Gidan Aunty Book 1Hausa NovelsHausa Novels

Gidan Aunty Book 1 Page 60

Sponsored Links

BOOK 1
Page 60💖

She was so speechless, gabaki d’aya ta kasa magana, ji take komai kamar a mafarki yake zuwar mata, bata san lokacin data rungumeshi ba tana sakin wani saban kuka me taba zuciya , ta rasa wani irin farinciki zatayi,sai kara rungumesa da tayi so very tight, murmushi ya saki yana hugging din ta back shima, a hankali ya fara shafa bayanta alamun rarrashi,”it’s ok , banasan wannan kukan please “,ya fada a hankali, duk da ta jishi hakan besa ta dena kukan ba sai ma kara masa karfi da tayi, ganin kukan ba me karewa bane ya hade bakinsu waje d’aya, bata hanashi kusan mintuna biyu kafin ya janye bakinta yana kallan yanda fuskarta ta baci da hawaye, tissue ya dauke ya fara goge mata hawayen amma duk da hakan ta kasa tsayar dashi,” i don’t like , stop it ok”, girgiza masa kai tayi a hankali zata bude baki ya dakatar da ita,”don’t even start it, banaso “, magana zata karayi ya girgiza mata kai tare da langwabar da Kai kadan “dady want to sleep”, murmushi ne ya subuce mata, ta saki dariya kadan,”Allah ya albarkaci rayuwanka, yasa ka fi haka,Allah ya cika maka burinka na duniya da lahira,Allah yasa ka gama da duniya lapiya , yanda ka sani farinciki Allah ya baka masu saka farin ciki fiye da haka “, batayi auneba sai ji tayi yayi sama da ita , da paper din hannunta,direct upstairs ya nufa da ita, be sauketa a ko ina ba sai akan wani bed me shegen kyau, daki ne babba a second floor sai faman tashin kamshi yake,takardun kuma ya sa mata cikin wani lock me anfani da turn print, “dare yayi, we have to sleep “, sai yanxu wani tsoro ya bayyana a fuskarta ganin zasu kwana waje daya , amma duk da hakan tana kokarin danneshi,dan tayi alkawari bazata taba hanashi a bunda yake so ba, ya na shiga toilet ta fashe da wani saban kukan farin ciki,dama oumma da taheer sunanan, nasan da sunfi kowa farin ciki da koma wata makaranta, cikin sauri kuma tayi istigfari tana goge idanuwanta gudun karya fito ya ganta tana kuka, ko da ya yafito kallo daya yayi mata yau dauke kansa, itama tashi tayi tashiga wankan, kayan da zata saka ta fara tunani tunda bata taba kwana a cikin dakin ba, tana fitowa taga wata red din Riga a ninke tare da yar karamar paper ,” wear it please “, tana daga rigan ta zaro ido waje sabida ganin ba ta inda jikinta zai rufu a cikin, rigar tayi shara shara da yawa sosai sai wani dan siririn pant, duba wardrobe din Wajan tayi taga duk manyan kayana ne a wajan babu ta yarda zata sasu yasata yin shahada ta saka kayan, ita kanta saida taji kunyar kanta sabida yanda jikinta yayi mugun fitowa,ganin bazata iya shiga cikin bedroom din ba ysa tayi zamanta a cikin dressing room din.

A bangaran king kuwa tana shiga , ya dauki wayarsa da aka turo masa abu ta cikin email, abunda aka rubuto ya karanta kafun ya dauki wani number yayi kiranta, ringing 1 aka daga wayar kamar ana jiran tsammaninta tun tuni, bai amsa gaisuwar da na wayar yake masa ba sai ma tanbayar da ya jefo masa “ ansamo details din inda suke”, banji me akace masa ba tsawan mintuna biyar kafun ya furta “ duk inda suke a binciko su, few days kawai na baku”, yana kammala zan cansa ya kashe wayar, abun hannunsa dake yawo ya dan kalla, me harafin M and T, abunda suka faru tsawan shekarune suka shiga yawo a kansa, take a wajan wani masifaffen ciwon kai ya kamasa, ya dade yana addua kafun ciwon kan ya lafa masa a hankali, lokaci ya kalla ganin har yanxu bata fito bane yasa shi bin bayanta, a hankali ya tura kofar, tana zaune kan wata kujera bacci ya dauketa, kallan yanda rigar ta fito da ainahin jikinta yayi kafun ya saki wani murmushi me kayatarwa, sosai ya ke bin surar jikinta da wani irin mayataccen kallo, ganin abunda yake san dannewa yana kokarin ta somasa ne yasashi saurin kauda ido, tare da daukarta a hankali, a zabure ta ware idanuwanta , kafun tayi saurin kullesu ganin rigar dake jikinta tana kara kankame jikinta, bece mata komai ba har ya kwantar da ita kan fadon, da wani irin mugun sauri ta kashe Wutar dakin tayi saura lamp,dariya ce taso kamasa da har saida murmushi ya bayyana a fuskarsa duk da kasancewar da duhu, gefen gadon ya zauna tare da jawo ta jikinsa, kokarin zame jikin ta take sanyi amma ya kara kankame ta,”ouchhh” da sauri ya kalleta ganin yanda take runtse ido, duk da a duhu duke ,”ciwo na”, ta fada a hankali,”am sorry bari na duba wajan”, kafun ya kai karshen zancen sa ta dora hannayenta biyu akan bakinsa Dan bata bukatar jin karshen maganarsa,”ok am sorry ,bazan karayi ba sai wajan ya warke ,ok”, ya fada yana dora kanta akan kirjinsa, aziyar zuciya tahee ta fara sauke lokacin da yake shafa mata baya,” sleep tight, I love you “, ya fada yana kara rungumeta,”same “ ta fada a hankali duk da batayi tunanin zai jiba, “ I won’t force you!!!!!! But Inaso nasan soyayyar da kike mun”dan dagowa tayi ta kallesa kafun ta kara dora kanta akan kirzinsa batare da tace komai ba, shima be damu da tayi maganan ba shiyasa ya cigaba da shafa bayan ta,bata dau dogon lokaci ba wani daddadan bacci me shegen dadi ya dauketa, ajiyar zuciya king ya sauke yana kara gyara mata kwanciyarta “ I love you to the moon and back sweetheart “, ya fada tare da sunbatar goshinta,addua yayi musu kafin shima wani bacci me dadin gaske ya daukesa.

🫧🫧🫧🫧🫧🫧

After 5 days, wata iriyar soyayya king yake nunawa tahee me tsayawa arai, tun yan gidan basu fuskanta ba har kowa yagane irin soyayyar da yake mata, a tsakanin su abeeey da ummey kuwa baza ace ga Wanda yafi nuna farincikinsaba, ummey har da kuka dan ganin d’anta ya fara samun farincikin da ta dade take biri ya samu, ammey ma sosai take jin dadin ganin yanda son dinta ya fara dawowa kamar rayuwarsa ta da, dada kullum cikin sa masa addua take Allah ya kawo mata jikokinta nan kusa, duk lokacin da ta fada hakan kuwa sai dai ya kalleta amma har cikin zuciyar sa yanajin dadin adduar, a fili kuwa sai dai ya dauke mata kai, sau da dama saida tace munafurci dai babu kyau Allah yasa ba jaraka kake zuwa kana yiwa yarinya ba. A cikin yan kwanakin nan kuwa wata iriyar shakuwace ta shiga tsakanin ta dasu ihsan duk da kasancewar sun dan girmeta, amma hakan be hana su ki girmamata ba a matsayinta na matar yan su, sau da dama indai basu da lectures toh suna ban garantane, wani lokaci kuma a part din su dada suke zamansu, duk tsawan kwanakin nan bata ganin amrah da basma, duk da yawancin lokaci ta naji su ihsan na maganar zaman dakin da take yi yanxu musamman da taji motsun king ko me take bari take ta gudu inda bazai ganta ba,ta bangaran basma ma ta koma gidan wata aunt dinta acewarta zatayi mata kwana biyu ne itama, babu Wanda ya hanata, kwafa kwai tayi ita kadai Tasan abunda ke cikin ranta, a cikin kwana biyar din nan small mom da mahma kowa ya koma gida suma, gabaki d’aya family din babu Wanda beyi missing Dinsu ba, rigimar da zoya tasa akan zata bi small mom ne yasa itama aka tafi da ita, yanxu gidan ya rage saura su kadai.

Yau ya kasance Saturday, Daidai da saura kwana biyu tahee ta fara zuwa makaranta. tana zaune kan 2 sitter cikin shigar kananan kayan da ya sabar mata, dan karamin plate din fruit ne a hannunta take yankawa ,lokaci zuwa lokaci tana sashi a bakinta, tun bayan tafiyar kulu take zaune akan 2 sitter din bayan bacci da ta dade tanayi akan, ringing din wayartane ya mayar da ita cikin dogon tunanin da ta fada, private number ne babu suna kwata kwata a jiki, gabantane yayi wani irin wawan faduwa, sabida mafarka da take yawanyi akan kiran, kamar karta daga sai kuma wani bangare na zuciyar ta ya bata goyan daga kiran, cikin sallama ta daga kiran , bata karasa sallamar tata ba sabida wani gigitacciyar karar da yasa tayi saurin cire wayar a kunnanta na yan sakanni kafun ta mayar da wayar a hankali, wani irin dariya mara dadin ji aka dauke dashi me ban tsoro kafun cikin hade rai taji an soma magana “Ba a mun taurin mai, duk Wanda yayi kokarin bujurewa umarnina ina kashe sa kamar sauran ne, kwanaki kadan na baki ki kashe mun mujin ki, dan jinin jikinsa mallakina ne ni kadai, idan kikai sabanin hakan kuwa ki tabbatar da samun gawarwakin mahaifiyarki da dan uwanki dan zan musu kisa irin kisan wulakanci ne , na turo miki sako ki duba “ kitt aka kashe wayar, TAHEE da ke zaune duk launin idanuwanta sun canza zuba launin ja me ban tsoro, wani irin tsikar jikintane taji yana tashi a jikin, cikin sauri ta bude private number din da babu suna ko daya a ciki,” KILLED YOUR HUSBAND “ wani irin gigitacciyar kara ta saki tare da jefar da wayar, gabaki d’aya launin idanuwanta sun canza zuwa launin ja, girgiza kai ta somayi kafun tayi ball da wani tanbuwal din glass me shegen kau, fashewar sa yayi Daidai lokacin da king ya bude kofar, da mugun sauri ya shigo falon,inda take ya nufa, cikin wata iriyar murya me amo ta dakatar dashi, “me nayi musu, me nayi musu,kaje ka kashe su dukansu bana san su mugayene,” da mamaki king yake kallanta ya rasa gane me take nufi shiyasa yayi yin kurin zuwa wajanta, wani gigitaccen ihu tahee ta saka, launukan idanuwanta na kara canza wa , cikin wata siririyar murya ta furta “ sun kashe mun NONNA,SUSAN, SUN KASHE MUN SIF DINA, Nima sun kashe ni , ka fada mun Menene laifin mu da suke san hallakamu “, kallo daya king yayi mata ya fahimci ba taheen sa bace, fuskarsa ya hade kicin kicin ba alamar fara’a yace kalleni”, amaimakon ta kallesan sai ta kuma dukar da kanta kasa, cikin gigitacciyar tsawa ya furta kalli cikin idona ynxu “, fashewa da kuka tayi tana girgiza kanta , ganin hakan yasashi yin taku daya, a mugun zabure tahee ta danki wukar da take ynxu apple da ita….

GIDAN AUNTY
07041879581

BOOK 1
Page 61

Tsayawa yayi a inda yake gabaki d’aya hankalinsa ya gama tashi ganin ta da wuka a hannunta, kalaman dazu take ta kara maimaitawa,gyada mata kai yayi shima “ ok zamu rama muma amma bani wukar nan tukunna”, kin bashi wukar tahee tayi saima fashewa da wani saban kukan tayi, jikinshi har rawa yake dan ya gane ba ita kadai ce ba, tsoransa karsu cutar da ita, sunan dazu da ta kira ne ya fado masa kafun ya kalli yanda take faman hada gumi duk da sanyin Ac dake fitowa, bayanta ya kalla kafun ya furta “NONNA”, da sauri ta juya tana sakin wukar hannunta, yana gani ta juya taku biyu yayi ya damki Dan tsan hannunta, kara ta sakar masa sai faman fusge fusge take ita kadai, wata iriyar gigitacciyar tsawa ya daka mata yana hade fuskarsa kamar bashi ba, “ki nutsu”, ya furta cikin kausashshiyar murya , nutsuwar kuwa tayi tana sun kunyar da kanta, “ ya sunanki “, shiru tayi tana kara sunkuyar dakanta, “karki bari na sake maimaita tawa “, cikin shashsheka ta furta “sunana LOLA”, dan kallanta yayi jin tayi magana da wata iriyar murya”wacece ke , me yasa kika shiga jikin mata ta”, yanxu ma shiru tayi masa, bece komai ba kafun a cikin dan daga murya yayi Bismillah, rawa jikinta ya fara ,” ah ah zanyi magana ka bari dan Allah “ ta fada cikin rikicewa, banza yayi mata kafun ya fara karatun alkuranin, yanxu kam ihu ta sa masa tana rokonsa karya konata, zaunar da ita yayi kan kujera har yanxu hannunsa na rike da nata kafun ya dakko wani bottle water da ke gefensa ya ajje mata a gabanta, da sauri ta saka hannu zata dauka ya matsar da ruwa nesa da ita “ ruwa , ruwa “ ta fara fada , “zakisha”, ya furta , bata jira ba ta amsa masa da Sauri” zan baki ruwa idan kin gama amsamun tanbayoyina, sabanin hakan kuma zan kona kine “, wacece ke, me yasa kika shiga jikin matata”, cikin wata iriyar murya ta fara kuka , “ ba cutar da ita nake ba, te makonta nake, suna san Kasheta ne kamar yanda suka kashe mun ahalina”shiru yayi na yan sakanni kafun cikin kausashshiyar murya ya furta “Menene hadinki da matata, sannan menene alakar ku da matata da zaki shiga jikinta”, ina bata kariyane kamar yanda Nima ta taba temakona a lokacin baya,ni ba muguwa bace, suna harin rayuwar tane”, su wanene” da mugun firgici ta kallesa , zasu kasheta kamar yanda suka kashe shi, bazan iya va”,wani irin rawa jikinta ya fara,”ruwa !!ruwa!!”, ruwan ya dakko kamar yanda ta bukata amma be bata ba,”banasan jin wannan tatsuniyar taki, kar na sake ganin ki a jikin matata, idan va haka ba zan konaki da ayoyin uban giji, ki gaggauta fita daga jikin matata yanxun nan”,kanta ta daga masa tana rike makoqwaranta, ruwan ya mika bata da mugun sauri ta fara sha, saida shanye duka kafin ta fara sakin ajiyar zuciya,”zan fita daga jikinta, Kai ma nagode da yanda kake kular mun da ita,nasan kana kula da ita amma ka nunkashi sabida kokarin kasheta da suke yi, ganin komai nasu ya fara lalacewa,ka kula da ita “, tana gama fadar hakan tahee tayi atshawa me karfin gaske,kafun ta sulale ta fado kan king da yayi saurin tarota, cikin zafin nama ya dauke tare da kaita cikin bedroom, kallan yanda take bacci peacefully yayi, kokarin kawar da tunanin yun kurin kashe masa mata da akace yake, iska ya furzar a hankali kafin ya furta “ it’s a lie”. System dinsa ya dauka bayan ya canza kayan jikin sa, ya jima yana operating a kanta,lokaci zuwa lokaci yana kara dubata duk da yana kusa da ita, kiran sallah la’asar ne ya tayar dashi, kan gadon ya karasa har yanxu bacci take peacefully abinta, goshinta ya danyi pecking kafun ya bar dakin.

Mintuna 15 da futarsa ta fara motsa idanuwanta kafun ta budesu gabaki d’aya, mamakine ya kama ganin ta kwance akan gado, wayar da akayi mada da text message ne kawai ya fado kanta, duk yanda zata tuna zuwan ta kan gadon ta kasa, sakkowa tayi daga kan gadon bakinta dauke da addua, agogon dakin ta duba, 4 ta wuce da sauri tashiga toilet kafun ta fito ta kabbara sallah , tana Idarwa azkar dinta tayi kafun ta mike , kara kallan agogo tayi mamakinta har yanxu be dauke ba ganin be dawo gida ba, dan karamun bakinta ta turo waje kafun ta bar dakin, shima falon shiru alamar ba kowa a ciki,3rd floor ta hau nan ma shiru sai ac da kamshin turaran da ke buso dakin,dacin da bakinta ya somane yasata nufar fridge din data gani, tana budewa kuwa idanuwanta ya sauka kan kayayyakin ciye ciye dake shake a ciki, fiye da saurin fridge din, wani abun ma bata taba ganin saba, strawberry ice cream din data ganine yafi daukar hankali, janyoshi tayi tana sakin wani murmushin jin dadi, waje ta samu akan gado tana shan ice cream din, tana sha tana sakin dariya sabida yanda dadin ke ratsa mata kwakwalwa, idanuwanta ne suka sauka kan wata yar karamar roba dake kan bedside dinsa, ajje Ice creams din tayi tana janyo robar “ANTI DEPRESSANT” shine abunda aka rubuta jikin robar, har zata mayar sai kuma ta fara karanta abunda ke jikin robar, da wani irin shock ta mike tsaye, tana karanta abunda ke jikin robar, wasu hawayene suka fara sakko mata kawai ta fada kan gadon ta fashe da kuka , saida tayi me isarta kafun ta mike dauke da robar a hannunta, zata bar dakin kenan shikuma yana shigowa da sallama a bakinsa kasa kasa, cikin zuciyarta ta amsa sallamar tasa fuskarta kwata kwata ba fara’a, kallan yanda fuskarta ta dan tashi yayi kafun cikin sauri yayi yunkurun nufar inda take”what’s wrong with my baby”, hannunta d’aya ta nuna masa alamar ya dakata karo na farko a rayuwarta, da wani irin expression yake kallanta, be gama tunani ba ta dago robar drugs din dake hannunta, “ Menene wannan”, ta fada tana zuba masa idanuwanta da suka kara haske sabida kukan da tayi,wani irin harbawa zuciyarsa yayi” sam ya manta daya sha drugs din ya barshi a fili”, cikin dan daga murya kamar ba ita ba ta furta “ maganin Menene wannan kakesha “, kokarin matsota yake ta kara dakatar dashi” please calm down, am sorry I will explain”, bata san lokacin da ta buga robar a ‘kasaba maganin ciki ya zube” me yasa , me yasa , I thought Dagaske kake da kace kana sona, i though da gaske kake da kace kai dady nane, kana shan wancan pills din dukda kasan illar su, u’re a doctor, I thought ka d’auke ni a matsayin matarka, Aushe nayi kuskure ba haka bane, you’re taking this drugs to…. to…”, ta kasa karasa zancan nata sabida wani saban kukan da yake kokarin zuwan mata tana dannewa, wani irin shock ne ya dake shi, jin kukanta yake kamar ana kara cakarshi da maki a zuciya gabaki d’aya ya rikice , cikin sanyin murya ya furta “ please don’t be angry, I will explain “, manyan eyes dinta ta zuba masa hawaye na sauka akan idon nata” bana bukata” kawai ta furta tare da barin dakin, wani irin jirine yaji yana neman kayan dashi yayi saurin samun waje ya zauna , ga baki daya hannayensa ya tusa cikin gashin kansa yana ya mutsasu “ I’m in a big mess , she’s more angry than ever”, ya rasa Wana irin tunani zaiyi , bayaso koka d’an tayi fushi dashi dan bazan iya daukan fushinta ba, da sauri ya mike ya nufi bayanta, yana shiga ya tarar da bata cikin bedroom dinta, ragowar bedroom din second floor ya duba , shima duk bata ciki, muryar da ya fara ji sama sama a falon kasane yasashi nufar falon kai tsaye, TAHEE ce a falon tare da su sumayya da suka zo falon, wani irin ajiyar zuciya ya sauke yana binta da kallo , adaidai lokacin da ta daga idanuwanta itama, tana ganinshi ta d’auke idanuwanta fuskarta a dan hade kadan ta yanda su Ihsan bazasu gane ba.” Oh my god “ ya furta cikin zuciyarsa har yanxu ya masa dauke idanuwansa akanta, su firdausi na ganinshi suka kara gaishe ganin yanxu yana amsa musu gaisuwarsu bakamar daba, kanshi ya dan daga musu alamar amsawa dan kwata kwata ba shi yake bukata ba,so yake ya rungumeta, ya lallasheta ko zata dena fushi dashi, he want to feel her warm , he can’t take it”, satar kallansa ihsan tayi ganin yanda ya tsaya gabaki d’aya hankalinsa na kan tahee dake dannawa waya,murmushi ta saki kafun ta kalli tahee,” sister yau dai bari na cika miki alkawarin Pam cake din ki”, bata jira amsar tahee ba ta mike ta nufi kitchen, firdausi da sumayya ma duk sun ankara dashi dan haka da sauri suma suka mike “muma bari mu tayaki” dukansu basu jira jin amsar taba sukayi saurin guduwa , bece komai dan Hakan yake bukata, ganin ta tashi zata bi bayansu yayi saurin shan gabanta, hannunsa biyu yayi hade alamun pleading, dauke kanta tayi daga kansa zata wuce yayi saurin riko hannunta, fisge hannun tayi kafin ta furta “ don’t touch me again “, tana gama maganarta tayi upstairs, waje ya samu ya zauna kansa na sara masa, gabaki d’aya launin idanuwansa ya canza Sabida yanda yaji xuciyarsa na masa zafi, ya dau tsawan lokaci zaune a kan kujera kamar ya bita amma yana tsoro karta kara wani fushin, ganin lokacin sallah yayi ne yasashi barin part gabaki d’aya .

Aban garan su ihsan kuwa suna shiga cikin kitchen din suka kulle kofar, kwai kwayar yanda suka ga king na kallan tahee suka fara, “wayaga Romeo and juliet “ cewar ihsan , dariya suka saki gabaki d’ayansu, kan kujerun dake kitchen suka zauna suna dasa saban hira , daman space suka basu kar king ya koresu, sun dade suna hira abunsu kafun su fito falo, ganin babu kowa ne yasasu sakin ajiyar zuciya , da Sauri ihsan tayi hanyar kofa ,kallanta sumayya tayi alamun karin bayani” kun manta pan cake mukace zamuyi mata, tana fitowa kara zaunar da mu zatayi , ni kuma ban shirya shan masga ba Wajan yaya”,ga baki daya basu yi wannan tunanin ba, gudun karta fito tazo ta samesu sukayi saurin barin part din.

Tahee kuwa tana shiga daki wani saban kukan tayi kafun ta shiga ban daki, Wanka tayi ganin ana kiran sallah tayi alwalarta, ta kabbara sallah bata bar daddumar ta ba sai da akayi isha’i, wasu English wears ta saka masu daukar hankali blue colour , cikakken gashin kanta ya sakko har bayanta duk da hular da ta saka, wani irin masifaffen kyau tayi na musamman amma fuskarta har yanxu a cin kushe take, Fararan hannunta da yan yatsunta sun fito fes da masu musamman da kunshin hannunta ya kara fito da farinsu,Daddadan kamshin turaran princess ne ke tashi a cikin dakin ta ko ina, message din data gani akan wayarta ne ya sata sakin baki “ sorry sis karkizo kiga bamanan ummey ce ta kiramu”, ba kowa bane ya tura mata text din face ihsan, hararar wayar tayi kamar suna gabanta,kafin ta fito daga dakinta, karo suka ci da king da gaba daya yanayinsa ya canza, kallo daya tayi masa kafun ta d’auke kanta “ sannu da zuwa “ ta furta zata bar wajan, ya rungumota ta baya yana sakin ajiyar zuciya, cikin disashewar murya kamar mara lapiya ya furta “ I can’t take it any more , please am so sorry, bayanda Kike tunani bane,” raba jikinta tayi da nashi kafun ta furta “ your dinner is ready”, am not hungry, ya furta yana binta da kallo, bata kuma ce masa komai ba tayi wucewarta kan dining, apple ta dauka guda daya ita ma, ta wuce dakinta, zuciyar ta na raya mata ta kallesa amma ta danne, tana barin Wajan ya dafe kansa dake sara masa, tayi masa kyau sosai yau , and he don’t like her frowning face, cikin sanyin jiki ya nufa dakin shima , yana kallan yanda take shan apple dinta cikin kwanciyar hankali, bece mata komai ba yace toilet,ya dade a ciki bayan ruwan sanyin da ya sakar wa kansa, ganin zazzabin nasa na kara yawa ne yasashi kashe ruwan, shima wasu kayan bacci ya dauka white colour masu kauri sabida yanda yake jin sanyi, turare kawai ya fesa ya fito, yana fitowa yatarar da fitula aka she sai lamp din da aka dan kunna, sai tun zuciyarsa ya rike yana cije lips ,sallar da ya saba yake so yayi amma ya kasa sabida ynda yake jin jikinsa, a tunaninsa tayi bacci ne shiyasa ya na hawa bed din ya janyota jikinsa yana sakin ajiyar zuciya,kara rungumeta yayi kamar wacce za a kwace masa ita, tun lokacin da ya rungumeta ta bude idanuwanta ga zafin jikinsa dake ratsa nata jikin,tausayi ya bata kamar tayi magana sai kuma tayi shiru har bacci ya dauketa, “ am so very sorry “ yake fada a cikin zuciyar sa….

Mss Lee 💖

Leave a Reply

Back to top button