Hausa NovelsWaminal Hoob Hausa Novel

Waminal Hoob 4

Sponsored Links

Waminal Hoob_* 4

_Asmy b Aliyu_

Kawu balele na parking motarsa ,motar Aliyu waxeer na tsayawa.saurin fitowa Aliyu yyi ya mikawa kawu balele Hannu sukayi musaba ha.Baba idan bbu damuwa Dan Allah inada magana.”sai da kawu balele ya karewa motar kallo yaga motar ta manya ce sa’annan ya saki fuska ,da kansa ya budewa kawu balele front side ya xauna .wani irin kamshi da sanyi A/c ya xiyarci hancin kawu balele ,masu kudi najin ddinsu Allah ka kaimu ga wannan ddin kafin rai yyi halinsa ,Allah karka kasheni yanxu sai naxama daya daga cikin masu kudin garin nan.”Ya fada yana wani murxa kunnensa,
“Baba Auren Yarka nakeso kabani nooriyah !!”” Jin maganar kawu balele yyi daga sama,kan wannan maganar xaka sakani a motarka,to bude min na fita nayi mata miji.”kawu balele ya fada shaye da toka.
Yana kokarin fita daga motar ,
Da wani irin yanayi Aliyu waxeer ya juyo ya xubawa kawu balele fararen idanunsa.xan siya maka gida xan baka irin wannan motar guda biyar inhar xaka auramin nooriyah.”nan take kawu balele Ya rude ya cakumo hannun Aliyu waxeer yake fadin Yaro da gaske kake Dan Allah.”Aliyu ya daga kafada yake fadin Aliyu waxeer baya magana biyu……
“Ko yau kake son Aurenta xan baka ,dama yar kanwata ce tun tana karama take hannuna marainiya ce Babanta mutunen Sudan ne, har ya komawa Allah bamu san dangin sa ba.Kasuwanci ya kawosa anan ya hadu da kanwata.” Amma sai dai wani hanxari ba gudu ba,inada wani yaro Wanda ke sonta nayi masa alkwarin xan aura masa ita.”nasan idan yaji lahira xai kaini bayada imani.”nan kawu balele ya shaidawa Aliyu halin Kabir ,Aliyu yayi murmushi yake fadin xan saka sojoji suka maminshi makarantar gyara hali xan kaisa ,xakayi Alfahari da Rayuwar kabir nan gaba.”
Rafar dubu Dari Aliyu waxeer ya damkawa kawu balele yana fadin gobe xaa xo nema min Auren nooriyah ,bana son Auren ya dauki lokaci sai ranar da aka dauramin aure da nooriyah xan cika maka alkawarin da na dauka ,jiki na rawa kawu balele ya fito daga mota yama kasa baiwa Aliyu amsa sai famar daga masa hannu yake yana bude baki.Dan ganin yake Aliyu na iya kwace kudin,
Motarsa ya koma ya xauna.ya shiga buda kudin yana sakin ihu Ahankali yana fadin”kudi !kudi!kudi!”duk yabi ya rude sai xufa yake hadawa…….Acikin motar yyi masu boye na musamman sa’anan ya fito ya nufi cikin gidan sa yana wani sakin blushing sai fadin “Yake na kusa xama Alhaji balele har naga yarda kofar gidan nan xai cika da yan maula.”A tsakar gida ya tsaya yana kwalawa Adama Kira ,yau kuma dakin bakonka ne da baxaka iya shigowa ba.” banda lokacin fitowa ina lissafin cinakin da nayi.
“Aike kinji tsiyarki duk lokacin da mutum keso ya fada maki abun Alkhairin da ya samesa ,ke kuma lokacin kike jin naki Rashin mutunci ya fada yana shigowa daga cikin dakin,bbu komai a dakin sai katuwar katifa da sauran tarkace na mata.
A bisa katifar yyiwa kansa masauqi ya dauki kafa daya ya Dora kan daya,yana yiwa adama din wani irin kallo…………..Tsoki ta kara bugawa kafadi abunda ke tafe dakai Dan Allah ka tashi kabani wuri.”Dan wlhi yau ddin bakin ka baxaiyi tasiri araina ba,ko kwandala baxakaci acikin kudin nan ba.” Ta fada tana kara boye sauran kudadenta acikin xani ,wani kallon raini yake mata cikin daga harshe yake fadin”ni xakiyiwa biyayya ko kya tsira na siya maki buhun shinkafa,,baki wangalau adama ta saki tana kallonsa,ganin tana masa kallon shasha yasa ya Ciro kudi a Aljihun sa yan dubu-dubu guda goma sabi dal”Ya watsa kan jikinta ,ki kara da wannan ki sayi koda itace ne.”wawurar kudin tayi tamkar mahaukaciyya ta soma hadasu jiki na Rawa tana yiwa kawu balele wani irin kallo,bata samu magana ba sai da ta hadasu waje daya ta shiga juya kudin a hannunta,idan ma da wasa kake wlhi naci waya’nnan kudin baxan dawo dasu ba”.Dama ina binka bashi har na dubu biyu da dari biyar, ta fada tana tura kudin duka cikin rigarta,daria Kawu balele ya saki yana buga kafa,dadina dake Adama a wajen kudi bakida imani kafura kike xama inhar xaki samu kudi.”ba wannan ba bude kunnenki na baki labari ,amma kafin nan Dan xubomin Abinci ya fada yana wani kara gyara xama,shaye da toka take fadin da xaka fita uban me kabar min nida Yara'”,ko kabir din dake ajewa Dan bakar yarinyyar can mai siffar mayu uban komai yau bai bada ba,bana dashi nima kadan na aje nasa a bakina”……..Ta fada tana jawo kwanon wake da shinkafa xuwa gabanta ,xama yayi kawu balele a kusa daita ya xura hannunsa,tsaki ta shiga buga masa tana hararar sa.Bbu dai kowa a gidan nan kou.” Dan bana son baki labari kabir na gidan nan,,tun safe da ya fita bai dawo ba ,ita kuma wannan mai kama da Aljannun na aiketa kasuwa ta auno min shinkafa su tariq kuma sun fita makota.”ajiar xuciya ya shiga saukewa nan ya soma bata labarin yarda sukayi da Aliyu waxeer,maimakon yaga Adama tayi farin ciki sai yaga ta shiga yimasa wani irin kallo cike da bakin ciki take fadin”wannan bakar yarinyyar xaka aurawa mai kudi har haka,,ita kuma safiyar ubanwa kakeso ya Aureta.???”ta fada cike da jin xafin sa,
Cike da mmki kawu balale ke fadin duka-duka safiyar nawa take shekara goma sha daya kike tunanin nayi mata Aure.”Uban mene bata dashi na halitta ajikinta,
Bakaga harta fi wannan bakar yarinyyar jiki ba,
Ita kuma gatanan kullum kamar takarda.’karma ka fara wannan ganganci bbu ruwana wlhi Idan kabir Yaji kasheka xaiyi wlhi.”ta fada tana bar masa dakin duka,
Xufa kawu balele kawai yake hadawa yasan halin Adama xata iya fadawa kabir shaidaniyace,
Mafita kawai xai nema lalubo yar karamar wayarsa yyi daga aljihunsa wacce tagama mannewa da bakin salatif ,neman wayar Aliyu waxeer ya shigayi kara ya shaida masa matarsa xata kawo matsala ,gara su gama da matsalar kabir ,tashi yyi ya kakkabe Rigarsa yabar gidan Adama tabisa da kallon takaici tana fadin”wawa kawai in banda wawanci ga yar cikin ka agabanka ,amma kana kokarin nemowa yar da bata kaba Hutu da jin ddi inhar ina Raye ni Adama matar balele nooriyah bata isa tayi Aure a gidan Hutu ba wlhi ,kenan bakin nata ma xaa daina ganin muninta gogewa xatayi fatarta tayi kyau.”to ba a gidan nan ba wlhi,muna nan daita anan xata mutu,ko kabir da xai aureta bai isa ya kaita wani waje daban ba ga gidan ubansa.”……..haka ta rika mita ita kadai a tsakar gida.
***
Ahmad waxeer shine Asalin mahaifinsa Dan kasuwane ,haka babban Dan siyasa ne.Ya Gina asibitoci daban-daban A gida nigeria harma a wajen Nigeria haka ya mallaki manyyan manyyan company’s da gidajen man fetur masu suna( waxeer) ,yabar masu dukia mai tarin yawa kafin yabar dunia matar Auren sa daya ,da yayan su ukku hajia Maryam itace mahaifiyarsu Asalin bafulatana CE Ibrahim waxeer shine babban yaron su .Wanda suke kira da Khalil sai Aliyu waxeer mai bimasa,sai kuma Auta Fatima batool ,basu San wani Abu waishi rashi ba a dunia dukan su koda mahaifinsu yabar dunia cikin gata suke ,har yanxu cikinsa suke sabida mahaifiyarsu ta tsaya masu ,haka suna tsaye akan dukiyar mahaifinsu bbu Abunda ya canja saima daukaka ta karayi ,tun tasowarsa yake matukar sha’awar tukin jirgi a rayuwarsa ,tare da taimakon Mahaifiyarsa da yayansa ya cika burinsa na xama pilot .lokaci daya ya xama millionaire ,haka duk magazine din da xaa buga ana maganar Dukiar Aliyu waxeer ne da aikinsa,bbu inda sunan sa baiyi fice a kasar nan ba tamkar mahaifinsa har ma yafi mahaifinsa suna.yana daya daga cikin Abunda yasa baya shiga cikin taron mutane ,
Ganin yarda Ammah ta xuba masa ido yyi saurin sauke kansa kasa,wani irin murmushi Ammah ke saki tana fadin”finally yarona xaiyi hankali kwanan nan.”da sauri Aliyu ya dago yana kallon Ammah yana hade rai yake fadin”Ammah Dama can bani da hankali ne.”bai cika ba sai ynxu xai cika,
“Munyi magana da Baffanku Khalil waxeer sai jibi xai iso kara su tafi agama magana ,bikin abarsa nan da 1 month haka akwai shirye-shiryen da xanyi.”da Sauri ya katse Ammah yana fadin”No Ammah bafa wani biki xaayi ba kawai Aure xaa daura ta tare shike nan,bana son mutane su San nayi Aure kin San social media.”da mmki Ammah ke kallonsa ,ganin taki cewa komai yasan bata karbi xancen ba .Ya rasa ta yarda xaiyiwa Ammah bayani yasan yarda aka kashe kudi ga Auren Khalil waxeer haka bikin ya kama yawo a dunia ,shikuma baxai iya fitowa da wannan yarinyyar a dunia ba a matsayin matarsa ae sai a raina matsayinsa.”jiki sabule yabar parlon yana fita kiran kawu balele na shigowa a wayarsa ,tsoki yaja farhaan ya hadasa da ciwon kai,harta tsinke bai daga ba.kiran captain bilal ya shigo a karo na biyu dagawa yyi captain bilal na fada masa sunyi nasarar kama kabir ,godia ya masu yace xuwa anjima kadan xai samesa barak su tatauna matsalar kabir din.da haka ya nufi part dinsa,yana Neman layin farhaan….

PAID BOOK
ASMY#??

Haske Writer’s Association #

Back to top button