Hausa NovelsHausa NovelsWaminal Hoob Hausa Novel

Waminal Hoob 41

Sponsored Links

Asmy Mom Aydah??: 41….

Komai na Room din kamshin noory yake,baya son wannan kamshin mai birkita tunaninsa,ko kan Bed dinta da yake kwance wani irin fitinannen kamshi ke tashi acikinsa,wannan kamshin yana saka sa cikin wani irin yanayi
Kan soofa ya koma yayi kwanciyarsa nan ma kamshin ya hanasa sakewa pillow
Ya dauka ya dannawa face dinsa,wani irin
Squeezing numfashinsa keyi,dakune fuska yayi
Gamida jifa da pillow hannun sa,kan window ya koma yayi tsaye gamida folding hands dinsa akan kirjinsa ya kurawa sky Wanda suka haskaka sararin samaniya ido,har kusan 1 ya kasa barcin tunanin noory manne aransa,sai kusan 2 barci ya daukesa anan saman rug ya dunkule waje daya tamkar mai jin sanyi kallo daya xakayi masa kasan a takure yake barci,3 na bugawa Ammah ta turo kofar dakin,dama tayi masa warning akan kar ya saka key jikin kofar,kallonsa akan rug yasa Ammah ta isa garesa ta dan fara jan dogayen yatsun ?afarsa,bude ido yayi wanda barci ke cikinsu ya dakune
Fuska yana fa?in.”Ammah mana.”
Ta ware masa ido tana fa?in.”ka tashi lokaci yayi,shaye da toka yake fa?in.”yanxu fa na kwanta zuwa Anjima dan Allah,lokaci daya taja dogon hancinsa da karfi ba shiri ya mike xaune,ka tashi yanxun nan Aliyu.”ganin Ammah baxata barsa ba ya mike ya nufi toilet sanin Ammah sai yayi wanka ,yasa ta juya tabar room din
Tana fada masa xata dawo idan ya koma ya
Kwanta ransa xai baci,
Wanka yayi gamida dauro Alwallah ,kusan ukku da rabi na dare Ammah ta dawo room din ,wata ajiyar xuciya ta sauke samun sa akan sallaya ya daga kai yana kallonta, murmushi tayi masa gamida girgixa kai ta
Juya tabar room din,
Sai kusan shidda da rabi ya koma barci,
Wannan karon Bed ya hau,yarda barci ke damunsa bai dde ba barci ya daukesa,Ammah ta kalli noory dake gyaran parlor tana fa?in.”ki shiga ki wanke masa toilet nasan motsinki baxai tashesa ba ,kiyi sauri kafin ya tashi,tunda ta shiga room din ta kurawa farar fuskarsa
Ido ,samun kanta tayi
Da sakin murmushi ko
Mai nasa mai kyau ne,
Agurguje ta wanke toilet ta fito,ta dauki sauran tarkacenta tabar masa Room din
Kitchen ta koma ta hade dasu Aunty Ramlah dasu Ammah
Suna hada abun karin
Kumallo,kusan karfe tara sun gama komai
Tana break fast ita dasu Aunty Ramlah taji sallamar Kabir da Adama, da wani irin
Murna ta juya tana kallonsu murmushi kwance akan kyakkyawar fuskarta,
Da gudu ta nufi Kabir,
Yayi saurin kaucewa yana daga mata hannu,shaye da toka ta ware masa ido,
Ya tabe Baki Yana fadin”kin girma yanxu Hajia haka kawai katuwa dake xaki zo kiyi hugging Dina,shafa kanta tayi cike da jin kunya taje ta kwanta bisa kafadan
Adama tana fada mata sannu da zuwa ummah.”ta shafa kanta tana fa?in.”sannu da gida ya’r Albarka,Ammah ta tarbesu cike da farin ciki,Kabir yana gaisheda su Ammah da ladabi,Ammah na murmushi take fadin”.
Kadawo Ashe??Ya shafa kansa yana dagawa Ammah kai,
Karin kumallo Ammah tasa aka kawo masu,
Adama ta fadawa Ammah itakam Alhmdullh sai dai Kabir dama shine bai karya ba dumame suka karya dashi ,shi kuma baya son tuwa,
Noory ta shagwabe fuska tana fa?in……”meyasa baki xomin dashi ba Ummah?”ae ban san xakici bane,bayan noory da Kabir sun fita
Adama ta kalli Ammah gamida fiddo da maganin cikin karamar jakarta ta hannu,ta mikawa Ammah tana fa?in.”wannan cikin ruwan xafi xai rika shansa,wannan kuma a ruwan wanka xa’a rika zubawa,Ammah tace ruwan xafi kamar tea kenan??”Adama ta daga kai tana fa?in.”ehh kamar haka
Ammah ta daga kai tana fa?in.”bari mu gwada Allah yasa zai sha kunsan halin Mutunen wlhi.”dan ubansa dole yasha bari naje na hada masa Black tea da wannan maganin tare xan dafasu ta yarda baxai gane ba,da haka Aunty Ramlah ta karbi maganin wurin Ammah tabar masu Room din,Ammah ta kalli Adama tana mata godia sosai,kafin ta ?ora da fa?in.”to ya kukayi da mai maganin nawa xa’a basa,Adama Tayiwa
Ammah wani kallo tana fa?in.”saboda Ni bana da arzikin siyawa Aliyu magani kike fa?in haka ,ta karasa maganar cike da rashin jin dadi acikin muryarta,da sauri Ammah ta girgixa kai tana fa?in”kiyi hakuri ba haka nake nufi ba wallahi,Adama tayi murmushi tana fa?in.”kawai muyi ta rokon Allah yasa ya dawo hankalinsa,hira suka taba da Ammah ita kuma noory hira tayi da Kabir yana bata labarin irin axabar da yake sha a school babu wani hutu,ji yake dama baiyi karatu cikin wannan makarantar ba,Noory na Daria tana fa?in.”kayi karatun ka yah Kabir kai namiji ne haka karatun ka yana da muhimmaci sosai cikin Rayuwar mu duka,wanda suka zama wani abu cikin Rayuwarsu sabida karatun ne,sabida karatun ne kake ganinsu har kayi sha’awar ka xama su watarana,karka karyamin zuciya dan Allah.”ta fada tana wani hade rai,xaija hancinta tamkar yarda
Suka saba tun suna gida,komai ya tuna ya jaye hannu ya maidasa baya gamida dan ware mata ido,murmushi tayi ta hade rai sosai tana fa?in.”meyasa ??ta tambaya tana kallonsa da dukkan idanunta take fa?in”sau biyu kenan,tana tuna masa da daxun da na yanxu,
Ya saki murmushi yana shafa kansa yake fa?in.”saboda kina matar Aliyu waxeer,jin ya ambace sa yasa ta mike afusace ta fara tafia yasha gabanta yana fa?in.”kiyi masa uxuri dan Allah ba haka fa yake ba,wani irin harara ta shiga xuba masa tamkar idon zasu fado duka,hawaye taji suna cika idonta lokaci daya,Ni ba kuka nace kiyi ba dan Allah kiyi hakuri ki kara hakuri
Nasan akwai ciwo ba yin kansa bane wlhi Captain ba haka yake ba,dame- dame ya faru?ki fadamin na baki shawara,Amma ban yarda da hukuncin da kike yimasa ba ,kuma Ni bana son wannan Hakeem din naki da kike kira Abokin ki ke bakinsa kishin namiji ba,namiji yafi macce kishi fa.shiru noory tayi xuciyarta na wani irin tafasa sai ga hawaye suka fara Rolling akan face dinta,Kabir ya dafe kansa yana kallonta.
.”Dan Allah stop being Quiet tell me idan yayi maki wani abu bana nan,cikin kuka take fa?in.”shima fa a gabana yake fita daita shopping agabana yake shiga room dinta,
Ko kallona bayayi an fada masa hakan da yake baya tabani ne??”ta fada tana fashewa da Kabir din wani irin kuka mai cin rai,Kabir ya hade rai yana fadin.”ina fatan bakiyi wani abu stupid
Da yasa ya daina kulaki ba,cikin shesshekar kuka ta kalli Kabir gamida yimasa wani irin kallo take fa?in.”shida yake yimin abubuwa fa,Ni ba mutum bace kamarsa kullum shi baya laifi nice Mai laifi,
Ae namiji ya kamata ya rika bin macce ba macce xata rika bin namiji ba,tun a waya na watsar da maganarka,dan baxan iya binsa ba wlhi kun cika son kanku dayawa,bude baki Kabir yayi yana kallonta,yaushe kika xama fitinanna haka ban sani ba??”ta juya ido tana fa?in.”shiya koya min,toh muje ki rakani wurinsa,ta girgixa kai tana fa?in”
Barci yake yi fa yaya?
Kabir ya duba agogon Rolex din dake kwance cikin damtsen
Hannunsa wanda kyauta ne ta hannu Aliyu waxeer,yace karfe goma fa?”xatayi magana Ammah ta karaso wajen su tana fa?in.”ka shiga ku gaisa da mutumin naka yanxu ya tashi barci,noory xoki daukar masa break fast dinsa sai kiyi masa jagora zuwa wajensa,wani iri taji
Suna isa kofar dakin
Ta mikawa Kabir tray din Hannunta tana rokonsa da idanunta,
Wani kallo ya mata yayi knocking na minti ?aya sannan ya tura kofar gamida barinta
Nan tsaye a wajen tafi minti ?aya a wurin kafin ta tura kanta cikin dakin ta hade fuska sosai,tunda ta shigo yake kallonta,
Kafin ya kalli Kabir yana fa?in.”idan xakayi aure ka auri macce biyu ,dan ko kadan macce daya a gida bata da ddin sha’ani idan wannan ta bata maka rai sai ka komawa wannan ,shiyasa nake da sha’awar tara mata Bama biyu ba hudu,Afusace ta nufi kofa tamkar xata tashi sama xuciyarta taji tana yimata wani irin zafi tasan daita yake,
Hawaye taji suna cika idonta har takai kofa
Ta juya da wani irin yanayi acikin muryarta
Take fa?in.”basai aga Wanda xai xauna da kishiyoyi ba ,wannan da Areefa mansoor kake ta fada tana bar masa kofar yabita da ido yana mamakin kalar rashin kunyarta,
Bata san lokacin da Kabir Yabar gidan ba,
Dan Adama ta rigasa
Wucewa tace zata shiga kasuwa,noory ta jata gefe ta damka mata dubi biyar tana fada mata ta ha?a dasu ta shiga kasuwar hawaye taji suna cika idonta lokaci daya,
Kowa na shirin zuwa
Kamu Banda noory
Da mamaki Aunty Ramlah ke kallonta kusan biyar da rabi take fadin.”ke baxaki bane??”naga ko shiri bakiyi ba, ance amarya ta dde da isa tun daxu nima wannan shegen telan ne ya tsayar dani,ki shirya sai ki jamu a motarki,nida Hajia saudatu,wato kawar Ammah,noory bata soba haka ta shirya cikin ankonta na less kalar Golding da orange cikinsa,Wanda in-laws na waxeer sukayi tayi kyau sosai acikin kayan,ta kalli Aunty Ramlah tana fa?in.”mayafin less din karamine Aunty nata jiran Hakeem waxeer
Ya kaini kantin sai da kaya na duba bai samu zuwa ba,abubuwa sunyi masa yawa,na saka wannan ta fada tana daga mata mayafin hannunta,baki bude Aunty Ramlah ke fa?in.”shi wannan mayafin meye laifinsa
Nima Baki ga Wanda
Nasa bane,idan kika saka mayafi kato
Baxa kiyi kyau ba wlhi,
Baki ganin yarda laylah ta ?ora mayafinta akan kafada,bikin gidane fah??’sa ki fito mu tafi Nooriyah Aunty Ramlah ta fada tana barinta tsaye a wajen kurawa mayafin ido tayi ,tasan baya son mayafi karami ,Allah kar ya hadata dashi har suje su dawo ,yayi tayi mata complain Akan laylah dashi ke Aurenta da yanxu sun samu matsala,sabida yanayin shigar da takeyi,Ammah ta kalleta tana fa?in.”kinyi kyau jewel murmushi tayiwa Ammah tana rufe fuskarta,Ammah ta kalleta tana fa?in.”ke baxaki karbi canjin kiyi liki ba,kije dakina acikin Bed side drower ki dauki naki,
Dagawa Ammah kai tayi ta nufi stairs Bata dde ba ta dawo su Aunty Ramlah sukayi gaba tabi bayansa,
Kusan karo sukaci dashi shi xai shigo ita zata fita,da sauri ya dafe kansa ya dago a fusace xai fara masifa
Sai kuma ya saki baki
Yana kallonta,mayafin da ta ?ora akan kafadarta yafi tsaya masa arai hade fuska tayi sosai tabi bayan Aunty Ramlah da sauri wani kallo ya bita dashi ,Afusace ya nufi parlor Yana kwalawa
Ammah Kira ransa yayi balain baci,irin wannan kira tamkar xaka tada gida meya faru??”Kinga mayafin da ta saka ki fada mata idan baxata saka
Mayafi babba ba ,ta dawo Ammah.”maxa nawa xasu shiga irin
Wannan wurin ki fada mata yanxu Ammah ta dawo,Ya fada sounding so very Angry a muryarsa,
Wani kallo Ammah ke yimasa tana fa?in.”igiyar Aurenka ke bisa kanta da xaka hana yarinyya motsi a duk inda ta shiga ,bana son shashanci Aliyu ka dawo Senses Dinka,
Ammah ta fada fuska a hade,ya dage kai yana jin kansa nayi masa wani irin ciwo zuciyarsa nayi masa wani irin zafi ,bai kara kallon Ammah ba ya nufi stairs Yana shiga kiran Areefa mansoor
Na shigowa a wayarsa.kallon wayar yayi tana ring har ta katse bai daga ba,ya harari wayar yana mamakin nacin Areefa bata gajia duk tabi ta ishesa, kashe wayar yayi duka ya xauna gefen bed,tuno
Noory kurum da mayafin da ta fita ya kusan tarwatsa zuciyarsa,wata zuciyar ke fada masa relax Ali..!””Dan taga kana kishinta ne shi yasa ta saka,jin yayi baxai iya hakura ba baxai bar noory ta shiga cikin maxa haka ba, car key ya dauka karo yaci da Ammah da mamaki take kallonsa tana fadin”.ka fasa cin abinci ne ??ya dakune fuska yana fadin.Akwai inda xanje Ammah sauri nake yanxu,da mamaki Ammah ke fa?in.”tun karin safe fa?”ya girgixa kai cikin sanyi murya yake fa?in.”bana jin dadin komai Ammah Black tea din ma dakyar na Sha dandanon sa yayi min wani iri duk bana jin
dadin jikina,cike da kulawa Ammah ke fa?in.”hop yau ka kira Areefa a waya karka kuma sakawa Yarinyyar mutane ido,
Nasan halinka da rashin daukar abu da muhimmanci,Ya kalli Ammah da wani irin
Yanayi yake fa?in.”xan kirata zuwa Anjima banda yanxu,da haka
Ya subbaci goshin Ammah yana fa?in……”kiyi min Addu’a a duk inda nake,ta girgixa kai tana fa?in “a koda yaushe addu’a ta na tare da kai,kaima kayi addu’a a duk inda zaka taka kafa ya daga kai
Ya fice daga parlorn
Ya kalli agogon hannunsa,yana tunanin minti nawa ya rage su nooryn su isa (waxeer hall)yasan Bata gudu da mota,har ta samu wurin zama dan su Aunty Ramlah can bangaren iyaye suka nufa,Batool waxeer taga tana nufota wanda fuskarta ta canja sabida make up.
Cikin muryar Rada take fa?in.”Aunty noory kije Yah Hakeem na nemanki
Yana a parking lot .”xaki gansa cikin motar Ammah,da haka Batool tabar wurin da sauri,cikin wani irin sanyayyen taku ta nufi cikin compound din xuba ido tayi taga ta inda xata hango motar Ammah,motocin na da yawa waya ta fidda da nufin ta kirasa da sauri Aliyu ya dalle mata fuska da hasken motar,wayar ta mayar cikin bag dinta ta nufi motar, Akwai tinted jikin motar bata hango wanda ke cikin motar
Hannu ta saka ta bude front side Bata kallesa ba sai da ta rufe kofar ya yayiwa motar key ,ido biyu tayi dashi gabanta yayi mummunan bugawa fuskar nan tasa tamkar hadari ya tada motar gamida fisgarta,da sauri security din wurin suka bude masa get ya fita da wani irin speed…..lokaci daya hawaye suka fara Rolling Akan face dinta.

Good day Everyone
Ga break fast na
Baku, xuwa da yamma xan baku sabon update…..

*Idan kika karanta min book baki biya ba ,ban yafe maki ba…*!!!

Littafin Waminal Hoob
Na kudi ne#500
Account Details
0004157137
Jaiz Bank
Asma’u Buhari Aliyu
Katin wayar MTN.ta wannan lambar#09060259200
Shaidar biya ta wannan lambar#08086207767

WM#.
ASMY#??
[9/15, 6:11 PM] Asmy Mom Aydah

Back to top button