Hausa NovelsHausa NovelsWaminal Hoob Hausa Novel

Waminal Hoob 38

Sponsored Links

Asmy Mom Aydah??: 38….

Kema meya kaiki kin san halin xuciyarsa”sai hakuri kije ki canja kaya.”wani kallon Banxa take jifan Ammah dashi,cike da balai da masifa take fa?in.”duk bake kika shiga tsakanina dashi ba muguwa axxalluma wallahi sai na dau munmunan mataki akanki.”keeee!””Hakeem waxeer ya fada yana daka mata tsawa lokaci daya ya bayyana a gabanta,hannu yasa xai xabga mata shegen mari da sauri Ammah ta rike hannun,tana kallon yarda jikin Hakeem din ke wani irin rawa,
Wlhi da ka tabani da ka tabowa kanka balai da masifa ,taja dogon mtswwww…..tabar masu parlorn a mugun fusace,Yau din nan xata bar gidan nan baxata kara koda minti ?aya ba,Ammah karki cemin no pls.”
Ya fada idonsa yayi mugun kadawa sabida bacin rai,kayi hakuri ka xauna muyi magana.”zama yayi yana damke hannayensa cike da wani irin ?acin rai,
Ammah ta kalli noory wacce tun fara rigimar take kallonsu,tana mamakin samun wuri irin na Areefa da haukanta,Nooriyah ki bamu wuri xamuyi magana da Hakeem,
Noory ta mike tayiwa Hakeem sai da safe,ya daga kai yana kallonta
Da wani irin murya yake fa?in.”kisha maganin ki karki manta,daga masa kai tayi ta nufi stairs,saboda shi yana mahaukaci ya yarda kuma ya auri wannan jahilar Ammah,meyasa baki barni na fasa bakin shegiyaba,wai ya ma akayi Aliyu ya yarda yayi dating da irin wannan jahilar matar,
Nifa ina tababar wannan ba cikin Aliyu bane,wani kallo Ammah tayi masa tana fa?in.”shiya fada maka haka,koh kasan Aliyu har ziyara yake kai mata a kasar Egypt
Kasar da tayi karatu,kuma itama tana samun sa uk idan ta samu hutu,Allah kadai yasan
Irin watsewar da sukayi baxan shaidi Aliyu ta wannan fannin ba,haka baxan yi saurin yanke hukunci yanxu ba,
Sai kusan 10 Hakeem waxeer Yabar gidan
Ammah duk ransa
A jagule ,sai ya koyawa shegiyar Yarinyyar nan Hankali
Washegari tana zaune
A parlor tun karfe bakwai kallo daya xakayi wa fuskarta kasan tasha kuka fuskarta ta kumbura tayi
Sukutum.door bell taji ana danna mata duk A
Zaton ta Khaleel waxeer ne ya dawo ,da
Sauri taje ta bude kofar kallon Areefa take da mamaki tana
Tunanin meya kawota
Gidan ta a irin wannan
Lokacin,jikin Areefa yayi sanyi lokaci daya
Ganin yarda fuskar Layla din tayi wani irin Ja,haka yatsun hannu sun kwanta ko wane gefen cheeks dinta
Meya ssmeki Naga fuskarki a kumbure??
Tamkar jira laylah take
Ta fashewa da Areefa
Kuka mai cin rai,cikin
Shesshekar kuka take
Fa?in”Khaleel ya daina
Yina yanxu kin san me
Nagani a wayarsa, wata Yarinyya yake soyayya daita a garin Sokoto naga chart dinsu a waya,zuwan nan ma da yayi har gidan su yaje,shine yanxu naga chart dinsa da Yarinyyar ,tana fa?in.”
Abbanta ya amince ya
Turo magabatan sa,
dana samesa da maganar kin san
Meya fada min??”ta fada hawaye na Rolling akan face dinta,Areefa ta girgiza kai cike da tashin Hankali,cewa yayi Aurenta yake so yayi taxo tabasa ya’yan da yake bukata tunda ni nakasa basa,kinji yarda naji a lokacin
Kama rigarsa nayi na yaga gida biyu haka na fasa wayar ,shine yata xabga min mari
Yana fadin”Aure xai kara bai taba jin ddin mu’amalar Aure dani ba ko kadan,an fada masa matan Sokoto sun iya gyara dan haka shi yana so ya canja yana son yaji wannan ddin,wlhi banyi barci ba Areefa sai kace ba Khaleel ba wanda yake gudun bacin raina ba,yau Ni yake tsayawa agabana ya fadamin bai taba jin ddin mu’amalar Aure dani ba,wlhi xuciyata xata buga duka baxan iya sharing din mijina da kowace macce ba,
“Saboda wannan kike xubar hawaye??”da mamaki take kallon Areefa?”mena fada maki tun farkon Auren ku da Khaleel waxeer.”
“Do you Remember??
Ko na tuna maki,ke niimar da Allah yayi maki ta isheki baxaki iya xube kudinki kisha maganin mata ba,kin tuna,ko Ni dake bin maxan titi ina using da kayan mata barantana keda kike matar cikin
Gida.”to ae yanxu kinga ya maki hankali
Ya bude ido ya fada Maki sai ki fara shiri
Laylah na girgiza kai
Take fa?in.”ta yaya ?
Jia fa ko kwana baiyi ba a gida ,ta fada hawaye na Rolling Akan fuskarta,Areefa ta tabe Baki tana fadin”xan hadaki da wata( Deejerh Berverh )ina jin yar Kano ce kayanta suna
Da kyau ina fada maki
wlhi tallahi yarda khaleel waxeer zai rinka binki ko uwarsa baxai bibah,
Ke dai ki xube mata kudi ta hadaki,kuma ki bude baki kisha dan wannan shegen bakin naki mai son Dadi,in har kina so ki juya Khaleel waxeer sai kin gyara,kema mugun yar matsala ce sai kice social life kawai kika saka a gaba,babu ruwanki da Rayuwar Aure,kice yana matsa maki ya fiye takura,
Wlhi Ba karamin kokari Khaleel waxeer yayi ba ,na zama dake
Kin manta har tym table na sex kike masa gudun kar ya matsa maki,in ban dake da abunki wane namiji ne zai daukarwa macce wai sex duk karshen wata ko farkon wata sau daya,Areefa ta kwashe da dariya tuni ta manta damuwarta tana fa?in.”kije dai ki binciki lafiar ki,shima yayi hakuri sosai na rike Abar cikin wandon sa ,Laylah ta harareta tana share hawayen idonta take fa?in.”Ni dai mubar wannan maganar dan Allah ki bani lambarta nayi mata magana ta chart,idan ban dawo da leel hankalinsa ba
Hankalina baxai kwanta ba,harda Abinci tana koyarwa kala-kala ta online da snacks masu shegen ddin gaske,idan naje Kano bana jin ddin kowane snacks sai nata,nasan leel ?inkin snacks sune cimarsa bai damu da abinci mai nauyi ba,ko tanan kina mallakesa wallahi,itama Areefa ta fadawa laylah irin wulakancin da Aliyu yayi mata jia agabansu Ammah.
Laylah na girgiza kai take fa?in.”munafuka ce matar nan itake tsarawa Ya’yanta duk
Yarda xasuyi Rayuwa
Ni bata gabana. na dawo da mijina hanya kawai, indomie laylah ta ?ora masu acikin parlorn sukayi break
Fast,sai gashi sunji ana danna masu door bell laylah ta kwalawa Yar aekin ta Kira Mai suna hafiza tana fa?in.”taje ta bude kofar,da ladabi ta gaishesa kallonsa kawai Areefa keyi har ya karaso cikin parlorn shima hankalinsa gaba daya yana kanta
Ya bude mata hannayensa da gudu taxo ta shige jikinsa
Ganin haka laylah tabar masu parlorn
Wani irin kuka ta fashe masa dashi,
Cikin kunne ya shiga fada mata .”am sowiee baby ke kika batamin rai shiyasa banyi nufin na bata ranki ba komai ya wuce,hawaye na xubar mata ta turo baki tana fadin”da na tura maka sako a waya ban dauka xaka xo ba,ya shafa bakin yana murmushi yake
Fa?in yanxu baga ni ba,naga idonka wani iri ka kuwa yi barci jia?
Ya daga kai yana fadin”mekika gani”ta ware masa ido tana fa?in.”na gansu wani iri,gira daya ya dage yana fa?in…….”tunanin ki na kwana ina yi wani dadi ya kama Areefa ,
Ta sakesa tana fa?in”
Mufita yawo baby,
Ur wish is my command madam.”wani irin juya ido tayi agabansa ta subbaci goshinsa tana fa?in,minti biyu bari nayi sallama da laylah da haka ta nufi room din laylah,ya bita da kallo yana lumshe idonsa a hankali yana jin wani abu na fisgarsa akan ta,sai bayan la’asar suka dawo daga yawon su,
Tare suka shiga gidan Ammah dauke da manyyan ledojin da suka ciko da kayan baby,Shirin fita tayi itada Hakeem waxeer xai sauketa wajen tela
Ta karbo dinki,sanye take da ruwan tokan Hijab mai hannu har kasa,haka baa hangen kalar kayan jikinta duk da haka tayi kyau sosai,sai wani sanyayyen kamshi ke tashi ajikinta,da murmushi ta fadawa Ammah xasu tafi ,Ammah tayi mata fatan A dawo lafia
Tare suka jera itada Hakeem waxeer saura kadan su ci karo da Aliyu waxeer lokaci daya suka kalli juna zuciyar kowanensu na bugawa,da sauri noory ta dauke kanta,shima lokaci daya ya wani hade ,ta raba sa ta wuce Hakeem ya kallesa yana fadin”daga ina haka??
Wani kallo Aliyu yayi masa yana fa?in.”ka aeke nine??”Hannu Hakeem waxeer ya hade Yana sakin murmushi yana girgiza kai yake fa?in.”ko daya Yaya Ali…….!”da haka ya wucesa,da wani mugun kallo ya bisa ,ita kuma wannan ina take tunanin xataje tare da Hakeem?”bai san rashin hankalin noory ya girmi tunanin sa ba sai yau,da sauri Areefa ta riko hannunsa,xatayi magana ya fisge hannunsa tana kallon yarda idonsa suka juye lokaci daya sakar mata ledojin hannunsa yayi anan suka watse ya juya a fusace tasha gabansa
Tana huci take fadin”
Meke damunka dan Allah,sai muna cikin nishadi da kaga wannan bakar Yarinyyar duk komai ya ruguje Ni wallahi na gaji.”ta fada a tsawace
Hannu yasa ya wani irin turata a haukace yabar parlorn koda ya fita har motar Hakeem waxeer ta dde da fita compound din gidan,
Hannu yasa cikin sumar kansa yana hargitsa ta kwallah na cika idonsa,a haukace ya koma part din Ammah yarda Ammah
Taga ya shigo mata a haukace ta bude ido
Tana kallonsa,xama yayi yana sauke numfashi hawaye na cika idonsa lokaci daya,baya son Ammah taga hawayen sa,xata dauka sabida noory ne,bai taba faduwa akan duk abunda yake nema ba,wannan ma baxai fadi ba,ba’a yi maccen da xata kassara zuciyarsa ba.Yaushe sallama ta zama abokiyar gabarka ban sani ba??””Ammah ta fada tana xuba idonta cikin nasa,Ammah kin san wannan ba dai-dai bane ta rasa da wanda xata fita sai Hakeem waxeer ,duk direbobin gidan nan,kuma haka xakiyi ta xuba mata ido tana gantali cikin gari bakya gudun surutun mutane…….”Ammah ta kallesa tana sakin wani irin murmushi ,take fa?in Hakeem waxeer har yafi direbobin gidan matsayi to meye laifi dan ya kaita a duk inda takeso taje,nan gaba kadan xata zama matarsa ta Aure na har Abada meye abun damuwa kuma.”da wani irin sauri ya dago Yana kallon Ammah,
Hawayen idonsa da ya kasa rikewa su suka sauka kan face dinsa abunda Ammah bata ta?a gani ba,Ammah ta tallabo fuskarsa ta kallesa ido cikin ido take fa?in.”menene Damuwar Aliyu waxeer pls ka fa?amin??,ta fada tana addu’a Allah yasa ya bude baki ya fada mata damuwarsa,da sauri ya Rungumeta hawayensa na sauka akan bayanta,ta dago tana Fa?in..”,Ko kana son Nooriyah har yanxu Aliyu?”Ammah tayi maganar cikin rawar murya da sauri ya girgiza kai yana fadin”bana sonta Ammah only Areefa Mansoor ,wani kallo Ammah ta shiga yimasa tana jin zafin kalmarsa ta karshe sai dai batace komai ba,
Har kusan 6 yana ta zama a dakin Ammah yana danna waya yaga ta inda su noory zasu dawo,ita dai Ammah tana kallonsa haka tana kula da duk wani motsinasa kusan shidda da rabi suka shigo gidan,kallo daya xakayi wa noory kasan tana cikin farin ciki sabida Abdul-Hakeem
Mutunne mai yawan fara’a da tsokana yana da shiga rai lokaci daya,suna turo kofar dakin Ammah Aliyu ya daga kai ya kallesu,
Sai kuma ya dauke kai,ya wani daure fuska ya mike yabar Room din……da fara’a Ammah ta tarbesu tana fa?in.”sun dawo zama Hakeem yayi ,
Ita kuma noory ta juya ta nufi nata dakin,
Tana turo kofar tayi ido biyu dashi yana xaune gefen bed ya wani daure fuska,itama fuskar ta daure tana mamakin meya kawosa dakinta.”me kuma ya shigo dakai dakina,wani irin kallo yake yimata cike da takaici yake fadin.”saboda rashin sanin ciwonka haka xaki fita dashi kuna zagaye gari,ta girgixa tana gajia da halayen na Aliyu lokaci daya,
.”ina da right din da xan fita da duk namijin da naga dama wannan ba damuwar ka bane,ae kaima naga yar gaban goshin naka tare kuke yawon.”wani murmushin takaici ya saki kina kishi kenan??”wani kallo tayi masa saboda me xanyi kishin ka,tunda ba sona kake ba,ae wanda ake so shi xa’a tsaya ana kishi a kansa.”idan yace baiji zafin maganarta ba xaiyi kara haka idan yace maganarta bai tabasa yayi karya,
Yana mamakin tsiwarta da taurin kanta,wani murmushi yayi lokaci daya ya daure fuska yake fadin.”bana zo nan dan muyi jayayya ba,
Ko ki gasamin magana yarda kika saba,umurni na baki daga yau babu ke babu kula Hakeem acikin gidan nan,idan kuma kin ki xanyi mugun baki mamaki wlhi.”Kallonsa ta tsaya tana yi har ya fice daga Room din xuciyarsa na tafasa idan baiyi hankali ba,.
Noory xata kone xuciyarsa cikin kwanan nan,ya gaji da duk rigimarta,yana tuna kissing din Areefa da yayi acikin mota sabida hakurinsa ya kai makura har kusan yin realising yayi,
Bayan kwana biyu da rigimarta itada Aliyu tun lokacin bata kara saka sa a ido ba,A ranar Kuma Ramlah waxeer xata zo,,wani irin dadi nooryn ta shiga ji da kanta ta shige kitchen tana ha?awa Aunty Ramlah lunch,Bayan Hakeem waxeer ya daukota daga airport direct Mention din Ammah tace xata sauka,sabida wannan karon babu yar uwarta sunje umra itada maigidanta baxata samu zuwa bikin Rumaisa waxeer ba,
Dama Ammah tasan anan xata sauka tuni ta saka aka gyara mata dakin baki dake kusa gana Areefa mansoor,a kitchen ya samu noory ya kalleta
Yana fadin”yunwa nake ji Madam irin wannan jan rai haka,
Ta game hannu tana fa?in”Afuwan yaya Hakeem yanxun nan zan kawo maka jirani
A dinning Area minti biyar,murmushi yayi ya juya yana fa?in.”ina jira,ita tayi serving dinsa ta fada masa xataje ta gaisa da Aunty Ramlah ta shiga wanka,ya gyada kai baice komai ba dan ya riga ya cika spoon
Daria tayi tana fadin”ko sai na saka maka pillow Yaya irin wannan cika spoon haka,ta fada tana fashewa da dariya shima dariar yakeyi,
Kamshin sa ya sanar daita zuwan sa,ta dauke kai da sauri ta nufi stairs ta fasa shiga wajen Aunty Ramlah dan tasan can ya nufa ,ko kallon Hakeem waxeer baiyi ba dake daga masa hannu ya nufi masauqin Aunty Ramlah sabida ita ya shigo gidan Ammah yau,kwanan sa biyu rabonsa da gidan sai dai ya kira Ammah a waya ya gaisheta, Hakama Areefa wacce suna raba dare suna waya tana fada masa dirty talks ,Wanda ba karamin rage masa xafi suke ba duk da yasan xunubi ne babba aekata hakan, knocking yayi a kofar dakin Aunty Ramlah aka basa ixinin shiga ya shiga da sallama,
Aunty Ramlah ta saki
Murmushi ya wani shagwabe fuska ya xauna cikin soofa yana shafa kansa yake fa?in.”kin daina sona??”tayi murmushi tana danna waya take
Fadin”nima ka daina sona ka daina jin maganata “ya hade rai yana fa?in….menayi kuma??”komai ma kayi,ya mike tsaye yana fa?in.”xan fita zuwa Anjima muyi magana,ta masa wani kallo tana tabe Baki.
Sai dare ya shigo gidan ya samesu duka parlorn Ammah suna hira harda Hakeem waxeer,Aunty Ramlah ta tsaya tana sai yanxu,ya kirkiro murmushi yana fa?in.”fita yayi Aunty Ramlah ta kallesa tana fa?in.”toh ya bayan Rabuwa ,haka kuma abubuwa suka rikice ,Allah ya tsare gaba Amman ban ji ddin yarda abubuwa suka faru haka ba.”babu komai Allah yasa haka shi yafi Alkhairi,ina ita Areefa ban ganta ba tun xuwana,,shi dai baice komai ba yayi shiru.Hakeem waxeer ya mike tsaye yana fa?in.”Ammah ki sha maganinki fa Allah ya kara sauqi ta kallesa tana murmushi take fa?in.Amiin ya kalli Ammah da mamaki yake fa?in.”baki da lfy ne Ammah,ta daga kai tana fadin.”mura ke damuna yanxu xan sha magani na kwanta,itama Aunty Ramlah ta miqe tsaye tana hamma take fadin.”nima sai da safenku barci ne acikin idona,ta kalli noory tana murmushi take fa?in.”dota sae da safe mu idar da maganar mu kou?”noory ta daga kai
Tana murmushi ,Aliyu ya kalleta yana fa?in”gud nyt Aunty.”ta shafa kansa tana fa?in.”nyt son,da haka ta nufi dakinta dama Hakeem ya wuce ya rage daga Ammah sai Aliyu da kuma noory,
Ammah ta mike tsaye tana fa?in.”muje Aliyu ya kalli Ammah ya hade rai,ya bisu da ido har suka wuce…..wani abu yake ayyanawa aransa lokaci daya ya saki wani irin blushing,fita yayi da mota baifi minti talatin ba ya dawo gidan Ammah,ya kalli Nana kusan karfe tara da yan mintuna,tana tsaye acikin kitchen din Ammah tana wanke kwanukkan da akaci abincin dare,
Sabida Ammah bata so a kwana da wanke-wanke,fridge ya Buda ya dauki ruwa marar sanyi Sosae,
Ya nufi small parlorn Ammah Wanda Bata fiye xama acikin sa ba,
Sai idan tana so ta huta ,bude bottle water yayi ya saka pills din aciki xaune yayi kusan minti goma sun gama narkewa acikin ruwan ya koma kitchen ya Kira Nana da sauri taxo ta xube gabansa,yasan a kaidar noory duk xata kwanta barci akwai ruwa a gefenta,tana yawan aje bottle water akan bedside drower
Ya mikawa nana bottle water din,yace ina noory.da ladabi ta fada masa tana dakin
Ammah,yace kije dakinta ki aje wannan
Ki dauko wanda ke aje gefen gadonta yanxu,
Da sauri Nana ta karbi goran ruwan kusan minti biyu ta fito da ragowar wanda tasha tabarsa ta fada masa ta kai ,ya daure fuska yana fa?in.”karki fadawa kowa kin kai ruwa dakinta kina jina??”jiki na Rawa ta daga masa kai,yace idan naji wannan maganar ya fita a bakin aekin ki.”da haka ya juya ya fice daga gidan gaba ki daya ,yasan noory baxata wuce karfe goma a dakin Ammah ba,,ya bata nan da awa daya…..Da haka ya saki wani iri blushing…

Allah ya isa idan kika karanta min book baki biya ba ,ban yafe maki ba…..”

Littafin Waminal Hoob na kudi ne #500
Account Details
0004157137
Jaiz Bank
Asma’u Buhari Aliyu
Katin wayar MTN.ta wannan lambar#09060259200
Shaidar biya ta wannan lambar#08086207764

Back to top button