Hausa NovelsWaminal Hoob Hausa Novel

Waminal Hoob 10

Sponsored Links

Waminal Hoob_* 10

LAST FREE PAGE#

_Asmy b Aliyu_

Haka kurum taji tana da nasanin biyewa shawarar farhaan ,yanxu gashi kowa Yana farin ciki da wannan Auren ranar da Kuma Auren su Ya kare da Aliyu waxeer fa??”kenan sun yaudari duka Familyn waxeer musamman mahifiyar Aliyu waxeer .kwata-kwata Bata farin ciki da wannan Auren ,tunda tayi sallar magrib take xaune akan rug tana so taga Aliyu a daren nan tana so a dakatar da Auren nan ,ita kam baxata iya cigaba da wannan pretading din ba…….sai Kai da kawo take a tsakiyyar dakin dai-dai lokacin hajia saudah ta turo kofar,kallo daya tayiwa Nooriyah tasan akwai Abunda ke damunta da Dan murmushi take fadin”lfy Nooriyah akwai Abunda kikeso ne,kokarin saita kanta tayi da murmushi take fadin bbu komai Mumy………”kin tabbata kuwa?”shuru Nooriyah tayi ta shiga wasa da yatsun hannunta,ki fadamin kina bukatar wani abune pls karki boyemin…..cikin Rawar murya take fadin dama Mumy ina so nayi waya da Aliyu ne….”murmushi hajia sauda tayi gamida wara ido take fadin kan wannan kike daga hankalin ki??”bari na Kira Ammah ta turomin digit din Aliyu,cikin sa’a Kuma Ammah ta daga wayar.sukayi Maganar da xasuyi ta katse wayar baifi minti biyu ba sai ga Ammah ta turo mata digit din Aliyu waxeer, mikawa Nooriyah wayar tayi tana fadin ga lambar sai ki Kira idan kin gama ki fito parlor kici kaxarki…….”da haka hajia saudah ta nufi kofa,ta dde tana juya wayar a hannunta kafin tayi dialling lambar Aliyu waxeer ,Har tagama Ring bai daga ba sake Kira tayi a karo na biyu nan ma bai da gaba,jikinta yyi sanyi maybe baya daga bakuwar lambar Kusan minti biyu da Kiran ta Kara gwada Kiran wannan karon cikin sa’a ya dauka da cwt voice dinsa yake fadin”who is on d line…” Shuru tayi yarda taji yyi Maganar cikin kasaita da izzah ,sai da ya Kara cewa hello .”Cike da natsuwa take fadin “Aliyu !!” ,da mamaki yake fadin”ina kika samu wayar kirana ?”kuma lafia xaki kirani bakida hankali ne”yyi Maganar so fed up.”ina so muyi magana ne kuma a waya baxaiyi ba ,kar na canye mata card plz….”tayi Maganar cikin Rawar murya Jin baice komai ba ta shiga fadin”Hello Hello!””tana duba wayar Ashe ya dde da kashe wayarsa ,da mmki take bin wayar da kallo .ring wayar ta fara da sauri tayi picking ki turomin Adrees din gidan da kike,ta xaro ido tana fadin Nima ban San unguwar ba.ki fadawa matar da kike gidanta Mana.”Yana fadin haka ya kashe wayar,
Mexata fada mata???”da kunya ta tambayeta Address dinta ,idan Aliyu yaxo wajenta yay mata me??”tafi minti talatin xaune A dakin ta rasa kalmar da xata fadawa hajia saudah ,dama akwai hijab din sallah ajikinta falon hajia saudah ta nufa,tayi sa’a tana xaune a falon da fara’a take fadin karaso Mana.”har Kun gama wayar ne,cike da Jin kunya take fadin”Yace xakuyi magana…….da haka Tayi dialling lambar Aliyu waxeer,A fusace ya daga wayar xai fara yimata masifa tace ga Mumy xata fada maka Address,da haka ta mikawa hajia saudah wayar ba yarda Aliyu ya iya ya gaisheda hajia saudah da ladabi ,dama Mumy sako xan kawo mata Address dinki.”Ya fada da ladabi murmushi hajia saudah tayi tana fadama sa ,godia yyi mata Yana fadin bayan sallar ishai xai shigo,kashe wayar Hajia saudah tayi tana girgixa Kai tana murmushi yaran wannan xamani sai abarsu ,kunya tamkar xata kashe Nooriyah.bara na xubo maki farfeson kaxa kafin ya karaso,da haka hajia saudah ta nufi kitchen…….Dakyar Nooriyah ke tura kaxar dake gabanta ,wani irin amai taji Yana Shirin xo mata,Dan Allah karki yi amai kaxar nan tana da kyau daure ki canye Nooriyah ta naci tana hada xufa ,sai da taci Rabi hajia saudah tace tabarsa haka xuwa anjima ta Bata wani tsimi na musamman Hadin sakwatawan Asali ,nan ma Dakyar Tasha 2 cup tana gamawa ta wuce dakin da aka sauketa toilet ta nufa da gudu tana kakarin Amai…….gaba daya ta gama jigata sai dai har xuwa lokacin bbu alamar xatayi aman,brush tayi yarda taji bakinta Yana yimata wani iri….sai Kusan 9 Aliyu waxeer ya iso har parlorn ya shigo ya gaisa da hajia saudah ,tace suyi xaman su a parlor
Nan ta shigewarta dakinta,da sauri ta kalli Aliyu tana fadin maganar nan baxai yuyu A falo ba.cike da Jin haushinta yake fadin plz tell me mexaki fadamin kina batamin lokaci??”tasowa tayi ta dawo a seat din da yake murya kasa-kasa take fadin plz Aliyu a fasa Auren nan wlhi inajin wani irin inajin ba dai-dai ba,xan jira Farhaan ko yaushe ne idan ya dawo muyi Aure.”Wani irin kallo taga Yana watsa mata ,da sauri ya Mike tsaye ya nufi kofa ganin da gaske tafia xaiyi yasa da gudu ta cimmasa Yana gafda ficewa daga kofar,rigarsa yaji ta jawo ta baya awani irin fusace ya fisgota Ya hadata da kofa,ganin yanayin sa kawai ya firgita ta idonta cike da kwallah cikin Rawar murya take fadin”Ka fahimce ni Aliyu idan mukayi Auren nan xai xama tamkar mun yaudari Ammah”……ko mu fada mata gaskiya ta fada hawaye na xubo mata,wannan karon rikon da yayi mata ba Mai sauki bane,cike da masifa yake fadin”shine mafi munin kuskuren da xaki aikata cikin Rayuwarki,xan gargadeki da babbar murya Koda wasa karki sake Ammah taji wannan sirrin,Idan Ammah taji komai na iya faruwa mahaifiyana na dauke da cutar ciwon xuciya idan wani Abu ya sameta baxan taba yafe maki ba”.magana na karshe karki Kara kirana a waya stupid girl ya fada Yana turata a xafafe a tsorace take kallonsa,
Hannu yasa Yana hargitsa sumar kansa,
Sai yanxu yake tuna Mahaifiyarsa na dauke da cutar ciwon xuciya Abu kadan xai faru ya kwantar daita,
Haka likitan dake kula da lafiar ta a wannan bangaren Ya gargadesu aguji Abunda xai daga hankakinta ko Yaya ne.”xasu iya rasata da xuciyar ta buga,
Hannunsa ya dunkule ya bugi bango dashi,meyasa??”meyasa na biye maka Farhaan??”dole ne Ya dauki Nooriyah xuwa wata kasar yasan Ammah baxata taba amince masa yabarta ba .juyawa yayi Yabar falon da wani irin Yanayi…..A/c motar yaji ya masa kadan sabida tashin Hankali driving yake baisan ma inda yake sa motar ba,da taimakon Allah ya Kai Mention din waxeer .Yarda ya shigo parlorn Ammah yasa Ammah ta saki Baki tana kallonsa ,Allah yaso ita kadaice a karamin parlorn sauran Baki duka sun n
tafi makwancinsu,jini taga a hannunsa Yana xuba.da sauri ta xaunar dashi tana tambayarsa meya samu hannunsa,kuramata ido yayi tamkar Yana son gano wani Abu acikin fuskarta ,xuciyarsa ta shiga wani irin bugawa.ganin baxai ce komai ba ta nufi dakinta da sauri ,ita tayi masa dressing hannun kafin ta rufesa da fada tamkar xata dakesa.gaskiyyar Noory ne kodai ya fadawa Ammah gaskiya.”ganin irin kallon da yake mata tasan da magana abakin sa,gabanta na faduwa take fadin Wai menene haka Aliyu?”idan kasan bbu alkhairi acikin kalaman ka plz karka fadamin Ammah ta fada cikin rawar murya.Yarda yaga Ammah ta wani Sha toka yasa yaji baxai iya fada ba.Da sauri Ammah ta Mike tsaye tana yimasa sai da safe ,haka kurum taji Abunda yakeso ya fada mata ba alkhairi bane.tana shiga dakinta ta sakawa kofar key……xama tayi agefen bed tana sauke numfashi tana
Fadin ya Rabbi .”tsoronta daya kar Aliyu yace a daga Auren nan,ko yace ya fasa tasan xai iya aikata hakan…..har ga Allah taji tana kaunar Nooriyah taji aranta Nooriyah ce xata Bata sanyi idaniya wato jikoki tunda matar Khalil waxeer Bata shirya haifa mata jikoki ba yanxu.”Aikin office da kyale-kyalen dunia kawai ta saka agaba.har ta gaji da Jin kananun maganganun dake yawo acikin familyn waxeer akan surukarta taki Bata jokoki har yanxu.,,da tayiwa Khalil Maganar Daria yayi Yana fadin”Ammah ya xaayi layla ta hada aeki da Kuma ya’yah ya kamata ta dan samu hutu tukuna.Duka-duka Yaushe akayi Auren”lokacin Ammah sakin Baki tayi tana kallon Khalil da gaske Khalil dinta bai San ciwon kansa ba sai Abunda macce ta tsara masa shi yakeyi…….Hawaye taji sun fara sauka akan fuskarta, addu’a take Allah yasa Auren Nooriyah da Aliyu ya xame mata Alkhairi ,
Kiran Aliyu ne ya shigo a wayarta ,tana ganin wayar nasa ta share karshe ma toilet ta shigewarta.
Yau jumu’a yau Kuma xaa daurin Aure Bayan an sauko masallaci ,karfe 11 na safe Ammah ta sauko down stairs cikin shiga ta alfarma,ta kalli Batool waxeer dake xaune cikin soofas tayi crossing leg nata tana juya tea acikin mug ,sanye take da kayan barci kalar Ash sai hular barci kalar kayan da ta axa abisa kanta.da sauri ta kalli Ammah ta turo Baki tana fadin sabahool khairi Ammah.”tayi Maganar sounding so very childless kafin ta Dora da fadin inata knocking kofar room dinki u did not answer me.”Ammah ta karaso ta xauna tana fadin ai Idan kikaji shuru ina wanka.”Yaya Aliyu ma ya shigo Yana ta neman ki.”Yaushe ya shigo?””ko minti goma baiyi ba,Ammah waya ta daga ta kirasa baifi minti goma ba ya bayyana cikin parlorn Baki sake Ammah ke kallonsa,farar jallabiyya ce ajikinsa Mai guntun hannu .da alamar bai dde da tashi barci ba,ya xauna kusa ga Ammah Yana gaisheta ,kana kallon agogo kuwa Aliyu.”da mamaki yake fadin Ammah meya faru ne.”ka manta yaune daurin Aurenka kana ta yawo a haka bbu wanka.shaye da toka yake fadin wane irin magana ne haka Ammah,kinfi kowa sani na Koda xanje massallaci sallar Asuba sai da nayi wanka.”bashi nake nufi ba wanka xuwa jumu’a da daurin Aurenka ka manta da anyi sallah xaa daura Auren.”yarda Yaga ran Ammah ya baci tana fada yasa ya shiga shafa kansa Yana fadin sorry Ammah”Xan Sha black tea.Ammah ta kalli Batool tana fadin jeki hada masa,da sauri yace Nooo Ammah naki nake so,
Batool tayi Daria tana fadin ka kyauta min Yaya wurin make up xanje ana jirana…”da haka ta nufi Kitchen ,
Ammah ta girgixa Kai tana fadin daga yau na huta matar ka xata rika hada maka komai,dakune Fuska yayi Yana fadin”ae naki yafi bbu maccen da xata kaiki iya hadamin tea ko wane iri,Ammah na hada masa tea tana masa mita.shidai haka ya rufe kunnuwan sa ya shanye yace xaije ya shirya ,Koda ya koma part dinsa Wanda aka canja da wasu sabbin Funitures Wanda Ammah tayi oder dinsu daga italy .phone dinsa ya dauka ganin Kusan 5 miss call daga farhaan ,yasa ya wani dakune Fuska ya kashe wayar duka gamida jefata kan royal bed dinsa ,kalar Golding ya shigewarsa toilet farhaan na saka masa ciwon Kai kan yarinyyar nan.”…….Bayan an sauko massallaci aka daura Auren Aliyu waxeer Galadima Da Nooriyah kan sadaki dubu dari biyu.acan gidan su Aliyu kawu balale dake cikin farar shadda da malun-malun ya kafa hula sai sauke rigar yake Yana gyarawa Bayan an dawo daga Reception Wanda friend’s dinsa suka hada masa,Ab ya kallesa Yana fadin Wai ina Amaryar take ne Aliyu tun jia baka kaimu muka gaisa ba,Aliyu ya dakune Fuska Yana fadin daurin Aure kuka xo ba ganin Amarya ba,Dan haka bbu ruwanku da ganinta.”Khalifa maska yyi Daria Yana fadin kenan baxamu ganta ba.”banxa Aliyu yyi masu ganin kawu balele na nufuso yyi saurin tarar sa kar yaje ya yarfasa a gabansu,sannu da gida Alhaji Aliyu Allah ya sanya Alkhairi ya kawo xuri’a Mai albarka,aran Aliyu yace ba Amin ba Amma a fili yyi smile,
Toh Wai ina Nooriyah ne??”ina so nayi mata khuduba,da sauri Aliyu yace kabarsa xuwa gobe Baba xansa akawo ka gida sai kayi mata yanxu tana hannunsu baffa na,toh shikenan Allah ya kaimu.ni xan koma,
Da murmushi Aliyu ke fadin a sauka lfy…….acan cikin gida Ammah na cikin friend’s dinta anata Hira,mamin farhaan tace waini Yaushe toh xaa je dauko Amarya an riga an daura aure,
Gaban Ammah lokaci daya ya fadi ,ta tattaro duka bajintarta da murmushi take fadin uban yarinyyar yace baxai bada yarsa ba,sai dai Aliyu yaje yaxo da abarsa.mami ta tabe Baki tana fadin shikam Aliyu wannan wane irin gidane ya jajibo Aure haka bbu tsari,wasu Kuma daga cikin friend’s din Ammah fadin suke hakama yyi kyau,Ammah tasan idan ta tashi cikin su xaa xargeta musamman Mahaifiyar farhaan dake da mugun saka ido da kananan magana,typing ta shigayi a wayarta ta turawa Aliyu sako akan yaje shi kadai a motarsa yaxo mata da Nooriyah dake gidan hajia saudah,Yana xaune acikin parlorn sa shida friend’s dinsa yaga sakon Ammah ya shigo, dialling number Ammah yyi tana fara ring ta katse Kiran,ta Kara tura masa “just goo!””karka yimin musu,mikewa yyi tsaye Yana fadawa friend’s dinsa xaije ya dawo,ya dde a kofar gida number Hajia saudah ya Kira Bayan ya gaisheta ya fada mata sakon Ammah ,ta masa umurnin ya shigo.har cikin parlorn ya shigo ,
Ta fito suka gaisa tana tambayarsa ya taro .”cike da Jin kunya yake fadin Alhmdullhi,kayi hakuri agama shiryata.sai ga Aliyu da Kusan minti talatin a gidan ,xuciyarsa bbu Abunda take sai tafasa ,sautin fitowarsu yaji da wani irin kamshin da yasa Aliyu lumshe ido na wucen gadi,tunda yake Jin kamshi bai taba Jin kamshi irin wannan kamshin ba,wannan kamshin it’s so different da sauran Wanda yake shaka ,Buda idonsa yyi ya xubasu wurin da yaga ana fitowa da Nooriyah tana sanye cikin farar lifaya Mai xanen gold ajikinta baya hango fuskarta,
Wani Abu Yake ji tun daga cikin xuciyarsa har cikin tafin kafarsa baisan sun kawo agabansa ba,sai da hajia saudah tayi magana da karfi ya dawo hayacinsa…..Jin yyi kamshi na neman kassara masa xuciya lokaci daya,da sauri ya Mike tsaye Yana shafa sumar kansa.da murmushi hajia saudah ke fadin “Kana lfy kuwa Aliyu.”gyada Kai yyi kurum batareda ya kara kallon su ba,muje ko hajia saudah ta fada tana nufar kofa rike da hannun Nooriyah ,wata irin ajiyar xuciya ya sauke gamida fadin ya Rabbi.!”duka kamshinta ya cika motar xuciyarsa sai wani irin bugawa take yi da wani irin reaction marar misiltawa ,ta kofar baya ta side din Ammah yabi dasu Dan a kofar ta gaba mutane ne cike da falon,Koda suka kawo wurin Ammah na tsaye cikin balcony tana jiransu,ta kalli Aliyu tace na manta gidan Baffan ku xamu tafi duka,dama bakuyi wahalar fitowa daga motar ba hajia sauda.smile Hajia saudah tayi tana fadin bbu komai,ba yarda Aliyu ya iya ya juya ya daukesu a motar ya kaisu A Kabir waxeer Mention.sunyi sa’a Yana xaune a falon da shida Ummah da wasu daga cikin danginsu da fara’a ummah ta Mike ta amshi Amarya ta xaunar daita daya daga cikin Royal chair’s din da suka yiwa parlorn kyau.sosai baffa Kabir da sauran uncle’s dinsa sukayi masu nasiha da fada sosai,
Haka Ammah da ummah suka Dora da nasu,sa’annan ummah ta fito da wani Dan kyakkyawan kit ta budesa saiga kyakkyawar sarkar xinari ta bayyana da murmushi a fuskarta tace taso son.” karba ka saka mata Allah yay maku Albarka,xufa Aliyu ya farayi tamkar baiji Abunda ummah ke fada ba,,Jin yyi sanyi wurin nayi masa kadan .saida Suka hada ido da Ammah ta ware masa ido da wani irin yanayi ya Mike tsaye ya nufesu,
Ummah ta yaye lullubin da akayiwa Nooriyah da murmushi ummah ke fadin Masha Allah.”cike da kunya Nooriyah ta saukar da kanta kasa xuciyarta na bugawa Jin kusancinsu da Aliyu waxeer,wani irin rawa hannunsa keyi wajen saka mata sarkar….Bayan ya saka mata sarkar ummah ta kallesa ta Mika masa hannun,kallon hannun yyi ya wani dakune Fuska laluba aljihunsa yyi bbu komai aciki. Kenan baxaka dauki amaryarka ba ??”Ramlah waxeer ta karaso agabansu ta bude jikarta ta fiddo rafar 1k guda biyu ta xube ajikin Nooriyah shewa falon ya dauka ,shi dai Aliyu Yana tsaye a wajen still baice komai ba ya rasa awane yanayi yake farin ciki yakeji ko akasin hakan, Ramlah waxeer ta mikar daita tsaye ta kama hannunta ta saka cikin na Aliyu waxeer wani irin shock sukaji lokaci daya,kaje da matarka Aliyu kuje guest hause Dinka ,ta huta xuwa anjima sai ku dawo kaga yanxu akwai mutane xasu dameta tana bukatar hutu Kuma,da sauri ya kalli Aunty Ramlah xaiyi magana suka hada ido da Ammah sai ya dauke kansa haka ya nufi kofa hannunsu sarke cikin na Juna ,
Kabita a Hankali Aliyu.
Suna isa wajen motarsa ya saki hannunta,Jada baya yyi Yana sauke numfashi tamkar Mai Asmaa front side ya hude mata ta shiga ya rufe kofar ya xagaya ya shiga ya tada motar…….samun kanta tayi da fashe da wani irin kuka,da sauri yaja burki da mugun mmki ya juyo Yana kallonta,cikin muryar da baisan Yana daita ba Yake fadin”kuka Kuma Yar baka??”da jajjayen idanunta ta juyo tana fadin plz kadaina kirana da Yar baka.”wani irin murmushi yayi yarda Yaga tayi Maganar hawaye na xubar Mata , itama sakin Baki tayi tana kallonsa bata taba ganin murmushin sa ba sai yau,saurin dauke kansa yyi yyiwa motar key sukabar wajen…

Anan na kawo karshen free Page. yanxu ne xamu shiga cikin labarin Aliyu waxeer da Rayuwarsa da Nooriiyah ,yanxu ne shafin Rayuwarsu xai bude bayada tabbas ko xai iya rabuwa da Nooriyah Anan da shekara daya kamar yarda ya daukarwa Farhaan Shagari Alkawarin haka??”Yaya xa yayi da mahaifiyarsa dake yiwa Nooriyyah wata irin kauna da Yake hangowa acikin idanun mahaifiyarsa.”
Areefa Mansoor xata dawo Cikin Rayuwarsa kuwa.”ko ta tafi shikenan ta yafewa noory”ta Ina alakar Areefa Mansoor ta fara da farhaan Shagari?”idan Aliyu waxeer ya gano cin amanar da babban Amininsa yayi masa da Kuma budurwarsa wane mataki xai dauka??
duk wannna Amsoshin na cikin Labarin *Waminal Hoob*

_littafin Waminal Hoob na kudi ne akan Naira 500#_

Account Details
0004157137
Jaiz Bank
Asma’u Buhari Aliyu
Katin waya ta wannan lambar#
08086207764
Shaidar Biya ta wannan lambar
08086207764#
Thank you for d love and support my written##??
[9/15, 6:11 PM] Asmy Mom Aydah??:

Back to top button