Hausa NovelsHausa NovelsWaminal Hoob Hausa Novel

Waminal Hoob 46

Sponsored Links

Asmy Mom Aydah??: 46….

Hawaye kawai ke Rolling akan face dinta,bude baki Ammah tayi tana kallonta ta xauna gefen bed tana fa?in.”kukan me kuma kikeyi??”keda xakiyi murna an samu ya dawo hankalinsa sai kuma akasin haka,ta wani rungume Ammah still hawaye na xubar Mata cikin shagwaba take fa?in.”Ni baxan bisa uk ba Ammah zan xauna anan,Ammah tace yayi tafiarsa kenan??”yaje kuma ya fara dating da wata jar fata.”ke wace irin shashace ana nuna maki gabas kina yin Yammah,so kike mu xauna acikin gidan,
Idan nayi kwaliyya kema kiyi mu xauna
Parlor muna kallon Movie.”haka kike so??
To ba Dani ba wannan sakarcin ki tashi kiyi wanka ke nake jira muje na saukeki gidan
Adama,ki kwana biyu kafin lokacin tafiar ku
Ga kayanki nan na hada tunda na lura ke baki san ciwon kanki ba,da haka Ammah tabar mata Room din
Kallo tabi Ammah dashi,idan ta tuna cikin Farhaan ne jikin Areefa mansoor wani mugun bakin ciki ke mamaye mata xuciya,Ammah nata jiranta a parlor Kusan minti talatin sai gata ta fito janye da karamar trolley bag nata,dai-dai lokacin Areefa ta fito daga kitchen rike da mug a hannunta tana juya cornflakes,lokaci daya Areefa ta maida hankalinta kan noory dake rike da bag,batayi niyar xama parlorn ba sai ta samu kanta da xama,tana murmushi take fa?in.”tafia xakuyi Ammah?ta fada sounding so very happy Wanda har hakan ya kasa boyuwa cikin fuskarta,Ammah tayi murmushi tana fa?in.”nooryn ce dai xata tafia xuwa Sokoto gidan Ramlah xata xauna acan ina son ta xauna acan ko
Xan samu ta fitar da Aliyu daga ranta,tunda ta kasa kwantar da hankali ta kula Hakeem,inhar Bata son Hakeem ga maza nan ae ba karewa sukayi ba,sai ta samu wani zaman ne ya isheni…..”Ammah tayi maganar tamkar gaske tana wani irin hade rai, wani blushing Areefa ta fara saki ta kalli noory tana fa?in.”kiyi hakuri Dan Allah noory ?addarar kice a haka,
Nasan ma very soon xaki samu miji wanda yafi Aliyu komai kiyi aurenki ki huta, da alama kam baya sonki nacin na menene??”,kema ya kamata ki nuna masa macce ce,kina da Aji
Idan bakya son Hakeem waxeer Shima bbu dole ga maxan nan xube a gari,kuma yarda nake jin maxan Sokoto suna bautawa macce idan suna sonta,ke dai Allah ya baki na gari,
Ta karasa maganar tana sakin wani irin blushing tunda take da noory bata ta?a yimata magana mai tsayi da kwantar da kai kamar haka ba,ita dai noory ko kallon Areefa batayi ta nufi kofa a mugun fusace
Da ladabi Areefa ke fa?in.”a dawo lafia Ammah,Ammah ta daga mata kai tana fa?in.”xanje na sauketa a airport ki kula da gida sai na dawo,da haka Ammah ta nufi kofa Ammah na ficewa daga parlorn ta saki wani irin Ihu,tana zagaye parlorn tana rawa,bata ta?a farin ciki ba irin wannan Ranar ,wa xata kira tayi sharing farin cikinta dashi???”.
Bata ta?a tunanin abubuwa zasu xo Mata da sauki ba,daki ta nufa da sauri ta sakawa kofarta key ta dauki wayarta tana kokarin kiran layin Siddiqa mansoor…..Ammah na driving ta kalli Noory fuska babu wani walwala take fa?in.”idan xakiyi hankali sai kiyi kinga ita har farin ciki take kibar garin duka ta samu ta kwace maki
Mijin kina nan kina sakarcin ki,toh ae sai ki kara rikesa da kyau kin dai ganarwa idonki,idan kuma kina so ta biki can da asirin ta wullaki a wata duniya ta kwace maki shi ae shikenan,juyawa tayi tana kallon Ammah sai dai batayi magana ba,har suka kai gidan kawu Ammah nayi mata fada tana nasiha,da wani farin ciki Adama ta tarbesu,
Ammah ta baiwa Adama labarin yarda sukayi da Aliyu gidan Baffa waxeer,babu abunda Adama ke saki sai kabbara.!”haka ta bata
Labarin yarda sukayi da Areefa da sakarcin da nooryn keso tayi na baxata bi Aliyu zuwa uk.ba baki wangalau Adama ta saki tabi noory da wani irin kallo,bata ta?a sanin noory sakarya bace sai yau amma xata gyara mata xama zuwa Anjima idan Ammah ta tafi,akwai kayan mata dana tura sako har Kano,
Wajen wata (Deejarh Berverh)nima wata kanwata dake Aure can ta bani labarin matar na siya nayi amfani dasu naga amfanin su wlhi nida ma ke haka na kwana biyu,baranta na keda kike sabon jini kin tsaya shirme. na tura mata wasu kudin
Shekaran jia ta turomin dasu ta mota kusan kayan dubu talatin na siya maki,wani irin dadi ya rufe Ammah dama har dashi takeso ta tattauna da Adama,itama xata bincika wasu anan zuwa jibi ta kawo mata ,Ammah ta dde suna tattaunawa kafin tayi masu sallama,
Har kofar gida Adama ta raka Ammah tana yimata godia,noory tana kwance cikin dakin Kabir wanda yanxu an gyara dakin sosai harda kayan kallo ya saka ga kuma fankar kasa,lumshe ido tayi a hankalin take tuna abunda ya faru jia,taji Adama ta shigo a dakin dama ko wancan zuwan da tayi a dakin ta tare nan take kwana tunda Kabir din yana makaranta,itama safiya tuni Aliyu ya samar mata gurbin karatu a (Queen Ameena)Adama ta hade Rai lokaci daya tana fa?in.”tashi ki xauna muyi magana,
Babu musu noory ta
Mike ta xauna dai-dai
Gamida fuskantar Adama,shaye da toka
Adama ke kallonta tana fa?in.”ki fadamin meyasa bakya son binsa acan kasar da yake aeki,lokaci daya hawaye ya cika idonta
Cikin takaici Adama ta girgixa kai tana fa?in.”Ni ba kuka nace ki xauna kiyi min ba
Baki xaki bude kiyi min magana,cikin rawar murya hawaye na xubo mata take fa?in.”kawai bana son binsa na fiso na xauna
a Nan ,ita dai adama baki bude take bin nooryn da shegen kallo babu sakarya irin
Noory,to bari kiji in fada maki daga yau bana son ki kara bude baki ki fadi kalmar baxaki bisa ba dan binsa tamkar kin gamane,ke ko kunya bakya ji agaban mahaifiyarsa kike fa?in haka kin san ko kadan ne baxata ji dadi ba a ranta,kuma gyaraki xan farayi daga yanxun nan kin san halina wlhi bana son musu da na baki abu ki buda baki ki shanye tas,dan wlhi baxan yi hasara ba Ni ba irin Ammah bace mai wani lallaba ki,xuwa Anjima xamu fara kici abuncin dai tukuna ki koshi,Bara naje na fara dafa maki sassaken baure da minannas,kanin fari maxan kwailah, dama da kuma zuma,dama kamar na sani na siyo su kasuwa jia,daga yau sune ruwan shanki acikin gidan nan har ranar da mijinki xaixo
Ya daukeki….Shasha kawai!”Adama ta karasa maganar tana bar mata Room din,
Da kallo noory ta bita har ta fice daga room
Din,ko kadan bata son waya’nnan kayan matan sun sakata shiga wani irin yanayi mai wuyar misiltawa,
Ita kuma bata shirya baiwa Aliyu kanta yanxu ba,kowa baya ganin abunda take hangowa sai wani tattalinsa ake tamkar sarki ,duk laifin da yayi mata ya tashi a banxa,
Komai xai faru baxata baiwa Aliyu kanta yanxu ba,ita ba sakarya bace baxai sameta a bagas ba su gama duk wani shiri akanta bai isa ta bashi jikinta ba,yaje ya gama
Tabe-tabensa da Areefa mansoor yanxu xai wani dawo kanta,kwanciyarta ta tayi bayan tayi sallar axxahar,kusun 3 Adama ta shigo dakin da abinci da kuma katon jug na sassaken bauren da ta ha?a mata,lokaci daya noory tabi jug din da kallo gabanta na mugun faduwa,da sauri ta kalli Adama
Adama ta hade rai gamida zama kan carpet dake malale acikin dakin Kabir,ta wani hade rai
Tana fa?in.”ga abinci ga kuma kayan dadi
A gefe tamkar Noory xatayi kuka take fa?in”ummah ae wannan abun yayi min yawa da wane ciki xan xubasa,acikin cikin ki mana..shinkafa da miyar kusan rabi taci tace ta koshi ,ta dauki jug ta kafa kai,tamkar xata shede ko rabi bata sha ba,ta fadawa Adama ta koshi Adama ta girgixa kai gamida daukar jug din
Tana fa?in.”mu hadu Anjima dan baxan bar maki ma jug din ba ,ki xubar Kara na Rika kawowa kina sha a gabana,haka ki shirya Anjima xaki fara shan kayan yar Kano,da haka tabar mata Room din,cikin kwana biyu Adama ta saka noory agaba da abubuwa da take loda mata cikin ciki,acikin kwanakkin nan har pad take sakawa ,sabida yarda
Ruwa ke xuba ta kasanta,tun tana yiwa Adama kuka idan taxo sha har ta gaji ta xuba mata ido,haka Ammah ta kawo wasu cikin kwana biyar duk taji gidan kawu balele ya fice daga ranta sabida
Kawai Abubuwan da Adama ke bata tana sha,Ni nasan irin shirin da nayi maki sai dai idan baku hadu da Aliyu ba,wlhi ko wuta kikace ya fada tsaf xai shiga batareda yayi maki musu ba,xaki tuna wannan maganar tawa watarana,ana sauran kwana ?aya su wuce Ammah ta kawo mata sauran kayanta ,turarrukan wuta na jiki da kuma na daki harda su humrar mata masu shegen kamshi,sosai Ammah ta kwantar da kai tana yimata nasiha a matsayinta na mahaifiyarta ba mahaifiyar Aliyu waxeer ba,haka ta ?ora da fa?in.”ki zama karuwa cikin gidan mijinki dan maxan yanxu idonsu a tsaye yake,sunfi son macce marar kunya har dai a shimfidar Aurensu,Ramlah xata kiraki vedio call idan an kwana biyu xatayi maki nata nasihan,gobe tun da safe xaixo ku wuce Abuja ya fada min jirgin karfe biyu xakubi zuwa uk.ki xama cikin
Shiri kuma kiyi ta hakuri Dan Allah.”Ammah ta fada muryarta na karyewa,itama Adama ta ?ora da nata,Ammah ta kalli Adama tana fa?in.”Aliyu yace xai shigo zuwa dare ku gaisa idan kawu ya dawo,dan yace ba lallai ya samu kawu da safe ba….sai gafda magrib Ammah tayi masu sallama,
Kallonsa kawai take cikin shadda kalar sararin samanyi, harda hulan kayan ajikinsa sai wani uban kamshi yake xubawa tamkar wani ango,komai na jikinsa sabone,gabanta na faduwa take kallonsa tun daga sama har kasa,tana fa?in.baby ina kuma xakaje yanxu??”ya xauna cikin soofa yana fadin.”xanje na gaisheda Baffa kin san gobe da safe xan wuce ba lallai bane mu ha?u,gaishesa shi xai saka kaci wannan gayun haka??”tayi maganar cike da kishi a muryarta,so kike naje masa da kaxanta ne wai meke damun kine Areefa??”yayi Maganar sounding so very harsh,Dan tanata kure hakurinsa,saukar da murya tayi tana fa?in.”yi hakuri dan Allah,ta dauki mayafinta da murmushi a fuskarta take fa?in.”muje nayi maka rakkiyya zuwa gidan baffan,wani shegen kallo ya shiga yimata,yana fa?in.”A saboda bakya da hankali !”wai bakya ma jin kunya kibi ni haka da cikin shege bakya jin wani iri aranki,ya nufi kofa yana fada mata sai ya dawo,wani kallo ta bisa dashi ta samu gefen bed ta xauna tana jin hawaye na cika idonta,ko kadan Aliyu baya jin shakkar kallonta ya fada mata
Magana,yanxu ta daina bin kaidar malam koda yaushe cikin shafa kwalli take
Amma ta lura baya wani tasiri akansa,dole ta nemi Aunty Siddiqa su koma wajen Malam,
Sosai kawu balele da Adama suka tarbi Aliyu cikin mutunci da giramawawa,tun shigowarsa ta fada dakin Kabir harda su tura kofa kuma gaya nepa ta dauke,haka nan tayi kwanciyar ta cikin duhu tana jin hirar su,xuba ido yayi yaga ta inda xai hangota Amma ko gilmawarta bai gani ba,kawu ya mike yana fadin.ni dai na tafi majalisar mu ta kofar gida idan ka fito ina waje,ya amsawa da kawu da toh.Itama Adama ta fada masa ya shiga Nooriyah na cikin dakin Kabir itama daki ta koma ,
Duhu ne sosai a dakin
Wayar hannunsa ya fidda gamida kunna fitilar wayar saurin tura kanta tayi cikin pillow kamshinsa ya sanar mata ya shigo dakin,
Kallonta kurum yake,
Haka kamshin turaren da dakin yake yana birkita tunaninsa,yasan ba barci take ba.saboda shi ta tura fuskarta cikin pillow gyaran murya yayi yana fadin.”ki tashi muyi magana ko na cire riga naxo mu kwanta tare,kinga ko kwana nayi a nan babu mai tambayata dalili sabida wurin matata na kwana,da sauri ta mike xaune tayi wani irin hade rai,shi daria ma take basa wlhi.Ya xauna gefen katifar ya kalleta cikin sanyi murya yana fa?in.”Ya kike??”shiru tayi masa
Tana dan jada baya alama bata son kusancin su,ya kalleta yana shafa kansa ya saki murmushi yana fa?in.Axumin magana kike kuma??”nan ma shiru tayi masa ya girgixa kai ransa a jagule yake fa?in….kiyi hakuri da duk abubuwan da suka faru ba dan na bata maki nakeyi ba kawai ina yine sabida
Na samu wani abu a tare da Areefa cikin hankalina nake yin komai,ban so mu gina Rayuwar Aurenmu da karya shiyasa tun farko ban boye maki alakarmu da Areefa mansoor ba,ban taba xina ba!!!”kiyi hakuri ki yafemin dan Allah.”ta bude ido tana kallonsa cike da takaici take fa?in.”kwanan da ta sabayi a gidanka na menene??ko shima kana nufin kace baka taba…..kasa karasawa tayi kalmar nayi mata wani irin nauyi a kirjinta,kallonta kawai
Yake yana mamakin mugun kishi irin na Noory ,ki karasa mana
Nasan ina kananan aekata xunnubai da Areefa amma wlhi ban taba xina daita ba,hawaye taji suna cika idonta lokaci daya wani kishi na sauka kan xuciyarta a fusace ta sauka kan katifar ta mike tsaye da shirin tabar masa dakin lokaci daya ya fisgota,ta fado kansa
Kokarin fisge kanta take ya daka mata tsawa,yana fa?in.”?aryar ce bana son yi maki shigowarki cikin Rayuwata komai ya canja na daina kula Areefa na daina aekata kanannun xunubbai daita,saboda ban taba sanin ba soyayyar Aure nake yiwa Areefa mansoor ba sai da kika shigo cikin rayuwata ,baxan yimaki karya ba. lokacin ina rage xafine tare daita amma duk da haka ban taba kusantarta ba idan kema kina tunanin sha’awarki nake ba wai soyayyar gaskiya nake Maki ba kinyi karya .”ban taba son wata Yah macce a dunia ba bayan ke,
Haka ba sha’awar ki nake ba,ina yi maki soyayya na hakika wanda babu haram acikinsa ,idan kina tunanin jikinki nake so kinyi karya”.da ina son jikinki da yanxu na gama kar?e wannan abun da kike yimin wulakanci akan sa ,
Haka baxan takuraki
Dole sai kin bani hakkina ba,kuma abunda kike jamin aji dashi kije kiyi ta jika kayanki ki sha.Ranar da kika sauko akan laifin da ban san nayi maki ba tunda na baki hakuri kinki saurarata kece macce ta farko da na buda baki ina fada mata siirina haka na bude baki na baki hakuri akan duk laifukkan da nayi maki A baya.,nayi ne acan baya kuma yanxu na tuba na dawo hanya,meyayi kuma saura?”ta fisge kanta hawaye na xubar mata take fa?in.”Har abada kuma baxan baka kaina a banxa ba,kaje na yafe maka Areefa kuje kuta sabon Allah yarda kuka saba,Ransa yayi mugun ?aci akan maganganun da ta xuba masa mikewa kawai yayi tsaye Yabar mata Room din,ko sallama baiyi da Adama ba,tunda tayi sallah adama ta hanata komawa barci,
Sai da tayi wanka
tasa tayi turareren xukunno,
Wannan abubuwan da ake yimata ya isheta,
Saboda Aliyu ake wannan gyaran su basu ma san baya gabansa ba, sai tsabar wulakanci da rainin
Hankali,tana gama break fast wajajen 8
Aliyu ya shigo gidan ya gaisheda Adama da ladabi ,ta amsa da fara’a tana fa?in.”an tashi lfy,ya amsa da lafia lau,ya aje mata rafar kudi daya na Naira dubu-dubu,sai godia Adama ke xubawa yasa aka fita da kayanta zuwa mota,nasiha Adama ta ha?a tayi masu shi kawu yayi tasa da dare jia,hawaye kawai ke Rolling akan face dinta,har suka dau hanya ko kallonta baiyi ba yayi mugun hade fuska tamkar hadari,har suka isa Abuja babu wanda ya kula wani acikin su,
A gidan nasir Waxeer sukayi lunch .Hakeem sai tsokanar Noory yake ita dai batace komai ba,kusan karfe biyu su Batool sukayi masu Rakkiyya zuwa air port ko acikin jirgi basu xauna wuri ?aya ba,a seat din baya ta koma shi kuma yayi xamansa a gabaa…..wata irin Rayuwa suke a kasar London babu ruwan kowa da kowa ,kara ma zamansu na farko da wannan lokacin shima Aliyu ba wani zama yake ba,kullum Yana busy,sai yayi kwana biyu bai hadu daita ba,lokaci daya tayi wata irin rama harda kashin wuya ta axa,satin su daya a kasar London Aunty Ramlah ta kirata vedio call irin ramar da taga nooryn tayi lokaci daya ya daga hankalinta,cikin rawar murya Aunty Ramlah ke fa?in…”meye haka
Bakida lafia ne kika axa wannan uban rama haka ina Aliyu kuma?? Aunty Ramlah tayi maganar da tashin hankali cikin muryarta,lokaci daya noory ta fashe da kuka mai taba zuciya duk tabi tasa Ramlah waxeer ta shiga mugun damuwa,tell me meya faru??”ko Aliyu yana yimaki ba dai-dai ba,cikin kuka take fa?in.”tunda muka xo uk baya kula Ni baya yimin magana ina kwana 2 ban gansa cikin gidan nan ba,nidai ki fadawa Ammah wlhi Nigeria xan dawo baxan iyaba wallahi !!!”tayi maganar cikin shesshekar kuka Aunty Ramlah ta Runtse ido tana jin wani irin zafi a xuciyarta take fa?in.
Kalleni nan noory ,
Noory ta kalli Aunty Ramlah still hawaye na xubar Mata,ki fadamin tsakaninki da Allah bake kika tabasa ba.”nasan Aliyu ba haka yake ba yana da xuciya kuma yana da hakuri ki fadamin meya faru,karki boyemin.”cikin kuka take yimata bayanin yarda sukayi a gidan kawu,bude baki Aunty Ramlah tayi tana kallon sakarci irin nan noory,to ba ya kwantar da kai ya baki hakuri ba,basai kiyi hakuri ba
Kuma gaskiyya ya fada maki ba sai ki godewa Allah da ya dawo dashi hannunki ba, sai kuma ki rufe ido ki gasa masa magana saboda mahaukacin kishi irin naki,ae ko nice Aliyu ki jika kayanki Kisha haka xan fada maki, Muna na Nan mun bude baki muna murna zaman ku lfy
Haka harka ta kankama muna bukatar muji abun Alkhairi ashe ba haka bane……..”kin bani kunya wlhi Nooriyah bari na fada maki duk soyayyar da namiji keyi maki karki bude baki.baki tauna magana ba ki wurgo masa ita,ba’a haka nan,yanxu share hawayenki.lokaci daya noory ta share hawayen idonta ,karfe nawa yake dawowa??
da 6 tayi yake dawowa bai kara fita kuma sai gobe,tunda kuka zo kinyi girki??”girgixa kai tayi toh yau ki shiga kiyi masa girki haka ki tabbata kin gyara gidanki,kinyi wanka
Ina turarrukan da Ammah ta baki.”suna nan aje,ki tabbata yau kinyi amfani dasu,yau
Nayi maki Alkawarin sai Aliyu ya kawo kansa,saura kuma kiyi masa wani abu stupid da xai sa ya kara fusata sa,bance ki kai kanki garesa ba ki xauna naki dakin ni xan kirasa yau dole yaje inda kike……sauran Abubuwa xanyi maki voice note ki saurari abubuwan da xan fada maki da kyau,da haka ta kashe wayar ta dde zaune tana juya maganganun Aunty Ramlah aranta,haushi duk ya cikata tun lokacin data fara shan kayan dasu Ammah suke bata take yawo da pad sabida yarda ruwa ke saukar mata,kunya tasa ta kasa fadawa Adama haka……

Idan baki biya ba kika karanta min wlhi tallahi ban yafe maki ba.”!

Littafin Waminal Hoob na kudi ne#500
Account Details
0004157137
Jaiz Bank
Asma’u Buhari Aliyu
Katin wayar MTN.ta wannan lambar#09060259200
Shaidar biya ta wannan lambar#08086207764

Thank you.

Back to top button