Hausa NovelsNoor Al Hayat Hausa Novel

Noor Al Hayat 5

Sponsored Links

By khaleesat Haiydar_

5…..

Fatima da bata lura da yanayin da Khadijah ta shiga ba tace “But ina jin kilan ya shiga schl ne, kinsan PhD din nan sai hankali, yanxu ma idan Abban Iman ya kira dole sai dai mu wuce kawai tunda ban san lkcn da xai dawo ba” Khadijah dai bata ce komai ba ta mike a hankali ta kwantar da babyn da uwarta ta kira da Iman, ta kirki murmushi tace “Bari in shiga kitchen” daga haka ta kunna masu kayan kallo ta wuce cikin kitchen, kauda damuwar da ya so dirar mata a rai tayi, ta jingina da kitchen cabinet tana tunanin light abinda xata girka masu da baxae dau lkci ba, can dai ta fiddo Irish ta shiga ferewa, cikin minti ashirin ta gama hadadden porridge din Irish da yaji kayan hadi da hanta da nama, tuni kamshin dahuwar abincin ya kauraye ko ina na gidan, fitowa parlor ta yi fatima dake xaune tana danna wayar hannunta tace “Sannu da aiki” Murmushi Khadijah tayi tace “Thank you, hope ba ku yi fushi ba na bar ku ku kadai” Fatima tace “Ayya ba komai ke da kike aiki” Khadija ta koma kitchen tayi serving abinci a plate tasa fork ta daura kan tray da glass cup na ruwa a gefe ta fito parlorn tun kan ta ajiye fatima tace “Toh fah, ni fa a koshe nake khadijah, wlh am nt hungry bamu dade da cin abinci ba” Khadijah ta d’an canxa fuska tace “Saboda ke fa nayi girkin” fatima tace “Ayya, to ban san xai ko anjima ba amma yanxu gaskiya a koshe nake kiyi hakuri” dai dai nan aka bude kofar parlorn duk suka kalli direction din, tsaye yyi bakin kofar kamar me examining din wani abu, Khadijah da xuciyarta ya kusa shigewa cikinta tayi saurin kauda kanta gabanta na faduwa, mikewa fatima tayi da fara’a da farko sai kuma ta hade rai tace “Yaya ai da sai ka ce min kar in xo baka nan, ka wani shanya ni a waje ina ta jiran ka,” karsowa yyi cikin parlorn da takalmansa ba tare da ya kalleta ba bare ya tanka ta, fatima ta xaro ido tace “Ana fa sallah yaya…. Ka cire takalmin” Bai ce komai ba ya duka yana kallon Iman dake kwance saman kujera, sai a snn yyi murmushin da ya bayyana light dimples dinsa yace “She’s…. growing” daga haka ya dau babyn ya manna mata kiss a cheeks dinta ya juya ya nufi kofa yana cewa “Wayata na silent I don’t knw u were calling,” Fatima tace “Uhn ai shikenan, ya karatun” bai tanka ta ba har ya fita, kallon Khadijah tayi tace “Nagode sosai Khadijah Allah ya saka da alkhairi” Khadijah ta kirkiri murmushin karfin hali tace “Welcm” fatima ta dau jakarta da abun daukan babynta tace “Bari in je mu gaisa” daga haka ta juya ta nufi kofa Khadijah tace “Toh abincin fa?” Fatima ta yi yar dariya tace “Toh shkkn bari dai in je da shi” dawowa tayi ta duka xata dauka ganin kayan hannunta khadijah tace “Let me help” fatima tace “Toh nagode” khadijah ta duka ta dau abincin, sai kuma tayi still tunawa da tayi hakan na nufin parlornsa xata shiga kenan?? Tuni fatima ta isa kofa, a hankali ta bi bayanta a sanyaye ba don ta so ba, fatima ta bude kofar yayan nata ta shiga da sallama, b’akin cover shoe dinsa na ajiye bakin kofa wato ita ya raina xai shigo mata parlor da takalmi, xaune suka gansa kan daya daga kujerun parlon yana rike da Iman dake 6a66aka masa dariya, kallo daya Khadijah tayi ma hadadden parlon nasa tayi saurin sunkuyar da kai gabanta na faduwa, fatima da har ta xauna tace “Ina yini yayana” yace “Ya kike” tace “Alhmdllh ya karatun” karasowa Khadijah tayi ta ajiye abincin hannunta ba tare da ta dago kai ba, ya kafeta da ido, kamar ta sani kuwa ta ki kallon inda yake, fatima tace “Yaya neighbor dinka tana da kirki sosai, ka taya ni yi mata godiya” yace “Koh?” Kallonsa fatima tayi ta kasa cewa komai jin kalan tambayar da ya jefo mata, sannan tafi kowa sanin halin wan nata, hakan yasa kawai ta bude jakarta tana murmushi tace “Guess what yaya….” Ya kalli jakar bai ce komai ba dai, Envelope ta dauka ta mika masa tana yar dariya tace “3 days ago su Ummu suka ba Abban Iman ya taho da shi” Karba yyi yace “Meye a ciki?” Ta buda ido tace “Invitation card din ku mana….” Mayar mata yyi yace “So?” Tace “Aa cewa aka yi in kawo maka” yace “To mayar” Fatima tayi murmushi tace “Ko dai Jawahir din ta tura maka ne” Ya hade rai yana kallonta sai kuma ya juya yare xuwa larabci, tuni khadijah ta nufi kofa dai dai lkcn da aka bude kofar, wata black American mai kyau ta shigo parlorn tana sanye da wasu damammun kaya, ta daga masu hannu gaba daya da murmushinta tace “Hi” daga haka ta nufi bedroom, lkci daya mood din fatima ya canxa ta bi yarinyar da kallo, shi kam ya dauke kai, Khadijah ta saci kallonsa suka hada ido, tabe baki tayi ta dauke kai ta juya ta bude kofar ta fice abin ta a ranta tace Allah wadaran naka ya lalace, ko kunya bai ji ba, Tana komawa apartment dinta ta shiga gyare gyaren ko ina na gidan, duk wani abu da tasan xai iya samun matsala a fridge duk ta tattara su gu daya don tafiya da su gidan Vanessa, kafin la’asar ta gama komai tayi wanka ta dauro alwala ta fito, tana idar da sllh ta shirya cikin kananun kaya ta daura kimono a kai ta yafa gyale a kanta xata fito parlor aka danna bell, karasawa tayi ta tsaya bakin kofar tace “Who’s there?” Muryar fatima taji tace “Ni ce Khadijah, dama nace in maki sallama xan wuce” Khadijah ta bude kofar tace “Ayya, har xa ku tafi” fatima ta kirkiri murmushi duk da Change din mood dinta tace “Wllh kuwa, Abban iman na jiran mu” Khadijah tace “Toh shkkn, Allah ya tsare hanya, ya kai ku gida lafiya” Fatima tace “Ameen ngd, tnx once more for the hospitality” murmushi kawai Khadijah tayi, aka bude kofa sai gashi ya fito rike da Iman, Fatima ta kallesa da kamar baxa ta ce komai ba sai kuma tace “Ya Khaleel da gaske baxa ka kai mu ba mu hau taxin kawai” a takaice yace “Ehh” ta langwabar da kai tace “Toh shkkn” majestically yyi wucewarsa waje, Khadijah ta bi sa da ido, fatima da ta bi sa da kallon ita ma tayi murmushi tace “Kinga da gaske taxi xai tsayar mana maimako ya ajiye mu da motarsa daga na gaya masa gaskiya….” Khadijah tayi murmushi bata dai ce komai ba, Fatima tace “Toh muje wayana na gun sa sai ki sa min digit din ki mu dinga xumunci” Khadijah ta bi bayan ta ba don ta so ba, ko da suka isa har ya tsayar da mai cab yana jiran kanwar tasa, fatima tace “Yaya idan ma fushi kake da ni kayi hakuri pls” ya kalleta bbu yabo bbu fallasa yace “Not at all, shiga ki tafi inda xa ki” tace “To bani wayar Khadijah ta sa min digit dinta” yayi kamar bai ji ba ya bude back seat yace “Shiga malama” fatima ta shiga ya mika mata yarinyarta sannan ya bata wayarta, tace “Bata sa number ba ai yaya” ya hade rai yace “Xan tura maki ta WhatsApp” rasa abinda xata ce masa tayi, ganin yanda ya hade rai tace “Toh baxa ka ba mai cab din kudi ba” yace “Bani da” yar dariya tayi tace “Kai ya khaleel ba ma haka da kai fa, kayi hakuri kar in tafi kana fushi da ni” Khadijah da ko kallonsa bata yi ba ta daga ma fatima hannu tace “Toh Allah ya tsare hanya Maman baby” daga haka ta juya da sauri ta koma ciki don bata son ta ci gaba da jin kayan takaici, tana shiga bedroom ta wuce direct ta dinga fiddo kayan da ta harhada, taje dauko na karshen taji an bude kofar parlor, still tayi na yan sakwanni sai kuma ta juya da sauri ta fito xuciyarta na bugawa.

*Haske writers association*💡

✨ *Noor-Al-Hayat*✨

_By khaleesat Haiydar_📚✍🏻

Back to top button