Hausa NovelsWaminal Hoob Hausa Novel

Waminal Hoob 19

Sponsored Links

Mom Aydah??: 19
Da mugun shock take
binsa da ido har motarsa tabar gate din gidan,hawaye taji suna Rolling Akan fuskarta wani irin ciwo takeji aranta,Kiran laylah ta shigayi a waya Amma Bata daga ba,sai ana ukkun ta daga cikin shesshekar kuka take fadin”he’s gone…….!”Da haka ta katse Kiran batareda ta jira Mai laylah xata fada Mata ba,a wannan lokacin beer kurum ce xatayi maganin damuwarta tana ganin farhaan Yana kiranta a waya ta kashe wayar duka Bata bukatar kowa da komai a yanxu,Shirin fita tayi taje ta nemowa kanta Abunda xai kwantar daita kar xuciyarta ta buga ganin komai take tamkar A mafarki…………..Kallonsa kurum take da mamaki har ya gama hada kayansa a trolley ya Mika Mata yace ta xuba kayanta na sati daya aciki ya tabbatar bag din xata ishesu na 1 week yasan ko wane lokaci Areefa Mansoor xata dawo gidansa yasan halinta Kara Yabar Mata gidan baxai saurareta ba wannan lokacin.sai ya koya Mata mugun hankali ita xata kirasa da mugayen sunaye munafuki Maci Amana.”dama tun a waya ya masu booking tsadadden hotel,ita dai Nooriyah bin wurin kurum take da kallo yayi matukar tsaruwa,ganin sunan dake jikin wurin ta juya da sauri tana kallonsa.hotel ya kawosu to meye dalilin yin haka”Kuma har kwana bakwai Bata ga fuskar yimasa tambaya ko daya ba,
Damuwarta daya ganin sun kama daki daya komai da komai akwai ciki ,ita damuwarta Taya xasu sharing daki daya.Bayan magrib ya fada Mata Idan tana bukatar wani Abu ko sako ta tura masa a waya xai sa akawo Mata xaije ya dawo ubangidan sa Yake yimasa Kiran gaggawa Addu’a yake Allah yasa ba tafia xasuyi ba. Dan muddin ya daga Yabar kasar Nan Areefa xata iya yin komai,Bayan ya fita ta samu tayi wanka harda su sakawa kofar key………lokacin da take Buda jakar kayansu har ajiyar xuciya ta sauke ganin kayan barcin da ta dauko duka masu kaurine ,bbu Mai bayyana tsaraici wasu riga da wando ta dauka ta saka farare sol.”dama da ta dauro Alwallah tada sallar ishaai tayi har Kusan 9 babu Aliyu bbu Alamarsa sa duk tabi ta damu,bata tura masa sakon tana bukatar wani Abinci ba, Amma yasa an kawo Mata Abinci Mai Rai da lfy,
Tayi xaune ita daya tana kallon Tv.sai wayar da tayi da Yah Kabir Wanda ya shiryu yanxu har Aliyu ya Samar masa gurbin karatu a N.d.A.dake kaduna ,dama Kabir Yana sha’awar xama soja Rashin wadata da kawayen banxa ya tarwatsa Rayuwarsa Kuma tunda Aliyu waxeer ya shigo cikin Rayuwarsa komai ya xama tarihi a kullum yanayiwa Aliyun Addu’a Allah ya cika Rayuwarsa da farin ciki fiyeda Wanda ya Basu ,ko mahaifiyarsa duk tsanar da ta nunawa Nooriyah yanxu ta xubar da makaman yakinta Addu’a take Mata da fatan Alkhairi acikin rayuwarta,aduk lokacin da ta Kira kawu balele Idan har Yana gida xai hadata da Adama ne ,a wannan fannin itama tanayiwa Aliyu waxeer fatan Nasara aduk kan lamarunsa Bata da abunda xata biyasa ,sai dai Addu’a dabin duk wani umurni nasa.”idan tana kirgar watannin Auren su har fargaba take,batasan mexata fadawa Y’an gidan su ba,ranar da Aurenta itada Aliyu waxeer yaxo karshe”………..Bata san ya xasu dauki hakan ba,dama kawu can ya tsani farhaan Shagari wacce bata san inda tsanar ta fara ba,kawu yace Dan iskane idonsa a tsaye suke baya basa girma komai a gadare yakeyin sa.murmushi kurum take Idan ta tuno hakan tasan kawun nata Bai fahimci Farhaan bane ,Dan Aliyu yafisa miskilanci da tsare gida,yayin da farhaan din keda fara’a da faram-faram da mutane……shikuma Farhaan acewarsa ya tsani kawu balele sabida xaluncinsa ga wacce yafiso fiye da komai a Rayuwarsa,
Kusan 10 Aliyu ya dawo ,har lokacin batayi barci ba,sannu da xuwa tayi masa kayan jikinsa Yake kokarin cirewa agabanta tayi saurin runtse ido gamida daukar pillow ta dannawa fuskarta ,Dan murmushi ya saki kunyarta na burgesa Amma ba Koda Yaushe ba.sai da taji ya shige toilet tayi saurin cire pillow tana sauke numfashi,Kusan minti Ashirin taji Yana kokarin bude kofa tayi saurin maida pillown Akan fuskarta,ya fito daure da towel babba da Dan karami Yana tsana jikinsa da ruwa,
“Idan numfashin ki ya tsaya bakina xan saka na xukosa Yar baka.”Yyi Maganar da wani irin sauti tana jinsa Amma Taki bude fuskarsa,Jin tayi an fisge pillow lokaci daya ta Buda ido ta kallesa gamida xaro ido tayi saurin rufe idon,har yau Bai saka kayan ba daga shi sai towel daure a kugunsa.xama yayi a kusa daita cike da tsokana,Yar Kara ta saki tana matsawa plz saka kayan ka.”ta fada still idonta a rufe to ki bude ido idan Baki bude idoba xan subbaceki.” yyi Maganar sounding so very serious Jin haka da sauri ta Buda idon da yasa ya saki wani irin murmushin da gefen kumatunsa suka lotsa murmushin da ya Kusan sumar daita ,Bai taba murmushi Wanda yayi masa kyau ba tamkar wannan.mikewa tsaye yayi ya saka kayansa na barci ya hau kan bed Yana fadin.””Ban yarda da kwana kan soofa ba Idan na farka na ganki ,xan maidaki Akan bed da Haka ya kwanta gamida Jan duvet ya rufe har fuskarsa,Kusan awa daya tana ta xama taji dai shuru da alamar yayi barci,kwanciyarta tayi kan doguwar soofa ta kashe wutan dakin…………..Koda safe da ta farka taganta kan bed a tsorace ta kalli gefensa barcinsa kurum Yake,wata irin kunya taji ta kamata ,da sauri ta sauka kan bed din xuciyarta na bugawa da gudu ta shige toilet gamida murxa key……kurawa fuskarta ido tayi cike da takaici take Fadi.” ,ki dawo hankalinki Areefa hankalinki nake bukata,Taya xan dawo hankalina laylah Bayan ke kika jawo yakai jikinsa wajen wannan kaxamiyar yarinyyar .” Baki sake laylah ke kallonta tayi mugun hade Rai take fadin ya shirya maki karya shine xaki yarda.”ta girgixa Kai xuciyarta na mata ciwo take fadin Aliyu baya karya laylah Bai tabamin karya ba Kuma baxai farayimin yanxu ba ,baya gidansa Babu ma kowa a gidan bana samun sa awaya.ya kikeso nayi laylah??”
Me xanyi maki tunda kin yarda dashi fiye Dani kinga karki Kara sakani a sha’anin ku Dan Allah duk Abunda kika yanke dai-dai ne ,da Haka tabar Mata room din Rai a bace.da wani irin kallo Areefa tabita har yau tana Jin kanta ya kasa dawowa dai-dai da ciwon kan da ta kwana dashi duk da a buge ta kwana,kwanan ta biyu bataga Aliyu ba Haka yasa tabi shawarar laylah ta koma Egypt ,ta fada mata yaudarar ta Aliyu kawai Yake Amma tabata lokaci su San yarda xasu bullowa al’amarin……..
10 month leap..watannin su goma da Aure xuwa wannan lokacin komai ya dai-daita tsakaninsu da farhaan Haka Areefa Mansoor ta basa hakuri ta fada masa baxata Kara xarginsa ba,cikin wannan lokacin ya shirya masu tafia gida Nigeria ya samu hutun wata biyu acikin Kuma wata biyun ne xaayi Aure a familyn waxeer Yar baffa xatayi Aure . shirye-shirye kurum Yake batareda ya sanarwa Noory ba,wacce yanxu ta xama Yar kasuwa Ammah ta sakata cikin harkar business dinta da take na online kudi Ammah xata turo ta siya English wears na Yara maxa da na Mata har na manyya bags shoe’s komai da komai na kyale-kyale ,
A tura gida Nigeria dama Ammah ta riga ta Buda manyyan shaguna a kaduna da Abuja ciniki ake na fitar hankali,sosai Nooriyah ta maida Hankali babu laifi ta xama Abunda Ammah take so ta xama Dan Aliyu har mamakin Wayewar Nooriyah Yake lokaci daya ,Idan bbu Kaya a London har kasar tukish take xuwa Dubai ma Haka ,
Haka sunje umra itada Aliyu wannan shekarar,
Ta xama wata irin big hajia.Alakarta da farhaan Shagari tana Nan bbu Abunda ya canja sae dai Bata jinsa aranta tamkar yarda take Jin Aliyu waxeer,dauriyace kurum take ana sauran kwana biyu tafiar su ya sameta a daki da laptop agabanta da farin glass Mai karama idonta gani wata biyu kenan da idonta suka fara samun matsala sabida yawan using da Hasken waya da Kuma laptop ,sanadin Haka sai da suka ga babban likitan ido ,har takai Idan Abu Yana daga nesa Bata cika ganinsa ba.dr.Ya dorata akan magani na wata daya still bbu Abunda ya canja dole akayi mata medical glass Mai karawa idon gani Wanda daga nesa xaka dauka na passion ne Wanda yayi Mata matukar kyau,ya fito da kyawawan fararen idanunta,wasu Kaya take turawa Ammah da tayo masu order dinsu daga kasar Pakistan dogayen riguna new designers.daga Kai tayi tana kallonsa,
Ya xauna kan soofa din dake cikin dakin Yana kallonta,Yana mamakin kwaxonta da son aekinta ,in har xasu samu Nooriyah acikin companyn waxeer ba karamin cigaba xata kawo masu ba,sai dai yasan mafarki kawai Yake Ammah baxata taba Bari ba,ko matar Khaleel waxeer Dan tafi karfin sune.turarensa duk ya gama cika Mata daki ta dago tana kallonsa,
Yayi murmushi yana fadin”jibi ne xamuje Nigeria Amma ban sani ba ko xaki samu xuwa,wara ido tayi gamida ture laptop din gabanta ,tareda wani irin farin ciki take fadin”meyasa baka sanarmin ba har sauran kwana biyu,Kuma ko daxun Nan munyi waya da Ammah ,Batool dukansu Babu Wanda ya fadamin.”dage gira daya yayi Yana fadin”dama surprising dinki xanyi oya ki shirya mufita shopping ,ta langabar da Kai tana kallonsa da kyakkyawan idanunta masu gigita Aliyu waxeer ,take fadin siyayyar me Kuma ina da kayan tsaraba Kusan trolley biyu na dde ina hada su ,kabarshi mutafi dasu.”Ya girgixa Kai Yana fadin ni ne bakiso Aljihuna yayi motsi haka bakyaso na Samu lada to naki wayon.!”ki shirya yanxu ya fada Yana bar Mata dakin murmushi tabisa dashi ,Rufe laptop din tayi wanka tayi ta saka wata rigar lace purple wacce ta kasance doguwar rigace sai mayafi wanda yayi shige da kayan,Buda Baki tayi tana kallonsa ganin ya xauna front seat ganin haka tasan meyake nufi.wato tayi driving dinsu ya dde da koya Mata mota,ta xagaya ta bude tana kallonsa tana fadin”Yallabai yau baxan iya tuki ba yau bayana na min ciwo ,Nasan da farhaan ne baxai barni nayi tuki ba.”ta fada cike da tsokana tana kallon reaction dinsa.
Lokaci daya ya wani irin fisgota ta fado kansa,Hade Rai yayi cike da kishi Yake fadin”mekika ce??”gabanta na faduwa take kallonsa ,
Hannunsa ya saka ya matse bakin da karfi karar axaba ta saki harda guntuwar kwallarta,Saboda bakida Hankali kina da Aure kike Kiran wani kato.”Gobe ma ki Kara ,yayi Maganar da wata irin Murya Mai tattare da kishi.da sauri ta kallesa ganin har yanxu tana kan jikinsa da sauri ta sauka ,ta rufe masa kofar ta xagaya ta xauna maxaunin driver taja motar suka bar gidan har lokacin fuskar Aliyu babu wani walwala.shopping yyi masu tamkar baisan xafin kudi ba,ita dai Nooriyah duk Abunda yace a dauka sai dai ta dauka karku ma ya Kara dalle Mata Baki,ta lura Abun laifi baya wuya a wurinsa musamman Maganar farhaan ta rasa dalili,Koda suka dawo mota bayan a saka acikin Booth ta tarar da Miss calls na farhaan ,gabanta ya Fadi yanxu Idan Kuma ta Kira xatayi laifi a wajen Aliyu silent ta saka wayar Idan sun Isa gida xata kirasa.sai ga Kiran farhaan ya shigo a wayar Aliyu dagawa yyi suna gaisawa,tana Jin yana fada masa baya gida ,ita dai Batace komai ba Bayan sunyi sallama ta juya tana kallonsa koxai ce wani Abu,
Ki kalli hanya karki xubar damu a titi.”yayi Maganar cike da bacin Rai ,hankalinta ta mayar kan titi itama ta daure fuska tana mamaki tana karawa duk wannan Fushin na minene…..?”koda suka koma gida kowa ya shige dakin barcinsa har washe gari Basu hadu ba,yinin ranar ma Basu xauna ba shirye-shiryen tafia suke sai ma yanxu takeji a bakinsa tare xasu tafi dasu laylah washe gari jirginsu ya daga nigeria shigowar yamma sukayi a Abuja suka sauka ,duka dama suna da gidaje acikin maitama sai washe gari suka karasa kaduna.Ammah tamkar xata goyasu Saboda farin ciki sai kallon Nooriyah take cike da damuwa ,ta xata ta ganta da ciki sai taga a kasin hakan,sabida da wuya suyi vedio call da Ammah sai dai waya ,sunfi yin vedio call da Batool mafi yawanci Kuma a school suke yin Haka,
Tare sukayi lunch da Ammah,cike da damuwa Ammah ta kalli Aliyu tana fadin”ko dai kaima baka shirya haihuwa yanxu ba tamkar yarda Dan uwanka ya fadamin A baya.”Ammah tayi Maganar cike da damuwa lokaci daya Laylah tayi mugun hade Rai, girgixa Kai Aliyu yayi Yana kamo hannun Ammah Yake fadin”Allah Bai kawo ba Ammah kiyi Mana Addu’a,ita dai Noory Batace komai ba saima saukar da kanta tayi a kasa cike da wani irin yanayi xuciyarta na bugawa.”kuyi wanka ku huta ku shiga ku gaisheda Baffan ku yayi Rashin lfy,ta kalli laylah da Nooriyah tana fadin kar wacce ta Dora girkin gidanta xan shirya Mana Abincin dare,da Haka ta Mike tana fadin”Allah ya hutar da gajia,wani irin banxan kallo laylah tabita dashi tana sakin wani irin murmushi,haka Aliyu yaji duk Babu ddi ganin halin da Ammah ta shiga,da sauri yabi Bayan Ammah har dakinta na barci ya cimmata ,xaune ya sameta cike da damuwa yaje ya durkusa agabanta ya riko hannayenta Yana fadin”Ammah damuwar Nan ta menene.”lokaci ne baiyi ba Idan lokaci yayi Allah xai bamu haihuwa duka -duka Yaushe akayi Auren.”girgixa Kai Ammah tayi cike da damuwa take fadin.”gobe ka shirya ni da Kai da matarka xamuje Asibiti a Auna ta agani Idan akwai matsala xuciyar Aliyu na bugawa Yake fadin”Ammah Baki yarda Dani bane.”kawai kayi yarda nace ,tashi kuje bangarenku ku huta Allah yay maku Albarka ,xuciyarsa na bugawa Yake fadawa Ammah Ameen.jin yayi kafafunsa nayi Masa wani irin nauyi ita dai Ammah binsa kurum take da ido ,tana ji ajikinta daga Aliyu har Nooriyah Bata yarda dasu ba.koma Menene xata bugi cikin Nooriyah taji gaskiyyar lamarin.”

Littafin waminal Hoob na kudi ne#500
Account Details
0004157137
Jaiz Bank
Asma’u Buhari Aliyu
Katin wayar MTN.ta wannan lambar
09060259200
Shaidar Biya ta wannan lambar
08086207764#

Back to top button