Duk KarfinIzzata Book 2Hausa NovelsHausa Novels

Duk Karfin Izzata Book 2 Page 22

Sponsored Links

Book 2

Page 22

Uk 1am

Tana kwance saman katafaren gadon sa ta kasa barci duk bayan minti ɗaya sai ta duba time shiru shiru Bgs bai dawo ba tun abun baya damun ta har ta fara shiga damuwa miƙewa tayi zaune saman gadon tana tunanin ina ya tafi Allah dai ya sa lfy tun da sukazo gidan nan bai taɓa wuce 12:10am a waje ba shin me ya daɗar da shi yau, gajiya tayi da zama ta miƙe tsaye ta fara kai kawo tunawa tayi ɗazun ta kalli waya a saman table ɗin da yake ajiye ta kardu da system nashi da sauri ta nufa wajen tana addu’ar Allah ya sa akoi sim a chikin wayar,hannun ta har karma yake wajen ɗaukar wayar ta kunna haske screen ɗin,wani Cool murmushi ta saki lokacin da ta ga akoi sim a chiki already ta haddace number sa a kai chikin sauri ta shigar da number ɗin sa chikin wayar burinta kawai ta kira shi batayi tunanin me zai je ya dawo ba, sau biyu tana kiran wayar sa bai ɗaga ba sai a na uku ya ɗaga tattara nitsuwar ta tayi gaba ɗaya chikin sanyin murya tace “ina wuni yaya Prince” shiru yayi na ɗan lokacin kafin yace “me menene!? “Babu komai daman naga baka dawo bane har yanzu shine nace…. Bata kai karshen maganar ba ya daga tar da ita ta hanyar chewa “kawomin black tea ɗakin bincike” “yaya Prince ban san ɗakin ba ai”guntun tsaki yaja kafin yace “ki fito palo awajen da ake ajiye remote ki duba zakiga farin remote ki ɗauka ki sai ta sama ki dan na open stair case zai sauko sai ki haura ina wajen” yana gama faɗin hakan ya katse kiran, murmushi ta saki kafin ta ajiye wayar ta fice daga ɗakin

Kitchen ta nufa ta haɗa masa black tea kamar yadda ya buƙa ta ta dawo palo kamar yadda ya sanar da ita haka tayi, tasha ruwan mamaki lokacin da ta ga wani ɗan siririn stair case na saukowa bayan ta danna remote,mutun ba zai taɓa zaton akoi wani abu a saman nan ba wai shi stair case tsoro hawa taji dan kar ta hau ta makale amma da ta tuna yaya Prince ɗin ta na wajen sai ta samu kwarin guiwa,
Chikin zafin nama ta haye saman stair tana hawa stair case ɗin ya naɗe kansa da kansa

wani katafaren ɗaki ne awajen mai chike da computers da na urori da ban daban gaba ɗaya ɗakin gauraye yake da hasken computers, yana tsaye gaban wata makekiyar desktop ya sanya wata na’ura a idon sa kamar glass sai aiki yake tika,tsayuwa tayi tana bin ɗakin da kallon kafin ta mai da kallon ta kansa sanye yake da yar gakeren wando wadda ta ɗame sa sosai babu riga a jikin sa da alama wandon ma dolece ta sanya ya sa dan kallo ɗaya zaka masa ka gane haka asalin kyakkyawar suran jikin sa ta bayyana gaba ɗaya hannayen sa da chinyoyin sa baki lallausan gashi ne a kwance awajen sai sheki yake kai kallon ta tayi saman ɗamtsen hannun sa daƙe murɗe dama dama wani mugun farinciki take a duk lokacin da ta kalli kyakkyawar bakin gashin dake kwance a saman faffaɗar kirjin, Cool murmushi ta saki lokacin da idon ta ya sauka a kan haɗaɗen bakin gashin kansa wadda ke baje har bayan sa kasan chewar bai ɗaure gashin ba ya sake ta har baya
duk da sanyin Ac dake ɗakin hakan bai hana shi zufa ba saboda Aikin da yake tika kusa da shi tazo ta tsaya tace “sannu da Aiki yaya Prince” bai an sa ba kuma bai juyo ba aikin sa yake sosai da alama aiki ne mai muhimmanci

Tana tsaye shi kuma yana ta aikin sa almost 10mins da zuwan ta sanna ya chire na’uran dake fuskar sa ya juyo kallon ɗaya ya mata ya ɗauke kai kayan barcine riga da wando a jikin ta fari tas masu laushi sai ɗan karamin hijabin da bai wuce kirjin ta ba ta sanya a kanta baki

ansan cup ɗin hannun ta yayi ya ɗora saman wasu takar du dake wajen chikin sanyi murya yace “wayace ki ɗauki waya har ki kirani? Banche duk wanda zaki kira sai kin sanar da ni ba!? Baya baya ta farayi tana girgiza kai tana addu’a a zuchiyar ta Allah ya sa kar ya bugeta,takowa ya farayi a hankali yana bin ta tana baya baya, “ba dake nake mana bane? Kasa magana tayi ta chigaba da yin baya tana girgiza yana bin ta kai har suka kure bango,runfa ya mata da faffaɗar kirjin sa chikin tsawa yace “bazaki bani amsa ba sai na ɓallaki”slowly ta ɗago kanta tana kallon saitin wuyar sa ta fara magana “daman naga baka dawo bane shi ya sa na kiraka amma kayi hakuri ba zan sake ba” har chikin ran sa yaji daɗin amsar ta dan duk yan uwan sa ba wanda ya taɓa damuwa ko ya kirasa awaya idan ya wuce lokacin dawowarsa ɗan garama Aryan daman shi duk abun da suke a tare suke duk kuma in da zasuje tare suke zuwa for the first time yau sister sa ta damu da bai dawo ba har ta kirasa awaya wow wanan abu yayi,afili kuwa ɗaure fuska yayi sosai chike izza yace “idan kika saƙe ɗaukan waya kika kira sai na hukun taki!” Ɗago kai tayi sosai dan ya fita tsawo sosai idan suna tsaye tana son kallon face na shi sai ta ɗaga kai sosai kwata kwata tsawon ta bazata wuche kirjin sa ba da kanta da komai

Kallon face na shi tayi kafin tace “In Sha Allah ba zan sake ba amma dan Allah idan ba zaka dawo da wuri ba ka faɗamin kafin ka fita” abu guda ɗaya ne ke burgesa da yarinyar nan koda batayi laifi ba idan ka mata faɗa tana ansan laifin tace kayi hakuri bata damuwa wajen dole dole sai ta sanar da kai ba tayi laifi ba da tayi da bayayi ba zatache kayi hakuri bazata sake ba kuma tana kokarin taga ta kiyaye abun da kayi magana a kai, yana sane ba ita take faɗawa Ammi yana mata mugun taba amma da yace idan tasake faɗa sai ya bugeta duk da ba ita ɗin che ta faɗan ba bata nuna ba ita ɗin bace hasalima hakuri ta bashi ta ansa laifin da ba tayi ba

Shiru suka tsaya yana kallon face nata, sunkuyar da kanta kasa tayi tana jiran taji me zai che da ita gaba
saukar hannun sa taji saman kanta zame mata ɗan karamin hijabin jikin ta yayi a jefar kasa shafa gashin kanta ya shigayi tare da jawota jikin sa, jin abun tamkar mafarki Hiyana take, sun daɗe a haka yana shafa gashin kanta kafin ya zame hannun sa daga kan nata ya ɗago habar ta suna kallon juna matso da face nashi yayi dai dai nata chikin sauri ta runtse ido kirjin ta na dukan uku uku kasa kasa yace “ki shirya gobe zan sanya a kira muku masu gyaran gashi” yana kai karshen maganar ya sake ta tare da juyawa ya koma wajen aikin sa ya ɗaukk tea ɗin da ta kawo masa ya koma saman sofa dake a ɗakin ya zauna,ya fara sha chikin nitsuwa

Juyawa tayi zata fita sai ta tuna da massage ɗin yaya Khalid in da yake chewa idan ya saura kamar kwana biyu alluran ya sake sa kirin ƙa yawan zama kusa da shi kina yawan yimasa magana ko da ba zai amsa ba domin awan nan lokacin duk karfin alluran ya ragu yana gab da karewa ne gaba ɗaya alokacin zai ɗan fara jin feeling kaɗan kaɗan,tuna hakan ya sanya ta koma wajen sofan da yake zaune ta na kokarin tsugunnawa kasa ya nuna mata gefen sa da hannu ba tare da yayi magana ba, nauyayyar ajiyar zuchiya ta sauƙe kafin ta zauna kusa da shi tana satar kallon sa ta kasan ido, kaɗan ya sha tea ɗin ya ajiye ya miƙe ya koma bakin aikin da yake yana miƙewa ta kwanta a wajen dan daman ta fara jin barci tana kwanchiya ba jimawa barci yayi awon gaba da ita

2am ya kammala aikin da yake gaba ɗaya ya kashe duk wani kayan wuta dake ɗakin nan take duhu ya gauraye ɗakin haske wayar sa ya kunna kasa kasa yace “tashi muje” shiru bata amsa shi ba tsaki yaja kafin ya nufi wajen da take kwance hannu ɗaya ya sanya ya ɗauke ta chak ya saɓata a kafaɗa ya nufi hanyar fita da ita sai da ya kai tsakiyar ɗakin ya danna remote stair case ɗin tayi kasa ya sauka yana sauka stair ta koma kai tsaye bedroom ya wuce,saman katafaren gadon sa ya shin fiɗe ta ya wuche ya nufi toilet wanka yayi chikin sauri yayi shirin barci dan dare yayi sosai, saman gado ya dawo ya haye tana kwance yadda ya kwantar da ita gefe ya kwanta ya karanto addu’oe in barci ya shafa sannan ya lunshe ido

Kamar jira take yana lumshe ido yana lumshe wa ta mirgino ta faɗo jikin sa slowly ya waro green eyes na shin karaf sai saman face nata, zuba mata ido yayi yana kallon ta barcin ta take chikin kwanchiyar hankali yauche rana ta farko da ya karewa face nata kallon, shafa nashi face ɗin yayi kafin yace “haka ne fa kamannin mu ɗaya da yarinyar nan” dawo da kallon sa yayi saman ɗan karamin bakin ta ya zuba mata ido zuchiyar sa na ingizashi akan ya sunbacheta ɗayan ɓangaren na zuchiyar sa yace “idan ka sunbace ta ka sunbaci wa keman?” da sauri ɗayan ɓangaren yace “ka sunbaci sister ka kuma zaka iyayin komai da ita a matsayin ta na sister ka, kawai ka ɗauke ta a matsayin abun rage kewar ka,shiru yayi sai tunaninnuka daban daban yake a zuchiyar sa amma ya rasa wanne ɗaya sai kama ji yayi ba zai iya jure kallon lallausan lips nata ba batare da ya sumbata ba

slowly ya kai bakin sa saman nata da niyar ya sumbace ta amma sai ya zarce ya fara kissing nata ba tare da ya sani ba, sosai yake kissing nata tare da kara jawota jikin sa sosai duk abun da yake mata tana jin sa dan daman batayi barci ba da gangan ta faɗo jikin sa yaya Khalid ne ya rubuta mata a massage kar ta yarda ta rinƙa barci ba a jikin sa ba tarinƙa nuna masa kamar barci take ta mirgino jikin sa ta nuna kamar bata san ta faɗo jikin na shi ba,kara matse ta yayi sosai a jikin sa yana bata hot kiss tula tulan breast nata dake sokin sa a kirjin sane ya fara damun sa ɗan sassauta rungumar da ya mata yayi dan ya samu su ɗan raba jiki, kaɗan kaɗan yake jin feeling akan ta sai da yayi kissing nata mai isar sa sanna ya zame bakin sa daga nata tare da raba jikin su ya ɗan juya ya lumshe ido shi duk a tunanin sa tana barci bata ji me ya mata ba ita kuwa mutuwar kwanche tayi dan gaba ɗaya ya gama kashe mata jiki ya ruɗar da ita dannewa kawai take tunani ta shigayi anya zata iya biyewa shawarar yaya Khalid da yaya Aryan kuwa? Gaskiya wanna aiki ne mai wahala ba zata iya ba gaskiya sai dai su kawo wani shawarar da wanan tunani barci yayi awon gaba da ita, kusan tare barci ya ɗauke su

KANO NIGERIA

Auty Amarya na kokarin fita bedroom nata dan lokacin chin abinci yayi tasan yanzu gaba ɗaya su Abba sun haɗu a palo dai dai zata fita wayar ta dake bedside drawer tafara rigging kamar bazata je ta ɗauka ba sai kuma ta fasa ta koma taje ta ɗauki wayar sunan hajj sadiya che ta bayyana saman screen ɗin wayar zama tayi a bakin gado kafin tayi picking call ɗin tare da manna wayar a kunnen ta

Daga ɗayan ɓangaren hajj sadiya tace “Hello hajj ya hajara Ykk”dogon numfashi Aunty Amarya taja kafin tace “lfy Ykk” “Alhadulillah daman nakira na sanar da ke ne yanzu gagarabadau ya mutu sai dai na kaiwa malamina dake bayalsa ya yi mana aikin Farida da Aisha” miƙewa tsaye Aunty Amarya tayi tare da dafe kirji chike da raza na tace “yaushe ya mutu!? “Yanzun nan gani nan ma a kofar gidan sa yanzu baafi minti ɗaya ba”komawa Aunty Amarya tayi ta zauna gaba ɗaya jikin ta ya mutu tama rasa me zata che wa haj sadiya “haj ya hajara ina zulaihat ne? Tun shekaran jiya bata kirani awaya ba itama malamin mu na Niger ya kusa kammala aikin ta tsakanin ta da Safras”tsaki Aunty Amarya ta ja kafin tace “zulaihat bata koma wajen ki ba ai ni tun shekaran jiya da na ganta da safe ban sake ganin taba na yi tunanin ta gaji da zama da nine ta koma wajen ki ai” “aa zulaihat bata dawo waje naba kai amma wanna yarinyar yanzu a gidan naki ma sai data fita yanzu tana chan kila wani saurayin nata tabi yarinya kwata kwata bata jin magana ni Allah yasa malamin nan ma ya gama aikin nan da wuri mu sa mu ayi auren nan kila idan ta shiga gidan Safras ɗin ta rage yawon banzan nan,barima na kira layin ta dan uban ta koma ina take ta wuce ta dawo” guntun tsaki Aunty Amarya taja dan ita gaba ɗaya yanzu haushi ma suke bata daga zulaihat ɗin har Haj sadiyar “haj sadiya sai munyi waya yanzu zanje palo muyi breakfast ne kowa ya hallara saura ni zamuyi waya anjima” tana gama faɗin hakan ta katse kiran ba tare da ta jira amsar haj sadiya ba mayar da wayar tayi saman drawer gefen gadon ta miƙe ta fice daga ɗakin tana mai bakin ciki mutuwar gagarabadau

Da sallam ɗauke a bakin ta ta shiga palon Abba gaba ɗaya wayan da suka rage a gidan suna zaune saman table diyana na zaune kusa da Aryan ɗin ta tayi shiru ta kasa chin abinci zama Aunty Amarya tazo tayi a kujerar kusa da Abba tana harara Aryan da diyana

“my diyana kici abinci mana” chewar Abba yayi maganar yana kallon diyana,sai lokacin Aryan ya ɗago kai tare da ajiye wayar sa a gefe saman table ɗin ya jawo plate na abincin nata ya ɗauki spoon ɗin ya ɗibo chips ɗin ya kai mata bakin ta, shiru tayi bata buɗe baki ba kuma bata ɗago ba tana kallon kasa, mai da spoon ɗin yayi chikin plate ɗin ya ɗan rungumota da hannu ɗaya yana faɗin “my jidda menene kuma….bai karshen maganar ba yaji ta sake masa jikin ta gaba ɗaya a jikin sa kokarin faɗuwa take dan bai riƙe ta da kyau ba chikin zafin nama ya rikota da kyau yana faɗin “my jidda lfy me ya faru” miƙewa Abba yayi yana faɗin “suma fa tayi Aryan” tun Abba bai gama rufe baki ba Haidar ya miƙe da sauri ya nufi fridge ya ɗauko ruwa, ɗaukan ta Aryan yayi chak suka koma tsakiyar palo ya shinfiɗe ta saman karpet Haidar ya miƙo masa ruwa, chikin sauri ya balle bakin robar ruwan ya tarbo a hannu ya fara shafa mata a face nata gaba ɗaya su Ammi sun kewaye su suna jiran farfaɗo war ta zama saman sofa Abba da Aunty Amarya su kayi Ammi da Ummi kam sun kasa zama suna tsaye Omar Haidar suma suna tsaye,sai kwaɓe fuska Aunty Amarya take

Sau uku Aryan na zuba mata ruwa amma shiru bata farfaɗo ba sai a na huɗun ne taja dogon numfashi tare da sauke ajiyar zuchiya tun bata buɗe ido ba ta fara sambatu “Aunty farida yaushe ne jirgin mu zan tashi wlh na kosa na ga su hiyana ina kewar yaya Aryan kin san me Aunty farida ina zuwa gida Ammi zan fara runguma sai yaya Aryan sai kuma hiyana da Aunty Zahra aa na manta Ammi ce first sai Abba tukun nan yaya Aryan” shiru palon yayi suna sauraron sambatun diyana Allah sarki wato shine maganar ta na karshe tana cikin hayyacin ta lokacin guda Abba yaji idon sa ya chiwo da kwalla ba karamin tausayi diyana ta basu ba,mutun ya zauna chikin fitar hayyaci ba karamin abu bane, amma Alhadulillah dan da alama ta dawo hayyacin ta tun da har tana iya sambatu da sunayen yan gidan

Ji Aryan yayi ba zai iya chi gaba da jin sambatun nan nata ba tana tayar masa da hankali hannu ya sanya ya shafa fuskar ta tare da matsowa kusa da ita ya riƙe hannun ta ɗaya chike da kaunar ta ya fara magana “my jidda buɗe idon ki kallemu ai tun ɗazun jirgin naku ya iso gida” jin muryan Aryan ya sanya ta waro blue eyes nata da sauri tare da miƙawa zaune tana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya miƙewa tayi da sauri ta rungumi Ammi tana murmushin tana faɗin “Ammi nayi kewar ki daman na faɗawa Aunty farida muna isa ke zan fara runguma” sosai Ammi ta rungume itama tana faɗin “my diyana nima nayi kewar ki sosai amma yanzu dai duk bamu ya kamata ki fara runguma ba mijin ki ya kamata ki fara nunawa farimcikin ki dan ya fimu bukatar ganin hakan” turun diyana ta tsaya chike da mamaki tace “Ammi miji kuma yaushe na samu miji” Abba ne ya ansa zanchen da chewa “Eh my daughter mijin ki” sakin Ammi tayi ta kariso wajen Abba tana faɗin “Abba wanene kuma mijin nawa? Da hannu Abba ya Nuna mata Aryan dake tsugunne ya kasa mikewa dan gani yake kamar har yanzu bata dawo dai dai ba a wani bangare na zuchiyar sa kuwa farincike yake yana godewa Allah da dawowar matar sa hayyacin ta

Kallon sa diyana tayi kafin ta ɗago ta kalli sauran jamaar palon chikin nitsuwa tace “Abba ni yaya Aiman nake so ba yaya Aryan ba da yaya Aiman mukayi alkawarin Aure ba yaya Aryan ba” tirkashi gaba ɗaya zuba mata ido jama’ar palon sukayi Aryan jin kalaman nata yake tamkar ana zuba masa garwashi a zuciya ashe Aiman yayi gaskiya shi diyana ke so chije lips nashi yayi lokaci guda idon sa ya sauya jijiyoyin kansa suka miƙe huci ya fara yi kamar wani zaki diyana ta haɗa masa zafi biyu lokaci guda na farko ta tuna masa da Aiman na biyu tace ba shi take so ba zuciyar sa zafi yake masa jiyake tamkar zata fasa kirjin sa ta fito waje,chikin zafin nama ya miƙe yana kokarin barin palon da sauri Abba ya dakatar da shi ta hayyar riko hannun sa yana faɗin “koma ka zauna” ba musu ya koma saman sofa ya zauna tare da dukar da kai kasa umarni Abba yayiwa su Ammi akan su zauna zama sukayi gaba ɗayan su, saman sofas

“Kai Omar kaje ɗakin Aryan zakaga wata jaka baka mai ɗan girma ka kawomin” chewar Abba da sauri Omar ya juya ya fice daga palon
Dawo da kallon sa Abba yayi kan diyana dake zaune kusa da Ammi ya fara magana “my daughter kiyi hakuri da Auren da na miki ba tare da na tambayeki ba, abu na gaba Allah ya yiwa Aiman rasuwa inason ki anshi Aryan a matsayin miji domin da Aryan da Aiman duk abu ɗaya ne kuma Aryan ya riga Aiman fara son ki kema kuma Aryan ki ka fara so ba Aiman ba nasan kinche Aiman kike so ne ba dan komai ba sai dan alkawarin da kika masa akan zaku yi Aure nasan da kin san Aiman ya rasu ba zaki che hakan ba,ina jinjina miki da kokarin chika alkawari da ki kayiwa Aiman duk da ba shi kike so ba” shiru palo yayi ba abun da kakeji sai kukan diyana kuka take sosai kukan da take ne ya sanya Aryan ɗagowa baya san kukan ta ko kaɗan idan tana kuka zuciyar sa zafi yake masa

Chikin kuka tace “Abba dan Allah ka chemin wasa kake yaya Aiman bai rasu ba wlh na yarda yaya Aryan nake so ba yaya Aiman ba pls kucemin wasa ne yaya Aiman na ɗakin sa” kuka take sosai kakar ranta zai fita kasa jurewa kukan nata Aryan yayi ya miƙe ya dawo kujerar kusa da tasu ya zauna chikin kulawa ya fara magana “my jidda ya isa kukan nan kiyi shiru” “yaya Aryan kai ma ka yarda yaya Aiman ya rasu kenan? “My jidda dole na yarda dan ba’a wasa da mutuwa yanzu dai ki dai na yin maganar kinji idan ba haka ba zaki sanya zuciya ta ta fashe” rage sautin kukan nata tayi dai dai lokacin Omar ya shigo hannun sa ɗauke da jakar da Aryan ya bawa diyana tsaraba lokacin da ya dawo makka

Ansar jakar Abba yayi ya buɗe ya fido da abubuwan dake chiki wayan nan Box guda biyu da Aryan ya ɓuye bai nunawa diyana ba Abba ya ɗauko ɗan babban ya fara buɗe wa, wani dangareren sarkan gold ne wanda ya ansa sunan shi gold ne awajen,mai matukar kyau da tsada sai ɗaukan ido yake ɗago kai Abba yayi ya kallin diyana da ta kwantar da kanta jikin Ammi tana kuka kasa kasa “my daughter ga sadakin ki 100m shine kuɗin sadakin ki daga mijin ki” hannu Ammi ta sanya ta ansa ta sanyawa diyana a tafin hannun ta tana faɗin “an sa ki gani my diyana” kuka kawai take taki kallon sarkan buɗe ɗayan kwalin Abba yayi ya miƙawa Aryan ansa Aryan yayi ya fito da wasu kananan Fararen box masu bala’i kyau daga chiki buɗe ɗayan yayi dan kareran diamond ring ne wadda ya amsa sunan sa diamond sai kyalli yake yana ɗaukan ido ring ɗin ɗauke yake da harafin A ajikin sa ta tsakiya ajiyewa yayi a gefe ya ɗauko ɗayar box ɗin ma ya buɗe shima ring ne irin ɗaya da wan da ya buɗe da farko komai nasu ɗaya sai dai wanan ɗauke yake da harafin D a jikin sa ɗago kai yayi ya kalli diyana dake ta faman kuka kasa kasa yace “my jidda tashi ki zo”tashi tayi tazo gaban sa ta tsaya dan saman sofa mai zaman mutun ɗaya yake zaune hannu ya sanya ya nuna mata saman chinyar sa akan ta zauna satar kallon su Abba tayi kasa kasa yana kallon chikin idon ta miƙewa Abba yayi yana faɗin “zama chikin turawa ya ɓatamin ƴaƴa basa kunya ta yanzu kwata kwata” ya kai karshen maganar tare da fice palo chikin sauri su Ammi suka bi bayan sa taɓe baki Haidar yayi ya fice shi da Omar suna mamakin yaya Aryan

Aryan Kamar jira yake su Abba su fita ya jawota jikin sa yana faɗin “my jidda ya isa kukan nan haka kwantar da kanta tayi saman kirjin sa kasa kasa tace “yaya Aryan kukan ne ai yaki tsayawa” hannu ya ɗaura saman face nata yana goge mata hawaye yana faɗin “to ya isa karki bari hawayen ya sake fitowa kinji? Gyaɗa masa kai kawai tayi ta kara lafewa a kirjin sa hannun ta ya riƙo ya sanya mata diamond ring mai tambarin harafin A sanan ya miƙa mata mai tambarin harafin D yace ta sanya masa ansa tayi ta sanya masa a ya tsan sa na kusa da karamin ba karamin kyau ring ɗin ya musu ba kamar dan su akayi shi
Kasa kasa da murya kamar mai raɗa yace “my jidda tashi muje na baki abinci” maƙe kafaɗa tayi chikin shagwaɓa tace “aa na koshi yaya Aryan” jan karan hanchin ta yayi chikin wasa yana faɗin “idan baki chiba zan miki Allura” chikin sauri tace zanci to amma kaɗan” ba tare da ya sake magana ba ya miƙe ya saɓata a kafaɗar sa tana faɗin “yaya Aryan dan Allah ka sauke ni zan tafi da kafana” bai tan ka taba ya wuche ya ɗauki Box na sarkan sadakin ta da sauran kayan ya fice daga palon kai tsaye part na shi ya wuce

Masu karatu mu damalmale da ku a soyayyar Habibi da jiddan sa gobe idan mai dukka ya kai mu su habibi yau abun nema ya samu 😹😹

Ina muku fatan alkhari masoyana masoyan Duk Karfin Izzata fatan Allah ya chika muku burin ku na alkhari

Ina miko gaisuwa da jijjina gare ku

Aunty Asma’u
Aunty Hauwa’u
Maman Twins
My mum
Dr Aisha
Aisha
Hauwa’u yar adamawa jinin yola
Sister Halima
Sister Deeja
Aunty Amira
Nana farida
Deenat Ahmad
Maman Amir
Hafsat Rabi’u Abubakar

Da duk sauran wayan da ban samu daman kiran sunan su ba ina godiya ina ganin comments na ku ya sanyani farimciki da nishaɗi yana rage min kishin hiyana da nake ki dan na lura hiyana ta fara shisshigewa masoyina 🥲

Pls a bani hot🔥 comments

💋Duk Karfin Izzata 💋

 

💖The Talent Troupe Writer’s 💖

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*

Maman Shureim gaba ɗaya wanan page ɗin na kine more love 🥰

Back to top button