Gidan Aunty Book 1Hausa NovelsHausa Novels

Gidan Aunty Book 1 Page 49-50

Sponsored Links

BOOK 1 📕

Page 49_50💖

🫧🫧🫧

AMRAH

Tana komawa part Dinsu ta fara sakin ihu, ihu take kamar wata zautacciya, data ga hakan be mata ba sai ta fara birgima a kasa tana kuka, sosai take kuka kamar wacce aka ce mata mahaifiyarta ta rasu, a haka aunty tazo ta tarar da ita , bata kulataba tayi shigewarta daki itama dan ita kadai tasan yanda ranta yake tafarfasa, “a wannan karan dole nayi wani abu”cewar aunty lokacin da take karasa shiga dakin ta. Wani saban bakin cikin ne ya kama amrah ganin yanda aunty ta shareta kamar bata san da wanzuwarta a wajan ba, itama a fusace ta shige dakinta, ko zama batayi ba ta dannawa mahaifiyarta kira , kusan missed called uku tayi mata babu Wanda ta daga a ciki,ihu amrah ta saki tana jefar da wayar tata a kasa baki d’aya, take a wajan wayar ta bada sautin kas_kas, a fusace ta juyo, juyawar da zatayi idanuwanta ya sauka a kan fuskarsa da take sanye da mask baki, sosai idanuwansa yayi jajur alamun bacin rai Tsanta kan fuskarsa, duk da tsoran da ya kamata ganinsa cikin tsiwa da bakin cikin dake ranta ta nuna masa kofa”me ya kawo ka dakina ka zo ka futar min a daki”, ba ta karasa zancanta ba ya fesa mata wani power a fuska ,take a wajan ta zube kasa, cikin Bacin rai ya daga ta dare da jefata kan gadon, ransa ba karamun baci yayi ba yau, sex yake da amrah kamar yasamu kayan wanki haka yake anfani da ita duk da kasancewar a bude take amma hakan sai da yayi mata kaca kaca cikin bacin rai, ya dade yana lalata da ita kafun ya sauka a kanta yana gyara mask dinsa dake kokarin cirewa,ko kallan inda take be kalla ba yabar dakin.

🫧🫧🫧🫧🫧🫧
🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧

WASHE GARI

Kiran sallar asuba ne ya tayar da ita sai faman ya mutse fuska take , adduar tashi daga bacci tayi tana dafe goshinta,Kallan jikin ta tayi kafun ta tuno abunda ya faru tsakanin ta dashi, dan karamin bakinta ta turo tana hararan gefen da ya zauna kamar yana wajan “mutum duk yabi ya lallatsewa mutum jiki” ta karasa tana mike . Wanka tayi kafun ta dora alwala ,ko da ta fito doguwar Riga ta saka mara nauyi Sabida yan jikinta yake mata tsami musamman breast dinta dake mata zafi. Tana idar da sallah karatun alkurani ta zauna tanayi kafun tayi wa oumman ta da taheer addua, sannan da neman zabin Allah akan Auran da akai mata duk da tasan ita din ba tsararsa bace bazai taba karban taba, har yanxu jikinta da sauran zafin zazzabi, dogon hijab dinta tasaka ta fito falo fuskart duk tayi fayau da ita, bata tarar da kowa ba a falon , yunwar da ta faraji ne yasata nufar kitchen , tea kawai Tasha dan kadan ,shima tana kammala shansa taje ta amayar dashi, bata kara zama a falon ba ta koma dakinta tayi wanciyarta.

💖💖

A bangaran king tun da ya bar part din kai tsaye part dinsa ya koma ,idanuwansa duk sun canza daga launin fari zuwa jajawur,jijiyoyin goshinsa duk sun ya fito asaman kansa rudu rudu, cikin zafin nama ya nufi kitchen din sa, bai tsaya a ko ina ba sai wajan coffeee maker dinsa, kadan ya hada ya kai ba ki, tana kai wa kuma ya furzar dashi daga bakinsa ,rumtse idanuwansa yayi duka biyu yana nufar lifter dinsa , ko da ya isa 3rd floor , toilet din white room dinsa ya nufa , ruwan sanyi kawai ya sakar wa kansa hatta kayan jikinsa ba cire ba , ya dauka sama da hour 1 ruwa na dukansa, ganin mura na kokarin kamashi yasashi kashe ruwan, kayan bacci kawai yasaka ruwan kansa sai tsiyaya yake ,fresh water yauka Mara sanyi tare da dakko wasu magun guna dake bedside dinsa, Yana kammala shansu, karfin gudun Acn ya kara tare da kwantawa, tunda ya kwanta nunfashinsa sai faman seizing yake kamar zai fita daga gangan jikinsa, tunda ya runtse idanuwansa be bude ba sabida yanda jake jin kansa, ya dade a haka kafun bacci ya dauresa.

Washe gari tunda ya tashi daga sallar asuba be koma ba, ransa a cunkushe yake yin komai , ko bayan da aka idar da sallah be nufi part din kowa ba ya koma part dinsa , kwata kwata babu digon murmushi akan kyakkyawar fuskarsa.

🫧🫧🫧🫧🫧
🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧
🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧

Karfe 12 da rabi ta farka daga baccin da ya dauketa, ganin yanda lokaci yaja ne yasa ta sake yin wani wankan ta shirya cikin doguwar rigar atanfa da ta fito da ainahin shape din jikinta, hakan nan taji sha’awar yin make up , powder kawai ta saka sai kwalli daya fito da fararan idanuwanta, lipstick ta dauka fari tasaka a dan karamin bakinta ,kafun ta daura dankwalinta daurin zahra buhari gashinta na sakko wa har gadon bayanta. Bin fuskarta tayi da kallo,”fatabarakallahu ahsanin khalikin”, iya kyau kyanta ya fito musamman yanda manyan kyawawan idanuwanta suke lumshewa ,idan ba sanin ta kayi ba sai ka dauka wata balarabiyace , kyanta na buzaye sosai ya fito da yawunta,ita kanta murmushi ta sakar wa kanta da ya sanya dimples dinta lotsawa,kamar wacce taga wani sai kuma ta saka duka hannayenta biyu tana kare fuskarta, kasa kasa take dariya ita kadai.

Tana fitowa falo ta tarar da su ihsan su hudu, ihsan, firdausi,sumayya ,sai wata da ban da bata taba ganin taba . Ihsan na ganinta ta zaro idanuwanta waje dan batai tunanin kyaun taheen ya kai haka ba, kallanta kawai take sosai tayi mata kyau iya kyau hatta su sumayya da firdausi binta da kallo suke Musamman gashinta da ya zubo har gadan bayanta,bakuwar da suka zo da ita ma bin tahee tayi da kallo lokaci zuwa lokaci tana sakin murmushi,mamakinta ina suka samo wannan balarabiyar.

A hankali tahee ta karaso cikin falon duk ta tsargu musamman yanda suke binta da kallan kurilla , murmushi ihsan ta sakar mata , amaryar yaya sannu da zuwa , wani iri tahee taji da ta kirata da wannan sunnan, dan guntun murmushi kawai ta saki tana gaishesu kafun ta gaishe da bakuwar itama, bayan gaisuwa kuma bata kara cewa komai ba tayi shiru da bakinta, lokaci zuwa lokaci suna sako ta a hiran da suke,daga uhmm sai eh ko aah ne amsarta. Sallamar mahma ne yasa suka maida hankulansu gabaki d’aya kanta, gaishe da ita tahee tayi , cikin kulawa kuwa mahma ta masa tana tsokanarta”wato har kin fara mantawa dani kenan ko”, dan sunkuyar da kanta kawai tahee tayi kasa tana wasa da yan yatsun hannunta, itama mahma bata kuma cewa komai sai waje da ta samu ta zauna cikin yan matanta, tana nuna bakuwar dake falon,” wannan sunan ta azeema, daga yau Itace zata dunga kula da abunda ya kamata kici , da gyaran da za ayi miki duk Itace zatayi miki,nasan baki santa ba,sannan inaso ki hada kayanki yanxun nan driver na Wajan part din nan ,zai kai miki kayanki part din da zaku zauna ayi muku gyaran jikin”, ta karasa zancanta tana nuna azeema itama” amzy wannan Itace amaryar tamu , please a gyaramun ita sosai da sosai”, murmushi amzy ta sakar mata ,”insha Allahu aunty baki da matsala za’a gyara miki ita sosai da sosai”, itama mahma murmushin ta saki “ nasan zaki iya ai “, ihsan ce ta kalli mahma ,”amma mahma har da mu za’ayi gyaran jikin ko”,kallansu tayi daya bayan daya kafun ta furta wanene yakeso ayi dashi,tunkan ta kai karshen zancenta ihsan ta daga hannunta, itama firdausi hannun ta ta daga acewarta bazata cutu ba ayi ba ita,sumayyace kawai bata daga hannun ba , ganin mahma na kokarin dauke kanta yasa ita ma ta daga hannunta, ranta duk ba dadi amma ya zatayi ta kara yadda dacewa king yayi mata nisa ,musamman ganin har yanxu yarinyar da take nunawa tsana ko saudaya bata taba daga mata yatsa da sunan rashin kunya ba,”Allah ya bani Nima nagari”ta fada kasan zuciyar ta dukda tsananin san king dake cikin ranta amma tayi alkawarin kokarin ciresa daga ranta itama .
Murmushin farin ciki mahma ta saki,”toh amzy ga wasu yan matan kin samu , bayan su ma akwia karin guda biyu, duk zasu koma part din , Inya so sai ayi musu gyaran”,cikin gamsuwa ta furta Insha Allahu. Maida kallanta mahma tayi kan tahee da kanta ke durkushe tana wasa da yan yatsu, “oya daughter tashi kije ki hada kayan naki, nan da 30 minutes za’a kai miki can part din da zaku zauna,cikin sanyin jiki ta furta “toh “ kafun ta mike ta shiga cikin bedroom dinta,ta kulle kofa kenan tana jiyowa taci kara da faffadan kirjinsa,baki tabude zatayi ihu hannunsa d’aya kawai ya saka ya toshe mata baki tare da jinginar da ita jikin kofar,fuskarta yabi da kallo musamman dan karamin lips din ta dayasha lipstick sai maiko yakeyi, Zara zaran lashes din ta suke faman kadawa yabi da kallo, sosai ya kare mata kallo tunda ga kan kafafuwanta har zuwa tummy cikinta, kafun ya dauke idanuwansa akan kirjinta dake faman harbawa , hannunsa d’aya ya dora kan breast dinta, da sauri ta saki karamar kara tana ya mutse fuskarta tare da jan jikinta kadan baya, fuskar da ta ya mutse ya kalla kafun ya kara mayar da hannunsa kan kirjin nata, yanxu ma baya ta kara ja tare da saurin rike hannusa, kwalla har ta fara tarar mata,”me ya faru” ya furta a hankali,cikin rawar murya ta furta”za..fi,zafi nake ji agurin “, be ce mata komai ba ya matsa daga wajan da take , Daidai saitin mirror din dakin ya koma yana bin wjan harabar filin da kallo, itama sun kuyar da kanta kasa tayi tana dan satar kallansa sabida kyan da ta ga yayi mata ga fuskarsa da tayi fiyau kamar mara lapiya,a bazata taji saukar muryarsa ,”baki iya gaisuwa ba”, dan karamin bakinta ta turo kadan kafun ta furta “ina wuni”, banza yyi da ita batare da ya amsa ba ,kara gaishe sa tayi a karo na biyu shima be amsa matan ba sai takowa da yayi har inda take dan rankwafo da fuskarsa yayi Daidai kan tata, “kalleni “ ya furta mata , amaimakon ta kallesan sai ta kara dukar da kan nata kasa,a fusge ya furta”karki kuskura na kara maimaita wa” dan dago da kan nata tayi kamar me shirin turo masa baki, tana daga da fuskarta ya bata hot kiss da ya dauke sa kusan mintuna biyu yanayi,ita kam tahee kunya ce ta kamata ta rasa yanda zatayi, zare bakinsa yayi daga nata yana binta da kallo”from today , wannan shine gaisuwar da zaki dunga yi mun”, kin amsa masa tayi sai ma sunkuyar da kanta da ta sake yi,” zan kai wa mahma kaya “ ta furta Adan tsorace tana niyar juyawa, “And then “, ya furta nan ma shiru tayi masa ta kasa bashi amsa , “who am I to you “ ya furta yana kallanta,”yaya king “ ya furta batare da damuwar kallan da yake binta dashi ba sai ma dan daure fuskarta da tayi ,”apart from that “, ya kuma furtawa,da sauri ta juya zata bar wajan ya janyota jikinsa , “idan ina magana kina tafiya ranki zai baci , answer my question , who am I to you “, kukan da taji yana kokarin zuwammata ta rike tare da furta “yaya king “ shiru yayi yana kallan yanda ta dan daure fuskarta,”say something “, yanxun kam kukan da take kokarin rikewa ne ya subuce mata, hannayenta biyu hade masa waje d’aya batare da ta kallesaba ta furta “ na rokeka ka fita daga dakin nan , banasan ganin ka,kace ka tsaneni dady to Nima ka fitar mun daga dakin”, murmushine yaso subuce masa kalmar dady data ambata,matsowa kadan yayi kadan kafun ya furta “ni Yaushe nace miki na tsaneki “ dan turo bakin ta tayi sam ta manta a gaban wa take “rannan “, eyes dinsa ya dan zaro “ni karki mun sharri Yaushe na ce miki haka , gashi har kin fara bata kwalliyar taki” ya karashe yana daga mata ido daya . D’auke kanta tayi daga kansa tunanin yanda zata hada kayanta yake ganin hour dayan ta kusa cika ,”am going “ bata san lokacin data furta “Tom “ ba cikin sauri , da mamaki yake kallanta ganin ta bashi amsa lokaci d’aya, ganin kallan da yake binta da shine yasata saurin matsawa nesa dashi kafin ta furta “daman fuskata zan wake “tana kai karshen maganar nata tayi sauri ta shige ban daki daga inda yake yana jin karar lock din da ta saka ,dariya abun yaso bashi ma , bece komai ba ya nufi wajan wardrobe dinta, wasu kaya ya ware mata gefe guda kafin ya dannan wani designer frame nake dakin, take a wajan wardrobe din ta bude wata kofa ta bayyana awajan,yana shiga kofar ta rufe kansa kamar wata kofa bata taba wanzuwa Ba awajan. Ta dade a toilet din jin shiru yasa ta bude kofar a hankali tana Leko da kanta ,ganin babu kowa a dakin yasata sakin ajiyar zuciya,sai yanxu take mamakin yanda akai yazo cikin dakin ganin babu me bata amsa yasa ta janyo babba f trolley zata bude wardrobe din ta kenan taga wasu kaya an futo mata dasu ,dukda tasan ba Itace ta futo dasu ba, bata kawo tunanin komai ba ta saka kayan a cikin akwatin tare da daukan underwear’s dinta ta saka a ciki, cikin sauri sauri take komai ganin awa d’ayan da aka bata ya wuce , tana fitowa ta tarar da ba koma a falon sai asabe, asabe na ganin ta , ta nufota sai faman washe mata baki take tunda ta samu labarin ta zama mayar king yanxu, kadan ta dauka tare da kai wa zaki dake cikin mota suka bar wajan yayi saura sai tahee kawai, waje ta samu ta zauna a falo,yau kwata kwata bata ga auntyn taba gashi tana kunyar su ummey, gabaki d’aya yau ita kadai ta yini sai zoya da tazo mata itama ma bata dade ba ta tafi saboda islamiyya,hatta abincin da zataci daga part din mahma aka kawo mata wacce ta ka famata sharadin ko wajan part din karta kuma zuwa , kwata kwata batasan abunda yake faruwa ba acikin gidan.

➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰

A part din dada Kuwa su ummey ne zaune cikin falon mahma, inda aka fito da wasu designers din akwatuna masu shegen kyau set uku,suna tattauna yanda za’ai wa tahee Jeren kayanta, bude kofar toilet din da akwai ne yasa mahma dakatar da maganar ta, a matukar firgice na zaro idanuwana , sanye take cikin doguwar abaya black colour , kwantaccen gashin kanta ya kwanta rup agefen fuskanta , ba kowa bace face matar da ta temakawa taheer ,har ta kaishi asibiti, murmushi ta zakarwa mahma ,cikin yaran larabci ta furta “dadi na dake mahma akwai saurin lissafi , Kalli su yaya ko wannen su ya tsaya kallanki “ ta karasa zancan nata tana zauna wa kan kujera , gabaki dayan su dariya suka saki ammey ce ta bata amsa “ shi yasa naga ai kina zuwa ko hutawa bakiyi ba kika dora ke da mahma bansan wann yafi zumudi ba”,dan girgiza kai matar tayi” Wlh yaya gashi ko amaryar tamu ban gani ba , yanxu so nake komai ya daidai ta “, tana kai karshen maganarta wayarta ta soma ringing , daga jikin wayar taga don ya bayyana , dan murmushi ta saki tare da daukar wayar tana barin wajan, su ummeey ma cigaba da tattauna wa sukayi ci gaba dayi.

 

9:30daidai mahma da kanta tazo ta dauki tahee ta kai ta saban part din da bashi da tazara sosai ,sai alokacin ta hadu da kanwar ummey da suke cewa small mom,sosai hajiya fatima ta yaba da hankalin tahee , tunda ta koma part din yarta take santin halin ta , duk da tace bazata zauna a gidan ba ,wani gida da ban zata zauna ,dagyar aka samu aka shawo kan small mom din dan har sai da dada ta saka baki a ciki.

Wani babban daki dake upstairs aka nufa da tahee, suna shiga amzy ta miko mata wasu sababbin kaya marasa nauyi ta saka , karban kayan kuwa tayi ta saka , bakomai a cikin dakin sai babban gado da wasu abubuwan gyaran jiki da aka harhada, ba bata lokaci amzy da yaranta guda uku suka fara aikinsu cikin kware wa, wani ruwa ne babba aka sa tahee tashiga me shegen kamshi, da ya kare za a dakko wani , gabaki d’aya part din ya daure da kamshi me shegen daki duk da kasancewar ba yanxu su ihsan zasu dawo part din ba sai nan da kwana uku,sosai su amzy suka gyara fatar tahee da ita kanta sai dataji canji a cikinta, basu suka kyaletaba sai wajan karfe 2 na dare bayan sun kunna wani burner me shegen kamshi da dadin gaske . Ita dai tahee binsu kawai take da kallo ganin komai da suke cikin kwarewa, sosai gyaran ya burgeta amma kuma tana tausayinsu kasancewar tasan wanda ake yiwan ma ba santa yake ba ,tuno da hakan yasa ta fashewa da kuka sai da ta sha kukan ta dan kanta kafun bacci ya dauke ta.

Washe gari ma bayan sallahr asuba su amzy basu zauna ba , wani gyara na musamman aka somayiwa tahee da ya banbanta da na jiya, tun abun na burgeta har ya fara bata takaici musamman towel din dake sata sawa shi kadai, har yamma kuma babu Wanda ta gani cikin family din sai abinci da ake aiko musu dashi, karfe 8 na dare mahma da small mom suka shigo dakin, ko wannansu sai yaga kyan da tayi yake yi ,gyaran da akayi a kwana daya mutum sai ya dauka wata biyu akai ana yi musamman duk yanda ka matso kusa da ita zakaji kamshi na ta shi ajikinta, hatta bakinta wani daddadan kamshin mint ne ke tashi, basu dade da zuwa ba suka tafi, bayan mahma ta bada umarnin kar abar kowa ya shigo dakin har sai lokacin da aka gama gyaran jikin, a tunaninta ammey ma zata zo sai taga sabanin hakan, harta kwanta bacci bata sanya ammeyn a idanuwanta ba .

Arana ta biyu ma haka su amzy suka canza saban style din gyaran jikin,gawasu abubuwa da ake bata tana sha , hatta abinci ta dena ci sai fruit din da take sha kullum , da kayan da ake bata , sai wata kaza da kullum sai ta cita ,tana ci tana kuka haka suke sata cinye wa dole , yanxu ma su mahma da small mom ne kadai suka shigo part din, banda tubarkalla Masha Allah babu abunda bakinsu yake furtawa, suma yanxu ko munti goma basu yi ba sukabar part din, dan takaici har kuka tahee tayi , a haka bacci ya dauke ta.

Arana ta ukun ma hakance ta faru kwata kwata basa bari ko kofar dakin ta nufa balanta ma tace zata dauki wani abun , ko me take so shi ake mata, cikin dan kankanin lokaci jikinta kuwa ya dumurmure sosai har wani santsi yake yi, suna cikin aikinsu suka fara jin hayaniya na tun karosu, kulle dakin da tahee take amzy tayi tare da nufarsu, ko wanne daki tasa aka bashi inda za a dunga musu gyaran jikin suma , duk yanda suka so ganin amarya abun yaci tura an hanasu hatta sumayya daukin ganin yanda tahee zata dawo take kawai a ranta. Duk yanda tahee taso abarsu su shiga an hanata ganin kowa , yau kwanan ta uku raban ta dashi ,sosai take kuka cikin dare ganin kullum soyayyar sa kara shiga cikin zuciyarta take .

**** Akwana a tashi ba wuya wajan Allah SWT yau ta kama kwana biyar kenan ana yiwa tahee gyaran jiki , bayan kyaran jikin da take mata kuwa kunya ta cire sosai take koyawa tahee dabarun aure da yanda zata shawo kan mijinta, cikin kwana kinnan ta koya mata abubuwa da dama hatta tafiya sai da ta nunawa tahee kala kala , wasu abun ma kunya suke bata da amzy ta fada zata sunkuyar da kanta kasa,har yau kuma bata kara saka kowa na cikin gidan a ido ba sai yar hirarsu da take ji lokaci zuwa lokaci, suma sosai aka gyara su sai faman santin kyan da sukai sukeyi,ita de amzy sai faman dariya take musu musamman tunawa da kankat din da tayi, idan suka ganta sukuma wani irin santi zasuyi.

Duk da amrah da basma sunsan abunda ke faruwa ,babu Wanda ya tako yazo inda ake gyaran, amrah na kwance tunda mutumin da yazo mata yaji mata rauni take jinya dan bakaramun rauni yaji mata ba ,kuma ta hana kowa sanin halin da take ciki sai Aunty da taji dadin abinda ya samu amrah. Kamar daga sama sai ga basma itama ta shigo cikin kananan kayanta da karamun trolley dinta,hakan da tayi sosai ya bawa kowa mamaki musamman yanda tasaka itama a gyara mata jikin nata.

Washe gari kunshi akayiwa gabaki d’aya mutanan gidan har dada ba a bari a baya ba, kowa da kowa part din ya shigo, hatta su aunty duk kowa yazo banda basma da tayi karyar bata san kunshi .dadace kai batazo part din ba aka je har nata part din akai mata, duk da hakan kuma an hana kowa ganin amarya, a ranar akayi mata kunshi ja da baki da ya kara fito da kyaun siraran yan yatsunta, kunshi sai ya fito tar dashi kamar daurashi akai ,da yamma kuma akai mata gyaran kai,suma ata ban garan mutanan gidan kowa anmishi gyaran kan, ana kammala wa kuwa aka umarce kowa da ya koma part dinsa, saida aka tabbatar da bakowa ne sannan mahma da small mom suka nufi dakin da tahee take,suna shiga ko wannansu ya tsaya ,tsabar mamaki ko kwakkwaran motsi sun kasa sai bin tahee suke da kallo da amzy tasa tashirya cikin wani hadaddan lace kamar yaune Auran, iya kyau ta tahee tayi kyau,ko makiyi ya ganta sai ya yaba kyan da tayi, kwata kwata kasa magana sukai sai hannunta da mahma ta kama soka fito falo inda su ummey suke, suma sosai yaka da irin kyaun da tahee,kunyace ta kama tahee ko kwakkwaran motsi ta kasa balantana dagowa ta kallesu sai hannunta da take faman wasa dashi.
Kafun goma gabaki dayan su kowa ya nufi part dinsa yayi saura daga mahma sai tahee , Zaunar da ita mahma tayi ,sosai tayi mata nasiha kamar yar cikinta ba abunda tahee take sai kuka ,karfe 12 tasa a kazo dau karsu kai tsaye part dinta aka nufa da ita batare da ta bari kowa ya gansu duk da kasancewar ba taro za’ayi ba kamar yanda abeey ya sake jaddada mata babu taran da za’ayi gobe za’a kai yarinya dakinta, duk da mahma tanbayeshi amma yace mata haka mijinta yace , jin hakan yasata kira wayar king amma kwata kwata ba yashiga ,kusan kwanaki biyar kenan ynxu bata sa shi a cikin idanuwanta ba , bama itama hatta mutanan gidan babu Wanda ya gansa, suna shiga part din dada wani daki ta nuna wa tahee akan taje tayi wanka ta Hutu , kamar tasan abunda take bukata kenan, duk da haduwar da dakin yayi hakan be sa ta tsaya kallan dakin ba sai ma toilet da ta nufa ,ta dade sosai a ciki kafun ta fito jikinta da white rub,kome ta taba kamshi yake tashi musamman dakin da ya cika da wani irin sanyi kamshi me cika zuciyar masoya, kwata kwata bata kallanta gabanta bayan. Tafi to daga toilet din, burin ta kawai ta kwanta ,Daidai tazo saitin gadon sai abu ya dan bigi takalmin kafar ta ,tayi baya zata fadi, hannu daya yasa ya janyota jikinsa suna fadawa saman gado ita a kansa……

 

💖💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖💖

 

Mss LEE 💖💖
💖💖GIDAN AUNTY 💖💖
( a heart touching love story)

Story & written
By
Mss Lee 💖

💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖

Wannan page din nakune MAMAN SUDAIS,UMMUN SAEED, ISARATU917 .

PAID BOOK

MAI BUKATAR COMPLETE DIN GIDAN AUNTY YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 07041879581

Leave a Reply

Back to top button