Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa Novels

Arubuce Ta Ke 99

Sponsored Links

Page 99

“Hajiya ina wuni”

“Lafiya alhmdlh,ya nauyin jiki?”

“Lafiya lau” ta fada a gaggauce,sannan ta zauna ta fara rattabo mata abinda ya faru.

Fiye da rabin maganar ta canzata, hajiyan tayi shuru tana saurarenta har ta gama fada sannan ta rushe da kuka

“Ya isa,kiyi shuru haka ki daina kukan ko don abinda yake jikinki,zan laluba gaskiyar maganar,indai na sameshi da laifi saina bata masa,ki kwanta kiyi bacci zan nemeki in sha Allah” a haka suka rabu da hajiyan,can qasan ranta tana jin haushi haushi,wai zata bincika taji,itama ta fara canza hali kenan.

Ajiyar zuciya hajiyan ta saki

“La haula wala quwwata illa billa” ta fada a fili,qaddarar abbas kenan shi kuma,kalar tasa jarrabawar rayuwar kenan,yunqurawa tayi ta miqe tana fatan ta sameshi a falo,duk da sha daya na dare ma ta gota,amma yace zai mata magana idan zai wuce.

Murmushi ya bita dashi sanda ta koma ta kwanta tana boye fuskarta,sai yaja mata bargon sosai,ya sunkuya yayi kissing dinta lightly,sannan ya motsa bakinsa zuw kunnenta cikin rada yace

“Kiyi bacci mai dadi babyn uncle” a dole murmushi ya subuce mata,hakan yayi masa dadi,sai ya rage mata hasken dakin sosai,ya sake lullubeta ya fice yaja mata qofar.

Dai dai lokacin hajiya ta fito a dakinta,sai sukayi kacibus,kunya ta dan kamashi,sai hajiyan ta kauda kanta

“Yanzu nake shirin shigowa muyi sallama” ya fada yana shafa kansa

“Gwara da baka wuce din ba ai,zo ka zauna muyi magana” tuni jikinsa ya bashi tayi halin,ya dawo gaban hajiyan ya zauna

“Matso” tace dashi,sai ya dawo saitin qafarta

“Wanne abu ne ya shiga kanka da zaka saka hannu ka mammari matarka da tsohon ciki?” Kansa ya saddar qasa na wasu sakanni,sannan ya dago

“Hajiya na fara gajiya da hafsat,na gaji da halayenta,inajin taqi kadan ya rage mu rabu”

“Aah,kada ka sake fadin haka,yanzun me ya hadaku?” Bai boye mata komai ba ya gaya mata,tayi shuru abun na tsumata,ko yaushe abun na hafsat gaba yake ba baya ba?

“Iya qoqarina hajiya inayi,ina dannewa,ban taba kai qararta ba,amma kome nayi ita bata gani,da qyar wani lokacin nake iya tanqwara zuciyata akanta,tana kaini bango,bani da guarantee din abinda zai iya faruwa gaba”

“Haquri zaka ci gaba dayi,ko don albarkacin zuri’a data ratsa tsakaninku”

Duk da ita kanta hajiyan abubuwan sunata kwance mata,to amma ita din uwa ce,duk yadda uwa take da juriya aka santa,ba yadda zataso abbas din yayi wani abu na rashin dadi ko kyautatawa,har abada da naka yayi cuta gwara shi a cuceshi,baki ta dinga baki da nasiha cikin hikima ta dattawan mutane masu hankali da sanin ya kamata,taga bacin rai da damuwa masu yawa a idanunsa

“Ku shirya gobe ku koma inda kuka fito kawai abbas,banason wannan tashin hankalin,mun yafe bikin” statement din hajiya na qarshe kenan,don shine kawai mafita.

Kamar dama ta shiga xuciyarsa,don darajarta ce kawai take sanyashi yawancin lokutta yake zama a garin har yayi kwanaki idan yazo.

Sha biyu da minti goma ya isa gida,tana falo zaune don ta kasa runtsawa,ta kuma ji shigowarsa,sai taci gaba da zama tana tsammatar shigowarsa ganinsu mimi,amma har aka qara mintuna talatin shuru babu shi babu bayaninsa.

Shikam sashensa ya shige,ya fidda kayan jikinsa yayi wanka,sannan ya shirya kayansa waje daya kafin nan ya kwanta.

Har qarfe daya na dare tana zaune shuru,ranta yana sake baci,zuciya na mata saqa iri daban daban,yana nufin har kwanan nata ma ya saraya kenan?,idan bai shigo yanzu ba ta tabbata da safe zai shigo,zata ga da wanne ido zai kalleta.

Daga sallar asuba ya zarce da wanka,kafin qarfe shida ya gama shirinsa tsaf,ya fidda luggage dinsa ya saka a mota.

Sale ya barwa envelope yace ya bawa matar gidan,kudaden hidimar gida ne a ciki,ya zare dukkan wasu kudade daya saba bar mata wanda suke kyautatawa ce kawai bawai na haqqin dake wuyansa na shari’a ba.

*********Da farko ta watsar dashi kamar yadda ya watsar da ita,don ba qaramin shaqar takaici tayi ba sanda ta karba saqon ta hannun sale,ya rasa wa zai bawa aiken kudin amfanin gidanta sai salen?,bata sake shiga rudu ba sai dataga kowanne kudi ya fadi na meye,babu ko qarin sile akan abinda ya saba bata,gashi buqatar kudin take da gaske saboda fara adashin asara data yi,ko cikin satin ummanta tace lallai lallai ta tanadi kudi,saboda ba zasu taba bari sakaci ya shigo cikin aikin da aka fara ba,wannan ya sanya ta sake qullatar widad din qwarai,a duniya idan aka bata bindiga akace ta kashe mutum daya widad din zata fara harbewa.

Yadda ya dauke mata wuta abin ya fara damunta,gashi tana fuskantar EDD dinta yana sake matsowa,wata zuciyar tana ta kirashi wata tana ta shareshi,a haka kwanakin suka fara tafiya, dole daga bisani ta karya billent ta kirashi,ta kuma maida komai ba komai ba,don lallai tana buqatar kudi.

*B a y a n wa t a u k u*

Bayan watanni uku hafsat din ta sauka,ta sake samun baby girl,zagayowar kwanaki hudu abbas ya dauki excuse don zuwa ganin baby,dole widad ta soma shirin binsa itama,don rabonta da bauchi tun wancan lokacin da suka samu sabani da hafsat,duk sanda zaije weekend tabar binsa,saidai yaje yayi kwanaki biyu ya dawo Kaduna,hakan yafi mata kwanciyar hankali,har ya zamana koda wasa batason taji ya ambaci xuwa bauchi da ita,yanzu zataji hankalinta ya tashi.

Ta shirya tsaf tayi sabbin dinkunanta,gyaran gashi zuwa lalle suka wuce bauchi,ranar ta shiga sassan hafsat din,wanda rabonta dashi har ta manta.

Ba wani mutane bane sosai, kasancewar ita din dama bata mutane bace,mai zuwa mata sha’ani sai wanda ya dubi Allah,anty ummee ce sai wasu baqi mata biyu sai ‘yar yayarta data dauko saboda aikace aikacen gidan,sai hajiya habiba.

Ciki ciki hafsat din ta amsa mata barkan data mata,itama sai bata saka kanta can ba,ta zauna daga hannun kujera,anty ummee ta miqa mata baby da aka gama yiwa wanka tana qarewa widad din kallo tsafff tana kaduwa da yadda taga ta sauya,ta karbeta tana jin sha’awar yarinyar har cikin zuciyarta,kasancewarta mai son yara sosai.

“Uhmmm…..ko a bar miki ita ne?,naga kin kasa daina kallonta” hajiya habiba ta fada tana wani munafukin murmushi tana kallon widad,sai ta saki murmushi kafin tace komai hafsat ta rigata,taja wani mugun tsaki tana gyara zamanta

“Ki daina irin wannan wasan hajiya habiba……haihuwa wasa ce da zaka dauki yaro danka ka baiwa yaro,wanda ko ciwon kansa bai sani ba?,tab….. garinsu da nisa ai,idan fitsari banza ne kaza tayi mana” tsaf ya fahimci abinda hafsat din take nufi,don haka ta miqe tsam ta miqawa anty ummee babyn tana cewa

“Allah ya rayata” ta fice a nutse a falon ta wuce sassanta,don saukarsu kenan ta fara shigowa nan din.

Tare hajiya habiba da anty ummee suka dauke kai daga kallon widad bayan ta bace musu,suka maida kan hafsat data fara qananun motoci tana sakin tsaki kamar ta tsinke harshenta

“Banso kika sanya baki ba,kallon me juna biyu nakewa yarinyar,naso na bugar mana cikinta muji akwai ko babu” hajiya habiba ta fada tana duban hafsat

“Ai banza ce,nima kallon da nakeyi yarinyar kenan tunda ta shigo,kamar me yaron ciki,canzawar tayi yawa,ni tsorata ma nayi dana ganta wallahi,ta zama wata babbar mace?” Anty ummee ta fadi tana kama bakinta.

“Allah ya kiyaye Allah ya sawwaqe,ni kuwa ina me zan zauna na barta tayi ciki?,haba don Allah,bazai yiwu ba” hafsat ta fada tana girgiza kai,cikin zuciyarta tana jin wani irin zafi kamar ma ance cikinne,tana qiyasta yadda zata cakuda ‘ya’yanta da ‘ya’yan wata matar?,ba zaiyuwu ba,ba zata iya ba,barin widad din ta samu ciki harta haihu shine babban kuskuren da zata tafka

“Idan ba mataki kika dauka ba sanda zai narka mata cikin sani kikayi?,kina nan kina bacci saidai ki tashi ki ganshi” hajiya habiba ta fada tana miqewa tsaye gami da daukar jakarta

“Bafa wannan maganar hajiya,matakin nasa aka dauka,shi yasa nake cika miki baki”

“To yanzu naji magana…..hmmm aikin hadu da alaqaqai ciwon zamani mai wuyar magani”

“Ko tunata banason yi wallahi hajiya,ban taba kawowa yarinyar nan zata shiga rayuwata tayimin karen tsaye har haka ba” hafsat din ta fada yana sauke idanunta a sassan widad din tana jin ranta yana mata ciwo.

Duk da jego take amma hakan bai sanyata ta barwa widad din kwananta ba,haka take diban jiki tabar masu tayata zama ta wuce sassansa ta kwana,ko daya widad din bata bari taga damuwarta ba,saita shiga sabgar gabanta kawai.

Da kansa yace me take buqata na taron suna,tace zata kirasa idan ya fita,saita dauki waya sukayi magana da anty madina

“Kiyi komai naki ta yadda ba ruwanki da abincin taronta,wanda ya shigo miki ki bashi,wanda ma baizo na ya hutasheki” da suka gama wayan saita kira hajjaa ita kuma ta gaya mata yadda suke komai na taron suna,ta yiwa abbas din waya ta gaya masa,ya ajjiye mata komai,da taimakon hajja takai aikin abincinta,masa da sinasir sai soyayyiyar shinkafa (fried rice).

Ana gobe suna ta yiwa uncle muhsin waya ya bar nujood tazo suka kwana tare,washegari aka tashi da suna.

Kwalliya ta dinga yi sosai,tana canza shiga cikin kayan da abbas din ya dinka musu,duk da na hafsat din ya dara nata,da kadan da kadan saiga mutane sun cika sashen nata, don duk wanda ya shigo din ga abinci nan zaici ya qoshi,sashen mai jego kuwa babu bayani,don kudinta ta adana,ta sada mutane da wata irin jallop din shinkafa data hadu da taqadiriyar dahuwa mara tsaro,dukka lemon roban da yasa aka jibge ta debesu,ta musanya da zobo dan dauri.

Daga qarshe dai sassan widad sai ya zamana kaman a nan akayi haihuwar,duk wanda ya shigo din kuwa saiya qoshi da abinci me kyau,hafsat na daga sassanta amma labarin abinda ke faruwa a sassan widad din tuni yaje mata,ta cika tayi fam,musamman matan abokan abbas din da suka yada zango a can bayan sun mata barka,don ba wadda ta zauna a cikinsu,saboda ba wani kyakkyawan mu’amala bace tsakaninsu,tsananin kirkin abbas din ne ma ya sanya suka kasa qin zuwa,dama kuma idan ka gansu a gidan to saifa irin hakan ta kama.

Kasa zaune bare tsaye hafsat din tayi,da yammar ta canza kaya na biyu shima bisa takurawar anty ummee

“Kiyita zama,suttura iya sutura an miki amma kin jibgesu,ga kishiyarki can kowa fadin shigar ta yakeyi,keda ake taron don ke amma kamar saboda ita akeyi” sannan ne ta sake saka wata atamfar.

Sanda ta fito falon tayi baqi ta hangi fitowar widad din ta window din falon nata da aka dauke curtains dinsa,ta yima matan abokan nasa rakiya,tana sanye da shadda ‘yar mali,baqa ce da aka yiwa adon mustard yellow,zo kaga baqar shadda jikin farar mace,an tsara mata wani mugun dinkin bubu,ido kawai ta runtse hafsat din tana dauke kanta daga wajen tana jin Zuciyarta kamar zata fashe.

Kwana biyu da suna suka koma inda suka fito,tabar hafsat din da tarin ciwo a zuciyar ta,da kuma K’ULLACI hadi da ALWASHI iri daban daban akan widad din.

Duka duka sati uku da komawarsu bauchi tafiyarsu ta taso,zasu tashi ta kano,don haka suka shirya zuwa bauchin yayi sallama da hajiyansa,ya kuma sallami gida sannan su wuce kanon.

Kamar ko yaushe,cikin tsoro da wani mugun bacin rai da qunci ta sauka a sassan nata,yau din tana jin tsanar gidan sosai fiye da ko yaushe,cikin qafafunta takejin kamar ba lallausan carfet take takawa ba,kamar qayoyi ne zube a sassan nata gaba daya,haka ta dinga qoqarin dannewa ta fara gyaran sassan nata tayi ta kammala ta samu waje ta kwanta,wata muguwar kasala da nauyin jiki suna mamayeta,wanda a kwanakin nan sai sake gaba abun yake,har abbas din yace muddin sukaje hajjin suka dawo babu wani sauyi to ko bataso dole taje taga likita.

Kamar wancan karon,wannan karon ma har bacci yadan fara fusgarta taji kamar an soma shaqeta,ta farka da sauri tana ambaton sunan Allah,sai numfashin ta ya ware ya koma dai dai,ta miqe a hankali tana sauke ajiyar zuciya,tana jin kamar ta fice a gidan kota yaya,sai ta zura slipper dinta kawai ta bude qofarta ta fito.
[3/22, 9:37 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)
*Arewabooks: Huguma*

Leave a Reply

Back to top button