Gidan Aunty Book 1Hausa NovelsHausa Novels

Gidan Aunty Book 1 Page 26-27

Sponsored Links

Free Page 26 and 27 🦋

“Dady na “ ta kara kira sunansa idanuwanta na zubar da hawaye, salati dada ta saki “ Innalillahi wa inna ilaihi raji’una, Allahumma a jirni fi musu bati , tahura wanene kuma dady”, dada ta fada da nufar inda tahee take , wani kukan tahee ta saka “karku tabani bana so, ku dena ta bani su wanene ku”, gabaki d’aya su abeey kasa motsi sukai sai Innalillahi da suke maimaitawa tun dasu , ammi ko tsayuwa ta kasa sai waje ta samu ta zauna ta cigaba da kukan da yazo mata.nunfashi king ya saki yana kara hade rai tare da kokarin banbareta daga jikinsa, kamar wacce ake karawa karfi haka ta kara kudun duneshi tana sakin kuka, nunfashi king ya saki me zafi , besan lokacin da ya data mata tsawa ba, sosai ta razana da tsawar da ya daka mata, hatta abeey sai da suka kallesa, kuka tahee ta fashe dashi, cikin futar hayyaci tayi kofa da niyar fita,ko karin riketa abeey yake ,wata karar tasaki “banaso banaso banaso, shima dady bayasona ,Nima banasan kowa” ta kara fashewa da kuka , cikin ta da ya murya ne yasata sakin kara tana durkushewa, a wajan tare da sakin wani saban marayan kuka tana dafe cikinta,taki bari kowa ya ta’bata sai kuka take, lumshe idanuwansa king yayi kafun a hankali ya tako inda take, jada baya ta soma tana girgiza masa kai tare da sakin wani saban kukan, be dena bin nata ba har ta jin gida da jikin bangon, tsayawa dada tayi zani a hannu tana kallan ikon Allah ,tun bayan kuka data sa mata ta buya bayan ummey dake tsaye itama , a hankali ya tsugunna a wajan kansa har ya fara sara masa, gefe tayi da kanta tana cigaba da kukanta ga ciwon cikin dake nukur kusarta sai faman rike ciki take, “kalle ni” ya furta a hankali yana binta da idanuwa,dan mitsitsin bakinta ta tabule kamar me shirin yin kuka “shhhhhh” yace mata , shirun kuwa tayi har yanxu taki dago da kanta sai hawayen dake biyo fuskarta,” me akai miki kike kuka “ ya furta a fusge kamar bashi ba, bakin ta bude daniyar kuka ya kara dakatar da ita “bana san kuka” kukai kuwa gaya dena “basu ne ba suna ta bani nace kuma sudena banaso, Kai ma bakasona ka koreni” ta karasa maganar tata tana turo dan karamin bakin ta kamar wata yar yarinya “ Wannan yarinyar Anya ba aljana bace “ ya fada a zuciyarsa, amma sabida buguwar datayi aka yasa bece mata komai ba, “toh shikenan mun dena , suma bazasu ta baki ba”, da sauri ta kallesa tana share hawayen fuskar tata, “dady da gaske kake”,girgiza mata kai yayi kawai ba tare da yace mata komai ba, da sauri ta fada jikinsa tana kara dukun kune shi” dady banasan su na tabani kaji”,be ce komai ba sai lips dinsa da ya datse “ dady ! You killed me “ ya fada a zuciyar sa , ganin ta fara kuka kasa kasa ne yasa ya kalleta, be auneba ta fashe masa da kuka, “dady cikina, cikina” ta fada tana rike cikin nata, kasan cewar yasan dalilin ciwon cikin nata yasa be ce komai ba , ya dauketa tare da barin dakin a hannunsa kamar wata yar baby, bin bayansu da kallo su dada sukai, kafun ta sauke a jiyar zuciya, kallan su ummey tayi” mude mun shiga uku, yanxu kenan sadauki yazama Baban ta, ku kalla fa , wai bata san muba “ babu Wanda ya kulata harta gama surutun ta kowa da abunda yake sa’kawa a ransa.

🫧🫧🫧🫧🫧

Tunda aunty ta koma part din ta tsabar murna bata bata sanar wa da amrah da bata falon komai va, yayarta da ta haifi amrah ta kirawo, “yar uwa rabun jiki, Al bishirinki “ banji amsar da aka bata ba sai dariyar da aunty ta saka “uhmmm tsinanniyar can ai ta mutu, yanxu aikin mu zaizo cikin sauki daman “ gabaki d’aya yadda ta ga taheen sai da ta sanar wa yar uwar tata suna yi suna dariyar farin ciki , tana gama wayar tata takirawo aminiyarta, bata jira komai ba ta nufi dakinta cikin kasa kasa da murya ta sanar da ita Abunda ke faruwa,banji me akace mata ba Amma sosai ta nutsu tana saurarar kawar tata , wata dariyar mugunta aunty ta Saki “ bar shashashu , a tunaninsa ina yin duk wannan abun sabida su, Kema kinsan wacece ni , ina gama an fani dasu zan zubar dasu”, kara kyalkyalewa tayi da dariya, sun dan jima suna wayan kafun ta kashe kiran.

******* wayace kare a kunnan amrah , sosai ta nutsu tana sauraran abunda ake ce mata, fuskarta dauke da yalwataccen murmushi, ta dauki dogon lokaci taba wayan kafun ta kashe , dariya ta saki sosai saida tayi me Isarta sannan ta tsaya “ Lalle yarinya da dani zakice zaki taka, cikin sauki na gama dake saura aunty inma in ta kammala mun aikin” ta karashe zan can nata tana sakin dariyar mugunta harda rike ciki, ta dade a hakan sai ga aunty ta shigo itama dakin, duk abunda ya farun saida auntyn ta sanar da ita, nunawa tayi kamar batasan anyi ba, ta kara shiga cikin murna dan tabbatar da zancan mahaifiyarta, tsabar murna har wata kwarya kwaryan liyafa suka hadawa kansu ko tunanin su duba a asibiti ba sayi , duk a tunaninsu ta mutu.

🫧🫧🫧🫧

Direct office dinsa ya nufa da ita sai faman kuka take masa, baice komai ba sai ajjeta da yayi cikin wani bedroom me kamar daki komai nacikin daki akwai a ciki ga wasu na urori dake dakin kamar ba cikin asibiti ba, murkususun ta cigaba dayi tana kiran “dady !! Dady”, kallanta yayi yana lumshe idanuwansa da suka fara gajiya sabida ciwon kan da yake ,kafun ya karaso a hankali inda take, wasu injection ya hada tare da nufar inda take, tana ganin injection dinnan ta kara sakin wani saban kukan, tana girgiza masa kai “banaso , banaso” be kulata ba har ya karaso wajan , a guje ta mike duk da ciwon dake cinta ta saka kafa zata gudu, taku daya yayi ya rike damtsen hannunta, kuka ta saka masa tana kokarin kwace hannunta da ya rike , ganin allurar hannunsa yasa taci gaba da kokarin guduwan, sosai tasaka iya karfinta tana san kwace wa , kwakkwaran riko daya yayi mata tare da zaunar da ita kan gadon har lokacin kuka take, alkuran ya ajje abayansa tare da kallonta “na fasa to, yimun shiru”, kallan hannunsa tayi ganin babu alluran yasa lokaci d’aya kukan nata ya tafi, jingina tayi da jikinsa tana dan turo baki , be ce mata komai ba har kusan minti daya tana wasa da abun rigarta, allurar da taji ya tsira matane yasata sakin kara da niyar mikewa, sosai ya riketa kwakkwaran motsi ta kasa harsaida ya kammala allurar tasa, hade rai yayi sosai kamar bashi ba , cikin kausashshiyar murya ya firta “yi mun shiru” tsit kuwa kukan nata ya dauke sai karamin lips dinta da take turo masa , tsawan lokaci suna a haka lokaci zuwa lokaci yakan dago da idanuwansa , jim kadan ya kara dago da idanuwan nasa yaga ta fara bacci, ajiyar zuciya ya sauke kadan” am dead “ ya furta kawai kafun ya dakko wasu na ura, sosai yayi bincike akan ta bayan Wanda yayi mata lokacin dressing , nunfashi ya fesar ganin kiran abeey, be dau dogon lokaci ba ya dauki kiran ,”kana ina “shine kadai abunda abeey yace masa, “office “ king ya furta tare da lumshe idanuwansa kamar abeey na kallonsa, ko minti biyar cikakkiya abeey beyi ba ya shigo office din, inda tahee take kwance ya kalla tare da girgiza kansa, “me ya sameta” ya kara tanbayar king din” she lost her memory abeey” da sauri abeey ya kallesa tare da furta Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, ganin hakan yasa king ya mike daga inda yake tare da nufar abeey din,” please abeey karka tayar min da hankali , kasan ba lapiya Kake dashi ba please abeey “, zuciyarsa abeey ya dafa tare da dafe kan sa, rikosa sosai king yayi duk da yanayin tashin hankalin da ya shiga amma a fuska ba alamun hakan, dago da idanuwansa abeey yayi da suka fara jaa alamun ciwon sa zai tashi,”kayi mun alkawari guda daya” kallansa king yayi da lumsassun idanuwansa, sosai abeey ya kara dafe zuciyarsa “KAMUN ALKAWARI ZAKA AURETA YAU DINNAN “.

Comment and share ✍️
Mss Lee 💖

Alhamdulillah yau na kawo karshen free pages dina , mea san cigaba da gidan aunty zai turo kudin sa fa wnn asusun 7041879581 palm pay Ayshatou galadima , sai a turo shaidar biya ta wannan number 07041879581.

Masu comment ina Godiya 💖🫶.
💖💖GIDAN AUNTY💖💖
( a heart touching love story)

Story & written
By
Mss Lee 💖

PAID BOOK

MAISAN COMPLETE DIN GIDAN AUNTY YAYI MUN MAGANA TA WANNAN NUMBER 07041879581

Leave a Reply

Back to top button