Gidan Aunty Book 1Hausa NovelsHausa Novels

Gidan Aunty Book 1 Page 16

Sponsored Links

BOOK 1 📕
بسم الله الرحمن الرحيم ❤️❤️…
Free page 16 🦋

Sosai tazaro idanuwanta waje tana faman girgiza kai,bata san lokacin da ta karasa kusa dashi  tana kokarin goge masa ba , gigitacciyar tsawar da ya daka mata a lokaci daya da lafiyayyen marin da ya sauke mata ne yasata kara firgita, ga kanta da yake tsananin sara mata, lokaci d’aya taji juwa na dibarta “Dan Allah kayi hakuri” shine abunda bakinta ya iya furtawa, be kuma cewa komai ba sai mikewa da yayi kwasan wayoyinsa,Daidai lokacin da tahee take kokarin fadawa kan wani designer dake gefenta , taku daya yayi ya riko damtsen hannunta tare da Jefata kan daya daga cikin kujerun tare da sakin siririn tsaki, cikin bacin rai ya bar part din azahiri Kuma fuskarsa tananan a yadda take, baka isa fassara yanayinsaba ” me ya Hana ban karyataba “ ya fada a cikin zuciyarsa ransa na kara baci , dogon tsaki yaja iya kasan makoshi, hatta zaki daya bude masa kofa yayi mamakin ganin sa haka amma bashi da hurumin magana a haka har suka koma part dinsa.

Tunda ya jefata kan kujerar da ya tashi har yanxu bata bar wajan ba , sosai taji kanta na sara mata, ta dau kusan minti biyar zaune a wajan tana addua, kafin lokaci daya ta nemi ciwan kan ta rasa gabaki daya, ajiyar zuciya ta sauke sai a lokacin kumatunta ke mata zafin marin dayayi mata , dafe wajan tayi tana sosawa “Mugu kawai” ta fada a zuciyarta tana turo dan karamin bakinta, amaimakon ta koma kitchen kai tsaye dakin ta ta nufa tare da fadawa kan gado tana sauke a  jiyar zuciya har yanxu hannunta na kan kuma tunta.

*******Ta dade kwance a ban dakin a sume, bugun ban dakin da ake da karfine ya farfado da ita, tayi mamakin ganinta kwance a kasa ga tsami da jikinta ke mata,kara bugun kofar da akaine yasata mikewa cikin din gishi, towel dinta dake Yashe a kasa ta dauka tare da daurawa, da Kyar take taka kafarta dake mata tsami, sai bin ko ina da kallo take, da kyar ta karasa jikin kofar, a tsaye ta sami aunty duk ta rude, tana ganinta ta saki ajiyar zuciya” me kikeyi acikin ban daki tun dazu, kinsan irin neman ki da nayi”, batasan lokacin da bakinta ya furta “bacci ne ya daukeni “,kallan ta aunty tayi tana sakin baki “bacci fa Kikace amrah “, gyada mata kai amrah tayi tana turo bakinta tare da rabata tawuce , binta kawai aunty tayi da kallo batare da tace komai ba tabar dakin. Samun waje amrah tayi kan gadonta tare da dakko wayarta dake ajje saman gadan, dogon tsaki ta saki sai a lokacin take tuno abunda tahee tayi mata,azabure ta mike tsaye “ ni amrah , nice yau nake bawa wata yar iska hakuri, ni amrah hmmm” girgiza kai tashigayi “ yau nice na kaskantar dakai na bawa wata shegiya hakuri, wallahi ko zanyi yawo tsirara sai na wulakanta ta sai na musgunawa rayuwarta sai tasan dani take magana “ ta kare zancen tana sakin kwallar bakin ciki…

******* Director part dinsa ya nufa sai faman taunar lips dinsa yake, be bi steps ba ta elevator ya hau , a second floor dinshi ya tsaya ko ina sai faman tashin kamshi yake da sanyin Ac musamman kamshin turaransa da ya kama ko ina na part din, rigar jikinsa ya cire kai tsaye faffadan zurar jikinsa ta fita fari tass dashi,sosai muscles dinsa da 6 spacks dinsa ya fito kallo daya zaka masa kasan ba karamin motsa jiki yake ba,kofar da take facing dinsa ya nufa, ya dau kusan mintuna 30 aciki kafun daddadan kamshi ya karade ko ina , sosai yayi kyau , a maimakon suit yanxu  kananan kayane a jikinsa ,tun daga kan bakar jigar jikinsa tare da bakin wanda jikinsa , sosai yayi kyau cikin kayan , sumammiyar gashin kansa ya fito sosai yau ma kadan daga cikin yalwataccen gashin kansa ya fito har wajan idanunsa, sabida tsananin bacin rai pink lips dinsa ba karamin turuwa yayi ba sai faman tsuke fuskar yake, cikin takunsa na kasaita ya hau elevator tare da nufar 3rd floor, a maimakon hanyar da ya saba bi yanxu wata daban yabi,babban waje ne nashakatawa gata iska me dadin gaske dake huro wajan,kayataccen wajan shakatawa ne a wajan sosai wajan ya hadu,ga gefe d’aya dayake abude ko ruwan sama akai yana dan shigowa kadan kadan , akan daya daga cikin kujerun shakatawan yazauna ne kama da sararin samaniya, sosai yanayin wajan yasakashi cikin nutsuwa sai faman lumshe ido yake, daga gefensa ma wani cup ne me shegen kyau cikin sa wani lemone kamana da sararin samaniya shima.sai faman lumshe idanuwansa yake yana budewa, wayarsa dake ringing a hankali ya dauka batare da bata lokaci ba, Ahankali yake magana ko nakusa dashi ba Lalle yaji me yake cewa ba,sai lumshe kyawawan idanuwansa da yake faman yi.

🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧
Futowar da ammi zatayi a kitchen ne taga babu king babu tahee, tsayawa bin falon tayi da kallo kamar anan ne zata gansu,a tunaninta tahee ta koma daki ne shiyasa bata bita ba ta dauki wayar ta da niyar kiran king, tana kara wayan a kunnenta ta haye stair case din din falon..

A dan kwanciyar da tayi batasan lokacin da bacci ya dauketaba, wasu matasan yara tagani da akalla befi su bata shekaru uku ba, kyawawa dasu sai faman kuka suke , daga gefensu wani farin macijine shima tass dashi, kallan tahee dake gefe sukai sai suka kara fashewa da kuka , suna kuka suna biyota , cikin tsorata tahee ta fara jan baya, girgiza mata kai suka shigayi, cikin daddadan muryarsu “sun kashe mana farin cikin mu , sun cutar damu, bamuyi musu komai ba, laifin me mukai musu, nace laifin me mukai musu” suka karasa cikin data tsawa , firgita tahee tayi da yanayinsu, ganin sun tsaye ne yasa itama tsayawa,cikin rawar murya tahee ta fara magana “su..suwane ku, me nayi muku”, dariya suka saki tare da kara sakin wani saban kukan, “SIF,LOLA,”sai kuma farar magan ciki ta shafa can macijin nan” SUSAN”, tana gama fadar haka suka kara sakin kuka tare da bace bat kamar basu taba wanzuwa ba. A firgice tahee ta farka daga baccin da ya dauketa bakin ta dauke da addua , shafa wuyanta da ya dan rike tayi” me yasa nake yawan mafarkin masu sunannan,su wanene su”ganin babu me bata amsa yasata mikewa , kayan jikinta ta cire tare da shiga wanka , mintuna kadan tafito daga nan dakin, daya daga cikin abayoyin da ammi ta bata ta saka , gaban mudubin dake shake da kaya ta nufa,kurawa fuskarta ido tayi ganin irin sahirtaccen kyan da tayi a cikin kwanaki uku da tayi a cikin gidan , sanye take cikin red Egyptian abaya sai faman walwali stone din jiki ke dauka,asalin farin fatarta ta buzaye ta fito tass a jikinta, yayinda cikakken yalwataccen gashin kanta ya sauko har wajan kugunta, sosai bakin kwantaccen gashin goshinta ya kara kwantawa tare da dogon siririn hancinta , ba make up ne a fuskarta ba amma fadin haduwarta bata lokaci ne musamman dan karamin lips dinta da ya fito tass dashi kamar wacce ta saka janbaki,bakin kwalli ta saka da ya fito da farin kyawawan idanuwanta, sosai kwallin ya fito da asalin kwayar idanunta,cikakkiyar gashin girarta da dogayen eye lashes din idanuwanta su suka kara fito da ainahin kyawun fuskarta , ba ma a bociyar lip gloss bace shiyasa tabar dan karamun lebenta a haka, ribbon dinta ta dauka shima red colour tana kichiniyar daurashi, sosai ta jigata kafun ta daureshi sabida cikowarsa,mayafin abayarta ta dauka tare da yafashi saman kanta, red din takalmin ta ta saka , gaban mudubin ta kara komawa tare da karewa kanta kallo , murmushi ta sakar wa kanta tare da rufe fuska , “ ke din me kyau ce “kalmar da kullum taheer ke fada mata, murmushi kawai ta kara saki , tayi kewarsu sosai, hanyar fita daga dakin ta nufa bayan ta gama feshe jikinta da turaruka, Daidai lokacin da yan matan ke shigowa part din,amrah sai faman dingishi take haryanxu jikinta be dena tsami ba, sakin baki tayi ganin irin kyawun da tahee tayi, bama ita kadai ba hatta su ihsan duk sakin baki sukai suna binta da kallo, gaishe da su tayi babu Wanda ya amsa mata sai ihsan dake faman sakin murmushi, “tubarkallah Masha Allah , gaskiya ke kyakkyawa ce tahee”,sun kuyar da kai kawai tahee tayi tana wasa da yan yatsun hannunta, binta da kallo su sumayya sukai kowa yana hadiye abunda ke ransa, dogon tsaki amrah taja tare da karasa kan daya daga cikin kujerun falon, sosai take bakinci, dama ace Itace take da wannan kyawun, wani dogon tsaki ta kuma ja tare da daukar wayarta suma duk yan matan waje suka samu tare da zama ,ihsan ce ke kokarin magana ,jin sallamar zoya ne ya katse mata zancenta, inda Ihsan take ta nufa “aunty ihsan” rungumeta ihsan tayi “na’am my baby”kallan yarinyar da aka kira da baby tahee tayi , Itace dai yarinyar da ta gani tana bacci,”aunty ihsan wai ina da wata aunty tana ina “murmushi ihsan ta saki, “toh daman bazuwan kowa kikai ba sai na auntyn taki ko”dariya zoya tayi tana rufe fuskarta , itama murmushi ihsan din ta saki “oya kinganta” juya wa zoya tayi tare da kallan Wanda aka nuna mata, zaro fararan idanuwanta irin na king tayi, “aunty ihsan tana kyau, harta fini ma, amma yaya king dina ya fita” dariya ihsan ta saki kawai , sai alokacin tahee taga tsananin kamanninta da Wanda yake zuwa part Dinsu,murmushi kawai tahee ta sakar mata, itama murmushi zoyan ta saki “Aunt ya sunanki” taheera shine kadai abinda tahee tace,kara zaro ido zoya tayi “sunanki me dadi , ni kuma zoya yanxu Kema kinzama aunt dina kinji”girgiza mata kai tahee tayi sosai yarinyar tashiga ranta, duk wannan abun su sumayya na zaune suna kallan ikon Allah musamman amrah dake jin kamar ta samu wuka ta caccakawa tahee..shigowar ammi ne ya katsemata tunanin da ta shiga,”yaude yan mata na sai yanxu nake ganinku” ko wannansu murmushi ya saki sabanin sumayya da amrah da suka saki na yake “Aah ammi kinsan akwai school shiyasa “gyada musu kai ammi alamun gamsuwa kafin ta mike ,”yanxu dai ku Tashi ku kaiwa son abinci sai a dawo a yi hirar”, cikin firgita kowannansu ya zaro idanuwansa tare da furta YAYA KING…..

Comment and share .

💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖
Duk karfin izzata
Gidan Aunty
Ya fita zakka
Jini daya
Sarki sameer
Baby .

MSS LEE💖..

‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/JyvVuOvzYyF19np8UmFKV4

💖💖GIDAN AUNTY 💖💖
(a heart touching love story)

Story & written
By
Mss Lee 💖

PAID BOOK
littafin gidan aunty na kudine akan 300 kacal ne so har karshe zai biya ta wannan bank din 7041879581 opay Ayshatou Galadima , sai a turo shaidar biya ta wannan number 07041879581.

Masu bukatar a tallata musu kasuwancin su , su tuntubeni cikin wannan number 07041879581.

Leave a Reply

Back to top button