Duk KarfinIzzata Book 2Hausa NovelsHausa Novels

Duk Karfin Izzata Book 2 Page 19

Sponsored Links

Book 2

Page 19

Jabir

_________dady wlh ni dai ba zan yar da ba koma yaya ne dole ni dai akawomin hiyana na rinƙa kwana da ita har sai na gaji” miƙewa dad yayi daga saman nashi kujerar ya dawo kusa da jabir ya zauna tare da ɗan rungumosa ya fara magana “am sorry my son kasan dai ko ba ka che hakan ba dole na hukun ta wanda ya taɓamin kai,bani kaɗai bama bakaji yadda mum ɗin ka ma ta ɗau zafi ba, munnemi yarinyar nan har mun gaji sai daga bayan nan na samu lbr basa kasar nan ashe ma yar gidan abokin gaba nane Abubakar saraki,yanzu kasani gaba biyu ne ba ɗaya ba bazan taɓa barin family Abubakar saraki su zauna lfy ba kayi hakuri yarinyar na shigowa kasar nan zamu kawo maka ita” chikin jin haushi jabir yace “dad why baza kuje har kasar da take ku kamota ba!? “Jabir calm down mana ina son kasani bamu isa mu shiga Uk mu kama yarinyar nan ba kai ko hanyar gidan da take ba mu isa mu bi ba kasan awani gida take kasan su wanenen yan uwan ta? Turo baki jabir yayi kafin yace “ni dad ina ruwa da in da take ni dai kawai ina son in ganta a gadona koma ta yaya ka kawomin ita “jabir you are watching news everyday an you knew who is Brigadier general Safras an You knew Lefternal general Aryan an general Yusuf, kai fa da bakin ka kake sanar dani irin haɗarin dake tattare da mutanen nan amma shine yau kuma kake chewa naje gidan su na ɗauko maka yar uwar su sokake na mutu ne ina son kasan shifa makiyi baa fuskantar sa gaba da gaba sai dai ayakesa ta bayan page” chikin tsawa jabir yace “dad it’s ok ni ka mutuma idan ka ga dama amma dai ka tabbatar ka kawomin hiyana kafin ka mutu” yana kai karshen maganar ya miƙe fuuuu ya shige betroom nashi ya banko kofa ya burza key,jiki ba kwari dad ya miƙe ya bi bayan sa murɗa cofar betroom ɗin yayi yaji a rufe alamar jabir ya murza key

Chikin muryan rarrashi dad ya fara magana “my son ka buɗe min kaji ko? i promise that zan kawo maka ita ko da zan mutu hakan yayi maka” daga chikin ɗakin jabir yace “dad pls leave this place I don’t want to talk to you again if you want to talk to me then you should go an bring hiyana for me first if not I will not come out from this room again I will die here” dafe kai dad yayi sai yanzu ya fara dana sanin me ya sa ya shagwaɓa jabir why yanzu gashi bai isa yayi masa magana ba duk abun da yake so zai yi,yana bala’l son jabir shi kaɗai ne ɗan da Allah ya bashi ba zai iya ganin bacin ran saba kuma yasan halin jabir idan yace zai yi abu tofa sai yayi, yanzu zai iya zama a chikin ɗakin kamar yadda yace idan baa nemo masa hiyana ba bazai fitoba,

chike da damuwa dad ya kuma cewa “ok my son yanzu zan tafi kuma na maka alkawari zan dawo maka da yarinyar amma pls idan mum ɗin ka ta dawo daga wajen aiki ka fito kuyi hira kaji haba my lovely son” “dad naji ni dai yanzu ka tafi kawai kuma karka dawo ba tare sa hiyana ba”murnushi dad yayi dan yaji daɗi jabir ya fara saukowa “ok my son yanzu kuwa zan tafi amma fa kai ma ka fito kaji” “dad pls leave ai naji ko dai sai ka sake batamin rai ne idan baka tafi ba ka sake wata magana Allah ba zan fito ba kuma ba zanchi abinci ba sai dai na mutu a nan” jin abun da jabir yace ne ya sa dad yayi saurin barin waje ya fice daga palon ya shiga motar sa ya bar gidan gaba ɗaya yana saka yadda zai ɓullowa family Abubakar saraki.

YOLA

Gaba ɗaya iyalan gidan su bellon yau suna zaune a tsakar gida innar buba da innar yaya bello suna gyara ganyen rama da zasuyi miyan dare,hasana na zaune gefen su,sun hanata aikin komai saboda chikin ta buba na zaune kusa da innar yaya bello yana gyara musu kifi, inna habiba na kwance saman tabar ma a gefe daga ɗan nesa dasu kasancewar har yanzu ita jikin nata bai gama warwarewa ba
Da fara’a yaya Bello ya shigo gidan hannun sa ɗauke da yan kananan buhu guda biyu, gaban inna habiba ya ajiye mata buhu ɗaya ɗayan kuma ya wuce da shi ya miƙa wa matar sa,zama yayi a tsakiyar innar sa da innar buba chike da farinciki ya fara magana
“inna mun yi waya da Ammi tace ranar Litinin zata turo mota ya ɗauke mu da ni da ke da ita” yayi maganar tasa ta karshe yana nuna hasana ba zai iya kiran sunan ta a gaban ta ko a gaban innar sa ba,hakan a chewar su rashin tarbiyya ce,chikin nuna damuwa innar yaya bello ta fara magana “aa Bello kuje dai kai da ita ni zan zauna da su habiba dan kaga dukkan su basu gama samun lfy ba” chikin sauri innar buba ta tari numfashi ta da chewa “aa innar Bello ku tafi dai karki damu In Sha Allah zamu kula da kanmu bamusun sanadiyar mu ki rasa jin daɗin ki” hmmm larai kenan ai na riga na gama magana babu in da zanje ya ɗauki matar sa suje yaje yaga yanayin wajen idan wajen yayi masa sai ya dawo musan shawarar da zamuyi” ta kai karshen maganar tare da miƙewa ta ɗauki kwaryar ganyen da suka gyara ta bar wajen ta shege kitchen

Dawo da kallon sa yaya bello yayi kan innar buba,hannu innar buba ta sa tana shafa kansa alamar kar ya damu yabi abun da innar tashi tace,jiki ba kwari ya mike ya nufi ɗakin sa yana tunanin ta yadda zai yi wanan tafiya ba tare da innar sa ba, anya zai iya barinta a nan kuwa? Chike da zulumi ya kwanta saman gadon chiyawar su

Alama innar buba tayiwa hasana da hannu akan ta miƙe ta bi yaya bello dan ta lura gaba ɗaya ya sauya da innar sa tace ba zata bishi birni ba,chikin jin kunya hasana ta miƙe tabi bayan mijin ta.

KANO

8am Aryan ya tsaka da barchin sa mai chike da daɗi da mafarkin diyanar sa,
a chikin barchi ya jiyo ihun ta har tsakar kansa babu shiri ya waro ash eyes nashi masu chike da barchi sunyi jaa saboda barchin bai ishe sa ba hannun sa ya ɗora gefen sa yana lalubar ta bata awajen chikin sauri ya miƙe zaune, da mamaki yake kallon ta zaune a tsakiyar ɗaki ta wargaza gashin kanta ta harɗe hannayen ta a guiwowin ta ta dunkule waje guda, kawar da kansa gefe yayi ya sauko daga gadon ya nufeta yana zanchen zuchi yau kuma kalar iyashegen da tazo masa da shi kenan

Sugunnawa kan yatsun kafar sa a kusa da ita ya sanya hannu yana kokarin chire hannayen ta data murɗe a guiwowin ta yana faɗin “my jidda wai me ya sa kin chika rigima ne? Yanzu me ya zaunar da ke awajen….bai idasa magana ba yaga tayi wani kukan kura ta hankaɗesa har sai da yayi baya ya faɗi, da sauri ya runtse idon sa ya kuma buɗe wa domin ya tabbatar wa kansa ba mafarki yake ba, ɗago kan sa yayi yana kallon yana yin garin tabbas karfe 9 zatayi yanzu,ya kamata a che lokacin karewar karfin maganin da Ahzan ke bata yayi, mamaki ne ya sake kamashi tuna irin turesa da tayi tabbas wanan ba karfin ta bane domin yana da tabbacin ko hannun sa idan ya sakar mata nauyin bazata iya ɗagawa ba, tuna hakan yasa ya miƙe tsaye chikin sauri yana yan waige waige bata a chikin ɗakin da sauri ya nufi kofar fita daga shi sai wando zuwa guiwa da singlet fari tas a jikin sa, bata a palo ficewa yayi waje yana mamaki, jin abun yake tamakar mafarki, tsayuwa yayi a harabar gidan ya rasa wani part zai shiga neman ta,ba zai iya komawa ɗaki ba tare da ita ba dan yadda ya gantan nan bai ga alamar mai lfy ba wani zuchiya nace masa ya nufi part na Ammi wani zuchiyar kuma nace masa ya nufi part na Abba, ya rasa wanne ɗaya zai ɗauka yayi nisa chikin tunanin da yake yaji wani razanannen ihu daga part na Aunty Amarya,chikin zafin nama ya nufi part ɗin

Abun da bai taɓa zato ba idon sa yayi tozali da shi turus ya tsaya a bakin kofar palon yana ganin ikon Allah, Aunty Amarya na dafe da goshin ta jini na zuba,ga Omar da diyana na tikar dambe duk karfi da kasancewar Omar namiji amma diyana ta faffasa masa jiki, sai kokarin take ta karisa wajen Aunty Amarya shi kuwa Omar duk chiwon da ta jimasa hakan bai sa ya kyaleta ta karisa wajen ba, sai faɗa suke Omar ya kasa da katar da ita dan jin karfi take kamar doki, mutuwar tsaye Aryan yayi yana kallon abun kamar Tv yana kasa motsawa daga in da yake.

Chikin ɗagawa war murya Omar yace da Aunty Amarya “Aunty Amarya ki gudu ɗaki wlh yarinyar nan ba wanda zai iya tare ta, tunkan ta illatamu mu dukka ki gudu” ya kai karshen maganar dai dai lokacin da gaba ɗaya Family suna iso ban da yan Uk dasu Aunty farida dake gidan mazajen su, “subhanallah subhanallah” abun da Abba ke faɗi kawai chikin sanyin murya Ummi tace “diyana lfy wai meke faruwa ne? Omar na kokarin yin magana diyana tayi kukan kura ta damki wuyar sa ta ɗagashi sama tayi wurgi dashi gefe,a fusace Haidar ya kariso wajen bai yi wata wata ba ya ɗauke ta da mari yana faɗin “ke wani irin kwaya kika sha yau? Ba zato ba tsammani Haidar yaji ta tanki wuyar sa da hannu ɗaya ta ɗagashi sama sai kokarin kwace wuyar nashi yake amma abun ya chi tura zaro ido ya farayi waje alamar ya ji shaƙa, ihu Ummi ta fasa tana faɗin “zata kashe Haidar ku kai masa ɗauki Ammi kam tana tsaye ko motsi ba tayi ba domin kallon ɗaya tayiwa diyana ta fahimci an haɗatane da manya manyan sheɗanun aljanu masu ji da karfi da mugunta kuma duk wan da ya tinkare ta idan bai yi Sa’a ba to zai iya mutuwa, gaba ɗaya su Abba sun ruɗe tashin hankali ya bayyana karara a kan face nasu

Chikin zafin nama Aryan ya kariso chikin ɗakin hannu ya sanya yana kokarin chire hannun diyana daga wuyar Haidar, amma ji yayi kamar kwaɗo akasa aka haɗe wuyar da hannun ta akan datse ko motsa hannun nata ya kasa ga Haidar gaba ɗaya ya gama gala baita numfashi sa na gab da ɗauke wa, karasowa wajen su Abba yayi chikin sanyin murya yace “dan Allah bai war Allah ki yi hakuri ki sake sa zai iya mutufa, Abba bai gama rufe baki ba Aryan ya furta “No” da karfi tare da hankaɗe diyana da iya karfin sa suka tafi gaba ɗayan su kasa ji kake dam karar harbin bin diga builet ɗin ya wuche ya fasa bango, gaba ɗaya mutanen dake chikin ɗakin suka chure waje guda ba karamin tsorata Abba yayi ba chike raunaniyar murya yace “Aryan wanna arbin bin diga fa daga ina? Dai dai lokacin Aryan ya mike zaune yana faɗin “bgs yayi harbin” “bgs kuma? Abba ya faɗa da mamaki a kan face nashi “eh Abba shine yayi harbin kuma nasan hakan zata faru tun danaga Haidar ya galabai ta” “amma Aryan Ina chewa Prince baya nan ta ina to yayi harbin?chewar Ummi tayi maganan da mamaki sosai a face nata mikewa tsaye Aryan yayi ya nufi diyana dake kwance a kasa kamar ta mutu yana faɗin “eh Ummi baya nan akoi wani Gun da ake baiwa manyan manyan sojoji da na ura gun ɗin take aiki, gaba ɗaya gidan nan akoi Camera sirri da muka sanya to idan kana son harbin wani daga chikin gidan nan tachikin Cameran da muka sanya zakayi amfani da motsin mutun sai ka sai ta nauran wanchan gun ɗin ka shigar da Cameran dake gidan nan ka sanya motsin wadda kake son harba sai ka sai tashi kawai ka danna Don shikenan, to daman kafin ka harbi mutun idan aka sai tashi da gun ɗi zaki ga alamar wata jan wuta a jikin sa, shi ya sanya dana gani na turesu” chikin faɗa da ɓachin rai Abba ya fara magana ” hauka Safras yake ne da zai harbeta wato kashe ta yake son yi baya ganin ba a hayyacin ta take ba ne?” chikin sanyin murya Aryan yace “kayi hakuri Abba bai da zaɓine dolece ta sanya ya sai ta harbin nata ku masa uzuri kunga baya nan ta chikin Camera yake kallon mu kuma da kuke nan ya ku kaji da ku kaga Haidar na gab da mutuwa a gaban ku bare kuma shi” ya karisa maganar lokacin da ya tsugunna kusa da diyana, tsaki Abba yaja kafin yace “wanna ba hujja bane ai rai bai fi rai ba… Abba bai gama rufe baki ba yaga diyana ta tamko wuyar Aryan,tare da mikewa zaune tana zaro ido,chikin zafin nama Aryan y ɓalle hannun ta daga wuyarsa ya haɗe hannayen nata dukka biyu ya rike yana faɗin “sa idon ki chikin nawa” wani kukan kura tayi tare da murɗewa waje ɗaya ta dakarkare ta kaiwa masa bugu da kafar ta wadda ya sanya shi yin baya baya ya faɗi dan daman bai tsugunna da kyau ba akan yatsun kafar sa ya tsugunna, miƙewa tayi, ta nufi Aunty Amarya,

a guje Aunty Amarya ta wuce bayan Abba ta buya, chikin zafin nama shima Aryan ya miƙe ya nufeta ta baya ya damko ta yayi yayi ya ɗagata saman amma jin ta yayi kamar dutse ko motsata ya kasa, juyawa tayi tana kokarin kokawa da shi akan ya sake ta kamar daga sama sukaji wata gigitatchiyar tsawa da basu taba jin Voice irin taba “ke Khadijah ki nitsu!!! a razane gabaɗayan su suka juya suka kai kallon su in da sautin tsawar ta fito, ba karamin razana su kayi ba lokacin da suka ga Ammi ce tayi wanna tsawar tana tsaye kamar gunki kusa da ita Abba ya matso kasa kasa yace “Aisha kina lfy kuwa? Ba tayi magana ba kanta na kallon kasa, lokacin guda diyana ta saki Aryan ta duka kasa chikin wata iriyar Voice mara daɗin ji ta fara magana

“Kayi hakuri oga ba laifin mu bane” chikin tsawa Ammi tace ta fara magana da muryan maza “ba laifin ka bane laifin wanene menene ya kawoka jikin ta? Ba su Abba ba har shi kanshi Bgs dake kallon su ta Camera ya tsorata ganin mahaifiyar sa na magana da muryan maza, kara matsowa Abba yayi kusa da Ammi ya sanya hannu ya na kokarin zaunar da ita, yanke jiki tayi ta faɗa jikinsa chikin sauri Aryan ya kariso ya dauke ta daga jikin Abba ya shinfiɗe ta saman doguwar kujera umarni Abba yayi wa kowa dake chikin palon akan su zauna ba musu kowa ya samu waje saman sofa ya zauna da kyar Haidar ya iya miƙewa ya zauna saman sofa shiko Omar ko motsi bayayi yana baje a kasa alamar ya suma

Ido a rufe Ammi ta fara magana da muryan maza kamar ɗazun “baka bani amsa ba menene ya kawoka jikin ta!? Chikin Voice mai bada amo mara daɗin ji diyana ta fara magana “turomu akayi akan mu haukatata ta dawo ita ba mutun ba kuma ita ba aljana ba” “waye ya turoku ashe akoi wanni daga chikin ku dake chin gashin kansa ashe bakujin maganar mai martaba babana” kuka mai sauti diyana ta fasa chikin kuka take faɗin “izirail kayi hakuri karka sanar da sarki Ni yanzu ma zan fita daga jikin ta amma fa ko na fita kasani ba zata samu lfy ba domin gaba ɗayan ta ogan mu ya riga ya sanyata a chikin kwalba, rayuwar ta na hannun shi ta yuwuma idan na fita a jikin ta ya kashe ta idan na fita zata dai na buge buge da duk wani abu kamar mahaukaciya amma fa bazata samu lfy ba kullun zata kasance chikin chiwo domin oga ya rufe komai na jikin ta har magana ba lallai ta iyayi ba, zaɓi biyu kuke da shi na farko ko dai ku chigaba da bata maganin da kuke bata daga 1 week baya zuwa shekaran jiya domin maganin kamar yana chan zatane gaba ɗaya komai nata zai chanza zaɓi na biyu kuma ko dai ku tinkari oga da kanku domin ya warware aikin shika ɗai zai iya warware Aikin” chikin tsawa Ammi tace “wanene ogan naku? Waye ya turoku? “Ka idar Aiki kasan bamu faɗa amma zan iya faɗa muku in da yake” “ai na yake?” “Garin yola yake” yana kai karshen maganar diyana ta yanke jiki ta faɗi kasa alamar aljanin ya fita

chike da bada umarni Ammi ta nuna Aryan da hannu ba tare da ta buɗe ido ba ta chigaba da magana “yanzu Khadijah ta zama nauyinka hakkine a kanka ka nema mata lfy sai ka shirya ya je ka nema mata magani idan kuma zaka iya zama da ita to zaɓi ya rage gareka” chikin sanyin murya Aryan yace “amma ya akayi ka kirata da Khadijah ba diyana ba ko dai har yanzu aljanin na nan ne bai fita ba kuma shine mai suna Khadijah” “ai Khadijah ne sunan ta ba diyana ba, da sunan Khadijah aka yanka mata rago, Khadijah na da bukatar abubuwa da dama daga gareka kayi amfani da matsayin da kake da shi ka nemo mata wasu ɓangarori na rayuwar ta” chikin sauri Aryan yace ban fahimta ba ɓangarori na yaruwar ta kuma kamar me kenan? Shiru sukaji Ammi ba ta sake magana ba sai ma wani attishawa da ta buga mai karfin gaske, shikenan sai barchi mai nauyi ya ɗauke ta

“Tirkashi to Aryan ka dai ji aikin da ke gaban ka ko” chewar Abba shiru Aryan ya ɗanyi kafin yace “Abba amma ya akayi sunan yarinyar nan ya sauya? ba tare da sanin kowa ba kuma ya akayi ko ita kanta bata san sunan ta ba? kuma wani ɓangarori yake magana kenan? ina son sanin asalin tushen yaran nan” miƙewa Abba yayi yana faɗin “sai dai ka nemi sanin asalin su ta fannin ma haifiyar su bata mahaifin su ba ta mahaifin su kam su Safras ne tushen su dan idan ba Aisha ba Bappan su bai da wasu yan uwa” shiru Aryan yayi na ɗan mintuna kafin ya miƙe ya saɓi diyana a saman kafatar sa ya fice da ita ya nufi part nashi, umarnin Abba ya bawa su Aunty Amarya akan su wuce ɗakin duba marasa lfy Aryan zai zo ya duba su, ba musu Aunty Amarya da Haidar suka wuce Omar dake sume kuwa Aryan ne bayan ya kai diyana ya dawo ya ɗauke sa, Abba da Ummi suna zaune kusa da Ammi suna jiran ta farfaɗo.

Uk

fitowa yayi daga ɗakin computers nashi bayan ya gama kallon su Ammi kai tsaye wajen hutawar sa na ɗaki ya nufa yana tafiya yana latsa wayar sa, zaune take a saman ɗaya daga chikin kujerun wajen sanin ba wanda yake zuwa wajen ne ya sanya tayi baje warata dan duk tunanin ta baya nan kuma ba zai dawo yanzu ba sai dare, sanye take chikin wasu shegun riga da wando sun matse ta sosai rigar yana da babban wuya kusan rabin tula tulan boobs nata awaje gashi ko breziya bata sanya ba hips nata kamar zasu fasa wandon ta baza gashin kan nan nata ko ɗan kwali bata sanya ba yau kam bare hijab dan tasan ba wanda zaizo wajen,ba karamin kyau tayi ba kamar yar india,tana riƙe da wayar ta tana buga game, ga wani haɗaɗen cofin glass dake saman table ɗin kusa da ita ta zuba ruwa mai sanyi a chiki idan tayi game ta gaji ta ɗau ruwa ta sha.

Jin tayi gaba ɗaya ta tsargu kamar wani yana kallon ta, slowly chikin tsoron abun da zata gani ta ɗago blue eyes nata, karaf idon ta ya sauka chikin nashi yana tsaye wajen ɗan karamin pool dake wajen ya harɗe hannu a kirji ya zuba mata ido, a tsorace ta miƙe jiki na kerma tazo ta raɓa gefen sa zata wuce hannu ya sanya ya damko gashin kanta da karfi ya jawota baya ya dawo da ita ta gaban sa suna fuskantar juna, tsuke fuska tayi dan ba karamin zafi jan gashin ta da yayi ya mata ba calmly da sexy Voice na shi ya fara magana “me ya kawoki nan? Bakin ta har bari yake lips nata sai kakkarwa suke tace “kayi hakuri yaya Prince bazan…. Bata karisa maganar ba ya ɗaura yatsa ɗaya a saman lallausan lips nata yace “shiiiiiii” shiru tayi shima yayi shiru ya zubawa tsoratachiyar face nata ido ita kuwa ganin ba zata iya kallon chikin gwayar idon sa bane ya sanya ta runtse idon ta, Almost 3mins suna tsaye a haka da kyar ta iya buɗe baki lips nata sai kerma yake tace “yaya Prince dan Allah kayi hakuri wlh zafin gashin yake min” kasa kasa yace “open your eyes now” chikin sauri ta waro blue eyes nata a kan face na shi tana jiran taji me zai che da ita “wai me nake miki ne da kike yawan kirana da mugu? Kara zaro idon ta waje tayi tana mamakin yaushe yaji tana zagin sa kuma “ba dake nake magana bane” da sauri tace “kayi hakuri yaya Prince ba zan sake ba”
“Nifa ba chewa nayi zaki sake ko baza ki sake ba chewa nayi me nake miki da har kike kirana da mugu kuma kika tsaneni” runtse ido tayi chikin tsoro hukuncin da zai mata idan ta faɗa masa ta fara magana

“kana kyamata kace baka sona baka son ganina komai na taɓa baka so,baka kaunar hanya ta haɗa ka da ni ma bare har jikin mu ya haɗu, ban san me na maka ba kamin irin wanan muguwar tsana duk da tsanar da kamin hakan bai hanani in sauke hankin ka dake kai na ba,hakan baya hanani kyautata maka amma komai nayi maka ba dai dai nayi ba….bata kai karshen maganar ba ya jawota ta faɗa saman faffaɗar kirjin sa da murya kamar mai raɗa yace “shikenan abun da ya sanya kike chemin mugu?har kike ikirarin kin tsaneni? Kasa magana tayi dan ji take kamar ba aduniya take ba,chi gaba yayi da magana “ok yanzu mun haɗa jiki kuma bana kyamar ki sai ki dai na kirana da mugu, because kalmar batamin daɗi” nan ma ahiru tayi ta kasa magana,hannu ya sanya ya ɗago habarta ya zubawa face nata ido, idon ta a lumshe dan gaba ɗaya kunyar sa take ji “open your eyes” slowly ta buɗe idon nata a kan face na shi “what is your name? Chikin sanyin murya tace “hiyana”shiru yayi bai sake magana ba sai hannun sa da ya ɗago ya ɗaura saman kanta a hankali ya shiga shafa lallausan bakin gashin kan ta, ya zagayo da ɗayan hannun sa ta bayan ta ya ɗaura saman kugun ta, kwantar da kai hiyana tayi saman kirjin sa ta lafe tana tunanin anya ba aljanin bane wannan ɗayan bangaren zuchiyar tane ya bata amsa da chewa idan ma aljani ne yau dai ba kin kwanta saman kirjin aljani mai kama da mutumin da kika fi so a rayuwar ki ba,tuna haka yasa ta kara lafewa a jikin sa tana shakar daddaɗar kamshin perfume na shi almost 10mins suna tsaye haka, kasa jure tsayuwar hiyana tayi dan ta lura Bgs ko shekara zasuyi a tsaye ba zai damu ba, kokarin zamewa take kasa dan kafofin ta sun gaji jin hakan ya sanya ya sunkucheta da hannu ɗaya ya koma da ita wajen kujerun dake rufar wajen, kwanchiya yayi da ita a saman faffaɗar kirjin sa kwantar da kanta tayi saman kirjin na shi tana ɓoye fuska,chi gaba da shafa lallausan bakin gashin kanta yayi, lokacin guda ya fara fita hayyacin sa dan daman shi mutun ne mai tsananin sha’awa, shi ya sanya dan ya kare kansa daga faɗawa neman matan banza yake allura,

ɗayan hannun sa ya ɗaura saman bayan ta yana shafawa a hankali, mutuwar kwance hiyana tayi ita har yanzu ganin abun take tamkar mafarki ne ko kuma aljanine yazo mata a suffar yaya Prince, tayi nisa chikin tunani bata ankara ba sai gani tayi ya juya da ita ta koma saman sofar shi kuma ya mata runfa da faffaɗar kirjin sa, waro blue eyes nata tayi waje ba shiri, tana kallon sa, lokaci guda tsoron sa ya dira mata a rai ganin yadda idon sa suka sauya zuwa jaa sosai chikin tsoro lips nata na kerma tace “yaya Prince in tafi ɗaki? Bai yi magana ba sai ma haɗe fuskar su yayi waje ɗaya a hankali ya kamo lips nata na kasa ya fara kissing, gaba ɗaya duk wani kofa da iska ke shiga a jikin ta ya buɗe domin ansan sakon da yaya Prince ke aika mata duk wani jini dake gudu a jikin ta sai da ya tsaya chan,ya baiwa sakon yaya Prince hanya ya wuce, sosai yake kissing nata tare da shafa gashin kan ta da hannu ɗaya, almost 10mins yana kissing nata kafin ya sake ta tare da miƙewa zaune chikin da sarke war murya yace “jeki kawomin abinci” tun bai kai karshen maganar ba ta miƙe da gudu ta barwajen

Masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kaimu

💖The Talent Troupe Writer’s 💖

 

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*

Wanna page ɗin nakine Hauwa’u jidda maman Abba ina godiya da comments naki ina matikar farinciki da jin daɗi Allah ya bar zumunci

Back to top button