Gidan Aunty Book 1Hausa NovelsHausa Novels

Gidan Aunty Book 1 Page 2

Sponsored Links

Free Page 2🦋

➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰
WACECE TAHEERA
TAHEERA yarinyace yar kimanin shekara 17 da dan biyunta TAHEER Wanda suke tsananin kama kasancewarsu yan biyu. Mahaifinsu Malam Mohammad  nada wadatarsa kafun yasamu karayar arziki ,yarasu shekaru biyar baya , Wanda a kazo  har gida akwai wa kisan gilla, kisan da haryanxu ba’a san ko suwanene ba , yana da mata guda daya me suna maryam wato oummansu taheera , haifaffiyar buzuwace fara tass da ita daga kasar Niger , anan suka hadu da mahaifin su taheera, Wanda yazo kasuwanci kasar. Mahaifiyarsu marainiyace wacce iyayenta suka rasu bata da kowa sai yayanta Wanda tun lokacin baya daya fita da daddare ba’a karajin labarinsaba .
Bakaramun wahala da gwagwarmaya suka shaba arayuwarsu , tun bayan rasuwar mahaifinsu taheera , kasancewar dangin babansu basu so ya auretaba, sun so ya auri yar dangi amma malam Muhammad ya nuna baya Santa maryam yakeso . Bakaramun wuya maryam Tasha ba a hannun dangin mijinta, babu me kaunarta sai KILISHI, wacce ta nuna mata so, ta tallafi yayanta har bayan mutuwar yayanta. Kilishi kanwace ga Malam Mohammad wacce suka hada baba dashi kasancewar shi kadai mahaifiyarsa ta haifa sai yan uwa . Ba karamun rawar gani ta taka arayuwarsu ba sabida irin yadda take temaka musu.Itace mace kwallinkwal da take fadar magana aji atake a wajan dalilin Auran wani hamshakin me kudi da take a Garin Lagos , shiyasa duk dangi akejin maganarta.Bayan shekara biyu da rasuwar Malam Mohammed, Malam bashari yanuna Yanasan auran maryam amma kememe maryam ta nuna bazata iya aure ta bar ‘ya’yanta ba , ba irin magiyar da Malam bashari beyiba har maganar tazo kunnen hajiya kilishi, sanin cewa bazata iya yiwa hajiya kilishi musu ba yasa ta Amince amma da Sharadin tafiya da yayanta. Wannan abu beyiwa Malam bashari dad’i ba amma haka yabar abun azuciyarsa. Hajiya kilishi ita ta dauki nauyin kome da kome na bikin maryam, tundaga kan kayan daki da sauransu, shiyasa ba karamun ganin girman matar takeji ba. Shiganta gidan bashari ba karamun wahala Tasha ba ita da yaranta, sabida tsangwaman da ake nuna wa ‘ya’yanta hatta abinci baya bawa ‘ya’yan maryam , ko ta tanbayeshi dalili kaitsaye ze ce mata sabida bashine ubansu ba. Wahalar dasu d’in da yake ne yasa maganar har taje kunnen kilishi Wanda takirashi tayi masa tatas harda i’kirarin zata kulleshi sannan ya saduda. Malam bashari yana da matarsa daya kafun ya auro maryam, asabe kenan wacce suke kira da mamy, mamy wata irin muguwar matace da batasan zaman lapiya , duk wani kulli kulli da tashin hankalin dake faruwa a gidan harda sa hannunta, da farko taso kullum su dunga danbe amma ganin maryam bata biye mata yasa ta canza taku take biyowa ta bayan malam bashari.yar ta d’aya Ameerah , yarinyace fitinanniya bata jin magana , ga rashin kunya a cikinta , Ameerah ta tsani y’ay’an maryam kasancewarsu farare tass kamar ka taba namansu ya fashe wani irin kyaune da su da baki baze musaltaba musamman tahee da take da asalin gashin buzaye har kugu, kasan cewar mahaifiyar su buzuwa mahaifinsu kuma bafulatani . Dalilin da yasa mamy da yarta suka dauki Karan tsana suka dora musu, dan ko ita mamin tasan maryam ta wuceta akomai amma sabida harsada da kyashi taki barinta, a haka har suka kwashe tsawan shekaru uku kafin yanxu rabuwarsu da Malam bashari.

➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰
BANANA ISLAND unguwace ta wane da wane da ta amsa sunanta, a jere motocin suke tafiya , tun kafin ayi horn sojojin dake gadin first gate suka wangale musu kofa, tare da Sara musu, wata iriyar koface a wajan kallo daya zaka mata kasan ba Karamun makudan kudi aka kashe akanta ba, cikin kwarewa motocin suke tafiya harsukazo gate 2, nan din ma wani abun kallo ne , karamun titi ne a wajan sai kananan shukokin dasukayiwa wajan kwawanya, wajan bakaramun haduwa yayi ba , minti uku kacal yakaisu main gate din gidan inda yafi ko ina tsare sabida sojojin da ke ke waye da wajan .sanin Wanda yake cikin motar yasa ba bata lokaci aka wangale musu gate , wow !! Wow !! Wow !! Shine abunda bakina ke furtawa tunkan na karasa shiga nasan bakaramun gida bane wannan, dan filine a wajan me dauke da korayen shukoki inda yayi wa wajan kwawanyaw, babban estate ne me dauke da part part na musamman, duk inda ka kalla zaka ga alamun hakan sabida giftawar da masu aiki keyi lokaci lokacin cikin shigar uniform Dinsu . Kai tsaye wani babban glass building motocin nan suka nufa Wanda yakasance daban cikin buildings din , Daidai parking lot din building din motocinnan suka tsaya , ba  bata lokaci duk suka fito daga motar, yanxun ma zaki ne ya bude masa kofa, sea da ya dau tsawan lokaci kafun ya fito gaba daya daga cikin motar, Sara masa sukayi a tare , ba Wanda ya kalla a cikinsu sai ma kara tsuke fuskarsa da yayi , a hankali ya fara tafiya cikin takunsa kamar bayasan taka kasa direct main door ya nufa , still zaki na biye dashi  har cikin farlon da ya gama haduwa , direct wata kofa ya nufa , shi kuma zaki files din hannunsa ya ajje tare da ficewa gaba daya daga cikin building din.

WANENE TAHNOON
TAHNOON Wanda ake wa lakabi da KING , shalele kuma mafi soyuwa a wajan mahaifinsa , saurayine Matashi dan kimanin shekara 33 a duniya . Mutumne me matukar dukiya , kasaita da kuma miskilanci , bayasan raini ko kadan,baya shish shigi da shiga sabgar kowa , King babban muskiline Wanda da yawan mutane ke yiwa kallan girmankai, dan da wuya kaji yayi dogon magana da mutum, yawancin maganarsa da idone,king ya kammala karatunsa na likitanci a kasar turkey, a yanxu haka doctor ne shi babba  daya karanci bangarori na lafiya, mutum ne shi me temako da sanin darajar mutane , amma in ba zama kayi dashi ba bazaka taba sanin hakan ba. King na da babban asibiti mai suna NAHYAN HOSPITAL, asibitine da yake temakawa marasa karfi duk da kasancewarsa asibitin kudi.wannan dalili yasa mutane ke ganin girmansa da kimarsa.Wanda duk Garin Lagos da ke wayanta zaka samu talakawa nazuwa Neman temako, Hakan yasa talakawa ke mugun sonsa da kaunarsa. Ko guri zaibi zakaga manya da yara na daga masa hannu tare dayi masa kirari, hakan yasa yayi suna sosai a fadin Nigeria dan ba Garin Lagos kawai yake temakawa ba , shiyasa da yawa masu kudi basa sanshi.
Mahaifinsa zayed-al-nahyan babban dan siyasane Wanda har mukamun shugaban kasa ya ruke , kuma hamshakin me kudine dayayi Fuce a kasar Nigeria gabaki daya da ke wayanta. Alhaji zayed mutumne adali me temakon jama’arsa,shiyasa ake matukar girmamashi, Adalin shugaban kasane Wanda har yanxu mutane suke kwadayin ya kara shugabantarsu.tsohon shugaban kasa yana da mata biyu, matarsa ta farko Itace hajiya suhaima, hajiya suhaima balarabiyar dubaice daga ita sai yayanta da kanwarta iyayenta suka haifa, macace me matukar miskilanci da kawaici, ga tarin dukiya da Allah ya bata , ga ilimin addini Dana zamani. Hajiya suhaima yayanta 4, Babban d’anta sunanshi mohammed amma Allah yayi mishi rasuwa shekarun baya da suka wuce sai ‘yarta ta biyu samreen suna kiranta UKTI , tayi aure yanxu tana saudiya ita da mijinta, sai king da autarsu zoya.
Matarsa ta biyu Itace hajiya kilishi , kamilalliyar mata wacce tasan ya kamata , macece me matukar wasa da yara , baruwanta Sabida kyautatawar ta yasa yawancin yayan gidan suna part dinta. Yar ta d’aya zulaiha wacce ta rasu tun tana yarinya. Suna rayuwane da familyn su cikin da Kaunar juna, tare da kakarsu dasuke kira Dada. Dada masifaffiyar matace gata da rigima ta bugawa a jarida, amma hakan besa ta wulakanta kowa ba , mutumce me temako da san jama’a, duk cikin jikokinta tafisan king duk da yawancin lokuta cikin rikici suke da ita , sai uncles Dinsu guda biyu uncle musaddiq da uncle salim, suma ko wannansu na rayuwa agidan tare da iyalinsa. Uncle musaddiq na da mata biyu hauwau wacce suke kira da mamy tana da ‘ya’ya 3 , kabeer , ihsan, sumayya sai matarsa ta biyu kubra ana ce mata momy tana da ‘ya’ya 2, haroon , firdausi(feedy). Uncle salim kuma matarsa daya mai suna amina ana ce mata aunty , basu da ‘ya ko daya sai ‘yar rikonta mai suna amrah, sabida duk dan data haifa baya dadewa suke mutuwa sai kanwarsu zarmeen wacce take aure a abuja da danta sha’aban.

Cigaban labari…

➰➰➰➰➰➰➰➰
Sai gabanin yamma suka karaso bunkure , lokacin ba karamun jigata sukayi ba, daidai babban gida na kasa daya kasance kamar family house suka tsaya , nan yara suka fara taruwa , ga yan birni , ga yan birni Wanda labari har ya fara karadewa . Nan mutanan gidan suka fara leke dan ganin ko suwanene, mutanan da suka ganine yasa su fara kuss kuss ana tuntsurar dariya , duk wannan abun da ake taheer and taheera na gefe, itama oumma  duk jikinta a sanyaye yake harta kammala biyan mai mota kudinsa bayan ya temaka musu ya sauke musu kayansu . Tun a soran gidan suka fara cin karo da kwano, ga Shara a wajan. Oumma ce tayi sallama yayin da taheer da taheera ke bayanta,gaishe da su oumma da su tahee sukai ganin babu raya yanxu agidan ma duk an aurar dasu sai wa ‘inda ba a rasa ba, cikin izgili da wulakanci suka fara amsa musu gaisuwar tasu, tare da habaice habaice kowa na fadar albarkacin bakinsa . Wata tsohuwa ce ta fito daga wani daki gashin kanta duk yayi furfura da kar take iya tafiya,”wa nake gani kamar maryama da bankadaddun ‘ya’yanta, me ya dawo daku kuma , ko da yake daman  kun saba zuwa ba nosis (notice).”to Nide wallahi babu ruwa na ga dakin kucan ba Wanda yake shigarmuku sabida hajiya kilishi ta Hana, amma wallahi bazaki takurani ba,”wai ma tsaya uban me ya kawo ku wannan karan kuma “, sun ku yar da Kai oumma tayi dan kwata kwata ta kasa magana ma, taheer da taheera kuwa ko wannansu hade rai yayi, in akwai abunda suka tsana a zagar musu mahaifiya. Tabe baki kaka ta bawa tayi” oh ni ‘yasu kujimun muna furci daga tanbaya sai ki wani fara sum sum da kai sai kace wata muna fuka”.tun tsirewa mutanan gidan sukayi da dariya, yayinda ko wa ke tofa albarkacin bakinsa. Ganin abun nasu ba me karewa bane yasa oumma mikewa tare da nufar dakinta Wanda ya kasance na hajiya kilishi ne mallaka musu,dakine a ciki da falo harda d’an kewaye da aka d’anyi mashi daga waje.Balefi kusan duk cikin gidan babu inda ya kai nasu kuma kilishi ta Hana kowa kwace musu acewarta wata rana in suka zo zasu dunga zama a ciki. Shigarsu cikin ‘bangaren sai da suka d’auki tsawan lokaci suna gyaranshi dan ba karamun daud’a yayi ba, suna gamawa duk sallah sukai suka mimmi’ke ga yunwa sunaji amma ba daman cin abinci sabida sunsan ko zasu mutu mutanan gidan bazasu basu ko ruwan shaba. Haka suka zauna oumma da tahee suna daki d’aya yayinda taheer kuma yake shinfida a falo dakin. Cab cikin dare lokacin da kowa ke hutawa wani ba’kin haya’kine ke tashi kad’an kad’an kafun daga baya wannan bakin ya bace batt…, can dakinsu taheera kuwa wani abune kamar silver yake faman she’ki a jikin taheera yayin da fatarta ke d’auke da wannan silver d’in kamar na maciji, kafun wani lokaci ta rikid’e tare da dawowa katuwar macijiya, ko munti 2 batai ba jikinta ya kuma dawowa Daidai, sai nan ta kara dawowa wannan macijiyar, daidai gabanin asuba jikinta ya dawo daidai, kwata kwata babu alamaun wannan macijiyar.

➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰

Comment and share  ✍️

‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA

💖GIDAN AUNTY💖
( A heart touching love story)

            By  Aysha galadima
( mss Lee)

💖The talent troupe 🔥

PAID BOOK

Leave a Reply

Back to top button