Hausa NovelsWaminal Hoob Hausa Novel

Waminal Hoob 26

Sponsored Links

ydah??: 26

Kallonsa kurum take,yarda yake jujjuya kansa sai abun ya bata daria ,lokaci daya kuma ya bude idonsa kallonta kurum yake cikin riga da wando na barci kalar sararin samaniya wanda sukayi mata mugun kyau,gashinta wanda bata kama da ribbon ba ya sauka har tsakiyyar gadon bayanta,kallonta kurum yake tamkar yau ya fara ganinta,
Ta bude masa hannuwa gamida ware masa ido ,wani irin blushing take saki a gabansa.lfy kake ta juya kae,kallonta yyi yana dakune fuska yake fadin”mafarkin Areefa mansoor nayi,
Lokaci daya yaga ta daure face,bata kara koda minti ?aya ba ta juya ta nufi kofar fita,ganinsa kawai tayi agabanta ya hadata da jikinsa yana kallon cikin idonta,lokaci daya ya subbaci gefen
Fuskarta ,yaja dogon hancinta yana fadin irin wannan hade rai haka Mrs Aliyu waxeer ta fisge kanta ta bude kofar ta fice daga dakin tamkar xata tashi sama,da ido ya bita yana shafa kansa,kallon agogo yayi ganin karfe biyar na Asuba,kai tsaye toilet ya nufa dan yin wanka,yana tuno mafarkin da yayi yana kara karya masa zuciya,kusan karfe biyu na rana tana ta xama a parlor Bata dade da dawowa gidan Ammah ba,
Door bell taji ana bugawa,ta dauka ma Aliyu ne.ta nufi kofar ta bude,ido biyu tayi dashi da wando sojoji ajikinsa sai kuma farar shirt Wanda ta kamasa sosai yayi kiba ya dora wani Quater million Wanda yyi mugun karbarsa
daka tsalle tayi da ihu ta rungumesa ,her one and only brother fighting mate ,and her best friend, kallon kurum Aliyu yake yana kallon yarda ta shige jikin Kabir kamar wata yar babyn tsana,gyaran murya Aliyu yayi da sauri ta saki Kabir din cike da jin kunya,Kabir ka xauna tunda na lura mutunniyar taka ta kasa koda baka wurin xama,Aliyu ya fada da dan murmushi a fuskarsa ganin irin kallon da Kabir din ke bin nooryn dashi, pencil Jean’s ne ajikinta,sai kuma wata yar bingilar riga kalar yellow mai hannun supergheti,Nooriyah xata kashesa da ransa
Kara ya dauketa da wannan shigar a gaban Kabir,Karasowa yayi ya dagata cak!”ta dakune fuska tana kallonsa,Kabir yayi murmushi Aliyu shima da murmushin a fuskarsa yake fadin”Kabir minti biyar ina xuwa Bara na fara kimtsa wannan kanwar taka,da haka ya nufi stairs ba tareda ya jira kabir mai zai fada ba,bai direta a ko’ina ba sai a dakin barcinta,ya hade rai yana fadin”dan baki da hankali haka xakije ki tsaya a gabansa kuma harda wani rungumarsa,yyi maganar da kishi acikin muryarsa,
Ta wara ido tana fadin”Yayana ne fa?”
Ya girgiza kai ya shiga jan wandon jikinta ta fasa ihu tana fadin”meye haka dan Allah,kicire wannan shegen kayan ,kuma traditional Kaya xaki sanyo ynxun nan da Hijab banda mayafi,
Ya fada yana bar mata dakin”,da wani irin kallo ta bisa tana murmushi,samun kanta tayi dabin umurnin sa, riga da skirt na atamfa ta saka,ta dauki Hijab har kasa ta saka ko turare bata saka ba,
Dan tasan halin fitinar Mutunen nata,koda ta
Koma parlorn Aliyu har ya cika gabansa da kayan ciye-ciye,
Ta xauna da murmushi A fuskarta tana fadin”Yaushe kaxo Yaya?”kaga yarda ka xama kato,
Fada min dame-dame suke baka haka??”Kabir ya harareta yana girgiza kai yake fadin”wai Captain ya kake handling din Yarinyyar nan,Aliyu murmushi ya shigayi yana shafa kansa,suna tareda Yah Kabir har kusan la’asar sai labarin cigaban da ya samu a makarantar da yake ya bata da kuma yarda Aliyu ya tsaya masa akan komai,kallon Aliyu kurum take cike da sabuwar kaunarsa.wanda xaiyi wuya ta daina………..sai da sukayi lunch tareda Aliyu yayi mata sallama,tamkar kar ya tafi gashi Aliyu ya hanata tayi masa rakiyya zuwa gida duk taji bbu ddi ,suna wucewa kiran Farhaan Shagari ya shigo a wayarta tamkar baxata daga ba sae kuma ta daga amma batayi magana ba,
“Idan har kina son Rayuwar mahaifiyar Aliyu waxeer ta tsira ki fito a motarki ke daya mu tattauna matsalar mu,idan kuma kinki
Xan dau mummunan mataki akanki xanje na fadawa Ammah wannan auren ba na gaskiyya bane,haka xan bi duk hanyar da nasan Aliyu xai yarda ke kika fadawa Ammah komai,ina da evidence akan duk maganganun mu ,yarda aka tsara Auren komai da komai
Xan turawa Ammah,
Da sunan ke kika tura.
Kuma xan turasa da sunan kine,kin san computer xata iya canja komai kudi kawai xa suyi aeki na baki nan da minti talatin xan turo maki da Address na wurin da zamu hadu,idan kika yi kokarin fadawa Aliyu baxai yi muna kyau ba.”Yana gama fadin haka ya kashe batareda ya jira mai xata fada ba,gumi ta shiga ha?awa iskan dakin taji yana yimata kadan,tasan Farhaan tunda ya fadi haka tasan xai aekata,
Kara taje taji meyasa yake son ya tarwatsa Rayuwar wa’yanda basu cancanci yay masu hakan ba,
Hijab kawai ta saka,
Dama car key dinta na hannunta ,na motar da Nasir waxeer yayi mata kyauta tun ta aurensu,
Kamar yarda ya fada cikin minti talatin ta isa cikin unguwar,
Waya ta daga ta kirasa
Ganin tayi an bude get Yana fada mata ta shigo da motar kallon gidan tayi ,tana gama parking ta fito daga motar ta shiga dube-dube taga ta inda Farhaan din zai fito,sai gashi ya fito tareda Areefa mansoor kowane dauke da murmushi a fuskarsa da mugun shock take kallonsu,
Har suka karaso gabanta, kallo daya Areefa tayi mata ta dauke kai tana fadawa Farhaan sai sunyi waya,tambayar kanta take me Areefa keyi tareda Farhaan acikin wannan gidan,mota Areefa mansoor ta shige tayi mata key,
Maigadi ya bude mata gidan ta fice da wani irin speed Farhaan Shagari ya kalli Nooriyah da take bin Areefa din da wani irin kallo ,mu karasa ciki
Ta girgiza kai take fadin”nan ma ya isa meyasa zamu shiga ciki.”bai jira mai xata kara fada ba ya shiga jan hannunta har zuwa entrance din shiga gidan,tsayawa tayi tana kallon parlorn babu abunda bbu cikinsa ya wurgata cikin soofas da sauri yaje ya sakawa kofar key xare key din yyi ,a tsorace ta mike xaune tana kallonsa ,ya xauna ya yyi crossing leg’s dinsa yayi mugun hade rai yana fadin”Yanxu ki fadamin gaki gani meye damuwarki.”meyasa kike shunning Dina haka??”mikewa tsaye tayi ta nufi kofa tana fadin”I’m not interested with ur silly drama Farhaan xoka budemin kofa.”wani murmushin takaici ya saki yana fadin”idan kinga kin bar gidan nan,an daura auren mune kuma a yau xan kawo karshen Auren naku,sai na gani idan xaki tsayar dani,
Kallonsa kurum take da tashin hankalin da yaki boyuwa acikin fuskarta,kiran Aliyu ya shigayi a waya kuma a vedio call sai dai Aliyu har ta gama karar ta ta katse bai daga ba,
Cikin minti biyu Farhaan ya tura masa sako a waya,sai gashi ya kirasa kuma a vedio call ,
Farhaan na daria yake fadin”ae nasan xaka kira sabida na fada maka Nooriyah na tare dani,Farhaan na dagawa ya dakune fuska haka yana hango sabon tashin
Hankali acikin fuskar Aliyu waxeer yake fadin.”ka hadani da noory yanxu Farhaan!””Ya fada yana daka masa tsawa,wane irin Rashin hankali ne noory xatayi haka,na haduwa da Farhaan”
da sauri nooryn ta karaso ta fisge wayar hawaye na xubar mata take fadawa Aliyu Farhaan yaudarar ta yayi,lokaci daya Farhaan ya fisge wayar gamida wullar da nooryn gefe ya kalli Aliyu ya hade rai yana fadin,nan da dare ka turowa noory takardar sakinta idan kuma kaki duk Abunda ya faru da mahaifiyarka kai ka jawowa kanka,
Yana gama fadar haka ya kashe wayar duka,
Nooriyah ta karaso gabansa ta daga hannu ta xabga masa mari ta cakumi wuyan rigarsa hawaye na xubar mata take fadin”mekake yi haka??yaushe ka xama haka,shi ya baka farin ciki kai meyasa baxaka basa koda so daya ba??”na tsani wannan halin naka Farhaan nayi mugun tsanarsa,kai da kanka kake kokarin ciremin soyayyar ka acikin xuciyata,a farkon haduwar mu na dauka Aliyu ne Mutunen banxa sai yanxu nake kallon banbancin ra’ayin ku.”idan kai akayi wa mahaifiyarka Abunda kake kokarin yiwa Aliyu xakaji ddi?”
Stairs Farhaan ya nufa da wata irin zuciya,
Sai gashi ya fito da kudade acikin wata yar karamar jaka,xip din jakar yaja sai da ya fice daga cikin jakar,kudine sosai acikin jakar rafar Naira dubu-dubu,fiddosu ya shigayi yana jefa mata ajikinta,yana fadin sadakin kine Noory naira miliyan biyar ne,
Haka ya cigaba da watsa mata kudin,sai da suka kare kaf.
Ya dawo gabanta yana fadin”nawa Aliyu ya biya sadakin ki?ki fadamin ya fada yana girgiza shoulders dinta tamkar xai ballasu,ba sadaki shine Aure ba??”ga sadakin ki nan,
Meyayi saura.”haka kawai zan xuba maki ido wani shege ya ware leg dinki ya shiga,duk tanadin da na dde ina yimaki
Ya tashi a banxa,
Xanyi testing dinki yau noory tunda yaki yarda ya rabu dake,xan rabaku ta karfi.”idan har na gano Aliyu ya taba gonata wlhi tallahi sae na kasheki shima sai na kashesa!”
With so much shock take kallon Farhaan Shagari , addu’a take Allah yasa mafarki take,jikinta bbu inda baya rawa sabida tashin hankali.hannunta ya shiga ja har zuwa master bedroom dinsa, sai da ya tabbatar ya sakawa kofar key………tana kallonsa ya shiga hada Allura gabanta na mugun bugawa take kallonsa,cikin rawar murya take fadin”me xakayi farhaan,mekake kokarin yimin??”tayi maganar cikin muryar kuka,bugar dake xanyi,nayi aeki da gangar jikinki tayarda baxaki yimin gardama ba.”Allah ya tsine maka albarka ya tsinewa mugun nufinka Farhaan,
Tsinanne kawai!!”ta fada masa cikin muguwar tsawa,hannu Farhaan ya daga ya xabga mata mari.baya tayi xata fadi ya fisgota
Hannu yasa ya yaga Hijab din jikinta ta karfin tsiya ,yana rike daita ya dauko allura ya danneta da karfi ya saka mata ita cikin damtsen hannunta,
Kallonsa kawai Noory keyi hawaye na xubar mata ta tsani Farhaan Shagari tsanar da bata taba yiwa waninsa ba.cikin minti biyar Allurar ta fara yimata aeki daukarta Farhaan yayi ya dora akan lafiyayyen bed dinsa ,sai wani bin jikinta yake da kallo
Yana hadiyar yawu,
Vedio call ya kira Aliyu waxeer yana dauka ya fara shafa fuskar noory,lokaci daya Aliyu ya mike tsaye jikinsa na mugun kadawa,bai taba tunanin Farhaan dan akuya bane sai yanxu,
Kayi sakin ko na afka mata da auren naka.”
Yana hango kwallar bakin ciki ,acikin idanun Aliyu waxeer yayi murmushi yana fadin”ina jira xan kashe wayar,bai jira mae zai kara fada ba ya kashe wayar,
Zuciyarsa yaji tana kokarin barin jikinsa kusan sau biyar yana gwada rubutu a takarda ya kasa,lokaci daya yayi jifa da takardar hannunsa…..Kara ya tari Ammah ya fada mata gaskiyyar komai yasan Ammah baxata juya masa baya ba,inhar tana son yayi zaman Aure da Nooriyah na har Abada ,a shirye yake ya kara daure igiyoyin Aurensa shida noory,
Zai gama da matsalar Ammah kafin ya koma kan Farhaan Shagari zai nuna masa shi karamin dan iskane,
Da haka ya dauki car key da wani irin speed ya nufi gidan Ammah zuciyarsa na wani irin bugawa………da Batool waxeer ya fara cin karo, sauran kadan
Batool waxeer takai kasa,taja da baya tana kallon Aliyu waxeer.am going to slap ur face Batool waxeer,bakya kallon gabanki ne.”ta dafe kanta tana fadin”dai-dai nake tafiana yayah.”kai dai ne baka kallon gabanka,Finally gaka gabana Yaya alkawarin da kayi min dan Allah.”gobe zamu je siyan anko,wani kallo yayi mata yana fadin”Anjima Batool Banda yanxu,xai wuce tasha gabansa tana fadin”Yaya me xai Hana yanxu ko jia haka ka fadamin busy-busy ka bani ATM din naka naje na cira,dafe kansa yayi maganganun Batool na kara jamasa wani ciwon kai,car key dinsa ya mika mata yana fadin akwai wani ATM.dinsa acikin mota taje ta duba,karbar key din tayi ta fice parlorn da gudu,kowane taka ?afarsa da xaiyi zuwa wajen Ammah sai zuciyarsa ta buga,
Koda ya samu Ammah tana waya,
Kasa Karasowa yayi cikin room din,Jin yake tamkar ya juya ya koma……Ammah ta aje wayar tana kallonsa take fadin”lafia?dukkan jarumtar sa ya hado ya shigo cikin dakin,
Ya samu waje ya xauna lokaci daya ya riko hannunta ,ita dai Ammah kallonsa take da wani yanayi da take hangowa acikin fuskarsa,Ammah!!!”ya kirata da dukkan kwarin gwiwarsa,
“Dama akan Nooriyah ne,cike da tsoro Ammah ke fadin”meya sameta.”kallon reaction din Ammah kawai yasa zuciyar Aliyu ta karye,ka Amsa min meya samu Nooriyah yarda yaga Ammah ta rude lokaci daya yasa ya Rungumeta sosai,
Zuciyarsa tana bugawa cike da wani sabon tashin hankali,
“Aliyu ya dago daga jikin Ammah ya ware mata ido,yana sakin daria A hankali yake fadin”Ammah haka kikeson noory?”Ya turo baki yana fadin”kinfi son noory Dani kou.??’Ammah taja kunnensa da karfi tana fadin”naxata wani abu ya samu nooryn,bbu abunda ya sameta dama ina son na Buda Restaurant da sunan Noory……”!ya kika gani Ammah?
Ammah na murmushi take fadin”matarka ce Aliyu xaka iya yimata kyauta fiye da hakan,
Ina son cikin jikinta yayi kwari na shirya mana tafia umra mu ukku ,Nooriyah laylah,da Ni kuma muyi Addu’a Allah ya kawo mana baby lafia,
Ya kawo mana mai suna Abba lfy.”Ammah ta fada tana tara kwallar farin ciki aciki idanunta,da sauri ya rungume Ammah………baxai iya karya zuciyar Ammah yanxu ba ya kamata ya nemo Khaleel waxeer a duk inda yake ya fada masa gaskiyyar Aurensu da Nooriyah maybe Khaleel waxeer xai iya samo masa solution,
Ya mike tsaye yana fadawa Ammah xai fita ,Allah ya kiyaye hanya tayi masa tana fadin”ta kira wayar noory kashe ya shafa kansa xuciyasa na bugawa yake fadin”tana barci ,da haka ya fice daga Room din waya ya fiddo yana neman layin Khaleel waxeer….

_idan kika cigaba da karanta book din nan batare da kin biya Ni hakkina na dari biyar ba ke ba yar halak bace,masu fitar min Allah yay maku fiye da abunda kuka yimin.”_

Littafin waminal Hoob na kudi ne #500
Account Details
0004157137
Jaiz Bank
Asma’u Buhari Aliyu
Katin wayar MTN.ta wannan lambar#09060259200
Shaidar biya ta wannan lambar#08086207764

Team#WM??
Team#NooryAli forever#

Back to top button