Hausa NovelsWaminal Hoob Hausa Novel

Waminal Hoob 31

Sponsored Links

Asmy Mom Aydah??: 31
Kallon Areefa mansoor Yake with so much shock,tashin hankalin da yake ciki baya faduwa,ba zato suka ga Aliyu waxeer ya fisgota ya bata mari Hagu da dama kafin ya shakota,kara ya kasheta da ta cinnawa familyn waxeer wuta,da sauri Sufyan mansoor yayi kansa sai dai sha?ar da yayi mata bana wasa bane,tamkar ba namiji ba haka ya zama ya kasa kwatar kanwarsa a hannun Aliyu waxeer,ya isa ga Ammah yana fadin”ki yiwa mahaukacin yaronki magana rai biyu zai kashe idan wani abu ya sami kanwata shima sai na kashesa baxan jira hukuma ba,
Lokaci daya Ammah ta share hawayen idonta ta nufi Aliyu ta fisgosa lokaci daya ta wanke fuskarsa da mari,xaiyi magana ta Kara xabga masa wani marin.wani irin ciwo kirjinta keyi mata dauriya kawai take a gabansu, fadamin gaskiyya da gaske cikin dake jikin Yarinyyar nan naka ne ko bana naka bane.??”Juya girman ?addarar da ta canja masa rayuwa yanxu -yanxu yake har Abada baxai yafewa Areefa mansoor girman laifin da tayi masa ba,Kallon noory kawai yake wanda ko zai samu hop a wurinta tana zaune akan rug,da alama tafi kowa shiga tashin Hankali,baxa kayi magana ba??”Ammah ta fada tana daka masa tsawa,sau kusan ukku yake so ya buda baki yayi magana ya kasa ,
Ga maganar yana jinta aransa fitar ta ya kasa.
Hawaye yaji suna cika idonsa lokaci daya,meke damun sane??””Kar ya dauki girman laifin xina ya ?orawa kansa,kallon Ammah ya shigayi yana girgiza kai, kallon sa kawai Noory keyi addu’a kawai take aranta ya ?aryata ba cikin sa bane,shurun sa ya tabbatar mata da Areefa mansoor gaskiyya take fada,wani irin ciwo taji kirjinta nayi ciwon da duk wata macce wacce ke son mijinta da kishinsa xatayi duk lokacin da taji Aliyu waxeer ya ambaci sunan Areefa mansoor a gabanta take jin wannan ciwon,haka ta sha jin yarda Aliyu waxeer ke fadin”Yana son Areefa a gabanta ko a bayan idonta,baya shakkar fadin haka .hawayen Ammah sun kasa tsayawa tana gogesu wasu na xuwa,shurun Aliyu ya tabbatar mata da gaskiyya Areefa ta fada,Ammah ta kalli Aunty wacce ta dan ji tausayin Ammah,wanda uwa kawai ce xata ji irin wannan ciwo.”ku taso muje gidan baffan sa,
Ammah ta kallesa ido cikin ido take fadin”ka wuce muje kayi masu jagora su maimaita a gaban uban naka.Wani irin kuka yaxowa noory lokaci daya Rufe bakinta tayi da hannayenta tana girgixa kai kishi na cin xuciyarta, Addu’a take Allah ya cire mata son Aliyu waxeer daga yanxun nan ta huta,daki ta shige ta shiga rera kuka mai ban tausayi,Bayan sun gaisa da baffa dakyar Ammah tayi karfin halin fadin”wurinka suka zo danka ya jawo magana.”Ammah ta kalli Areefa mansoor wacce gaba daya hankalinta na akan Aliyu ,take fadin”fada ma mahaifinsa gashi zaune a wajen ,nan ta fada masa akwai cikin Aliyu waxeer a jikinta.
Kallonta kawai baffa yake tamkar wanda keson ya gano wani abu cikin fuskarsa kafin ya maida kallonsa ga Aliyu,da gaske cikin dake jikin Yarinyyar nan naka ne??”Baffa yayi maganar cikin karyewar murya shiru yayi masu tamkar yarda yayi a parlorn Ammah,hawaye yaji suna cika idonsa lokaci daya,ka buda baki kayi magana dan Allah Aliyu karka karyamin zuciya…….Baffa ya fada cike da karaya a muryarsa ,Ammah ta kalli Baffa tana fadin”baxai yi magana ba fa,tunda yasan ya aekata.”wannan Yarinyyar xata xauna tare dani harta haihu,
Daga ranar da ta haihu tayi Arba’in Aliyu xai Aureta,haka kuma dayan matarsa ya shirya bata takardarta,
Baxata kara zaman Aure da maxinaci ba.”
Baffa ya katseta yana fadin”kiyi hakuri kar abubuwa suyi masa yawa,idan yana son matarsa fa??”Ammah ta mike tsaye ta kalli su Aunty tana fadin”suje,a parlorn Baffa suka bar Aliyu tamkar an dasa sa a wajen,hawaye kawai ke xuba a idonsa,
Meyasa ya kasa ?aryata Areefa mansoor agaban baffansa,meyasa ya karbi cikin da shi yasan baida alaka dashi,me Areefa take nema da zata yimasa irin wannan sakayyar??”.,tashi kaje Aliyu Allah ya sauwakke,wata irin kunyar Baffa taxo ta rufesa wacce bai san yana yimasa ita ba sai yau.bai san yana kewar Khaleel waxeer ba sai yau da baya tare dashi,da yake Khaleel waxeer baya gari yaje Sokoto kan wani business dinsu,haka itama laylah tana Abuja ana bikin kanwarta,a wannan daren noory kawai yake son kasancewa tare daita,
Shi kawai xai sata jikinsa ya rarrasheta ya fada mata ba laifin sa bane,baya da alaka da cikin Areefa mansoor,yasan a duk inda noory take yanxu tana can cikin tashin hankali ,yasan kalar kishinta da yana da dama da ya dauketa daga gidan Ammah,
Sai dai yasan hakan ba mai yuyuwa bane…..acikin daren Ammah tasa aka gyara dakin da Areefa xata xauna harta haihu,su Aunty godia sukayiwa Ammah,har suka bar gidan suna jinjina karamci irin na Ammah,ko kadan basuyi tunanin haka abubuwa zasu xo da sauqi har haka ba,Sufyan mansoor na driving Yana fadin”dama kun daina mamakin saurin karbar ku da sukayi.ko kadan basa so a taba mutuncin gidan su.idan ma sunki karbarta baga yan jarida da media ba…..a wannan daren mutum ukku sunfi kowa shiga tashin hankali da jimami,Ammah Aliyu,da kuma noory idan sunce sunyi barci acikin daren nan,sunyi karya,tunda tayi sallar Asubah take zaune akan carpet idonta sun kumbura sabida kuka,duk lokacin da ta tuna akwai dan Aliyu waxeer kwance acikin wata sai taji duniar na birkice mata,idan tace bata kishin Aliyu waxeer xatayi karya,idan ta Runtse idonta hango Aliyu waxeer take tareda Areefa mansoor cikin wani irin moment da kwalkwalwar kanta baxata iya dauka ba,baxata iya sharing dinsa da wata macce a duniya ba,tunaninta ma yanxu yafi karkata da koda ma can Aliyu na neman wasu matan ,tasan Areefa budurwarsa ce wani irin rashin hankali xai saka Aliyu su aekata irin wannan babban xunubin,turo kofar dakin da take akayi.Ammah ce itama tareda Hijab din sallah ajikinta kallo daya xaka yiwa Ammah zaka san bata cikin natsuwarta,sallamar Ammah ta amsa tana tare hawayen idonta da suka kasa tsayawa,
Ta gaisheda Ammah cikin rawar murya,Ammah ta amsa cike da jin nauyin Nooriyah,da wani irin tausayin ta .
“Ban san kalaman da xanyi amfani dasu wajen baki hakuri ba Nooriyah ,ba kowace macce ce xataji abinda kika ji ba a jia kika kwana dashi acikin ranki,sai maccen da ?addarar ta fada kanta,baxan iya cewa komai akan wannan lamarin ba,shurun Aliyu ya tabbatar min da Yarinyyar nan gaskiyya take fada,haka baxan yarda ki cutu da Aurensa akan ki ba,dama Auren contract ne wanda akayi Auren dominsa ya riga yabar mana duniar meyayi saura,kara ya dauke maki wannan Auren kowa ma ya huta xan tsaya maki,Koda yaushe ina bayanki…….”kiyi hakuri Nooriyah dan Allah kiyi hakuri,hawayen idon noory suka kasa tsayawa itama Ammah hawaye ne a idonta,cikin rawar murya take fadawa Ammah meyasa take bata hakuri da laifin da ba ita ta aekata sa ba.hukuncin Ammah na karshe ne yafi taba mata xuciya ,baxata iya Rayuwar Aure da wani inba Aliyu waxeer ba,shine komai nata haka baxata iya kallon idon Ammah ta fada mata ta yarda ta raba Aurenta da Aliyu ba,A ganinta Ammah duk ta girmi waya’nnan Abubuwan a wajenta,
Amsar ki nake jira Nooriyah amsar ki kawai ce xata natsar da xuciyata ,dan Allah karki ce kin amince zaki cigaba da zama da Aliyu a matsayin miji,dan Allah karki bani kunya Nooriyah ,
Yanxu ne xaki nunawa Aliyu asalin ko ke wacece??”Haka nayi farin cikin da baki baiwa Aliyu budurcinki ba,sai nayi mugun koya masa hankali,
Ki kwanta ki huta ban Amince kafarki ta taka kofar kitchen ba tunda dukan mu muna azumi Areefa kawai ce xa’a ha?awa break fast,dagawa Ammah Kai kurum tayi.bayan fitar Ammah ta kwanta nan a kasan carpert tana tunanin maganganun da sukayi da Ammah.”
Kusan karfe tara na safe har daki Ammah taje ta duba Areefa wacce har tayi wanka taci uban kwaliyya sai kaice mai shirin zuwa party,ta ?ora kafa daya kan daya tana danna waya,ga kayan marmari nan ajeye an yanka su cikin madaidaicin tray ,Kallonta Ammah kawai keyi ta tashi xaune tana kallon Ammah tana fadin”Ammah ina kwana,Ammah ta amsa da lafia tana fadin”a kawo mata break fast ko zata je a dinning area tayi ,dan murmushi Areefa tayi tana fadin”muje nayi acan Ammah dama duk zaman ya isheni,Ammah tasa mai aeki tayi serving din Areefa.
Areefa ta kalli Ammah tana fadin”Ammah ke baxaki xauna muyi ba,
Ammah ta girgiza kai take fadin”ina azumi ne kin san yau Litinin,
Shiru Areefa tayi tana kallon Ammah wacce ta koma cikin parlor ta xauna tana ta kiran wayar Aliyu a kashe,
Har Areefa ta gama break fast ta dawo cikin parlor tana jan Ammah da hira,dai-dai lokacin Nooriyah ta shigo cikin parlorn suna hada ido da Areefa ta wani dauke kai,taxo ta xauna kusa ga Ammah,Ammah ta kalleta cike da kulawa take fadin”har kin tashi barci,ta daga kai tana fadawa Ammah ta tashi ta gaji da kwanciya a daki.da yake itama ta dauki azumin tamkar yarda ta ga Ammah nayi litinin da Alhamis…..Ammah ta kalli Areefa tana fadin ga matar Aliyu ku gaisa Areefa,wani kallo Areefa ta yiwa noory ,kafin tace ya kk
ganin yarda Ammah ke kallonsu yasa Noory tayi karfin halin fadin”ina lfy ya jikin ki.”babu abunda tace ta shiga danna wayar hannunta,Aliyu ne ya shigo parlorn dauke da sallama a bakin sa,
Tunda ya shigo parlorn idonsa ke kan noory,wacce kallo daya tayi masa ta dauke kai xuciyarta na bugawa da sabuwar soyayyar sa,Areefa na ganin sa ta shiga sakin murmushi,ya gaisheda Ammah ta amsa can ciki fuska babu walwala ,Ammah ta kalli Areefa tana fadin.”kin taba zuwa Asibiti??Areefa ta girgiza kai tana fadin”.sau daya tun lokacin da mukaje tare da Aunty Siddiqa,Ammah ta kallesa tana fadin
Ya kamata kuje Waxeer hospital a Buda Mata file,a dubata a san watannin cikin.”Ammah muje yanxu ma dan ina jin yana yimin wani iri.”Areefa tayi maganar tana kallon Aliyu wanda ya hade rai lokaci daya,jin haka yasa Nooriyah tabar masu parlorn Ammah ta dan yi murmushi tana fadin”toh kije ki shirya ki fito,shi dai Aliyu yyi tsaye a parlorn yana so yabi noory A daki sai dai ganin Ammah ya kasa,Ammah ta hade wani abu da ya tsaya mata arae kafin tayi breaking silent dinsu da fadin.”ina jiran takardar Nooriyah nan da kwana ukku,Ni har nayi mata miji.”a wani irin haukace ya juya yana kallon Ammah,
Xaiyi magana sai ga Areefa ta fito da dan mayafinta wanda ta axa a kafadanta sai kuma bag dinta,ta mikawa Aliyu bag din fuska bbu walwala take fadin”rika min Captain wani irin kallo yake yimata itama ta tsaresa da idanunta ,wani abu yaga yana fitowa cikin nata idanun,tamkar walkiya haka gabansa yayi mugun faduwa,karbar jakan nata yayi da sauri hannunsa ta kamo ta saka cikin nata,ta kalli Ammah da jikinta yayi sanyi lokaci daya tana fadin”Ammah sai mun dawo pls Ammah ki saka noory tayi min sakwara da stew na egusi,nasan ta iya girki sosai kisa tayi min dan Allah xanfi jin dadin nata fiye da na yan aeki.”Ammah ta sauke ajiyar xuciya tana fadin insha Allahu ,da haka suka fice daga parlorn tana sakin wani murmushi,Ammah xuciyarta na harbawa tabisu da kallo.Haka ya rika driving tana masa hira wani ya amsata wani yayi shiru,ta kallesa shaye da toka tana fadin”Yaushe xaka saki wannan Yarinyyar ba naji Ammah na fadin ka saketa ba .”me kake jira kuma.xan saketa Areefa ta bude masa ido tana fadin da yafi dai ,dan Ni bana sonta ko kadan,
Nasan kaima haka ??”ko ba haka ba ta fada tana tsaresa da idonta dake saka sa shiga cikin wani irin yanayi,muga wayar ka, mika mata wayar yayi tana fadin.”
Yanxu nake so kayi sakin nan a waya.”
Bari kawai na saketa tunda kai baxa ka iya ba,Ammah tana ta fadin ka saketa ka wani nace mata ko ka fara sonta ne??”tayi maganar cikin daga murya tana kara tsaresa da idanunta,cikin rawar murya yake fadin”ban fara sonta ba, typing ta shigayi a wayarsa
Tana fadin”idan Ammah ta tambayeka kai ka saki Yarinyyar nan,ka fada mata Ehhh kana jina??”da sauri ya daga kai,
Zuciyarsa na bugawa.
Taya xai saki noory ya Rabbi kana gani,
Typing ta shigayi cikin minti biyar ta tura ta basa wayar tana fadin”mu tsaya ka siyamin mitpie,bana awa biyu ban ci wani abu ba, ta fada tana rike da hannunsa tana murxawa,tun fitarsu Aliyu da ta shige daki take famar rera kuka,
Wanda ta rasa ko na menene.xuciyarta take jin tamkar xata fita sabida kishi,tana kokarin cire Aliyu daga ranta,sae kara sonsa takeji a xuciyarta ,
Xata fadawa Ammah ta amince Aliyu ya sauwake mata wannan Auren ,idan ta fita daga Rayuwarsa A hankali xataji soyayyarsa xata fice daga ranta batareda ta sani ba….Wayarta ta dauko taga sako ya shigo a wayarta,kuma da sunan Aliyu .da sauri ta buda sakon,
Abun da ta gani a wayar ya saka ta fasa wani irin ihun,da Ammah na zaune a parlor sai da taji ihun,girgixa kai ta shigayi tana fadin”pls karkayi haka Aliyu Dan Allah karkayi haka,banyi fushi ba hakama ina sonka a yarda kake ina sonka.”
Na amince ko mata ukku xaka aura a lokaci daya xan xauna da kai a haka,Ammah ta riketa tana girgixa ta take fadin”meye haka noory meya faru??”so kike kiyiwa Kanki illah sabida soyayyar da namiji,
Hannunta na rawa ta mikawa Ammah wayar hannunta,tana murmushi take fadin”kice idona ne Ammah ba gaskiyya bane,,kice soyayyar Aliyu da kishinsa suka mai dani a haka…

Littafin waminal Hoob na kudi ne# idan kika karanta min book baki biya ke ba yar halak bace,Allah ya isa!””Allah ya isa!!!
Account Details.
0004157137
Jaiz Bank
Asma’u Buhari Aliyu
Katin wayar MTN.ta wannan lambar#09060259200
Shaidar biya ta wannan lambar#08086207764

Back to top button