana shafawa ,sukan su wani irin sirrukkan kamshine acikin su.Bayan tagama Aunty Ramlat ta Mika mata wata plain gown kalar sararin samaniya ,juyawa tayi ta nufi toilet da sauri Aunty Ramlat ta dakatar daita.ki saka abunki Anan Nooriyah Sam -sam ban yarda ki daukeni matsayin suruka ba.kin ji kou.”daga yau ni kawarki ce kuma Auntyn ki ,xaki iya fada min dukkan damuwarki karki ji komai keda Aliyu duka ya’yana ne ,ko acikin ya’yan Yan uwana Aliyu shine Fav Dina …..Kaunar da nake masa Mai girmace plz kibasa dukkan farin cikin da Yake nema,kinyi dace sosai da samun miji irin Aliyu watarana da bakin ki xaki rika yaba kyawawan Halayen Aliyu believe me noory.”Aunty Ramlat ta fada tana kallonta da murmushi a fuskarta,
    Jikin Nooriyah lokaci daya yayi sanyi ,ta rasa mexata fara tunani akai tana ganin yarda mutanen nan suka dauki Auren Aliyu waxeer da muhimmanci fiye da komai ,Ranar da Kuma Auren su da Aliyu waxeer ya kare batasan ya xasuji ba”.kenan xasu rusa dukkan farin cikin su,musamman mahaifiyarsa xasu koma gefe Kuma su cigaba da Rayuwa.juyawa tayi ta koma toilet Aunty Ramlat na kwala mata Kira Bata saurareta ba,
    Kiran Aliyu waxeer ne ya shigo a wayar Aunty Ramlat,juyawa tayi tabar room din tana daga wayar lokaci daya tana fadin my fav….”

    ASMY#??
    Team#NooryAli forever#

    Haske Writer’s Association#
    [9/15, 6:11 PM] Asmy Mom Aydah??:

  • Waminal Hoob 14

    Waminal Hoob*_ 14

    PAID BOOK
    _Asmy b Aliyu_

    Washe gari bata shiga kitchen taya peter girkin Rana ba ,sharar gidan kurum tayi gamida saka Room fresherner,kwanciyar ta tayi a daki har Bayan sallar la’asar bata fito ba,sai Kusan 5 ta fito parlorn turus tayi tsaye a bakin kofa ganin Wanda ke dinning Area Yana cin Abinci xuwa lokacin yyi wanka ya canja kaya xuwa kayan Shan iska ,wata irin sanyayyar ajiyar
    xuciya ta sauke a boye.jin motsi cikin parlorn yasa ya dago manyyan idanunsa ya kalli inda Yake Jin saitin motsin ido biyu sukayi daita ,tana sanye cikin doguwar rigar Bahrain baka tayi Rolling kanta da veil din duguwar rigar,a hankali yaji xuciyar sa na budewa da sabon wani yanayi akan Nooriyah din,ta karaso acikin dinning area tana masa sannu da xuwa da hanya,Yana danna waya Yake fadin”kin samu sauqi kenan??”ya fada batareda ya kalleta ba ,”Alhmdullh kurum ta iya fada dibar Abinci tayi ta koma cikin parlor ta xauna tana ci tana kallon Tv.dake aiki a parlorn ,Har akayi magrib Yana xaune a parlorn shigewa dakin barcinsa yyi itama ta shige nata dakin,
    Basu Kara haduwa ba sai washe gari da safe yyi knocking a kofar dakinta ,fitowa tayi da alamar Bata dde da tashi barci ba.Kallonta yyi sama da kasa,Yana fadin ta shirya xuwa anjima xasu fita shopping Dan sanyi taji aranta dama Kuma xaman gidan duk ya isheta,sai Bayan axxahar suka fita acikin motarsa.duk inda suka wuce sai binsu ake da kallo, shopping yyi Mata na tashin hankali ,suka dawo gida kowa ya shige nashi dakin.A hankali suka fara gaisawa sama-sama Yana samunta a parlor yaxo ya xauna Yana aiki da laptop dinsa Yana Hira daita sama-sama Yana fada Mata taga Amfanin karatu da yanxu baxatayi wannan xaman banxan ba gayanan sai narka kiba take tana axa wasu kumatu.Yana yawan tsokanarta da fadin”Yar baka kin ga Yarda kikayi haske har kin kusa kaini Haske ,Ashe dama kina Haske har haka cikin sati biyu kurum A kasar London…….”sai dai ta kallesa tayi murmushi a hankali suka fara sakewa da Junan su,duk wannan kiyayyar da Yake fadar yana Mata a fatar Baki ne kawai Bai Kai har a xuciyarsa ba.,,ta dayan bangaren farhaan suna waya da akwai Ranar da farhaan ya Kira Aliyu waxeer Yana tambayarsa meyasa Nooriyyah ta canja masa yanxu kodai Yana yimata wani Abune??”nima ban sani ba ka tamayeta Mana.”sai gashi yau Farhaan Shagari yayi masu xuwan baxata a kasar London,malamar ta Linda Wanda Ammah ta bincika Mata baturiyace Yar Asalin Pakistan ce Amma ko Mai na rayuwarta a London Yake ,,bbu laifi tana Dan fahimtar Linda duk da har yau turancin kasar na balain wahalar daita,tasha yiwa Aliyu waxeer complain akan hakan,budar bakin sa yake fadin bbu ruwansa karta hadasa da Ammah.
    Tana kitchen tana hada Abincin Rana Wanda Linda ce ta Bata shawarar ta rika shiga internet da wayarta ta hannu tana serching dishes kala -kala Wanda harda na larabawa akwai Idan ta tsayar da hankalin ta xata iya sosai,ranar farko da tayi hada dinner agidan,wani tsoro ya kamata tun a kitchen ta saka peter agaba yaci yaji yyi ddi cikin harshen turanci yake fada Mata ae tama fisa iya girki,Da Aliyu ya dawo tana kallo yyi serving kansa .har ya faraci ya wani dakune Fuska ,Yana kallonta gabanta taji yyi mugun faduwa shikenan baiyi ddi ba.”yau peter wane irin abinci ne yyi haka??”Yana hango tashin Hankali akan fuskarta,cikin rawar Murya take fadin nifa nayi baiyi ddi bane ??”Yarda tayi maganar tabasa Daria,
    Murmushi yyi wanda ya tsaya mata arai,
    “Kinyi kokari Yar baka.”Ta hade Rai tana fadin bana son wannan sunan.””Ya wara ido Yana fadin ni Kuma Yana yimin ddi,haka ya cigaba da tsokanar ta tamkar ba Aliyu waxeer ba Mai girman Kai da nuna isa,yau ma haka ta kasance ita ke hada masu lunch tareda taimakon peter taji an danna door bell,ta kalli peter tana basa umurnin yaje yaga waye.”ya fita da sauri minti kadan ya dawo Yana fada Mata oga ne shida friend dinsa.”da mmki take ta maimaita Friend kuma??tunda taxo kasar London Bata taba ganin wani Abokin Aliyu yaxo gidan Nan ba…..tana cikin Maganar xuci ,taji an shigo kitchen din kallo yabita dashi na Kusan sakan biyar wandon Jean’s ne ajikinta da Kuma rigarta da ta sauka har kan gwiwarta,sai hula Wanda ana hango tulin yawan gashinta acikin hular.Aliyu ya karaso gabanta fuskarsa bbu wani Annuri Yake fadin”saboda Rashin sanin ciwon Kai xaki tsaya agaban peter haka??”yyi Maganar cike da kishin da baisan Yana dashi ba,
    Kayi hakuri kawai ta iya fada masa,kixo kina da bako tunda kin gayyato min shi a gida bbu sanarwa.”Yana fadin haka ya juya gaba daya yanayin sa ya canja,lokaci daya jikinta yyi sanyi Koda ta fita parlorn Bata ga kowa ba,dakinta ta shige tayi wanka gamida dauro Alwallah tana cikin sallah Aliyu ya shigo dakin ya saka key jikin kofar,Yana tsaye har ta gama sallar.Ya kalleta yana fadin kixo ku gaisa bana son doguwar Hira Kuma da hijab xaki fito,
    Da haka ya juya Yabar dakin farhaan yaxo kenan??”to me Aliyu keyi haka.”sai taji duk Bata ji ddin xuwan farhaan ba,kamar yarda Aliyu din ya fada haka tayi hijab ta saka har kasa,ranta duk a jagule ta fito falon tana kallon farhaan din dake xaune cikin soofas ya xuba Mata ido har ta karaso gabansa,a daddare ta xauna dayan soofa ta kwakwalo murmushi tamkar na dole take fadin”Sannu da xuwa ,
    Murmushin sa Mai kyau yyi Yana kallon yarda ta canja lokaci daya,ya Dan bude ido Yana fadin me besty ke Baki haka my Noor.”Kallon sa tayi Bata ce komai ba sai dai tayi murmushi ,Hira ya Rika yimata tana binsa da ido .da haka Aliyu ya samesu a parlorn ,
    Ganin haka Nooriyah ta Mike ta nufi Kitchen da kallo dukan su suka bita ,dama ta riga da ta gama shirya Abinci ta fito tana fadin Abinci na jiransu ,farhaan sai binta Yake da ido ran Aliyu gaba daya a jagule Yake har suka gama lunch,daki Aliyu yyi shigewarsa itama da hanxari ta Mike xata bar wurin farhaan ya wani fisgota ta fado kansa cike da tashin Hankali take kallonsa xuciyarta na tsananin bugawa cikin rawar Murya take fadin”Farhaan meye haka sakeni Mana,
    Ya hade Rai ,Yana fadin me na maki kike guduna?”gaba daya kin canja ya fada da Dan daga Murya a muryarsa,tana so ya saketa kar Aliyu yaxo ya samesu a haka Amma yaki sakinta ,
    Xuciyarsa na ta fasa gabansa na mugun bugawa ,kar dai Nooriyah ta fara son Aliyu??”da sauri ya kauda tunanin aransa Dan baxai ma yuyu ba,
    Sakinta Yayi ya mike Yabar parlorn cikin bacin Rai ya fice daga gidan juyowar da xata yi sukayi ido biyu da Aliyu waxeer ,kallon da Yake Mata yasa Tasha jinin jikinta.bayan farhaan yabi ,acikin garding ya samesa cikin kujerun da aka kawata awajen ,Yana xaune da fuskar damuwa a fuskarsa.xama Aliyu yyi Yana fadin”meya faru Besty??”iska Mai xafi farhaan Shagari ya furxar da jajjayen idanunsa yake fadin me ya canja Nooriyah haka.??”Mena Mata take wani shareni tamkar Bata farin ciki da xuwana,a baya na maka maganar Noor ta canja baka dauki magana na da muhimmanci ba,,meyasa Mata basu da tunani da tabbas akan soyayya??”na fara shakku akan soyayyar da Nooriyah keyi min.”Ya fada muryarsa na karyewa,
    Xuciyar Aliyu na bugawa da wani irin yanayi da sabon Abu dake xiyarta xuciyar tasa Yake kokarin dannewa,ko xaya mutu baxai taba cin Amanar besty ba.”Kai watarana sai ka koma karamin yaro akan macce ka natsu Dan Allah.”xanyi magana daita ,Amma ko kadan Bata maraba da xuwanka baxai xama hujja ba believe me??”
    Xo muje ka shaki iskan kasar London xuwa anjima xan xauna daku ,ko wanen ku xan tambayesa meye damuwarsa.”Dan sanyi yaji aransa tunda har Aliyu Bai fara sonta ba ,xae yi kokari ya gano hakan a tattare da Noor inhar hakan ya kasance baxai taba yafewa Nooriyah ba,Kuma muddin Yana numfashi a dunia Bata Isa tayi xaman Aure da Aminin sa ba,,koda hakan xai sa ya rasata shima.suna tafe a motar Aliyu Kiran Areefa Mansoor ya shigo a wayar farhaan shagari,,wata irin faduwar gaba ya tsinci kansa aransa yake fadin.’”ita Kuma wannan Jarababbar me xatayi masa da take kiransa,Aliyu ya bude ido da mamaki yake fadin ana ta kiranka a waya baxa ka dauka ba ,tsoro da mugun fargaba suka hade a fuskar farhaan Shagari lokaci daya,maimakon ya dauki wayar kamar yarda Aliyu ya fada sai ya kasheta duka.sai Bayan ishaai suka shigo gidan bbu kowa a parlorn sai kamshin Room freshener dake tashi ya hade da sanyi Ac. Aliyu kallon dinning area yayi ,kafin ya maida kallonsa kan farhaan .
    Abinci ko wanka??”wanka dai na gaji ,master bedroom din Aliyu ya shige Yana rage kayan jikinsa.kai tsaye ya tura kofar dakin nata, tana xaune kan sallaya, ba sallar take ba,Amma tayi nisa cikin tunaninta kamshin turarensa da taji tayi sauri dagowa gamida xuba masa fararen idanunta ,shima kallonta yayi kafin ya janye idonsa cikin nata .rufe kofar dakin yayi ya karaso ya xauna cikin soofa ya maida hankalin sa kanta,meyasa kika canjawa farhaan Shagari lokaci daya??”Tambayar da taji ya jefo Mata kenan,danne xuciyarta tayi tana fadin shiya fada maka haka.”Ya girgixa Kai Yana fadin Bai fada min ba ,na lura da hakan ne.”ki shirya ki saka hijab dinki kije kibasa hankuri , he’s ur boy friend Kuma shi din abun so ne a wajenki,,ita dai batace komai ba har ya fice daga dakin tabisa da kallo cike da Jin haushin Farhaan akan me xai Kai karar ta.wannan ma karon hijab ta saka ta fita parlor fuskarta bbu wani walawala tana ta Zama a parlor sai gasu sun fito daga dakin,ko wanen su cikin kayan Shan iska kallo daya ta masu ta dauke Kai ta rigasu Isa dinning area .ta xuba Abunda xata iyaci ta fara ci ba tareda tayi serving ko wanen su ba ,Aliyu duk Yana kula da yanayin ta ,cin Abincin ta kawai take duk ranta a jagule ,
    “Irin wannan cin Abinci haka ae sai ki kware my luv.”Farhaan yayi Maganar cikin kwantar da Kai hararar sa tayi taci gaba da cin Abincin ta,ta riga su gama cin Abincin tabar dinning area din.parlor ta koma tayi xamanta ,
    Aliyu duk yana kula da yanayin ta farhaan binta kurum Yake da kallo tamkar wani Wawa,shima dawowa yayi cikin parlorn ya fuskance ta da dukkan kwarin gwiwarsa Yake fadin Laifin me nayi maki kike gasa ni haka.”
    da dukkan idanunta take kallonsa take fadin”Canjin me ka gani a tattare Dani ,meyasa xan canja maka Kuma.”
    Yyi murmushi Yana fadin shikenan ya wuce kaina bisa wuyana,.”Besty ya fadamin Ammah ta hanaki xuwa jami’a ke Kuma kika biyewa Ammah ko.”wannan ba matsala bane farhaan meye na sauri ko yanxu akwai damar haka agaba,Idan munyi Aure sai nayi karatun.”Kalmar da ta shiga cikin kunnen Aliyu waxeer ke Nan,
    Wannan kalmar ta kusa rabe masa xuciya gida biyu,,kallo daya yyi masu ya dauke Kai da sassarfa Ya nufi dakin barcinsa Yana kokarin danne wani irin kishi da ya cika xuciyarsa,dauriyar duniya Aliyu waxeer ya tattaro yyi lokacin da ya shige dakin barcinsa Yana Rufo kofar gamida jingina kansa jikin kofar xuciyarsa na wani irin tsalle tamkar xata fito daga kirjinsa sunayen Allah kurum Yake fada aransa ko xai samu sassaucin Abunda Yake ji Akan Nooriyah,yanayi Yana duba agogon dake daure a damtse hannu nsa,mintunan da suke tare yake kirgawa Yana Jin sautin dariar Farhaan shagari da alamar hirar tayi masa ddi.”Wata xuciyar ta fada masa karka ga Laifin Nooriyah tana da shiga Rai,ita Kuma ta biye masa ta saki Baki tana yimasa daria kenan ta manta matsayin ta.”Ya fada aransa kishi na cin xuciyarsa,car key ya dauka Yana fadin bari na bar masu gidan kar su konani tun ban gama tafasa ba…..”Farhaan da mmki yake tambayarsa inda xa yaje wannan daren,karya ya masa wani Abokin kasuwancin sa xai gani yanxu gobe xai bar London ,Yana fada masa haka yabar parlorn batareda ya kalli inda Nooriyah take ba,Kusan 9 ta fadawa farhaan barci takeji xata je ta kwanta.tana wucewa dakin barcinta,ya shige Master bedroom din Aliyu waxeer,ya kunna wayarsa saiga sakon Areefa Mansoor ya shigo ,kiranta yyi tana dagawa ta fara xuba masa Ruwan balai tamkar xata canyesa ta wayar.yaushe ka fara yimin karya Besty??””Ya dakune Fuska Yana fadin karyar me nayi maki,
    Wata Daria tayi a wayar.ka hanani xuwa Cyprus na Kai maka xiyara ,kaki xuwa ka kawomin xiyara Amma sai gashi kaje ka kaiwa budurwarka xiyara a kasar London.”gabansa na faduwa yake fadin duk waya fada maki haka??” bakin da naji baxai yi karya ba,
    Kasan baxan iya jure Rashin ka na kwana biyu ba,baka ji yarda nake ji bane kasan Aliyu Kuma baya son wannan harkar kansa a duhu Yake har yau,
    Nayi booking jirgi ka xuba ido xuwa ko Yaushe xaka ganni,
    Wannan tafiar takace Kai kadai bata Aliyu waxeer ba.”cikin Tashin hankali Farhaan Shagari ke fadin Baki da hankali Areefa,ni dae na gama magana bana Jin tsoronka karka yimin Ihu!””……Jin yyi ta kashe wayar Yana kokarin kiranta ta kashe wayar gabaki daya,wani irin xufa Yake hadawa yasan Areefa Mansoor ba wani hankali ne daita ba tunda ta fada da gaske xata xo.”Wai meya ma kaisa fara wannan harkar da Areefa Mansoor??”wane irin Rashin hankali ya tafka haka.”sai Kusan 11 Aliyu ya shigo gidan ko kallon dakin Nooriyah baiyi ba,yyi mmkin idon farhaan biyu har lokacin, Ya fara rage kayan jikin sa yana fadin”Baka kwanta ba kenan,yanxu nake Shirin kwanciya ya fada cike da Rashin
    walwala a muryarsa,
    Tabe Baki Aliyu yyi gamida shigewarsa toilet…

    Littafin waminal Hoob na kudi ne#500
    Account Details
    0004157137
    Jaiz Bank
    Asma’u Buhari Aliyu
    Katin wayar MTN. ta wannan lambar#
    09060259200
    Shaidar Biya ta wannan lambar
    08086207764#

  • Waminal Hoob 1

    Waminal Hoob 1

    Waminal Hoob_* 1

    PAID BOOK
    Free page.

    _Asmy b Aliyu_

    A fusace ta nufi stairs da axamarsa ya cimmata gamida fisgota ta fada kan jikinsa,farar fuskarta ya kurawa ido.Wanda yana daya daga cikin Abunda yakeso ajikinta,haka Allah yayisa A rayuwarsa yana son farar Macce.lokaci daya ta fara Tara kwallah a idanunta,kara narke mata yayi .cikin fushi take kokarin fisge hannunta,daukarta yayi gaba dayanta ya nufi part dinsa daita,kafa yasa ya tura kofar dama a bude take bai direta koina ba sai akan farar soofa ,kokarin mikewa take .ya xuba mata blue Eye’s dinsa,Wanda yasan sune weakness dinta.Hannu ta saka ta koina tana kai masa duka take fadin”I hate you .”I hate you Aliyu waxeer!!””ta fada da dukkan karfinta hawaye na Rolling akan face dinta,Dora kanta tayi akan kafadarsa tana kara volume kukanta,Sam shi baya jure kukan macce ko kadan,ya tsani kuka…..
    Ya rike kyawawan hannayenta yana murxawa a hankali ,cikin sanyi muryarsa yake fadin. “I miss you my girl,
    ” you did not tell me xaki xo ae.”ya fada yana Dan daga kafada gamida Dan buda kyawawan idanunsa,wata irin harara take yimasa da fararen idanunta Wanda suka fara canja kala.sau nawa Haidar?””Har sai yaushe xaka daina wahalar da xuciyana.”muna gari daya,na dawo Hutu ka kasa xuwa ka dubani.sai nice xan rika biyoka naku gidan,nice xan rika daga waya na kiraka nice mai xuwa hira gidan Ku.wannan wace irin soyayyace marar tsari.?”ta fada cikin sanyi murya,Dan karamin bakinta ya kaiwa kiss ya saki murmurshi gefen kumatunsa duka suka lotsa..fuskarta ya kara kaiwa kiss yana fadin”Am sorry my girl friend my one and only.”ke kinsan baxan shareki ba haka kurum ina busy ne kuma Bestyna ya shigo gari ,harara ta shiga watsa masa cikin shagwaba take fadin”Dama nasani ka fison Farhaan Shagari akaina,da karfi ya shiga fadin “Nooo kowa matsayinsa daban,duka ina sonku wlhi,ya fada yana Jan kumatun ta tamkar wata Bby haka ta rika turo masa kyakkyawan bakita.ya mikar daita tsaye yana fadin mu fita yawo yau tym dinki ne….

    ? ??
    Baki sake Mami ke binsa da kallon takaici,kallonsa ya mayar kan daddy Wanda yaki yace komai.sai ma jarida da ya dauka gamida saka farin gilashinsa mai karawa idanunsa gani,salati Mami ta shiga xubawa tana fadin anya kuwa kanka daya Farhaan?”tayi maganar a mugun fusace,shuru yayi batare da ya kalli Mami ba…….Ya rabbi Allah yasa mafarki nake,Allah yasa ba gaskiyya bane Mami ta fada tana rufe idanunta Dan tabbatarwa,tana buda idanunta taga farhaan xaune agabanta.” Farhaan gobe ka shirya kayanka kabar kasar nan,
    Wlhi baxaka kunyatani ba,shekarar ka talatin da biyu fah.”yayunka duka mata ne,kaine kawai nake dashi da xan jingina a kafadarsa nayi alfahari dashi a matsayin Namijin da ya fito daga cikin tsatsona,Farhaan ba yanxu nakeso kayi aure ba,,ka fahimta ina son ka xama wani Abu a rayuwarka,ina son ka kasance cikin manyyan attajiran da xaa rika gogawa dasu a kasar nan,me malami ya fada maka.”kasan dai halin dangin ubanka kou.”bawani kaunata sukeyi ba,kuma duka Rabin su a karkashin companyn mahaifinka suke aiki,,Allah kadai yasan cutar da ake yi masa.”idan ma Hajia Yasira taji baxata ji ddi ba,ji yarda take son kaxama surukinta ,nan ba da jimawa ba Idan Alh.Azzex Ali ya hau kujerar governor shi xaa tsayar da ixinin Allah.,Allah kadai yasan irin alkhairin da xamu samu.”ka mayi shuru da wannan maganar kar aji a waje ayi mana daria Dan Allah.”ya dago da idonsa da suka kada sukayi ja yana kallon maminsa yana mamakin ta yana karawa,
    Akan wani ra’ayinta marar tushe…..kiyi min rai Mami,ya fada da wani yanayi a muryar sa gidan su noor sunce ta fiddo da miji Idan ba haka ba xasu aura mata duk Wanda sukaga dama.”su Aura mata mana me ake da gayyar talakkawa ,dama baka rabu da wannan matsiyaciyar yarinyar ba,,idan mafarki kake ka farka.tana nuna sa da yatsa cikin natsanin fushin da bai taba gani a idanunta ba take fadin”idan kana son kanka da lafia Farhaan shagari ,inhar ni na haifeka na dau cikin ka watanni Tara nayi nakudarsa,karka kara kawomin xancen yarinyyar nan,batayi Isar da xan hada jini daita ba.”Farhaan shagari tun daga kansa har yatsan kafarsa yake hada gumi duk da sanyin split dake ratsa falon,haka Mami ta tsallake sa cikin fushi tabar masa falon…Ya juya kan Alh.Omar shagari Wanda har lokacin yaki yace komai akan xancen……dajan duwawu ya karasa gaban mahaifinsa ya rike kafafun sa gagam,hawaye na xubar masa yake fadin”Daddy kayi min rai idan ban samu Noor ba mutuwa xanyi wlhi.”ka fahimtar da Mami hakan Dan Allah,shafa kansa daddy yayi yana fadin”kayi abunda mahaifiyarka keso Muhammad, nan shima daddy yabar masa falon,dafe Kansa yayi Wanda ke baraxanar yimasa ciwo,ya rasa waya’nne irin iyaye Allah yabasa masu akidar nasara……

    ???
    Wani mugun kallo Aliyu kebin Farhaan dashi,Ahankali ya shiga girgixa kai yana sakin murmushin da shi kadai yasan ma’anar sa.da alamar bakada hankali Farhaan ka samu tabin kwakwalwa,
    “Ni kake tunanin naje na auri yarinyyar da kake so har na tsawon shekara daya.”Aure ta kurane Farhaan Shagari ko kusa ban kawowa kaina Aure nan kusa ba,,kaima kaji xaka iyane yarinyya duk tabi ta wani shanyeka sai kace manyya.” Kama daina wannan maganar ko nayi fushin da ban taba yimaka irinsa ba,ya fada so pissed up yana hade rai,Farhaan ya lankwasa kai yana kallon Abokin nasa da idonsa da suka fada lokaci daya,
    “Nasan nooryna bata cikin kalar matan da kakeso ,nasan ba ajinka bace,nasan baka sha’awar (BAKAR MACCE).”
    Nasan ka nasan natsarinka Mr.Aliyu waxeer galadima.Abokin ka xakayiwa wannan alfarmar,da xarar na kammala masters dina xan dawo gareta muyi Aure.”Nasan karatuna shine burin Mami ni kuma burina na mallaki Noor,xan mallakawa Mami duk abunda takeso.”nima xata barni na Rayu da wacce nakeso,xan saka Noor makaranta bayan Auren Ku ina son Noor ta samu ilimi sosai,nasan baxaka ci amanata ba xaka kular min da Noor fiye da yarda xaka kula dani idan ina kusa.”girgixa kai Aliyu ya shigayi yana fadin ka haukace Farhaan wallahi ka haukace…!”

    PAID BOOK
    ASMY#??

    Haske Writer’s Association #
    [9/15, 6:11 PM] Asmy Mom Aydah??: *_Waminal Hoob_* 2

    PAID BOOK
    Free page.