Hausa NovelsNoor Al Hayat Hausa Novel

Noor Al Hayat 68

Sponsored Links

Kallon direction din daki yayi kafin ya kalli Shureim yace “Je ka dauko min wayar Anty a daki” yaron na wucewa ya mike ya dawo gefenta ya xauna ta d’an matsa ta dauke kai, a hankali yana kallonta yace “Don Allah kiyi hakuri Khadijah, I wasn’t happy with what happened also, and… Plss forgive Jawahir for the sake of….” Katse sa tayi tace “Toh ni nace na riketa a rai ne? Not at all, don bata min komai ba” Ya lumshe ido ya bude yace “Don Allah kiyi hakuri Khadijah” tace “Wllh nayi, Kuma komai ya wuce a wajena, ita ma xan sameta idan na taba mata wani abun ta yafe min” Shiru yayi bai iya yace komai ba, mikewa tayi xai rikota tayi saurin barin wajen tana hararansa tace “Meye haka?” Kallonta kawai yake, ta tabe baki tace “Am coming now” daga haka ta wuce ciki sai ga ta ta fito da kati ta iso kusa da shi ta mika masa, Bai karba ba yace “Meye wannan?” Tace “Ka amsa ka duba mana” da kamar baxai karba ba sai kuma ya karba yana kallon katin, a hankali ya dago kai yana kallonta, ta rungume hannayenta tace “Xa ka samu xuwa kuwa duk da baka gayyaceni naka ba?” Ya sauke idonsa bayan few seconds yace “Why not” ta koma ta xauna a hankali tace “Toh nagode” Jujjuya card din kawai yake bai ce komai ba, can ya dago yana kallonta cikin sanyin murya yace “Ur happiness is mine khadijah, since this will make u happy, this is what u want for ur self, I am wishing you the best in it, Allah ya kai mu lokacin yasa ayi a sa’a” kasa cewa komai tayi tana kallonsa, yace “But I am happy for a reason, soon xan maki abinda xai sa ki farin ciki na har abada in sha Allah” daga haka ya mike yace “Kice ma Umma na tafi” har ya nufi kofa ya fita bata samu bakin magana ba, ta sauke idonta a hankali taji xuciyarta ya mata rauni. Tun ana biki saura kwana shidda Umma da Nanny suka fara shirye shirye ba ji ba gani, da kanta ta kai ma Kawun Khadijah katin bikin, kusan guda ashirin ta tafi da domin ya ba sauran yan uwansu can, Bata tsaya ta sauraresa ba balle matan sa da yanxu suka xama abun tausayi don miji ba shi da shi, ga yayansu duk aure ya mutu ana xaune gida, duk da bakaken maganganun da suka dinga jifanta da shi ita dai bata tanka su ba ta fita, wai don ma basu san da kaddarar da ta afka ma Khadijah ba kenan wannan, gidansu sadeeq ta shiga ta ba Mahaifiyarsa ma katin bikin sannan ta juyo xuwa kano. Tun da bikin ya gabato kullum sai baby ta xo gidan da close frnds dinta uku ganin da gaske khadijah bata da kawaye kamar yanda ta ce, tare suke shirin komai da xuwa kasuwa, babu wanda bai yaba kayan lefen da Sudais ya hada ma khadijah ba, as in abun ba a cewa komai, ya kashe mata kudi ba na wasa ba, Umma ta xuba kudi me yawa ta sa aka fara gyara khadijah, xuwa yanxu kam khadijah ta kara xama wani silent har da rama, hakan bai wani damu Umma ba sanin ko wace Amarya na experiencing haka, tun da bikin ya karato Sudais bai wani cika xuwa ba sai dai su yi waya, hakan yasa hankalin khadijah ya kwanta don ko ya xo bata jin ma xata iya fita gun sa. Mumy ta gama hada gudunmawarta gaba daya tana kallon Aliyu dake xaune yana danna waya dakin nata tace “Abuturrab ko kai xaka taimaka ka kai don Allah” sai a sannan ya dago yana kallonta, Mumy ta xauna gefen gado tace “Na fa ce ka cire ma kanka damuwa Abuturrab, you are never destined to be married to khadijah, ba kadarraku ba kenan kuma baka isa ka ja da Allah ba, ga mijinta nan ka gani so plss take her off ur mind, ka samu mace kayi aure…” Ya sauke idonsa kasa cikin sanyin murya yace “But I have never for once complained Mum, kina gani har kiranta nayi na mata Allah ya sanya alkhairi” Mumy tace “You are not complaining but ur mind is, gashi nan duk ka fita hayyacin ka, ga shi nan kana neman jefa kanka cikin wani hali, dama mutum na auren matar da ba tasa ba Aliyu? Why not behave like a good Muslims and be happy with Allah’s plan?” Wani murmushi yayi yace “I am not complaining Mumy, am telling you the fact, but the thing is that don Allah ki taimaka ki mata magana ta bar min yaron, tayi hakuri ta bar sa gun ma, anytime she wants to see him xa a iya dinga kai mata shi, ko kuma yaje ya dinga hutu gunta, I know baxan iya rabata da Dan ta ba, but I just want to save him some humiliations, har duniya ta nade a gidan nan babu mai masa gori, babu mai masa kallon a child gotten out of wedlock, sannan babu mai takura masa, in da tayi aure fa, ko xai samu abubuwan da nayi mentioning a nan wllh it won’t be 100% don haka plss Mumy ki nusar da ita ta bar sa gidan nan” Mumy ta sauke ajiyar xuciya a hankali ta kasa cewa komai. Duk yanda Mumy ta so fadi ma khadijah sakon Aliyu da taje gidan kasawa tayi saboda kunya, she don’t even know where to start from, haka ta koma gida daga karshe, da Aliyu ya bukaci feedback din khadijah, ta kwantar da murya tace “Abuturrab ka bari kawai bayan bikin, it will look as if we are not happy with her marriage, xa a ga kamar mun so kan mu da yawa, kaga bayan biki sai ayi masu bayani, Ina ga xai fi” yace “Toh shkkn mum, nagode” tace “Hope ka ci abinci” yace “Sure mum” daga haka ya mike ya nufi kofa ta bi sa da kallo cike da tausayinsa har ya fita, she know he is just trying his best to be okay, Kuma taji dadin yanda yake harkokinsa duk da kana ganinsa kasan akwai damuwa sosai tattare da shi, addu’a tayi masa na cewar Allah ya fiddo masa da mace soon shi ma yayi auren nan. Ana gobe daurin aure aka xo har gida aka ma Khadijah gyaran gashi da lalle, all this while baby da kawayenta na tare da ita, Yanxu kam shirun nata ya fara isan Umma ga rashin cin abinci duk tayi mugun rama, Khadijah na son sanin ko Khaleel ya koma ko bai koma ba amma bata san ta ya ba, har lkcn maganar sa na karshe ya tsaya mata, Wai xai mata abinda xai sa ta farin ciki na har abada to meye wannan bayan xuwa gobe tana gidan Sudais, she will like talking to him before tomorrow amma ta kasa kiransa duk da ta ma kashe wayar kar Sudais ya kirata, a haka ta kwanta ranan cike da tunaninsa, tun daga ranan da ta fara ganinsa har xuwa yanxu, tayi wani murmushi ta gyara kwanciyar ta ta lumshe ido tana fatan bacci ya dauketa ko xata samu saukin ciwon kan da take ji. Washegari tun da Sudais ya tashi yake ta kiran layin khadijah a kashe gashi ba shi da number baby, shi kuma baxai iya kiran Umma ba, yana xaune gefen gado misalin karfe takwas Jiddah ta shigo dakin, tsaye tayi bakin kofa tana kallonsa tana murmushi tace “Happy married life in Advance Aliyu” ya dauke kai daga kallonta bai ce komai ba, wani murmushin ta kuma yi ta juya ta fita dakin, mikewa yayi ya fita parlor jin kamar kanninsa da few relatives da suka xo tun shekaranjiya sun fito parlorn, Kamar yanda yayi xata haka ne suna kitchen suna nema ma kansu abinda xa su ci don tun da suka xo ko ruwa jiddah bata taba debowa ta kawo masu ba, sai ma idan sun girka ta tafi ta diba ta ci, komawa daki yayi ya kwanta don sai bayan an sauko juma’ah daurin auren. Tun da khadijah ta tashi take kukan da bata san dalilinsa ba, baby tayi lallashin har ta gaji, Umma tun da ta tambayeta kukan me take taki bata amsa ta fita harkanta, gida ya cika fal da abokan arxikin Umma da yan uwanta da mutan garinsu, Babu Wanda xai ce ba ita ta haifi khadijah ba, yau dai Nanny har da yan uwanta a gidan, Mumy ma tun safe ta xo gidan da kawayenta biyu, Hajiyarsu Sadeeq ma da safe ta shigo gidan, da kyar khadijah ta mike ta shirya bayan Umma ta mata Jan ido taki ko da shafa kwalli a ido. Karfe sha biyu wata kawar Umma ta fita bayan gidan kiran Umma, ba a dau lkci ba Umma ta shigo parlorn don ce mata tayi wasu baki sun shigo kuma cewa suka yi uwar amarya suke nema, kallon Jiddah da kawayenta su kusan biyar kawai Umma keyi don bata taba ganinsu ba, Jiddah na murmushi tace “Ke ce uwar Amaryar Mama” Umma tace “Nice daga Ina haka?” Jiddah tace “Kawayenta ne mu mun taba islamiyya daya mama” Da mamaki Umma ke kallonsu don Khadijah bata taba bata labarin tayi kawaye a islamiyya ba, sannan ga wani irin daurin dankwali na ture ka ga fitina da suka yi gaba daya, sun cakare cikin ankon super wax gaba daya, ita jiddah irin make up din da tayi sai ka rantse ita ce Amaryar, Umma tayi karfin halin cewa “Toh sannun ku da xuwa” Jiddah na murmushi har da ritsinawa tace “Mun gode mama, Toh ina amaryar take” Umma ta sa yar wata kawarta ta kai su dakin da su khadijah su ke, yarinyar na gaba suna biye da ita har suka shiga dakin, khadijah na xaune tare da Baby da kawayenta sai jujjuya wainar shinkafar da Mumy ta kawo mata ta ci ganin bata ci komai ba tun safe take, Su kuma su baby suna ta make up tunda ita har rantsuwa tayi baxa tayi ba, tun da su jiddah suka shigo Khadijah da su baby ke kallonsu, Jiddah na murmushi tana kallon baby tace “Amarya Sannu….” Baby na masu wani kallo ta nuna Khadijah tace “You are mistaken, ga amaryar can xaune” daga haka ta dauke kai ta ci gaba da shafa powder dinta don ko kadan ji tayi gaba daya jiddah da kawayen nata basu mata ba, Khadijah dai sai kallonsu take ko kiftawa babu, Jiddah ta iso kusa da ita tace “Ke ce Khadijah, Amira, Kuma Ummu Shureim koh?” Khadijah taji gabanta yayi mugun faduwa bata dai ce komai ba tana ta kallonta, Jiddah tayi wani dariya tana kallonta da kyau tace “Ke ce ke Shirin shigowa gidan Barrister a matsayin matarsa ta biyu Koh?” Khadijah ta hadiya abu da kyar still ta kasa ce mata komai, xuwa lkcn kam ta fara dago wacece ke tsaye gabanta ko tantama babu matar Barrister ce, Baby ta mike tace “Ke malama ance maki gidan radio ne nan wannan tambayoyin da kike jefo mata?” Jiddah ta mata wani matsiyacin kallo ta daga mata hannu tace “Dakata Hajiya ban yi da ke ba, ki xama yar kallo a nan, ja gefe ki tsaya kawai” daga haka ta mayar da dubanta kan Khadijah tana mata mugun kallo tace “Wato tsaurin idon ki yakai har ki rasa wanda xaki makale ma wa ya aure ki sai mijina Barrister Aliyu Sudais?” Tuni hawaye ya kawo idon Khadijah duk jikinta yayi sanyi, Jiddah ta fashe da dariya ta juya tana kallon kawayenta tana nuna Khadijah tace “Don Allah wacece xaune nan?” Kamar hadin baki suka ce “karuwa” Jiddah tace “Da ta yi me?” A tare suka kara cewa “Cikin shege….” Tuni duk mutanen dake parlor suka yo daki da sauri jin hayaniya a daki, Jiddah na kallon Khadijah da kyau tace “Toh don kaza kazan ki in har kin haifi cikin uwar ki da ubanki ki yi kuskuren shigowa gidan Aliyu yau, ke don fitsara ki gama yawan karuwancin a gidan aiki ki haifi tagwaye sannan daga mijina ya taimake ki sai ki makale masa, daga taimako???? Har yana ikirarin tausayin ki da yake kadai yasa xai aure ki ba wani abu ba, kin xata badan uban tausayin da Allah ya xuba masa ba xai ce xai aure ki bayan yasan ke wacece? Toh bari ki ji, babu komai naki da ban sani ba, duk sirrin ki na tafin hannuna, babu abinda Aliyu ya boye min game da ke, tunda mijina ne shi din baya komai sai yayi shawara da ni, da farko na xata abun arxiki ne bayan ya bani labarin ki na amince ya aure ki don ya rufa ma ke da shegun ki asiri amma kawai daga baya tun baki shigo gidan ba na fara ganin canji, wato kin fara shanye min miji sai yanda kika yi da shi daga na amince masa ya aure ki ya rufa maki asiri koh? To wllh kinyi kadan, yau xan ga ta yanda xa ayi auren nan da kaxa kaxan ki sai dai ki koma ki ci gaba da karuwancin….” Baby bata san lkcn da ta mike ta cakumota ba ta makure ta….. Kan kace me fada ya kauraye tsakanin jiddah, baby, da kawayen jiddah, frnds din baby su ma suka shiga, da kyar mutanen da suka yi mutuwar tsaye parlorn suka raba fadan, Khadijah ta hade kai da gwiwa jin numfashinta na sama, ko kwakkwaran motsi ta kasa daga gun da take xaune, Jiddah ba irin xagi, cin mutunci da gorin da bata mata ba kawayenta na taya ta, har Umma sai da suka xaga, Baby ma bakinta bai mutu ba, da kyar aka fidda su dakin ana Allah wadaran Jiddah, sai a sannan hawaye ya dinga xubo ma baby taji tausayin Khadijah sosai duk jikinta yayi sanyi, Umma kam xaunawa tayi ita ma hawayen na sakko mata ta kasa cewa komai, Mumy kanta tsaye tayi ta rasa abin cewa duk jikinta yayi sanyi, Wata kawar Umma ta durkusa ta dago kan Khadijah a hankali cike da tausayinta, hawaye ne ke xuba idonta kamar an bude pampo, Baby ta durkusa kusa da ita ita ma hawayen na xubo mata ta rasa abinda xata ce mata, Khadijah ta kamo hannunta cikin rawar murya tace “is it my fault that I was raped baby? Is it my fault that I am an orphan, is it my fault that I had kids out of wedlock? Dama maraici….” kasa ci gaba tayi ta fashe da kuka sosai tana girgixa kai a raunane tace “Alhamdulillah for my fate… irin tawa kaddarar kenan kuma na amsa hannu bibbiyu, Amma me yasa mutane baxa su yi considering dina ba, ni ban so ma kai na haka ba, Allah ne ya kaddara min, but ya xan yi baby, dole in gode masa, ban taba karuwanci ba amma sun ce min karuwa, ban san Sudais baxai iya rike min sirrina ba he betrayed….” Mikewa Baby tayi ta dau wayar Khadijah ta fice daga dakin, Ta kunna ta shiga neman layin Sudais, Bata yi wahalan ganin number ba don Barrister tayi masa save as, tana dialing ba a dau lkci ba ya dauka cike da damuwa yace “Why did you switch off ur phone Amira…” Baby ta katse sa a xuciyarta na tafarfasa tace “Malam dama ka san baka iya rike sirri ba ka nace sai ka auri Khadijah??? dama kai din mijin ta ce ne sai yanda mahaukaciyar jahilar matar ka tayi da kai?” Kasa cewa komai Sudais yyi da farko don gaba daya he was lost, can cike da karfin hali yace “Wacece wannan?” A mugun fusace tace “Ba Lallai ka ji wacece ba, wllh ka ci amanar Khadijah, ka xalunce ta, and am advicing you ka janye batun auren ta kaje jahilar matar ka ta ishe ka, Kuma sai Allah ya saka mata” tana kai wa nan ta fashe da kuka sosai taci gaba “Naga ba ita ta ta xabar ma kanta wannan kaddarar ba har xaka xaunar da warce xa su xauna a matsayin kishiyoyi ka tsara mata komai na rayuwarta daga farko har karshe ta xo har gidan biki ta mata tonan silili ta gaya mata son ranta, tayi mata cin mutunci da cin fuska, tayi mata gori” katse wayar Sudais yyi kansa na juya masa ya mike daga xaunen da yake ya fito parlor, ya kusa minti sha biyar tsaye sai ga jiddah da kawayenta sun shigo parlorn, ya taka har gabanta ya sauke mata tagwayen mari, yana kallonta da jajayen idanuwansa yace “Na sake ki saki daya jiddah”

Back to top button