Hausa NovelsWaminal Hoob Hausa Novel

Waminal Hoob 24

Sponsored Links

Waminal Hoob_* 24

_Asmy b Aliyu_

Baki wangalau Aunty siddiqa ta bude tana kallon Areefa mansoor da wani irin shock,
Cike da takaici siddiqa ke fadin”ki rasa da wanda xakiyi tarayya sai Farhaan Shagari,
Wai meke damun kwakwalwar ki.”Siddiqa mansoor tayi maganar cike da wani sabon bacin rai,hawaye na xubarwa Areefa mansoor take fadin”A dan iska na tarar dashi kuma bariki ta hadamu,toh yanxu meye mafita.”wani daria Areefa tayi wacce bata tattare da nishadi take fadin”kin san irin maganganun da ya datsamin a waya.”lokaci yaxo da ya kamata na nunawa Farhaan Shagari the other bad side Dina,
“Yanxu yaji cikin nasa ne ya yarda amma so yake a xubar ni kuma ban shirya mutuwa ba,idan har aka xubar da wannan shine ciki na bakwai kuma Dr.Saleem Bakura ya tabbatar min muddin na cire wannan cikin xan iya rasa rayuwata gaba daya,kuma Ni ban shirya tafia yanxu ba,sai dai ban fadawa Farhaan hakan ba.
“Toh yanxu meye mafita??”Abunda yasa naxo Kaduna kenan ina so kibani shawara dan ko Aunty bata san ina da shigar ciki ba,
“Kin san watarana munafuka ce xata iya fadawa Abba ta kowace hanya,kuma kin san hawan jininsa kar zuciyarsa ta buga ,duk kin jina ina kaunar mahaifina bana son Abunda xai tabasa,daga shi sai ke sai Yah Safwan ku kawai ne nake kalla naji sanyi.dama Aunty kuma ruwa biyu ce ,a munafurci watarana ta nuna mana soyayya watarana akasin hakan,nasan idan Safwan mansoor yaji wannan zancen kasheni xaiyi.”
Bakyaji Areefa magana daya bata ta?a zama acikin kunnenki,kudi kawai xaki kawo mu tafi wajen malami na ae mana aeki cikin ruwan sanyi,samu xamuyi ya kwantar da cikin bayan Aurenki da Aliyu sai ya tadasa,wani murmushin takaici Areefa mansoor tayi tana fadin ,nifa kin san bbu hannuna acikin wannan biyan malamman a cinye maka kudi bbu biyan bukata,wani kallo siddiqa mansoor tayiwa Areefa din,
Tana fadin toh kina tunanin Aliyu xai Aureki da cikine.”nasan ko an kwantar da cikin nan Aliyu bazai Aureni ba baki san waye shi bane,Ni nasan ta yarda xanyi kawai na samesa,plan Dina na farko ya saki wannan Yarinyyar,na biyu xan kutsa cikin rayuwarsa da dukkan kwarin gwiwata,xan fadawa mahaifiyarsa kai tsaye shiya yimin ciki xan nuna mata Evidence a wayana ko ta tsiya kota balai kin ga dole ya Aureni,nasan Mahaifiyarsa bata goyon bayan xalunci.!”bayan nan xan dawo muje wurin malamin naki a rufe min bakin sa dana mahaifiyarsa na rika juya su,dan bana son matsala ko kadan,
Abu na karshe xan gargadi Farhaan Shagari da babban murya ,baya da alaka da cikin dake jikina har Abada……….idan kuma har yabani matsala ,xan tarwatsa Farin cikin Rayuwarsa wanda nasan Nooriyah ce.”Kallonta kurum siddiqa mansoor keyi tana mmkin makircin kanwarta ta,gyada kai ta shigayi tana bata dukkan kwarin gwiwa.
Bari nayi wanka naje naji ya xamuyi da Farhaan kara ya uxurawa Aliyu yayi maxa ya bada takardar sakin nan…..
Tsaresa da ido Areefa mansoor tayi xuciyarta na bugawa,kar dai Aliyu ya fara son Yarinyyar nan,cike da gajia da xancen Farhaan Shagari ke fadin”wai meke damunka Besty tsoron fadawa Ammah kake yi ko menene??”idan baxa ka iya ba Ni xanje na fada mata gaskiya kaga xata fahimce mu kuma nasan komai xaixo muna da sauqi,
Da sauri Aliyu waxeer ya shiga girgiza kai yana fadin”ku bani nan da sati Daya xan gyara komai,da sauri Areefa ta dafa kafadar sa take fadin”bby sati Daya yayi yawa,bakaji yarda Abba ke maganar ka fito ayi maganar Auren mu ba,insha Allahu Ammah baxa taji komai ba auren contract ne kuma ya riga ya kare….”ta fada tana wani shafa chest dinsa ,tana ganin yarda noory ke bin hannun nata da kallo tana wani hade rae,
Farhaan ya kalli Nooriyah da hankalinta baya kanta ya dan shafo gefen fuskarta yana fadin”baby babu Ruwan sha.”saurin jada baya tayi karshe mikewa tayi ta nufi kitchen dan daukowa Farhaan ruwa tamkar yarda ya bu?ata ,bayanta yabi da mayen kallo yarda yaga kugunta yyi wani irin cika ya hade wasu yawu,duk da akwai mayafi ajikin nooryn haka traditional kayane ajikinta Basu fidda mata da tsaraici ba,Aliyu yana kallon yarda Farhaan ya kasa dauke idonsa akan noory din har ta shige kitchen din,da sauri nooryn ta fito daga kitchen din Dan tasan ba karamin aekin Farhaan bane ya bita a baya,ta aje masa ruwan haka fuskarta babu wani Annuri ganin yarda Areefa ke shigewa Aliyu yana kona mata xuciya ta kalli Farhaan tana fadin xanje nayi sallah kana bukatar wani Abu.”karya kawai tayi masa duk da tana fashin sallah amma ta gaji da xaman parlorn bazata iya jure kallon yarda Areefa mansoor ke taba Aliyu waxeer a gabanta ba,Farhaan ya mike tsaye ya tako zuwa gabanta yana kallon cikin fuskarta tamkar mai son gano wani abu,ya saki murmushi xai subbaci kuncinta tayi saurin kaucewa da sauri tana wani hade rai,kallon da yaga tana yimasa yasa ya shiga shafa kansa Yana fadin”Sorry manta komai da kowa nake idan ina tare dake.”sai munyi waya,da haka ta juya batareda Tayiwa Farhaan magana ba,duka su ukku suka bita da ido…..kije Farhaan ya saukeki a gida xamu fita da Khaleel waxeer,
“Areefa mansoor ta dakune fuska tana fadin”da daren xaka shigo,yana shafa kansa yake fadin”idan na samu lokaci,karka shanyani dan Allah ……”Ta fada tana subbatar gefen kuncinsa,sai da yaga fitarsu ya juya ya koma cikin gida kai tsaye stairs ya nufa kofar dakinta ya bude xaune take gefen bed……”tayi mugun hade rai kiris take jira ta fashe,tayi crossing hands dinta Akan kirjinsa,tuno yarda Areefa mansoor ke taba Aliyu waxeer kurum yana saka xuciyarta ciwo.”Haramun ne namiji ya kai hannunsa jikin maccen da ba muharramar sa ba,Karasowa yyi gabanta gamida zama gefen zai Jawota jikinsa tayi saurin matsawa tana yi masa wani irin kallo.”Are You jealous Yar baka.?yyi Maganar da Muryar tsokana ta bude hannu gamida ware masa ido take fadin”Allah ya kiyaye nayi kishin ka,gaskiyya kawai na fada dani ce na rika taba Farhaan da yanxu ka cika gidan nan da ihu,Yyi murmushi yana girgiza kai yake fadin”ae ni namiji ne,
Kuma ae ita xan Aura.!”da wani irin sauri ta dago tana kallon sa,dauke kanta tayi ta nufi hanyar toilet a fusace Yana kallo ta wani bugo kofar,da yaga bata da niyar fitowa yabar mata dakin,yana mmkin karfin halinta wannan fushin duk na menene?”da dare ya kashe wayarsa kar Areefa Mansoor ta damesa Kusan hakane,kiran da tayi masa baya da adadi, number sa a kashe.
Wani murmushin takaici tayi tana fadin”kwana kuma nawa ya rage Aliyu,ka gama duk wani gudun ka,sai na koya maka hankali wlhi.”
Har sati Daya Aliyu ya kasa samun solution,har wata irin rama yyi ya axa kasumbar da bbu gairi bbu dalili,Ramar da ta daga hankalin Ammah.wata ranar Assabar Ammah ta saka sa a daki,ta kallesa itama da Tata kalar damuwar take fadin”kana da lafia kuwa Aliyu meke damunka??”ka rame kai da matarka tamkar waya’nda suka kwanta ciwo,duk kun daina walwala ita xan iya yimata uzuri sabi da juna biyu take dashi,kai kuma duk wannan Ramar ta menene?”Ammah tayi maganar da Muryar Rarrashi, kallon Ammah yyi zuciyarsa na cigaba da bugawa,
Jin yake tamkar ya fada mata gaskiyya sai dai bai san mexai faru idan ya fada mata ba.kiyi min Addu’a dan Allah Ammah.”da sauri Ammah ke fadin”Ni ban isa naji damuwarka ba kenan.”Yana girgiza kai muryarsa na karyewa A hankali yake fadin”Am sorry Ammah.sauke ajiar xuciya Ammah tayi tana shafa kansa take fadin”Allah ya tsareka a duk inda kake ya kuma shiga lamurranka ya kawo ma sau?in damuwarka,Ya dan ji sanyi aransa yana murmushi yake fadin”Amin Ammah.
“Na turawa Nooriyah mai aeki ta dawo min daita batayi mata bane?Ammah ta fada tana kallonsa,Ya girgiza kai yana sakin murmushi shi yasan dalilin da yasa ta kori yar aekin shima da yayi mata magana,budar bakinta take fadin”ita bata son yan aeki farare.”tayi maganar tana wani hade rai,daria ta baiwa Aliyu da ta fadi haka da mmki yake fadin”toh meyasa?saboda kai,ya dde yana juya kalmar sabo da shi,,tambayar kansa ya shigayi ko noory ta fara sonsa ne??”da sauri ya girgiza kai yana fadin ae xaiyi wuya ta sosa…….. shi kawai ne ke kidin sa da rawar sa,bata ma san yanayi ba.Yau tun da safe Farhaan ne ya fara buga masu kofa,
Cikin magagin barci noory taji ana buga kofar,Hijab din da tayi sallah dashi ta saka,
Ta sauka down stairs,
Cikin muryar barci take fadin”Waye?shiru taji haka aka cigaba da buga kofar,budewa tayi kafin tayi magana ya wani shigo cikin parlorn yana hadata da jikinsa tamkar maye sai sauke numfashi yake,A haukace yake fadin”ina Aliyu yake?
Idan ba so yake naje nayi xina ba ya sakar min ke mana,haba wannan wane irin Abu ne??”wlhi tallahi hakuri na ya kare idan na tafi dake sai yace ya sakeki maxa jeki kwaso kayanki,wani irin warin sigari taji Farhaan din nayi haka tamkar baya cikin natsuwarsa yake magana,fisge kanta tayi tana binsa da wani shegen kallo.”zama tayi acikin soofas ta ?ora kafa daya akan daya ta hade rai,tana kallon Farhaan da yyi tsaye yana kallonta,Farhaan baxan iya Auren ka ba.”tayi maganar da dukkan kwarin gwiwarta,wani irin Daria farhaan ya fashe dashi yana kallonta da sabon bacin rai yake fadin”saboda kin fara sonsa??”ta girgiza kai cike da takaici take fadin”ba saboda Aliyu waxeer bane,saboda mahaifiyarka ne,Auren mu baxai taba Albarka ba.muddin mami bata saka masa Albarka ba.”kuma ni baxan iya barin iyayena na bika mu gudu wani wurin ba,daga hannunsa yyi cike da mugun bacin rai xai xabga mata shegen mari yaji an rike hannun,kallonsa yake zuciyarsa na tafasa yake fadin”ko mai sai kace ka kaiwa macce Hannu ,ba girman ka bane pls ka xauna muyi magana ta fahimta.”Aliyu waxeer yyi Maganar sounding so very cool.”ya cakumi kwalar rigarsa Yana xare masa ido yake fadin”baxaa xauna ba,na baka nan da Awa Ashirin da hudu ka bata takardar sakinta ko wallahi duk Abunda ya sami mahaifiyarka kar ka xargeni.”da haka ya nufi kofa tamkar zai tashi sama,da wani irin shock suka bisa da kallo musamman Aliyu waxeer da yaji kafafunsa tamkar baxasu iya daukarsa ba,sama ya nufa da gudu sai gashi cikin minti biyu ya sauko rike da car key a hannunsa,da ido noory ta bisa har ya fice daga parlorn a yinin ranar cikin fargaba ta yini da tashin hankali ,bata san iya adadin kiran da Tayiwa Farhaan Shagari a waya ba ,amma bai daga ba.Har dare bata saka Aliyu cikin idonta ba,.sai bayan sallar ishaai ya shigo gidan tana zaune a parlor ta xubawa Tv ido Wanda a xaharin gaskiyya kallon tv.kawai take xuciyarta bata tareda daita,a hargitse ya shigo gidan kallo daya xakayi masa kasan yana cikin damuwa,
Kallo daya yayi mata ya nufi stairs xuciyarta na bugawa take binsa da ido,bai jima da shiga master bedroom dinsa ba,tayi knocking ya bude kofar a fusace ya fisgota cike da jin haushinta yake fadin”menene kuma??”pls ki kyaleni na Sha iska,ya fada da tsawa yana turata waje gamida buga kofar, ,xuciyarta na rawa take kallon kofar.
Haushinta yakeji duk ita ta saka su cikin wannan balain da bata shigo cikin Rayuwarsu ba,da duk waya’nnan Abubuwan basu faru ba,idan wani Abu ya faru da Ammah baxai taba yafewa kansa ba,
Dakinta na barci ta nufa tuni hawaye suka fara yimata Rolling Akan fuskarta…….Mami har tayi shirin barci kusan sha daya da rabi na dare bata ga shigowar motar Farhaan ba,tana tsaye jikin window acikin master bedroom din Mai gidanta tana kallon compound din gidan,
Cike da matsanaciyar damuwa,shi dae daddy da ido kurum yake Binta ganin tunda ta shigo room din nasa bata xauna ba,gyaran murya yyi yana fadin”lfy kin kurawa window ido,wakike jira.”cikin sanyi murya mami ke fadin”Farhaan nake jira daddy yau xaiyi mugun yabawa aya xakinta,komai na harkar auren sa nice gaba yaki ya saka hannu ayi komai dashi,sai kace Ni xan auri Yarinyyar Ni xan xauna masa daita,
Tun shekaran jia nake lallaba sa,har kunyar gidan su Yarinyyar nakeji wlhi ,anyi dashi zai sameta ayi masu pree weeding ficturers .Ashe yaron nan bai jeba sai yau uwar Yarinyyar ta kira ta fada min sai dai nayi mata karya,daddy ya girgiza kai yana fadin”ae kun fi kusa.
Jin horn yasa ta koma jikin window ganin yarda Farhaan Shagari ya shigo a guje da motar yyi mugun daga hankalin mami saura kadan yabi takan maigadi da yyi tsalle ya fadi gefe daya,ganin yanayin da Farhaan ya fito daga motar yasa mami tayi saurin dafe kirjinta tana ambaton Allah…. Addu’a take Allah yasa ba gaskiyya bane ,Farhaan baxai yi shaye-shaye ba har ya shigo da kwalbar giya a gidan ubansa,jin tayi wani duhu na rufe idanunta,Ita dai ta bude ido ta ganta jikin Alh.omar Shagari,da sauri ta mike xaune tana fadin”Daddy barci nayi,mafarki ne kou.”Farhaan dina baxai taba xama dan giya ba.”ta fada tana mikewa tsaye da dukkan karfinta,Alh.omar ya rikota ,ina kuma xakije??”xanje na duba Farhaan,toh a haka xaki fita ki saka Hijab Mana,ya fada yana mika mata Hijab tare suka nufi sashen Farhaan din,Abunda suka fara cin karo dashi kwalaben giya ne an faffasa su,da sauri ta kalli isah wanda shine ke kula da bangaren Farhaan Shagari,cikin tsawa mami ke fadin”isah meye haka menake gani ta fada da Muryar tashin hankali,Alh.omar ya girgiza kai yana kallon Farhaan din dake kwance akan rug ko hannunsa baya iya dagawa,ya shata har tayi masa yawa.Xubewa mami tayi akan soofa hawaye ne suka fara Ambaliya akan fuskarata addu’a take Allah yasa mafarki ne……….da wani irin barcin rai Alh.omar Shagari yabar part din na farhaan har Kusan 2 na dare Mami na bangaren Farhaan har zuwa lokacin bbu alamar zai farka,idon mami sun kumbura sabida kuka,isah ta kalla tana fadin ya kwana da Farhaan din xuwa safe xata shigo ,da ladabi isah ya amsa mata aransa kawai yake fadin”Allah kadai ne zai sakamin sabida wani bugagge an hanani barci ,mami na fita ya koma kan doguwar soofa ya kwanta yana fadin”nima na dana waya’nnan kujerun kara nasan banyi gadin banxa ba,ga kuma Ac.ko a haka Allah ya kwatar min hakkina ya fada yana washe baki,ba tareda ya kara bin ta kan Farhaan Shagari ba….

_duk wacce ta karanta min book bata biya ba,Allah ya hanata abunda take nema,Allah yabi min hakkina tun a dunia_!”

Littafin waminal Hoob na kudi ne#500
Account Details
0004157137
Jaiz Bank
Asma’u Buhari Aliyu
Katin wayar MTN.ta wannan lambar#09060259200
Shaidar biya ta wannan lambar#08086207764

Back to top button