Gidan Aunty Book 1Hausa NovelsHausa Novels

Gidan Aunty Book 1 Page 1

Sponsored Links

UK WRITERS (Unique kingdom writers)📚
Sabuwar marubuta masu tafiya da saban salo me kayatarwa.

Littafina kirkirarran labarine banyi dan cin zarafin wani no ko wata ba, duk Wanda labarina ya zo daya da nashi yayi hakuri rashin sani ne.

Yadda na fara littafinnnan a Sa’a Allah ya bani ikon kammalashi..

Bismillahir rahmanirrahim…..

Paid book

Book 1📕

Free page

1

TAHEE!!! TAHEE!!! “Naam oumma “ cewar wata yarinya wacce kallo daya zaka mata kasan bazata wuce 16 to 17 years ba, ta fito daga cikin wata kofa da kallo daya zaka mata kasan daga kitchen take, sabida flour da ya Dan bata mata jiki.” Har hanxu baki gama kwabin ba , kinsan abbanku ya kusan dawowa kuma kinsan inyazo ya taddaku haka ran mune zai baci duka ko!”kiyi hakuri oumma na kusa gamawa TAHEER nake jira ya taimakamun …”bata kammala magana ba sukaji anshigo falan ko sallama babu, Mai da hankalinsu sukayi kan kofa . Wata yarinyace itama da bazata wuce 15 to 16 ba a tsaye sai faman ya tsine take kamar wata babba, kura mata ido TAHEE tayi dan jiranjin mai zatace, dan tasan zuwan ameerah ba alkairi bane. Kamar kuwa ta shiga zuciyarta , “maryam dake da TAHEE wai Kuzo inji abba…, bata kammala maganar ta ba sabida saukar marukan da taji a waje maban banta. Kuka ta saki mai kara tana jiyowa. Karo taci da TAHEER da TAHEERA a tsaye sai faman huci suke saki, TAHEER ne ya soma magana “sau nawa zan fada miki duk lokacin da Kika kwaso rashin kuryarki ki dunga ajje ta a waje kafun ki tako mana daki, mahaifiyar Tamu kike dan baki da kunya “, kuka kawai ameerah take dan ba karamun zafin marin tajiba, dafe kuncinta tayi dagudu ta bar dakin .

Kallansu oumma tayi cikin hade rai,”sau nawa zan ja muku kunne kudinga hakuri da mutanan gidan nan, ko so kuke kudinga ganin raina yana baci” , kamar hadin baki TAHEER da TAHEERA suka ruke kunnuwansu ,”oumma kiyi hakuri bazamu sake ba “, Daman ta San halinsu, dungure musu kai tayi, atare suka saki dariya dan dama sunsan ba fushi tayiba.
Kamo hannayensu tayi tare da hadewa waje daya , TAHEE!! Naam oumma! TAHEERA ta amsa mata, maida kallanta tayi wajan taheer shima ta kira sunansa, amsa mata yayi shima yana kallanta. Numfashi oumma ta saki kafun ta soma magana cikin Sanyi , “ku kadai Allah ya bani, banaso kuna saurin fushinnan, inaso ko bayan raina kuzama masu kaunar juna kunji, ku zama masu hakuri da kawaici, Musamman Kai TAHEER , kafi saurin hawa”. Murmurmur taheer yayi tare da dan sosa keya, oumma kiyi hakuri, hararar wasa tasakar masa daman anan kafi kauri wajan bada hakuri. Kema taheera ki shiga taitayinki , hada ido Taheer da taheera sukai tare da hada baki , oumma kiyi hakuri bazamu sake ba .
Girgiza kai oumma tayi kawai, basuyi wata wata ba suka rungumeta, hado kansu tayi su biyun ta rungume a jikinta. Suna cikin zamannan sukajiyo bugun kofa da karfin gaske , duk mimmikewa sukai tsaye, bakowa bane face abba sai faman huci yake bayansa kuma mamy ce hannunta rike dana Ameerah sai faman cika take . Baiyi wata wata ba ya tsinkawa oumma mari, Maryam sau nawa zan fada miki ki fita harkar yata,me yasa bakyajin magana, Tom bari kiji na fada miki na gaji da wannan halayen naki, ki tattara kayanki kije na SAKEKI.
Kafun na dawo gidannan banaso naga fuskarki data yan iskan yayanki , sannan fuuu ya bar wajan. Shewa mamy ta saka toh maza maza azo abar mana gida tunda anzama bazawara, budar bakin ameerah sai cewa tayi da Yayan zawarawa sanin cewa ba mai tabata tunda uwarta na wajan , sai da mamy ta gama babatunta da zafesu tasss sannan takama hannun yarta sukabar wajan.

Zubewa umma tayi a kasa zuciyarta na faman ta farfasa ga kuncin da zuciyarta ke mata, fashe wa kawai tayi da kuka, TAHEE ma zubewa tayi a kasa tana kuka sosai, TAHEER ne mai dauriyar cikinsu yake lallashinsu, abun yayi masa ciwo sosai, asaki mahaifiyarsu agaban idansu dan basu da gata. Abbu nayi kewarka , ALLAH YAJIKANKA ABBU!! Shima sai ya fashe da kuka , haka suka kwashi kusan minti 15 suna abu daya , ganin sunki daina kukan Yasa oumma tsayar da nata kukan, tashiga lallashinsu.
Ganin sunyi shiru yasa ta mikewa, daki ta shiga ta tattaro musu Kayan sawarsu cikin jakunkunansu, sannan tasa taheer yasamo mata motar akurki dan kwashe mata kayansu, ba jimawa kuwa sai gasu, lokacin abba ya fita shiyasa mai akurkin ya shigo ya taimaka musu suka kwashe kayan.Mamy na labe ita da wata kawarta sai faman kwasan dariya suke , bayan sun gama kwashe komaine suka fito waje , oumma ta janyo kofar bangaransu Wanda ko cokali datasan natane bata bar musu shi ko daya ba.
Awaje ta tarar da mamy ta fito sai habaici take tana kwasar dariya kawarta na tayata, sabida rashin tarbiyya har ameerah ce ke kiransu zawarawa da yayan zawara wa uwarta na biyemata. TAHEER da TAHEERA kuwa suna gefe sun cika bamm ji suke Idan suka kama ameerah ba abunda zai hanasu lallasata .
Kamar oumma tasan abunda ke ransu takamo hannunsu suka fita , saida suka fita oumma ta fara tunanin ina zasu koma da zama.
Ba yadda ta iya dole su koma BUNKURE da zama , Wanda ba tsoran komawa take ba , aah yadda rayuwar yayanta Zata koma , batasan abunda zai kuntata wa yayanta, ganin tsayuwar ba mai anfani bace yasata yiwa me motar magana , bawan Allah bunkure zaka Kai mu nawa zan baka, 7k zaki bayar. Haba bawan Allah kadan duba mana, shikenan ku kawo 6k , kallan TAHEE da TAHEERA tayi da su shiga , ko wannansu jiki a sanyaye yashiga inda abunda suka tsana shine zuwa bunkure yadda ake gallazamusu suda mahaifiyarsu, ba adau lokaci ba suka fara tafiya kowa yayi jigum ba meyiwa wani magana kowa da abunda Ke cin ransa.
ASALINSU…..

➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰
GARIN LAGOS
Wasu dankara dan Karan Motocine kefaman zuga gudu akan titi, duk Wanda yazo wucewa sai ya tsaya motocinnan sun wuce tukunna sabida tanbarin da motocin ke Dauke dashi .Duk uban motocinnan basu tsaya a ko ina ba sai a NAHYAN HOSPITAL, one of the best hospital in Nigeria , ba karamun hospital bane da kallo daya zaka masa kasan ba karamun kudi aka kashewa asibitin ba , Kai tsaye wajan parking space suka nufa , cikin wani irin slow motocin suka tsaya , Wanda hakan ba karamun birge masu wucewa yayi ba . Bude motocin akai , wasu blacks American ne suka fito daga cikin motocin ko wannensu sanye da bakin suit da sunglasses,fuskarnan ba fara’a kwata kwata , yayin da hannunsu ke dauke da bindigogi. Daya daga cikinsu ,Wanda ya kasance kamar ogansu ne ya nufa wata black tinted Lamborghini sai faman sheki da daukar ido take.bude kofar motar yayi sai da aka dau kusan 40 seconds kafun ya zuro da kafarsa Guda daya , tubarkallah Masha Allah , wani irin takalmine a kafarsa kamar na sarauta, fatar kafarshi sai faman daukar ido take, wacce take fara kal cikin takalmin kafarsa, an dau kusan 2 minutes kafun mamallakin kafar fitowa. Oh my god , tubarkallah masha Allah , tabbas Allah madaukakin sarki yayi halitta anan, ba kowa bane face TAHNOON , one of the youngest billionaire kenan, daga tsohon president zayed Al_Nahyan, irin su ake kira one in thousand,dan guy din ya hadu tako ina ba Karya. Sanye yake cikin kuftan sai faman maiko da daukar ido take , wacce ta kasance blue colour , bakaramun kyau tayiwa surar jikin  saba , wacce ta kasance kakkar fa, kallo daya zaka masa kasan yana motsajikin sa ,farine irin asalin fari mai shegen kyau da tsari, yana dauke da wasu irin sexy eyes fari tass dasu, kwayar idanshi ba Baka bace sannan ba brown bace ,wasu irin idanuwane dashi mai ladaftar da makaryaci, Wanda idanuwansa ba karamun tafiyar da yan mata yake ba, hancinshi dogone ba irin over dinnan ba, amma dogone da yayi matukar yiwa fuskarsa kyau , bakinshi dan madaidaicine Wanda ya kasance pink colour , yana da saje a fuskarsa wanda ya hade da gyaran fuskarsa. Kallo daya zaka masa kasan irin mutanan nanne da ake Kira half cast , ta ko ina gayen nan ya hadu, cikin taku da kasaita ya fara tafiya , Wanda da yawa mutane suke wa kallan girman kai, musamman in ya hadu da kasaitarsa da muskilanci , dan ba karamun miskili bane na bugawa a jarida, amma a hakan ba karamun tafiya yake da imanin mutane ba .
Direct cikin premises din hospital ya nufa , duk inda ya wuce sai ma’aikata da majin yata sun gaishesa , daga musu hannu Kawai yake ,yayin da wadannan kattin ke binsu a baya , Daidai wata kofa naga sun nufa wacce ta kasance ta glass , kai tsaye wannan mutumin dazun ya bude masa kofa , lifter ce a wajan , shi kadai ya shiga wajen tare da wannan mutumin , yayin da Sauran suka tsaya . A flour 4 suka tsaya inda yakasance bakowa a wajan ( abun mamaki sai na tarar da wannan kartun sunja layi kamar masu jiran karban sadaqa😂), duk inda ya wuce sai sun Sara masa . Daidai wata kofa suka tsaya , anan ma wannan mutuminne ya bude masa kofa , tafiyar muntuna 2 biyune ya kaisu wata kofar , wata koface tsararriya a wajan me shegen kyau , direct cikin kofar suka shiga , babban office ne iya tsaruwa office dinnan ya tsaru, daga gefan hagunsa wasu dan ubansun cushion chairs ne masu shegen daukan ido ash colour , medium carpet din office din ma ash colour , daga gefan damansa kuma wani gadan duba marasa lapiya ne , daga inda kake kana iya hango table dinshi sai faman daukan ido yake ( irin na yan gayun nan😂), wajan sai faman daukar kamshi da sanyin freshener yake . Samun waje yayi kan daya daga cikin cushion chairs dinnan yayi tare da crossing legs, kallan mutuminnan yayi , cikin husky voice dinsa ya fara magana ,”zaki” shine Sunan da naji ya Kira mutuminnan Wanda in ba natsuwa kayi ba bazaka taba Jin mai have ba, “yes sir “Cewar zaki , “yaushene meeting dinnan”, “sauran few minutes sir “cewar zaki, jinjina masa kai kawai king Yayi tare da Mika masa wasu files karba zaki yayi tare da Sara masa tare da ficewa daga office din , duk wannan abun da yake fuskarshi kwata kwata ba annuri a ciki , ba a dau dogon lokaci ba daya daga cikin wayoyinsa ya fara ringing , sai da ta kusan katsewa sannan ya dauki wayar dake kusa dashi akan center table din gefenshi , UKTI shine sunan da ya bayyana akan screen din wayar , ajiyar nunfashi ya sauke ganin me kiran, dauka yayi cikin kamilalliyar muryarsa, “Assalamu alaikum”Shine abunda yace , ya dau sakanni kafun ya sake cewa komai, “masa’ul khair ukti( barka da Yamma yaya)”, bansan mai akace masaba amma ganin yadda ya natsu zai tabbatar maka da magana ce me mahimmanci suke tattaunawa,ya dau kusan 10 minutes yana wayar wacce ba abunda nakeji a ciki kasancewar cikin larabci yake maganar , baka Jin sautin muryarshi sai bakinsa dake motsawa, a haka zaki yazo ya tarar dashi , sannan suka dunguma zuwa inda aka kebanceshi dan yin meeting . Sun dau kusan 1 and half hours suna tattaunawa game da asibitin da kuma tsare tsaren da za a sake , basu sukabar NAHYAN HOSPITAL ba sai wajan karfe 5 na yamma, Kai tsaye NAHYAN ESTATE dake cikin BANANA ISLAND suka nufa .

🌹GIDAN AUNTY🌹

By mss Lee💕

👑 UK WRITERS 👑

https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA

🫶 Dedicated dis page to my masoyiya ‘yar fillo ta zara’u our star lady ! I heart ❤️ you 🫶…

PAID BOOK

Leave a Reply

Back to top button