Gidan Aunty Book 1Hausa NovelsHausa Novels

Gidan Aunty Book 1 Page 43-44

Sponsored Links

BOOK 1📕

Page 43_44💖

Dan karamin duka king ya kai masa a kirji yana jan dogon tsaki,”matsalata da kai har yanxu you are not serous “, kallansa sosai sha’aban yayi kafun ya furta “wannan ba maganar serous bace Gee,idan baka san me yasa abincin da take so kaji”,gajeran tsaki king yaja ba tare da yace komai ba,dariyar shakiyanci sha’aban ya saki” toh shiknn tunda baka santa ai ga su basma sai ka hadasu ka aura “,wani banzan kallo king ya jefawa sha’aban,shima be damu ba sabida yasan halin king ,in a serous tone ya furta “ Gee karkayi wasa da damarka,ina guje maka ranar da yarinyar nan zata dawo sense dinta, ta gane baka santa,ka nutsu kafuskanci future dinka gee,I’m advising you as your brother and best friend in ka bari damar ka ta kwace maka shikenan ka rasa ta,kwanda ka rike matarka hannu bibbiyu,kafin muzo suna Muma Allah ya bamu matayan mutashi daga kauraye “ ya karasa maganarsa yana kashewa king ido cikin zolaya,kafun yayi saurin barin office din,kofar king yayi da kallo lokaci d’aya yaji zuciyarsa ta buga ,kalaman sha’aban na sake dawo masa,kallan da tayi masa dazu ne yafi komai tsaya masa arai, lumshe idanuwansa yayi yana tuno yadda idanuwanta suka tara kwalla, kokarin share zancen yayi amma lokacin da suke toilet ya kara fado masa arai musamman lokacin da ta fado jikin sa”Ya Allah “ ya furta afili ganin har yanxu tana masa gizo arai.

➰➰➰➰➰
🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧

BASMA

Tana shiga dakin ko zama batayi ba ta dauki wayarta,dialing number mom dinta kawai take a kagare, kusan 2 missed calls tayi mata bata daga ba ,amma duk da hakan bata hakura ba ta sake kiran wayar, a karo na uku, har ta kusa tsinkewa aka daga kiran, tana ganin mom dinta ta daga ta fashe mata da kuka ,cikin tashin hankali tacikin wayar ta soma magana“baby na waya taba minke “ sosai take kukan ko sauraran abinda mom din tata take cewa batayi,da gyar ta cikin wayar ta lallasheta kafun ta tanbayeta abunda ya faru, gabaki d’aya sai da ta zayyana mata tun zuwan ta part dinsa da marin da tahee ta yi mata,hatta abunda ya faru sai da basma ta fadawa mom din nata a shagwabe. Shiru momyn nata tayi kamar me nazari kafun ta soma yi mata maganar da banajin me take ce mata, sosai basma take sakin dariya ganin lokaci kankanin ta samo wa kanta mafita, har zata kashe wayar kuma sai ta kara karata a kunnanta “momy ina so nasan wacece ita, yanxu momy fa “ banji me aka ce mata ba sai kada kai da take kamar wata kadangaruwa,tana kashe wayar tata, ko mintuna talatin ba ayiba aka turo mata text din bayanan da take so,wata shegiyar dariya tasaki” zan ci uban kine,zakisan dani kike magana “,tana kammala zancan ta tabar dakin nata bayan ta dakko wani abu a cikin jakarta.

🫧🫧

A bangaran su tahee ma,tun bata sake wa mahma harta sake mata ,itama mahma lokaci d’aya taji wani san yarinyar yashiga ranta jinta take kamar ‘yar da ta haifa da cikinta,wasu turaruka masu shegen kamshi mahma ta fito dasu cikin wata yar kwalba me shegen girma,da kanta ta gyarawa tahee dogon gashinta kafun tayi mata dan ado da gashin,ba karamin kyau tahee tayi ba kamar ba ita ba,ba zata ba tsammani basma ta shigo dakin ,kallanta mahma tayi bayabo ba fallasa”baki iya sallama bane”bin tahee tayi da kallo kafun tayi sallamar,har yanxu idanuwanta na kan tahee dake Shan fura ,ji tayi kamar ta zabga mata mari ganin ko kallan inda take batai ba ga wani kyau data danyi kamar wacce aka bawa wani abu,ta gefan ido take kallan mahma dake zaune itama tana Shan furar ta kwata kwata hankalinsu ma baya kanta,idanuwanta basma ta tsayar kan tahee da gefan gashinta ke yawo a gadan bayanta,dan siririn scarf din data daura yana kokarin zamewa a kanta. Mikewa tahee tayi tana kallan mahma, “mahma bari naje wajan dada” gyada mata kai mahma tayi ,Nima ganinan zuwa ai, murmushi tahee ta sakar mata batare da ta kalli basma dake binta da kallan kurilla ba tabar part din, itama mahma tashi tayi ta nufi cikin bedroom dinta, wani bakin cikine ya kama basma ganin yadda suka shareta gabaki d’ayan su , a zuciye ta bi bayan tahee da ta nufi part din dada. Tana kokarin shiga part din basma tayi saurin Shan gabanta,”keee yar matsiyata” cewar basma,a hankali tahee ta dago da kanta dake faman sara mata kadan kadan tun dazu, batace mata komai ba tayi gefe zata wuce, wani irin shakota basma tayi tare da mai dota baya, dafe kanta tahee tayi jin yadda kanta ya fara sara mata”taheera kike kowa ,ke din ba sa’ar yi na bace ko uwarki maryam ba sa’ar yina bace balantana ubanki Muhammad dake kabari,tun wuri ki fita harkar mijina ,idan ba haka ba sai na karar da duk zuri’arki,shegiya me zubin karuwar”, tunda ta ambaci sunan taheera da maryam kan tahee da taji ya kara sara mata, saurin dafe kanta tayi jin yadda kanta ke juya mata, kwata kwata bata gane me basman take cewa ,abu take san tunawa amma ta kasa sabida yadda yake faman sara mata, shako wuyanta basma tayi cikin bacin rai ta kalleta ,”bari na fada miki abunda baki sani ba, king mallakinane ni kadai duk wannan haukar da kike ba sanki yake ba dan haka ki fita harkarsa,banza dangin matsiyata”,wani irin hankadata tahee tayi da yayi sanadin buguwar hannunta,a zuciye tahee ta dafe kanta hawayen da batasan na Menene ba ya fara zubo mata ,”taheera ,maryam ,Mohammad su ne abunda suke mata yawo cikin kwakwalwa “baya sankiiii kalmar da basma ta furta mata ne ya dawo kaikawo a zuciyarta,cikin futar hankali ta juya a guje tana hada gudu gudu sauri sauri harta bar part din dada ba tare da ta karasa shiga ba, har yanxu hannunta dafe da kanta, Daidai lokacin da motocin su king suka danno kai, tun daga nesa ya hangota dafe da kanta,kamar bazai bitaba ganin ta nufi part dinsa yasa ya nufi part din shima cikin takun nutsuwasa, tana shiga ta fara kwala masa kira,” Dady!!! Dady!!! Dady”,cikin bedroom din kasa ta koma tana cigaba da kara kiran “dady” ,ganin baya cikine yasata fitowa da sauri zata kara kiran dady ya shigo part din, da Sauri ta kara so Inda yake tana rike hannunsa fuskarta duk ta baci da hawaye, bin kyakkyawar fuskarta yayi da Kallo ganin yadda take hawaye “me akai miki” ya furta kalmar a fusge Yana lumshe idanuwansa,amaimakon ta amsa masa tanbayar da yayi mata sai ta kara rike tafikan hannunsa” Dady kana sona “da Sauri ya zuba mata idanuwansa ,”kana sona din da ta fada na Dakar masa zuciya ,ganin be amsa matan bane yasa ta kara furta “dady kana sona “har yanxu hawayan fuskarta be dena zuba ba,kokarin sassaita kansa yayi kafun ya kalleta “what’s wrong with you”, yanxu ma bata kulasaba sai ma kara daga muryarta da tayi “dady kana sona “, cikin kosawa da zancanta ya furta “bana sanki ok”,hannunsa da ta rike ta saki tana binsa da kallo kafun ta fara ja baya a hankali “baka sona, daman tace baka sona”, tana gama furta wannan kalaman ta juya a guje tana fashewa da kuka ,cikin zafin nama ya rikota ganin tana kokarin barin Wajan, ba tare da ta kallesaba tasaka hannayenta biyu ta ture shi daga cikin ta,kafun ta kalleshi haryanxu hawayen idanuwanta basu dena sauka ba, ido cikin ido ta kallesa kafun ta furta “Bana sanka”, tana gama fadar hakan ta juya a guje,kasa motsi king yayi sabida yadda kalamanta suka daki kirjinsa,lokaci d’aya yaji wani irin tashin hankali na taso masa da ya rasa na menene,dafe kansa yayi cikin sauri kafun yabi bayanta ganin tana kokarin barin part din, tahee kuwa Daidai ta saka kafarta zata fito kenan taji an hankadata da mugun karfi, cikin zafin nama king ya nufi inda take ganin tana kokarin faduwa,kafun ya riketa gabaki d’ayanta kanta ya bugu da jikin bangon wajan take a wajan Jini ya barke mata ta suma a wajan,kasa motsi yayi ganin yadda Jini ke fita daga kanta,sosai idanuwansa suka rine kalar abun tsoro,basma dake kokarin barin Wajan ya shago tare da bugata da jikin bango kamar ya samu kato haka ya dunga tsinka mata mari kafun ya kai mata wani irin muguwar Shaka ya kai mata kwata kwata baya kallan gabansa,kakari basma ta fara saki na azama kamar wacce nunfashinta zai dauke gabaki d’aya ,har yanxu kuma bashi da niyar sakin ta Daidai lokacin da sha’aban ya shigo falon , cikin sauri sha’aban ya karasa wajansu su yana kokarin banbareta amma abun ya ci tura ganin irin muguwar shakar da yayi mata ,zaki sha’aban ya kirawo da Kyar aka samu king ya saki basma da ta fadi itama take a wajan tana sakin haki ga gefan fuskarta da yayi bala’in kunbura,gabaki d’aya baya kallan gabansa kokarin kara shakota yake cikin daga murya sha’aban ya furta “she’s bleeding “,be karasa zancan nasaba ya sabi tahee da kanta ke faman bleeding yana kokarin wajan ,kafun cikin Sauri ya juyo inda basma take, itama da hannu d’aya ya fincikota tare da jefata wani daki dake kusa da wajan, turn print din hannunsa ya sa awajan take kofar dakin ta kulle,ya bar wajan cikin sauri, kafin ya fito daga part din nashi zaki ya ja motar a guje suka bar wajan.Tunda ya dora ta akan cinyarsa yake kallan fuskarta,”bana sanka “shine ya kara dawo masa,a hankali ya furta “please don’t do this now”ba tare da ko ita taheen da take sume zata jishiba, hannu d’aya yasa gabaki d’aya ya rungume a jikinsa kamar wacce akace za’a kwace masa ita,gabaki d’aya jikinsa ya baci da jiki dukda abun da yasa ya danne mata wajan,cikin saurin aka wangale babban gate din asibitin NAHYAN,ko gama parking zaki beyi ba ya bude kofar bayan ya lullube jikin tahee, tunda jami’an asibitin suka gansa suka fara sara masa , ba Wanda ya kula a cikinsu, ko cikakken muntuna biyar ba’ayiba manyan likitocin asibitin suka hallara a 3rd suna jiran umarni,doctor halima ya bawa umarnin tayi mata dressing ,kafun ya kalli wasu Likitoci mata gudu biyu” at the theatre “kawai ya furta masu,cikin sauri kuwa ko waccen su ta nufi wajan shiryawa,cikin kankanin lokaci shima ya canza zuwa kayan theatre din , gabaki d’aya likitocin mamakine ya ka masu ganin zaiyi theatre da mata zalla wannan karan abunda be taba faruwa, direct dakin theatre aka shiga da tahee bayan anyi mata dressing din.

Sha’aban kuwa cikin sauri ya nufi part din dada,a zaune ya tarar dasu ummey zaune a falan suna hira ganin yadda yashigo ne yasasu mikewa,kallansa dada tayi”Kai kuma kamar Wanda aka jefo”!Be tsaya saurarar taba ya fara labarta musu abunda ya faru,gabaki dayan su sallallami suka saki ,hatta su abeey da ke kokarin shigowa part din,kasan tuwar kowannansu da gyale a jikinsu ba ‘bata lokaci abeey yasa a tayar da mota sai NAHYAN hospital ko takan basma da aka kulle ba Wanda yabi, sha’aban da abeey sai su uncle saleem suna baya ,suma su mahma Itace take tuki yau da kanta,daga ita sai dada sai kuma ummey suka nufi asibitin.

➰➰➰➰➰➰
➰➰➰➰➰➰
🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧
🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧

Karfe 8:50 na dare taheer ya soma motsa hannayensa lokacin matar tana kan dadduma bayan ta idar da sallarta, a hankali ya soma furta”zasu kashe mu, zasu kashe mu”ganin yana motsine yasa ta mike wa tare da nufo inda yake, a zabure ya bude idanuwansa yana kwalla kiran sunan “zasu kashe mu” kallan sa matar tayi kafun ta soma magana “kwantar da hankalinka ba Wanda zai kashe ka”, da Sauri taheer yaja baya yana kallanta, “Kema mayar dani zaki wajan nasu”, girgiza masa kai matar tayi “ba inda za akaika sannan babu me kara daukeka, su wanene zasu dauke ka sannan ina yan uwanka “, sai a lokacin taheer ya fashe da kuka tuno su oumma da yayi,batace masa komai ba sai data barshi yayi ku kansa iya yinsa kafun tayi serving dinsa abinci abinci da kanta, kamar mayun Wacin zaki haka yasoma cin abincin ganin yana kokarin shakewa ne ysa ta mika masa ruwa,yanxu ma cikin sauri yake shan ruwan, saida ta tabbatar ya koshi ya fara dawowa hankalinsa kafun ta kara yi masa tanbayar dazu,gabaki d’aya ya labar ta mata abunda ya faru tun lokacin da ya fito daga gidan nan wasu mutane suka tare masa hanya cikin wata bakin mota,yana kokarin barin wajan suka fesa masa abu, be kara tsintar kansa a ko ina ba sai gidan da aka dunga azaftar dasu.
Share hawayen ta mayar tayi jin labarin da ya bata,Aushe dagaske hakan na faru ga yara kanana, kallansa tayi cikin tausaya kafun ta furta ,kanaso ka koma gida , cikin wata irin zabura ya girgiza kansa alamun ah ah , kallansa tayi cikin mamaki kafin ta kara tanbayarsa,naam kai ya girgiza mata cikin tashin hankali, fahimtar halin da ya shiga ne yasata mikewa da niyar kiran likita,da sauri ya riko hannunta ,”dan Allah ki dauke ni anan kullum dukanmu suke”wani saban tausayinsa ne ya kamata kafun ta sakar masa murmushi “karka damu babu Wanda zai kara tabamun kai,zan kirawo likita ya duba kane” gyada mata kai yayi har yanxu be dena jin tsoro ba,”karka damu yanxu zan dawo kaji”, Tom kawai yace mata itama bata kara cewa komai ba ta bar dakin.

🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧
🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧

Har suka karaso asibitin su king basu fito daga dakin theatre din ba, kasantuwar ansan ko suwanene yasa aka kaisu suma can 3rd floor din, gabaki d’aya hankalinsu a tashe yake ,tunanin ta ydda zasu sanar wa ammey kawai suke, suna cikin wannan tunaninne aka bude kofar theater din, gabaki dayansu kan tahee da kanta yake nannade suka nufa,dada harda yar kwanlanta,wani babban daki aka nufa da ita suna binsu a baya har lokacin ba Wanda yaga king a cikinsu,sha’aban ne ya kalli daya daga cikin doctors din kafun ya tanbayeta lokacin farkawarta, cikin jinjina wa ta furta “ba wani babban rauni ta samu ba, and all the necessary Dr yayi shi, zata iya farkawa nan da 2 hours time “, jinjina mata kai yayi amaimakon ya nufi dakin da aka kwantar da ita kai tsaye office din king ya nufa, koda ya shiga be tarar da kowa a falon ba, wata kofa ya nufa a cikin office din bayan yayi dan tafiya kadan ta kaishi wani kofar, yana budewa wani babban dakine a ciki nan ma be ga king ba sai motsin ruwa da yake dan ji, fita yayi daga dakin yana tare da komawa cikin office kusan 1hour har da mintuna 20 sai ga king ya fito cikin shigar fararar kaya,gabaki d’aya fuskarsa ba annuri,kallo d’aya yayi masa tare da dauke kansa ,kan d’aya daga cikin sofas din falon ya zauna har yanxu yanayin fuskarsa be sauyaba,wasu injection ya dauka har yanxu be kuka sha’aban dake zaune ba, ganin yana kokarin fita ne yasa sha’aban bin bayansa,Kai tsaye dakin da take suka nufa, ko da suka shiga dakin babu Wanda ya kalla a cikinsu kai tsaye inda take kwancan ya nufa har ya juya da niyar komawa yaga hannayenta na motsi, be san lokacin daya kama hannayenba yana kallan fuskarta, a hankali ta fara motsi da idanuwanta, kafun ta bude su tar sai kuma tayi saurin kara kulle idanuwan,tayi hakan kusan sau uku kafun ta bude su gabaki d’aya, abunda ya faru ne yashiga dawo mata daya bayan daya tundaga kan batan oumman ta, hannunta dataji an rike ta kalla,a hankali ta janye hannunta daga nasa kafun ta kalli ummey dake gefanta a hankali ta furta “UMMEY”, cikin tsananin farin ciki ummey ta kalleta,kin ganeni,jinjina mata kai tahee tayi,maida kallanta tayi kan abeey kafun ta furta abeey,wani yalwataccen murmushi ya saki me kayatarwa “ya jikin naki” cikin sanyin jiki ta furta Alhmdllh ,kallan dada tayi ta kira sunan ta itama ,wata irin kabbara dada tasa da yasa kowa ya kalleta, mahma tahee takirawo sunanta a hankali , murmushin jin dadi mahma ta saki ganin ta tuna da ita, gefenta ta kalla dan ganin ta inda zata bullo amma har yanxu bata ganta,”ammey ko”ummey ta tanbaya,saurin sunkuyar da kanta kasa tahee tayi kafun ta soma wasa da yan yatsunta Wanda aka sawa ruwa,murmushi yan dakin suka saki banda king dake binta da kallo ta kasan ido,Allurai ya hada guda uku yana kokarin yi mata su abeey suka fita daga dakin, itama dada mikewa tayi kafun suma su mahma suka bar dakin yayi saura daga king sai ita, wani irin sansa ne taji na taruwar mata a zuciya tuna yanda ya kula da ita lokacin da tayi rashin lapiya ,kalmar bana sanki da ya furta ne yasata hadiye duk fargabar da take ji a kansa, ko kallan inda yake batayi gigin kalla ba, a hankali ya matso inda yake kafun ya dakko injection dinnan,cikin kankanin lokaci yayi mata su wannan karan ko kokarin guduwa batayi ba ballantana tayi masa raki, sunkuyo da kansa yayi Daidai saitin fuskar,saurin dauke kanta tayi tana hade ranta dukda masifaffiyar tsoransa da take ji,Daidai saitin kunnanta ya furta “ya jikin ki”,tsikar jikintane ya tashi jin saukar muryarsa acikin dodan kun nata,ba tare da ta kalli inda yake ba ta furta “Alhmdllh “kalleni ya furta a hankali, kin kallansa tayi kamar yadda ya umar tan sai ma kara sunkuyar da kai da tayi,da dan zafi ya furta ba magana nake miki ba, da sauri ta dago da fuskarta amma har yanxu taki yadda su hada ido,ga wata masifaffiyar kunyarsa da take ji”Me kikeso”, ba tare da ta kallesa ba ta furta “babu”, yanxu ma kara sunkuyo da fuskarsa yayi “me Yasa babu” atsiwace ta dago tare da furta “sabida bana….” Be bari ta karasa zancan nata ba ya mata kiss abakin ,”Sabida bakya me”, kin dago da fuskarta tayi jin wani irin masifaffiyar kunyarsa da take ji,”batanbayarki nake ba”yanxun ma dago tayi tare da furta “sabida bana…”bata kai karshen zancan nata ba ya kara kai mata wani kiss din a karo na biyu, bai san jin abinda zuciyarsa zata bugane shiyasa ya kara tanbayarsa,ki amsa mun tanbayata,cikin dake wa kamar me shirin yin kuka ta furta “sabida bana sanka”, tana kai karashen zancan nata ya hade bakinshi da nata waje d’aya ,bata san lokacin da wani karfi yazo mata ba ta ture shi daga jikinta tana juya masa baya, shima be kara cewa komai ba ya bar dakin, fashewa da kuka tahee tayi tuno rayuwarta ta baya ko ina su oummanta suke oho,shima king wata sabuwar soyayyarsace take faman rura hutar zuciyarta amma tayi alkawarin ko zata mutu bazata taba nuna masa ba tunda yace baya santa.

💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖

Mss Lee 💖
💖💖GIDAN AUNTY 💖💖
(a heart touching love story)

Story & written
By
Mss Lee 💖

💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖

DEDICATED THIS PAGE TO YOU MRS BBK (JINI DAYA),ALLAH YA BAKI LAPIYA 🙌❤️🌹.

 

PAID BOOK

me bukatar samun complete din gidan aunty yayi nun magana ta wannan number 07041879581.

Leave a Reply

Back to top button