Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa Novels

Arubuce Ta Ke 56

Sponsored Links

Page 56

Sanda yayi kiran farko har ta katse bata daga ba,bai qosa ba ya sake kira,dab da zata katse aka daga.

Sallama ya fara yi mata,cikin muryar bacci ta amsa

“Badai bacci ba?” Ya tambayeta da muryarsa da ta sake sanyi sosai

“Uhmmm….bacci mana,isan banyi bacci ba me zanyi,ka wuni hidimar gida data yara,kiranka ne ma ya tasheni,da banjin zan tashi har zuwa nan da asuba” idanunsa ya ragewa kaifi kadan,sarkin qorafi da mita,ya kauda wannan a kasalance yace

“Sannu da qoqari”

“Yauwa” ta fada a gajarce

“Ina yaran duka sunyi bacci?”

“Eh” ta sake amsa masa a tsaye

“Good……Allah yayi musu albarka”

“Ameen” ta kuma amsawa a gajarce,shuru na sakanni ya ratsa,ya zaci daga sound dinsa zata karanci wani abu,amma baiga alamun hakan ba,don haka yace da ita

“I missed you, that’s why I call you,ko zan samu wani abu special haka who will cheer me up da daren nan” baki ta tabe daga can,zuciyarta na mata zafi,ya ma raina mata wayo ne kawai,me zata masa tunda ya zabi ta zauna a nan?,ai sai kowa ya zauna da lalurarsa

“Kai da kake da amarya?,me zaka nema a wajena?” Duk da baiso ba qaramin murmushi sai daya qwace masa,there is jealousy in her words,bai kuma shirya gamsar da ita ba,don haka yace

“Sister din taki yarinya ce qarama,she can’t take all my needs,so dole ki tallafa mata kamar yadda kikacemin zakiyi” idanunta ta runtse tana jin wani ciwo,kamar da gayya abbas din yake gaya mata hakan,yanason ce mata yana samun kulawa daga wajen yarinyar kenan?

“It is better to go back to her” ta fada cikin haqiqancewa

“She’s sick” shima ya amsa mata a gajarce,ba dacewa bane ya bata qofan da zata karanci me yake gudana tsakaninsu,wannan wani abu ne daya shafesu su biyu.

Bata shiryawa tashi ta zauna ba amma sai gata a zaune,qirjinta ya buga sosai,me ya sameta?,kodai ya aikata?,indai da gaske bata da lafiya to tabbatar suna tare a yanzu haka,tafi kowa saninsa,yana da tsananin tausayi da kulawa akan iyali,idan baki da lafiya kulawarsa ta musamman ce

“Tana ina?”
“No need ki sani….. just relax me madam” a yadda hankalinta ya daga bata jin zata iya masa komai

“I feel sleepy….so i can’t do anything” Maimaita words din data fada din yayi a kunnuwanta sannan yace

“Alright…. good night” sai ya kashe wayar ya ajjiye ta a gefe yana shafa kansa zuwa fuskarsa hadi da furzar da iska,tunani kala daban daban cikin ransa da zuciyarsa,yana ganin kiranta amma sam bashi da interest na dagawa,saboda yana da yaqinij ba ta kirashi don tayi masa abinda yake da buqata bane,wala’alla ma ta kira ne ta bishi da qorafi ko kuma mita.

Kamar yadda ya zata kuwa saiga gajeran tex bayan ta fahimci bazai daga kiran ba

_Na gode da wulaqantani da kayi,ka daga wayar ka bani ita zamuyi magana,i called her,but bata daga wayan itama_

Tsaki yaja ya ajjiye wayar,mamakin halayen hafsat har yau basa barinsa,she call her to tell her what?,a wannan daren?,she refused to do what he wanted amma kuma tana son magana da weedad for what?,baisan sanda zatayi hankali ba da gaske,duk sanda tayi masa irin wannan sake fita takeyi daga ransa,daga qarshe qur’ani ya rungume sannan ya samu bacci ya daukeshi.

*_W A S H E G A R I_*

Ta jima da gama shiryawa cikin uniform dinta,amma ta kasa fitowa,tayi zaune gefan gadonta tana duban fuskarta time to time ta madubi,batasan yadda zata fuskanceshi ba,haushinsa takeji a zahiri,a badini kuma idan ta tuna abinda ya farun jiya sai taji kamar ta nutse a qasa,da qyar ta samu hawayen ta ya tsaya.

Tana jin an taba qofar za’a bude ta runtse idanu,idonsa a kanta,qaramar dariya tana cinsa,yasan wannan rufe idanun duka nasa ne

“Kin fasa zuwa school dinne?” Kai ta girgiza da sauri alamun a’ah,sai ta tashi tana juya masa baya,ta rataya jakarta tayo bakin qofa,a lokacin tuni yabar wajen.

Tayi tsammani Samuel ne zai kaita kamar jiya,sai data shiga motar sannan taga shine ashe,ya tada motar suka fara tafiya,babu wanda ke cewa da dan uwansa komai,har suka isa makarantar,ya cira kudi ya bata

“Ga kudin break,idan an tashi ki jira,idan ban samu zuwa ba samuel zaizo” bata iya hada idanu dashi ba tasa hannu biyu ta karba

“Na gode” ta fadi qasa qasa sannan ta juya da hanzari tana yin hanyar class,yana zaune cikin motar yana kallonta har ta shige sannan ya tada motar yana kada kai da qaramin murmushi kan fuskarsa yayi reverse yabar makarantar.

Wunin ranar sukuku tayishi,don ma ‘yan ajin nasu suna da saurin sabo da jan mutum a jiki,nan da nan tadan fara sabawa dasu bayan tasan sunayen wasunsu,da azahar aka tashi,bata tsammaci ganinsa ba still sai gashi,yana sanye da uniform dinsa din nan dake qara masa wani mugun kwarjini haiba da kamala,da suka isa gida ta dauka zaya koma aiki ne,sai taga ya canza kaya ya kirata suka shiga kitchen.

Koda suka gama kowa ya diba nasa,dakinta ta wuce dashi taci a can,bata sake jin motsinsa ba kamar yadda ta wuni a kwance,sai da yamma ya leqo yace tasha magungunta ta shaida masa tasha,hakanan tun bayan magariba daya leqo ya tabbatar tasha maganin dare bata sake jinsa ba.

Wanka tayi tayi shirin bacci kamar yadda ta saba,saidai bacci yaqi zuwan mata,data gaji ta dauki wayarta ta duba,taga tana da kati a ciki sosai,kusan katin tun sanda aka siya wayar yake cikin layin,batasan na nawa ya loda mata haka ba,though dai bata fiya kiran waya ba,mostly saidai ayi kiranta.

Mutanen gida ta dinga kira,ummunta ta fara kira,sai abbanta,anty madina hajjaa sai anty deena,wadda sunfi jimawa da anty deena din,tana ta mata hannunka mai sanda da jirwaye mai kama da wanka akan kula da miji,saidai hankalinta baima wani kawo mata ba,tadai jita ne,sai kusan tara na dare sannan sukayi sallama.

Sam bacci ya qauracewa idanunta,ta dinga juyi ita daya tana tuna daren jiya,rabon da tayi cikakken baccin mai dadi irin na jiya har ta manta,saboda ita din mutum ce da tayi sabo da kwana a jikin ummu,shi yasa a kullum idan zatayi bacci da qyar yake zuwa mata tun bayan tafiyar latifa.

Karar wayarta ta katse mata tunaninta,har tadan tsorata ma saboda ta manta da ita,sunan mommy hafsat data gani ya sanyata tashi ta zauna ba shiri,gabanta yayi mugun faduwa,hakanan takejin mummunan faduwar gaba a duk sanda taga wani abu daya danganceta,kamar sunanta muryarta da sauransu.

Muryarta na dan rawa ta daga wayar tana sallama tare da yunqurin gaisheta

“Kina ina?” Ta tambayeta kanta tsaye ba tare da tabi takan gaisuwar da take mata ba

“Ina daki”

“Wanne dakin?” Ta tambayeta daga can gabanta yana faduwa

“Dakina”

“Abbansu mimi yace baki da lafiya jiya,me ya sameki?” Gabanta ya yanke ya fadi data tuna cewa a dakinsa ta kwana jiya,kuma koda ra farka cikin jikinsa ta ganta,ta fahimci hakanne?,kota gane?

“Ciwon mara” ta amsa mata muryarta nadan rawa kadan,abinda ya sake sanya shakku a zuciyar hafsat din,tsoronta ya ninku

“Kodai wani abun kukayi ke dashi?” Tambayar daketa mata yawo tsakar ka ta subuce ta fito daga bakinta,da sauri ta hau girgiza kai kamar tana a gabanta ne,hawaye kuma suka jiqa mata fuska

“A’ah mommy….wallahi ba komai,ciwon mara ne kawai Allah ki yarda gaskiya na fada miki” boyayyar ajiyar zuciya ta saki,sanin weedad din bata qarya sai hankalinta yadan kwanta,amma saita fuske saboda ta samu nasarar sake dasa tsoron hakan a zuciyarta

“Ohon miki idan ma wani abun kika yarda yayi miki,mutuwa zakiyi…..ina ruwan wani,nima ina gaya miki ne don ina sonki banaso ki mutu”

“Allah mommy ba komai” sai kawai hafsan ta kashe wayar donta qara tsoratata.

Sosai hankalin weedad din ya tashi,tana shirin bin kiran taji ya turo qofar,ta daga kai tana kallonsa,har qasan ranta tana jin haushinsa,ya danji wani iri ganin tana kuka,yana fargabar ko wani abunne ya sameta,yasan yau bai leqota da kyau ba,duka yau ya kulle kansa ne a daki yana aikin tracing din wani criminal a sirrance,abinda yasa ya baro office kenan,bayaso kowa yasan abinda yakeyi

“Yaaya?…..jikinne?” Kai ta girgiza tana turo baki,ta kuma tura masa qeya taqi kallonsa

“To ma sha Allah”ya fada duk da ya fuskanci kamar cikin fushi take,shuru ya ratsa tsakani na sakanni kafin ya miqe

“Ki ajjiye komai ki kwanta” sai ya juya yana shirin barin dakin,binsa tayi da kallo,tana jin kamar ta bishi,amma da ta bishi ya tabata gwara ta zauna a dakinta.

A jikinsa yaji kamar tana kallonsa,don haka ya dakata ya waiwayo,suka hada ido saita dauke kai,kamar xaiyi magana sai kuma ya fasa,ya saka kai ya fita.

Tun bai kai tsakiyar falon ba yaji ihunta,ya juyo da sauri,sai gata sunyi kacibus a hanya har tana fadawa jikinsa,taja baya da sauri jikinta yana rawa

“Mm….mage”

“A ina?”

“Bakin window” ta fada tana duban qofar dakin

“Muje na gani” ya fadi yana sakata a gaba,kafada ta maqale tana sakin kuka,kome zaiyi mata bata jin zata yarda ta bishi,haka tayi tsaye a wajen ya shiga dakin,bai jimaba ya fito

“Bata shigo ba,infact ta wuce ma,zaki iya komawa” waiwaya tayi inda yake,taga da gaske tafiya yake zuwa dakinsa,ta daga qafarta da sauri tabi bayansa.

Batasan ta cimmasa ba sai da suka tsaya suna kallon kallo shi da ita,yana riqe da handle din qofar yana dubanta,itama shi take kallo saidai batace komai ba sai aukin hawayen da take faman zubarwa

“Don Allah…zan karka tafi ka barni”

“Bacci nakeji” ya amsa mata a taqaice,saita sake fashe masa da kuka,hannu ya sanya ya dafe goshinsa

“Oh my goodness” ya furta a hankali,saiya maida manyan idanunsa kanta

“Me kike so?” Shuru tayi kamar ba zata amsa ba,sai kuma tayi qasa da kanta

“Zan kwana a nan” ta fada a hankali gabanta yana faduwa,zuciyarta na gaya mata girman laifinta,ta yaya zata hada dakin kwana dashi?.

Qaramin murmushi ya saki
“Silly girl” ya fada qasa qasa,ga dan banzan tsoro ga shagwaba da sakarci harda na siyarwa,sai ya matsa gefe daya

“Bismillah” ya furta a hankali,ta rabeshi sosai ta shige dakin,ya rufe qofar ya sanya key sannan yabi bayanta.

Ta jima a zaune har ya gama komai na shirin kwanciya bacci tana binsa da idanu,pillow ya dauka ya jefar a qasa sannan yabi pillow din ya kwanta idanuwansa a rufe yana karanto addu’an bacci,ya gama ya shafe jikinsa,ba tare daya bude idanun ko ya dubeta ba yace

“Ki kwanta kiyi kuma addu’a” a takure take sosai saman gadon,duk kuwa da cewa ita daya ce,duk juyin da zatayi idanunta a kansa,har sai data ji saukar numfashinsa a hankali alamun bacci yayi awon gaba dashi,sannu a hankali itama jikinta ya saki,wani bacci me dadi wanda babu fargaba a ciki ya sureta.

KI KULANI miss xoxo

DAUDAR GORA Billynabdul

RUMBUN K’AYA hafsat rano

IDON NERA Mamuhghee

A RUBUCE TAKE huguma

_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

0022419171
Maryam sani
Access bank

Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070

*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261

*Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63

*Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥*H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)

*Arewabooks:huguma*

Leave a Reply

Back to top button