Gidan Aunty Book 1Hausa NovelsHausa Novels

Gidan Aunty Book 1 Page 57

Sponsored Links

Book 1

Page 57

Tana idar da sallar isha’i tasaka rigimar bazata kara kwana a dakin ba sai dai ya mayar da ita wajan ammey,yasan abunda take cewa ba mai yuwa bane dan bazai taba yadda ba shima , a hankali ya kama hannunta da take kokarin kwacewa fuskarta a hade ta ki yadda ta kallesa,”am sorry please,ki canzamun wani punishment din amma banda wannan please, I can’t “,kuka ta fashe masa dashi”ai daman ka fadamun bakasona shiyasa kayi kokarin kashe nii, ni dai Allah ka mayar dani”,kwantaccen gashin kansa ya dan shafa kansa har ya fara yi masa ciwo, shi kadan yasan yanda kukanta ke cakarsa har cikin zuciyarsa, har yanzu zazzabinsa be tafiva shima,”look at me”, ya furta a hankali,kin kallansa tayi sai ma kara kawar da kan da tayi, gyada kansa yayi kafun ya taba button din rigarsa “ok shikenan kamar Kari kikeso bari muyi round two”,ba karasa zancan saba tayi saurin rike hannunsa da yake kokarin cire rigar jikinsa,hawaye har sun fara cika mata ido,yanda tayin ne ya so bashi dariya amma ya danne gudun karya kara janyowa kansa wani saban rigimar,a fili kuwa dan tabile bakin sa yayi kadan yana d’auke idanuwansa shima ,marairaice masa fuska tayi ashagwabe ta furta “kace mun fa bazaka kara ba”,be kalletaba ya cigaba da kokarin cirewa “toh yanxu na fasa tunta bakyajin magana “, da sauri ta girgiza masa kai” Allah inajin magana , tsoro nakeji “, yanda ta karasa dinne ya bashi tausayi, kara rike hannunta yayi kafun ya goge mata hawayenta “idan wannan hawayen suka kara sauka toh zanshanye kayana”,da sauri ta goge hawayen nata,”ya ciwonki fa”, kawar da kanta tayi kafun tace masa “Ni lapiya ta kalau”, Tohm shikenan zamu iyayin wani kenan” cewar king ,ynxu ma kanta ta girgiza masa “Allah ban warke ba wajan da zafi,kuma kace mun ka dena fa”, rungumota yayi a jikinsa “ am really sorry zawj, nayi leafi Amin afuwa, kinji, am so sorry “a hankali ta gyada masa kai”banaso ka dena mun kaji”, murmushi ne ya subuce masa a fuska Ba tare da ya amsa mata ba sai dan shafa mata bayanta da yake.”zaki iya tafiya”, kanta ta daga masa alamar eh, mikewa yayi shi yana miko mata hannu “let’s eat something kar ki wanta haka”, a shagwabe ta turo masa bakinta “uhm uhm bana jin yunwa “, lumshe idanuwansa yayi kafun ya kalli bakin nata “ you’re making me to ad more “, ai be kai karshen zancen nasaba ta rufe bakinta ruf,dariya ta so bashi amma ya Waske, taku ta somayi a hankali duk da zafin ya ragu makamar dazu ba, duk yana kallan yanda take tafiyar , da te makonsa suka karasa falon, da kanshi ya ja mata kujera kafun ya soma serving dinta, kadan taci tace ta koshi, be kyaletaba saida ya tabbatar ta koshi sosai kafun su koma ya bata magani.
wajan wanciyama sai da yasha rigimar bazata kwana a dakin ba, saida yace mata ba abunda zai mata sannan ta yadda ya kwanta a gefenta amma taki yarda ya tabata, shima din be tabata har saida yaga tayi bacci kafun ya rungumeta a jikinsa yana kashe gabaki d’aya dum light din.

➰➰➰➰➰➰➰

Zaune su amrah suke a falon Ammeey gabaki d’aya yan matan su ke su 5, ihsan, sumayya, firdausi,amrah da basma , kowa yana sabgar gabansa, su ihsan suna zaune kan carfet din Ammeey lokacin ta tafi part din data, suna shan fruit jifa jifa suna hira, amrah na kwance kan 3 sitter , basma kuma na zaune kan 1 sitter kafa daya kan daya yayinda take latsa babbar wayarta sai faman ya tsine take, cikin da rigar da sumayya take dannewa ta dan kallesu kafun ta kashewa su firdausi ido d’aya da dan karfi ta soma magana “ Nifa yau banga sis tahee ba, ko da mukaje part din ta kinga yaya king yace mana bacci take ,Anya kuwa su yaya bari dai nayi shiru,” kyalkyalewa da dariya sukayi jin iskancin da sumayya take wa su amrah dan sunsan halinta , itama firdausi dariyar take dannewa” uhm ke dai bari , a yan kwanakin nan da muke zuwa part din ai kinga baya hade mana rai kamar da yanxu fa har gaisuwar mu yake amsawa amma da dane ai bamu isaba,” wata dariyar suka kuma saki , ihsan sai satar kallansu basma take da suka cika fam , daga karshema basma mikewa tayi tare da barin part din ba tare da ta tanka musu ba, amrah kuwa harara ta dunga sakar musu, tayi alkawari kuwa sai ta haddasa musu wutar da bazasu iya kashewa ba,tunanin abunda zata musu take kafun ta dan saki murmushin mugunta tana barin wajan ba tare da tace musu uffan ba suma . Suna ganin ta bar wajan suka tafa gabaki dayan su , ihsance ta soma magana “wallahi bamu da mutumci, kun iya tsiya, ku kalli yanda fuskar su tayi kamar wanda aka fadawa mummunan abu”, itama firdausi dora tayi “ rabu da yan iska wai su soyayya , in banda ma iskanci irin nasu su kalli kamar yaya king suce wai sai sun aureshi ko da bala’I ai suma sun kwasowa dala da ganmu”, dan murmushi sumayya ta saki” Aah feedy, so sone fa, Kema kinsani duk Wanda ya kalli zubin yaya king ,ko baya sansa sai yaji wani abu aransa ,musamman idan aka samu marasa tsoran Allah, ko ni kunsani naso yaya king kamar raina tun bansan Menene so ba, har zuwan amrah muka fara samun sabani akan shi, amma yanxu na hakura dashi har abada Sabida yayi mana nisa nesa ba kusa ba , ku duba ku gani fa wa ya taba kawowa zai auri sister , duk da irin abunda mukayi mata bata kullacemuba lokacin da mukaje mata, gaskiya masu irin halin sister kadan ne”, jinjina kai sukayi gabaki d’ayansu kufun ihsan ta furta “ Allah sarki AKHII Allah ya jikanka da rahma, har na tuna lokacin da idan yaya king zai hukunta mu zai hana sa , ko uktiii ta hanashi, ban taba sani yana jin maganar su ba sai lokacin da mukai masa lefi akhiii moha ya bashi hakuri shi da ukhti, sai gashi kuwa beyi mana komai ba , da Yaya kabeer ne ko yaya haroon ina tunanin rugu rugu za suyi mana , duk da suma suna tsoran yaya king sosai kamar sunga mala’ika “,gabaki dayan su saida suka shiga jimamin mutuwar akhiiii kafun kuma su fara bada labarin laifikan da suke yake tema kar su da Wanda king yake Zanesu ukhti ke cecensa.” Ku naji fa Ance sun kusa dawowa suma duk da sun makale a turai sunki dawowa gida ,amma naji ance boss yace su dawo nan da one week kafun ransu ya baci” dariya suka sani kin yanda feedy ta kira king da boss, “itama ukhti fa taji anacewa zatazo tunda batazo bikin yaya king ba , ni har na matsu tazo dan nasan dole ko yayane sai anyi mana dinner indai taso kuma yaya king nasan zai amince ko sabo da ita ne”, gabaki dayan su kuwa jin hakan sai suka fara tsara yanda abun zai kasance duk da basu da tabbacin hakan, sunayi suna dariyar kansu musamman in suka tuno yanda king zai ci ubansu.

➰➰➰➰➰
➰➰➰➰➰➰➰

PART DIN DADA

Ga baki d’aya manyan iyaye ne zaune a falon dada , shiru ko wannansu yayi yana sauraran dada, saida ta kai aya kafun abeey cikin girmamawa ta amsa mata” dada Insha Allahu nan da sati d’aya zasu dawo kamar yanda kikai magana akai, sauran yaran ma insha Allahu zasuyi Auran lokaci ne kawai beyi ba”sallallami dada ta saki” zayeedu,lokaci ne kace beyi bafa , ko dai Bakuyi niyar aurar dazu yanxu ba, Ance zankada zankadan yaya haka babu aure , da alokacin mune ai sai ace baki akai musu , mu duk wacce tayi girman haka ai bazata auru ba, ni dai nagaji inasan ganin jikokina suna zagayeni, Allah ya ji kanka mahamuda Allah ya gafarta maka nasan da kana raye da tuni na fara ganin yan jikokina”, tana kai karshen zancenta ta fara goge hawayen da suke kokarin fitowa, gabaki d’aya sai da tasa jikin kowa na falon yayi sanyi musamman Wanda ta anbata da kowa bazai taba mantashi ba a cikin rayuwar sa, lallashinta suka fara gabi dayansu,kowa yana tofa albarkacin bakinsa. Allah sarki ummey tun lokacin da aka anbato moha jikinta yayi sanyi , addua ta fara masa cikin zuciyar ta , tana kokarin dannewa, amma duk yanda taso boyewan sai da abeey ya ganota, yayi shiru ne kawai bece komai ba dan shima abun yana taba masa zuciya har yanxu.sai da aka gama tattauna na tsawan lokaci kafun mahma ta kalli dada ,toh dada kingama anbato kowa zaiyi aure bamuji naki ba,wani babban salati kaka ta dauka tana kallan mahma da kananan idanuwanta “yanxu auta da yake kin mayar dani kakarkii ni zaki kalla kice na kara aure , toh Allah ya shiryeki dan nasan yanxu ina bude baki masu yan uwa zasu tarar miki” murmushi kowa ya saki dan kowa yasan da su uncle saleem yake , dukda haka kuwa sai da ya tanka,”wannan haqqun ne dada duk Wanda ya taba auta zamu shigar masa “, dan ta bile baki dada tayi tana mikewa tsaye “ daga kai har itan sai na Hana na ci muku mutunci sai naga me shigar muku, ni kunga tafiya ta bacci zanje nayi ma” gabaki dayansu seda fase sukai mata har ta bar part din kafin su dan tattauna gabaki dayan su, ana gamawa kuma kowa ya ya wuce part din da zashi.

➰➰➰➰➰➰
➰➰➰➰➰➰➰
🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧
🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧

Yau ya kasance Friday kamar kullum kiran sallah azubane ya tashesa, yanxun ma hakan ce ta faru a hankali ya bude fararan idanuwansa da suka kara yin haske dasu gwanin sha’awa, kallan yanda take rungume a jikinsa yayi, yana san mikewa amma bayasan tashinta, gudun kar lokacin sallah ya wuce shi yashi raba jikinta da nashi kadan yana gara mata kwanciyar tata, Dan ya mutsa fuskarta tayi bakinta ature,”stubborn , kina baccin ma bazaki hakura ba”.

Wanka yayi jikin brown din jallabiya da ta kara haska kalar fatar jikinsa , gashin kansa a kwance kamar na larabawa ya nadawa rawanin irin nadin larabawa, duk da fuskarsa ba a sake take ba amma wani irin annuri da annashuwane akan fuskartasa da ya kara wa fuskar tsa kwarjini da haiba, gabaki d’aya kamshin turarensa ma imperial majesty ya cika ko ina, hatta tahee dake kwance lafe kan gadon tana shakar kamshin turaren har cikin ranta.tun motsa warsa ta farko ta farka itama amma taki motsawa , yanxu ma tunanin yanda zata tashi take yi , fatanta d’aya Allah karyace yau ma a dakin zaiyi sallah. Yana kallan motsinta tun dazu yasan ta farka , karasawa yayi inda take kafun ya sunkuyo kadan yayi pecking kumatunta, ai kuwa da sauri ta ware idanuwanta akansa , dan Jan hancinta yayi kadan kafun ya furta “morning “,ya karasa yana tayata mikewa zaune, a hankali ta zuro kafafuwanta kafun ta mike tsaye, tana mikewa kuma ai ta koma tana rintse idanuwanta, ganin hakan yasashi saurin kamata” let’s me help you “, girgiza masa kai tayi,”zan iya, gashican ana kiran sallah kar jam’i ya wuce ka”,ta karasa tana kara mikewa kafun ta soma tafiya a hankali duk da yanda take kokarin daidaita tafiyarta,kallan kafar yayi kafun ya furta “ I have to check it again”, yana ganin shigewarta toilet din ya bar dakin bayan dan jotting din da ya bar mata a cikin wat small paper da wayarta a gefe. A toilet kuwa daurewa tahee tayi ta gasa jikinta sosai kamar yanda taga yayi mata kafun tayi wanka da alwala, sosai taji dadin jikinta kuwa, wani pink material mara nauyi ta saka a jikinta tare da feshe ilahirin jikinta da daddad’an imperial majesty me shegen kamshi, a hankali take yin komai , har ta idar da sallah tayi karatunta kafun , a hankali ta sake mikewa ta koma kan gadon, yar paper din data ganine yafi Jan hankalinta,tana daga gawa taga wani hadaddan handwriting me shegen kyau” take care of your self , I love you “, shine abunda ke jikin paper , bata san lokacin da ta fara murmushi ba ita kadai, rike paper tayi a hannunta kafun ta kwanta baccin da take ji na fusgarta, tun tana Hana kanta bacci har yazo ya dauketa gabaki d’aya .

****Yana shigowa ya tarar da ita kwance lullube da bargo ga kamshin turaransa da ya cika dakin sosai, doso inda take yayi yana kara jin kamshin turaran na kara karfi alamar Itace ta saka , yana sunkuyowa kuwa ga daki hancinsa, kwanciyarta ya gyara mata kafun yayi mata peck a goshinta. A maimakon ya koma bacci system dinsa ya dauka ya fara operating, ya dade akai kafun ya je ya dakko coffe dinsa , har zai kai baki ya tuna lokacin da barar da shayin tana cewa da akwai guba aciki, kawar da coffee din yayi ba tare da yasha ba, kiran wayar sa da akai ne ya dauka ganin me kiran, a hankali yayi sallama, kafun ya dan saki murmushi jin abinda taci kin wayar kecewa, ukhtii ya kike, banji amsar data bashi ba , sai dan murmushin gefen fuska da yayi kadan, sun dade suna tattauna a wayar kafun ya ajje wayar ga ba d’aya , aikin da yake a cikin system dinsa ya cigaba dayi har wajan 11 , har lokacin kuwa tahee na bacci.

11 :30 am ta fara mutsi mutsi da ido kafun ta bude idanuwan gabaki d’aya cikin hasken dakin, a hankali ta mike zaune babu kowa a dakin sai system dinsa da daya daga cikin wayoyinsa da ke wajan. Mikewa tayi da niyar yin wani wankan da brush taga wayarsa na haske kamar ana kira, sharewa tayi kamar zata wuce taga ta karayi, cikin karan bani ta dauki wayar tasa da niyar kaimasa,message din da aka turo masa ne ya dan dauki hankalinta, bata san lokacin data fara karantawa ba “SWEETHEART NAJIKA SHIRU,BAYAN KACEMUN KAYI MISSING”. saura kadan wayar hannunta ta fadi cikin karo da message din da tayi, a Daidai lokacin da yake shigowa cikin dakin hannunsa dauke da plate.
Mss Lee 💖
07041879581.

Leave a Reply

Back to top button