Gidan Aunty Book 1Hausa NovelsHausa Novels

Gidan Aunty Book 1 Page 67

Sponsored Links

BOOK 1

Page 67 💖

YOLA

Wani irin kururuwane yake tashi a cikin falon, a haukace suka fara surutai cikin yaransu da bashi da dad’in ji ko sauraro,hayakin da suke bankawa suka ci gaba da bankawa cikin russunar da kai , sun dau dogon lokaci suna haka kafun wani irin ba’kin hayaki ya karad’e ko ina na cikin falourn, cikin wani Sauti mara dad’in ji aka soma magana , “ kunyi sake da damar ku, ayyukan da kuka dade kuna jiran cikar burinsa yana neman rugujewa cikin kankanin lokaci, samuwar jini a cikin jini tabbas yana nufin rugujewar ayyukanku baki d’aya hhhhhhh” aka karasa zancen cikin sakin wata iriyar dariya mara dad’in ji , gabaki d’ayansu zubewa sukai akan gwiwowinsu kafun su sunkuyar da kansu ‘kasa ,” tuba muke shugabanmu, tuba muke abun share musu hawaye , a nema mana mafita “, suke ta nanatawa gabaki d’ayansu, wata sabuwar dariya aka kara ‘narkewa dashi , a kausashe ta furta “ dama d’aya ce ta rage muku, kusalwantar da abunda ke cikinta , idan kukayi sake da damar jinin nan yazo duniya tabbas abunda ke ‘Boye zai fito fili” tana kammala zancenta ta ‘bace batare da ta basu damar sake yin wata maganar ba. Shiru sukai gabaki d’ayan su kowa yana tunanin mafita , a zuciye wacce ake wa la’kabi da Abar kauna ta mike ,” bazai sabuba, dole cikin nan ya zube idan ba haka ba gabaki d’ayansu sai na kashe su har lahira, bazai taba bari burina ya salwanta ba, bazai taba faruwa ginin da na fara tsawan shekaru ya rugeje ba dole nayi wani abu, wannan karan da kaina zanyi yakin, da kaina zan fuskanceta”, itama bata jira cewar suba ta ‘bace , gabaki dayan su sunji dadin kalamanta, shiyasa tana fita suka fara jinjina mata daman duk cikinsu tafi kowa hatsabibanci, tunda tace zatayi toh tabbas zatayi din kamar yarda tace .

♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
♾️♾️♾️♾️♾️
♾️♾️♾️
♾️

Kallansa tayi ganin yanda fuskarsa take a had’e, a hankali ta furta “ am sorry,sweetheart “, bece mata komai ba sai kyakkyawar fuskarta da ya cigaba da kallo kamar yasamu TV. Tunda zaki ya dora bindigarsa akan Tj, wani irin gudawa ya kwace wa Tj, sai wari da sutar da yake matsewa ce ta fito, ba shi da ka nuna wa bindigar ba, gabaki d’aya kusan Tsure wa yan makarantar sukai ganin abunda ya dauke musu kai kamar a film, kowa tanbayar da yake yiwa kansa meyasa balaraben can yaje wajan Tahee, suma su zuky wani irin gumine ya fara tsats tsako musu , tun ba’azo kansu ba jikinsu rawa yake . Saida ya gama kare mata kallo yadda yakeso kafun ya furta “ are you ok”, kanta ta d’aga masa kafin ta sakar masa murmushin da yake sanya ya masa zuciya , duk da ransa abace yake hakan be hana yaji bacin ransa kaso mafi yawa tafiya ba Amma duk da hakan be nuna mata ba, dauke kansa yayi kafin ya riko hannunta guda d’aya , gabaki d’aya wani irin mube musu hanya sojojin sukai kafun su sara masu, a hankali yake tafiya da ita hannunsa d’aya cikin nata,ba dalibai ba hatta malam suma sakin baki sukai ganin wani irin kyawu da sukai musu, ganin sun kusa karasa wa cikin motar ne yasa zaki bugawa Tj kan bindiga dayasa Jini fara zuvowa , wani irin kara Tj ya saki gabaki d’aya ya daburce, bude mata mota king yayi da kanshi, kafun ya zagaya inda Zaki ya bude masa yashiga, babu Wanda ya kalla acikin malaman har me makarantar da yake basa hakuri, tsoransama karya sa a kulle masa makaranta. Shima zaki cikin motar suka shiga kafun gabaki d’aya ragowar sojojin su tafi su tsaka motar king a tsakiya subar wajan, banda mota da aka bar sojoji guda biyar , suna ganin bace war motar king d’aya ya zabgawa TJ mari” kai dan iska ko”ya furta kafin ya umar ta akawo masa ragowar abokan Tj din, su musty har Anfara kuka tun ba aje ko ina ba, hatta yan untouchable sai da yasa aka kawo masa, be mari matan ba sai wankin ba daki yasaka sukai, kamar zasuyi Hauka haka suka wanke bandakin , tsabar mugunta babu ta kalmi yasa suka shiga haka suka saka kafafuwansu a ciki, gabaki d’aya toilet din makarantar yasa su wanke har su Tj din da yake tafiya a kwale sabida kashin da yayi a wando, duk da Anzo daukar su basu bari sun tafi ba sai da yasa su tsallan kwado da zaman kujera, tun student nanan har aka tafi aka barsu , yawanci student Allah shikara suke musu dan kowa ya san halinsu, saida sojojin nan suka tabbatar bazata moruba kafun su bar makarantar bayan wani horon punishment din da suka da aka yiwa su Tj , da Sauri kuwa me makarantar yayi na’am dan yasan wanene king, baya magana biyu, dama shima ya gaji da ba’kin halinsu da suke kokarin sawa a kulle masa ba shiri, da rarrafe su TJ suka soma tafiya sabida yanda kafarsu tayi tsami ko motsata basasan yi gabaki d’aya ko wannansu fuskarsa ta jike da hawaye, su musty sai faman tsinewa Tj da su Ruky suke.

****** Tunda suka shiga cikin mota be ce Mata komai ba sai hannunta guda d’aya da yake murzawa a hankali, d’an d’ago da idanuwanta tayi ta kallesa ganin ya dauke kansa yasata matsowa kusa dashi sosai, dan short din unique labulen da ya karesu ta gyara kafun ta danyi dage Daidai kunnansa “ My love “, ta furta cikin wani irin salo, lumshe idanuwansa yayi duk da wani irin abu da yaji ya taso masa amma sai da ya danne ya shareta, kara dagowa tayi akaro na biyu amaimakon tayi masa magana sai ta Dan ciji kunnansa kadan, da wani irin shock ya kalleta, ido daya ta kashe masa kafun ta dan marairaice masa fuska Daidai lokacin da zaki yayi parking . Door din mota ya bude mata, suka nufi part dinsu har yanxu hannunsa yana cikin nata. Har suka shiga cikin daki be ce mata komai ba , saida ya tabbatar tayi wanka , yasata cin abinci , duk yanda taso yi masa magana yaki bata damar hakan, ruko hannunsa tayi cikin nata “ Am sorry “, kallanta kawai yayi kafun ya lumshe mata ido har yanxu bece mata komai ba, ko karin tashi yake tayi saurin d’anewa kan cinyarsa “Am sorry babyna, ni banasan wannan shirun naka , kana so shima babyn mu yayi fushi?” Ta karasa tana dora hannunsa akan cikinta, lumshe idanuwansa yayi kafin ya kara rungumeta a jikinsa, “ you won’t be going to school for now , okay?” Tasan ransa zai baci daman, bata yi masa musu ba ta d’aga masa kai, food din tayi serving dinshi, dakanta tayi feeding baby dinta “ are you upset?” Cewar king , yalwataccen murmushi ta sakar masa kafun ta cusa hannunta kan lallausan gashin kansa tana wasa dashi” me yasa zanyi fishi da sweetheart d’ina?,Am not angry”, how are you feeling, do you need anything “, da Sauri ta daga masa kai alamar eh,” inasan choki choki, goruba, taura sai magarya”, kai ya jinjina mata “ zansa a duba miki a super market “, dariya ce ta kwace mata wai super market,pillow d’aya ta dauka ta buga masa zata gudu yayi saurin rukota, cakulkulu ya fara yi mata tana dariya “ no please na dena , na dena please “, tahee take fada , ganin tana kokarin kwarewa ne yasa ya lafa da iya mata cakulkulun, hira ta fara yi masa, yana sauraronta har lokacin sallahr la’asar yayi ya tafi masallaci.

Karfe 8:40pm ihsan ta kawowa Tahee abinci wai inji ummey, duk yanda Tahee tayi da ita akan ta zauna ta’ki zama ta gudu,Sabida kwata kwata bataso king yazo ya tarar da ita a part din. Tana bud’ewa taga kafiyayyiyar masa da miyan Taushe da yaji man shanu,ya wunta ne ya tsinke shiyasa bata jira king ba ta dakko plate ta soma cin abin cinta. Sosai taji masan saida taji ta Ko shine ta ajje ragowar masan tana maida nunfashi, ta mike da nufin komawa kawai taji juwa na neman kada ita da Sauri ta koma ta zauna, sai da ta kara kusan mintuna 10 a zaune kafun ta mike da niyar ta shi,‘kulle war da cikinta yayine yasa ta sakin karar azaba kafun ta rike cikin nata tana ambatan sunan Allah,’kara kulle wa cikinta yayi da yafi na farko a zaba, “ya Allah cikina”, Nunfashinta ne yake kokarin futa daga jikinta sabida wani irin azaba da tajii a cikin ta , take a wajan Jini ya fara bin kafarta,’kara Tahee ta saka “Jini,jini,jini” ta kuma sakin gigitacciyar kara, banko ‘kofar da akai ne yasa ta d’ago kanta a wahala , Wanda ta ganine yasa ta fashewa ta kuka ta yanke jiki ta fadi, da wani irin masifaffen sauri king ya ‘karasa inda take be tsaya bata lokaci ba ya d’auketa kamar baby bayan ya lullu’be mata jikinta sai cikin motor , ga baki d’aya ya rud’e ,zaki zaiyi driving king ya hana tare da kar ‘bar mu motar, idanuwansa har sun fara canza wa a kausashe ya furta “ kar Wanda ya sani a cikin gida , duk Wanda yazo neman ta mun d’an fita ne “ yana kammala zan cansa ya ja motar cikin matsiyacin gudu sai asibitin NAHYAN.
GIDAN AUNTY

07041879581 ( mss Lee 💖)

Leave a Reply

Back to top button