Hausa NovelsNoor Al Hayat Hausa Novel

Noor Al Hayat 45

Sponsored Links

Bayan kusan minti talatin khadijah dake ta xaune daki hankalinta ya ki kwanciya ta kalli wayarta da sauri jin yana ring, ganin khaleel ne ta mike ta sa Hijab ta fita tana addu’ar Allah ya sa twins din ya dawo da, Nanny kadai ce parlor ta ce mata tana xuwa sannan ta fita waje, hade rai tayi dai dai lkcn da su shureim suka sakko daga cikin motar ko wannensu rike da leda khaleel ma ya fito, rungumeta suka yi gaba daya cike da farin cikin ganinta, fuskarta daure tace “Oya mu wuce ciki…” Suka juya suna kallon khaleel da ya rungume hannunsa, jallabiya ne sanye jikinsa ya dinga kallon yaran suka daga masa hannu sudais yace “Uncle are u coming tomorrow plss” Khaleel yyi murmushi yana gyada kai yace “Sure” khadijah bata basu daman sake ce masa komai ba ta tunkudasu cikin gida, Hijab dinta taji khaleel ya riko ta juyo da sauri, murya can kasa yace “Wait” ta kalli yaranta da har sun shige gate, ta kwace Hijab din fuskarta daure tace “Meye haka pls” yana kallonta a hankali yace “Ba gaisuwa xa ki wuce?” Hararansa tayi tace “Wanda na maka daxu a waya fa?” Jinginar da ita yyi da mota, yace “Daban” ta sauke idonta kasa xuciyarta na bugawa jin bai ce komai ba ta dago kanta taga kallonta yake, da sauri ta kara sunkuyar da kanta, yyi murmushi murya can kasa yace “Can I come gobe mu gaisa da Umma?” Ba tare da ta dago ba tace “Why?” Yace “Haka nan, twins suka ce in xo in gaida Ummansu she will like me” kin cewa komai tayi, bayan few seconds yace “Khadijah” dauke kai tayi tace “Allah ya kai mu” Ya d’an yi murmushi yace “Ameen, to yaushe xa ki koma?” Sai a sannan ta kallesa, lkci daya ta sauke idonta tace “Monday in sha Allah” ya dan wara ido yace “Har Monday?” Shiru tayi, murya can kasa yace “Alryt then, we go together” kai ta gyada masa kawai, yace “Toh sai da safe” ta saci kallonsa a hankali tace “Allah ya kai mu” daga haka ya bata hanya ta wuce ciki ya bi ta da ido. Umma dake parlor ta bi ta da kallo har ta shiga daki sannan ta mike ta bi bayanta, xaunawa gefen gado tayi tace “Saurayin ki ne wanda ya xo Khadijah?” Khadijah ta xaro ido tace “Saurayi kuma Umma, aa ba saurayina bane” Umma tace “Kawar ki ce kenan, it’s high time you settle down with a husband daughter…” Khadijah ta kalleta da sauri, Umma tace “Ehh, kuma ban son ya wani dau lkci, in dai kina da wanda ya kwanta maki kika yaba hankalinsa, ki fito da shi, kin ga wannan dama ce da xa mu samu na xuwa katsina…. Idan ma kawun nan ki baxa su daura maki aure ba baxa ki rasa wanda xai daura maki ba” Rasa abun cewa Khadijah tayi, don ita dai tasan bata da saurayi, Umma tace “You think over it daughter” daga haka ta mike ta bar dakin. Kasa bacci daren ranan Khadijah tayi maganar da Umma tayi mata ya tsaya mata sosai, ko kadan aure ba ya cikin tsarin da tayi ma rayuwarta, babu abinda ke sake daga mata hankali sai ganin how serious Umma tayi xancen, gashi ta ma kasa ce mata ta hadu da Aliyu saboda bata ma son xancen, sai dai kuma ko don Aliyun ma ya kamata tayi auren ko xai fita rayuwarta da yake kokarin shiga yanxu, har asuba bata wani ritsa ba, sai a sannan ta fara da ta sanin dawowa ma da tayi.
Aliyu ya kalli Mumy a karo na farko tun shigowar ta dakin tana masa magana babu yabo babu fallasa tamkar dai umarni ma take ba sa, ya d’an yi murmushi sannan yace “Mumy ba fa aure tsakanina da Iklima….” Strictly Mumy tace “Haka kace?” Yace “Ehh mumy, domin kuwa da ciki aka daura auren, yanxu kuma naga alamar sun je sun xubar da cikin” Mumy ta dinga masa wani kallo ko kiftawa babu, juyawa tayi ta fice daga dakin rai a bace, yyi murmushi ya na ci gaba da analysis din da yake tun safe amma ya kasa arriving komai, ya lumshe ido keenly, yana naxari… it all started bayan ya sha coffee da safe ranan, and then? Kawai ya dai ji ya kasa fita aiki, and… Bude kofar da aka yi ya bude ido ya juya da sauri, Saleem ne ya shigo dakin Aliyu ya masa kallo daya ya dauke kai, murmushi ya dinga yi ya ki cewa komai, aliyu ya kallesa a karo na biyu, ya mike yace “Ya aka yi malam?” Dariya saleem yyi yace “Wani xance naji yan gidan nan ke yi yaya, is it for real?” Wani kallo Aliyu ya dinga masa cikin cool voice dinsa yace “Get out and close the door behind you saleem” Saleem ya daga kafada yana murmushi yace “But I neva expect that from you, ni da ake ma warning a da, sai gashi kuma…..” Dariya yyi ya fita ya rufe kofar, Aliyu ya xauna xuciyarsa na tafarfasa ya ji duk ya tsani yan gidan nasu gaba daya, ya hade kansa da table din gabansa….
Khadijah na kitchen tana girkin lunch misalin sha biyu Shureim ya kawo mata waya dake ring, Karba tayi ta daga ta kai kunne, muryarsa ya daki kunnenta, yace “How was your nyt?” Tace “Twas good, ya gida” yace “Alhmdllh, ya twins?” Tace “They are fine” yace “Alryt. Anjima xan xo” tace “Allah ya kai mu” daga haka yyi mata sallama ya katse wayar, ta juya xata mika ma Shureim wayar, wani mugun faduwa gabanta yyi ganin irin tsayuwar da yyi yana jiranta, lkci daya Aliyu ya fado mata ta mika masa wayar a sanyaye, yaron ya karba ya juya ya fita ta ci gaba da abinda. Aliyu ya fito daga bedroom dinsa rike da makullin mota xai bar gidan ganin he is nt arriving at anything better a tunanin da yake tun safe, baby ma da fitowarta kenan daga dakinsu ta juya ta koma ganinsa, tun ranan da Anty khadijah ta fadi ma yan gidan abinda ya faru tsakaninsa da Khadijah kusan duk suke canxa hanya idan sun gansa, gaisuwa ma sai sun ga dama, duk wannan baya masa ciwo sai irin yanda Saleem ke making jest of him ko da yaushe cikin masa dariya yake, he is just trying hard to control his self baya kulasa, Mumy ce ta fito daga dakin Anty Khadijah tana kwalo ma Saleem kira hankali tahse, shi dai Aliyu na tsaye don har ita bata bin ta kansa a gidan, Saleem ya fito tace “Maxa ka dauko makullin motar iklima ce ba lafiya, kayi sauri don Allah” Aliyu na jin haka ya sauka Downstairs ya bar parlorn ya hau motarsa ya fice a gidan, direct gidan Farouq ya nufa, yana isa bakin gate ya kira sa ya sanar da shi yana kofar gida, fitowa yyi daga motar bayan Farouq yace ya shigo yana ma compound, Aliyu ya shiga gidan yana amsa gaisuwar mai gadi, can ya hango Farouq su biyu xaune kan biyu daga cikin kujerun dake wajen, har ya isa wajen idonsa na kan wanda ke xaune tare da farouq, shi ma dai dai nan ya dago kai suka yi ido hudu, kallon kallo suka shiga yi da wani ex gaba daya fuskarsu, Farouq dake nuna ma Aliyu kujera yana murmushi yace “The great Dr, mu dai mun je daurin auren ka baka nan, ban kuma kira ka ba saboda ba aji mutuwar sarki a baki na ba” kin xama Aliyu yyi yace “Ehh naga alama, I was just passing by dama nace in shigo mu gaisa so ba dadewa xan yi ba, ana jirana a mota, I will leave now” Farouq ya masa wani kallo yace “Bana son walakanci fa, daga xuwa sai tafiya, yaushe ma ka dawo Nigeria” tuni Aliyu ya juya ya bar wajen da sauri, Farouq ya mike yace “What’s the meaning of this Aliyu!” Ba tare da ya juyo ba yace “Sure, a gaida min su Haiydar da Madam am in a haste” Farouq ya bi sa da kallo baki sake kafin ya kalli abokin sa dake xaune yana danna waya, dago kai khaleel yyi shi ma ya kallesa yace “Kila don ya gan ni ne yasa ba ya son xaunawa….” Farouq ya ma khaleel wani kallo, sai kuma yyi dariya yace “Toh ai ina ya san ka da xai ki xama saboda kai kai kuma da wani xargi, that’s Aliyu for you, haka nan yake ba wai don saboda kai bane it’s his habit” murmushi Khaleel yyi yace “Toh ya ji dadi, nima yanxu xan wuce ina da inda xan je” daga haka ya mike Farouq yace “Haba dai, so early yaushe rabon mu hadu Dr Ayman?” Khaleel yace “Assuming babu inda xan je I will stay kai ma ka sani” Farouq yyi murmushi ya mike yace “Toh shkkn, wai ya Jawahir din ka, saura watanni nawa bikin?” Khaleel yyi murmushi da kamar baxai ce komai ba sai kuma yace “Uku kawai” Farouq yace “Toh Allah ya kai mu, my regards to her, Anty kuma kace mata plsss tayi hakuri ina nan xuwa in gaisheta” Shi dai khaleel bai ce komai ba suna tafiya har suka fita gidan, sai da suka isa gun motar khaleel, khaleel ya juya yana kallon Farouq strictly yace “Don’t dare say anything about me to that guy that just left Umar, tell him nothing about me if he shud ask” da mamaki Farouq yace “Anything? Like? Ka taba sanin sa ne?” Khaleel yace “No ban san shi ba, I just know xai yi ma tambaya a kai na, kar kuma ka gaya masa komai” daga haka ya shiga motarsa Farouq ya dinga kallon sa yace “shi aliyun?” Dariya yyi yace “Yanda kake haka yake shi ma ai, banbancin ku kadan ne, soo nasan baxai ma min tambaya a kan ka ba, beside shi ma a UK yake ai, a Dr also” Shi dai khaleel bai ce komai ba ya ja motarsa ya bar wajen. Yau dai Khadijah mayafi ta daura kan atamfar jikinta ta fito amma ba tare da su Sudais ba, duk da bata yi kwalliya ba amma tayi kyau ne ba kadan ba, ta glass khaleel ke ta kallonta ganin jingina tayi da motar bata bude ba ya sa ya bude ya fito ya xagayo ta inda take, ba tare da ta kallesa ba tace “Ina yini?” A hankali yace “Cool, ya boys dina” tace “They are inside, mu je sai ka gaisa da Umma” daga haka ta nufi cikin gidan ya bi ta da kallo da farko kafin ya bi bayanta, Sosai Umma ta tarbi khaleel da yaki kallonta kansa a kasa, xaman ma bakin kujera ya xauna kana ganinsa kasan duk a takure yake, Umma ta tambayesa mutanen gida yace duk suna lafiya, dariya ya ba Khadijah don bata tana xaton yana da kunya haka ba don ko da wasa ya ki dago kansa, Umma da ta lura da haka ita ma ta bar masu parlorn, sai a sannan khaleel ya dago kamar munafuki, khadijah dake ta murmushi tana xuba masa lemo a cup tace “Kamar gaske” mikewa yayi ya mata wani kallo murya can kasa yace “Karya ce dama, am outside” da sauri ta kallesa tace “Me xa kayi a waje” yace “I can’t stay here” ta bata fuska tace “Abinci fa xan xuba maka” yace “Ni bana jin yunwa, kawai ki turo min twins” daga haka ya nufi kofa kamar ana hankada sa, Khadijah ta bi sa da harara har ya fita, tsaki ta yi ta xauna kujera tana turo baki, Ba a dau lkci ba ya fara kiranta a waya har ya katse bata dauka ba, ya sake kira ta ki dauka, text ya turo mata yace “Plss Khadijah, ina mota fa ni baxan iya xaman parlorn ba, idan baxa ki fito ba ki turo min su sudais kawai” tashi tayi ta wuce dakin Umma don suna can suna kallo basu ma san ya xo ba, Umma na ganinta tace “Barin sa ki ka yi shi kadai a parlor?” Khadijah ta tabe baki tace “ya fita yana waje” Umma tace “Saboda me?” Tace “Wai baxai iya xama a parlorn ba” Murmushi Umma tayi tace “Shi kuma haka yake da kunya, Khadijah ina kika samo balarabe?” Xaro ido Khadijah tayi lkci daya ta fashe da dariya tace “Ba balarabe bane fa shi” hararata Umma tayi tace “Ya xa ki ce min ba balarabe bane” Murmushi Khadijah tayi tace “Toh ni dai haka yace min” Umma tace “Ya dai ce maki hakan ne, to ki fita ki samesa tunda baxai xauna parlor ba” Tare da su Sudais ta fita, khaleel ya fito daga motar yana kallonta bayan yyi pecking yaran da suka yi murnan ganinsa yace “Har da walakanci koh?” Tace “Nima ae shi ka min” shiru yyi yana kallonta, can yyi murmushi yace “Baki san ina da kunya sosai ba ko” Khadijah bata san lkcn da tayi dariya ba ya dinga kallonta don bai taba ganin dariyarta haka ba, har da rike ciki, ganin yanda yake kallonta ta hadiye dariyar tana murmushi tace “Amma a nan Nigeria kake ajiye kunyar idan xa ka UK koh?” Xaro ido yayi ba don yaranta dake gun ba da babu abinda xai hanasa jawota jikinsa tayi bayanin abinda take nufi, dariya kawai khadijah take tana kallonsa, khaleel ya kasa cewa komai, kawai ya 6uge da shafa lallausan bak’in gashin kansa, ta sata kallonsa ta sake kyalkyalewa da dariya, yyi murmushi ya cire glass din idonsa murya can kasa yace “Xa ki yi bayani ai xa mu koma UK din” ta hade rai tace “So?” Yana murmushi yace “Nothing, ki gaya ma Umma xa mu je shopping da su sudais plss har da ke” khadijah da bata sake kallon fuskarsa ba tace “Noo ban da ni” yace “Plss” tace “Ni baxan je ba da gaske, su dai ka tafi da su” da kyar da kyar khaleel ya lallabata bayan ta sa ya rufe idanuwansa da glass din da ya cire sannan ta yarda xata bi su, amma bayan ta gaya ma Umma idan xata yarda, ganin tare da su sudais ne Umma ta yarda suka tafi bayan tace kar su dade, front seat ya bude ma su Shureim suka shiga, ganin haka ta bude back seat ta shiga, sai da suka yi nisa khaleel yace “Mu je ki gaida mum dita nima, it’s just malali here ba nisa….” Da sauri khadijah tace “Noo plss, sai in je a wa?” Yana kallonta murya can kasa yace “A surkarta to be” shiru khadijah tayi ta na kallonsa da mamaki, ya mayar da dubansa kan titi yana driving, da sauri tace “Noo, sae dai a matsayin friend dinka, and am not ready for that Dr don ban ce ma umma xan je ko ina ba daga inda kace xaka kai mu” a hankali yace “Ohk then, amma xa mu biya gidansu jawaheer mu dauketa, I think she wants to shop also” kallonsa Khadijah ta tsaya yi ta ma rasa abinda xata ce masa, ai ko suka isa anguwarsu jawaheer din yyi parking ya dau waya ya kirata yace yana waje, khadijah tayi karfin halin cewa “Toh su sudais su dawo baya” Khaleel yace “Noo xata xauna baya ita ma, no probs” Ba a dau lkci ba jawaheer ta fito, she is a real definition of black beauty, kyakkaywa ce ita din ta karshe, ta bude front seat tace “Sweetheart ashe da gaske xaka xo din” ganin su sudais da Shureim ta wara ido tace “Waoww cuties, ina ka samo su swthrt? They are so cute” gaisheta yan biyun suka yi, duk ta yi masu kiss a goshi, Khaleel dake kallonta yace “Yarana ne” dariya ta yi tace “Kai dear, don Allah waye su, sun min kyau wllh” ya kalli khadijah ta madubi yace “Ga Aunt dinsu a baya nan” sai a sannan jawaheer ta kalli baya da sauri tace “Ohh ban lura ba, hello” Khadijah tace “Hi” jawahir na murmushi tace “You’ve got sweet siblings” murmushi khadijah ta kirkira, kamar baxa ta ce komai ba sai kuma murya can kasa kamar ana tilastata tace “Thanks” jawahir ta bude bayan motar ta shiga ta rufe khaleel ya ja motar suka bar wajen, ta madubi yake ta kallon khadijah da ta kauda kai tana kallon waje, ita kuma jawahir na ta basa labari da siririyar muryarta da ya cika motar. Farouq dake ta kallon Aliyu da d’an mamaki yace “Ko meye dalilin da yasa kake son sanin sa Dr?” Aliyu ya hade rai yace “Idan xaka gaya min ka gaya min” Farouq yace “He is my good friend, tare muka yi karatu a England degree and masters, his mum from Saudi Arabia, the most simplest woman I have ever known, his dad a Nigerian from kano, shi kadai ne namiji gidansu with 4 siblings duk mata, Dr Ayman ba shi da matsala, he is free with everyone sai dai he don’t make friends easily, he is a genuine… He was among those that graduated with d best result during our time, yanxu haka PhD dinsa yake a Uk…” Katse sa Aliyu yayi yace “Am not asking you about his life history or how intelligent he is, ina gidansu yake?” Farouq ya dinga kallonsa da tuhuma kafin yace “I don’t think i wil tel you that Aliyu” murmushi Aliyu yyi yana shafa beard dinsa.

Tun da suka shiga shopping mall din Khaleel ke kallon khadijah ganin yanda ta daure fuska, duk yanda khaleel yayi da ita ta dauki abubuwan da take bukata nuna masa ta yi bata bukatar komai, Jawaheer da twins suka dinga daukan abinda suke so a gun, khaleel dai na biye da su a baya, xagawa Jawaheer tayi gun chocolates da biscuits duk wanda yaran suka dauka ita ma sai ta dauka, khaleel dake ta kallon khadijah bayan jawahir ta bar wajen yace “Wait, wai me yasa baxa ki dau komai ba Khadijah, or did I offend u in any way plss?” Khadijah ta tabe baki ba tare da ta kallesa ba tace “To lallai ne sai na dauki abu a mall? Kuma don ban dauka ba sai ya xamanto anyi offending dina? Am not just interested” Shiru yyi yana kallonta, a hankali ya juya ya bar ta tsaye gun ya koma gun twins da jawahir, nesa da su wani mutum ne tsaye yana dauke da wata yarinya da baxata wuce shekara uku ba an mata kitso irin na yara gashinta har kusan bayanta, kusa da shi kuma wata mace ce rike da trolley tana xuba kayan da ta dauka, kallon su Shureim kawai yake ko kiftawa babu, har sai da matarsa dake gefensa tace “Barrister mu je mana” sai a sannan yyi saurin dauke idonsa kan yaran ya bi bayan matarsa, ya sake juyawa yana kallon yaran da khaleel ke rike da hannunsu har ya bar wajen ya daina ganinsu, khaleel ya biya kudin abubuwan da suka siya yana kallon khadijah da ke bakin kofar fita tana jiransu, ganin kallon da yake mata ta dauke kai da sauri dai dai lkcn da idonta ya sauka kan barrister sudais dake tahowa rike da kyakkyawar daughtern sa, matarsa na biye da shi tana rike da ledan siyayyar da suka yi, still Khadijah tayi a gun da take tsaye taji komai nata ya tsaya cak, yanda take kallonsa shi ma haka yake kallonta ko kiftawa babu har ya iso dab da ita ya sauke idonsa kasa ya mika ma security dake bakin kofar receipt din kayan da ya biya aka mayar masa sannan ya fita mall din, matarsa na biye da shi.

Khadijah ta bi sudais da kallo cikin shock sosai, fita tayi da sauri tana ci gaba da kallon sa xuciyarta na bugawa, dai dai lkcn da shi ma ya juya bai san ta fito ba suka kara hada ido yayi saurin dauke kansa, motarsa ya nufa ya bude, matar ta bude back seat ta ajiye ledan hannunta sannan ta bude seat din gaba xata shiga ta dakata da sauri tana kallonsa tace “Lahh Barrister na bar masu wayata a counter…” Bata jira cewarsa ba ta juya da sauri ta koma mall din, Sudais ya kara daga kai ya kalli khadijah, bata san lkcn da ta nufesa ba tana kallonsa ta fashe da kuka sosai cikin raunin murya tace “Why are you pretending you don’t knw me? Did I deserve that Sudais…. Me yasa kake yin kamar baka taba sanina ba” sosai hawaye ke xuba idonta, Ya kasa kallonta ya kuma kasa cewa komai ba, ganin Jiddah na fitowa mall din ya sa ya shiga motarsa ya rufe, gwiwa a sake Khadijah ta koma baya tana kallonsa ko kiftawa babu kai kana ganinta kasan she is over shock, Tun daga nesa jiddah ke kallon khadijah da tayi saurin share idonta, har ta iso tana mata wani kallo daga sama har kasa tace “Baiwar Allah, do you have any problem? Tsayuwar me kike a nan” Khadijah bata kalleta ba ta juya da sauri ta bar wajen ta koma can jikin wani mota xuciyarta na mata xafi, ta fashe da wani matsanancin kuka, me yasa ko da yaushe a cikin mall take haduwa da abinda ke mugun daga mata hankali, yau ga ta ga sudais yyi kamar bai taba sanin ta ba, me tayi masa xai mata haka, ta sulale wajen ta hade kai da gwiwa tana kuka sosai, bata yi deserving yyi mata haka ba da ya bari ko godiyar abinda yyi mata a rayuwa ta kara masa don tasan baxa ta iya biyansa ba kuma ba lallai su sake haduwa ba. Jiddah na shiga motar ta kalli sudais fuska a murtuke tace “Wacece ita Aliyu?” Buda hannu yyi alamar bai sani ba, ganin kallon da take masa yace “Kawai ce min fa tayi in ara mata waya xata yi making call, ni kuma nace bani da airtime, that’s all madam” tsaki jiddah tayi cikin bacin rai tace “Da ta fada a gabana in koya mata hankali yau wllh, irin yan iskan matan nan ne masu bin maxajen mutane a titi, banda haka ta baka ajiyar kati ne xata ce ka ara mata waya?? dear idan baka son matsala da ni wllh ka bar ko da responding wa ennan mutanen, idan xa su shekara suna ma magana kar ka ko da kalli inda suke balle ka bude baki ka basu amsa ka xama kamar deaf and dumb, domin kuwa yawancinsu da asiri suke xuwa, ni dai na gaya maka kada a fara jin kan mu kuma” “Toh” kawai Sudais yace ya tada motarsa ya bar harabar mall din tana ci gaba da mita, Khadijah taji xuciyarta ya mata nauyi ta dinga kuka ko xata samu relieve amma kamar ana kara mata ciwon da take ji, babu irin neman da khaleel bai mata cikin mall din ba amma bai ganta ba, jawahir ma sai dube dube take tana neman ta, atm dinsa ya mika ma jawahir yace “Dear gashi you pay the bill” tace “But the pin?” Fada mata yyi ya fita mall din ta bi sa da kallo a sanyaye, little Sudais na kallon jawahir yace “Anty ba mu ga Antynmu ba” jawahir ta duka tana masu murmushi tace “Yanxu Dr xai nemo mana ita cuties” daga haka ta mike ganin an xo kanta a gun biyan kudin. Tafiyar few minutes sudais yyi ya tsayar da motar, Jiddah dake kallonsa ganin yanda ya ja tsaki tace “Ya aka yi Abban Amira?” Ya d’an dafa kansa yace “Wannan matsalar dai da nace maki motar ta bani last week, I don’t knw what’s wrong with this car” tace “Yanxu baxai tashi ba kenan?” Yace “Sai wani ikon Allah, gashi ban san ko Ahmad na garage ba da na kirasa ya taho yanxu… Am just bored of this car” ta hade rai tace “Toh ni ya xa muyi yanxu ga ranan yamma” ya kalli cute angel dinsa me suna Khadijah yana kiranta da Amira ya ja hancinta ganin yanda take kallonsa da kwala kwalan idonta yace “Kar Amirata ta sha wahala bari kawai in tsayar maku da adai daita ku wuce gida ni xan taho daga baya” Jiddah tace “Wai to ka kara gwada tada motar mana, ba girman ka bane barrister a gan ka bakin titi mota ta lalace” Murmushi yyi ya bude motar ya fita ya tsayar da adai daita ya gaya masa sunan anguwar su sannan ya xaga ya bude motar yana kallon jiddah yace “Ki fito ku wuce yanxu xan taho nima in sha Allah” ta hade rai tace “Aa mu je gaba daya kawai, ai babu me satar motar idan ya so sai Ahmad yaje gida ya karbi makulli ya lallaba ya kai motar gareji” kallonta ya tsaya yi kafin yace “Plss be a good wife and humbly come down kinga na tsayar maku da d’an sahu, you don’t worry about me I will be okay sai kace ba namiji ba” da kyar ya lallaba ta ta sauka ta shiga napep din ya mika mata Amira da kayan da suka siya a supermarket, yana tsaye har napep din ya sha kwana sannan ya shiga motarsa da sauri ya tada yyi reverse ya koma mall din at high speed kamar xai tashi sama. Babu irin duban da khaleel bai ma khadijah ba a haraban Shopping complex din, har yyi give up a xaton sa gida ta wuce sai dai kuma haka kawai ya ji ransa ya baci, ya juya kenan xai koma ciki ya hangota durkushe bayan mota, da mamaki ya dinga kallonta lkci daya ya isa gabanta ya durkusa yace “Me ya faru Khadijah me kike yi a nan?” Ta kasa cewa komai sai shessheka take hawaye na sakko mata, a rikice yace “Ki min magana don Allah khadijah, me ya faru” ganin ba shiru xata yi ba ya daga ta ya nufi gun motarsa bai damu da mutanen dake kallonsu a gun ba ciki har da jawahir da ta fito da su shureim ya bude back seat ta shiga ya rufe, Sudais ya taho gun khaleel da sauri hankalinsa tashe yace “Uncle what’s wrong with my Anty” Daukan sa Khaleel yayi yana murmushi yace “She is having a headache” kokarin sauka ya shiga yi a jikinsa kamar xai yi kuka yace “Uncle ina son in xauna kusa da ita I don’t like d front” bude masa bayan motar khaleel yyi ya shiga sannan ya rufe, shi dai shureim na tsaye can kawai ya fashe da kuka, jawahir ta duka tana kallonsa da mamaki tace “Me ya faru handsome” Khaleel na ganin haka ya karasa ya daukesa shi ma ya bude back seat din ya xaunar da shi sannan ya rufe, jawahir dai na tsaye tana kallonsu ya bude mata front seat ta karaso ta shiga, ya xaga ya shiga maxaunin driver, Khadijah ta hadiye kukan da take da kyar ganin yanda yan biyunta suka rikice su ma suna kukan tana yin shiru su ma suka yi shiru, khaleel sai kallonta yake ta madubi duk ya ji ba shi da nutsuwa kamar ya jawo ta jikinsa ya lallasheta, Jawahir ma sai kallon khadijah da yaranta take, Khaleel na fita mall din da motarsa sudais ya shigo shi kuma da tasa motar, ko parking din kirki bai yi ba duk da maganar da securities din gun ke masa ya wani rikice ya dinga duba nook and cranny din wajajen yana nemanta har ciki sai da ya shiga amma babu khadijah, ya fito jikinsa a sanyaye ya hade kansa da motar sa.

Khaleel ya fara ajiye jawahir a kofar gidansu, yana lura ranta bai so ba ta bude motar ta fita da kyar ma ta dau ledan siyayyar da tayi kamar baxa ta dauka ba, ko sallama bata yi masa ba ta dai daga ma su sudais dake kallonta hannu ta wuce ciki abun ta, ya lumshe ido ya bude sannan yyi reverse ya bar layin, yana isa kofar gidansu khadijah ya bude motar ya fito sannan ya bude back seat yana kallonsu sudais da suka yi jigum kamar xa su shige jikin uwarsu, yyi murmushi yace “Toh ku fito” da taimakonsa suka sauko kasa ya basu ledojin yace su shiga ciki, Khadijah xata fito khaleel ya dakatar da ita, sudais dake lekanta yace “Uncle Anty bata sakko ba” khaleel ya shafa kansa yace “Xata sakko yanxu ku shiga ku kai ma Umma chocolates din ku ta ajiye maku” yaran suka wuce ciki suna yi suna waiwayowa, khaleel ya shiga motar yana kallonta da damuwa yace “Ki gaya min plss me ya sa ki kuka khadijah, is it me?” Girgixa masa kai tayi a sanyaye wasu hawayen na gangarowa idonta, ya kasa daurewa ya rungumeta yace “No plss I don’t want to see you cry, it hurt me, don Allah ki gaya min meye matsalar ki, me ya sa ki kuka a supermarket?” Tayi lamo jikinsa taji ta kasa kukan kuma, duk kamshin sa ya cika ta, murya can kasa yace “Khadijah” a hankali tace “Uhn” yace “Kukan me kike yi?” Ta lumshe ido cikin sanyin murya tace “Sudais” still khaleel yyi na kusan 10 seconds kafin ya dake cike da karfin hali yace “What about him?” Har lkcn idonta a lumshe tace “I saw him” dagota khaleel yyi da sauri yana kallonta at first a bit shock, sai kuma ya hade rai yace “Where?” Ta ki kallon kwayar idonsa tace “A inda muka je shopping” da kyar ta ci gaba wasu hawaye na taruwa idonta tace “He shunned me, he pretend he don’t knw me….” Kasa ci gaba tayi ta fara kuka a hankali, khaleel ya lumshe ido, jin ta a jikinsa kuma yasa tayi shiru, a hankali yace “Khadijah…” Cikin sanyin murya tace “Na’am” dai dai kunnenta yace “forget about sudais plss, forget him….” Sai kuma yyi shiru, Khadijah taji kamar an xare mata radadin da take ji a xuciya, taji ta samu relieve, hankalinta ya kwanta fiye da xaton ta, murya can kasa tace “Toh, nagode” ji yayi kamar yyi kissing dinta but yyi controlling kansa bai yi hakan ba, har lkcn idonsa a lumshe yace “I… I know I love you from day 3 of our encounter…..” Duk da yanda gaban Khadijah yyi mugun faduwa don bbu Wanda ya taba fadi mata wannan Kalmar duk tsawon rayuwarta hakan bai hanata fara tunanin me ya faru a rana ta uku da suka fara haduwa da khaleel a UK ba.

Khaleel ya dago kanta yana kallonta, tayi saurin rufe idonta, murmushi yyi murya can kasa yace “Kin tuna ko in tuna maki” dauke kanta tayi xata bude motar yace “Wait” still tayi a wajen bata yi motsi ba, yace “promise me baxa ki sake kuka a kan hanya ba, sannan you wil forget your past and face the future” shiru ta yi ba ta ce komai ba, ya kamo hannunta cikin sanyin murya yace “Khadijah” ta gyada masa kai kawai, yace “Noo, say it out” bata san lkcn da tayi murmushi ba a hankali tace “Ohk” yace “Ohk kadai” kamar bata son ya ji ta tace “I promise” yyi murmushi yace “Yauwa baby” ta turo baki tace “Tana can kayi dropping dinta a gida” wara idanuwansa yyi yace “Wai jawahir?” Khadijah ta ki dago kanta, murya can kasa yace “Ita daban ke daban…” Daga haka ya bude side dinsa ya fita ita ma ta fito yana kallonta, a hankali tana fidgeting fingers dinta tace “Thanks” bata jira cewar sa ba ta wuce cikin gida da sauri, ya bi ta da ido. Aliyu na jin alamar Farouq xai shigo parlorn ya jefar da wayarsa dake hannunsa kan kujera kusa da wanda yake, yyi concentrating kan nasa wayar dake hannunsa, Farouq yace “Toh baka taba abincin ba har ynxu Dr” Aliyu yace “I told you I am not hungry fa, ni xuwa ma xan yi in tafi yanxu” Farouq yace “So soon” mikewa Aliyu yayi yace “Sure, tun da baka da kirki” Farouq yyi murmushi yace “Ko da kai da khaleel baku fada min komai ba na dai san akwai yar tsama tsakaninku, domin kuwa kamar yanda ka min xancensa haka shi ma yyi min naka, amma bai yi requesting karban digit dinka ba ko sanin inda kake, shi yasa kai ma baxan baka na sa ba” ko Kallonsa Aliyu bai yi ba ya nufi kofa Farouq ya bi bayansa yana murmushi, Aliyu na isa gida direct sama ya tafi, har xai shiga dakinsa ya dawo ya bude kofar dakin baby, tana linke kaya ya same ta, ganinsa ta hade rai ya karasa cikin dakin, da farko rasa abun cewa yyi can kuma yyi karfin halin cewa “Ina yan gidan?” Ba tare da ta kallesa ba tace “Suna asibiti” yana kallonta yace “Who is sick?” Tace “Iklima” sai a lkcn ya tuna yana kokarin fita mumy ta kira saleem yayi driving dinsu xuwa asibiti, yace “Anyi hospitalizing dinta ne?” Baby ta gyada masa kai, yace “Su waye a asibitin?” Tace “Su mumy, mun dawo daukan abu ne da Anty Khadijah” yace “Tana ina?” Tace “Tana dakinta ina ji” fitowa yyi daga dakin har xai wuce nasa sai kuma ya bude na anty Khadijah, babu kowa a dakin ya gani, ya dinga kallon jakarta dake kan gado an xaxxage komai na ciki, karasawa yyi ya ga duk tarkacen takardu da kayan kwalliya ne sai wani kulli a fallen zani, dauka yyi yana jujjuyawa yana kallo, murya ya ji kasa kasa a bathroom, yyi still ya kasa kunne don saurare, “Wllh ban sani ba, sai bayan da aka daura auren alamomin cikin ya fara bayyana….” Aliyu yyi tiptoeing xuwa bakin kofar bayin ya jingina da bango yana jin muryar Anty Khadijah radau amma fa a hankali take maganar “Ko kafin bikin sai da na fita tsakar dare na duba ajiyar yana nan yanda yake na kan dutse” shiru ta d’an yi sai kuma tace “Aa gaskiya ta gun angon kadai ne da matsala, shi ma da bai gano cikin ba nasan da idan ya sha wannan garin da ka bada a ruwan shayi shkkn sai kuma yanda muka yi da shi to bai sha ba, to bai sha ba” da damuwa tace “Haba na kan dutse tuni fa aka cire cikin ban san meye matsalar ba tana dai can a kwance har yanxu cikinta ciwo kamar baxa tayi ba, kilan rashin sabo ne, kasan da karafuna ake cire cikin, ni dai yanxu abinda nake so shine ka taimaka ka karkato mana da hankalin shi yaron, wllh shi ke ba mu matsala” tace “Ehh Aliyu sunansa, wlh taurin kansa ya fi karfinsa, ka ladabta min shi… ka tuna wani hadi da ka taba min da dadewa shekaru masu d’an yawa na xuba masa a ruwan tea….?” Da sauri tace “Yauwa to ka kara min irinsa ta haka ne kadai xa mu samu abinda muke so, sai ya tattara ta ya tafi da ita, ita kuma ‘ya ta ka tada min kafadunta” runtse ido Aliyu yyi jin furucinta na karshe ya dinga nanata innalillahi wa inna ilai hi raji’un a xuciyarsa, Anty Khadijah tayi wani ihu tace “Dubu Dari da hamsin kuma na kan dutse??? Haba haba a dube ni domin Allah mana, yanxu kudaden wuya suke wllh, ina xan samo har dubu dari da hamsin ni ba Sana’a ba, sai fa yayata ta bani…. Da ma atm dinta na guna ne ban ki in sa ta ba, Duk fa yan kudadena sun kare ta dalilin xuwa gun ka da nake na kan dutse” ta kwantar da murya bayan wani lkci tace “Amma ka fa san nace ni baxan sake wannan harkar da kai ba kake ambatosa yanxu, sai in ce ma yayata xan je ina? Kawai duk ka bi ka wahal da mutum haba na kan dutse, wajen fa da nisa” da sauri tace “To to na ji, ko xuwa jibi xan taho, sai kuma batun yan gidan don Allah ka kara gume min bakinsu wannan karan har da wata kakarsu ta gun uba ana ce mata yaya naga xata bani ciwon kai ita ma, da yake ta fi shekara 10 a gun yar ta dake aure kasar waje to dai yanxu ta dawo duk da ba gida daya muke ba amma dai ance prevention is better den cure, ita ma a kulle min bakinta plss, sannan abu na karshe, ina yarinyar nan da na sa kayi ma Aliyu hadin nan saboda ita, wata warce nace yayata ta dauketa shekarun baya……” Da sauri tace “Yauwaaaa na kan dutse, to ina son yau dai a bincika min ita, a wani garin take yanxu, kuma ya rayuwa ta kaya da ita, ta haife cikin ne ko ta xubar? A bincika min na kan dutse” cike da confusion Aliyu ke kallon kofar bayin don bai gane komai ba a xancen ta na karshe ba, wani hadin take nufi aka yi masa, wani cikin? kuma wacece?? daga haka tayi sallama tace “Toh sai ka ji ni na wajena” Aliyu dake ta xufa yyi saurin barin bakin kofar sai dai tun bai bude kofar dakin ya fita ba ta shigo dakin, wayancewa yyi kamar shigowarsa kenan, tayi tsuru tsuru tana kallonsa, ya sunkuyar da kai yace “Ina yini” kasa amsawa tayi, just to make her comfortable yace “Yanxu na shigo baby ke ce min an kwantar da iklima ban sani ba” ta hadiye abu da kyar tace “Toh ya aka yi?” Ya isa gefen gado ya xauna a hankali yace “Anty ina son mu yi magana dake plss” tana kifta ido tace “Ina ji” yyi kasa da murya yace “Anty ki taimaka ki taya ni ba mumy hakuri, nasan tana fushi da ni, Anty abinda yasa ku ka ga na damu hada ni aure da aka yi da iklima naga ba jituwa muke ba, kuma fa kuna ganin bata jin maganar kowa gidan nan, idan ta fita sai lkcn da ta ga dama take dawowa to ta ina xan fara bata umarni ta bi a matsayina na mijinta yanxu?” Tuni hankalin Anty Khadijah ya kwanta ta kara tabbatar da shigowar sa dakin kenan bai ji wayarta ba, tace “Toh Aliyu hannunka na rubewa ka cire ka yar ne! Sannan ikliman da ka sani da ba ita ba ce yanxu, wllh wllh ta canxa fitan nan xuwa gidan kawaye da take duk ta bari, wllh ta nutsu saboda rokon Allahn da ake mata” a hankali Aliyu yace “Toh shi kenan Allah sa hakan ne mafi alkhairi” Anty Khadijah tayi mugun jin dadi ta na murmushi tace “Toh Amin, amma ka dade baka sanya ni farin ciki irin yau ba my son, Allah ya maka albarka, kuma duk abinda ya faru a da can mu yafi juna Sharrin shaidan ne” yace “Haka ne Anty, yanxu asibitin xa ku koma?” Ta girgixa kai tace “Yanxu daga nan ma kasuwa xa mu da baby kayan ciki xan siyo in farfesa mata shi ke ran ta….” Aliyu yace “Toh mu je sai in ajiye ku a kasuwan daga can in karasa asibitin dubata” Anty Khadijah ta dade bata shiga farin ciki irin na ranan ba, ta kasa yarda Aliyu ne ke mata wannan jawabin, ta dau jakarta ta bi bayan sa tana shi masa albarka. Tare da baby suka tafi kasuwar, Aliyu ya tsaya cikin mota ya jira su gama siyayyarsu ya ajiye su gida sai ya wuce asibiti kamar yanda ya ce, har lkcn he was very shock, ya kasa gaskata abubuwan da ya ji, duk jikinsa ya yi mugun sanyi, Anty Khadijah ta dinga sa ana yanka kayan ciki har na dubu shidda duk na Iklima kadai, Baby dai na tsaye kusa da ita tana kallon ikon Allah, kamar ance baby ta juya ta wara ido tana kallon wasu twins dake tafiya tare da wata dattijuwa duk tana rike da hannunsu, da sauri tace “Innalillahi Anty kalli yaran can” da sauri Anty Khadijah ta juya ita ma idonta ya sauka kan yaran ko kiftawa bata yi, Baby tace “Anty don Allah da wa suka maki kama?” Anty Khadijah ta share wani xufa tana ci gaba da kallon yaran tunani kala kala a ranta, kamar daga sama suka ji ance baxawara??? Duk suka juya da sauri, kyauta suka gani tsaye cikin shiga ta alfarma gun mai kayan miya tana rike da haba baki bude tana kallon Anty Khadijah, Baby tayi wani kara xata tafi ta rungumeta da gudu Anty Khadijah ta fixgota, kyauta na rike da haba har sannan tace “Ikon Allah su baxawara ashe rai kan ga rai? Ana nan ana xawarcin gidan mutane ko anyi aure?” Anty Khadijah da kamannin ta suka canxa tayi kan kyauta kamar xaki kan kace me ta cakumota tana kunduma mata xagi tace “Ni kike kira baxawara don kaza kazan ki, a ina kika taba sani na” dambe ta fara yi da Kyauta da ta xage ita ma lkci daya sai gashi ta na na Anty Khadijah ta da kasa ta dinga duka tana tula mata kasa a fuska mutane suka taru kansu amma kyauta taki saketa dukarta take kamar an aikota tana tula mata kasa a fuska da baki, Baby da ta rude ta tafi da gudu ta kira Aliyu dake mota, Cikin masu kallon fadan har da Nanny da ta ja yan biyun hannunta suka tafi wani rumfa suka tsaya kallon ikon Allah, da kyar aka janye kyauta kan Anty Khadijah da jini ke ta dalala a hancinta da baki, Kyauta ta kunduma mata wani mugun xagi tace “In kin cika yar halak cikin uwar ki da uban ki mu hadu a ba wani shege gobe mu da sa daga inda aka rabamu, axxaluma yar uwar shaidan kawai” daga haka kyauta ta bar wajen tana cewa “Alhmdllh na san inda na dosa a rayuwa yanxu, ke kam a cin arxiki xa ki kare kina rabe gidan mutane” Aliyu ya bi ta da kallo baki bude, Da kyar aka daga Anty Khadijah dake kunduma ma kyauta xagi bayan ta ga ta tafi, Baby ta kama hannunta suka nufi gun mota da sauri ganin yanda ake kallonsu, naman da basu amsa ba kenan duk da ta bada kudi, Aliyu dai ya kasa motsi inda yake, a hankali ya juya xai bar wajen ya ji ance “Uncleee” ya juya da sauri idonsa ya sauka kan twins dake wani gefe a tsaye Nanny kuma na siyan abu a shago bayan taga karshen damben, ya wara ido ya buda hannunsa shureim ya taho da gudu ya daga sa sama ya rungumesa yace “What are you doing here sweetheart?” Shureim ya washe fararen kananun hakoransa yace “We came with nanny and Anty to get something, Ga Nanny a cikin shop Anty kuma tana cikin mota tana jiran mu” kallon sudais Aliyu yyi ya ga yana tsaye ne yana kallonsu, a hankali ya ajiye shureim yana rike da hannunsa ya isa gun sudais haka nan yaji gabansa na faduwa ya duka dai dai height dinsa yace “How are you angel?” Sudais ya sauke idonsa yace “Am good” daga haka ya shiga shagon da Nanny take ciki, Aliyu ya bi sa da kallo, shureim yace “Uncle what are you doing here?” Aliyu yace “I came to get something also, why is ur twin behaving strangely, and he looks sick…” Fitowa sudais yyi don ba can cikin shagon ya shiga ba yana kallon Aliyu yace “Because I don’t like you, stay away from me and my brother” Kallonsa Aliyu yake ko kiftawa babu, Shureim ya tura sudais yace “You are mean….”

Back to top button