Gidan Aunty Book 1Hausa NovelsHausa Novels

Gidan Aunty Book 1 Page 8

Sponsored Links

BOOK 1📕

Free page 8 🦋

Karfe uku na dare ko ina yayi shiru kasan cewar ko wana bawa yana wutawa a irin wannan lokacin , wani macijine tass dashi ya fito cikin wani rami tare da kwanciya a bayan tahee ,cikin mafarkin da take ta fara lalube lalube, har hannunta ya kai kan wannan siririn macijin, jin abu me laushi da san tsi besa ta bude idanuwan ba , sai faman shafashi ,a firgice ta farka daga baccin da take “mewam “ta furta cikin firgici, juyawar da zataine idanuwanta Suka sauka kan macijin , azabure ta Kwala ihu”oumma, oumma” ta fada a tsorace ganin duk ihun da tayi oumma bata motsaba, ja da baya ta fara ganin macijin na kokarin biyotan itama ,” Innalillahi me nayi maka kake biyoni, oumma ki temakamun”, duk ta firgice ganin macijin yayi Kuri da ido yana kallanta, ga oumma da ko motsawa batayi ba,kara nufota macijin yayi ta fara girgiza kai “ Dan Allah ba danni ba kayi hakuri , ni bansan me nayi maka kake bina ba, kayi hakuri dan Allah “ ta karasa fada tana fashewa da kuka, kamar daga sama taji saukar yar muryan dan yaro” ni ba abunda zan miki , kawai inaso na zauna wajanki “, waro manyan idanuwanta tayi kamar zasu fado kasa jin maciji na magana abunda bata taba jiba a rayuwarta,mintsinin kanta tayi dan tabbatarwa”kodai mafarki nake”, ta fara tanbayar zuciyarta,”Aah ba mafarki kikeba “ta kara jin saukan muryarsa , kara fashewa da kuka tayi fuskarta duk ta hada zufar wahala “ na rokeka koma wanene kai kayi hakuri ka kyaleni, ni ban muku komai ba”, be ce mata komai saima biyota da ya fara cikin tafiyar macijar, itama baya ta faraja tana girgiza masa , wani dan kwanan da  ta gani tayi saurin dauka da niyar kwala masa , kamar wacce ta tuna wani abu sai ta tsaya tana kallansa”Mewam”a hankali ta fadi sunan, cikin sauri majicin ya karasa jikinta yana zagayeta , itama sai faman dariya take , duk wannan abun ba wanda ya farka daga baccinsa duk da tsananin ihun da ta kwala.

Yau sun makara dukansu basu tashi sallar asuba da wuri ba, suna idar da sallah aikin gidan suka fara kafun mutanan gidan su fito,wanke wanke oumma ta fara su tahee na ebo mata ruwa , suna kammalawa tahee ta share tsakar gidan , sosia suka gyara gidan ganin yadda yayi Datti sosai kamar ba a gyarashi , Daidai lokacin da mutanan gidan ke futowa, daya daga cikin yayan gidan da suka zone tabi su da kallan kaskanci,”ke” ta fada tana nuna tahee , banza tahee tayi da ita kamar batasan da itaba,”bajini ina kirankiba ko sai na zageki zaki gane”, kallan tahee oumma tayi ba magana ake miki ba,dan karamun bakinta ta tura tana bin HAJJO da kallo, dan siririn tsaki hajjo ta saki”Aushe duk karyar banzace, ki jira ynxun ki mun wanki dan ba Hutu kuka zoyi mana gida ba”tana gama fadar hakan rai wuce warta, kande ma dake daki wuff ta fito”Nima yanxu zan gito miki da wankina “,da daidai da daidai mutanan gidan suka fara fitowa, kaka ta bawa da ke faman amma je ta karaso wajan , ke kuma uban me kike mana anan wajan ,muryar su hajjo taji”inna aiki muka sata , Kema in kina da wanki ki kawo tayi miki”,kaka ta bawace ta amsa mata “Aini baba rasa aikin sawa, yo inba aiki ba Menene anfanin katuwar budurwa haka har yanxu batai aureba”, da Sauri Dije ta fito hannun ta rike da mafici “ai inna kwara kiyi mata aure,ki duba  ki gani ko bintalo da take 13 dududu saura mako uku bikinta”, dago da idanuwanta tahee tayi tana bin Dije da kallo sai kuma tayi saurin maidashi kan oumma da ta sun kuyar da Kai, zabura tayi da jin zancen inna” kuma kin kawo shawara me kyau dije, daman tanimu me guga ya dade yana santa,ubanta ne ya Hana yanxu kuma kin ga bayanan in yaso sai a hada Dana bintalo “, sosai mutanan gidan suka kwashe da dariya dan Sarai sunsan tahimu babban dan iskane a Garin ga shaye shaye da yake ,wuce wa oumma tayi daki batare da tace komai ba, taheer na tsaye duk ya hade ransa, dije kawai yake kalla yana girgiza kansa,kwallace ta tararwa tahee” ni zasuyiwa Auran dole , Auran ma da dan iska dan shaye shaye “ kawai sai ta fashe da kuka yan gidan kuwa sai faman shewa suke, tare da watsewa bayan uban tulun wankin da suka ajje mata, TAHEER ne yashiga lallashinta har tayi shiru sannan ya taimaka mata sukai wankin tare , duk jikinsu yayi sanyi musamman tahee dakanta ya fara ciwo. Suna gama wankin daki suka koma, oumma suka tarar tana gyara kayan sawansu”oumma “ tahee ta fada hawaye na kara zubomata, dakatar da ita oumma tayi tana daga mata hannu”bana san jin komai”tana gama fada ta dakko wa taheer ya mutsats tsiyar dariya biyar, ta lissa fa masa abunda zai siyo mata , karba yayi tare da fita daga dakin, itama tahee waje ta samu tare da juyawa tayi kwanciyarta, bunta da kallo oumma tayi tana kokarin share kwallar da take ta faman dannewa” ya Allah kai kadaine me iyawa ka kawo mana mafita “ ta fada a zuciyarta,itama taheen duk da yadda oumma ta share zancen tasan abun yana damun ta ne ba yadda zatayi ne , har taheer ya dawo daga aiken ko wannansu yayi jigum jigum, taliyar da oumma tasa ya siyo ma kasa cinta sukai saida oumma ta hade musu rai sannan suka tsast tsakura.

➰➰➰➰➰➰➰➰
Yau tun safe ba Wanda ya ganshi , hatta zaki bayan sun dawo daga masallaci be kara sanyashi acikin idanuwansa ba.
Kwance yake kan kantamemen ‘kayataccen gadonsa, idanuwansa lumshe suke kamar mai yin bacci amma a zahiri ba baccin yake yiba, tsananin yanda kansa ke saramasa yasashi lumshe idanuwan, yunwa yake ji amma ba ze iya cewa a kawo masa a binci ba, a hankali ya bude kyawawan idanuwansa da sukayi matukar canza kala daga launin fari zuwa launin ja ja,idanuwansa ya maida kan agogon dakin kafun ya kara lumshe idanuwansa ya mike, sanye yake cikin wasu white kaya Riga da wando, wandon iya kwiwa , sosai kakkarfar jikinsa ya fito, inda coffee maker dinsa yake ya nufa, cikin kankanin lokaci ya hada coffee din , yana siffing a hankali bayan ya kammala Sha kai tsaye wani dan buttun ya dannan, take wata kofa dake jikin bango budewa da kanta, babban wajen Shaka tawa ne a wajan me girman gaske sosai , iya haduwa wajan ya haduwa , daga gefe daya wasu set din kujerane kawai a wajan sai wasu korayen flowers dasukayi wa wajan kawanya, sosai wajan ya hadu iya haduwa, inda take a cikin kejinta ya nufa,tana ganinsa ta fara bude fuka fikinta cikin muryan aku ta fara”gashinan yazo, gashinan yazo,king yajo “dan sakin fuskarsa da take a hade yayi tare da bude mata cage din , a guje kuwa ta fito tana zagayeshi kafun ta sauka a kan kafadunsa, shafa kanta yayi kadan kafun ya bude bakinsa” how’re you”, abun mamaki se ga tanan ta amsa masa, be kara cewa komai ba ya fito daga wajan .tabbas yasani a part from his family babu me damuwa dashi kamar zaki, wayar hannun sa ya dauka tare da danna wani number , seconds kadan aka amsa wayar sai da ya mula dan kansa sannan yasa wayan a kunnensa, sallamar zakice ta daki kunnensa, kamar baze ce komai sai kuma ya amsa, zaki zai kara magana yaji saukar muryar boss”am fine, you should rest too” yana gama fadar hakan ya kashe wayarsa.

*****************************
*****************************
Zaune su amrah suke cikin  wani kayataccen garden din da ya gaji da hanuwa, komai na wajan ya hadu sosai ba kadan ba ,ga sanyayyar iskar dake kadawa me shegen kamshi, sosai garden din ya hadu , amrah da ihsan suna zaune kan lilo be hade da flower gwanin ban sha’awa, sumayya da firdausi kuma suna zaune kan wasu kujeru, daga gefe daya yan aiki ne ke fan yi musu hidima, sosai suka cika gabansu da abubuwan ci kafun  cikin isgilanci amrah tace musu subarwajan, suna barin wajan kuwa ihsan ta fara musu dariya, sosai take dariya musu tana binsu da kallo, dukan su sunsan dariyan me take shiysa suke binta da harara, sai data gama sannan ta kallesu “ wallahi yaya king halinsa saishi, ni Allah ne ya kubutar dani ,saura kadan na saki fitsari wallahi musamman yadda naga idanuwansa “, dukkansu dariya suka saki ,sumayyace ta kalleta “ Aini baku sani ba wallahi suma ne kawai banyi ba , dan ba karamun tsorata nayi da yanayinsa ba,zuciya tace kawai ke bum bum, amma duk da haka munci uban mu, Allah ne ya temakemu kuka tsaya a jan kunne be kada da tsitstsinka mana mariba”, yanxu ma duk dariya Suka saki tuno yadda yasasu tsallan kwani, ya tsine fuska Amrah tayi” ni kuma kunga ko a jikina dan my king ya samu wannan punishment din a Hakan ma ai na kalleshi da kyau “ dogon tsaki firdausi taja “shiyasa naga kin fi kowa rudewa ai , se shegen cika baki amma da kin gansa zaki fara ma kyarkyata” tana gama fadan haka ta tashi ta bar wajan, da harara Amrah ta bita” inma bakin cikin zan aura yaya king kike sai dai ki gama dan shi din nawa ne ni kadai”, babu Wanda ya Tanka mata tsakanin ihsan da sumayya sai binsu da kallo da sukai , inda sabo sun saba fada akan yaya king , kowa tace na tane sudai nasu ido kawai , daga nan suka canza hirar zuwa wata da ban suna yi suna dariya da Shan kayan da aka kawo musu har yamma suna wajan kafun su tashi kowa yayi part Dinsu.

➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰
BUNKURE

Dije ce rike da buta a hannu, yayinda take sanye da daurin kirji, daya daga cikin abubuwan da aka cika da ruwa ta nufa ganin ko wannansu cike taf da ruwa yasa cikin mugunta ta waiga ganin babu kowa a wajan duk sun shiga bacci yasa ta dauki a bu ta fasa daya daga cikin randar, take a Wajan ruwan ciki ya zube daman tafi ko wacce girma a ciki, d’ayar ta nufa da niyar fasa ta itama taji saukan Mari a fuskarta, ihu ta saka tare da sakin butar hannunta,wani kwakkwaran mari aka kuma yi mata , dafe kumatun nata tayi tana fashewa kuka, juya wa tayi dan ganin wanda ya marenta amma wayan bata ga kowa ba , a tsorace ta juya sai faman zare ido take , a hankali ta daga kafarta da niyar guduwa, sai Jinta tayi timmmmmmm a kasa ta fadi, wani a zababban kuka ta saki “ ku kuke ganin mu bamu muke ganinku ba , dan girman Allah kuyi hakuri”sai kawai ta kara fashe wa da kuka, jin shiru na wasu yan mintunan yasa ta mikewa da niyar guduwa , wasu kwararan maruka aka kara sakar maka , take a wajan ta suma fitsari na bi ta jikinta.

******

💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖

      DUK KARFIN IZZATA( star lady )

GIDAN AUNTY( mss Lee )

     SARKI SAMEER( xeenat love)

YA FITA ZAKKA (maman sayyid)

        JINI DAYA ( mss Bbk)

‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA

💖💖GIDAN AUNTY 💖💖
( A heart touching love story)

         By mss Lee 💖

💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖

PAID BOOK

MAI SON AI MAI TALLAN KAYANSA YAMUN MAGANA TA WANNAN NUMBER 07041879581

BOOK 1 📕

Leave a Reply

Back to top button