Hausa NovelsMatan Ko Mazan Book 1

Matan Ko Mazan Book 1 Page 40

Sponsored Links

EPISODE 4️⃣0️⃣

Kina neman class na matan aure da akeyi da turenci??? To look no more ga MAJAL WELLNESS nakawo muku💃
Indai class ne da ake tafarfasa karatu kan harkan abenga da turenci trust me bazaki taba samin a class better than SAMOHHACK by Majal ba so hurry and join her waitlist group ko kiyi chatting nata up now now now!!!

wa.me/+2349043619538
Check out her IG page @majalwellness💃

You will come thank me later oo💃

https://chat.whatsapp.com/H50w7C7Lrbv8ZiPKzKxm5l

Ijiyan zuciya yasauke bayan yagama magana da Hadiza kafin ahankali yayi dialing number Hajiya ringing daya ta dauka kaman daman wayan na hannunta tana jiran kiranshi ne tana dauka tace “Nura ya jikin ka sanar da ita yakukayi?” Dan shiru Nura yayi kafin ahankali yace “Hajiya Ummi Ummi……” saikuma yayi shiru, ahankali Hajiya tace “talk to me Nura, meya sami Ummi? Metace”? Cikin very breaking voice yace “she begged me to do 2 things for her wai tanaji ajikinta mut……” “ba abinda zai sameta!” Hajiya tafadi cikeda damuwa, Nura yace “tace nadawo da Maman su Aman, sanan nakira mata Gwaggon ta da kanninta” dan shiru Hajiya tayi sai chan tace “Nura Allah kyautan Ummi kawai yadauka yabaka, nadade banga mace irin ta ba! Zuciyarta Alkhairi ne cike acikinta kuma da izinin Allah bazata mutu ba, Nura idan namiji yaşamı mata tagari sai ya kasance miji nagari agareta ance kyawun tukuici godiya hope ka kira Mahaifin Hadiza ka sanarda shi” gyadama Hajiya kai yayi kaman tana gabanshi yace “nakira amman banda wanda zai wakilceni Hajiya” Dasauri Hajiya tace “zan tura Murtala da Shamsu” ahankali yace “thank you Hajiya” ahankali Hajiya tace “thank you for honoring maganan Ummi, I feel very proud of you ina matukar alfahari dakai Nura, Ummi zata samu lpy kuma dukanku zakuyi zaman lafiya kaji, gobe muma ina ganin zamu shigo, yanzu wazaka tura yaje yadauko maka su Gwaggo a kauye” ahankali yace “yanzu zan kira Alhaji Musa” Hajiya tace “to shikenan” sukai sallama yashiga kiran Alhaji Musa cikin 30min aka daura auren HADIZA da NURA akan Sadaki 200k bata dauko komi ba banda handbag dinta wani lafiyayyen ubansun abaya tasaka su Baba suka mata fada da wa’azi Baba yakaita airport tahau jirgi sai Abuja tana kaina taga manager Nura yazo daukanta sai murmushi take school na yaran tawuce tadaukosu suka wuce sabon gida dan nan Nura yace tazo gateman yabude mata side nata tashiga ga set na akwati sababbi guda 6 afalo aksatın dayay order since bayan auren Ummi ne dan baisamu yamusu akwati ba, yaran tagama attending to them ta shiga kitchen da kanta dan musu girki da wanda zatakai asibiti.
Dakin Nura yakoma bayan yayi sallan azahar a mosque samin Ummi yayi tana bacci, yana zuwa yakama hannunta dasauri tabude idanunta takalleshi murmushi yamata yace “natasheki?” Girgizamai kai tayi daidai wata Nurse tashigo tawuce wajen ledodin asibitin da Nura yakawo tana ciro ledan pampers tace “Yallabai can u excuse us zan shiryata ne?” Kallon Pampers din da rigan asibitin Nura yayi ahankali yatashi tareda mika mata hannu yace “bani zan shiryata dakaina” kallon Nura nurse din tayi saikuma tabashi ahankali tace “bari nabaku wuri” wucewa tayi tafice yaje wajen kofan yarufe tareda murza key yadawo gaban gadon ya kalli Ummi daketa binshi da idanu yace “na shirya ki?” Gyadamai kai tayi ahankali tana kallonshi tsayawa yayi shiru yana. Kallon fuskanta kaman yanda take kallonshi kafin ahankali yace “I love you Zainab” sake lumshemai idanu tayi tabudesu ahankali wani boturi ya danna agadon, gadon yataso kaman kujera hannunta yakama yasa tabayanshi ya kwantar da kirjinta ahankali nashi yasa zip gently yabude rigan hannunshi yakai yayi unhooking brlack bra dake bayanta ya maidata jikin gadon tareda zame rigan daga hannunta ahankali ya zame bra dinma ijiyan zuciya yasauke yasake danna botur din ya kwantar da gadon kafin gently with so much care kaman zai daga kwai yakama jikinta ya juyarda ita side, Ummi jitayi hawaye yazo mata ganin yanda ake mata komi kaman gawa, zip din skirt dinta yaja kasa sannan yazo takama yazame skirt din yana kallon black pant din dake jikinta dan ijiyan zuciya yasauke ahankali ya kwabe mata, sannan yadauki pampers din yakalla kafin ya kalleta hawaye yaga sun zubo daga idanunta dasauri ya daure shi asanyaye ya sakamata yadauki gown din yasamata shima yana kallon yanda hawaye ke fita daga idanunta sanan ahankali yazo kusada ita kawai ya rungumeta kaman jira take fashewa tayi da kuka sosai a kirjinshi yanajin yanda hawayenta ke jikamai gaban riga murya chan kasa yace “it’s okay, ya isa am here for you kinji, babu abinda zai sameki is okay” bayanta ya bubbuga yana shafawa ahaka akı knocking dakin maidata yayi ya kwantar ya kwashe kayanta ya linke tsaf yasa a wardrobe na dakin sannan yawuce kofan yabude Doctors guda uku ne da nurses hudu suka shigo akasa Nura yafita.

Yana zaune awajen wayanshi yahau ringing number Hadiza ne hakan yasa yadauki wayan cikeda so tace “gani a asibitin Nura nakawo muku abinci kana ta ina” ahankali ya mike daga inda yake zaune yace “ina zuwa” katse wayan yayi yana tafiya ahankaali yafito daga ta wajajen parking space ya hango Hadiza tayi parking wani motarshi datazo dashi tafito rikeda basket a hannunta tana waige waige yadade yana kallonta kafin yakarasa saida yakawo ta wajajen taganshi hada idanu sukayi for the first time in her life saitaji tana wani jin kunyanshi da nauyinshi tuna abubuwan datamai hakan yasa takasa motsi sai kallonshi datake wani kalan wutan sonshi na tashi azuciyanta, anatse Nura yakarasa gabanta ya tsaya chak yana kallonta kasa daurewa kallon tayi da sauri tasauke kanta kasa ahankali tace “ina yini Nuri, yamai jiki?” Kara one step Nura yayi kafin ahankali yawani kalan bata warm hug Hadiza jitayi jikinta yasaki gabaki daya she missed her Man, she missed his body this thight hug just gave her the comfort data dade bataji kalanshi ba almost 30secs yayi ahaka da ita kafin cikin wani cool calm voice yace “welcome Didi, how was your flight”? Ahankali tace “smooth ya jikin Ummi?” Gyadamata kanshi yayi tareda dauke ijiyan zuciya ahankali yace “Alhamdulillah, let’s go” yasaketa tareda sa hannunshi daya ya karbi basket din dake hannunta yasa dayan hannunshi yakama hannunta suka wuce ciki ahaka bini bini take kallonshi yanzu take kara ganin abinda tayi loosing Nura is a man dazai kula da matarshi ba ruwanshi look at yanda ya karbi basket din daga hannunta to da dataketa kukan feminism mema exactly take nema dan Nura always treat her like a queen, gaban dakin sukaje daidai zai bude kofan ta karbe hannunta daya rike dasauri dan yanzu she’s a change person tasan Nura nasonta no need to show Ummi ko the world yana sonta banda hai bazataso ta sama mara lafiya bakin ciki ba koyaya badadi kaga mijinka na lovi dovi da kishiyahka tasan zafin hakan sama da kowa dan juyowa yayi ya kalleta him ta karbe hannunta kafin ahankali yabude kofan dakin ya shiga ciki Ummi ce kadai adakin su Dr basu dade da fita ba an samata drip guda biyu a manna mata wasu abubuwa haka akafan da massage sukeyi tsotse hakan sukayi oho bata saniba dan batajin komi ganin Hadiza yasa tasauke ijiyan zuciya ahankali Nura yazo gadon da sauri yaduko da kanshi saitin nata kaman zai hadiyeta yace “ya jikin wani abu namiki ciwo?” Girgizamai kai tayi alamun a’a, ahankali yace “Dr yamiki allura”? Sake girgizamai kai tayi yace “ga abinci Hadiza ta dafa miki zakici” gyadamai kai tayi ahankali takalli Hadiza data tsayavtana kallonsu ahankali Ummi tace “An……ty” matsawa Nura yayi hakan yasa Hadiza ta tako tazo gaban gadon taja kujera tazauna tana kallonta cikeda kulawa dakuma mutuntawa tace “yajiki Ummi sannu Allah baki lpy Allah kara sauki”.
Ahankali Ummi tace “Anty har yanzu kina fushi dani?” Dasauri Hadiza ta girgiza mata kai tace “no banayi Ummi” har ranta kuma batayin dan Ummin tabata tausayi hannunta Ummi takama tarike tace “kiyafemin idan nataba batamiki rai please” dasauri Hadiza tace “nayafe miki nima kiyafemin all abubuwan dana miki Ummi kinji” gyadamata kai Ummi tayi tace “Nayafe daidai lokacin Nura yakawo plate na rice din da stew daga gadon yayi kaman dazu yazauna akatifa gefen Ummi yace “bude baki kici haaaaaam” ahankali Ummi tabude baki yasa mata tadanci like 4spoons tace ya isheta juice din tasha sosai ahaka azaunen Nura na gefenta rikeda plate wayanshi yahau ringin yadauka ganin Alhaji Musa ne that means yasauka a Adamawa jin saukan kan Ummi a shoulder shi yasa yakalleta ganin tayi bacci yasa yamikama Hadiza plate din yasauka yana magana da Alhaji Musa ya kwantar da gadon yarufa mata bargo da kyau yagama wayan abakin gadon yazauna yakalli Hadiza sai kawai yaja mata hancı dan murmushi tayi tace “bari nakoma gida yaran nan su kadai nabari” Gyadamata Kai yayi yace “muje narakaki” har mota yarakata takoma gida, babu wani available flight daga yola to Abuja dole sai gobe zasu zo.
Shiya kwana da Ummi shiya sake chanza mata pampers bayan ya tsaftace mata jiki yamata alwala tayi salla anan kwance agadon suka kwana tana jikinshi.

Cikin dare firgitan dayaji tayi ya farkan dashi bude idanunshi yayi yakalleta idanunta a lumshe but jikinta yayi zafi kaman wuta lips dinta sun bushe kaman basu taba ganin ruwa ba daidai lokacin Nurses sukazo dubata arude Nura yace “kudubata pls” tamper türe ta kadai suka duba akace akira Dr, Dr nazuwa sai akahau cema Nura yafita daga dakin arude Nura yace “what happen” fitar dashi Dr yayi yace “I will explain anjima” yakoma dakin da sauri Nura rasa inda zai sa kanshi yayi chan saiga Dr yafito Nura yabi shi dagudu zuwa office dinshi Dr yace “Nura condition din wife naka yakai hannayenta” baya Nura yayi zai fadi yadafa banyo da sauri yana nishi da karfe yana addu’a Dr yace “but we are trying our best Kari damu, jeka ganta” da kyar Nura ya iya daga kafanshi yafice daga office din yatafi dakin yana kallon Ummi idanunta a lumshe ga hannayen kaman sanda ajiye gefenta juyawa yayi dasauri ya kalli kofa yadaura hannunshi kan bakinshi saikuma yajuyo yazo gaban gadon tazuba tagumi yana kallonta kaman ciwon yadawo jikinshi yakeji, kaman ba Ummi daya tafi office ya barta lafiya agidaba kaman tai ciwon shekara wannan wani irin paralyze ne Innalillahi har gari yawaye baccin dabaiyi ba kenan yatafi mosque bayan yakira Hajiya itama tace “gatanan zuwa garin”.
Wuraren 6:30 yadawo dakin idanunta biyu amman sun kankance looking so weak Allah kadai yasan meke mata ciwo, yunkurin amai takeyi anan kwance da güdü yayi gaban gadon dan bata iya daga hannu ko kafa kaman jaririya dagota yayi yadauki Rohan amai na hospital yatara tadingayi anan she’s so weak kaman paper yadanna bell nurses sukazo suka tayashi tai aman tagama aka bata ruwa da kyar ta iya bude bakinta tace “Gwag…….g……” hannunta Nura yakama gam yace “tana hanya kinji” lumshe idanu tayi ta bude alamun to.
Wuraren 8 Hadiza tashigo hospital din takawo musu abinci takwoma Nura another set na cloth itama yanda taga Ummi saida taji kuka yazomata Nura yahanata yi karşı tada mata da hankali around 10 na safe Alhaji Musa yashigo asibitin dasu Gwaggo dasauri Nura yabar Hadiza da ita dan zuwa shigowa dasu.
Gwaggo na sanye da atampa mai kyau an mata dinki Bubu da Zani dawani dan Madinan silipas akafanta ta yafa farın lullubi aka, same with su Shatu suma irin atampan Gwaggo ne ajikinsu sai lalle lalle suke a tsakar hospital din Gwaggo na hango Nura kafinma yakaraso ita tafara tafita dasauri gabaki daya hankali ta tashe tana kaiwa dan dashi tace “ina jikana?” Ajiyan zuciya Nura yasauke yace “tana ciki Gwaggo sannu da zuwa” gyadamai kai Gwaggo tayi ta wuce Nuran tayi inda taga yafito kaman tasan dakin bata damu da yanda ake kallonsu ba dasauri Nura yabiyo bayanta shikuma Alhaji Musa yakalli Shatu da Zakiyya yace “ku muje masu kuka a jirgi” binshi sukayi, suna zuwa ciki Nura yabude kofan dakin Gwaggo tafada ciki kaman an jefata tashi Hadiza tayi daga kan kujera tana kallon tsohuwan tace “sannu da zuwa Gwaggo” jin an ambaci yasa Ummi tabude idanunta kadan tajuyo Gwaggonta tagani tsaye gaban kofa ta dafa bango tana kallonta ga Nura a gefenta gasu Shatu abayanta, kokarin daga hannayenta take tamikama Gwaggo takasa gwanin ban tausayi hakan yasa Gwaggo ta daga kafa tafara tafiya ahankali har zuwa gaban gadon sai kawai ta tallbo fuskan Ummi cikeda so ta goge mata fuskanta tasss tace “dena kuka Gwaggon ki tazo ko yanzu” ta dago kanta takalli Nura da Alhaji Musa tace “kuzo ku dauketa ku kaimin ita mota mukoma kauye na nema mata magani” dasauri Nura yataho wajen hakama Alhaji Musa anatse Nura yace “Gwaggo nan asibiti ne bakigama Karin ruwa ake mata ba ki barta anan Gwaggo” cikeda masifa tace “kai kaga jikin jikana ne, yooo asibiti da alluran nan nasu kara mata karfin ciwo zasuji, dauji ne ciwon nan muna zuwa kauye dakaina zan shiga daji na samo mata sassake assake na magungunan na jika dana sha dana shafawa kafin kace mene zata warke” cikeda lallabawa Alhaji Musa yace “Gwaggo to shikenan ki bari agama na nan saiki tafi da ita kauyen” fashewa da kuka Gwaggo tayi Tana nuna Ummi dake kallonta da kyar tace “yarinyar nan haka ciki ke wahalar da ita, kubani ita natafi da ita kauye nasama mata magana iyye, Shatu keda Zakkiya kuzo ku cicciba mini ita abaya na goyata mutafi tasha ai Alhamdulillah nayo guzurin kudina, kuzo ku cicciba mini ita abaya” zasu fara tahowa da sauri Hadiza tasa baki hannun Gwaggo takama cikeda lallashi tana magana ahankali kaman mai whispering but zaka iyaji tace “Gwaggo kiyakuri kinga kukanki zai kara tadama Ummi hankali hakan baida kyau agareta, yanzu kiyakuri tadanji sauki koda kadan ne saiki tafi da ita, yanzu kinga ayanda take zaman mota kona jirgi zai mata wuya ko Nuri” dasauri Nura shima cikeda lallashi yace “eh Gwaggo kiyakuri kinji, yanzu kiyi magana da ita tun jiya ketaketa nema” juyawa Gwaggo tayi takalli Ummi tana kuka sosai Hadiza tasaki hannunta, bayan riganta tasa ta share idanunta tass sannan tazo gaban gadon ta duka ta shafa fuskan Ummi cikeda so tace “gani nan nazo, Gwaggon ki na nan dake Ummi zakiji sauki kinji, me kikeso ciki gayamini nizan miki dakaina” tai maganan tanakai kunnenta saitin bakin Ummi, ahankali Ummi tace “Gassashen dankalin hausa amurza kulikuli akai” dasauri Gwaggo tadago takalli su Shatu daduk ke tsaye tace “buhun tsaraban damukazo dashi nasa dankalin hausa? Kaina yayi chaji na manta nasaka Shatu”? Whispering Alhaji Musa yama Nura akunne yace “kai kaga zabgegen buhun tsarabane saida nabiya extra luggage fee a airport” dasauri Zakiyya tace “eh akwai” dasauri Gwaggo ta zame lullubin dake kanta taci dammara dashi aciki takalli Alhaji Musa tace “Zakiyya ta bika kabude buhun, ke Shatu samomin manyan duwatsu da makamashi na gasa mata dan kali” takalli Hadiza tace “zan sami mai” Nura dafe kanshi yayi Hadiza ma tsoron rigiman tsohuwan yahanata magana Alhaji Musa ne cikin dabata yace “Gwaggo nan asibiti ne” “yo masallaci ne dabazan iya hada makamashi ba naga ba girki zanyi ba gasa dankali zanyi” gefen Gwaggo Nura yabi yazo gaban gadon yakalli Ummi kaman yar babyn shi yace “dankali zakici gashashe?” Gyadamai kai tayi Gwaggo tace “da murjajjen kulkuli da man gyada” kallon Gwaggo yayi yace “Gwaggo saidai aje gida ayi baza’a bari ayi anan ba” dasauri tace “kaga nabar dakin nan jikata tabar shi ne su Shatu dai akaisu gidan suyi” dasauri Alhaji Musa yace “kuzo duk muje gidan sai Gwaggon tazauna” cikin turenci Nura yace “someone needs to stay what if Doctors needs anything” ahankali Hadiza tace “kaje kai inyaso saikai wanka i will stay with them” Gyadamata Kai yayi ahankali yace “thank you” shima murmushi Alhaji Musa yayı ganin changes from Hadiza, sake dukawa yayi ya shafa fuskan Ummi yace “bari muje gida okay” Gyadamai kai tayi takalli kannanta da ido hakan yasa Nura yace “Shatu kuzo” Kaman jira suke dasauri sukazo gaban gadon rungume Ummi sukayi duka sai kuka Gwaggo tace “mehaka kuka nace kuzo kuyi?” Wannan karan kowa na dakin saida yayi dariya har Nura saida ya murmusa wacce tagama kukanta yanzun nan ne take Hana wasu tashi sukayi duk suka tafi Alhaji Musa yatukasu har zuwa gidansu dasukakai gidan baki suka büfe suna kallo har flat na Ummi yakaisu gateman ya shigo da tsaraban shidai yabasu grill nashi da charcoal aciki a bayan gida shida Alhaji Musa suka fito da kayanshi da Hadiza takawomai asibiti flat nata yawuce yabude kanshi ko ina tsaf tsaf yatafi sama kaman ba gidan Hadiza ba wanka yayi ya shirya ya sauko shida Alhaji Musa sukaci abincin dake nan dinning a warmer yaşandı ba laifi sannan yatafi duba su Shatu abubku da charcoal harya gama gasawa Shatu ta daka kuli tasa maggi da dan yaji Nura yabasu kul da kanshi suka zuba yakawo musu abinci daga side din Hadiza da drinks tass sukacinye sannan yadaukesu Alhaji Musa yawuce dasu asibiti shikuma yadauki wani mota dan zuwa dauko Hajiya da Meena a airport.💫MATAN?? Ko MAZAN??💫

✍🏻M SHAKUR

Back to top button