Hausa NovelsWaminal Hoob Hausa Novel

Waminal Hoob 3

Sponsored Links

*Waminal Hoob*_ 3

PAID BOOk
Free page.

_Asmy b Aliyu_

Tun daga karkashin xuciyarta takejin wani bacin rai na saukar mata,da gaske Aliyu waxeer ya daina yayinta kwana biyu duk yabi ya canja mata, ido biyu sukayi da batool waxeer wacce ta crossing hand’s dinta akan kirjinta tana bin Areefa mansoor da wani irin kallon da ta kasa fassara sa.lokaci daya ta wara hannayenta gamida buda ido tana sakin daria,Dan Allah bakiji kunya ba.”kinxo wajensa hira ya koraki kina matsayin macce,duk wannan ajin da kike tunanin kina dashi ina yake?”sai na hadaki da Ammah billah.”batool ta fada tana wani bude mata ido,bata karabi takan Areefa ba ta juya da sauri tabar part din Dan taga yarda Areefa mansoor ta fusata .
Yana kwance cikin doguwar soofa daga shi sai farar vest da trouser ba barci yake ba,sai dai idonsa a rufe suke ya kure A/c da volume din T.v tamkar zai tada gidan so yake koda so dayane ya manta fuskar bakar Yarinyyar nan,amma ya kasa da ya rufe idonsa ita yake gani,yana cikin wannan yanayin yaji ana buga kofar tamkar xaa ballata ,
Ya Riga da yasan bbu mai wannan Aikin sai batool waxeer.yana buda kofar ya wani fisgota tamkar xai rabata gida biyu,
Wayyoni Yah Aliyu ko ba Ammah bace tace na kira ka.”ta fada tana wani turo baki gamida shigewa jikinsa,cike da balai da masifa yake fadin sau nawa xan fada maki ki daina bugamin kofa??jikinta ne ya kama kyarma ko ba Ammah bace tace na kiraka.”turata yayi da karfi ta dafa bango tana kallonsa a tsorace,ya daka mata tsawa yana fadin ba magana nake maki ba.”hannu ta fara yarfi dashi tana fadin sau dayawa mana……..ta fada tana jada baya gamida yarfi da hannunta,Am sorry karka dakan Dan Allah.”da haka ta ceci kanta ta fita da gudu,kwala mata kira ya shigayi tayi masa banxa.
Yarda ta shigowa Ammah a falo yasa Ammah kallonta tana girgixa kai take fadin kin jawo rigima kou.”ko takan Ammah bata bi ta nufi nata dakin……da sallama Ya shigo falon ya nemi wuri ya xauna wani irin kallo Ammah ke binsa dashi ganin yarda ya shigo mata falo,jeka ka sawo jallabiyya Aliyu nan ba cikin barak bane.”
Ammah mana.”Ya fada yana wani hade rai,
Wani irin kallo Ammah ke masa ya Riga da yasan ma’anar kallon bbu musu yabar falon bai dde ba sai gashi sanye da brown jallabiyya Wanda yayi mugun karbarsa ,mai guntun hannu .sai da ya xauna ta kallesa tana fadin wacece taxo part dinka??”shaye da toka yake fadin Ammah wake kawo maki irin waya’nnan maganganun??”ya xaayi macce taje part dina.”Ya fada yana wani hade rai,
Karya nake kenan??”Ammah plz…………”yyi maganar cikin daga murya da alamar ya manta agaban wa yake,yana mmkin yarda baya iya controlling din fushinsa,
Ni kake dagawa murya don ubanka.”Ammah ta fada cikin bacin rai,Am sorry ya fada cikin sanyin murya yana kamo hannunta,fisge hannunta tayi tana yimasa wani irin kallo take fadin Aliyu na baka nan da sati daya ka tsaida maganarka akan Yarinyyar nan,xanyi magana da baffanka ajey aga magabatan ta ya ,na gaji da wannan rashin kunyar xanyi abunda kake so….”kasan bana cikin iyayen dake tauyewa yayansu hakkinsu ae kai xaka xauna daita Right.”duk rashin kunyarta idonka a rufe yake baka gani gaka ga wayewa ,nidai na gama magana baxa awuce sati daya ba nagama magana.”Ahankali ya shiga hargitsa sumar kansa da wani irin yanayi yake kallon mahaifiyarsa,
Kusan sau ukku yana sauke ajiyar xuciya da wani irin yanayi a muryarsa yake fadin”kiyi hakuri Ammah Dan Allah kar ranki ya baci,xanyi aure kwanan nan tunda kin matsa, Amma ba Areefa ba wata daban.”da mmki Ammah ke kallonsa karka fara irin wannan wasar Aliyu bana son xalunci.”!lumshe idonsa yayi ya rasa ta yarda xaiyiwa Ammah bayani yasan muddin ya fada mata irin auren da xaayi shida farhaan baxata barsa ba,
Ammah karki damu watace daban kin san Areefa bata kammala karatun ta ba,,murmushi kurum Ammah ta saki ta San akwai wata a kasa.
Sai dai bataso ta kuresa ,
“Allah ya kaimu ya kuma nuna mana lokaci .”da sauri ya mike tsaye yana fadin” Ammah bara naje masallaci….da ido kurum tabisa.

****
Bokitin dake tsakiyyyar gidan Wanda yasha gyara ya koma kalar ruwan toka sabida dauda ,shi kawu balele ya kaiwa hauri……..Adama!!”Adama wai kina ina ne?”Adama dake cikin kitchen tana kasa shinkafa da wake na siyarwa ,tana xubawa kowa kwano-kwano .ga yara nan sunyi layi harda samari,
Afusace ta fito tana gyara daurin xaninta wanda yasha gyara tana fadin”wai lafia malan kake xabgamin kiran Ya’n wuta.”tayi maganar so pissed up..da alamar ta gama raina sa,ina bakar yarinyyar nan ta shige ne.”wato da ixininki take xuwa xance kofar gida,kuma kin San matar kabir CE da xai aura??”shaye da toka take fadin can Ku karata kaida yaron naka,ni kabarni naje ga sana’ata ta fada tana barinsa a wajen.wani Dan karamin daki ya nufa yana fadin”ina kike bakar munafuka mai bakin hali,Nooriyyah najin muryar kawu balele ta kara lankwashewa kan tsohuwar tabarmar da ta gama yagewa sabida tsufa .idan akwai abunda ke hargitsata yake firgita ta to masifar kawunta ne,,ta sansa tun tana karama Allah yayi masa masifa da fadan tsiya.”sanin halinsa yasa ta fito a tsorace har tana batun cire babban yatsan kafarta,kafin tayi magana taji saukar mari sai da taga wuta daga hannu yyi xai kara sauke mata wani Marin yaji an hankadasa gefe Allah yaso sa ya dafa bango ya xube a kasa yana sakin salati……….da balai da masifa ya dago yana kallon wane arnen ne yay masa wannan danyen aikin sukayi ido biyu da kabeer Wanda ya xaro ya’r karamar wuka a kugunsa,yayo kan kawu balele yana shako masa wuya,.tarin axaba ya soma saki dakyar ya banbari hannun kabir a wayunsa.
“Don ubanka ni kake kamawa wuya kabeer??”ni mahaifinka.?”kawu balele ya fada yana tsare kabir din da ido ,kara shakosa kabir yayi yana hadasa da bango wukar hannunsa ya dorawa kawu balele .nan take wandon kawu balele ya cika da iska………Baba !” Baba!””baban.”ehhhh na’am ya fada a mugun tsorace .sau nawa na kira sunan ka.”shaye da toka kawu balele ke fadin sau ukku mana.”sau nawa xanyiwa kowa kashedi akan yarinyyar nan?”Ya fada cikin maye da alamar baya cikin hayacinsa,tari kawu balale yaso mayi A tsorace nooriyah ta rike hannun kabeer pls yah kabeer ta fada hawaye na Rolling akan face dinta sakin kawu yayi yana riko hannunta,kwace hannun tayi tana goge hawayen idonta.Ya tsani ganin wannnan fuskar da kuka ,juyawa yayi yabar mata dakin batareda ya kara magana ba.
***
Sautin talkamin ta masu kama da tangaran su ya sanar dasu xuwanta,kowace sautin tafiar Areefa mansoor na buga xuciyar Aliyu waxeer .bai San ya xai fuskanci Areefa mansoor ba farhaan yana kallon yarda Aliyu ke hada xufa .kamshin turaren da yaji ya sanar dashi xuwanta da sauri ya daga kansa yana kallonta ,Dinkin Riga da skirt ne ajikinta na atamfa Wanda ya kama jikinta sosai………….tayi kyau tamkar wacce xata shiga sarauniyyar gasar kyau ta dunia,kallonsa Farhaan yyi sai yaga hankalinsa yana kan Areefa mansoor ,mikewa tsaye farhaan yyi agaban Areefa mansoor ya kame gamida bata salute .”sannu da xuwa Mrs.Areefa Aliyu waxeer,Ya fada batareda ya dauke hannunsa ba.ta wara ido tana sakin murmushi jin an kirata da sunan da tafi kauna a dunia,ta rausayar da kai tana juya yan kananun idanunta.farhaan ya saki daria ,ta xauna kusa ga Aliyu ta langabe kai tana masa kallon so.murmushi ya saki gamida riko hannunta yana murxawa cikin sanyin murya yake fadin kinyi kyau fiye da koda yaushe.”………..Fisge hannun ta tayi tana harararsa take fadin bbu wani can tunda ka manta dani farhaan ya fini.”ta karasa maganar shaye da toka,
Farhaan ya karbe xancen yana fadin wani nan ae ban isa ba,tana hararar farhaan take fadin bbu wani ae ina ganin Ku Ku biyu nasan akwai magana.”ta fada tana kallonsu,
Yarda farhaan keyi mata bayani ko fahimta batayi so kawai take yakai karshe,tuni hawaye suka fara Rolling akan farar fuskarta wacce taji make up .Yarda Aliyu yaga ta rude yarike hannayenta yana fadin Relax Areefa mansoor……….”Ya fada da wani irin tone a muryarsa ,ta fisge hannunta tana matsawa kusa garesa cikin shesshekar kuka take fadin taya ya??wannan wane irin Aure ne.”Yarda jikinta ke mugun rawa yasa Aliyu sakata duka acikin jikinsa .Ahankali ta kwantar da kanta cikin jikinsa.tana shesshekar kuka take fadin Aliyu please karka yimin haka ,kace wasa farhaan yake ahankali ya xagaye hannayensa da kugunta da sexy voice dinsa yake fadin open ur eye’s Areefa mansoor??Ya fada da wani irin tone ta bude ido tana kallonsa ya rike hannayenta ya saki murmushin karfin hali,anan ya warware mata matsalar farhaan,wani irin kallo take masa gamida mikewa tsaye Ahankali taji jiri na kwasarta har ta daina ganin komai da kowa.nan take ta xube a hannun Aliyu waxeer sumammiya ,cikin tashin hankali yake kwala mata kira gaba daya ya gigice .kusan minti goma sha biyar sun samu Areefar ta farfado tareda taimakon Yayarta Aunty Siddiqa ,farhaan mota ya koma yabar Aliyu da Areefa ,cikin taushin murya Aliyu ya riko hannunta.”kin San kece maccen da nake so a dunia Areefa taimakon besty xamuyi bakiga yarda yake sonta bane,,
I’m Gone Haidar!!”
Tayi maganar cikin sanyi murya ,
‘gone where??”…….Ya fada yana tsareta da ido .
Egypt….ya wara ido yana fadin har hutun ya kare,bata kallesa ba ta mike ta fara tafia yasha gabanta yana fadin.”Areefa wannan wane irin wulakanci ne bamu gama magana ba,wani irin kallo take masa ta daga waya ta kira sufyan mansoor a waya yyi mata booking first flight xuwa Egypt.duk da she’s not sure xata samu ,,nan ta wuce Aliyu bude da baki.

 

Back to top button