Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa Novels

Arubuce Ta Ke 100

Sponsored Links

Page 100

A hankali take taka harabar gidan,tana jin kamar magnet ke janta zuwa waje,har ta kusa da gate din ta taka wani dan qaramin dutse mai tsini,zafin da ya soketa ya sanyata furta

“Subhanallah” ta tsugunna tana dub qafar,Allah ya taimaketa bata huje ba,banda zafi da radadin da takeji kawai,koda ta dago sai ta tsaya tana duban qofar fita daga gidan dake kulle,tare da tunanin meye ya fito da ita a wannan daren?,saita girgiza kai ta juya tana komawa ciki.

A hankali yake takowa zuwa dakin solar na gidan,don ya duba yana tunanin kamar sale bai kulle ba,cike da mamaki yake kallonta sanda take takawa zata koma sashenta,to daga ina take?,da alama ma bata ganshi ba,sai ya canza akala ya dosheta.

A tausashe ya kamo lallausan tafin hannunta ta baya,tadan firgita kadan sannan ta waiwayo suka hada ido,ta saki waya ajiyar zuciya mai nauyi

“Ina kikaje haka”

“Babu ko ina,kawai na gaji ne” qarara ya karanto zallar gajiya da qin da takewa garin na bauchi a idanunta,sai ya jinjina kai

“Muje kidan motsa,dama kin fara qiba ba dole ki dinga gajiya haka kawai ba”.ya fada cikin salon tsokana yana lakuce mata kumatu,sai ta shagwabe masa tana tabe baki kamar mai.shirin sakin kuka,sakato.yayi yana kallonta tana sake tsumashi,don dama duka.yau din baiga wannan narkakkiyar shagwabarta ta ba,sai tsomoshi da shigar data dinga yi a sunan data dinga yi,duk sanda zai.shigo kuma sai yayi tozali da ita,ya dinga jin kamar ya dauketa subar gidan ya samu ya rage zafi,amma sanda yaga yawan jama’ar dake sashenta dole ya haqura ya hadiye,hafsat kuma ko a yanzun a dakinsa ya barta,ko kwana daya bata yarda ta bariwa widad din ba.

Sassanyar iskar daren dake kada jikkunansu ta dinga haifar musu da wani yanayi cikin zukatansu,kada ma abbas din yaji labari,ya sake matsowa ya.kama hannunta suna ci gaba da strolling

“Jibi zamu wuce,gobe ki kammala komai naki” da mamaki take dubansa har batasan murmushi ya subuce mata ba,bata dauka zasu koma da wuri haka ba,saboda taji yana cewa babu cinkoson aiki sosai,ya waiwaya a hankali ya sauke mata narkakkun idanunsa

“Oh……murna ma kikeyi?” Nata fararen idon ta juya,lallausan murmushin dake qara fidda quruciyarta ta saki tana maida dubanta gefe

“Dole ne ai……zan sake da uncle dina” murmushi mai dan sauti ya saki yana kallonta cikin mamaki,sannan cikin tsokana yace da ita

“La la la…..eh lallai zan gayawa uncle muhsin,yarinyarsa tasan dadin mijinta” ya fadi qasa qasa dab da fuskarta,sai ta saki dariya tana zame hannunta daga nasa cikin jin kunya

“Don Allah uncle karka fada” ya bita da sauri yana son cimmata yana sake tsokanarta kan sai fa ya gaya masa.

Kamar yadda yace din kwana daya suka qara suka tattara suka koma kaduna abinsu,hafsat din tana ta cika tana batsewa,don ko fitowa batayi ba,daga daki sukayi sallamarsu suka gama.

Ajiyar zuciya mai nauyi widad ta sauke sanda motarsu ta fita daga qasar bauchi tahau ta kaduna,har sai da abbas din ya juyo ya kalleta.

*********Cikin wata muguwar zabura ta farka tare da miqewa zaune saman gadonta tana rarraba idanu,gumi sharkaf ya jiqa mata ilahirin rigar atamfar da take jikinta yana zartarwa cikin jikinta,kadan ya rage ta danne baby yusra dake bacci a gefanta,ji tayi kamar alqiyamarta zata tsaya,wannan wanne irin mafarki ne mai muni mara dadin gani?,me mafarkinta yake nuna mata kenan,widad dauke da baby tana miqo mata ita?,me hakan yake nufi?.

Wayarta ta jawo tana dubawa kamar me neman wani abu,a sannan tayi ido hudu da number abbas,waddda itace kira na qarshe a jerin lambobin da aka kirata ko tayi kiran,awanni hudu da suka wuce,yake gaya mata jibi zasu iso bauchin,duk da sai da suka kusan dan samun sabani saboda a maganarsa ta fahimci da widad din xasuzo,abinda duk duniya ta tsana kenan a yanzu,take kuma neman hanyar da zata kawo qarshen faruwarsa.

“Anya ba ciki ne da yarinyar ba?” Wata zuciyar ta gaya mata,saita hau girgiza kai da sauri kamar hauka sabon kamu,kai kace ita da wani suke magana a dakin

“Inaaa,inaaa,bazaiyiwu ba” ta fada a fili,ba zata taba barin haka ta faru ba muddin tana raye,cikin abbas ace ya tabbata a jikin wata?,da kuwa lallai ta rako maya duniya,ta kuma cika hasararriya,iya qiyasta hakan kawai da tayi sai taji kamar zuciyarta zata tsinke tabar qirjinta,haka fa na nufin ya hada shimfida da ita?,ya santa a matsayin diya mace

“Aah….. a’ah” ta sake fada tana girgiza kai da sauri.

Ji tayi kamar ta kirashi tace su taho gobe,lallai kuma yazo da widad din, saboda tanason ganewa idanunta,shin da gaske ne abinda zuciyarta ke raya mata?,ko hasashe ne hadi da shirmen mafarki?.

Wanann daren sai ya zame mata baqin dare,don tunda ta farka ta gagara komawa,saidai ta zauna idan ta gaji takai ta kawo har asuba ta risketa a haka.

********Sau biyu yana duba agogonsa sannan ya maida dubansa ga qofar fitowa daga sassanta,kusan minti goma tace tana zuwa,amma har yanzu bata fito ba,bata saba hakan ba,ba halinta bane,duk sanda zasuyi tafiya ko zasuje waje bata fiya bata masa lokaci ba,idan yace qarfe kaza kome takeyi ta kammalashi kafin wannan lokacin.

Fitowa yayi daga motar hannunsa sanye a aljihun wandon yadin cashmere mai asalin kyau da tsada,wanda ya karbeshi qwarai,ya tunkari sassan nata yana fatan samunta lafiya.

Saman kujera ya sameta zaune,tayi likimo a ciki kamar bamai shirin tafiya daga kaduna har bauchi ba,sai daya isa kanta sanann ta daga idonta ta kalleshi,saita miqe cikinmu mutuwar jiki tana sauko da qafafunta qasa hadi da gyara rufin veil dinta tana cewa

“Sorry uncle,yanzu nakeson fitowa”

“Me ya sameki?” Ya tambayeta kansa tsaye yana tsare sosai da idanu,qas tayi da kanta,batason gaya masa amai tayi kuma jiri take ji,batason hankalinsa ya tashi

“Me yake faruwa dake ne?,ki gayamin gaskiya,karki yadda kicemin ba komai,jiya da daddare na ganki,tashinki nawa kina shiga toilet,na tambayeki kuma kikacemin lafiya qalau” yadda yayi tambayar cikun seriousness sai ya koma mata ASP abbas sosai,miskilin nan mai tsare gida da baiwa masu laifi tsananin tsoro,dole ta buda baki a hankali tace

“Amai nayi,sai jiri,sai kuma fitsari da nakeji,idan naje yi kuma sai naga dan kadan,marata tayi kamar an saka dutse” shuru yayi yana kallon fuskarta,wani abu ya darsu a ransa,amma sai wata zuciyar ta kawar,don ba haka ya saba gani ba,ya miqa hannnunsa a hankali ya taba wuyanta ya janye hannun jin babu zazzabi

“Subhanallah,amma shine kike ta cewa ba komai baby?” Kai ta langabe batace komai ba,sai qishirwa dake damunta,kamar ya gane me take nufi,ya isa fridge ya ciro mata ruwa mai madaidaicin sanyi ya bude ya miqa mata,tana tsaka da sha ya nema gefanta ya zauna yana murza agogon hannunsa

“Banajin tafiyar nan zata yiwu……”

“……don Allah uncle” tayi saurin katsar numfashinsa,tunda taji zasuje ayi mata vaccination na tafiyarsu wadda duka duka saura kwanaki biyar ta matsu suje din,ido ya lumshe yana dariya

“Bance wai an fasa ba,nima inason zuwa naga hajiyata,bazata yiwu ya mota ba,bari na duba mana rocket ko zamu samu koda evening flight ne” ido ta rufe tana dariya,kunya kuma tana kamata na yadda tayi saurin yanke masa hanzari

“Kayi haquri uncle”daga kansa yayi daga danna wayar ya kalleta yana murmushi,bai taba zaton bada haquri abu bane mai sauqi wajen diya mace ga mijinta ba sai daya zauna da widad,kalmar haquri kalma ce mai matuqar tsada da wahalar furtawa a wajen hafsat,tsahon shekaru bakwai,adadin lokuttan da ta taba buda baki ta bashi haquri tsaf zai iya qidayesu da yatsun hannunsa.

Kafin su fita daga gidan zuwa airport ta qarfafa jikinta,duk don wai ya sake yadda ba wani ciwo take ba,ya kuma janye maganarsa na suna sauka yau din gobe zai kaita a dubata.

Sau uku tana kiransa wayarsa a kashe,ta qagu su iso tayi ido hudu da widad din kamar yadda ummanta tace ta fara tsaiwa ta tabbatar da gaske da cikin?,ta duba idan taga wani canji tattare da ita,idan akwai alamunsa to zasu bincika su dauki matakin da duk hafsat din taso.

Tana parlor tana shayar da baby yusra,su nawwara sunata sabgarsu cikin falon,sassan dai kamar ko yaushe sauqi sai wajen Allah,duk da ta dauko diyar anty ummee ta tayata zama har zuwa sanda zatayi arba’in,to amma itama yarinyar aikij ya mata yawa,abinda taga zata iya shi takeyi.

Ko kusa ko alama bataji alamun shigowarsu ba,don mota ya dauko daga airport,ba kamar yadda ya saba ba,idan flight zai biyo yana kiran umar yazo ya dauka motarsa dake nan ya daukoshi ya kawoshi gida.

Yusra ta cire daga shayarwar da takeyi,idanunta a kansa sanda yaran suketa rige rigen isa wajenshi.

Mummunan kishi ya kama zuciyarta,duk sanda zaizo mata weekend sai taga ya canza,sai taga ya qara fresh ya qara murmurewa fatarsa tayi wani lumaui,komai nasa fes kamar wanda akewa wankan inji.

Qarasowa yayi ya duqa yana shirin karbar yusra,dai dai sanda take masa sannu da zuwa,ya amsa yana dan dauke numfashinsa hadi da daukan yarinyar yana kallonta,tausayinta yana cika zuciyarsa,ba alamun qamshi jikinta bare na mahaifiyarta,yadan ja kumatunta yana mata wasa duk da ba gane komai takeyi ba,yayin da hankalin hafsat ke kansa,tanason jin tare suka zo?.

Amsarta ta fito kuwa sanda mimi ke tambayarsa ina anty widad?,yauma batazo ba?.

Murmushi ya sake,qauna ce sosai da shaquwa me yawa tsakaninsu da widad din,tamkar ma itace ga haifeta ba hafsat din ba

“Tazo,muje ku gaisa” sai ya sanyasu a gaba suka fice,suka bar hafsat da lissafin yadda zata shiga ta ganta din,don yarinyar ya canza hali,wani irin canji da tafi zaton akwai masu zugata na gasken gaske daga gefe,tasan tsaf daga halinta ba zasu hadu ba sai ranar da zata koma Kaduna.

Ya sameta harta cire kayan jikinta,ta saka wata black rmless gown A shape,tabi lafiyayyar farar fatarta ta.kwanta,ya bita da kallo tsigar jikinsa na zubawa,yana jin wani abu mara dadi na masa yawo a rai,yasan yau da gobe duka zaiyi missing dinta,saidai yasan zasu hade a kano,kuma tabbas zaya fanshe kafin su tashi.

Bakinta har kunne ta karba yusra tana mata wasa,ita da mimi da nawwara duka sun zagaye yarinyar,tana mata waqa suna mata amshi,sai ya koma gefe ya harde hannayensa yana kallonsu murmushi yana qwace masa,yana hasashen yaranta kamar haka.

Daga kai tayi suka hada ido,sai ya kashe mata ido daya yana mata murmushi,ta maida masa martani,Allah ya zuba mata son yara,baisan wanne irin son yara gareta ba,abinda ko uwarsu data haifesu bata damu da yi musu ba amma ita saita bata lokaci tana wasa dasu hadi da kula dasu.

Anan yabar mata duka yaran ya wuce sashensa, pampers din yusran da widad din taga ya cika da kashi ta cire mata cikin jin tausayin yarinyar

“Tun dazu da take kuka na cewabmommy kashi tayi sai tace ba yanzu zata cire mata ba” duban mimi widad tayi cikin mamaki,itadai ta sani,yayyenta da matan gidansu duk sanda yaro yayi bayan gida cire masa shi sukeyi,takanji sunce yana cin jikin yaro sai wajen yayi ja ya zama ciwo.

Wanka tayi mata da ruwa mai dumi sosai,ta shafeta da farar powder ta goyata ta fara gyaran sashennata,tana aikin yarannna biye da ita,yau daya nishadinsu ya canza,sashen ba aiki sosai don ba datti bane sai qura,nan da nan ta gama ta cikashi da wannan qamshin da ya zamewa gurin jiki.

Ko kafin ta gama ma yarinyar tayi barci,saita kwantar da ita tayo wankan itama ta sauya kaya ta zura hijab ta tayar da sallah.

Tana idarwa hafsat tana sallama,ta shigo idanunta akan widad din kamar zata cinyeta,bata lura ba don zuciyar a wanke take,ta gaidata ba yabo ba fallasa,ta amsa tana sake qare mata kallo.

Tabbas tayi qiba,ta kuma yi fari sosai fiye da farinta nada,amma kuma sanda ta miqe zata dauko mata yusra dake bacci bataga tudun komai a tare da ita ba,wannan shi ya saka mata shakka a ranta,ta debi yaran suka baro sashen tana lalubar number ummanta.

Bayani tayi mata na canjin data gani din daga wajenta,sannan ta dora mata da

“ta danyi watanni umma da wannan canjin,idan ciki ne ya kamata zuwa yanzu ya fito,amma banga alamar komai tare da ita ba” shuru ta danyi tana nazari,ta sauke ajiyar zuciya sannan tace

“Ba’a nan take ba hafsatu wai an dannewa bodari kai,zanyi magana dashi,kome meye yake akwai su basa rasa ganinsa”.

Yana zaune daga bakin gadonsa,hannunsa dauke da tab,yana bibiyar statement na wasu masu laifi dake tsare a hannunsu,hafsat na daga gefe tana lallaba yusra tayi bacci fuskarta aa hade ranta a bace,tunda abbas din ya gaya mata kafin ta iso gadon tayi wanka take kumbure kumbure harta gama ta maida kayan jikinta ta dawo gadon,yayi haka na bawai don yana da bauqatarta ba,kawai ya fuskanci idan ba wanna titsiyen ya fara yi mata ba haka zata ci gaba da tafiya,sau daya ya kalleta bai sake dubanta ba,baisan me yasa har abada take sha’awa shigo masa bedroom da kayan data wuni dasu cikin gida ba,baisan sau nawa zai kwatanta mata bayason hakan ba,a yanzun da yake ganin sauyi daga wajen widad,sai abun ya daina bata ransa,tunda at least yana samun sassauci idan ita din taqiyi masa yadda yakeso,sai mamaki kawai da take bashi,sau tari tafi ganewa ta kwana da tufafinta,atamfa ko shaddar da tasha kwaramniyar yini guda da ita.

Dakin shuru kamar ba kowa har ya gama aikinsa,koda ba aikin yake ba haka zaman yake dama,ita bata iya hira da miji ba,shi kuma dama tun asali miskili ne,yayin da take kallon miskilancinsa a matsayin zallar wulaqanci ne kawai (bata iya tsaiwa ta karanci ya yake).

Tab din ya ajjiye a bedside drawer yana jan duvet dinsa zuwa qugunsa yana kallonta

“Kiyi qoqari gobe da sassafe ki rubuta duk abinda kuke da buqata na kamar wata biyu haka,idan Allah ya kaimu ranar alhamis zamu wuce hajji ni da widad”.

Kamar wadda wuta taja ta kalleshi da sauri

“Kai da wa?” Ta sake tambayarsa ba tare data bi takan sauran bayanansa na baya ba,sunan daya fada sai taji kunnenta kamar baiji mata dai dai ba

“Widad” ya sake fada yana kallonta hankalinsa kwance idonsa yana dan lumshewa saboda baccin daya fara ji.

Cikin zafin nama ta miqe ta zauna sosai, kaman zata bige yarinyar saboda yadda ta tashin da sauri

“Kasan me kake cewa abbas?,da widad zaka tafi hajji?” Dubanta yayi

“Me na fada da yake alamta ba cikin hayyacina nake ba?” Yadda yayi maganar cikin bagararwa kamar ba wani mummunan abu ya aikata mata ba,ta tsareshi da ido,wani yayyafin zafi yana sauka daga zuciyarta yana ratsa kowanne sashe na jikinta,tafasa sosai zuciyarta ta dinga yi,ta rasa wacce kalma ce ta dace dashi,saita kuka kawai.ya balle mata,ta miqe tana sauka daga kan gadon cikin hargagi masifa da daga murya ta fara sake masa maganganu marasa dadi,ya rufe ido yana jinta har zuwa sanda tace

“Kuma duk munafukan da suke sake shirya wannan abun Allah ya tsine musu albarka idan basu fasa ba,ni dasu shege ka fasa”

Wata gigiyacciyar tsawa ya daka mata,yana dubanta da idanunsa da suka fito waje

“Shirmenki ya isheni haka,fita ki bani waje shashasha mara hankali,a gabana zaki tsaya kina furta tsinuwa munafukai da sauran shirmenki!,zaki fita ko sai na baki mamaki?” Hannu tasa tana son dauke yusra daga kan gadon,tsananin bacin rai yasa ya janye yarinyar gefe,saita koma ta tsaya tana cewa

“Mamaki kuma na nawa?,aika gama bani mamaki,wallahi tallahi inda nasan haka kake da bazan taba aurenka ba,amma kaje na barka da Allah” ta juya da gudu tana kuka da qaqqarfan sauti ta fice a dakin.

Hannunsa gaba daya qaiqayi yake,tabbas inda wani ne a waje yayi masa hakan yau sai ya gane shayi ruwa ne,bayason shaidan ya dinga tunzarashi ta sanadinta ya zama madoki,sai ya dinga ambatar Hasbunallahu wani’imal wakil.

*********Karfe goma na safiya ta gama shiryawa,tun jiya cikin zumudi ta kwana,tayi zaune a parlor tana jiransa.

Da sallama ya shigo falon,muryarsa tayi laushi sosai saboda baccin da bai samu ba isashe daren jiya,ya zama wani so cool yayi kyau cikin shigar qananun kayan da ba kasafai ya fiya sanyasu ba,yau din yayi amfani da sun glasses wanda zai hanaka gane ainihin qwayar idanunsa,sai ya qara masa wani mugu mugun kyau,har widad ta kasa dauke dubanta daga kansa.

Duk da yadda ya sakaye qwayar idanunsa amma hakan bai hanata ganin canzawar mood dinsa ba

“Oga zumudi….. let’s go,banaso rana tayi mana sosai,inason na dawo gida na huta”ya fada yana duba agogon hannunsa.

Tare suka jero zuwa harabar gidan yana riqe ds hand bag dinta tana gyara rolling na mayafinta tana masa shagwabar don Allah idan anzo yin allurar ya tsaya a wajen.

Murmushi ya sake,ko yaushe tabararta na nasarar korar bacin rai ko damuwarsa,wannan ya sanya koda daga office wani abu ya bata ransa,tattara komai yake ya dawo gida,yana da yaqinin zai samu magani sa sassauci,koda batasan me yake damunsa din ba,koda batayi komai da nufin korar bacin ransa ba.

Da kansa ya bude mata seat din motar ta shiga,ya tsugunna ya tattare mata rigarta data fito sannan ya miqa mata hand bag dinta.

Hadawa tayi da hannunsa ta riqe tana kallon qwayar idanunsa

“Me?” Ya tambayeta ganin yadda ta bata fuska

“Smile mana uncle,kayi kyau yau,amma kaqi kayimin dariya…..haba mana uncle” ya qarasa fada a shagwabe.

Don dole bai shirya ba siririn murmushi ya kubce masa,ya duqa a tausashe yayi kissing goshinta sannan ya zagaya ya tayar da motar.

Suman zaune hafsat dake kallonsu ta dakin solar dinsu dake daura da wajen tayi,taji jiri kamar yana dibanta,har sai data samu waje ta zauna ta wucin gadi,kafin kuma kuma ya qwace mata,ta jima zaune a wajen tana kukan,har sai dataji shigowar sale sannan ta miqe tana barin wajen don kada ya sameta a haka raini ya shiga tsakani,saidai tana jin zuciyarta ta tsike gaba daya,zuwa yanzun komai ta fanjama fanjam,don haka wayarta kawai ta dauka ta fara neman number ummanta ba tare data damu da kukan da yusra ke tsalawa ba, wadda ta tashi daga bacci tun dazun taji ba’a Kula da ita ba.

Idanunta fal tsoro,ta waiwaya tana dubansa sanda zata shiga dakin da ake bada rigakafin tana kallonsa

“Please uncle,don Allah ka rakani”

“Muje” ya fada yana maida wayarsa aljihun wandonsa suka shiga dakin a tare.

Yadda taga suna gaisawa da likitar ya tabbatar mata akwai sabo tsakaninsu,tadan kalleshi,abbas din badai miskilanci ba,ya sansu amma ya maze mata,suka hada ido ta masa sing na zan rama,ya dage mata girarsa daya kawai.

Fitsarinta suka fara buqata,tayi ta kawo mata aka bada gwaji.

Gyara zaman glass din fuskarta likitar tayi sannan ta dago kai tana duban abbas din

“Sir,bakasan madam nada juna biyu bane?” Sosai ya kalli likitan,sai ya zare gilashin idanunsa

“Juna biyu?,Kina nufin,she’s pregnant?”

“Yes sir…..alamu ma sun nuna kamar yafi wata biyu”

“Ya salam ya Allah”ya fada zuciyarsa na wani irin bugawa da matsanancin farinciki,kamar wanda aka yiwa albishir da samun haihuwa karon farko bayan wasu shekaru daya diba yana neman haihuwar ba tare daya samu ba,ya bude idanun nasa fuskarsa na fidda wani irin murmushi yana sauke dubansa ga widad.

*H A F S A T*

Kamar zata zauce sanda taketa kiran ummanta ba tare data daga ba,muryar umman kawai takeson ji ta isar mata da saqon abubuwan da takeso a gabatar mata akan widad din,tana jin idan bata d’ai d’aita rayuwar yarinyar,ta gigita mata rayuwa ba tabbas mata ta rako duniya,indai bata dauki mataki mafi muni a kanta ba bata cika hafsatu ba,yarinyar tayi mata abubuwa masu.muni dake da yawan gaske,ba zata yaba qyaleta ba itama,ta rabata da abu mafi soyuwa a wajenta,halittar da duk duniya ba wadda take qauna sama da ita ABBAS dinta.

Sai data yi mata kira biyar a jere,ana shidan ta dauka,kafin hafsat din tace komai ta rigata

“Yauwa,nima ke naketa nema ai,ina hanyar dawowa daga gun aiki ne……,akwai gagarumar matsala hafsatu,akwai matsala” kalmomin umman nata da kuma tashin hankalin dake cikin nata kwanyar suka hadu suka kusa fasa mata kwanya,saita sulale ta zauna sosai a wajen tana jiran jin gagarumar matsalar dake tunkarosu din.

*A L H A M D U L I L L A H*

*_Masu karatu….. bakuji komai ba,baku karanta komai ba,kawai abinda zance daku shine……kuyi jumirin bibiyata,muje zuwa bayan hutun azumi,in sha Allah ina tafe da kashi na biyu na labarin A RUBUCE TAKE k’addarata,nima ba haka naso ba,amma yanayin yadda labarin ya dauko tunda farko,bazai taba qayatarwa ya bada ma’ana ba sai an cimma gacinsa,zanyi qoqari da ikon Alalh bayan sallar pages din sunfi wadan nan da muka gama tsaho in sha Alllah,fata na Allah ya bamu aron rai da lpy_*

ina muku fatan ALKHAIRI AREWABOOKS FOLLOWERS dina,wadanda baku gajiya da bibiyata, alkhairin Allah ya kaimuku a duk inda kuke,ayi ibada da bukukuwan sallah lafiya,na barku lafiya

Leave a Reply

Back to top button