Hausa NovelsWaminal Hoob Hausa Novel

Waminal Hoob 20

Sponsored Links

Waminal Hoob*_ 20

PAID BOOK
_Asmy b Aliyu_

Dakin barcinta ta nufa kai tsaye , daman Ammah ta saka kowane gida an shiga an gyarasa daga gidan Khaleel har na Aliyu,tana shiga ta saka key jikin kofar toilet ta wuce wayarta ta fiddo ta shiga Kira daga dayan bangaren aka daga,kana jina ko Sabi’u ehh ina jinki Hajia plz ka kawomin maganin da kasan Yana saka tashin xuciya Idan aka shasa yanxu -yanxu ina gida??da mamaki Yake fadin Ban fahimta ba??Dafe Kai tayi kafin tace kwaya Mai karfi nakeso wacce xata iya saka mutum Jin jiri har ma da Amae,a dauka mutum Yana da shigar ciki ka fahimta yanxu??tayi Maganar a Dan hasale nagane Hajia Nan da awa daya nake bukata Idan ka kawo kayimin waya,da haka ta datse Kiran tana sakin murmushin mugunta tana wani juya ido ,xatayi wasa da hankalin Ammah xata xuba ido kurum Tasha kallo Yar Daria ta saki tana tafa hannu har ta hango yarda Ammah xatayi ,ta dakune Fuska tana kallon mirror din toilet din tana xaro ido take fadin”Allah yasa Aliyu shine ajalinki !!”Allah yasa ma ki mutu kowa ma ya huta ,wlhi tallahi yarda Baki kaunar ganina cikin farin ciki Nima Haka ,kin hanani Jin ddin Rayuwar Aurena yarda kike min wasa da farin ciki agidan Aurena Haka Nima xan tarwatsa farin cikin ki.”Da Khaleel baya tsananin Sona da na shiga ukku na lalace.”cire kayan jikinta ta shigayi wanka tayi tana son taga wanna dramar………Ta lura tunda Ammah tayi Maganar Rashin samun cikinta duk Aliyu ya shiga damuwa,itama a bangarenta Kusan hakane,wani irin soyayyar Ammah da tausayinta taji ya tsaya Mata arai,duk ranar da Ammah ta gano matsayin Auren su Bata San mexai faru ba.”Hawaye taji suna cika idonta Wanda Bata San ko na menene ba,a karo na bbu adadi tana da na sanin yin wannan Auren,duk da Auren ya kawo Mata Alkhairi sosai acikin Rayuwarta ,ta tabbata data Rabu da Auren Aliyu waxeer babu ita ba sauran farin ciki Koda ta Auri farhaan Shagari kuwa.”Bata yiwa farhaan Shagari soyayyar Aure,da tayi wanka daki tayi ta kwanciya har Kusan 5 har lokacin Bata San halin da Aliyu Yake ciki ba,gajia da kwanciyar tayi ta fito parlor bude Baki tayi tana kallonsa Yana kwance akan soofa Yana barci ,Bata taba ganin Wanda barci Yake yiwa kyau ba kamar Aliyu waxeer……….ta dau tsawon lukkuta tana kallonsa,lokaci daya ya Buda ido Yana kallonta wara ido tayi ta juya masa baya cike da wata irin kunyarsa.”xo Nan.!”taji ya fada mata Juyawa tayi a hankali ta fara tafia kanta na a kasa ,
Kallonta Yake tun daga sama har kasa ,wandon Jean’s ne ajikinta Wanda ya kamata sosai sai farar shirt tayi parking kanta tsakiyyar kanta ko hula babu akanta ,tayi wani irin kyau.har ta karaso wajensa xuciyarsa Bata daina bugawa ba,xama tayi tana kallonsa.” Mekika shirya Akan Rabuwar mu??”da sauri ta dago tana kallonsa xuciyarta na wani irin harbawa,Batayi tsammanin Jin waya’nnan kalaman daga garesa ba.”wata biyu ya rage Mana,ban san me xai faru da Ammah ba Idan wannan Auren yaxo karshe,Dan murmushin Nooriyah tayi da dukkan kwarin gwiwarta take fadin”karka damu acikin watanni biyu din Nan xan samo Mana mafita insha Allahu Ammah baxatayi blaming Dinka da komai ba believe me??”tayi Maganar tana kallon cikin kyawawan idanunsa,saurin dauke nasa idon yayi ya mike tsaye Yana fada Mata Bayan sallar magrib xasuje su gaisheda Baffa waxeer ta hada tsarabarsa shida Ummah,da Haka ya nufi dakin barcinsa Dan yin wanka.Bayan sallar magrib kamar yarda ya fada sukayi shiri dukansu cikin shiga ta alfarma sai xuba kamshi suke A mota daya suka hade,cike da fara’a ummah tayi masu tarba ta musamman ,Haka ta masu jagora a parlorn baffa shima yayi murna da ganinsu sai saka masu Albarka Yake,cike da girmamawa Nooriyah ta baiwa Baffa tsarabarsa Wanda turarruka ne masu tsadar gaske na maxa,sauran ledar ta mikawa ummah itama turaren ne da dogayen riguna masu kyan gaske ,lokaci daya Laylah tayi mugun hade Rai shima Khaleel cike da kunya ya saukar da kansa kasa ganin Bai rikowa baffan nasa komai ba,
Idan Yana biyewa laylah yasan babu Abunda xaa taho dashi,tana ma iya yin fada tace Mai suka nema suka rasa ae suna da komai ,kyautar ma idan anyi masu ae bayarwa suke meye Amfanin yinta.basu Jima ba sukayi masu sai da safe har sun nufi gidan Ammah laylah ta kalli Khaleel ta Dan shagawabe fuska take fadin”sweetheart Ice cream din Aliyu ya kaini na karbo,Baki na duk Babu dadi”.gyaran Murya Khaleel yayi Yana fadawa Aliyu ya juya motar laylah xata Sha ice cream ,Aliyu yasan da gangan tayi haka baice komai ba ya juya kan motar…….dukansu a mota suka xauna laylah ce kurum tafita karbo ice cream din da kallon takaici yabita ganin wasu shegun Kaya dake jikinta wanda dakyar take Buda Kafa tayi tafia acikin su sabida yarda suka kama jikinta,mayafin shi Kuma a kafada kawai aka dorasa,wani tsakin takaici ya saki .Yana taya yayan sa jimami da Rashin dacen Abokiyar Rayuwa.bata Jima ba sai gashi ta fito gefen da Noory ke xaune ta bude ta ajey Mata nata ledar ,da Dan murmushi Nooriyah ke fadin nagode,tun a mota laylah ta fara Shan nata .itama Nooriyah da ta kwana biyu Bata Sha ice cream ba ta dauko daya ta Buda ta gefen ido take kallon Aliyu,
Ya girgixa Kai Yana fadin kin San sanyi baya Baki lfy why not….”ki Bari sanyin nasa ya rage,yayi Maganar sounding so very cool.”..Yama fara yin melting ba duka Yake da kankara ba,
“Idan kika dameni da dare kina min korafin Akan hancinki ya toshe sai na fasa maki baki.”Yayi Maganar Yana dakune Fuska kallonsu kurum Khaleel keyi cike da burgewa ,Yana mamakin yarda Wai Aliyu waxeer ne ya iya kula da macce har Haka.”ita dai laylah murmushi kurum take,
Dukan su suka samu Ammah a parlor tana using laptop da medical glass a idonta,xubewa sukayi a gabanta suna kwasar gaisuwa ta daga Kai tana kallon Nooriyah tana fadin Kara da Allah yasa kuka taho yanxu mugama cin Abincin dare ki tayani caculating kayan Nan,
Da sauri Nooriyah ta karbi laptop din tace bara na maida a daki idan mun gama xan xo na duba.”da Haka ta nufi dakin Ammah na barci laylah tabita da wani mugun kallo haka ta hade wani Abu da taji ya tsaya mata arai.kowa shi yayi serving mijinsa,
Nooriyah tun da ta fara serving Aliyu taji xuciyarta na wani irin tashi haka kamshin Abincin na wani irin hautsina cikinta,dauriya kurum take bayan ta gama xuba masa ta koma ta xauna Ammah ta kalleta da mmki tana fadin”ke baxaki xuba Abincin bane,xatayi magana taji amai yaxo mata da gudu ta rufe bakin ta nufi hanyar kitchen da sauri Ammah ta Mike tsaye tabi bayanta shima Aliyu Bayan su yabi , Khaleel waxeer yayi murmushi Yana fadin”Allah yasa mun samu karuwa.”shima yayi Maganar sounding so very happy Wanda Jin kawai yayi Maganar tafito masa ,da sauri laylah ta kallesa da mamaki cikin hade Rai take fadin”mekake nufi da hakan??”Ya Dan fiddo manyyan idonsa ya kalleta yana fadin ,kawai na masu fatan Alkhairine .”tsaki laylah tayi tana fadin ni bana son munafurci Kara ka fito fili ka fada kaima ka shirya son haihuwa .”Tayi Maganar cikin bacin Rai xaiyi magana sai gasu Ammah sun fito Aliyu rike da Nooriyah wacce tabi duk ta galabaita lokaci daya,
“Bari na dauko mayafi muje Asibiti ,da sauri Aliyu ya katseta yana fadin”Ammah wane irin Asibiti Kuma yanxu xata dawo normal maybe akwai Abunda taci Wanda ya lalata Mata ciki.”wani irin Kallo Ammah tayi masa da yasa shi saurin saukar da kansa kasa gabansa na mugun bugawa ,har ga Allah baya son aje Asibiti sabida kar agano babu ciki a karya xuciyar Ammah ,tunanin hanyar da xai dakatar da Ammah Yake,da sauri Ya kalli Khaleel waxeer Wanda shima kallonsa Yake,ka fada Mata Yaya plz…….”Khaleel ya girgixa Kai Yana fadin”kabari aje a duba Yar mutane Mana,xaiyi magana sai ga Ammah ta fito sanye da hijab waya a hannunta tana neman layin Dr.Billy wacce ke aeki acikin Asibitin waxeer Kusan shekaru biyar itace family doctor dinsu,komai da komai itake dubasu ta fannin Rashin lafia,Jin yayi hankalinsa yayi mugun tashi,rikata muje Ammah ta fada tana nufar kofa da sauri tamkar itace Bata da lfy,Allah kawai ne ya kaisu Asibitin Dan baima San inda Yake jefa motar ba,duk sanyin Ac.dake motar xufa Yake hadawa.sunyi sa’a tana office dinta ,
A kofa Aliyu ya tsaya ya kasa shiga cike da tsoro Ammah ce da Nooriyah suka shiga,
Sun shiga da minti biyu sai ga Dr.billy ta fito dama Aliyu ya tura Mata sako,tana ganinsa tace lfy Aliyu meyasa baka shigo ba??”da sauri ya saukar da Murya Yana fadin ina son muyi magana private Aunty kafin ki duba Nooriyah plz.”owk ina xuwa??”ta fada tana komawa office din ta kalli Ammah da murmushi tana fadin”bara naje na dawo Ammah pls minti biyar toh ina Aliyu Kuma??”Ammah ta girgixa Kai tana fadin”Auh komawar sa yayi”.Dr.Billy ta nufi kofa tana fadin ina Jin baiyi nisa ba fa”……Dan Allah Aunty ki tabbatarwa da Ammah Nooriyah nada ciki ajikinta plz kiyimin wannan alfarmar,Baki sake Dr.Billy ke fadin”kasan kuwa hukuncin wannan karyar shin meyasa ma xakayi Mata wannan karyar.”Aliyu waxeer ya girgixa Kai xuciyarsa na karyewa yake fadin”Sabida farin cikinta xanyi haka kin San ciwon Ammah damuwa kadan ke dagasa duk tabi ta daga hankalinta na rashin samun cikin Nooriyah,
Inhar xaki taimaka Mana da maganin da xata dauki ciki Nan da wata daya pls ki taimaka Mana,na rasa yarda xan nunawa Ammah hakan daga Allah ne,idan Nooriyah ta fara Shan magani Nan da wata daya Idan Allah yayi xata samu cikin kinga karyar mu Bata tafi a banxa ba.?””Toh Anya kuwa Aliyu kana kusantar matarka akai-akai kuwa”Haka Kuma Kai daita duka Kuna lfy,lafiar mu kalau Aunty.”ya fada Yana Jin xuciyarsa nayi masa wani irin nauyi da karyar da ya Saba tun da Nooriyah ta shigo cikin Rayuwarsa,yasan muddin Ammah taji Nooriyah Bata da ciki sai ta gano gaskiyyar meya hanata yin cikin,
Yasan halin Ammah da saka Abu agaba ,Haka Kuma da wuya taki yin Nasara,
Duk ta gano basa zaman Aure da Nooriyah komai xai iya faruwa.”naji na aminta da bayanin ka ,Amma ka dawo gobe Kai da matarka na binciki lafiar ku kafin na Baku maganin da xakuyi Amfani dashi,godia sosai yayi Mata Yana Jin wata natsuwa na saukar masa,mota ya koma yayinda Dr .Billy S fari ta nufi katafaren ofeshinta ,gwaje-gwaje ta saka akayiwa nooriyah din Wanda ta gano akwai Abunda ya hutsina cikinta magani ta rubuta ta ajey takardar gefe. Wanda Aliyu ne ya kamata tabaiwa takardar,ta kalli Ammah da murmushi a fuskarta tana fadin”Hajia Allah fa ya karba Addu’arki kin kusa xama Kaka.”!”wani irin dagowa Ammah tayi da kwallar farin ciki a idonta tana kallon Dr .Billy wacce take daga Mata Kai Alamar tabbatarwa ,wani gefe tausayin Ammah ne ya rufeta.da mugun shock Nooriyah ke kallonsu,Hawayen rudewa taji suna cika idonta lokaci daya,
“Duka kudaden Jakarta ta xube a table din dr.Billy cike da Hawayen farin ciki take fadin”ban san Dame xan biyaki ba doctor ga wannan ,su kawai ne a jakana xuwa gobe xaki ga babban Goran Albishir ,Aliyu ta shiga Kira cike da murna take fadin”yayi sauri yaxo office din Dr. Billy dama yasan hakan xata faru wani irin soyayyar mahaifiyarsa da tausayinta yaji suna cika masa xuciya,Dr .Billy ta Mika masa takarda tana tayasa murna haka ta fada masa yabiya pharmacy ya karbowa Nooriyyah maganunnukan dake jikin takarda,kallonsa kawai Noory keyi da mugun shock shi Kuma yaki yarda ya kalleta,A mota ma duk yarda taso su hada ido yaki bada damar hakan,a hanya ya tsaya babban wani pharmacy ya karbi magani,suka nufi gida tun a hanya Ammah ke sanarwa ya’n uwa da abokan arxiki a waya ,tana jira Ammah tayi gaba ta tsaya tareda Aliyu .Ammah Taki bada damar hakan suna gama parking ta rika hannunta suka nufi Entrance din shiga cikin gidan,laylah da Khaleel ne xaune a parlorn Ammah suna kallo,
Dama laylah Taki tafia ne har su Ammah su dawo daga Asibiti suji meya faru .”da fara’a Ammah ta karaso cikin parlorn ta kallesu tana fadin”dama Baku tafi ba,no Ammah muna jiran dama ku dawone.”laylah ta fada tana kwakwalo murmushi ,Ammah ta xauna ita dai Nooriyah tana ta tsayi xuciyarta tana Jin ba dai-dai ba,
Ammah ta kalleta tana fadin”xauna Mana Nooriyah ta kalli Khaleel waxeer da dukkan farin ciki Akan fuskarta Wanda Khaleel Bai taba hangowa ba take fadin”ka kusa xama daddy Khaleel.”!shima Khaleel wani irin farin ciki Ya bayyana akan fuskarsa yake kallon Aliyu waxeer Wanda yayi tsaye tamkar an dasa sa a wajen ,wata irin ruguma Khaleel din yayi masa Yana sakin dariar farin ciki.
Har kwallah na cika idanunsa,ita dai laylah kallonsu duka take a rude,Taya hakan ta faru??”Taya Nooriyah xatayi ciki yanxu.”wani abun takeji wani iri tamkar a wasan kwaikwayo ,Dan murmushi tayiwa Nooriyah tana fada Mata tana tayata murna,ta kalli Ammah tayi Mata sai da safe ta riga Khaleel barin gidan,tun a hanya take Kiran Sabi’u Yana dagawa take fadin”wane irin magani ka bani wannan daga shansa sai ciki.”tayaya?”da mmki Yake fadin”hajia sai idan dai dama akwai cikin,xufa ta fara hadawa ta katse Kiran ta ta gwada Kiran Areefa Mansoor naso ba adadi a kashe wannan daren Bata taba ganin dare Mai tsawo irinsa ba a tsayin Rayuwarta.matsuwa tayi garin Allah ya waye.nooriyah Bata samu damar ganin Aliyu ba Dan agidan Ammah ta kwana,shima dama Yana tsoron haduwar daita Dan Bai shirya karbar tambayoyinta a yanxu ba.”sai Kusan 12 ya shiga gidan Ammah,bbu kowa a parlon Kai tsaye bedroom din Ammah ya nufa,dama bedroom din nata biyu ne Wanda Yake tunanin Nooriyah na ciki can ya nufa,Yana tura kofar sukayi ido biyu daita,tana ganin sa da sauri ta Mike ta nufosa idonta na cika da hawaye,xatayi magana yayi saurin Dora yatsan sa a bakinta,lokaci daya ta fashe da kuka ganin haka yasa yayi saurin Jawota ajikinsa gamida rungumeta.”

Littafin Waminal Hoob na kudi ne #500
Account Details
0004157137
Jaiz Bank
Asma’u Buhari Aliyu
Katin wayar MTN.ta wannan lambar
09060259200
Shaidar Biya ta wannan lambar
08086207764#

ASMY#??
WM#??
Team#NooryAli forever??
[9/15, 6:11 PM] Asmy

Back to top button