Hausa NovelsMatar Makaho Hausa Novel

Matar Makaho 80-81

Sponsored Links

Page 8⃣0⃣&8⃣1⃣
Maciji ne babba duk da darene amma macijin fatarsa na sheki, Girgiza kai gidado yayi Alamu dai ba sarinsa yayi ba, da gudu Muhammad ya jawo wani katon reshen itace babba, ya bugawa macijin da karfi akai, ya sake buga masa take kan macijin ya wargaje, mikewa muhammad yayi ya taimaka wa gidado suka mike, ganin maciji a wajen yasa su cigaba da tafiya duk da dare ne, saida suka isa wani wajen yashi kafun suka yad’a zango, agun suka kwanta.

Basu suka farka ba sai washe gari, harma gari ya waye kafun suka farka, taimama sukayi, sukayi sallah zuwa lokacin hannun Muhammad yayi mugun kumbura sosai, badaru ne ya tsinko wani ganye ya mursuke yasaka masa a ciwon, mangoro suka tsinko mai yawa suka sha ga ruwan korama suka iba, sukaci gaba da tafiya.

A haka su Al’ameen sukayi ta tafiya kusan sati biyu, suna fasa hanya saidai su shiga wannan dajin su fita suyi wannan, gabaki d’aya wahala ya canja su, hannun Muhammad yayi dan sauki, kafafunsu tun yana musu rad’adi har suka saba, ga giransa daya tsage, da ace a garine dinki za’a masa, Amma haka sukaci gaba da tafi giran na warke wa, amma fa fatar bai hade ba sai yayi kamar tsagun wuka wajen yayi, sai yayi matikar karawa fuskar tasa kyau.

Saida su Al’ameen sukayi kusan wata biyu, suna tafiya a kafa bayan zama da sukad’anyi a wasu kauyuka, yaukam tsintar kansu sukayi a sahara mai zafin gaske, Allah yasa ma sunyi guzuri saboda kauyen da suka baro sun sanar dasu gabansu sahara ne, suna tsallake sa nijar zasu shiga.

*********
Ta bangaren sumayya basu farka ba sai mangariba, Bathroom suka shiga sukayi Alwala, bayan sunyi sallah sumayya ta kalli khadija”ki shiga kitchen a cikin cefenen da kukayin nan ki d’auka ki dafa mana koh abu mara nauyi ne”

Toh Aunty khadija tace ta wuce wa kitchen in, dayake duk a falo yake basai ta fita waje ba flat ne babba, khadija na shiga kitchen saiga yar laila mai shekara biyar ta shigo d’akin da sallama

Amsa mata sumayya tayi ta karbi kulan da ke hannunta, ina kwana aunty, ta gaida sumayya.

Murmushi sumayya tayi tace”Ina wuni dai baby”

Ina wuni?

“Lafiya munira, Dady ya dawa koh?

Eh ya dawo gashi momy ta bani na kawo miki, tace tana mikawa sumayya kulan

” wai gaskiya mungode wa momy kinji kice nama dady sannu da zuwa.

Toh yarinyar tace tana fita a falon, kwalama khadija kira sumayya tayi, bayan ta fitoh ne sumayya kece mata, Laila ta kawo musu abinci tabar girkin, ta d’auko musu pure water biyu dake kitchen in, A plate d’aya sumayya ta zuba musu abincin, tuwo ne miyar shuwaka da kifi busheshe, sosai sukaci tuwon suka sha ruwa tashi khadija tayi tarufe musu kofar falon, tabar kee a jikin kofar wanka sukayi dayake Abuja akwai nepa yasa ta kunna AC dake makale a falo, don sunyi sa’a akwai Ac a falo, shiyasa sumayya tace susa katifa a falon in, kwanciya sukayi akatifarsu.

Washe gari tie da kwai suka karya dashi khadija ta wanke musu d’an plate insu da kwanon laila,khadija ce ta maida mata kwanukan da safe, sumayya had’a laila tayi da khadija da zata fita aiki akan suje ta kai khadija makarantar da yaranta ke zuwa, tunda transfer ne ba sabon register zatayi ba.

Khadija ta samu gurbin karatu a school in, sai dai fa kudin makaranta 50k ne duk team nan ma wai makaranta daidai gwargwado kenan,sai kudin school bus, a ranan suka bawa khadija uniform nata Daman tazo da kome na makarantan ta harda note book, shiyasa washe gari da safe tana karyawa ta sanya uniform nata, siket ne da riga sai necktie da baby hijab, bayan khadija ta tafi makaranta dayake school bus na jiranta a bakin titi, Karyawa sumayya tayi ta koma ta kwanta tama rasa me zata kama, ta gaji da zama waje d’aya tashi tayi ta shirya ta fita, da kwatance taje clinic don yanzun cikin na neman 4 months shiyasa takeson fara zuwa awo abinka da yar boko dakanta, ta gane asibitin, ta bude file a wajen sannan zatana zuwa clinic harta haihu, daga asibiti kasuwa ta wuce tad’an saisai musu kayan masarufi.

Bayan ta dawo wanka tayi ta dafa musu abinci sai yamma khadija ta dawo, uniform nata ta wanke ta had’a da kayanda Auntin ta ta saka jiya, tayi moping tayi musu girkin dare, yayin da sumayya ke kwance akan katifa tana kallo a system nata.

Bayan mangari ba saiga laila ta shigo lokacin sumayya da khadija nacin abinci a kasan tiles, sumayya na zaune akan filo saboda yanayin ta da ba’aso ta dabasu a kasa.

Ah ah hajiya sumy haka ake makwantakan koh nokin babu.

“Kai laila kin cika iyayi maigida ya dawo basai mu baku waje ku sarara ba, tukunna”

Karasowa falon laila tayi, lallai ma sumayya wani irin bamu waje, kaman sabbin aure

Ina kwana Maman munira?

Lafiya khadija ya school in?

Lafiya klau, tace tana iban abinci a wani plate ta wuce daki.

“Kai laila ga abinci bismillah”

Zama tayi a bakin katifar, sumayya nayi magana da baban munira yace min za’a samu shago, amma nidai gaskiya sumayya hankalina bai kama ki bude shago yanzun ba, duba da halinda kike ciki bai kamata ki dukufa wajen lalle ba?

“Toh yanzun laila in banyi lalle ba me xanyi? kinsan dai kudin hannuna bazai isa na zauna nayita ci ba ga ciki”

Eh gaskiya ne sumayya Amma ni a ganina gwara dai ki tsaya iyya make-up, kuma kinga bude shago ba karamin kudi zaici ba ina laifin ki bari, ni zanna tallata miki kwalliyar a office namu kinga koh mutane biyar kike samu a sati, tunda yanayin biyan Abuja daban da jalingo saiki d’an tara abinda kika samu kina biyawa khadija school fees daidai ki haihu.

“Kai nagode yar uwa, kuma inba damuwa tunda khadija ta iyya kitso koh a weekend ne saita samu customers itama, kinga zamu d’an karu kad’an”

Au ta iyya kitso ne? ai koh a gidan nan zata samu customers every week students ke kitso, koma kitson nan ba’ayi kasa da 1k

“Shikenan kikam laila nagode kuma na yarda da shawaran ki zanbar zancen shagon saina haihu”

Toh Allah ya sauke ki lafiya ga wannan na kawo miki tsaraba ya kawo jiya, tayi maganar tana mikawa sumayya laida.

“Kai gaskiya munfa gode muna masa sannu da dawowa” ta karasa maganar da bude laidan kwakwane na ruwa manya manya guda biyar.

Bayan fitar laila ne, sumayya ta kira khadija tazo ta fasa musu kwakwan, guda biyu suka ci.

Washe gari bayan laila ta dawo office, take sanar da sumayya, kanwar matar minister office nasu d’aya, toh Addan ta ta haihu kuma ta sanar dasu, sumayya ta iyya make-up da lalle Amma ciki ne da sumayya make-up kawai zata iyya, kuma sun amince washe gari da laila zata tafi office ta raka sumayya gidan minister, kuma Alhamdulilah matar tama kwalliya da yaranta harda kannen ta, bata koma gida ba sai yamma da kud’ade masu yawa, ga customers da sukayi booking.

Kafun wata d’aya khadija da sumayya sun saba da rayuwar Abuja, yanzun ma khadija kema matar wani mai kudin unguwan kitso da yaranta duk sati, sunyi za’ana biyan ta duk wata,sumayya ta bude ma khadija wani account in da take tara kudin kitson ta a ciki, ga yaran dake gidan hayan duk suna zuwa, ga wa’inda take ma a class in sunje school lokacin break .

Alhamdulilah sumayya rayuwa yanzun tana musu dadi, sunaci suna sha ga kudi suna samu ba laifi a make-up da lalle Amma kullum tarawa suke, banda Kayan abinci da abin bukatan yau da kullum basa kashe kudi.

Yanzun cikin sumayya nada wata biyar da yan satitika, sosai ya fitoh kamar na wata bakwai, tayi nauyi sosai tabar makeup in ma yanzun khadija kad’ai ke kitso, don yanzun daga weekend yayi mutane ke shiga da fita harda ma’aikata wasu kamma Christian ne.

****************
Muhammad fa gabaki d’aya sun jirkita har gwara su gidado sun saba da yawo a daji ba kamar shiba.

Yau suka diro wani kauye gabaki d’aya sahara ne kasar, gasu da rakuma, sosai garin ya basu sha’awa ganin musulmai ne saidai fa sam basu iyya hausa ba, Gidado ne yake sanar dasu cewa buzaye ne, sun samu tarba mai kyau kwanan su biyu suka kama hanya, don ba jin yaren yan kauyen suke ba, don haka zama a ciki wahala zasu sha, tafiya sukayi na kwana hudu kafun suka shigo cikin gari koh ince birni d’aga ido muhammad yayi yana bin garin da kallo.

Wani bawan Allah suka tare ganin fa garin ba kauye bane, garine koh ince birni, Tambayar sa sukayi ganin kamar bahaushe da hausa Al’ameen ya gaidashi aiko da hausar ya Amsa duk da hausar bata fita sosai.

Tambayar sa yayi koh a wace kasa suke, nijar ya basa amsa, kuma suna babban birni ne, shuru Sukayi, suka koma gefen wani gida mai ginin kasa suka zauna, gabaki d’ayansu sun ma rasa ina zasu saka ransu suji sanyi, sai yanzun Gidado ya samu sararin tuna baya, wai yau shine gidado babu bappa babu inna? babu lantana babu indo da yarda aka haifa masa? kai gaskiya yaga jarabawa Allah ya basa ikon cinyewa wannan shine fatansa gabaki d’aya ya shiga damuwa, har baisan hawaye sun sauka a kumatunsa ba, ji kawai yayi ana share masa hawaye da hannu mai laushi, figigit ya farka daga dogon nazarin da ya fad’a.

Gidado Awad’a muyal kaji kome yana da karshe, kayi hakuri mu rungume jarabawar da Allah ya d’aura mana, kaga badaru ma daya rasa iyayensa gabaki d’aya, aka yayyankasu a idanunsa yayi hakuri, insha Allah wata rana zamu hadu dasu inna.

Gaskiya ne gidado abinda Al’ameen yace maka kayi hakuri, Allah yana son masu hakuri.

Badaru bazaku gane yanda nake ji ba, gwara dai nayi kuka koh zan rage rad’aden dake dankare a raina.

Kayi hakuri gidado muhammad yace masa yana kama hannunsa, yaron yayi matukar basa tausayi, A haka sukaci gaba da zama a bakin kofar gidan, har aka kira mangari ba masallaci suka shiga sukayi sallah, bayan an idar kofar gidan suka kara komawa, atakaice dai har bayan isha’i suna kofar gidan sai kusan karfe 9,suka ga wani buzun dattijo kyakkyawa yana sanyi da riga babba, irin na buzaye da riga fantalele, yayi rawani ya rufe fuskarsa da shi, hannunsa d’auke da wasu ciyayi, kallonsa suke kamar yanda shima yayi sakaki yana kallonsu, Amma dai baiyi magana ba bude kofar gidansa yayi ya shiga ciki baice kome ba.

Suma muhammad zamansu sukaci gaba dayi agun, gabaki d’aya yunwa ya ishesu wannan birnine ba kauye ba, dan kauyukan da suka tsallaka kafun su iso nijar koh basu bukaci abinci ba, ake musu tarba mai mutunci abasu abinci suci su kwana su wuce, Amma a nan kamma an maidasu kamar wasu Abin kallo.

Mutumin d’azun ne ya sake fitowa, kallon su muhammad yayi sai kuma ya had’a fuska ganin har yanzun basu bar masa kofar gida ba, kai bayin Allah lafiya ya zakuzo ku zauna mini a kofar gida tun yamma har yanzun baku zakud’a ba? tun shigowa ta unguwa aka sanar dani wasu fulani sun yad’a zango a kofar gidana?

Shuru sukayi dukansu suna kallon sa sun ma kasa magana, ido kawai suke binsa dashi.

Kai ku daina kallona tunda baku iyya magana ba ai kun iyya ji? ku barmin kofar gida yanzu yanzun nan, yace cikin hausar sa dake dishe, alamu dai bai wani kware sosai a hausar ba.

Badaru ne yayi magana, Kayi hakuri baba mu bakine wallahi bamu da inda zamuje.

Sai akace kuzo kofar gidana?

Kallonsa muhammad yayi A hankali yace, Ah ah kamana aikin gafara ka barmu mu zauna in Allah ya kaimu safiya insha Allah zamu tafi.

Kala mutumin baice ba ya koma cikin gida abinsa, yabar su Al’ameen zaune a wajen, da misalin karfe 1 na dare aka fara yayafi kamar da wasa ruwa ya tsinke, suda suke makale a kofar gidan da gudu suka koma jikin rumfar yayi, amma duk da haka ruwan na tabasu.

Mutumin ne ya sake fitowa da buhu a kansa ya tare ruwa, hannunsa d’auke da touci, haska su yayi ya gansu a bare a cikin rumfa, Kai kuzo nan.

Da sauri su Al’ameen suka karaso inda yake cikin sassarfa.

Ku shigo kawai mutumin yace musu ya bude kofar ya shiga, ba musu suka bisa ciki, tsayawa sukayi a bakin kofar d’akin da ya shiga, bai jima ba sai gasa ya dawo hannunsa d’auke da kaya kala uku,musu iso yayi cikin d’aya d’akin dake gefen nasa, ya fita ya basu waje su shirya, dayake dare ne duk a d’akin suka chanja kaya, jikekin suka fitar dashi baranda mutumin ne ya kawo musu shayi a babban buta sai kananun kofi guda uku.

Aje musu yayi tare da musu bismillah, ba musu suka zauna suka fara shan shayin, shikam fita yayi bai jima ba sai gasa ya dawo da kwano d’auke da nama a ciki aje musu yayi ya fita, bayan sunci abinci kwanciya sukayi don har lokaci mutumin bai dawo ba.

Washe gari bayan sun dawo sallan asuba ne, mutumin ya dawo d’akin zama yayi akan kujera da akayi na kaba a d’akin, ya dubesu gabaki d’ayan su suna zaune a kasa, sauke idanunsa yayi akan muhammad tun jiya yake kallonsa yana wani nazari akansa, tunda yaga yaron yake zullumi, tambayar su yayi daga ina suke kuma maiya shigo dasu nijar don basuyi kama da yan kasa ba.

Kome gidado ya sanar dashi akan abinda ya faru a kauyen su, Amma bai fad’a masa Asalin muhammad ba.

Tambayar su yayi kuna nufin duk garinku d’aya, kuma gudun hijira kukayi?

Kai Al’ameen ya d’aga masa Alamu eh.

Toh nidai yanzun zan tafi aiki, kuma sai dare nake dawowa tunda baku da mafaka ku zauna agidan nan, har randa Allah zaisa ku koma inda kuka fitoh, Ni da zuciya d’aya zan zauna daku Ba cuta ba cutarwa ina fata kuma a wajen ku hakan take?

Insha Allah baba bazaka samemu da wani mummunan abuba.

Toh Allah yasa akwai masara a rumfar tsakar gida koh xaku dafa ?shine kad’ai dani a gidan nan, yace yana mikewa wanka yayi ya fita a gidan bayan ya dafawa su Al’ameen wani shayi mai masifar dadi, bayan fitarsa Al’ameen shara ya masa gidado kam kayansa ya ibo masu datti daya gani a makale a igiya ga omo a gefe ya had’a ya wanke masa, badaru kam butotin shayin da suka gani a gindin murhu duk ya wanke, bayan Al’ameen ya gama sharan, masaran da ya gani d’anye ya d’aura a wuta, yana nuna shi sukaci da rana, suka kwanta don sun rasa Aikin da zasuyi.

Da misalin karfe hudu na yamma bayan su Al’ameen sun dawo daga masallaci suna zaune a tsakar gida, hira kawai suke a tsakanin su, suna tuna rayuwar su na baya da abubuwan da ya faru, kamar a mafarki sukaji ana dukan kofar gidan da karfi, cikin yaren buzanci ake magana ga muryoyin mutane na tashi kota ina……………🍀🍀🍀

✨Ruqeenjalal✨

🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
~ Na ~

🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

Back to top button