Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa NovelsHausa Novels

Arubuce Ta Ke 3

Sponsored Links

Koda ta shigan bata zauna ba kamar yadda anty deena tace tayi sauri,ta sameta tana yankawa momma albasa,sai zabga gumi taje gami da hawaye,duk da cewa kitchen din kitchen ne irin na zamani,da ya wadatu da iska da manyan windows,dukka a qoqarin momman na koya mata girki,kada ta tashi kamar widad,wadda bata cas bare as a gidan,abinda ya damu wasu cikin gidan,yake kuma basu haushi sosai,suna gajun gatan da ummu ke nunawa widad din yayi yawan da ya kamata ta rageshi ta sanwa wasu cikin jikokinta.

Budewa Aafiya kayan tayi tana cewa

“Zabi duk abinda kikeso a ciki” kanta ta leqa cikin ledar tana cewa

“Ummm,yar gatan ummu,inda nice nace mata ta siyon kayan nan qi zatayi,sai tace naje na tambayi yayuna maza”

“Yaaya mahfood ne nima ya kawomin” daga kai tayi ta kalli widad,dududu itama Aafiyan ba zata wuce sa’ar widad din ba,saidai ta danfi widad din girman jiki kadan

“To me yasa ba zakiyi amfani dasu ba?” Tura baki tayi tana tsuke fuska

“Banaso,ni bana son sa,banason ana min zancensa,ki dauka anty deena zata aikeni” ido ta fidda

“Yaushe tazo?”

“Yanzu” saita ajjiye wuqar tana zura hannu a ledar,ta zabi abinda takeso tana cewa

“Aiko na godde wlh,bari nayi sauri na gamawa momma aikinta na fito” tana dan lila ledar ta fice abinta ba tare data tsaya sauraronta ba,ta samu anty deena a falo,ta bata leda tace ta kaiwa anty madinan,ta amsa ta fice da dan guntun gudunta.

Ta dan samu yaran sassa sassan gidan da dan dama a sashen anty madinan,kasancewarta mai fara’a haba haba dasu da jan kowa a jiki,kowa nata ne,hakanan kowa yana jin dadin xama dasu,bayan sa’anninta masu kamar shekarunta data samu,harda yayyensu da ake dab da bikinsu,kuma suna tare da anty madinan,da alama akwai abinda take koya musu,sauran sa’annin nata suna daga gefe sun buda tasu chamber din.

Bayan ta miqa mata ledar sai ta kalleta

“To wannan dayar kuma fa?”

“Kayan kwalliya ne na kawowa su rafi’ah”

“A ina kika samu kayan kwalliya masu yawa haka?” Basma cikin ‘yammatan dake shirin amarcewa ta fada tana dubanta bayan ta dago kanta daga danna wayar da takeyi,kanta tsaye ba kwana kwana ko damuwa tace

“Yaa mahfood ne ya kawomin”

“Shine kuma zaki rabar?” Anty madina ta tambayeta tana bada hankalinta sosai a kanta,kamar zata saki kuka tace

“Banaso anty wallahi,ni banaso”

“Barta don Allah ta rabar,miqomin na zabi nawa” basman ta sake fadi tana miqa hannu,ba wani damuwa tattare da ita ta miqa mata ledar ta qara gaba tana cewa

“Anty basma idan kun gama su na’ima zasu zaba” anty madina data bita da kallo tana kallon zallar quruciya ta saki ajiyar zuciya

“Allah ya zaba abinda yafi zama alkhairi,baaba mahfood dai kam to”

“Uhmmm,wai laifin widad kuke gani?,ni nafi ganin laifin baaba mahfood din ai,kamar maye,yarinya tun tana ‘yar tamilo kake faman mata hidima,jikinka da aljihunka basu huta ba,ta fara wayo ta nuna baka so basai ka haqura ba,dui gidan ita dayace ‘ya?,ko ita kadai ce jika?” Kai anty madina ta girgiza

“A’ah fa basma,har yanzu widad akwai quruciya tattare da ita,ai ba’asan maci tuwo ba sai miya ta qare”

“Uhmmm,anty madina,yarinyar nan fa daurin gindi ta samu,Allah kuwa,kuma sai yaushe?,bayan mu kadai ne muka haura zuwa SS,mu dinma gashi SS one kawai aure ya tashi,bare su da jikinsu da alama mai saurin girma ne,Allah yasa su gama JS ma”

“Allah ya shiga lamarin” anty madina ta amsa mata

“To Ameen”basman ta fada tana maida kanta ciki ledar,don tuni marwa ummee da nujood suka gama zabar nasu,anty madina nata musu tsiyan girma ya fadi,raqumi ya shanye ruwan ‘yan tsaki,su da za’a kawo musu akwati me zasuyi da toshin qanwarsu.

Widad kam bata sake bi takan kayan ba,a nan suka gama gantalewa,duka ta rabar,dan abinda yayi saura ya gangarar dashi anan wajen anty madina,tayi komawarta sassansu.

Sanda ta koma tuni abbanta ya tafi,sai ummu kawai

“Ina kikakai kayan?” Ta tambayeta tana tallafe da kuncinta tana dubanta,maimakon ta amsa saita narke fuska,ta kuma shige cikin kujera abinta ta lafe taba mus mus da baki,juyin duniya ta gaya mata inda takai kayan taqi,dole ga qyaleta,tasan indai cikin gidanne zata ji.

Tun tana zaman likimo har bacci yayi awon gaba da ita,bata tashi ba sai kusan azahar,sanda latifa ta kammala abincin rana,ta kuma tattaro panties da undies din widad din zata wanke.

Sai datayi sallar azahar kamar yadda ummu ta horar da ita,ta karba abinci,saita zagaya baya inda latifan ke mata wankin,ta zauna tana ci suna hira da latifan…

***********

Kamar kowacce safiya a ranakun makaranta,school bus din gidan ke tattara kan duka yaran gidan zuwa makaranta,wanda kusan yawancinsu makaranta daya suke zuwa,wadanda kuma suke mabanbantan makarantu sai ta miqa su sannan ta dawo gidan zuwa lokuttan tashinsu.

Daga can sassan ummu widad ce zaune saman kujera,sanye da sabbin uniform dinta kamar yadda komai nata a ranar yake sabo a matsayinta na dalibar da ta shiga secondry school a ranar,ummu na zaune daga qasan carfet hannunta riqe da plate tana miqawa widad din plantain din ciki

“Maza maza kici kafin ‘yan azalzalar nan su biyo sawunki,idan ba haka nayi miki ba haka zaki tafi,yanzun latifa zata kawo miki lunch box dinki” fuska a nake a kuma sakalce take duban ummu

“Wallahi na qoshi ummu,ya isa haka”

“A’ah,qarashe wannan dai” ta fada cikin nuna kulawa,hakanan ba don taso ba ta daga cup din hannunta dake cike da tea tana shanye ragowar na ciki,dai dai lokacin basma ta shigo,sanye take da kayan gida,kasancewar ita din a yanzun sai daina zuwa,saboda kusantowar bikinsu,bawai don sun gama bane,haka al’adar gidan take,alhajin salim mai fata tsoho mai ran qarfe,kaka kuma uba ga ahalin gidan wannan sbine tsarin da ya dora dukka yara da jikokinsa,mutane da yawa ‘yan bani na iya da kuma ‘yan gaza gani kance

‘Gidan me fata ai da wuri suke aurar da yaransu,da sun ga mai kudi sai su cire yarinya daga makaranta,basa ko gamawa,don sunga suna samun masu danshi ne,suma masu kudin da shegen kwadayi,suna ganin kyawawan mata sai su rude’ duk da wannan jita jita na dawo musu kunne amma sunyi banza da zantukan mutane,abu daya tsoho kuma dattijon ya sani shine,mutuncin mace dakin mijinta,hakanan duk wadda tayi katari da samun mijin dake da ra’ayin karatu tana ci gaba da karatunta ne cikin dakin mijinta.

“Goyon kaaka,sai a fito ko?,kin tsaida mutane kina bata musu lokaci” ta fadi tana harararta,ganin yadda ummu ta zauna dafa’an tana bata abinci kamar wata yarinyar goye,waiwayowa ummun tayi tana danqara mata harara

“Ke kuma da bake za’ayi tafiyar wa ya sakoki a maganar?”

“Yo fisabilillahi ummu saita makarar da kanta fa makarar da wasu?” Tayi maganar tana miqa hannu gami da fusgar sabuwar school bag din widad din dake ajjiye kusa da ita,kafin su sake cewa komai.muryar dattijon ta ratso falon

“To….to,ya akayi?” Ya fada yana qarasowa a hankali zuwa cikin falon,kafin ya samu waje ya zauna yana dubansu.

Russunawa basma tayi ta gaidashi,dai dai lokacin latifa ta qaraso dauke da lunch box din widad din

“Gashi an gama” ta fadi tana ajewa gabanta

“Ko muje motar na rakaki dashi” latifan ta sake fada tana kuma dauke lunch box din daga gabanta,tabe baki basma tayi sannan tace

“Tabdi!,gigin primary,kina shiga dashi ansan burbushin primary ce,meye hadinki da wani lunch box tsabar sangarta?,Allah latifa ke kike sake taya ummu ana sakalta yarinyar nan” ta qarashe maganar tana hararar widad din

“Wato kedai anyi babbar banza ko?” Alhj salim ya fada yana duban basma

“Allah alhaji bata sanin ta fara girma”

“Wuce ku tafi ga iliya can yana horn” ya fada yana daga musu hannu,sai a sannan widad ta sauko daga kan kujerar,ta maida takalmanta suka fice ummu tana muta addu’ar dawowa lafiya.

Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta tabbatar da fitarsu,ta maida dubanta ga alhj salim din

“Yaran nan sam basu da zurfin hankali,ta yaya zan banzatar da widad ta gaza samun kulawata?,yarinyar da tun tana watanni a duniya mahaifiyarta ta tafi ta barta?,idan ban kula da ita ba waye zai kula da ita?” Murmushi dattijon yayi yana qarashe janye ragowar carbin da ya rage a hannunsa sannan ya ajjiyeshi gefe

“Iya tasu fahimtar kenan,amma duk da haka saboda gudun ci gaba da samun sabani da yadda suke jin haushinta ganin kamar kinfi sonta,kiyi qoqarin boyewa da rage wasu abubuwan”

Dan sunkui da kanta ummu tayi

“In sha Allah” ta amsa masa cike da ladabi,duk da bata da tabbacin yiwuwar hakan.

“Kunun za’a kawo maka ko dumame?”

“A fara kawomin kunun da qosai tukunna” ya amsa mata yana gyara zamanshi sosai saman kujerar,ta yunqura ta miqe zuwa kitchen da kanta,duk da tsufanta hakan bai hanata yi masa tasa hidimar da kanta ba,koda zata bawa latifa tata hidimar tayi mata,amma ta alhajin ita keyi.

Awannin da tayi a makaranta a ranarta gane banbamcin secondry school da primary,sosai makarantar tayi mata dadi,lokacin tashinsu da yayi tun a cikin motar suke hayaniya,labarin sabon aji da kuma sabuwar makaranta

“Don Allah kuyi mana shuru,kun cika mana kunne ha’an” ramziyya wadda take cousin a wajen widad ta fada,ita din gaba take dasu,don a qalla ta basu shekara kusan biyu,ita dinma wannan shekarar ta shiga js three,kuma akwai yiwuwar shekara mai zuwa a karba kudin aurenta kamar ‘yan uwanta,dole suka rage hayaniyar,saita maida hankalinta ga iliya driver

“Ko ka wuce damu gidan baaba mahmud?,muga lefen najwa tunda yau babu islamiyya”

“To shikenan,babu laifi” ya amsa mata.

Kicin kicin widad tayi,ko kusa ko alama bata qaunar zuwan gidan nasu,koda hutun makaranta akayi kuwa,gidan ba gurin zuwanta bane,zata iya cewa banda mahaifinta bata da kowa a cikinsa,sai yayanta wanda.ba kasafai kake samunsa cikin gidan ba,yawancin lokutta yana makaranta,duk da yadda mahaifinta ke nacin ta dinga zuwa din amma ummu ta hana,idan ta kama saidai ta wuni ta dawo.

Tun daga harabar gidan matan gidan suka fara jiyi hayaniyarsu,babu wadda ta motsa,don kowacce dan data haifa kadai shine nata,har suka qaraso cikin ainihin babban falon gidan

“A’ah,kada dai kucemin daga makaranta kuke?” Ta tambayesu tana tafa hannuwa cike da yaqe da kuma riya,saboda mai gidan na nan,daga inda yake din kuma zai iya jiyo komai

“Ga alama kuwa umma” najwa dake fitowa daga dakinsu ta fada tana dariya gami da qoqarin daura dankwalinta

“Lefe mukazo gani” widad ta fada tana dan dariya,ganin yau yau umman ta sake mata fuska,ramziyya ta harareta

“Shegen son kallon kayan lefe,caraf ta bada amsa”

“Da gaskiyarta,gaba su za’a kawowa ai” umman ta amsa bayan ta qwalawa me aikinta kira kan ta zubo abinci, murmushi widad tayi maganar tana bata mamaki da dariya,yanzun wataran itama sai a ciko akwatuna da kayan lefe ace nata ne?.

A nan suka ci abincin rana suka kuma baje suka kalli kaya son ransu,alhaji mahmud ya fito a shiryensa,suka hau gaisheshi ya amsa musu cikin fara’a da jin dadin ganin ‘ya’yan ‘yan uwansa,ya bisu da kyautar dari bibbiyu sababbi,duka harda widad din bai banbantata da kowa ba a cikinsu,sannan ya fice yabar gidan.

“Ni kunzo a dai dai ma,ku taimakamin na fidda kayan da zan kai dinki” ramziyya ce ta dinga tayata zabin,widad na hade mata su waje daya

“Basuyi yawa ba wadan nan kayan anty najwa?, duka zaki kai dinkin?” Inji widad dake zaune daga gefe

“Saina ma qara wasu,kin manta haka amare keyin dinki da yawa?” Kai ta jinjina kawai tana ci gaba da kallonsu,bayan sun gama najwa tace

“Ki kwana anan widad,saiki rakani nakai dinkin,gobe saina maidaki gida”.

Cikin murna da zumudi ta amsa da to,ko ba komai zata yita kallon kayan lefen dake burgeta sin ranta,don haka ta baiwa su Aafiya jakarta suka wuce mata gida da ita.

Sanda ummu taji shigowarsu sai tayita sanya idanu taji shigowar widad din amma shuru,har ta gaza daurewa ta aika latifa sassan su marwa ko sassan anty madina ta dubo mata widad din me ta tsaya yi bata shigo taci abinci ta sake wanka ta canza kaya ba.

Da latifa ta dawo mata da batun sun barta gidan baaba mahmud shuru tayi,cikin ranta duka babu dadi,don bataso ko kadan widad din tayi nisa da ita,to amma tasan mawuyacine itama ta yarda ta kwana din,ta tabbatar da wahala bata nema a kawota gida ba.

Sanin hali yafi sanin kama inji hausawa,don kuwa tun bayan sallar magariba bayan sun dawo daga wajen dinkin ta lafe a kujerar falon gidan tana raba idanu,ta cika tayi fam,gida kawai takeson komawa,har umma ta fahimci haka,itama hakan ya mata dadi,don duk randa yarinyar ta kwana a gidan ko yaya ne sai sunga wani abu na bacin rai daga mai gidan dangane da yadda yake nuna mata kulawa

“Rabu da ita umma,kin ganta fa ta fara girma,Allah har qirga dangi naga ta fara,amma.har yanxu bata girma da kwana a bayan ummu ba,yau dai a gidan nan zaki kwana,idan bikin nawa yazo ma ba zaki iya kwana ba kenan?” Itadai batace komai ba har zuwa sanda baaba mahmud ya dawo,tare suka zauna da ita suna cin abinci amma sam taqi sakewa,qarfe takwas na dare ta fara musu hawaye,dole ya tashi driver ya maidata gida

“Maidata,kada ta hanamu barcin dare” cewar abban nata.

Karfe tara saura suka isa gidan,sanda motarsu ta tsaya daidai sanda motar uncle haisam abban su marwa qani ga mahaifinta ta tsaya

“Aah,wa nake gani haka da daren nan kamar widad?” A ladabce drivern ya amsa shi

“Itace,taqi zama ne abba yace a dawo da ita”

“Ikon Allah,to muje ciki” ya fada yana kulle motarsa,sukayi sallama da drivern yabi widad din zuwa sassan iyayensa.

Ummun da kuma alhaji suna falo a zaune,sai a sannan yake cin abincin dare sunadan taba fira sama sama da ummun.

Bataji sallamar widad ba sai fadowarta jikinta data ji,tana shirin dagata sallamar uncle hisham ta biyo baya

“Tare kuke ne?” Ummu ta jefa masa tambayar,yana rage tsahonsa gami da neman wajen zama yace

“A’ah,can na ganta drivern gidan yaaya mahmud ya sauketa”

“Yar nema,shine kike biyo dare kika gudo?,ba zaki qyalemin mata dai ta huta ba kenan?”cewar alhaji yana tsokanarta,daga ummu tayi tana turo baki

“Bakaji dadin gani na ba?,bayan ko cigiyata ma bakayi ba….. shikenan” tayi maganar tana miqewa daga jikin ummu tana wucewa daki

“Ahaf……me kika sani banda takura?”. Bata ansa ba har ta isa daki ta tura ta shige abunta,dariya suka saka gaba daya, alhaji ya girgiza kai

“Quruciya me dadi” ya fada a hankali,sai ya maida dubansa ga hisham yana tattara hankalinsa zuwa gareshi.

*_RIGIJI GABJI!_*🔥🔥

*_WANI KAYA SAI AMALE_*🔥🔥🔥

*FITATTUN ZAFAFAN DA BABU NA BIYUNSU*🔥🔥

*JERIN GWANON LITATTAFAI ABOKAN TAFIYAR JUNA MASU MABANBANTAN LABARAI DA FASAHA*

*_’YAN BIYAR DIN NAN NE FA_*

*_SARAKAN LABARUN_*

*NISHADI*
*CAKWAKIYA*
*GWAGWARMAYA*
*BARKWANCI*
*TSANTSAR DARASIN RAYUWA*

*TARE DA*

*ZAZZAFAN SALO NA SOYAYYA MAI RIKITA TUNANI DA TSUNDUMA MAI KARATU CIKIN TAFKIN SHAUQI*

*SUN SAKE SHIRYAWA TSAF,DAUKE DA WANI TARAGO MAI CIKE DA LABARAI MASU ZAZZAFAN ZAFI!!!*

*KIN SHIRYA MADAM?*

*MAZA ANTAYA NAKI KUDADEN KIBI SAHUN AYARIN MATA MASU AJI TA HANYAR BIYAN KUDIN NAKI KARATUN WADAN NAN LITTAFAI KAMAR HAKA*

*DAUD’AR GORA* Billynabdul

*KI KULANI* Missxoxo

*IDON NERA* Mamuhghee

*RUMBUN K’AYA* hafsat rano

*A RUBUCE TAKE* Huguma

*ZAKI IYA BIYA KAI TSAYE TA WANNAN ACCOUNT DIN*

0022419171
Maryam sani
Access bank

Saiki tura shaidar biyanki ta wannan number

09033181070

*MASU TURA KATIN MTN KO VTU KUMA ZASU TURA WA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANSU*

09166221261

*Yan nijer kuwa zasu tuntubi wannan number*

+227 90 16 59 91

*Muna godiya da ci gaba da zabin zafafa biyar a koda yaushe*🙏🏾🙏🏾
[1/23, 6:13 PM] It’s Queen Meenali👸🏻: *HUGUMA*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addara ta)

Page 04
—————————————————-
*MAAB LUXURY HOME*

*_idan kaji gangami akwai labari_*
*_SABUWAR DUNIYA CE_*
*ALFAHARIN UWAR GIDA*
*FARINCIKIN AMARYA*
*MAIDA TSOHON GIDA SABO*
*DUNIYAR QYALE QYALE*
*KAYA NA ALFAHARI DA TAQAMA*

*_Ba iya kyawun idanu suka tsaya ba,harma da ingancinsu da kuma qwarkonsu,ka dade kana mora kana kece tsara a tsakanin tsararraku da sauran mutane_*

*nasan zaku tambaya ina ne nan?*

*MAAB LUXURY HOME*

😊 *Kai daga jin sunan ma babu tambaya*

*_duniyar qawata muku gidajenku ku ganku kamar a wata nahiya ko wata duniyar_*

*Suna kawo kayan kitchen rankatakaf manya da qananu*

*Kayan gado dana parlor*

*Kai…suna kawo kowanne nau’in kayan ado na cikin gida*

*Karkiyi qasa a gwiwa kuma kada kiyi sake ma dafe,maza garzaya ki nemesu a*

_adress dinsu dake No 22 Ahmadu bello way,kano state_

*Ko kuma kuyi order din kayanku kuna daga gida ta shafinsu na instagram*

@maabluxuryhome

*Facebook*
@maabluxuryhome

*Ko ku nemesu ta lambar wayarsu kamar haka*
08034631010

*Kyau inganci da rahusa shine takenmu*😊😊🤝🤝🤝🤝
_______________________

Leave a Reply

Back to top button