Hausa NovelsNoor Al Hayat Hausa Novel

Noor Al Hayat 67

Sponsored Links

Sudais yace “Uhm is it necessary?” Mikewa khadijah tayi ta dau mayafinta tace “Toh baxa ku gaisa da Umma ba?” Yace “Sai nayi shawara da ke? Even the day before yesterday ai na xo, gaisheta tare ma muka je da Little Meerah” Murmushi khadijah tayi tace “Ohk then gani fitowa” daga haka ta katse wayar ta kalli Baby tace “Baby mu je ki raka ni sai ku gaisa dama kin ce baki san sa ba” Baby tace “A’a je ki dawo ke dai, just extend my greetings” Khadijah ta bata fuska tace “Don Allah ki taso mu je plss” Baby tayi yar dariya tace “Toh naji” tashi tayi ta dau gyalenta suka fita dakin, sai da Khadijah ta fara shiga dakin Umma ta sanar mata xasu fita gun Sudais sannan suka fita, Yana tsaye jikin mota sanye cikin kananun kaya ya rungume hannunsa, tun da suka fito yake kallon khadijah, Baby ce ta fara sallama tace “Ina yini?” Sai a sannan ya dubeta da murmushi ya amsa sallamarta yace “How are you?” Tace “Lafiya Alhmdllh, ya aiki?” Yace “Mun gode Allah” daga haka ta juya tace “Toh Iman sai kin shigo” tana fadin haka ta shiga cikin gida, khadijah ta dawo gefensa ta tsaya tace “Welcome My Barrister” ya wara ido a hankali yace “Really?” Boye fuskarta tayi tana yar dariya, yace “Kun xo lafiya dear?” Tana kallonsa tace “Alhmdllh” yace “Ashe dama kina da kawaye?” Ta xaro ido tace “Uhm Baby ce fa kanwar Aliyu” Shiru yayi yana kallonta, can yace “Tana xuwa nan kenan?” Khadijah ta girgixa kai tace “A’a tun bayan rasuwar takwaran ka sai yau ta sake dawowa” yace “How did she know u are back, ko kuna waya ne?” Tace “A’a fa, nasan Aliyu ne xai ce mata mun dawo” yana kallonta a hankali yace “Ya aka yi Aliyu yasan kin dawo” shiru tayi ta kasa kallonsa, bayan few seconds ta dago kai tace “Sorry I didn’t tell you shi yayi accompanying din mu jiya, coz Shureim was sick” Ya langwabar da kai yace “Da gaske?” Bata ce komai ba, ya d’an yi murmushi shi ma bai ce komai ba, tayi breaking silence din tace “We where very close da baby, farkon xuwa na gidan su ne kadai muka samu problem, after that she was kind to me, she took me just as her sister, tana so na sosai, nima kuma ina sonta, and I really want us to be frnds now tunda bani da kawaye” a sanyaye ta kare maganar, Yana gyada kai yace “That’s nyc then…” Tace “Me yasa baka xo da little Amira ba?” Yace “Ba daga gida nake ba” Khadijah tace “Ohk, Toh ko ruwa ban kawo maka ba, shud I bring some?” yace “Daga eatry fa nake yanxu haka” ta d’an buda ido tace “Kai da xaka koma gida kuma meye na xuwa eatry da daddare Barrister” murmushi yayi yana shafa beard dinsa bai ce komai ba, can yace “Shureim fa?” Shiru ta d’an yi, ta dago tana kallonsa tace “Yayi bacci” ya wara ido yace “So early? duk da nasan ba gaskiya kika fada ba” xaro ido tayi tana kallonsa, yayi murmushin sa mai kyau yace “Yea, sai ki ce min Aliyu ya tafi da shi” da mamaki tace “How did you knw” yana murmushi har sannan yace “From ur facial expression, and don’t forget my field….” Yar dariya tayi tace “Kai My Barrister” yace “Sure My Meerah” ta boye fuskarta a tafin hannunta tace “Gobe ai xai dawo in sha Allah” yace “Alryt then, bari in tafi Amira, gobe xan dawo mu yi hira sosai am exhausted gaba daya yau” tace “Ayya, kana komawa gida kayi wanka ka kwanta you will feel relieve” Yana murmushi yace “Toh Amaryata” juya masa baya tayi tace “Uhn ni dai bana so” a hankali yace “Xa ki so ne ma ai” Bude motarsa yayi ya dauko leda ya dawo gabanta yana kallonta ya mika mata yace “Though Shureim na kawo ma amma tunda kin min rowar ganinsa gashi sai ke da meye ma kika ce sunanta…” Khadijah tayi murmushi tace “Sunan mu daya, Amma baby ake ce mata ita” ya wara ido yace “Ashe Mami na ce ita ma” a hankali khadijah ta gyada masa kai, yace “Toh ina gaisheta specially, she’s having a great name, and naga suna kama da yayan nata ma” Khadijah ta amshi ledan tace “Toh xata ji mun gode sosai” murya can kasa yace “Noo thanks sweetheart” sunkuyar da kanta tayi, yace “Gobe xan kawo maki IV in case you have people to give” tace “Toh Allah ya kai mu” yace “Ameen dear, let me get going” daga haka ya bude maxaunin driver ya shiga, ta koma baya tana kallonsa, sai da yayi reverse ta daga masa hannu ya sakar mata murmushi sannan ya ja motar ya wuce, juyawa tayi a hankali ta koma cikin gida. Washegari karfe goma baby tace xata koma gida, duk khadijah ta ji ba dadi, babu yanda bata yi da ita ta bari sai da yamma ba tace inaa ita lokacin xata wuce, Khadijah tace “Toh ki kira yayanki ya dawo min da yarona nima” dariya sosai baby tayi tace “Sai kace baki da number sa, ke ki kirasa mana” Khadijah ta dau wayarta ta shiga kiran Aliyu, yana dagawa tace “Ka dawo min da yarona tunda wucewa baby ma xata yi yanxu” yace “Koh?” Tace “Eh mana, nace ta bari sai da yamma ta ki” kamar xata yi kuka ta kare maganar, Aliyu yayi murmushi a hankali yace “Toh bata wayar” Mika ma Baby wayar tayi, baby ta amsa tana dariya ta kai kunne yace “Baby ki bari da yamma” tace “Toh yayanmu an gama” daga haka ta ba khadijah wayarta, kashewa khadijah tayi tana murmushi tace “Me yace?” Baby ta harareta tace “Ba don halin ki ba xan kai yamma” sosai khadijah taji dadi tace “Yauwa ko ke fa, kinga kafin nan Barrister ya kawo katin da yace sai in baki ki kai ma su Mumy” shiru baby tayi tana kallonta, khadijah ta wara ido tace “Ko bai yi ba hakan?” A hankali Baby tace “Ke dai ki kai da kan ki xai fi” Khadijah tace “Toh shkkn ko ran Friday sai Sudais din ya kai ni in kai” Baby tace “Khadijah Ina son maki wani magana amma Allah yasa baxai bata maki rai ba” Khadijah na kallonta tace “Ina ji baby” Baby ta kamo hannunta tayi kasa da murya cikin sanyi tace “Khadijah me yasa kika ki amincewa Ya Aliyu ya aure ki bayan ya nuna yana son yin haka, kin ga akwai advantage din hakan biyu xuwa uku, na farko shureim… Idan yau ace Ya Aliyu xaki aura har duniya ta tashi ba lallai yaron yasan irin kaddarar da ta afka maku ba da yanda aka yi aka samesa sai in ku kuka fada masa, he will neva ever know wllh, idan wani gidan kika yi aure fa? Wllh komin daren dadewa watarana sai ya sani, sai ya san matsayinsa khadijah, na biyu Aliyu baxai taba maki gori a rayuwa ba idan ma yayi wlh yasan kansa yayi ma, kunya a kansa, balle ma wllh baxai yi ma don yasan shi ya cuce ki, sannan kin ga babu wani matsala da xaki samu gun Mumy, da mu yan uwansa, Anty khadijah ce problem dama, toh tana can har yanxu asibiti sai karaya ya dauko warkewa abu ya dawo baya, ga cikin shege jikinta har ya fito, don haka ta kanta take yanxu, kowa yaje sai tace ya yafe mata har masu gadi da driver… toh wanda xa ki aura fa khadijah? Though nasan Barrister yasan everything about you amma khadijah ki kyale namiji wllh ko ba directly ba watarana sai ya maki gorin nan barin ma wannan da kika ce yana da mata, ko cikin bacin rai wataran sai ya jefe ki da bakar magana irin ta gori ba tare da kilan yasan yayi hakan ba, kawai ta dalilin bacin rai, balle a je ga yan uwansa da relatives, sannan uwa uba matarsa, yanxu duniyar da wuya wllh a rike maka sirrin ka, khadijah ki duba wannan xancen nawa plss ba wai don ina son ki da yayana bane amma it’s better ku rufa ma kan ku asiri ku hadu ku rike sirrin ku, kin ga sai ki kara haifo mana wasu kyawawan yan biyun……” Da xolaya ta kare xancen, Khadijah dake ta kallon kofa ta xame hannunta daga nata a hankali tace “I really like you baby, Ina ji da ke har raina saboda kin min halaccin da baxan taba mancewa da ke ba, plss baby kada ki sa in fara jin haushin ki in ga kamar ke ba masoyiyata bace, baby mu bar wannan xancen plss bana so, Kuma kar ki sake min irinsa” A hankali baby tace “Toh Allah ya baki hakuri” Khadijah tace “Ameen, So baki gaya min level da kike ba yanxu, Kuma yaushe xa mu sha naki bikin?” Da murmushi ta kare maganar tana kallonta. Bayan la’asar Sudais ya kira Khadijah yace yana waje, da kyar ta lallaba baby da har ta kira Aliyu ya xo ya dauketa ta gama shiryawa suka fita waje gun sa, yau ma yana tsaye jikin motar suka fito, Baby ce ta fara gaishesa ya amsa da fara’a yace “Lafiya lau Mamina ashe baki koma ba” Baby tace “Ehh wllh ina jiran yayana ne” Sudais yace “Alryt, ya gidan” tace “Lafiya lau” Kallon Khadijah yayi yace “Ya aka yi Madam?” Tayi murmushi tace “Lafiya lau, ya aiki?” Yace “Alhmdllh… Ya Ummar mu” khadijah tace “Tana ciki” juyawa Baby tayi tace “Toh sai anjima xan shiga ciki” yace “Alryt nagode da gaisuwa” daga haka ta wuce ciki, Sudais ya bude motar ya fiddo invitation card ya mika mata yace “Here dear” amsa tayi tace “Nagode, Ina Amira fa” yace “Tana gida” mota ce tayi parking kusa da na Sudais khadijah ta dinga kallon motar har Aliyu ya fito, Shureim ma ya fito ta daya side din, da gudu ya taho ya rungume Sudais yace “Unclee…” Sudais ya daga sa sama yana pecking goshin sa yace “Evening son, where are you coming from?” Ya wara ido yace “From my kind Mama’s home” Sudais yace “That’s good” karasowa Aliyu yayi gabansa ya mika masa hannu yana murmushi yyi masa sallama, Sudais ya basa hannun shi ma suka gaisa sannan ya kalli khadijah yace “Good evening” tace “Evening ya su Mumy?” Yace “Suna gaishe ki” kallon Shureim yayi yace “Go inside kace baby ta fito ina jiranta yanxu” Shureim ya shiga gidan Aliyu yayi ma Sudais sallama ya koma motarsa yana kallonsu ta ciki, Sudais bai sake cewa komai ba yana jingine da mota har baby ta fito, ta iso gun khadijah tana murmushi tace “Khadijah ni xan koma, ki taya ni yi ma Umma godiya idan kin koma ciki, nagode sosai” Khadijah tace “Toh nima nagode Baby ki gaida min mumy sai na kawo card din, and I will give you a call later” Baby tace “Alryt dear” sallama tayi ma Sudais ta wuce motar Aliyu ta shiga ya tada motar ya bar layin. Ranar Friday kamar yanda khadijah tace ma Baby misalin karfe sha daya ta shirya taje gidansu tare da Shureim don Sudais yace yana da wani case ranan. A hankali ta murda kofar parlorn ta ji a bude, ta shiga hade da sallama, Aliyu ne xaune parlorn tare da Salim yana operating laptop, ya daga kai yana kallonsu, ta sauke idonta ta karaso cikin parlorn, ta gaida Salim sannan ta kalli Aliyu tace “Ina kwana” Yana xaunar da Shureim dake gaishesa kusa da shi yace “Lafiya lau ya gida” tace “Alhmdllh, Mumy fa?” Ya d’an yi shiru kafin yace “Bata nan, ki jira ta xasu dawo yanxu” tace “Baby fa?” Yace “Tare suka fita” tace “Toh bari in baka sako ka ba Mumy” Ta bude jakarta ta fiddo IV din tana kallonsa ta mika masa, karba yayi idanuwansa a kan content din Invitation card din, a hankali ya dago yana kallonta ko kiftawa babu, bata sake yarda ta kallesa ba tace “You help me deliver it to her plss” daga haka ta sauko da Shureim dake xaune kusa da shi ta juya ta fita daga parlorn yana ce mata shi ta bar sa a gidan, ganin yanda Aliyu yyi still wajen, Salim ya karbi card din don ganin na menene. Gida khadijah ta koma tana ta ma Shureim dake mata kukan bata bar sa gidan ba masifa, tana sauka kan napep din tace “Don uwar ka ba sai ka koma ba tunda gidan dangin uwar ka ne can din” Ta bude jaka ta ba mai napep kudinsa ta wuce ciki abun ta, ya bi ta yana kuka kamar xai tsaga gidan, Ta fi seconds goma tana kallon takalman dake bakin kofar parlorn, can ta bude kofar ta shiga a hankali, Khaleel ta gani xaune parlorn Umma ma na xaune, ta wani hade rai bata sake kallon parlorn ba xata wuce daki Umma tace “Khadijah” tsayawa tayi ta ki juyowa, Jin Umma bata ce komai ba ta juyo a hankali tace “Na’am Umma” Hada ido suka yi da shi, ta sauke idonta tace “Ina yini?” Yace “Lafiya lau” Tana kallon Umma tace “Mun dawo Umma, ba mu sameta ba ma” Umma na kallon Shureim da ya makale bakin kofa yana kuka tace “Shi kuma me ya samesa?” Harara ta balla masa tace “Au kuka kake min har yanxu, nace ka koma gidan koh” a hankali yace “I don’t know the road” Umma tace “Me yasa baki bar sa ba” Tace “Mumy fa bata nan, Baby ma bata nan, to ina yake son in bar sa” yana kallonta yace “Wajen Uncle dina mana” Khaleel ya juya yana kallonsa yace “Come over dear” sai a sannan Shureim ya gansa ya taho gun sa da sauri yace “Uncle when did you come?” Khaleel ya xaunar da shi gefensa yace “Today” Murmushi yayi yace “Uncle kun xo da Anty na?” Khaleel ya shafa kansa yace “Sure” tabe baki khadijah tayi ta juya ta wuce daki abun ta, Tana xaune gefen gado tana danna wayarta Umma ta shigo dakin, ta xauna gefen gadon ita ma a hankali tace “Ashe abinda ya faru kenan Khadijah?” Kasa kallonta Khadijah tayi lkci daya hawaye ya kawo idonta, sai a sannan ta dinga jin xafin maganganun da Jawahir tayi mata, maganganun suka dinga dawo mata sabo, Umma tace “Ni ban ce kiyi kuka ba, ki share idon ki kije ki samesa ki ji abinda xai gaya maki” cikin rawar murya tace “Ni baxan je ba Umma” Umma tace “Ban isa da ke ba kenan” goge idonta ta dinga yi a hankali ta mike ta dau gyalenta ta fita a sanyaye, tun da ta fito yake kallonta har ta karaso ta xauna kujera ba tare da ta yarda ta kallesa ba, a hankali taji yace “Khadijah” sai a sannan ta daga kai tana kallonsa.

✨ *NOOR-AL-HAYAT*✨

Back to top button