Duk KarfinIzzata Book 2Hausa NovelsHausa Novels

Duk Karfin Izzata Book 2 Page 3

Sponsored Links

Book 2

*Episode 3*

Da sallama ɗauke a bakin ta Aunty farida ta shigo chikin palon Bgs rike da hannun Hiyana daketa faman sharara kuka dan ita gani take shike nan kwanan ta ya kare, kai tsaye betroom nashi suka nufa ita kanta Aunty farida fargaban shigar betroom ɗin take

Zaune yake a bakin katafaren gadon sa sanye da jallabiya baka ya dafe kansa da hannu biyu yana kallon kasa da alama wani tunani yake, jin Sallamar Aunty farida che ya sa ya ɗan ɗago kai kaɗan, batare da ya kalli in da suke ba kasa kasa ya Amsa sallamar, ƙarisowa chikin ɗakin sukayi jin shesshekar kuka yasa ya ɗago idon sa kallo ɗaya ya musu ya kauda kansa gefe yana kara yamutse fuska gefen gadon Aunty farida ta zauna tare da zaunar da Hiyana a gefenta, Chike da So da kaunar ɗan uwan nata tafara magana

“Prince ina ne ɗakin Hiyana? Shiru yayi kamar bai ji me Aunty farida tace ba “Prince Magana nake maka fa nache inane ɗakin Hiyana!? Ta karisa maganar tana ɗan kwaɓe fuska alamar bataji daɗin shiru da ya mata ba, shiru dai Bgs bai yi magana ba kamar ma bai san da shigowar mutane ɗakin ba, shiru Aunty farida tayi bata sake yi masa Magana ba dan a tsorache take da shi Almost 10mnt suna zaune shiru chikin muryan rarrashi Aunty farida ta fara magana

“Haba prince dan Allah ka bani amsa mana nasamu naje na kaita ta kwanta ta ɗan huta” shiru shiru kamar bai san da zaman su a ɗakin ba ganin hakan yasa Aunty farida ta miƙe ta kama hannun Hiyana ta nufi waje da ita ɗakin dake kusa da nashi Aunty farida ta shiga rike da hannun Hiyana, komai na chikin ɗaki iri ɗayane da nashi sai dai ban ban chin colour domin komai na ɗakin sa farine tas na hiyana kuma sky blue, a bakin katafaren gadon dake chikin ɗakin Aunty farida ta zaunar da Hiyana ta juya batare da tayi magana ba ta nufi waje gaba ɗaya ji tayi jikin ta yayi sanyi wani mugun tausayin hiyana ne ya sake dira a ranta, tunani take tana tafiya lallai Prince ya tabbata baya son hiyana ko kaɗan Allah sarki bai war Allah, ɗakin Bgs ta koma

Da Sallama tashigo ɗakin kamar yadda ta barshi haka ta dawo ta same sa gefen sa ta dawo ta zauna chike da fargaban abun da zai biyo baya ta fara magana

“Kayi hakuri Prince na san ba’a kyau ta maka ba amma idan ka daure kayiwa iyayen mu biyayya zamuyi nasara arayuwa kaji? shiru Bgs yayi bai yi magana ba da alama bai da niyar magana kwata kwata, chigaba da magana Aunty farida tayi “pls ɗan uwana kaji tausayin yarinyar nan marainiya che ba uwa ba uba kuma kana sane da irin wahala da ta sha arayuwar ta to dan Allah ko da ba zakuyi zama a matsayin mata da miji ba ina neman alfarma da ka ɗauke ta kamar yadda ka ɗauke ni dan Allah idan kamin hakan ka gama min komai pls” wani iska mai zafi ya furzar daga bakin sa kafin ya fara magana

“Pls Aunty babba zaki iya tafiya!!” chikin sauri Aunty farida ta ɗago tana kallon sa shima ita yake kallo ba karamin razana tayi da kallon yadda green eyes nashi suka sauya izuwa jaa sosai ga jijiyoyin kan san nan duk sun tashi duk da A.c dake ɗakin hakan bai hana shi zufa ba chikin murya irin na rarrashi Aunty farida tace “dan Allah prince ka saurare ni nasan baa kyau ta maka ba amma kasani ba laifin Hiyana ba che wlh bata san komai ba yarinya bai war Allah ita kanta yanzu kukan dana sanin zuwan ta duniya gaba ɗaya ma take, ta sha wahala a rayuwar ta pls my blood ka karɓi Hiyana a matsayin kanwa ba mata ba kaji? ta karisa maganar kamar zata yi kuka kawar da kansa gefe yayi chikin nitsuwa ya fara magana

“Naji zan yi tunani a kan hakan zaki iya tafiya”wani nauyayyar ajiyar zuchiya Aunty farida ta sauke dan tasan halin Bgs idan yace zai yi abu to zai yi ne addu’a take Allah ya ɗora su a kan shi, da wan nan tunanin ta miƙe ta fice daga ɗakin, wani dogon tsaki yaja tare da miƙewa ya kwanta yana kwaɓe fuska

A ɓangaren Khalid kuwa

Aunty salma rike da hannun Zahra wadda ke ta kuka suka shiga palon sa, kwanche suka same sa saman sofa mai zaman mutun 3, yana ganin su ya miƙe zaune yana faɗin “sannu ku da zuwa” murmushi Aunty Salma tayi tana mai farin chikin yau ɗan uwan ta yayi Aure kuma abun farin chikin ma Autan su ya Aure

Gefen sa Aunty salma ta zaunar da Zahra san nan ta koma gefe ɗaya ta tsaya chike da farinchiki ta fara magana “to ga amanar kan wata na baka ka kulamin da ita sosai fa” da murmushi a kan face nashi yace “gaskiya na karɓi wan nan Amanar hannu dubu dubu In Sha Allah zan kula da sis love na sosai kamar kwai a kan bajejjen faranti” dariya Aunty Salma tayi kafin tace “oh Allah ko kunya ta bakaji ba ko? Sunkuyar da kansa kasa yayi chikin raha yace “to Aunty babba gashi nan naji kunyar taki” tsaki Aunty salma taja chikin wasa tare da nufar kofar fita tana faɗin “ai, Ni ban soma Abba ya baku matan naku yanzu ba so nai ya bari sai nan da wata 2 masu zuwa” tana kai karshen maganar ta fice daga ɗakin

Dawo da kallon sa Khalid yayi kan Zahra dake ta faman sharɓan kuka, hannu yasa ya goge mata hawaye chike da so da kauna yace “my wife kukan me kuma ki keyi ne? Shiru Zahra tayi bata tan ka shi ba kuma bata dai na kukan ba, murmushi Khalid yayi tare da miƙewa ya naɗe hannun rigan sa ya duƙa ya ɗauke ta chak kamar yar baby ya nufi betroom nashi da ita

A tsakiyar katafaren gadon sa ya zaunar da ita tare da zama daga ɗan gefen ta ya kwan to da kan sa kan chinyar ta kasa kasa ya fara magana

“My wife wai kukan menen hakan? Baki san zama da nine? Sunkuyar da kai kasa Zahra tayi ta chigaba da kukan ta, “oh my god Khalid ya furta tare da miƙewa zaune yasa hannu ya ɗago haɓarta, chike da so da kauna yasa harche ya lashe hawayen nata tas tare da haɗe fuskokin su yana kallon chikin idon ta “now zaki yimin magana ne ko kuma dai sai na chiji ɗan bakin nan naki? Chike da shogoɓa tace “Ni Allah yaya Khalid bana so ka mai dani part ɗin Ammi na” murmushi yayi kafin yace “au shine dalilin kukan naki? Gyaɗa masa kai tayi alamar eh “ok to bari zuwa gobe zan mai dake kinji amma yanzu tashi muje na miki wanka na shiryaki muje na baki abinchi a baki” turo ɗan bakin nan nata tayi chike da shagoɓa tace “ni na iya wanka da kai na ai”
“Aa ni gaskiya ban yarda ba kizo kawai muje na miki idan ke kikayi bazaki fita sosai ba, bata san lokachin da dariya ya kubche mata ba zuba mata ido yayi yana kallon yadda take dariya sai da tayi mai isar ta san nan ta raba fuskantar da nashi tana faɗin “to ai ni nake wankana tun dama chan kuma ina fita sosai ai a haka ma ka ganni kache kana so” ta karisa maganar tare da rufe fuskar ta da hannun biyu “eyeee a lallai my wife ta girma babu zan chen ɗaga kafa kenan” “ɗaga kafan me kuma dama ai ni ban che kaɗaga kafaba” “au haka kika che? “Eh mana yaya Khalid ni ban che ka ɗaga kafa ba to ma idan ka ɗaga kafar ka kai ta ina

Fisgota yayi da karfi ta faɗa kan kirjin sa, rungumeta yayi sosai yana faɗin “ai ko ba zan ɗaga kafar ba” ɗago da fuskan ta tayi daga kan kirjin nasa chike da shogoɓa tace “yaya Khalid ka kusa karyamin hannu fa Allah” “sorry my wife to muje na kai ki toilet kiyi wanka ko?tun da bakya so na miki, Ba tare da ya jira Amsar taba ya miƙe ya ɗauke ta chak ya nufi toilet da ita.

A ɓangaren Yusuf kuwa Aunty Mardiya na fita ya matso kusa da Amaryan sa kasa kasa yace “my baby ya jiki? Kan ta a sunkuye tace “da sauki amma har yanzu kai na na min chiwo sosai” eyya sorry kinji In Sha Allah zai dai na yimiki chiwo yanzu dai ki kwanta ki huta bari naje wajen Abba a fada ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya nufi waje ita kuma lamrat karisa hayewa saman gadon tayi ta kwanta ba jimawa barchi yayi awan gaba da ita

A ɓangaren Fahad kuwa

Koda Aunty mardiya ta shigo tare da Amrat shiru palon babu kowa kai tsaye betroom nashi suka shiga tare da sallama babu kowa a ɗakin sai dai karan ruwan dake tashi daga toilet da alama wanka yake
Karisawa su kayi chikin ɗakin a bakin gado Aunty mardiya ta zaunar da Amrat tace ” amrat ki zauna kijira mijin ki yana wanka ne zan koma ɗakin Ummi kinji? Batare da tajira amsar amrat ba ta juya ta fice daga ɗakin.

Almost 20mnt Amrat na zaune shiru tana sunkuye da kanta kasa tana wasa da yatsun hannun ta, jin An buɗe kofar Toilet ɗin ne yasa ta ɗago kai tana kallon kofar tana jiran taga mai fitowa dan ita kwata kwata batama san wanene mijin nata ba

Ɗaure da farin towel mai laushi da kyau a kugun’sa ya fito bai ma lura da mutun a ɗakin ba kai tsaye gaban mirrow ya nufa, ganin sa haka yasa Amrat fasa ihu dan ba karamin tsorata da ganin halittar jikin sa tayi ba, A’sukwane ya juyo yana bin in da akayi ihu da kallo, da mamaki yake kallon razanan ne fuskar ta a nitse yace “ke wacece ke? Sai lokachin Amrat ta dawo chikin hayyachin ta da sauri ta miƙe tsaye ta kwasa da gudu ta nufi hanyar fita daga ɗakin taku biyu Fahad yayi ta damko kugunta ta baya tare da ɗaga ta sama ya dawo da ita chikin ɗakin wurgi yayi da ita a saman gadon chikin tsawa yace ” wacece ke!? Me ya kawo ki ɗakin nan!?

Amrat ta gama tsorata murya ta har rawa yake ta fara magana “Aunty mardiya che ta kawo ni” ” wacece ke!? “Sunana Amrat” shiru yayi yana tunanin chikin ran shi yana mai mai ta sunan Amrat tabbas na taɓajin sunan Amma na manta ko ai nane “to naji sunan ki Amrat me kika zo yi a ɗakin nan!? “Aunty Mardiya che ta kawo ni kuma tace na zauna na jira miji na ya fito sai yanzu Fahad ya tuno in da ya taɓa jin sunan lokachin da limamin babban masallacin juma’a yake faɗin an ɗaura Auren Fahad Abubakar Saraki da Amrat Ahmad guntun tsaki yaja tare da juyawa ya nufi gaban mirrow ya fara shafa mayu kan sa masu kamshi da tsada, Amrat kuwa shiru ta kwanta a saman gadon nasa ta runtse idon ta tana jiran taji me zai sake che mata

“Ke tashi ki shiga dressing room na ki ɗauko min kayan da zan sa dan ni yar Aiki aka kawomin da sauri Amrat ta miƙe chikin sanyin murya tace “yaya ina ne wajen kayan naka kuma yaya sunan ka, da mamaki ya ɗago yana kallon ta ta cikin mirrow wai yarinyar nan ko sunana ma bata sani ba amma Abba ya san yadda ya shiga ya fita ya haɗa mu Aure nan take kuma yaji wani irin tausayin yarinyar ya kama shi chikin sanyin murya yace “sunana Fahad ki buɗe wan chan kofar ki shiga zakiga kayan na awajen ki kawomin set ɗaya, chikin sauri Amrat ta nufi dressing room ɗin

Jim kaɗan ta fito hannun ta ɗauke da kayan nashi gaban sa ta dawo ta sungunna chikin nitsuwa tace “yaya Fahad ga kayan nan shiru yayi kamar bai jita ba, shiru ita matayi ta sunkuyar da kanta kasa tana jiran ya amsa kayan, sai da ya gama gyara gashin kansa san nan ya goma gefen gado ya zauna tare da miƙa mata hannu alamar ta kawo masa kayan, miƙewa tayi tana tafiya a hankali kamar bata son taka kasa, sugunnawa tayi a gaban sa tare da miƙa masa kayan, bin kayan yayi da kallo ba tare da ya ansa ba

“Waye ya koya miki zaɓen abu mai kyau? “Babu kowa ni da kai na na iya, shiru yayi bai sake magana ba yasa hannu ya Ansa kayan, shiru tayi ba tare da ta miƙe ba tana ɗan satar kallon sa “tashi ki zauna a saman gadon mana, ya faɗi hakan tare da miƙewa ya shiga dressing room ɗin bin bayan sa da kallo Amrat tayi har ya shige room ɗin san nan ta miƙe ta koma gefen gadon ta zauna.

Maiduguri

“Ahzan ai na ka buge wan nan kyakkyawar yarinya haka? Kuma ina iyayenta da yan uwan ta suke? “dady wan nan yarinyar fa mahauniya che bata da hankali” ” aa Ahzan wan nan yarinyar ba mahaukachiya bace ka dubi jikin ta mana ka kalleta da kyau zaka gane hakan” “to dady Ni dai a yadda na ganta sai naga kamar mahaukachiya che “To mu bari ta farfaɗo tukun nan sai muji daga bakin ta ko? Yanzu dai bari naje na sanar da mom ɗin ka sai mu dawo gaba ɗaya dan ta chigaba da kula da yarinyar” to kawai Ahzan yace miƙewa dady yayi ya fice daga ɗakin, dawo da kallon sa Ahzan yayi kan yarinyar dake kwanche bata ko motsi sosai ya zuba mata ido chikin ran shi yana yaba irin kyawun yarin yar…..

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan Allah ya kaimu

NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER’💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(Star Lady)

*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat….love)

*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)

P*💫STAR LADY💫*4

💖The Talent Troupe Writer’s 💖

*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

Back to top button