Hausa NovelsMatar Makaho Hausa Novel

Matar Makaho 78-79

Sponsored Links

Page7⃣8⃣&7⃣9⃣

“Zamu bar garin”

A matukar Mamaki khadija tace, barin gari kuma Aunty?

“Eh khadija barin garin zamuyi don wallahi baxan iyya xama a gidan muba, yanzun kwata-kwata naji bana kaunar gidan, da zama a cikinsa, kinga yanzun ma tashi ki tafi wajen shagari kice masa karya rufe shago, bayan isha’i muna zuwa akwai maganar da zanyi dashi, kibi gidan goggo ki d’auko abubuwan ki masu Amfani harda takardun ki, kiyi sauri kizo mu shirga kaya”

Aunty ban gane ba?wani irin abune haka ni gaskiya nama hakuri, ki koma gidan naku Allah ya dawo da yaya lafiya, yanzun in muka tafi yaya ya dawo bamu nan ba?

Cikin jin haushi sumayya tace”sai dai ke ki zauna, koh zaki bini koh bazaki bini ba zaman garin nan bazan yisa ba kinji na fad’a miki”

Shuru khadija tayi tana nazarin sumayya koh dai bata da lafiya ne? ace mutum lokaci d’aya ya birkice haka, Amma dai batayi magana ba tasa hijab nata zata fita.

“Khadija”

Na’am aunty.

“Ban saki ki sanar da kowa maganar nan ba, koh goggo ban yarda ta sani ba, inta tambaye ki me zakiyi da abinda kika d’auko kice mata nina ce ki d’auko kayayakin ki, na nan yayi datti”

Toh aunty kawai khadija tace ta fita.

Bayan fitar khadija, akwatuna sumayya ta saukar, tana shirga kayan ta kama daga na sawa harna amfani, daman har yanzun akwai wa’inda bata dinka ba, hotonan su data lika a bango duk ta cire ta saka a akwati,da system inta, sauran kaya daya rage ta barsu a wardrop, kayan muhammad ne kawai bata taba ba, kome nata ta d’an tattara harda make-up ket nata, saida ta cika akwatuna hudu da kit da kaya, ta barwa khadija akwati d’aya tasa kayanta a ciki.

Khadija na dawowa ta sata had’a kayanta a akwati d’aya, da dare ita da khadija suka shiga keke-napep da akwatunan kaya, ba tare da y’an unguwan su luraba shagon shagari ta kai ta ajeye, shikaran kansa yayi mamakin kuma ya tambaye ba’asi, amma sumayya tace ya bari gobe zata masa bayani yanzun dai karya sanar da kowa, gobe da asuba ya bude shago tana zuwa.

Ba musu ya aje mata kayan, bayan sun koma gida waya sumayya ta d’auka ta kira principal nasu khadija, ta masa bayanin tafiyan gaggawa ya same su, suna bukatan transfer letter na khadija, ba musu yace gobe da safe tazo school ta karba.

Karfe uku na asuba sumayya ta tashi, tafasa ruwan zafi tayi, tayi wanka tasa khadija wankan asuba suka shirya cikin hijabai manya da socks, saboda yanayin garin, zanin gadonta guda uku dake d’akin ta dauko ta lulube gado ta da d’aya, d’ayan kuma kujera ta lulubawa, d’ayan kuma wardrop, zaninta babba ta lulube TV dashi.

Dayake sunyi Alwala sallah kawai sukayi taja kofar d’akin ta rufe da kwado, key ta aje a inda Al’ameen yake ajewa in basanan, fita sukayi ita da khadija kam sai binta take, ba halin magana babu kome a hannun sumayya sai purse nata, wanda waya da ATM ke ciki sai y’an changen da baza’a rasa ba, shagon shagari suka wuce kamar yanda sukayi Alkawari, haka take don shagari ya bude musu shagon, tattara akwatunan sumayya take don burinta kar gari ya waye tana sintali bata fita ba.

Aunty sumayya wai don Allah meke faruwa ne?

“Shagari zamu bar gari ne da khadija”

Barin gari kuma Aunty, wani abin aka miki?

“Ba kome shagari gida akeson na koma ni kuma yanzun bana kaunar komawa gida”

Toh yanzun wani gari zaku tafi, gashi jiya na saro kaya, kwata-kwata dubu 100k ne a hannu na bara na d’auko muku?

“Tsaya shagari daman Wannan kudi bana muhammad bane na Ammar ne, don haka kaci gaba da kasuwancin ka kamar da, duk ranan da Ammar ya nemi kudinsa saika basa, uwar kudin kuma saika kama kasuwa dashi nasan zuwa yanzun ka kusa ninka kudin biyu, abinda nake so dakai shine in muka tafi kayi Register n jamb in lokaci yayi, ka koma makaranta, har ka kammala da kudin da kake nema, tunda mai shagon baya nan babu Amfanin kana ta tara Arziki bakaci,kayi Amfani dashi Allah yasama kasuwar Albarka.

Ameen Aunty nagode Allah ya bayyana oga, amma don Allah ki karbi kudin aunty sumayya karki ce ah ah.

Ganin ya nace yasa sumayya karban 50k tabar masa sauran don yaro tausayi yake bata.

in babu damuwa ki bani number ki duk lokacin da akaji labarin oga saina kiraki, yace yana kallon khadija dake rabe a gefe tana hawaye haka kawai yau take jin wani irin kewar sintali, yanzun tafiya zatayi tabar sintali harda garin gabaki d’aya.

“Gashi ” sumayya ta mika masa wayar sa daya bata tasa masa layin ta,shiya tare musu keke-napep da asuban nan ya loda musu kayansu, akwati shida rus a ciki mai keke yaja machine insa, a hankali khadija ta leko kanta tana d’agawa shagari hannu wanda hawaye ya cika masa ido, don shi harga Allah son khadija yake kawai kunyar fad’a mata yakeji ganin kankantar shekarun sa, dayasan irin wannan rana zaizo dako ba kome tasan da sonta a ransa, koh ina taje tasan tana ransa.

Bayan su sumayya sun tafi road block da asuban nan, tama rasa wani gari zatace zata kuma gashi tana son barin khadija taje ta karbo mata transfer letter nata, na makaranta maganar karatunta karya koma baya, aje khadija tayi a gefen tashar ta kama hanyar science, ba ita ta samu ganin principal ba sai kusan 7:30, ya kaita wajen exam officer daker dai ta samu transfer letter in, tasha ta koma amma zuwa lokacin duk mototi sun tashi sai kalilan suka rage, wajen da khadija take ta nufa, har lokacin tana zaune da tulin akwatunan su a gaba, abin duniya ya dame ta.

“Kee khadija tashi ga mota shan naga ya kusa cika muje muji na wani garine”

Mikewa khadija tayi, aunty kin samu lettern ne?

“Eh na samu khadija daker baki ga har gari ya waye mini ba”?

Gaskiya ne muje toh aunty .

Wajen motar suka nufa suka tambaye ta wace gari ne, akace musu motar Abuja ne saura mutum uku, babu wani shamaki sumayya suka shiga, dayake motar babban mota ne ba karami ba, akwai space, Alelen akwa sumayya ta sai musu na 200, da gyada na 100, ta had’a musu da goran faro biyu, sai masa na 150, suka shiga dashi motar, suna shiga koh, aka samu mutum d’aya ya shigo aka tada mota, lumshe ido khadija tayi hankalin ta a tashe yau za’a bar gari.

Sumayya kam koh a jikinta, sai cin Alelen ta take tana had’awa da ruwa, koh a jikinta bata san inda zasu ba, bata da wanda ta sani a Abuja Amma koh a kwalar riganta.

Haka khadija da sumayya suka wuni a mota, don an sauke su sun sake shiga wani, khadija ta kasa cin kome, amma banda sumayya kome ta gani in an saya a hanya, saya take taci abinta, har mangari ba suka isa Abuja aka sauke su a tasha saboda yanayin tafiyar su .

Sumayya gabaki d’aya tayi laushi likis don ita ma ba wani tafiye tafiye take a mota ba, sai yanzun takejin gajiya ga karamin ciki, tama rasa ina zasu nufa gabaki d’aya gashi mangariba yayi, a gefen tasha ta samu suka zauna ga kayansu a gabansu tirim, gabaki d’aya ta galabaita a zaune suke har isha’i suna tasha, a zaune tama rasa wazata tambaya inda zasu samu wajen kwana, banda hotel.

Kamar daga sama taga wata ta dafa mata kafad’a da sauri da d’ago”laaa laila kece”?sumayya tace cikin mamaki.

Oh duniya nifa tun mangari ba danazo tashan nan, nake ta kallon kamar kece kamar bake ba, sumayya naga kinyi jiki gaki a tasha nasan kuma kinfi karfin tasha, wallahi har zan tafi daga baya kawai na fasa nace bara dai na sake tabbatar wa bake bace.

“Wallahi nice laila”

Amma sumayya meya ajeki har war haka a tashan nan, gaku mata kuma ba sana’a ne ya kawo kuba?

“Wallahi laila bana da inda zan sauka zaman da nayi nan, ina tunanin ina zani kowa na tambaya sai yace wai sai dai hotel”

Toh yanzun dai dare ne ki tashi muje mijina baya gari saiku kwana washe gari zamu tattauna ki dubi gabaki d’aya kin jirkita.

Mikewa sumayya tayi a hankali laila da khadija ne suka tattara kayan zuwa cikin mota.

Suna isa wani gidane d’an madaidaici mai kyau sosai irin gidajen hayan nanne na zamani, ba ruwan wani da wani, kowa sa sassan sa amma dai gidan ya had’u, sashen laila suka shiga, yana d’auke da two bedroom da falo da toilet a ciki sai daining Area, ga tiles kota ina, irin dai gidajen hayan Abuja nan, gashi a unguwa mai kyaune akwai gidajen manya a unguwan sosai.

Bayan sun shiga kofar laila d’aya d’akin laila ta sauke sumayya, wanka sumayya tayi da khadija, laila ta kawo musu abinci sukaci, kwanciya sumayya da khadija sukayi a kan katifar dake cikin dakin, kayayyakin su a gefe, a haka bacci ya d’auke su tsabar gajiya.

************
Ta bangaren mutanen jalingo…
Tun da safe Ammar ya shirya yazo gidan su sumayya, lokacin karfe 9 na safe, yana isa kofar Adara ya tura yaro ya kira masa sumayya, amma yaro ya dawo yace masa sumayya bata nan kofarta a rufe.

A zaton Ammar koh su abie da sassafe suka zo suka tafi da sumayya, hakan yasa-sa wucewa gidan goggo ya aika yaro ya kira masa khadija, ba’a jima ba saiga goggo da yaron sunfitoh tare.

Bayan sun gaisa goggo ke sanar dashi ai khadija na gidan sumayya agun ta koma da zama, da mamaki ammar yace ai gidan yaje ya tura yaro, yaro yace basanan.

Da mamaki goggo ke kara maimaita basanan kuma?kamar ya don ita dai batasan wainar da aka toya ba jiya.

Kadai san halin yara wani sa’in suna da iyya shege taima ma basu je kofar sumayyar ba suka dawo sukace maka bata nan, inba haka ba ina sumayya zata da safen nan?

Ammar baiyi magana ba ya juya ya koma kofar gidan Adara, wannan karo da kansa ya shiga har kofar sumayya, turus yayi ganin kwado a makale a kofar abin Al’ajabi toh koh yan gidan nasu sun d’auke tane? gashi yan gidan Adara ba mutunci bane dasu bare ya Tambaye su.

Fita yayi kofar gidan ya tsaya yama rasa me zaiyi don shi gabaki d’aya tunanin sa ya basa khadija tabi sumayya gidansu kenan, kuma me yasa basu ma goggo sallama ba,motar sa yake kokarin shiga saiga mototin su abie, dakata wa yayi yajira sukayi packing yana mamakin ganinsu.

Matsawa yayi garesu suka gaisa, Anan nefa yakejin wai sunzo d’aukar sumayya, da mamaki yake sanar dasu ai sumayya bata nan kofar ta a rufe tun 9 yazo mata sallama amma bai ganta ba.

Ai abie baisan lokacin da ya zauna a dakalin kofar gidan adara ba, ya dafe kansa shikam ya shiga uku, Anya sumayyar sa daya sani ne mai tsananin sonsa da masa biyayya Amma yau ya zana mata layi ta ketare, sai yanzun yake nadamar auren ta a gidan Adara, don shi duk ya ta’alaka rashin jin sumayya, da auren tan nan da suka mata, tunda har tasan tasa kafa ta gudu, don dada da kanta taje kofar sumayya ta sake lekawa taga a rufe, ga shagari dayazo wucewa ma ya musu bayanin tun asuba sumayya suka bar gari, waya Ammar ya fitar yayi ta kiran sumayya amma bata d’agawa, Abie ma yayita kira Amma ba’a picking karshe dai dukansu suka d’unguma har tasha, Amma koh maikama da su basu gani ba, kowa suka ma kwatance sai yace bai gansu ba.

Haka abie suka dawo da sanyi jiki gabaki d’aya hankalin sa a tashe, yar yarinyar sa guda d’aya dayake da ita, tasa kafa ta shiga duniya ita da ba sanin kowa tayi ba ina ta shiga, Ammar karan kansa tafiyar sumayya ya d’aga masa hankali, wani irin abune haka sumayya ta aikata yanzun barin gari da tayi menene Amfanin sa, yau in muhammad ya dawo fa, me zaifad’a masa don Allah, gashi wani Al’amari mai girma dake zuciyar sa yana shirin fiddawa sumayya tasa kafa suka gudu da khadija shidai ya bonu.

***********
Washe gari bayan sumayya sun tashi da asuba sunyi sallah wayar ta ta d’auko wanda tasa a silent ta bude ganin miss call na yan gidan su, da sabon number har da messenge yasa ta bude wayar ta zaro sim in dake ciki ta bude Aljuhun akwatinta ta saka sim in a ciki, sannan tama khadija gargadin karta fad’awa kowa gaskiyar abinda ya kawo su Abuja, koda kuwa laila ce ta bari da kanta zata mata bayani.

Khadija ce tama laila shara da moping in tiles, sumayya kam bacci ta koma don har yanzun akwai gajiya a jikinta, sai kusan 10:00 suka karya su uku saboda yaran laila biyu ne kuma duk sun tafi makaranta abinsu.

Laila ce ta kalli sumayya,sumayya gaskiya nayi mamakin ganin ki a tasha jiya, garin yaya zakizo gari bakisan kowa ba?gari ma irin Abuja sumayya wallahi jiya ban d’auka ke bace don rabon mu dake tunda muka gama school, ban sake saki a ido ba,dayake a lokacin bata mu ake ba manyan yara.

Dariya kawai sumayya tayi tana kallon laila, Allah sarki rayuwa da laila ba karamin sonta take da kawance ba, amma kullun sai tayita wulakanta ta , gashi yau itace ta mata rana gaskiya ne da akace A rayuwa koh wani mutum yana da ranan sa”wallahi laila tafiyar gaggawa ce, bamma sa tsamanin Abuja zanyi ba”

Bangane ba sumayya?gaki na ganki da ciki don nasan wannan jikin naki da biyu ne.

“Hhhh kai laila ba halin nayi jiki kenan”?tayi maganar tana kallon khadija data mike ta koma d’akin da suka sauka, jin hiran nasu na manya ne.

Ah ah sumayya wannan jikin yafi karfin jikin jin dadi, kinga yanda kirjinki ya ciko ga hips yafi kome cika kamar me, ga jikin ki ma yayi d’anye.

“Ke abar zancen nan ni duk ba wannan ba, a ina xan samu gidan haya kamar nakun nan, na kama”?

Ah ah sumayya baki bani Amsa ta ba tukunna?cikine dake koh ba ciki ba?

” cikine laila”

Ok Aure kikayi ne, kuma meya kawoki Abuja da yarinyar shan?

“Aure nayi laila, dalilin zuwa na kuma mijina akayi kidnap insa shiyasa nima na gudo daga Taraba na dawo nan”

Baki da gidan iyaye ne? naga dai ke yar masu haline baza’a rasa tsaro a gidan kuba ai?

“Kinga laila rabu dani bana sha’awar komawa gidan mu kwata kwata wallahi, kawai in zaki nema mini mafita ki nema min tunda kikace mijinki yau zai dawo kinga bai dace mu zauna miki a gida ba”

Kwantar da hankalin ki sumayya, in gidane zaki samu don wannan gidan ma za’a samu waje, Amma sumayya kinsan rayuwar Abuja ba d’aya bane da Taraba koh? gidan nan da nake ciki dubu dari biyar ne a shekara , haka mijina ke biya.

“Karki damu indai kudin hayan ne zan biya laila ba damuwa, har school nake son ki taimaka naje na saka khadija”

Sumayya kamar nawa kika shigo dashi abuja ne wai?

“Million d’aya da dubu d’ari hudu”

Hhh lallai sumayya don kunzo da wa’innan kudi kike tunanin zama a Abuja, nifa bawai na yarda dake da abinda kikace bane, na sanki sarai da zurfin ciki, Amma fa ki sani wallahi wa’innan kud’aden da kikazo dasu wallahi bazasu miki kome ba, saidai in kin shigo da result naki nasa mijina ya nema miki aiki koda a office insu ne?

“Laila banzo da kome daya shafe karatuna ba, sannan ni ina da sana’a wanda nake saka tsammanin zan iyya neman na kaina da shi, kuma yarinyar nan kanwar mijina ce, marayu ne su biyu Iyayen su suka haifa,mijina bayanan shiyasa narike ta a hannu na, kuma karatun ta nada muhimmanci aguna”

Toh wani sana’a kenan kike bayan Lalle sumayya? Ita khadijar bata da dangi ne?

“Harda make-up kuma khadija ta iyya kitso inso samune shago nake so na kama sai mu fara muga yanda Allah zaiyi damu”

Anya kuwa sumayya gaki da ciki in kika haihu d’awainiyar abinda kika haifa zai dawo kanki, ga khadija ga kudin haya ga kayan da zaki sawa d’akin da zaku kama, ga kudin makarantar ta anya abinnan zai hadu kuwa?

“Insha Allah laila Allah zai dafa mana, yanzun dai so nake kimin hanyar da zansamu dakin gidan nan da kikace ya saura, don so nake kafun mijin naki ya dawo mun bar muku kofa, tunda kikace jiya ma kinje d’aukosa a tasha kika samu bai iso ba, motar su ta samu matsala”

Ba kome tashi toh muje gidan, mai gidan yana tsallaken titi bara na kira mijina na fad’a masa.

Ok sumayya tace suka wuce gidan mai gidan hayan, bayan laila ta nemi izinin mijinta a waya.

Bayan sunje a take sumayya ta wuce bank dayake babu halin transfer, tunda ba sim a wayar ta, kudin hayan suka kawo wa mai gidan,bayan sun dawo kudi sumayya ta baiwa khadija da laila suka tafi kasuwa, ita kuma bude d’akin da suka kama tayi, sashen mai kyau two bedroom da falo ga daining area ga toilet a cikin koh wani daki, ga kitchen a ciki daki dai mai kyau dashi yasha tiles kamar d’akin laila, kome a ciki.

Bayan su khadija sun dawo katifa suka sayo babba, da zanin gado sai hot plate mai kai biyu, da sandan moping sai bokati biyu, soson wanka dadai d’an abubuwan Amfani daidai talaka, bujuwan su biyu, khadijar ce ta ibi ruwa a panpon gidan ta wanke musu d’akunan tayi moping, yana bushewa suka shimfid’a katifar a falon, suka kai sauran kayan da suka saya kitchen, suka shigar da akwatuna su cikin d’ayan d’akin, suka kwanta a katifar su ita da khadija a falo sosai gidan ya musu d’adi ganin kowa na d’akinsa babu tsegumi kamar gidajen hayan da suka sani.

***********
Ta bangaren Al’ameeen, suna zaune a gindin bishiyar ga gajiya ga yunwa, Gidado dake gefene ya fashe da kukan bakin ciki, Al’ameen da yaron fulanin nan sukayi wajen sa da sauri, duk da raunukar dake jikinsu, don gabaki d’aya kafafunsu kayoyi sun bula gashi hannun muhammad sai yanzu yake jin tsamin sa ga giransa dake ciwo, Gidado lafiya kuwa ?sukace har suna had’a baki.

Kuka gidado ya sake da karfi, sai kuma ya bude baki Amma ya kasa magana, da hannu kawai ya nuna musu gefen jikin bishiyar da yake.

A matukar kidime muhammad yace, innalilahi wa’inna’ilahi raji’un sarin ka yayine gid’ado………… 🍀

✨Ruqeenjalal✨

🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
~ Na ~

🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

Back to top button