Hausa NovelsSakayyah Book 2 Complete

Sakayyah Book 2 Page 18

Sponsored Links

 

*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH book 2… Page 18*

 

        Na

*Aysha Aliyu Garkuwa*

 

 

*WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*

 

_Ina kuke Ma’aurata masu sha’awar ganin sun zama taurari
kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen
gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau’ikan sirrin sahihan
magungunan ma’aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma ta
dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki
ki zamto tauraruwa a idanun mijinki…Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_
:_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin
ilanwaddihi, Gumbar da ba’a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin
al’khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin Maliƙi mai masifar
ƙarfi da matse mace, ka masin Daɗi har Maɗigan Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace
mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni’ima yanada abubuwa
masu kyau haɗinsa, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa
jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni’imantaccen damshi,
Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi
sadidan, da dai sauransu…Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu’umin ƙamshi
wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba…._  _Shin ko kina da labarin Miskilinci da
ƙasaitar Rayyan  Naaan amma lokaci ɗaya
ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face
sirrinkan gyara da kuma shu’uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu
Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar
bawa_

_Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta
zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)…Tabbas Mahmud ya zamto
zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi
da budurwa(Namiji  Baya Kaɗan) ko kinsan
hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu’uman humran Aysha
Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke
dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta
yake tamkar budurwa ‘yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da
Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta
da kuma Ma’aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba’a iya rubutun littafi
ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma’aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun
abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 09097853276 muna iya
tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah ‘yar uwa
idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci…._          

      🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo.
sayan na gari maida kuɗi gida,

 

Ummi kuwa cikin sanyi jiki da raunin zuciya take kallonsa
sam, jikinta bai faɗa mata cewa wannan ɗan ta bane, amma zuciyarta yaƙi
amincewa da hakan.

    Juyawa tayi ta
kalli Asma’u da hawaye ke cigaba da zuba daga idanunta, kai ta girgiza kana ta
maida idanunta kan Moddibo dake cewa.

“Wallahi Ummi wannan ba Jameel ɗinki bane. Nima kaina na
gamsu da komai nashi na *J* ne amma ɗabi’unsa ba irin na *J* bane sam sun
bambanta tako wacce siga ta hali da ɗabi’a”.

A hankali Dr Jameel dake durƙushe gaban Ummi ya kalli
Modibbo tare da rausayar da ƙwayar idanunta acikin nasa alamar kada ka zubar
min da mutuncina agaban idonta.

 

Numfashi Moddibo ya fesar fahimtar kallon Dr Jameel ɗin
yamasa shi yasa yayi shiru…

Innayi, Asiya, Aunty Ruƙayya, Aunty Hajara da duk suke tsaye
daga gefe suna kallon ikon Allah da Al’ajabi na tsanananin kamannin Dr Jameel
da marigayi M Jameel.

Zama Ummi ta gyara tare da jan dogon numfashi kana ta sauƙe
cikin sanyi tace.

“Shikenan na gamsu Moddibo, na yarda da kai saboda sanin kai
nane,  baka taɓa yimin ƙarya ba, kuma
koda wasa kake min baka min ƙarya aciki, dan haka na yarda na gamsu wannan ba
Jameeluna bane”.

Ta ƙare mgnar tare da lumshe idanunta hawaye masu zafin
gaske suka zubo kana ta cigaba da faɗin.

“Amma wannan kamanni da yawa yake.

Kuma Alhamdulillah na godewa Allah daya da wannan Rahma da
yayi min na nuna min mai kamannin Fuskar
Jameeluna har muryarsa irin na Jameeluna da komai nashi fa”.

 

Dr Jameel kuwa cikin yanayin buɗe war ido, da kuma gskyar
zuciyarsa ya kalli Ummi duk da kuwa yana cikin rauni da tausayinsu, a hankali
ya fesar da numfashi tare da maida idanunsa kan Asma’u kana Yace.

“Ummi”.

Da sauri Ummi ta ware idanunta dake cike taf da hawaye jin
ya kirata da Ummi.

 Sake langwaɓar da
kansa yayi idanunsa na kan Ummi ya cigaba da faɗin.

“Ummi da zan samu a bani Asma’u in Aura wlh ina so.

Kinga shikenan sai na zame miki ɗanki Jameel  In maye maki gurbin shi”.

Ware idanu Ummi tayi tarexa kallonsa cikin mmkin mgnar shi
da tazo mata a bazata, sai kuma taji murmushi ya suɓuce mata batare da tace
komai ba ta miƙe ta shiga bedroom..

 

Asmau kuwa, wani irin fitinennen sanyi kalamashi suka sakar
mata, so take ta yunƙu ta mike a guje ta bar wurin amman ta gaza hanan, sabida
yadda gaba ɗaya guiwowinta suka sake.

 

Aunty Hajara, Aunty Ruƙayya, Asiya atare suka saki murmushi
kana suka miƙe cike da gamsuwan cewa ba Jameel bane kawai dai kamanni ne, domin
da Jameel ne bazai ce zai Auri Asma’u ba wannan kalmar kaɗai ta gamsar dasu
cewa ba Jameel bane, domin idan M. Jameel ne babu ta yanda za’a yi yace zai
Auri ƴar uwarsa ƙanwarsa da suka kasance uwa ɗaya kana suka sha nono ɗaya, da
wannan

 gamsassun hujjoji
suka bi bayan Ummi zuwa bedroom.

Innayi kam murmushi tayi cike da gamsuwa cewa lalle wannan
ba M Jameel bane kamanni ne kawai, fuskarta ɗauke da amintaccen murmushi ta
kalli Dr Jameel tare da faɗin.

“Toh an baka”.

Saurin kallonta Moddibo yayi babu walwala atare dashi yace.

“Kece me bada Asma’u koni ne mai bada ita?”.

Still Innayi na murmushi tace.

“Kaine Mai bada ita amma kaima ai ina da iko akan ka”.

Kai ya jinjina tare da faɗin.

“Eh kina da iko akaina Innayi, amma ai shi Aure ɗan bincike
ne sai na bincikesa nasan ingancin sa tukunna kafin na bashi Asma’u”.

Asma’u kuwa tun lokacin da yace yana sonta data daskare
zaune, sai yanzu taji tayi azamar miƙewa sabida jin kuzarinta ya dawo,

Da gudu ta miƙe tabar wajen yayin da Khausar ta miƙe tabi
bayanta.

Cikin lumshe idanu Moddibo yabi Khausar da kallo har ta ɓacewa
kallonsa idonsa na kanta wani sassayyan numfashi ya  fesar tare da lumshe ƙwayar idanunsa.

 

Zakariyya kuwa tunda suka shigo idonshi na kan Aseeya  gaba ɗaya ya gaza ɗauke idanshi a kanta.

Ibraahim kuwa shiru yayi yana kallonsu kawai.

 

Ganin duk sun watse yasa Innayi maida kallonta kan Moddibo
kana tace.

“Bismillah kuje kuci abinci naga kamar abinci kuke ci na
tada daku”.

Kai suka gyaɗa tare dayi mata sallama kana suka tafi.

 

Suna shiga Falon Dr Jameel ya kamo hannun Moddibo tare da
langwaɓar da kai kana cikin sanyin murya da neman alfarma yace.

“Na roƙeka da girman Allah Moddibo kada ka faɗi wani abu da
zai zubar min da kima da daraja a idon Ummi”.

Kallonsa kawai Moddibo, Ibraahim, Zakariyya sukeyi Shi kuwa
cikin sanyi da neman alfarma ya cigaba da cewa.

“Na lura tana kallona da kima da daraja kuma Wallahi har
cikin raina ina ƙaunar Asma’u kuma Aurenta zanyi”.

Cikin sauri Moddibo ya tari numfashinsa ta hanyar cewa.

“Gaskiya ayanayin kan nan dana lura da kai. Wallahi bazan
baka Asma’u ba, Asma’u nine nan mai bada ita,Tana da mahaifi, Lallai Mahaifinta
shine zai bada ita.

Amma bisa yaƙinina zai bada ita. Ni kuma bani da yaƙini akan
ka”.

Sai kuma ya ɗan furzar da iska mai zafi yana tuno yanayin
munanan halayyar Dr Jameel kai ya girgiza kana yace.

“Baka da tsarkakan da zan baka tsarka-kakkiyar yarinya
saboda Asma’u tsarka-kakkiyar ce.

Kallonsa kawai Dr Jameel keyi cikin rauni da nadama ɗabi’unsa
da yakega zasu kasance mihsi barazana daga mallakar ƴarinyar da yakeji in bai
setaba zai zauce.

 

Moddibo kuwa cikin yaƙini da gaskiya ya cigaba da faɗin.

“Saboda Faɗin Allah ma ɗaukakin sarki ne, cewa. Mazinaci
baya Aure sai Mazinaciya ƴar uwarsa Asma’u kuwa tsarka-kakkiya ce ba Mazinaciya
bace kai kuma kafi kowa sanin kanka”.

 

Ahankali Zakariyya da tausayin Dr Jameel ya gama cikawa
zuciya ya kamo hannun Moddibo  suka zauna
kana cikin nutsuwa yace.

“Kayi haƙuri Moddibo ai abu da yawa yana zama sanadin
shiryuwar mutum kada kayi mamaki Auren Asma’u ya kasance hanyar shiryuwan Dr
Jameel”.

Kai Ibraahim dake gefe ya jinjina tare da cewa.

“Hakane Yah Aleey tunda har yace yana sonta da dai ashige
masa gaba ba ba mamaki wannan abin da yake rashin mata ne”.

 

Dr Jameel kuwa cikin gaskiya da gaskiya ya kalli Moddibo
kana yace.

“Wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! In dai za’a bani Asma’u Ni
dai nayi al’ƙawari zan rabu da duk wata ƴa mace”.

Ganin gaskiya acikin ƙwayar idanunsa yasa Moddibo fesar da
numfashi tare da cewa.

“Shikenan ka fara rabuwa dasu tukunna idan na gamsu ka rabu
dasu.

 Ni kuma zan baka ita
In dai har na gamsu”.

Cike da farin ciki Dr Jameel ya gyaɗa kai kana yace.

“Ni kuma nayi maka al’ƙawari daga yau daga yanzu na rabu
dasu”.

Ya ida maganar tare da zaro wayarsa kana ya shiga contact
tare da blooking ɗin Number duk ƴan matan sa kana ya nunawa Moddibo.

Murmushi Moddibo yayi kana yace.

“Toh Allah yasa kayi iya deleting ɗin su acikin Mind ɗin ka
da zuciyarka kamar yanda kayi awayarka”.

Asanyaye Dr Jameel ya furta.

“In sha Allahu babu kowa a raina”.

 

Juyowa Modibbo yayi ya kalli Ibarahim dake miƙa mishi
woyoyinsa,

Murmushi Ibraahim yayi tare cewa.

“Tun da safe Abualeey ya bani su yace amman in bari sai dare
in baki”.

Murmushi Modibbo yayi tare da cewa.

“Ummm yayi kyau”.

Cikin wasa Ibraahim yace.

“Nasa maka caji ne dan naga sun mutu sabida kiraye-karen da
akayi ta maka”.

Miƙewa yayi tare da cewa.

“Yoh ba dole su mutuba moko guda”.

 

“Eh amman ai yanzu duk a cike suke”.

Cewar Ibraahim.

Kai Modibbo ya gyaɗa mishi yana mai kunna woyoyin nasa.

 

Acan ɓangaren su Khausar kuwa tunda suka shiga bedroom take
sakin murmushi idanunta akan Asma’u da duk tayi zuru-zuru da ita kana tace.

“Asma’u Wallahi wannan ba Yan Jameel bane”.

Kallon mamaki Asma’u tayi mata Still hawaye na bin fuskarta
tace.

“Kamar ya zakice ba Yah Jameel bane”.

Hannunta Khausar ta riƙe tare da cewa.

“Asma’u  jikina ya faɗa
min ba Yah Jameel bane.

Ki sani da Yah Jameel ne ko cutan hauka yayi ba zai kalleki
yace yana sonki amatsayin matar Aure ba”.

Sai kuma ta sake damƙe hannun Asma’u acikin nata cikin son
tabbar mata da gaskiya ta cigaba da cewa.

“Ki tuna fa Nono ɗaya kuka sha mahaifiya ɗaya ce ta haife ku
fa wallahi Asma’u ba Yah Jameel bane, kawai ni inajin farin ciki araina ne.
Alhamdulillah bazan rayu Ni kaɗai aƙasar nan ba zan rayu tare dake, zai ɗakko
min ke ya dawo min dake ƙasar nan mu rayu tare”.

 

Zazzafan Ajiyar zuciya Asma’u ta sauƙe idanunta akan Khausar
tace.

“Wallahi nifa Khausar har yanzu ban gamsu cewa ba Yah Jameel
bane”

Kai Khausar ta girgiza tare da cewa.

“Wallahi Asma’u ba Yah Jameel bane ya za’a yi Yah Jameel
yace yana sonki zai Aure ki, Asma’u kiyi tunani mana hakan bazai taɓa faruwa
bafa”.

Haka dai sukaci gaba da tattaunawa.

A daren wannan ranan haka suka cika da alhini da al’ajabi…

 

Acan Side ɗin Didi kuwa zaune suke da ƙannenta da kuma
Yayyanta da suka zo.

Baki ɗaya hirar tasu akan Khausar ce suna yabon kyawu da
kuma haibar da Khausar tayi kowa na faɗin albarkanci bakinsa.

A wannan ranan haka duka ahalin suka kwana cikin yalwataccen
farin ciki.

 

Washe gari aka shirya taro na alfarma wanda baki ɗaya manyan
Fada da kuma manyan Masarautar Morocco ne taro ne wanda yafi na jiya sai dai
wannan taro ne na maza zalla saboda an gabatar da Moddibo amatsayin Sarki mai
jiran gado kana ana gabatar dashi a baki ɗaya idon Fada sosai Moddibo yayi
jawabi daya ratsa zukatan mutane kasancewar shi aka bawa Microphone ya rufe
taron da addu’a.

Al’amarin da ya gigita jama’ar masarautar jin yanda ya dinga
zazzago addu’oi yana rerawa cikin zazzaƙan muryansa.

Wani irin farin cikine ya mamaye zuciyar Abualeey ya
tabbatar da cewa ɗan sa ya samu kyakkyawan tarbiyya da jigon da zai iya mulkar
masarautar Mouley.

Cikin jin daɗi yake kallonsa,

 

Shi kuwa Modibbo addu’oin daya ta jerawa na yayi dai-dai da
lokacin da aka kira Sallar Azahar.

 

 Limamin masallacin
Fadan dake zaune gefe wanda tsohone tukuf ya tsufa sosai bisa alamu kuma sa
yanayin jinya na tsufa.

Cikin jin dadin ya sauke A tare da karɓan Microphone ɗin
kana yayi jawabin cewa,

 Shi ya fahimci wannan
Yariman yana da cikekken ilimin addini dan haka daga yau ya sauƙa daga kan
karagata na limanci shine zai cigaba da limanci masallacin masarautar su
kasancewar tsufar da ya cimasan da kuma sanyin da muryasa keyi wacce wasu
lokutan bata isarwa mabiyan jam’inshi.

 koda Modibbo yaji
haka  yayi ƙoƙarin maida tayin da limamin
yayi mishi amman ina yaƙi sabida da gskyarsa sufa tacin mishi.

Sai kallon Modibbo yake cikin so da

Amintaccen murmushi mai cike da yarda da yaƙini kamilin
dattijon yake bin Modibbo da Addu’o’i kana ya ɗaura da cewa.

Hakan za’a yi kuwa domin Modibbo ya cancanta sai dai ko in
baka kusa ko kayi tafiya ko wani abu dai to sai in jamu.

Daga haka taron ya tashi da yaƙin cewa an bar mishi
Limanci…

 

 Aranar Modibbo ne
yaja limancin sallar Azahar, wanda baki ɗaya sautin zazzaƙan muryarsa ya cika
masarautar.

Wanda baki ɗaya al’umma cikin Masarauta ke yaba zaƙin
muryansa.

  

Bayan an idar da sallar Azahar Direct sashen Didi Ibraahim
ya nufa cike da farin ciki ya zauna gefen Didi tare da riƙe hannunta kana yace.

“Didi kinsan waya ja mana jam’i?”.

Kai ta girgiza tare da faɗin.

“A’a sai ka faɗa?”.

Cike da matsanancin farin ciki yace.

“Wallahi Yah Aleey ne Kai Didi wlh Innayi ta gama mana
dukkan gata na duniya”.

Fuska ɗauke da yalwataccen farin ciki Didi tace.

“Kai Alhamdulillah”.

 

A ɓanƙaren su Modibbo kuwa, Sheiyk Jabeer ne tare Modibbo
sai Jabeer bin Jabeer cikin kulawa Modibbo yace.

“Sheiykh yau yau kuma zaku koma?”.

Gyaran murya Sheikh Jabeer yayi tare da cewa.

“In Allah kuwa yanzuma zamu tafi airport dama kafin mu tafi
masallaci nayi sallama da kowa na Fada harma da Didinku munyi sallama.

Tafiyar ce ta gaggawa ta sameni zan koma ne saboda gobe da
yamma muna da zama da ƙungiyar *MI YETTI ALLAH* Akam matsalolin Garkuwa da
mutane ƙasarmu ke fuskanta.

Toh yadda ake maida akalar zargin kan cewa Fulani ne keda
alhaƙin hakanne yasa ƙungiyar *TABITAL POOLAKU* shiga mgnar da keɓance ƴaƴanta
Fulani da wonkesu daga zargin da ake musu domin suma fulanin basu tsiraba,
anayi musu wannan zalumcin su a ƙara da kashesu ma”.

Cikin sauƙe nannauyan numfashi Modibbo yace.

“Gsky wannan ƙudurine mai kyau, domin abune daya addabi
ƙasarmu, kaga wala Allah cikin haka a gano masu aikata hakan”.

Cikin kulawa Sheiykh yace.

“In sha Allah kuwa, domin fulanin zamu wakilta mu naɗasu
aikin bamu rahoton duk abinda ke gudana cikin dajukan za mu rabasu ko wanne
state na Nigeria”.

Sai kuma suka kalli Jabeer bin Jabeer dake cewa.

“Musamman Zamfara Sokoto Katsina abun yafi tsamari a can”.

Moddibo ne ya ɗan fesar da numfashin mai zafi kana yace.

“Ni kuwa ina so a ruɓanya masu binciken Taraba yankin
Gembulan domin anayi musu illa sosai, a sanadin su na rasa J na”.

Sheykh ne ya ɗan kali agogo dake hannunsa tare da cewa.

“Eh nima da batun Jameel da kayi mana bayani na kuduri
aniyar in sha Allah, sai na gano waɗanda suka yi masa wannan kisan gillan, in
ban mantaba kace min akwai wacce taga mota bibiyarsu kuma har ta ɗauki number’n
ko?”. Da sauri Modibbo yace.

“Eh Khausar ce”.

Cikin samun cikekken yaƙini kan binciken Sheykh yace.

“Toh ba matsala idan kun nitsu, ka nemi min cikekken bayanin
a wurinta, sai ka tura min komai, in Allah ya yarda jininshi bazai tafi a
banzaba”.

Kai ya jinjina tare da cewa.

“In sha Allah kuwa”.

Daga nan sukayi sallama, Abualeey da kanshi yayiwa surkin
nashi da ƙanin matarsa rakiya zuwa Airport, bai dawoba saida jirginsu ya tashi.

 

Acan ɓangaren su Khausar kuwa zaune take kan sallayar tun
bayan data idar da sallar Azahar bata motsa ba.

Innayi dake gefe ta saki murmushi tare da faɗin.

“Kai Alhamdulillah naji daɗin nagartar Moddibo ina farin
ciki da hakan”.

Kai Ummi  dake gefenta
ta jinjina kana tace.

“Ai dai kam Alhamdulillah”.

Daga haka suka cigaba da hira wanda mafi yawa akan Moddibo
ne…

 

Acan ɓangaren Hajiya Bunayya kuwa zaune take a bedroom ita
kaɗai yayin da Asiya ke toilet tana wanka.

Hajiya Bunayya kuwa wayane maƙale a kunnenta  tana magana da Amina dogon tsaki taja tare da
faɗin.

“Ke dai Amina bari wallahi dana san haka daular nan take da
mu mukayi sihiri kika Auri Moddibo”.

Amina dake zaune acikin wani ƙaton falo na al’farma a Abuja
tayi murmushi tare da faɗin.

“Umma kada ki damu nan ma wallahi muna cikin daula kinga
gidan da aka kama nin kuwa, dan dai baki zo kinga gidan da aka kawo ni bane
gidane mai masifar kyau na nunawa sa’afa”.

Sai kuma ta juya idanunta tare da kallon mashshurin falon
nata kana ta cigaba da cewa.

“Kinga manyan falona guda biyu da 3bedroom atsakiyar birnin
Abuja fa muke inda muke ma ai alhamdulillah kuma kin manta muma zamu tafi
Indi’a ne kwanan nan da Uncle Naseer”.

Dogon tsaki Hajiya Bunayya taja kana tace.

“Ke bakiga daular dake cikin nan bane shiyasa kike faɗin
hakan”.

Murmushi Amina tayi tare da faɗin.

“Umma kema fa bakisan daular da nake ciki bane ki kwantar da
hankalin ki in kin dawo kinzo zaki sha mmaki”.

Cikin gaskata wa Amina ta cigaba da kwantar wa da
mahaifiyarta hankali kana ta ɗaura da faɗin.

“Umma kada fa ki manta muma Indi’a zamu tare kuma Indi’a ma
ai tafi Morocco sanuwa da suna”.

Kai Hajiya Bunayya ta girgiza kana tace.

“Hmmm Amina kenan ta yaro kyau take bata ƙarko, abine da
baki gani ba,  duk labarin da zan baki
bazaki gane bane irin cigaba, da nasara, wadatar da Khausar ta riska awannan
masarauta ya wuce zatonki”.

Sai kuma ta ha ɗiye wani yawu mai masifar ɗaci kana ta
cigaba da cewa.

“Bazaki taɓa fahimtar abinda nake faɗa ba har sai idonki ya
gane miki.

Yoh Naseer da ko Sarkin Tasha Uban sa bai taɓa mulka ba, ina
za’a haɗashi da Modibbo, kina sane da cewa Khausar kuwa mijinta shine Yarima
mai jiran gadon mulkin Ƙasar Morocco gaba ɗayanta fa, sannan kuma shine babban ɗa
Namiji awajen Mahaifinsa”.

Amina dake zaune ta dafe ƙirji cike da ƙyashi da hasadar jin
matsayi da kuma nasaran da Khausar ta samu.

Hajiya Bunayya kam cikin ƙunan zuciya da tarin hassada ta
cigaba da faɗin.

“Wannan tsinanniyar tsohuwar Innayi ta cucemu data ɓoye mana
wannan al’amari nasarar Modibbo da mun san da wannan nasaba da yake dashi haka
ai wallahi ko zan tafi tsirara ne wlh sai kin Auri Moddibo”.

 

Zazzafan Ajiyar zuciya Amina ta sauƙe kana tace.

“Umma ke kam kada ki damu”.

Kai Hajiya Bunayya ta girgiza ji take kamar ta ɗaura hannu
aka tayi ta zunduma ihu cikin damuwa tace.

“Ya bazan damu ba Amina dole in damu gaba ɗaya hankalina ya
tashi baƙin ba, yanda ban samu ba suma su rasa Wallahi, duk yanda zanyi Amina
nayi miki al’ƙawarin sai na raba Auren Khausar da Moddibo ko ana Hamaza ha
mata.

 In dai dawo Nigeria
ne kawai yafi wuya”.

Cikin sauƙe numfashi Amina tace.

“Gaskiya dai nima yanda kike zuzuta wannan cigaban nata, da
dai ta wuceni gwara a kaso Auren nata ta dawo gida ta zauna”.

 Yamutse fuska tayi
tare da gyara zamanta kana ta cigaba da cewa.

“Ƴar banza agola kawai tazo tafi ƴaƴan masu gida nasara”.

Ƙwaffa Hajiya Bunayya tayi kana tace.

“Ke dai bari”.

Dai dai lokacin da Asiya ta fito daga wanka kallonta tayi
tare da girgiza kai cikin yanayin sanyinta tace.

“Hmmmm Allah ya kyauta”.

Alalace ta kalleta tare da faɗin.

“Toh shegiya mai baƙin hali meye?

Ƴar masu matacciyar zuciya da bakisan abinda yake miki ciwo
ba sai wani yaƙe baki kike kina murmushi adole kinga nasarar wani”.

 

Tana zama gaban dreesing mirror tace.

“Umma idan har bakayi baƙin ciki da nasarar wani ba kaima
Allah zai kawo maka naka narasan”.

Ahantare Hajiya Bunayya ta harareta tare da cewa.

“Dalla can rufe min baki,Ki ɓace min daga ɗaki”.

Kai ta gyaɗa tare da ficewa daga dakin kasancewar tasa
kayanta kai tsaye ɗakin su Khausar ta nufa…

 

   Acan ɓangaren
Moddibo kuwa bayan sun Sheykh Jabeer sun tafi. suka cigaba da gaisawa da Manyan
baƙi.

Har aka kira La’asar bayan an idar da sallar La’asar baki ɗaya
baƙi suka tafi anci ansha wasu irin abinci na alfarma aka dafa wanda ma’aikatan
manyan restaurant aka ɗebo sukayi girkin gargajiya dana zamani domin afita
kunya.

 kuma Alhamdulillah
kwalliya ta biya kuɗin sabulu.

 

Moddibo kuwa gaba ɗaya wunin yau ɗin duk abinda yake Khausar
ce ke faɗo masa arai da Zaran ya lumshe Idanunsa zai tuna sanda ya rungumeta
yana budewa kuwa lokacin da yake wanke mata hannu acikin Madarane ke masa gizo
duk wani abu da yake dauriya kawai yake.

Yayin da wani ɓangare na zuciyarsa ya tafi ga halin da
Asma’u ke ciki kasancewar har suma tayi a daren jiya kana ko bayan barinsa
sashen da sukenma bata cikin nutsuwarta, tun safe yaso zuwa dubata amma bai
samu ba saboda hidindimu da suka yi masa yawa…

 

Acan Falon su Khausar kuwa suka zaune Jakadiya ta shigo
bayan sun gaisa ta kalli Innayi tare da cewa.

“Innayi Didi na buƙatar ku baki ɗaya asashenta amma banda
Khausar sannan abarta da mutum ɗaya kada ta zauna ita kaɗai”.

Kai Innayi ta jinjina tare da cewa.

“Toh ba damuwa sai abarta da Hajja Nana”.

Ta ida maganar tare da miƙewa ta nufi ƙofa yayin da Hajiya
Bunayya,Aunty Ruƙayya, Aunty Hawwa, Aunty Hajara Asiya, Dije suka mara mata
baya.

 Kai tsaye suka nufi
sashen Didi bakinsu ɗauke da sallama suka shiga tangamemen Falon suna shiga
idanunsu ya sauƙa akan Wasu Mashahuran Akwatuna set biyar ko wannen kalansa da
ban.

 

Lalla Khadijah ne ta ɗaga kai tare da kallon Innayi kana
tace.

“Ku shigo ku zauna mana”.

Murmushi Innayi tayi kana suka shiga suka zazzauna akan
lumtsa-lumtsan kujerun na al’farma.

Ɗaya daga cikinsu ne Yayar Didi wacce ta kasance ƴar farinsu
ce Mai suna Afreen wacce kira da Ashshe matsawa tayi suka gaisa kana cikin
sakin fuska tace.

“Toh Alhamdulillah ga lefe nan mun gama haɗawa na.

 Amaryanmu so mun kira
kune kuzo ku gani in Sha Allah za’a bawa Hadimai su kaishi Side ɗin da zasu
zauna ne”.

Cike da tarin farin ciki Innayi ke kallon Set ɗin akwatunan
kana tace.

“Masha Allah Alhamdulillah”.

Ummi kuwa cikin yanayin farin ciki tace.

“Kai masha Allah wannan duka lefene!?”.

 

Lokaci ɗaya Hajiya Bunayya ta nemi ƴar nutsuwarta ta rasa
atake yanayin fuskarta ya rikiɗe afili zuwa hassada da ƙyashi ta kasa ɓoye
baƙin cikinta.

Cikin fusata taja wani dogon tsaki tare da sauƙe numfashi
wanda yaja hankali da yawa daga cikin mutanen falon suka kalleta.

Asiya dake gefenta tayi saurin dafa kafaɗarta ganin yanda
ake kallonsu yasa tace.

“Umma lafiya?”.

Kai ta gyaɗa tare da yamutse fuska kana tace.

“Ƙirjina ne yake ciwo sai to kareni yake”.

A yatsine Lalla Hafsat ta kalleta tare da cewa.

“Ok ba matsala bari na kira Dr Jameel yazo ya duba ki da
jiki sai ya baki magani”.

Ta ƙare mgnar a yaysine dan har ga Allah matar bata konta
mata a raiba….

 

 

 

Littafin SAKAYYAH dai na kuɗi ki biya ki karanta cikin
Aminci.

 

 

Leave a Reply

Back to top button