Hausa NovelsHausa NovelsWaminal Hoob Hausa Novel

Waminal Hoob 45

Sponsored Links

45…..

Yafi minti goma xaune ya rasa kalar tunanin da xaiyi sunan Farhaan kawai yafi damunsa cikin hirar su,girgixa kai ya somayi yana fatan ba Besty ba,wata xuciyar ta fada masa Besty baxai mayi wannan harkar da Areefa mansoor ba tun da yasan budurwarsa ce,
Sanin da yayiwa Farhaan Shagari bai tana neman matan banxa ba,abarsa da shan sigari,tafukkan hannunsa ya saka cikin fuskarsa,komai na duniar na juye masa,sabida noory duk yake wannan abubuwan ,ya gaji da wahalar da take baiwa xuciyarsa ,Ya Rabbi help me out!”yayi maganar cikin sanyi murya,yayi missing komai nata,acikin kwanakkin nan ba karamin azaba yake sha ba ,sabida Rashin noory.washe gari wajajen karfe takwas ta haura sama,dai-dai lokacin noory ta fito dakin Batool. Areefa mansoor lokaci daya ta hade rai ta karasa bakin dakin Aliyu ta murda kofar ta shiga kasa tafia noory tayi
Jin wani abu yana tsaya mata a xuciya wani kallo Tayiwa noory.ta tura kofar
Da sauri noory ta sauka kasa tana dafe kirjinta da yake mugun bugawa,kallonsa ta tsaya tana yi yarda yayi kyau cikin barcinsa,hannunta ta saka tana shafa fuskar tasa a hankali,
Cikin barci yaji ana taba fuskarsa da sauri ya bude ido ya wani xare ido ganinta a tsakiyyar bed,yaja da baya lokaci daya yana kallon Kofa addu’a yake Allah yasa Ammah ko noory basu ga shigowarta ba,mekike anan Areefa?? yayi maganar da kakkausar murya ta dage kafada tana fadin.”naga baka zo ba kuma kasan yau zamu fara zuwa asibiti,kawai kije dan Allah bana jin dadi”bude baki tayi tana kallonsa xatayi magana ya dakatar daita yana fa?in.”pls Areefa idan kin dawo sai kiyi min bayanin ko mai ya faru,ya fada yana sauka daga kan Bed din ya shige toilet kwafa tayi gamida bar masa Room din,koda yayo wanka bata dakin wata ajiyar xuciya ya sauke kayansa ya saka a gurguje ya sauka down stairs Kai tsaye dakinta ya bude ya shiga harda murxawa kofar key,duk ta hargitsa kayan dakin
Ga wasu nan da ta fito dasu tabarsu a watse da alamar wankakki ne gogaggi,wadrop ma a bude tabarta,sosai laptop din dake kasan kayanta ya dau hankali sa,xubo da sauran kayan yayi saiga waya ya fado da kuma laptop binsu yayi da kallo zuciyarsa na mugun harbawa,
Wayar Farhaan Shagari me Areefa keyi da wayar farhaan,??jujjuya wayar ya shigayi a hannunsa kafin ya maida kallonsa kan laptop din,yasan ba haka laptop din Areefa take ba,tunani ya shigayi waya sani da wannan laptop din??”xuciyarsa na dokawa bakinsa na wani irin rawa yake fa?in.”Farhaan !!!”lokaci daya. daga tsaye ya xauna dabas akan Bed ,Yana kokarin dai-daita numfashinsa
Zuciyarsa na wani irin rawa,hawaye yaji suna cika idonsa a hankali,
Sunan Farhaan kawai
Yake fadi acikin ransa,
Mayar mata da kayan yayi yarda suke,yana fitowa yaci karo da noory wani irin kallo tayi masa gamida dauke kanta ,ta nufi stairs shi Kuma ya nufi kofar barin parlorn kallo daya xakayi masa kasan baya cikin natsuwarsa,haka yaja motarsa duka jikinsa babu wani kwari ya nufi Mention dinsa,
Sai da ya fara fadawa mai gadi idan akaxo neman sa yace bayanan,da haka ya nufi Entrance din shiga gidan ya kashe wayarsa duka yasan Areefa xata iya kiransa kowane lokaci,
Sai da ya samu natsuwa ta hanyar addu’a ya shiga juya wayar farhaan a hannunsa zuciyarsa ta kasa yarda wayar farhaan ce a hannun Areefa,kunna wayar yayi ya ajeta gefe hakama laptop dinsa,
Addu’a yake Allah yasa bai canja pin ba
Haka Allah yasa ya samu wani evidence
Sai yaga wayar babu security cord ajikinta. wurin kira ya shiga
Yaga kiran da yayi masa kafin a kashesa,
Cigaba da duba kiran wayar yayi,duk kiran Areefa mansoor yafi
Yawa a wayar farhaan
Yayi serving sunanta da Areefa mansoor,batareda ya boye sunan ba kuma lambar mtn . messages ys shiga nan ma akwai messages din Areefa da yawa,ya koma cikin
Voice note,A hankali ya saki wayar yana kasa rike hawayen idonsa,
Farhaan Areefa kawai
Yake fada cikin wani
Irin sauti marar Amo,
Abu daya ya kasa fahimta yanxu ya tabbatar cikin jikin Areefa na Farhaan ne,
Sabida ga gaskiyya nan ta wayarsa haka
Ga pics Nan kala-kala
Da suka dauka tare,
Wani baxai ma kallu ba,sabida yarda munin kallon nasa yayi yawa,
Tambayar kansa yake
Ko Areefa tana da saka hannu acikin mutuwar Farhaan Shagari???a laptop dinsa ya koma ya ta gwada pin yaki budewa karshe sunan Noor yasa cikin sa’a
Ya bude ,yafi awa daya yana bincikar laptop nasa bai samu komai na mutuwarsa aciki ba sai badakalar da sukayi da Areefa da sauran matan da Farhaan din yayi mu’amala dasu bata hanyar Aure ba,dafe kansa yayi xuciyarsa
Tana wani irin bugawa,tunda ya shigo gidan wani irin mugun xaxxabi ya rufesa jikinsa har wani kadawa yake sabida tashin hankali da shiga shock,har akayi sallar magrib yana kwance a master bedroom dinsa,har wani irin jiri yake ji
Idan ya mike tsaye sabida yunwa tun safe babu abunda ke cikin
Cikinsa,lalubar wayarsa yayi dakyar ya samu Dr.Arhaam a waya,yace ya samesa gidansa baya jin dadi ne,kusan awa daya Dr.Arhaam yaxo ya dubasa yace xai rubuta masa magani
Amma ya fara cin abincin dama yunwa ce da damuwa tayi masa yawa,kasan Ni bana shiri da magani
Kayi min allura kawai,
Dr.Arhaam ya girgixa kai yana fadin.”taya xan baka injection bbu komai acikin ka,ka kira gida wani ya kawo maka abinci kafin nan
Naje na karbo injection,bana son asan Ina gidan nan,Aliyu ya fada yana jaye idonsa cikin na Dr.Arhaam da mamaki yake fa?in.”meyasa ??Ni na manta ina matarka??tana gidan Ammah ,xaiyi magana Aliyu ya daga masa hannu yana fa?in.pls doctor,da haka Dr .Arhaam ya mike tsaye har ya kai kofa yake fa?in.”na karbo maka abinci ko na Restaurant ne,daga kai yayi yana kallon Arhaam din ,sai dai baice komai ba ya dauke kai,bayan ya karbo injection din da xaiyi masa kai tsaye gidan Ammah ya nufa ,wayar Ammah ya kira anyi Sa’a wayar na parlor Addu’a Ammah keyi Allah yasa Aliyu ne tun daxu take buga wayarsa a kashe.ganin bakuwar lamba yasa ta daga amma batayi magana ba,daga can bangaren Dr.Arhaam jin an daga wayar yayi mata sallama yana fada mata koshi wanene,
Ta saki fuska ya gaisheta da respect ta amsa tana fa?in.”Ashe kaine bana da wannan lambar naka,Ehhh Ammah dama gani a kofar gida ina so muyi magana, murmushi Ammah tayi tana fa?in.”kai kuma sai kace gidan bakon kane da baxaka shigo ba,ka shigo mana ya kashe wayar tareda fadawa Ammah gashinan shigowa ta fadawa Nana ta bude parlorn baki haka ta kai ruwa da drinks,
Sama Ammah ta nufa dan dauko Hijab,nana ta aje masa tray ta gaishesa tana fada masa ga Ammah nan xuwa,da haka ta mike tsaye tabar parlorn yana danna wayar hannunsa Ammah ta shigo da sallama dauke a bakinta ya mike tsaye yana amsa sallama gamida kara gaishesa,Ammah ta amsa tana yimasa umurnin ya xauna mana.xama yayi ya soma yiwa Ammah bayanin matsalar Aliyu,Ita dai Ammah sakin baki kurum tayi tana bin Dr .Arhaam da kallo,ban san bayada lfy ba wlhi duk yinin yau ban sakasa
A idona ba, muje naga jikin nasa..
Ciki Ammah ta koma
Ta hadowa Aliyu abinci mai rai da lafia
Ta kalli noory tana fa?in.”xataje ta dawo yanxu noory tayi mata fatan sauka lfy,dai-dai lokacin Areefa ta fito daga nata dakin,jin hayaniya ta dauka Aliyu ne ya dawo ganin Ammah da Hijab da Kuma basket a hannunta yasa ta dan saki fuska tana fa?in…”sannu da gida Ammah fita xakiyi ne??Areefa ta fada da murmushi a fuskarta tana kallon Ammah ,
Ita dai noory wucewarta tayi sama
Dan ta tsani Areefa mansoor ko kusa daita bata son tsayawa,Ammah ta fadawa Areefa xata fita idan ta tashi cin abinci dare gaya can taje ta xuba da haka ta nufi kofa Areefa mansoor ta bita da kallo tana tabe Baki,dama kuma harda yunwar yasa ta fito kai tsaye dinning Area ta nufa.da mamaki ya kalli Ammah ,kafin ya maida kallonsa kan Dr .Arhaam da yake yiwa Ammah jagora cikin room dinsa,ruwan xafi Ammah ta shiga ha?awa,tea ta ha?a masa ganin irin yarda Ammah ta hade rai babu musu ya karba
Ya shanye,fried rice ammah ta xuba masa kadan cikin plate da kayan hadinta,ta mika masa karba yayi kusan spoon biyar yayi ya aje jin kamar xaiyi amai,ruwa ya dauka yana sha kafin ya maida kallonsa kan Dr.Arhaam yana hararar sa yake fa?in kaxo kayi min ,shi dai murmushi kawai yake
Kusan minti biyu yayi
Masa allurar yana fa?in.”gobe xai shigo yayi masa wata,Ammah ta bisa da kallo tana fa?in.”An gode bayan fitarsa da minti biyar Aliyu ya mike tsaye ya dauki car key yana fa?in.”Ammah ki kira noory a waya ta fito yanxu driver ya sauketa gidan Baffa ina son muyi magana,
Saboda ka fara Shaye-shayen!”ita maganar baxaka barta sai da safe ba.yanxu fa akayi maka allura,
Ya girgixa kai cikin rawar murya yake fadin.”baxan iyaba Ammah,ganin ya nace Ammah yasa ta daga waya ta fara kiran driver kafin ta Kira noory ta fada mata driver xai sauketa gidan Baffa waxeer yanxu,sallar Ishaai kawai ta gama kiran Ammah ya shigo a wayarta ko shafai da wutri bata samu damar yiba,koda ta sauka kasa Areefa tabar parlorn ta kalli plate din da taci abinci dashi tabarsa nan yashe tsakiyyar parlor
Da Kuma sauran lemun da tasha shima tabarsa ko rufesa batayi ba,wani irin faduwar gaba ta samu kanta dashi ganin motar Aliyu a compound din Baffa waxeer,,haka bugun xuciyar nata ya kasa dainawa,cikin gida ta wuce wajen ummah
Ta gaisheta da ladabi ummah ta amsa da fara’a kin karaso kenan??”Ehhh toh Ammah tana sallah Baffa da Aliyu kuma sun shiga Masallaci
Kema idan xakiyi sallar kije dakin su Aysha kiyi,ta girgixa Kai tana wasa da yatsun hannunta take fa?in.”nayi sallah kafin na fito…..suna dawowa daga masallaci ummah tayi masu jagora parlorn Baffa,ya gaisa da Ammah,noory ta gaishesa cike da girmamawa ta samu wuri ta xauna akan rug din da aka malala tsakiyyar parlorn,ummah xata juya ta fita Ammah ta tsayar daita tana fa?in.”ina kuma xaki kixo ki xauna dama xaman na Aliyu ne,Ummah ta dawo ta xauna tana murmushi take kallon Aliyu tana fa?in.”Allah yasa muji Alkhairi,shiru Aliyu yayi yana jin zuciyarsa na wani irin zafi tsanar Areefa mansoor yakeji
Tana zagaye xuciyarsa gabaki daya, Baffa waxeer ya kalli Aliyu yana fa?in.”kai muke saurara kayi shiru ita dai noory ko kallon inda yake batayi ba,
Dama kan xancen Areefa ne Baffa,cikin dake jikin Areefa bana da alaka dashi wlhi!”haka sakin noory ma haka Areefa ta dauki wayana tayi wannan sakin,tun lokacin da taxo da maganar ciki ,cikin gidan nan nake so nace ba nawa bane,ina jin maganar a bakina sai naji na kasa fadar cikin dake jikinta banawa bane,hakama sakin noory.aduk lokacin da xan buda baki nayi bayani akan bani na saki noory ba sai naji bakina yayi min wani irin nauyi a lokacin ban san meke damuna ba wlhi,kawai na samu kaina da bin duk wani umurni nata
Haka bana iya yimata musu,daga hannu Ammah ta shigayi tana yiwa Allah godia,
Baffa ya girgixa kai cike da shock yake fa?in.”to kai kana da wata shaida da xai tabbatar da cikin jikinta baka da alaka dashi.”wannan karon Kallon gefen noory yayi suna hada ido ta wani dauke kai lokaci
Daya,dama lokacin Asiri tayi maka shiyasa baka iya musawa Areefa da taimakon Allah da taimakon mahaifiyarka ka dawo hanya.”mikewa tsaye yayi ya fada masu xaije mota ya dauko shaida,duka text din wayar farhaan wanda yayi mata da wanda tayi masa ya gwadawa Baffa ,Baffa yanata kallo yana sanye da farin gilashi mai karawa idonsa gani,Haka ya saka masu voice note na Maganar Areefa da Farhaan,kuma Farhaan yasan tana dauke da cikinsa,Runtse idonta tayi tana sauke numfashi,tana jin xuciyarta na matsewa wuri ?aya sabida ciwon da take yimata,
Farhaan!!”ta fada hawaye na mirginowa akan fuskarta,kasa rike kukan da yazo mata tayi da gudu xatabar parlorn Ammah ta dakatar daita ,cikin raunin murya take fadin”ina xaki ba’a gama ba,
Anan wurin noory ta xube ta shiga rera masu kuka mai taba zuciya babu wanda
Yayi yunkurin rarrashinta,kukan ta yakeji yana tabasa.
Ji yake tamkar ya jawota ya rarasheta cikin jikinsa ,ya fita jin ciwo shi a xuciya yake jin nasa ciwon,kowa na parlorn jikinsa yayi mugun sanyi,haka Aliyu ya shiga kamo pics din Farhaan da Areefa wanda sukayi a tare wani ma ba’a negeria bane,a Egypt da kuma Cyprus idan ta kai masa ziyara,
“Kuyi min Alfarma Baffa dan Allah ,bana son Areefa tasan mun san gaskiyya yanxu,sabida cikin jikinta karami ne kar ya samu matsala….”cikin tsawa Ammah ke fa?in wane irin shirme ne wannan
Meye amfanin zama da shaidaniyya irinta,
Ya girgixa kai yana fadin.”Ammah ba ita nake jiba cikin jikinta nakeji ina son Dan Farhaan yaxo dunia ko saboda mami,tun Rasuwar Farhaan rayuwar mami ta canja duka,rashin Farhaan ya tafi da dukkan walwalarta,
Duk da nasan ba dan sunnah bane ko a haka mami xata sosa,sabida kasancewarsa jinin Farhaan Shagari,
Idan kuma Areefa tasan mun san komai xata dauki mataki,
Nasan halinta nasan wacece ita tasan hop Dina Yana kan noory,
Xata iya yin komai dan ta hana noory zama cikin Rayuwata,yanxu idan taji Rayuwar noory na cikin mugun ha?ari .inada tabbacin akan mutuwar Farhaan da saka hannun Areefa,sabida mami tace sun karbi wayar hannunsa da laptop ,abun nufi anan me Areefa keyi da wayar Farhaan da kuma laptop nasa ya akayi suka zo hannunta??””tsit kowa yayi a parlorn yana juya maganganun Aliyu waxeer aransa ,sabanin noory da hankalita baya tare dasu gaba daya,alfarma ta biyu xan dauke noory mu koma uk.xuwa wani lokaci kafin nan cikin Areefa ya girma,sai na dawo mu fuskance ta
Ko zamu iya samun mutuwar Farhaan awajenta,haka duk wani Evidence na cikin wayar farhaan na turasa a laptop da kuma wayana,xan mayar mata da komai
Ta yarda baxatayi zargin wani abu ba,ya juya kan Ammah yana fa?in.”kiyi irin dabararku na mata Ammah kice xaki shiryawa noory tafiya zuwa Sokoto na watanni idan ta cireni aranta duka sai ta dawo,kinga anan ma an batar da hankalin Areefa,nikuma xan fada mata xan koma bakin aekina,duk karshen wata xanxo na dubata,wanda xan fada mata hakane kurum baxan dawo ba Ammah sai lokacin da na diba ya cika watan haihuwarta, na tsani koda ganin fuskarta ne,ki cigaba da lallabata Ammah har zuwa lokacin,haka xamu rika waya…..Baffa ya girgixa kai yana fadin.”shawarar da Aliyu ya kawo shine dai-dai ya kalli Ammah da ummah yana fa?in.”ko akwai gyara??lokaci daya Ammah da ummah suka girgiza kai ,ya kalli Aliyu yana murmushi gamida dafa kafadarsa yake fa?in.”ina Alfahari da kai ,kaje ka fara shiri daga yau din nan,Allah ya kareka a duk inda zaka axa kafa..Ameen Aliyu ya fada yana kallon noory da ta nufi kofa tamkar xata tashi sama dukan su suka bita da kallo lokaci daya……

_wlhi ban yafe maki ba idan kika karanta min book baki biya ba Allah ya isa ban yafe ba,hakkina baxai barki ba wlhi_…!

Littafin Waminal Hoob
Na kudi ne#500
Account Details
0004157137
Jaiz Bank
Asma’u Buhari Aliyu
Katin wayar MTN.ta wannan lambar#09060259200
Shaidar biya ta wannan lambar#08086207764

WM#
ASMY#??
[9/15, 6:11 PM] Asmy Mom Aydah??

Back to top button