Duk KarfinIzzata Book 2Hausa NovelsHausa Novels

Duk Karfin Izzata Book 2 Page 24

Sponsored Links

Book 2

Page 24

…. Kallon su Aryan ya fara yi daga sama har kasa kafin ya mai da kallon sa ga sauran sojojin checkpoint ɗin dake nufo su,tsaki yaja tare da komawa ya zauna saman kujerar motar chikin sanyin murya yace “my jidda ya isa kukan nan wai da me kike so ɗaya na jine da wayan nan da suka ɓatamin rai ne ko kuma da kukan ki?” Rage sautin kukan nata tayi chikin shesshekar ta fara magana “yaya Aryan mu koma gida ni tsoro nake ji ban san wajen nan ko kaɗan” yana kokarin yin magana wayanchan sojojin suka iso wajen babban chikin su ya sanya hannu ya damki kwalar rigar Aryan yana faɗin “wuce muje” ɗago kai Aryan yayi yana kallon sojan kafin ya mai da kallon sa saman wuyar rigar sa a razane sojan ya saki wuyar riga chikin tashin hankali ya duka gasa yana faɗin “innalillahi wa Inna ilaihir rajiun Lefternal general Aryan” ba shiri sauran sojojin ma suka zube kasa dan sun san sunan Aryan fuskar sa ce dai basu taɓa gani ba tsaki Aryan yaja kafin yace “kuna kan dai dai ai bakuyi laifi ba in da nine na kama mutun zai yiwa yarinya fyaɗe to da yanzu maganar jana’izar sa ake ku tashi ku koma bakin Aikin ku amma ina son ku sani wanan matatace ba sato ta nayi ba” miƙewa sukayi chikin rawar murya babban su ya ɗan leko kai yana faɗin “sannu madan” hannu Aryan ya ɗaga musu chikin sauri yana faɗin “ba ta bukatar sannun ku ku wuce bakin Aikin ku kawai nace” jikin su har kerma yake suka wuce suka bar wajen
dawo da lallon sa yayi kan diyana “my jidda am sorry na wahalar da ke ko? Haka kawai yau naji ina son in tukaki a mota da kai na muyi tafiya mai nisa muna tafiya muna hutawa a hanya, Abuja nake son muje zaki iya jure tafiyar ne ko kuma in kira waya akawo helicopter mu karisa da shi?fa ɗowa tayi jikin sa tana kuka kasa kasa mai do da kafar sa chikin motar yayi tare da ɗaka kugerar motar ta dawo dai dai ya jawo kofar motar ya rufe ya tada motar,ganin ya kunna motar ya sanya ta ta tashi daga jikin sa tana kokarin komawa wajen zaman ta ta zauna da kyau “me yasa kika tashi? Ya tambaya dai dai lokacin da ya juya kan motar suka bar wajen wayar sa ya ɗauko ya fara kiran layin Bgs,wayar na ta ringing Bgs bai ɗaga ba sai da wayar ta kusa yanke wa sanna ya ɗauka manna wayar Aryan yayi a kunnen sa yana faɗin

“menene next? Daga ɗayan ɓangaren Bgs yace “kaje zuwa idan ka isa in da ya dace zan sanar da kai” yana kai karshen maganar ya katse kiran,ta chikin mirrow motar ya kalleta ta kwantar da kanta a jikin kujerar mota tana kallon hanya da glass na gaban mota,gudu yake shararawa sosai kamar zasu tashi sama lokacin kan kani suka isa
tsakanin zaria da kaduna kafin su kai jaji ya karya kwana ya sauka daga kan titi ya shiga daji yayi tafiya mai ɗan nisa tun suna iya hango titi har suka dai na hangowa chikin tsoro diyana tace “yaya Aryan wai ina zamuje ne?naga sai shiga daji kake” ta kai karshen maganar dai dai lokacin da ya tsai da motar a kasar wata bishiyar dalbijiya,juyowa yayi ya jawota jikin sa chikin sanyin murya yace “my jidda kina matar Lefternal general Aryan bai kama ta ki ji tsoron wani abun ba kuma fa karki manta tare kike da jarumin mijin ki” “ni yaya Aryan ba fa tsoro nake ji ba kawai ina mamakin me ya kawo mu ɗajin nan ne” zai yi magana wayar sa tayi kara alamar shigowar sako chikin sauri ya saketa tare da ɗaukan wayar ya duba sakon Bgs murmushi ne ta kubche masa lokacin da yake karan ta sakon, sakon ne kamar haka “kai zaka rabu da yar kutane ka fita kayi aikin da ya kawo kane ko dai sai ka rusa mana target” reply ya shiga rubutawa Bgs kamar haka “wai kai Bgs a motar ma bazaka barni na ɗan huta ba sai ka samin ido ko? to wlh wata rana sai kaga abun da zai hana ka barci wato kai na lurama har first night ɗina ma sai ka gani ko? To ka shirya idan my jidda ta sume kai zaka zo ka du bamin jikin ta” yana gama tura sakon ya turawa bgs tare da kwashewa da dariya har da riƙe chiki, baki buɗe diyana ke kallon yadda yau yaya Aryan ke tikar dariya ko me ya sa shi dariya oho

sai da yayi dariyar sa mai isan sa kafin ya ɗago yana kallon ta “my jidda lfy kike kallo na haka? Kawar da kan ta gefe tayi kafin tace “daman yaya Aryan kana dariya haka ne? Me ya saka dariyar? Ka faɗamin sai nima na rinƙa maka dan karinƙa yin dariyar sosai kayi kyau over da kana dariyar nan” “my jidda tsiya nayiwa yayan ku shiya sanya nake dariya nasan yanzu yana chan ya karanta sakon yana chika yana batsewa na san ma sai tsaki yake ja yanzu haka ji yake kamar ya shako ni ya buga” guntun tsaki diyana taje kafin tace “wanchan mugun zaka che ai ni ba yaya na bane wlh da ina sane Allah hiyana ba zata Aure shi ba sai dai ta mutu batayi Aure ba zan kirata awaya ai anjima ta layin Aunty Zahra wlh zan gaya mata ta sa ya sake ta idan ba haka ba mugayen yara zata haifa masu kama da shaɗan” jikin Aryan yayi mugun sanyi da jin kalam diyana a kan ɗan uwan sa yasan wacece diyana duk abun da zata faɗa iya gaskiya take faɗe daga zuchiyar ta kuma bata faɗin abun da ba shi ba yanzu daman haka suka ɗauki dan uwan sa kenan? Mugu azzalumi kai ina ai ko dan kallon mugu da akewa ɗan uwan sa dole ya san yadda zai yi ya chanza sa ya zamar da shi yadda mutane ke bukata yanzu babban tashin hankali sa ɗaya shine Bgs yaji duk abun da diyana ta faɗi ya Allah ya sa kar ya kara tsanar sister akan abun da yar uwar ta tayi

ganin yayi shiru ne ya sa diyana tace “yaya Aryan karka damu ba amatsayin ɗan uwan ka na zageshi ba a matsayin ɗan uwana ɗan goggona na zageshi kai ma ka kalli abun ta wanna fuskar” girgiza kai kawai yayi dan idan ya biyewa diyana zata iya sanya Bgs ya tashi motar su da bom “yaya Aryan na gaji da zama a nan dan Allah mu bar dajin nan” buɗe baki Aryan yayi zai yi magana sukaji alamun takun tafiyar mutane daga bayan su chikin sauri ya ɗauki piston gun dake saman glass ɗin motar ya ɓoye ta a jikin kujerar da diyana ke zaune ya juyo ta chikin mirrow motar yake kallon mutanen dake tin karosu wasu jibga jibgan mutane ne sanye suke chikin bakaken kaya sun sanya safan hannu baki sun rufe fuskar su da bakin kyalle ba abun da kake iya gani a jikin su sai ido akalla mutanen zasu kai 20

massage ɗin Bgs ne ya shigo wayar Aryan chikin sauri Aryan ya buɗe sakon fara karanta sakon yayi kamar haka “tun yaushe nace ka rabu da yarinyar nan kayi abun da ya kawo ka kaki nace ka ɗauko yarinyar nan ne ba dan komai ba sai dan mu kama mai neman sister ta dan mu gane wanene amma ka zauna kana shirme to yanzu komai ya kwaɓe ka kwachi kan ka da kanka tun yaushe nake faɗa maka mata rauni ne kaki yarda to yanzu dai sai dai in che maka all the best” dogon numfashi Aryan yaja lokacin da ya kammala karanta sakon dai dai lokacin mutanen suka iso waje motar da karfi ɗaya daga chikin su ya ja murfin motar ya ɓalleta damko kwallar rigan Aryan yayi ya fito da shi waje ihu diyana ta fasa tana faɗin “yaya Aryan ba shi ya sanya tun ɗazun nace maka mu tafi gida ba wayyo Allah Hiyana na ta” chikin zafin nama ɗaya daga chikin mutanen ya buɗe kofar motar ta gefen da diyana take ya fisgota waje

Atare suka jerasu ita da Aryan ihu diyana take sosai tsawa ɗaya daga chikin mutanen ya daka mata “kiyi mana shiru!!! Ba ku yan lekan asiri ba wlh yau kwanan ku takare a nan zamu kashe ku ba sai mun je wajen oga ba” chikin kuka diyana tace “wlh baku isa ku kashe mu ba kasan ni kanwar wacece nifa kanwar bgs ne Brigadier general Safras ni na san yayana ba zai taɓa bari ku kashe ni ba” asukwane Aryan ya juyo yana mamaki wai ba yanzu ta gama zajin Bgs ɗin ba,yanzu fa ta gama chewa shi ba yayan ta bane amma daga ganin mutanen nan har ta chan za magana itako ko ajikin ta ihu take tana faɗin “mai kama da hiyana ina kake kazo ka chechemu wayyo karka bari a kashe ni hiyana zatayi maraici” shi kan shi Bgs dake zaune gaban desktop computers yana kallon su ta hanyar Cameran dake liƙe da bottin ɗin gaban rigar Aryan sai da yayi dariya dan diyana tayi mugun bashi dariya

A fisace babban chikin su ya ɗaga hannu zai zabgawa diyana mari dan ta ishe su da ihu takiyin shiru zata tona musu asiri, chikin sauri Aryan ya riƙe hannun sa yana faɗin “Sorry oga zan sa ta tayi shiru” fisge hannun sa mutumin yayi ya wuche yayi gaba sauran tawagar tasa suka tasa Aryan da diyana a gaba suka fara tafiya kasa kasa Aryan yace “my jidda kiyi shiru kinji yanzu zamu bar wajen nan” tana son ta rungumesa amma tana tsoron kutanen dake bayan su dan haka sai ta hakura ta kame jikin ta tayi shiru

Sunyi tafiya mai ɗan nisa kafin su isa wani kewayayyen waje mai girman gaske chikin wajen suka shiga manya manyan yan ta’addan ne awajen ga dilolin coken,daga gefe guda wasu majiya karfin samarine ke haɗan bomabomai ga manya manyan akwatina chike da bindigogi da kayan yaki
Aryan na ɗago ash eyes nashi karaf ya sauka kan zulaihat dake zaune saman kujera kusa da wani alhaji yasha Ruwan mamaki daman ya san zaa rina tun da yaga Bgs ya saki zulaihat kuma yace ya fito tare da diyana su bi hanyar Abuja ya san da biyu ashe zulaihat dilar kayan maye ce lallai Bgs yaci sunan sa Brigadier general Safras ba abanza ashe aka bashi mukamin ba baya kasar amma yana yiwa kasar sa Aikin da ko shugabannin da suke kasar basa yi lallai a yau ya kara sarawa Bgs

Miƙewa zulaihat tayi daga saman kujeyar ta kallon dadyn jabir tayi kafin ta juyo ta kalli Aryan chike da izza ta fara takowa ta nufo su Aryan sanye take chikin wando zuwa chinya da rigar sa da bata gama rufe chibiya ba sai busan sigari take tana taku chike da sheɗan chi

gaban Aryan tazo ta tsaya kallon sa ta farayi from head to toe kafin tace “ba laifi dai zan ɗan lallaɓa da kai muje dan a hannu nake wlh naso a che wanchan banzan ne ya bibiyemu da ya gane kuren sa dan a bukace nake da shi ya kwanta min a rai sosai amma kaima ba laifi zanyi maleji” juyawa tayi ta dubi dadyn jabir tace “dady zamu shiga daga chiki kasa su murkus su kawomin giya kwalba biyu” bata jira amsar dadyn nata ba ta juyo ta kalli su murkus tace “ku samin shi a chikin ɗaki” suna kokarin kama Aryan diyana ta riƙe hannun sa chikin kuka take faɗin “wlh babu in da zaku kai min mijina sai dai muje tare” damko gashin kanta ta chikin hijabi zulaihat tayi tace “ni ma zan so mu tafi dake ɗin dan kiga yadda akewa namiji fyaɗe idan na gama da shi kuma sai kema na ɗan ɗana miki daɗin duniya dan daga ganin ki zakiyi daɗi kai murkus idan kun kai shi ɗaki ku ɗaure min shi a saman gado sosai fa ita kuma yarinyar ku ɗaure ta a gefe ta yadda zata ji daɗin kallo na a saman mijin ta da kyau” tana kai karshen maganar ta hakaɗe diyana sai da tayi tangal tangal kamar zata faɗi, da kyar ta kame jikin ta ta tsaya

Gyaran murya Aryan yayi kafin yace “kafin su shiga da mu ciki ina son in yi magana da babanki” tsaki zulaihat ta ja kafin tace “ba zaka samu wanan damar ba kai shege murksu ku wuce min da su chiki” kakkama Aryan su murkus su kayi su 6 ɗaya daga chikin su kuma ya nufi diyana yana kokarin kamata kamar daga sama sukaji harbin gun tasss dai dai sai tin goshin wan da yazo kama diyana builet ɗin ya sauka nan take ya faɗi kasa gawa, chikin sauri su murkus suka saki Aryan suka nufi wajen gun nasu suna faman ɗaukan gun ɗin wani wawan bugu Aryan ya kaiwa wani ɗan ta’adda dake kusa da shi yana rike da gun faɗuwa kasa ɗan ta’adda yayi tare da yasar da gun ɗin hannun sa a sukwane Aryan ya ɗauki gun ɗin kai kallon sa yayi kan dankareren agogon dake manne a hannun sa call ɗin Bgs ne ya shigo chikin agogo ba tare da ɓata lokacin ba yayi picking tare da fara sakewa yan ta’addan ruwan buleit da hannu ɗaya “ka fara kashe ta kafin kowa” abun da Bgs ya faɗi kenan ya katse kira

rungumo diyana Aryan yayi da hannu ɗaya ɗayan hannun kuma ya riƙe gun yana ruwan builet gaba ɗaya yan ta’addan neman gudu suke dan Aryan wuta yake sake musu ba na wasa ba juyawa yayi ya goyi diyana a bayan sa sosai ta kankame sa ta runtse ido ta kwantar da kanta a bayan wuyan sa sai ta zulaihat da ke kokarin guduwa Aryan yayi ya ɗauke ta da buleit tass a dai dai tsakiyar goshin ta nan take ta faɗi kasa wanwar sai gawa ihu dadyn jabir ya fasa yana kiran “my daughter!! My daughter!!! Amma ina ko motsi zulaihat ba tayi ba, sai ta dadyn jabir Aryan yayi zai harbesa builet na shi ya kare kan kace me yan ta’addan sun kewaye shi da bin digu,umarnin dadyn jabir kawai suke jira su harbi Aryan da diyana shi kuwa dadyn jabir ya durkushe kan guiwowin sa gaban gawar zulaihat yana kuka yana kiran “my daughter ki tashi kin san kece rayuwa ta ki tashi my daughter!!! Kamar wani mahaukaci dadyn jabir ya zama

“Oga umarnin ka fa kawai muke jira muɓarar da wanna mutumin” chewar murkus sai lokacin dadyn jabir ya ɗago idon sa wadda suka sauya sukayi jaaa sosai miƙawa tsaye yayi ya nufi wata kofa dake wajen yana faɗin “ku kashe su dukkan su ko gawar su ban yarda abari ba ku kasamin namar jikin su ku kawo min shine zai zama abincin darena” yana kai karshen maganar ya shige ta chikin wanna yar kofar

Ɗana bindigogin su su murkus suka yi suka sai ta Aryan dake goye da diyana wadda ta ɓoye fuskar ta abayan wuyar sa ta runtse idon tana jiran taji ta a lahira kawai, kamar daga sama sukaji murya mai sauti ana faɗin “kayi kasa oga” duƙawa kasa Aryan yayi goye da diyana kan kache me ko ina na wajen ya kaure da ruwan albirushi ban da karan manya manyan jiga jigan bidigogi ba abun da zakaji a dajin nan wasu jibga jibgan sojoji ne suka jiro chikin daji suna rike da manya manyan gun masu lfy da numfashi lokacin guda suka yiwa yan ta’addan nan rubdugu kan kace me sun kashe su gaba ɗaya

sauke diyana Aryan yayi a fusache ya nufi ɗakin da dadyn jabir ya shiga yana shiga wajen sai yaga ashe ba ɗaki bane hanya ce awajen hakan na nufin dadyn jabir ya gudu ina ba zai yiwu ba dole mu kamo mutumin nan dole mu kashe sa amma kafin mu kashe sa sai ya faɗa mana me haɗin sa da family Abubakar saraki me tsakanin sa da Abba dayake bibiyar mu chike da ɓacin rai Aryan ya juya ya koma wajen sojojin su

diyana ya tsugunne yadda ya barta ta kasa miƙewa dan ita gani take mutuwa zasuyi chikin jin haushi Aryan yace da sojojin sa “ku tashi dajin gaba ɗaya da bom ku tattara gun ɗin nan ku mikasu a headquarter ayi min bincike akan tayaya akayi aka shigo da su kasar nan gashi dai dukka gun ɗin sabbi ne waye yayi order su ina san amin bincike akan su nan da 2dys in samu result” yana kai karshen maganar ya duƙa ya ɗauki diyana ya saɓa ta a kafaɗar sa suka nufi wajen motar sa

Bayan sun zauna chikin ɗaya daga chikin motan da sojojin sa suka zo da shine tun da nasu motar su murkus sun ɓalle marfin slowly ya juyo ya dubi diyana dake zaune a mazaunin ta na kugerar gaban mota tana kuka kasa kasa,chikin nitsuwa ya fara magana “my jidda kiyi hakuri yau nayi miki wasa da rayuwa ko?dolece tasanya ni yin hakan bani da zaɓi dolene nayi hakan kin ga yanzu sanadiyar yin hakan munyi babban kamu muna son mu kama mai bibiyar sister ki che dan an sanar da Bgs akoi mai bibiyar sister yana neman ta shi ya sanya muka shirya yin hakan to gashi yanzu a dalilin yin hakan da mukayi gashi mun ragewa kasar mu mugun iri kuma munga fiskar makiyin mu duk da ya gudu zamu kama shi ba jimawa tun da yanzu mun san face nashi kuma in Sha Allah zamu kama mai bibiyar sister ma duk da shima ina da tabbacin yana da allaka da wanchan makin namu domin binciken Bgs akan mai bibiyar sister nan ta bashi result kin ga kenan suna da alaka amma koma me dole nima na koma bakin aiki dan mu ragewa kasar mu mugun iri” faɗowa jikin sa tayi ta kan kame sa tana faɗin “ni dai yanzu yaya Aryan ka mai da ni gida tsoro nake ji kabar yin duk wata magana yanzu sai mun koma gida ni yanzu ma bana jin abun da kake faɗe ni dai kawai inason in ganni kusa da Ammi na” Aryan ya lura diyana na chikin tashin hankali har yanzu bata nitsuba dan haka sai ya kunna motar ya ja da gudu suka bar dajin

Uk

Wuni yau gaba ɗaya Bgs a gaban computer ya wuni sai karfe 12:10am ya fito daga ɗakin binciken na shi kai tsaye betroom na shi ya wuce yana shiga ya nufi toilet har ya kai bakin kofar toilet ɗin sai kuma ya juyo ya dawo ya zauna a bakin gado tare da chiro wayar sa ya fara kiran layin Khalid,

lokacin da call ɗin Bgs ya shigo wayar Khalid zaune suke a palon part nasu shi da Zahra da Hiyana dariya Khalid yayi lokacin da ya ga kiran ɗago ido yayi yace “sister bgs ne ke kirana wata kila ya sha wahalar neman ki ne da bai ganki ba shine ya kirani ko zan taimaka masa bari dai na ɗaga naji me zai che, chikin sauri yayi picking call tare da sanya wayar a H-free yana faɗin “hello” daga ɗayan ɓangaren Bgs yace “kai Khalid kace yarinyar nan ta kawomin black tea mara suga sanan kuma bata ga time ɗin chin abin cina yayi bane da bazara kawomin abinci ba” chikin dakiya Khalid yace “wace yarinya kuma? Tsaki Bgs yaja kafin yace “ban sani ba kaji? kai ma ka shirya na kusa dawowa ta kan bari dai na gama binciken da ya ɗauke min hankali yanzu na baku 2mins kasa yarinyar nan ta kawomin abinci idan ta haura 2mins” bai sake magana ba ya katse kiran da mamaki Khalid ya juyo ya kalli su Zahra tun bai yi magana ba hiyana ta miƙe tare ɗaukan jakar shopping da sukayi da yaya Khalid ta fice daga palon chikin sauri tana tunanin wai shin yaya Prince ɗin nan kam mutun ne ko aljani wai yanzu yana nufin yasan yaya Khalid ne ya ɗauke ni tab, da wanan tunanin ta nufi kitchen ta ɗauko abinchin sa ta fito ta haura sama

Lokacin da ta shigo ɗakin baya nan sai saukan ruwa da taji a toilet ne ya tabbatar mata yana wanka ne saman sofa table ta ajiye masa abincin tana ajiye masa ta wuce chikin sauri ta shirya kayan da suka sawo da Khalid a trolley ɗin ta ta dawo ta wuce dressing room na shi ta fito masa da kayan barci riga da wando farare tas masu laushi ta fito ta ɗaura masa saman gadon chikin sauri ta chire kayan jikin ta ta ɗauko wando da rigar da ta ajiye da safe ta sanya a jikin ta haɗaɗen perfume da yaya Khalid ya saya mata a shopping da sukayi yau ta sanya a jikin ta ba karamin kyau tayi ba kayan sun fito da ita sosai sai dai dasu da babu duk ɗaya ne iya chinya wandon ya tsaya mata shi kuma rigar iya chibiyar ta ya tsaya tara gashin kanta tayi zata ɗaure zuchiyar ta ya tuna mata da chewar da alama Bgs yana matuƙar son gashin kanta dan haka bai kamata ta rinƙa rufe gashin ba tuna hakan ya sanya ta saki gashin har gadon bayan ta ta koma saman sofa mai zaman mutun 3 ta zauna ta takure waje guda tana jiran sa wani mugun kunyar sa take ji ji take kamar ta tashi ta sanya hijabi

Da zaman ta bai fi 10mins ba sai gashi ya fito daga toilet ɗaure da towel a kugun sa ta kasan ido ya kalli in da take ba tare da ya tanka taba ya wuce gaban mirrow chikin sauri ya shafa body lotion nashi tare da sanya perfume nashi mai bala’i kam shi chikin sauri ya gyara gashin kansa bayan ya kammala ya juya ya nufi wajen gadon ya ɗauki kayan barcin da ta fito masa da shi ya wuce dressing room nashi

Jim kaɗan ya fito shirye chikin kayan barcin da ta fitar masa ba karamin kyau kayan suka masa ba sai murna hiyana ke yi ya sanya zaɓin ta ajikin sa wajen da take zaune ya nufo tana ganin ya nufo wajen ta miƙe tsaye saman sofa mai zaman mutun 2 ya zauna tsugunnawa kasa tayi chikin sanyin murya tace “ina wuni yaya Prince” bai am sa ba kuma bai ɗago ya kalle taba ta san ma tsalar dan haka sai ta kara matsowa kusa da shi sosai tare da ɗan kama kafar sa tace “kayi hakuri yaya Prince ba zan sake ba wlh ni ma nayi nadamar sosai” hannu kawai ya ɗaga mata alamar ya ji chikin sauri ta fara zuba masa abinci da sexy voice yace “iya tea kawai ya isa” mai da abincin tayi ta rufe kulan ta ɗauko cup ɗin tea ɗin ta miƙa masa ansa yayi tare da yi mata nuni da gefen sa da hannu akan ta zauna

Miƙewa tayi ta zauna kusa da shi tana jiran taji me zai ce “wanene ya sayamin kayan nan da na gani a dressing room na!? Ji tayi zuciyar ta ya fara dukam uku uku lokacin guda ta sha jinin jikin ta tsoro take karya ce ta kwashe kayan ta zubar “ba dake nake bane!? Daɗɗaɗar muryan sa ya daki dodon kunnen ta kashe murya tayi kamar yadda yaya Khalid ya rubuta mata ta fara magana “kayi hakuri da naje wajen shopping ɗin ne sai na ga kayan sunmin kyau kuma naga zasu maka kyau shine na ɗauka maka” harchikin ran sa yaji daɗi amma afili sai ya ɗaure fuska yace “nache miki ina bukata ne? Girgiza kai ta shiga yi tana faɗin “aa bakache ba kayi hakuri ba zan sake ba” shiru yayi bai sake magana ba har ya kammala shan tea ɗin ya miƙe ya nufi saman gado,

Miƙewa ita ma tayi ta kwashe kayan abincin ta mayar kitchen ta dawo ta haye saman gadon daga ɗan nesa ta kwanta “Khalid ya kai ki wajen gyaran gashi? Ya tambaya yana jawo blanket ya rufe jikin sa “eh ya kai ni” shiru suka yi ba wan da ya sake magana

After 10mins

Mirginowa tayi ta dawo jikin sa lokaci guda ya sauke nauyayyar ajiyar zuchiya tare da waro manya manyan green eyes nashi waje kallon ta yake sosai kafin ya matso da face nashi dai dai sai tin nata saukar da idon sa yayi yana kallon tula tulan breast nata da kusan rabin su awaje,ji yake kamar ya sanya hannu ya taɓa amma zuciyar sa na faɗa masa idan yayi hakan zata raina shi tuna hakan ya sanya ya kawar da kallon sa tare da ɗora hannun sa saman kan ta yana shafa lallausan bakin gashin kanta yana mai da numfashi duk abun da yake mata tana jin sa kudur tawa tayi a ranta in sha Allah gobe bazata sa riga ba zataga karshen tsiyar sa wlh sai ta kure sa

To masu karatu mu haɗe daku ranar Monday mugani da Bgs da hiyana waye zai yi na sara zamu ga ya wasan zata kaya love u all my masoya 🥰🥰

💋Duk Karfin Izzata 💋

 

💖The Talent Troupe Writer’s 💖

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*

 

 

Back to top button