Hausa NovelsWaminal Hoob Hausa Novel

Waminal Hoob 15

Sponsored Links

_*Waminal Hoob*_ 15

PAID BOOK
_Asmy b Aliyu_

Doguwar rigace a jikinta ta less kalar milk da ratsin lemon green ajikin less din sai mayafin kayan ,ko powder bbu akan kyakkyawar fuskarta dama Kuma haka Allah yyi ta bamai yawan son kyale-kyale bace.
Sai mayukkan da take amfani dasu Wanda basu da surkin karawa fata haske ko kadan sai dai suna gyaran fata.kallonta kurum Yake har ta karaso cikin parlorn da murmushi a fuskarsa shima yyi kyau har ya gaji,salute yyi agabanta Yana fadin”Anya irin wannan kwaliyyah haka xan iya tuki kuwa.”Tayi murmushin da ya tsaya iya fatar bakinta ,tana Dan bude ido take fadin”ko mu fasa fitar,shima murmushin yyi Yana fadin mutafi kawai ganinki kurum Yana sakani nishadi,
Kitchen ta nufa tana fadawa peter yau Linda baxata xo ba,sabida bakon da suke dashi ta fada masa ko Mai xaiyi masu na lunch …….peter ya bita da ido Yana mmkin kwaliyyar da tayi Kuma da Abokin ogansa xasu fita,sai yaji Yana Jin haushin kwaliyyar haka ta dayan bangare Yana taya ogan nasa kishi,
Kallo ya bita dashi har ta fice daga kitchen din,dama Aliyu Yabar masa car key ko Yana bukatar fita wani wajen,tunda ya kanxo kasar ba bakon wajen sa bane ,sai da suka hau titi ya Kira Aliyu wanda ya fice tun safe daga gidan ,
Tun jia da dare rabon Nooriyah dashi.mun fita yawo munata jiranka kaki dawowa…….”Kaida wa??”taji Aliyu ya fada ta cikin wayar,Farhaan ya bude ido Yana fadin nida Nooriyah mana.”Allah ya taimaka ya fada Yana kashe wayarsa ,acan bangaren Aliyu waxeer Jin yyi xuciyarsa na tafasa tamkar xata kone duka saboda kishi da tashin Hankali ,Idan shi farhaan baida hankali ita Nooriyah fa??”daukar Laifin duka yyi ya Dora akanta ,meya fada maka A wayar?”Nooriyah ta fada tana kallon farhaan dake tuki cike da nishadi,kin San halinsa miskili ne mefa xaice .Shuru Nooriyah tayi gabanta na faduwa,ta fara sanin Halayen Aliyu Dan xaman da sukayi ,ta tabbata Yana can Yana fushi.
Amma ya xatayi bashi ya bada kofar hakan ba,kawar da tunaninsa tayi daga ranta karma yaxo ya hanata sukuni…….sai Bayan sallar la’asar suka dawo dauke da manyyan ledoji Wanda peter ne ya daukosu , xuwa cikin parlorn, farhaan ya juya kan motar Yana fada Mata sai magrib xai dawo,da yake Yana da family friends Wanda suke makaranta acikin London din,wata irin faduwa taji gabanta yyi da suka hada ido da Aliyu waxeer dake xaune cikin parlorn ya daura kafa daya kan daya yyi mugun hade Rai,ko sallamar ta Bai amsa ba shima peter Yana ganin yanayin ogansa yyi ta kansa,Jin tayi jikinta yyi mugun sanyi dakinta xata wuce taji ya daka mata wata irin tsawa gamida fixgota ,,daga gidan ubanwa kike??”tana ganin yarda idanunsa suka koma jaa hawaye suka wanke fuskarta cikin rawar Murya take fadin”Tare da farhaan muka fita.”Wannan karon turata yyi ya shiga ball da ledojin da peter ya dire a tsakiyyar parlorn dafe kansa yyi dake neman tarwatsewa sabida kishi da xafin xuciya,wani irin numfashi ya shiga ja Yana dafe da kirjinsa tamkar xai shede Mata a wurin cike da tashin Hankali ta karaso gabansa tana rikosa wani irin turata yyi da karfi yana fadin”don’t touch me.”
Yana gargadinta da babbar Murya Bata taba ganin tashin Hankali irin wannan ba,da wani irin yanayi ya nufi dakin barcinsa Yana bugo kofar,itama da gudu ta nufi nata dakin.kan bed ta fada tana Fashewa da wani irin kuka……….”Shin Yaya Aliyu yakeso tayi ne,duka sun sakata a tsaka idan ta kaurace ma wannan ,wannan ya nuna ba haka ba
Gaba daya taji duniar ta Mata xafi,ko Bayan magrib da farhaan ya dawo kiranta yyi a waya ta fada masa kanta na ciwo.da haka ta kashe wayar duka Bata Kara saka su a ido ba sai washe gari,
Ta fito xataje Kitchen da safe ta samesu a parlorn suna break fast suna Hira dukan su ,su biyu din suka bita da ido cike da kulawa farhaan ke fadin”ciwon kan ne har yanxu ko sai munga likita,tana nufar kitchen take basa amsar ta samu sauqi,acikin kitchen ta tsaya tayi break fast dinta,sai ga farhaan din ya sameta a kitchen din,Hannu ya Kai xai taba goshinta tayi saurin janyewa tana hade Rai .ya wara ido Yana fadin xanji ya yanayin jikin naki Yake.”Nagode na samu sauqi tana gama Abunda take ta kallesa tana fadin bbu Abunda kake so xan koma daki,ya langabar da Kai Yana kallonta Yake fadin.”ke kurum nakeso ,xanje nayi wanka ta fita tana nufar kofa,Koda ta fito parlorn still Aliyu na xaune a parlorn ta kallesa ta dauke Kai da sassarfa ta nufi dakinta yabita da wani irin kallo.tana shiga dakin shima ya shigo dakin ya saka key jikin kofar xaro ido tayi tana kallonsa da mmki jingina Bayan sa yyi jikin kofar fuskarsa har ta Dan fada,shi yyi breaking silent din da fadin”Saboda saurayinki ya kawo maki xiyara ko Yar gaisuwar da nake samu kin watsar,na lura kin ma rainani da yawa ,yyi Maganar cikin kwantar da Murya Yana kallon fuskarta,tamkar jira take hawaye suka fara sauka kan fuskarta A hankali har lokacin Taki cewa komai .Juyawa yyi ya fice daga dakin,Kusan tare suka yini a gida da farhaan ,sosai farhaan din ya damu da Rashin fitowar Nooriyah a daki,
Ya kalli Aliyu Yana fadin”Wai meke damun Nooriyah ne.??”Aliyu yyi tamkar bai jisa ba ,sai da farhaan ya Kara maimaitawa Yana kokarin danne bacin ransa,ni yaronta ne da xan Rika kula da yarda take” .ba kana da kafafuwa ba,kaje ka dubata Mana.”Yyi Maganar cikin Rashin walwala a fuskarsa,
Tamkar jira farhaan yake a basa umurni ya nufi dakin nata da sassarfa da wani irin kallo Aliyu ke binsa dashi xuciyarsa na bugawa,tsaye yyi a kofar dakin sai da ya fara yin knocking kafin ya tura kofar dakin,
Xaune ya sameta da waya a hannunta tana dannawa ,mamaki ya Kusan kasheta da ta gansa tsaye a tsakiyyar dakin daga ita sai Yar shimi da wani shegen skirt da Yake tsage har kan cinyoyinta rarumar hijab tayi ta saka,
Da mamaki Yake kallonta a fusace ya fisge hijab din gamida jefar dashi kasa,da mugun shock take kallonsa ya fisgota ya matseta a bango Yana wani irin jifarta da mayen kallo ,xatayi magana ya Dora yatsan sa akan dan kyakkyawan bakinta da Yake mafarki a kullum,kokarin turesa take ya riketa jikinta har rawa Yake tamkar ba farhaan din da ta sani acan shekararun baya ba,Mai sonta Mai tausayinta haka Mai girmama soyayyar ta,
“Meyasa Noor meyasa kika canja meyasa kike guduna.”meyasa kike xama da hijab aduk lokacin da muka hadu,shi Aliyun haka kike masa.”Ya fada da tsawa cike da matsanacin kishi a muryarsa,sai ga hawaye sun fara ambaliya akan fuskarta cikin rawar Murya take fadin”Farhaan ina da Aure kana so tsinuwar Allah ta hau kaina,, na tambayeka jikina kakeso koni kakeso.”Wata Daria farhaan yyi Yana fadin duka komai naki ina so Noor kina bani haushi .Aduk lokocin da muka hadu saiki xurma hijab,tamkar kinga mugun Abu.”Auren da kike magana Kuma ai contract ne kin manta.”bbu Aure contract a Rayuwar mu ,ko contract ne ya kamata mu kiyaye dokokin dake cikin sa,kirjinta ya kafe da ido Wanda yyi balain daukar hankalinsa dama haka take da manyyan na Fulani,gaskiyya xaya more…turasa tayi da karfi ta saka hijab dinta tabar masa room din duka tana Fashewa da kukan bakin ciki duk taji ta tsani kanta ta tsani wannan Auren tantamar ma soyayyar da farhaan ya Rika nuna Mata a baya take ,wannan sabon farhaan ne Mai kokarin karya dokar Allah Yana kokarin Kai hannunsa jikinta,
Bbu kowa a parlorn acikin garding ta wuce ta hada Kai da gwiwa tana shessheka Jin tayi ta fara tsanar farhaan,ganin irin kallon da Yake bin jikinta dashi da kalar idanun da Bata taba gani ya kalleta dasu ba,ta window din dakinsa yake hangota .Kura Mata ido kurum yyi tamkar Mai son gano wani Abu acikin fuskarta,
Ya lura tunda farhaan yaxo farin cikin ta ya ragu,wata xuciyar tayi saurin kwabarsa da fadin Kai Kuma ina ruwanka.”ae sunfi kusa,karar bude kofa yaji ya kalli farhaan da ya fara hada kayansa da mamaki Yake fadin”ina Kuma xaka tafi??”hotel xanje na kama na lura gaba daya Nooriyah ta canja min koma dai menene xan shawo kan matsalar Yana gama hada kayansa ,
Ya kalli Aliyu waxeer Yana fadin xan tafi da motarka,muyi waya da haka Yabar dakin da sassarfa.xuciyarsa da Yake Jin tayi nauyi tun xuwan farhaan yaji ta fara sauka tamkar an axa masa wani katon dutse,sai da yaga fitar motar farhaan ya nufi cikin garding din.”Yau a matsayin Aboki naxo maki ba matsayin miji ba ,shin meye damuwarki Yar baka.?””kina tareda Wanda ke maki soyayyar tsakani da Allah sai Kuma rikici da damuwa.”Wannan karon ya fada da rauni a muryarsa,ta dago da jajjayen idanunta tana kallonsa,cikin Murya Mai rauni take fadin”ina so nayi maka tambaya Dan Allah.”Idan kana son mutum tsakani da Allah xaka so shine.”ko Dan wani Abu nasa,juya tambayarta ya shigayi aransa Jin yyi tamkar akan shi tayi tambayar,Farin Areefa Mansoor da kasancewar ta kyakkyawa shine Abunda ya fara fisgarsa akanta,daga wannan baxai iya cewa komai. Ba”meyasa xakiyi min wannan tambayar,ka Amsani Dan Allah.”Yana girgixa Kai Yana fadin”Ban San komai ba a wannan fannin gaskiyya,na dauka Idan kana son wani Abu da Allah ya halicce mutum dashi ajikinsa shine soyayyar kawai.”kallonsa take da mugun mamaki,
Kenan ko xaa Dora masa wuka Bai masan meye so ba.”Sai dai wata xuciyar tana fada Mata karya Aliyu yyi Mata, murmushi kurum tayi masa xatayi magana wayarsa ta fara ring,barin wurin yyi ya tsaya can gefe Yana Amsa wayar……….Saukarta kenan a filin jirgi shiya je daukarta bbu wani Bata lokaci suka nufi hotel din da ya kama masu,suna shiga room din da ya kama masu ta wani rungumesa tana fadin”I miss you,wanka Tayi taci Abinci ta saka wasu tsinannun nyt wears Wanda su da bbu duka daya ,ta kalli farhaan dake kwance kan bed yyi xurfi cikin tunaninsa,ta fada kansa tana shafa gashin kirjinsa take fadin”Besty Wai lafiar ka kalau kuwa ,tunda ka daukoni a Air port Naga baka cikin farin ciki.ko kunyi fada da mutunen ka ne??”Bai Bata damar magana ba ya jawota jikinsa ya hade bakinsa da nata,
A daren sun faranta ran Junan su ,haka yasa ya Dan manta da bacin ran da Nooriyah ta dasa masa ,Tun da safe wayar Aliyu waxeer ta tashe sa barci,cikin barci ya daga wayar
“A wane hotel ka sauka ??”jin yyi barcin dake cikin idanunsa na rugujewa a hankali,
Jin tambayar da Aliyu ya jefo masa kallon Areefa yyi wacce ke kwance cikin jikinsa tana sharar barci.kaga ni barci nakeyi kabari xuwa anjima Idan na tashi xan kiraka.”da mamaki Aliyu ke fadin
Barcin da kakeyi shi xai Hana ka fadamin masaukin da ka sauka.”muyi magana xuwa anjima plz Besty.”kashe wayar Aliyu yyi Yana mamakin sabbin Halayen farhaan Wanda Bai yarda dasu ba,shima sharesa yyi ya cigaba da sabgoginsa ,itama Nooriyah tun daga ranar Bata Kara ganin farhaan ba. Haka bbu wayarsa bbu dalilinsa ,itama Bata ga Abunda xai saka ta Kara kiransa ba.haka Linda ta cigaba da xuwa wajenta tana maida hankali sosai ,
Mu’amalarta da Aliyu Kuma girmamasa take sosai da wata irin soyayyar sa dake cin xuciyarta a hankali sai da tana kokarin kwatanta boye hakan agabansa,Saboda kare mutuncin ta da martabarta na Diya macce.sai da Areefa Mansoor ta kwana ukku kasar London suna faranta ran Junan su, itada farhaan sa’anan tayi Shirin komawa Nigeria dama ba Egypt xata koma ba,sun samu hutu.Ranar da ta tafi sai ga farhaan ya Kai masu xiyara a yammacin da ya cika kwana 4 da barin gidan,peter ne ya bude masa kofa,Aliyu Yana cikin soofa din dake xagaye da parlorn Yana turawa Baffa waxeer sako ta email dinsa na cigaban da companyn waxeer ya samu Bayan dawowarsa,Haka kudaden da suka Bata yabi diddigi ya gane ta hanyar da suka salwanta,Laylah waxeer ta account dinta kudin ke shiga Wanda ko Khalil waxeer baida labarin hakan,da Yake duk a karkashin wannan company suke aeki itada mijinta wato (Waxeer motors)duk da ba company daya bane,akwai na kayan sakawa ,,company da ake sarrafa abincin Nigeria , Ana sarrafa wasu ana shigowa da wasu ….. Khalil waxeer shima acikin London din Yake Rayuwarsa sabida company waxeer dake Nan,A tsakanin gidan Khalil da gidan Aliyu ba wani nisa ne dashi ba ko a kafa kana iya takawa ka tafi….sanye take cikin riga da skirt na atamfa tayi Rolling kanta da veill Wanda yyi shige da kayan fitowarta kenan daga kitchen rike da cup glass Mai dauke da sanyayyen lemun inibi acikin sa.dai-dai lokacin da Farhaan ya sanyo Kai cikin parlorn suka hada ido nooriyah tayi saurin dauke nata idon ,ta nufi Aliyu waxeer .dama Kuma Shirin fita suke xai sauketa a wajen saloon,ta ajey masa Akan Dan madaidaicin center table gamida jansa gabansa,dakinta ta nufa da sassarfa batareda tasan Allah yayi halittar farhaan Shagari a wajen ba,Aliyu ya daga Kai ya kallesa
Ya maida kansa kan aikinsa Yana fadin Ashe kana cikin kasar Nan har yanxu.”Farhaan ya xauna Yana kallonsa ya hade Rai Yana fadin,wannan wane irin tambayace tun ranar ka Kara nemana,da mutuwa nayi ae baxa ku sani ba,
Ayi tattaki akawowa mutum xiyara Amma sai wulakancin Yake fuskanta,sosai farhaan ke fada Yana hura hanci Aliyu waxeer ya tabe Baki Yana fadin”Ae bani ka kawowa xiyarar ba da xaka cikamin kunne da ihu matsalarka ce wannan,yanxu ma Shirin fita muke da baxaka samemu ba,
“Xuwa ina kenan?””
Saloon xan kaita ,tunda ka doramin nauyi.Ae tun da gani na hutar dakai ni xan kaita na daukota,wani irin faduwa gaban Aliyu waxeer yyi ya kallesa da sauri Yana fadin”ka kaita ina??Da mamaki farhaan ke fadin saloon din mana,
Shuru Aliyu yyi Yana kallon farhaan din,
Dai-dai lokacin da Nooriyah ta fito dauke da karamar handbag a hannunta.

Littafin waminal Hoob na kudi ne#500
Account Details
0004157137
Jaiz Bank
Asma’u Buhari Aliyu
Katin wayar MTN.ta wannan lambar#
09060259200
Shaidar Biya ta wannan lambar
08086207764#

Thank yhu#
[9/15, 6:11 PM] Asmy Mom Aydah??: _

Back to top button