Gidan Aunty Book 1Hausa NovelsHausa Novels

Gidan Aunty Book 1 Page 58

Sponsored Links

58
Kallo d’aya tayi masa ta dauke kanta, a Daidai lokacin da wani message din ya sake shigowa, dan kallan Rubutun da akasawa baby da yar love a jiki tayi kafun tayi saurin d’auke kanta , batasan lokacin da ta jefa wayar kan sofa ba tayi shigewarta , kallan fuskarta yayi yaga ta dauke kanta gabaki d’aya,mamakin abunda tayi yanxu yayi kafun shima yadan fuske ya zauna kan sofa din, wayar da ta jefa a wajan ya kalla daidai lokacin da saban message ya kara shigowa, kamar zai share sai kuma ya dauki wayar, eyes dinsa ya dan ware kadan kan screen din wayar yayi kafun yayi saurin kallan kofar da tashige, maida kallansa yayi kan wayartasa, messages din dazu yagani da private number, alamu ya nuna ankalli message din sai wanda aka turo na ukun “Baby”, ya nanata a kasan zuciyarsa kafun ya saka hannunsa d’aya cikin sumar gashin kansa,” oh my god ,kenan wannan message din ta gani yanxu”,duk da kasancewar private number ce amma sai da number ta fito kan wayarsa , lips dinsa na kasa kawai yake dan taunawa time to time, sosai wani bacin rai ya bayyana a kan fuskarsa, ransa ba karamun baci yayi ba a zafafe yayi dialing wani number , ringing biyu aka daga kiran kuwa, ko amsa gaisuwar da na wayar yake masa Beba sai ma umarni da ya bada cikin kausashashshiyar murya” na baka daga nan zuwa lokaci kadan ka binciko mun wata number yanxun, koma wanene akawomun ita ko shi immediately “
“, kitt ya kashe kiran batare da yace komai ba sai forwarding din number da yayi, wani irin huci yake futar wa shi kadai, bayasan binta ciki, shiyasa ya zauna ,yanaso kawai ya kalli fuskarta , yanda ta bar wajan kuma har yanxu yana jinsa, wani irin bugawa zuciyarsa take, tsawan lokaci yana jirin fitowarta , ganin bata da alamar fitowane yasashi nufar kofar shima.

****Aban garan tahee kuwa tana shiga ciki ta fashe da wani saban kuka me cin rai, kuka take sosai kamar wacce akace wani abu ya sameta, ita kanta bazata iyacewa ga dalilin kukan nata , sai wani abu da takeji ya tsaya mata a makoshi, a hankali ta furta “ Baby ko,har da wani sweetheart , sai yaje su karata ai, har da wani nayi missing dinka”, dan karamin tsaki taja cikin bacin rai ta goge hawayenta, launin idanuwanta har sun canza daga launin fari zuwa ja , Wanka tashiga shaf shaf ba dadewa ta fito fuskarta kwata kwata babu annuri, gefe d’aya na wajan wardrobe dinsu ta bude take a wajan kayan Sawarta suka fito reras dasu gwanin ban sha’awa , a hankali take takawa Sabida har yanxu ciwan ta be gama warkewa ba,shiryawa tayi cikin doguwar rigar abaya me milk colour me kamar bazar bazar , sosai abayar ta zauna mata ajiki duk da bata kamata ba, babu abunda ta shafa sai dan mai da lipstick a bakinta kadan, wani mountain din turare ta fesa a cikinta kadan, take wajan ya bade da kamshin turaran, cikakken lallausan gashin kanta da ya kara rinewa baki sak ta fara tajewa a hankali, har yanxu ranta ba dadi musamman I missed you din da ya fi komai tsaya mata a rai. Tana cikin taje kan ya shigo dakin amma ko saudaya bata dago ta kallesa sai ma cigaba da abunda take takeyi,a hankali ya tunkaro inda take, tana gani yazo daf da ita ta ajje coom din hannunta zata bar wajan, hannu d’aya yasa ya tsayar da ita, kin kallansa tayi sai ma kokarin kwace hannunta dake yi, “why all this please “, ya furta a hankali, a kufule ta kallesa cikin jin haushin maganarsa ta furta” your sweetheart is waiting for you, so please leave me alone ka tafi wajanta”, kallan dan karamin bakinta yayi,kafun wani dan murmushi ya subuce masa a saman labba, wani haushin ne ya kara kamata, tayi kokarin fusgar hannunta amma ta kasa, matso da fuskarsa yayi Daidai tata yana bin kyakkyawar fuskarta da kallo” toh ai gani a gaban ta, me yayi saura”, bata san lokacin da ta zuba mishi idanuwanta kafun tayi nasarar kwace hannunta, kara riko hannun ta yayi tare da rungumota jikinsa, turaren jikinta dake ta shin kamshi ya fara shinshina,a tsorace take kallansa duk da haushin sa da take ji,”kina kishinta ne “,kara kuluwa tayi da maganarsa a zuciye ta furta “akan me zan yi kishi,karshe sai ka dawo da ina kusa da kai ai sai kuyi karshen soyayya”, ita kanta bata san lokacin da bakinta ya furta hakan ba, a zafafe ya daka mata tsawa” are you mad , ni kike fada wa haka, are you on your senses,”sosai ta tsorata da yanayinsa, ganin yanda ya har zuko mata ne yasata fashewa da kuka, duk da yanda kukanta ke sukan zuciyarsa haka y daure bata re da yace mata komai ba ya bar wajan dakin gabaki d’aya , zubewa a kasa tahee tayi tana kara fashewa da wani kukan , kamar wacce aka tsikara kuwa ta mike tsaye tare da goge hawayenta, fuskarta tawanko tare da gyara fuskarta , mayafin abayar ta yana akanta a matsayin dan kwali bayan ta tufke kan da kyar, wani turaren ta kara fesawa kadan kafun ta bar dakin itama. Zaune ta samesa kan d’aya daga cikin sofa din dakin idanuwansa a lumshe, wuceshi tazoyi itama fuska ba fara’a taji saukar muryarsa “ come back here , dawo ki zauna “ ya karasa zancan cikin sanyi kamar bashi ba, wajan da ya nuna matan ta koma ta zauna, a hankali ya bude idanuwansa, kallan yanda fuskarta take ba walwala yayi kafun ya dan sun kuyar da kansa , abincin da ya zo mata dashi ya dan iba ya kai bakinta, ba musu kuwa ta bude bakin, a hankali ya soma bata a baki har saida yaga ta koshi tukunna ya kyaleta,”nagode “ kawai tace tana kokarin barin wajan ya kamo hannun ta cikin nasa” please stop it, zuciya ta ba dadi”dan sunkuyar da kanta tayi kasa ba tare da tace komai ba” I don’t like it, inason naga daughter dina tada ba wannan va,inasan wacce takewa daddy wasa , take masa hira,take rungumesa,inasan ganin wannan smile din na fuskarta,musamman idan zata kirani dady,I need the old you,zuciya ta ba dadi,anytime na bata miki rai , tell me , ki fada mun, kinji”, maganarsa ta dan sanyaya mata zuciya , kanta ta daga masa kawai , “are you jealous “,kin bashi amsa tayi sai kokarin mikewa datayi ya mayar da ita” tell me are you jealous “bakinta ta turo kadan kasa kasa ta furta harda wani cewa baby, murmushi ne ya bayyana a fuskarsa kafun ya dan ja hancinta kadan yana rungumeta,” my jealousy wife,Nima ban santa ba and karkisa hakan aranki,sabida ke kadai ce a zuciyar TAHNOON zayed al_nahyan”,kafun ya raba jikinsa da nata”you look so beautiful,har da wani kumatu kika kara sai kace ne yaya biyu a ciki”, kunyar maganarsa taji kafun ta dan kallesa ,”inaso naje na gaishe dasu Ammeey “, ta fada a marairaice, hancinta ya karaja kafun yayi mata peck din daya sa ta dan lumshe idanuwanta,”as you wishes, amma ba yanxu ba sai na dawo daga masallaci,okay”, gyada masa kai tayi kafun ta furta “Allah ya kaimu”, ciwan ki fa, saurin Tashi tayi daga cikinsa tana furta “ni lapiya ta kalau”. Wayar ta tadauka kafun ta dauki plate din da taci abinci, zaiyi magana tayi saurin tsayar dashi, “zan iya “,lumshe mata eyes dinsa yayi kawai Batare da yace komai ba, ganin hakan yasa tabar dakin cikin tahunta a hankali.

*******
*********
Tana sakko wa kasa ta tarar da komai a gyara tsaf tsaf sai tashin kamshi yake falon, tazo zata gifta wajan kitchen kenan taga shigen paper din da take ganin, da sauri ta dauke paper din ta cukwi kwiyeta a hannunta kafun ta kai plate din kitchen , tana budewa sakon da ta saba gani ta gani a jikin paper yau ma, gabanta ne ya fadi yau, tsoranta kar wani abu ya samesa,da sauri ta yaga paper din ta saka a shara gudun kar yazo yaga takardar ,kwanukan da ta bata ta wanke da kanta,abinci take san girkawa ,amma ta rasa me zata dafa, pounded yam ne ya fado mata a rai da miyar efo riro, murmushi ta saki yalwatacce , tuno da abincin oummanta. Doya ta dakko manya guda uku, ta feraye tare ta dora a kan wuta, kafun ta fito da Ganda, nama, kifi da kuma kayan ciki, gyarawa ta farayi cikin kankanin lokaci ta gama gyarawasu ta dora namanta a wuta , Ganda ma haka bayan ta gyara bushashshen kifinta, Attaruhu tayi greating shima kafun ta fara yanka albasa, Daidai lokacin da su firdausi keyin sallama, daga kitchen din ta amsa musu ,amaimakon su zauna sai suka bita kitchen din suma, sakin baki sukai suna kallanta ganin yanda take yanka uban albasa,”sister me nake gani haka , amarya da yin girki”, cewar feedy, murmushi kawai ta sakar musu, aunty feedy sannunku da zuwa,amsa mata sukai gabaki d’ayansu, cikin zolaya ihsan tace “sister amma yaya baya nan ko shiyasa kike tikar aikin nan, kar ya dawo ya tarar da ke haka yasamu tsallan kwado”, dan waro ido tahee tayi kafun ta furta “gashinan a bayanku ai”, ba ihsan da akai wa maganar ba ,gabaki dayansu zuyawa sukai a tsorace,dariya suka bata ta dan dara “wasa nake muku yana sama” wata ajiyar zuciya suka sauke kafun su ajiye mayafansu ,”yanxu me zamu tayaki dashi dan wallahi banshirya yin tsallan kwado ba,tukunna ma me zaki dafa haka ne, ya Wuna ya fara tsinkewa fa inaso naci girkin amarya”,cewar ihsan ,murmushi kawai take “pounded yam da miyar efo riro,”zaro mata idanuwansu sukayi”Menene shi kuma “ wata sabuwar dariya ce ta kamata amma ta danne kafun ta furta “ynxu dai a ina za a samu alayyahu please “, tunani suka fara kafun summy tace bari nasa anemo, cikin kankanin lokaci tasa kuwa aka kawo alayyahun da yawa, ganin doyar ta dafu ne yasata tsane ruwan kafun ta juyeta a flask gudun karyasha iska, message ne ya shigo wayanta dan short” take care of your self, karki famamin ciwona please,ki kula , I love you “, tana ganin message din ta fara blushing ita kadai, hade baki sukai su uku kafun su furga “Awwwwwwwwwqqqn” kunyace ta kamata, ta fara dariya kasa kasa, doyar suka fara daka wa tunda sun hanata yi , kujeran dinning din ta zauna tana nuna musu ynda zasuyi,ita kuma tana ta yasu murmulawa da kyau, ana gamawa tahee ta fara hada miyar efo riro, take a wajan wani kamshi ya karade ko ina , su feedy sai faman santi suke tun kafun su dan dana abincin.miyar ba karamun kyau tayi ba musamman yanda komai ya fito aciki,ainahin miyar efo riro ta yarabawa tayi da taji ganda,nama ,kifi, da kayan ciki.wani hadaddan cooler me shegen kyau aka dakko mata tazuwa sakwara guda uku a ciki sai miyar da ta iba itama ta ware da ban, kafun ta sakasu su fito mata da wasu flasks masu shegen kyau,abeey ta fara zuwa ba , sai su dada da ummey da Ammeey,sai taga kuma bata kyauta ba in baka kaiwa su mamy ba suma, suma haka ta zuzzubamusu, tasa aka kai musu,abunda tayi ya farantawa su ihsan rai sai suka karajin wani girmanta da kimarta ya kara shigarsu,bayan ankai ko wana part a babban tray ta zuba musu nasu gabaki d’aya suka zauna kan carfet suna cii, suna hira kwanin nan sha’awa, suna gama ci kara gyara gidan sukayi sabida kiransu da ake tayi a cikin gida.har zasu tafi ta roki alfarmar su jirata ta shirya sai su tafi tare , kallan juna sukai kafin su gyada mata kai, a hankali ya’ke taku har ta kai sama, suna ganin wucewarta suka gudu, ihsan ce me cewa” ban shirya yin tsallan kwado ba da Shan mari”, suma gabaki dayan su dariya sukai dan sun san zasu sha drama in sun koma.

Wanka tayi shaf shaf ta shirya cikin wani material blue colour me plazo din wando blue white colour ,mayafin ta ma dark blue ne tare da takalmin ta, shigar tayi mata kyau sosai, kadan ta dan fesa turaransa da ta gani, wayarta ta fara dubawa amma bata gantaba,tunanin inda ta barta tayi kafun ta sakko down stairs, bata tarar da kowannansu a falon ba, sakin baki tayi tana bin falon da kallo, girgiza kai kawai tayi kafun ta nufi kitchen , wayarta data ajiye lokacin da suke aiki ta dauka tana barin kitchen din.

Bata dade da zama ba ya shigo cikin falon sanye da light blue din yadi me shegen laushi , kwantaccen gashin kansa ya kwanto masa , gashin kansa sa faman shining yake baki kirin da shi, fuskarsa kwata kwata ba walwala amma ba a hade take ba, gabaki d’aya falon ya saje da kamshin turarensa da na tahee, bata san da shigowarsa ba , sai faman game take cikin wayar, jitayi an fiske wayar, a firgice ta mike zata gudu ko kwallan Wanda ya kwace wayar batayi ba, rike hannunta yayi kafin ya furta “it’s me, nayi sallama har na shigo baki sani ba”, ajiyar zuciya ta sauke tana dafe saitin zuciyarta dan ta tsorata,”kayi hakuri ban kulaba”,Kai ya daga mata kafun ya dan ware mata hannunsa , ba musu kuwa tayi hugging dinsa kamar ynda ya bukata “am hungry “, ya furta a fusge,”ka farayin Wanka sai na kawo maka abincin,” ta fada a rarrabe gudun karya ga zakewarta, ido daya ya kashe mata , “yo muje kiyi mun”, ai da sauri tayi baya tana ware masa ido,murmushin da ya saka dimple dinsa lotsawa yayi , tsayawa kallan dimples din tayi kamar taje ta saka hannu a wjan haka takeji,” matsoraciya kawai”, yana kai karshen zancen maganarsa ya haye sama, itama shaf shaf ta fito masa da abincin da ta girma tare da lemo me sanyi, ta hau masa dashi sama , bai dade ba ya fito sanye da wasu kayan daban sai faman tashin kamshi yake ,zubawa sarautar Allah ido tayi ta kasa ganewa shigarsa ta ynxu da ta dazu waccece tafi kyau take a wajan kuma sai taji wani kishi ya daki zuciyarta” yanxu kamar ynda yake ganin kyansa haka matan waje ma zasu gani kenan”, kamar yasan me ke ranta ,sai saura “You’re the only mine and I’m the only yours,” murmushi tayi ba tare da tace komai ba duk da taji dadin maganarsa. Waje ya samu kan wani dan chair me zaman mutum biyu tayi serving dinsa , bin abincin yayi da kallo kafun ya kalleta alamar Menene wann,”pounded yam with efo riro”, abincin ya ravawa zanci kenan yau,Kai ta daga masa alamar eh , tana gama serving din ta mike da niyar barin wajan ya jawota jikinsa ya dorata kan cinyarsa tare da saka hannunta cikin abincin, batace komai ba ta soma bashi abaki, lumshe idanuwansa yayi jin yanda dadin abincin ya ratsa masa baki, be ce komai harta kara sa masa wani abakin, nan ma still be ce komai sai da yaci sau biyar kafun ya dan kalleta,”wanene yayi abincin nan”,a da rare ta Kallesa,”nice “, dan tabile bakinsa yayi kafun ya ya mutsa fuska kadan “shiyasa beyi dadi ba aushe “sakin baki tayi tana kallansa kafun ta mike daniyar kwashe kwanukan abincin ya Mayar da ita,”your cook is the most amazing part,I love the test so much,inaso wannan hannun ya dunga mun abinci”turo masa bakin tayi kafun kuma tayi saurin daukewa, ganin lokaci na tafiya yasa ta cigaba da bashi abincin,duk ci daya sai ya dan tsotsi yan ya tsunta kafun ya saki, har ta kammala bashi a baki.

🫧🫧🫧🫧🫧🫧

Karfe 6:54 aka kara kiraye kirayen kiran sallar maga riba, sallah tayi har yanxu kuma bata cire hijab din jikinta ba sai kallan agogo take yi ita kadai, shigowarsa cikin dakin ne yasa ta mikewa da sauri ,”sannu da zuwa”, lumshe mata idanuwa yayi alamar amsawa , ruwa ta kawo masa me sanyi yasha,tsawan lokaci tana jiran taji yace su tashi ya kaita part din su dada kamar yanda yai mata alkawari amma sai taji shiru. Duk motsinta yana ankare da ita sai ma gyara kwanciya da yayi, ganin hakan yasa ta yin saurin magana”Yaushe zaka kaini part din su dadan”ta karasa masa a maraice, eyes dinsa ya waro kadan “Yaushe nayi miki alkawarin zuwa part Dinsu, ni ba inda zani dan nagansu”,sakar baki tayi tana kallansa amma duk da hakan bata sadu daba”dazu fa ka fada hakan”, toh shiknn amma da sharadi daya kinyarda”, batare da jiran jin sharadin ba ta amsa da sauri “eh na amince”, kyataccen murmushi ya sakar mata da ya sata tsarguwa, ganin hakan ya fuske tare da dauke kansa, “let’s go amma ba dadewa zamuyi ba “, da sauri tabi bayansa kuwa ya rike mata hannu, suna fitowa waje zaki ya bude masa mota, a maimakon yashiga sai ya zaga ya bude mata kafun shi ya shiga, satar kallansa zaki ya dungayi abunda be taba gani va, Kai tsaye part din dada suka shiga, duk Wanda ya kallesu zaiga alamar kwanciyar hankali da natsuwa a tattare da su, musamman yanda sukai matching da juna, ganin irin kallan da suke binta da shine yasa ta jin kunyarsu, sakin baki aunty tayi tana bin tahee da kallo kamar ta mayar da ita kitchen , mommy da mamy kuwa murmushi suke sakar mata dan ko dazu sai da mamy ta kara cin sakwarar da aka kawo mata dan ba karamin dadi yayi mata, gaishe da gabaki d’aya falon tayi cikin jin kunya, suma cikin kulawa suke amsa mata gaisuwar ta tare da yi mata godiyar abincin da ta basu kowa sai yaba daddadan abincin ta yake , amrah tuni zuciyarta ta tsinke ganin yanda a dan kankanin lokaci tahee ta wani irin murmurewa, ko ita data dade a gidan jikinta bata shining kamar na tahee, basma bata falon. Lokacin, TAHEE kuwa ko ajinkin sai ma dan hararar su ihsan dake mata dariya kasa kasa tayi ,kafun su koma gefe suna hira sai faman tsokanar ta suke, king kuwa ko a jikinsa waje ya samu ya hade ransa kwata kwata babu bara ‘a amma duk motsinta yana ankare dashi,har karfe tara suna zaune a falon. Ganin basu da alamar mikewa mahma ta koresu part dinsu, suna komawa koma wajan shi ya nufa, ita second floor ta nufa shikuma ya wuce 3rd floor , Wanka tayi shaf shaf sabida bancin da take ji na neman fusgarta, cikin wani guntuwar rigar bacci da bata boye komai na jikinta ba ta saka , har da kulle kofar Sabida kar ya shigo, ba dadewa kuwa wani bacci me dadi ya dauketa. Tana cikin baccin ne taji kamar abu na yawo a jikinta,bata motsaba sai da taji abun na mata yawo a Daidai mararta, a mugun tsorace ta farka, cin Karo da kyakkyawar fuskarsa ta soma ja baya tana hadiye yawun da ya tsaya mata da kyar,a mugun tsorace ta furta”’me kakeyi anan bayan dare yayi”, bece mata komai Sabida yanda idanuwansa suka fara canza kala sai faman lumshesu yake, hannunta yake kokarin rikowa tayi saurin mikewa tsaye tana Jan baya, a mugun tsorace take kallansa ganin shima yana bin bayanta, kara ja da baya ta dunga yi shima yana biyota , bata san lokacin da ta karasa jikin bangoma shima a Daidai lokacin ya karaso inda take yayi mata runfa, cikin muryarsa da tayi mugun Dusha shewa ya furta “ i need you now”.

 

 

*******
Barkanku da Shan ruwa da fatan ansha ruwa lapiya , Allah ya amsa mana ameen.💖
Mss Lee 💖
07041879581

Leave a Reply

Back to top button