Hausa NovelsNamijin Zuma Hausa Novel

Namijin Zuma 50

Sponsored Links

This book is 1k 08101626484
[8/1, 9:12 AM] Maman Aslam: 50….

A bangaren su Hajiya mommy seda Sukayi 17days aka sallamesu daga asibitin, dukkaninsu jikinsu yayi sauki, sede har yanzu akwai shadin bulala a jikin na’eema har yanzu be bace ba, da wuya ma ya bace saboda bulalar bame bacewa bace, da hajiya mommy ta kalleta se taji Wani irin bacin Rai, tana kara daura damarar daukar fansa a kan Aeezad din domin bata sassauci a kan yarta, duk Wanda ya tabata seta tabashi,ita ba kanwar lasa bace. Inta tuna Wai Aeezad ne yama yarta wannan cin mutuncin, toh har itama be bari ba, A gaban wad’anda take nunawa ita watace yaci mata mutumci. Bata tunanin a duniya zata yafewa Aeezad da nabeelah wadda a knta yayi musu cin mutuncinnan, dole ta hukuntasu, shima Aeezad seta barsa da mummunan tabon dase ya damesa kamar yadda itama yasa mata damuwa. Karfe goma na dare suna cin abincin dare a kan dinning table, hajiya mommy da na’eema se alhaji sunusi Wanda keta Allah-Allah ya gama cin abincin ya tashi yaje yaga triplets dinnan sun tsaya masa a Rai, dazu Zaks ya kirasa ya sanar masa an sallanesu suna sabon gidan Aeezad din, harma yasa ya tura masa address din gidan, shi Kuma ya turawa dreva dinsa, yau beje ko Ina ba, Yana gidan tin dazu yake dabarar yadda zeyi ya bar gidan Amma hajiya mommy ta tattare ko Ina ta hanasa rawar gaban hantsi, se makirci kawai take kissima masa iri iri, tana kara nuna masa irin cin mutumcin da Aeezad ya mata gaban kawayenta, Gashi labari ya isa har inda batayi tsammaniba, video din da akayi ma har grps aka tuttura da take ciki,. Duk bashi hajiya mommy ta bayar ynzu take Shirin daukar fansar bashin, ai sata gidan barawo rance ne. “Alhaji inasan magana dakai…” Cewar hajiya mommy da tayi mgnr tana ajiye spoon din hannunta. Alhaji sunusi yace “inajinki hajiya….” Cikin isa da iya lafazi na makirci ta fara magana. “Yanzu ya auren me aiki Nan yake da Aeezad? Gabaki daya wannan ai zubar maka da mutumci yayi, ace d’anka na auran me aiki’ me aikinma wadda ta rainesa, gaskiya da sake, Kuma kasan bazeyu diyyata ta zauna da kishiya ba..” Ta karashe mgnrta suna hada Ido da na’eema wadda taji dadin abinda mahaifiyarta tace. Alhaji sunusi yayi humming kana yace “To yazanyi hajiya? Kinsan yaran yanzu Ka haifesu ne baka haifa halinsu ba, balle ma Aeezad wlhi na rasa yazan dashi hajiya…” hade Rai hajiya mommy tayi tace “Kamarya? Ka haifesa da cikinsa kace Ka rasa yaza kayi dashi? Wannan ai batsa ce kakeyi, gaskiya bazata sabu ba Alhaji!!” ta karashe cikin daga murya, na’eema Kam Dena cin abincin tayi, Ubangiji ne kawai yasan a Wani hali take ciki, data tuna da nabeelah matar Aeezad ce, sannan ga cikin jikinta ma na Aeezad din ne, se na’eema taji komi ya fitar mata a rai, ba ita ba har uwarta ma, ita abinda takeji ma ya wuce na Yar tata, a cikin azabar data tanadarma Aeezad harda nabeelah ciki,ta dauki alwashin inde tanada Rai cikin jikin nabeelah bazezo duniya ba. Alhajii sunusi yabi hajiya mommy da Ido, Ba tare dayace komi ba. Cikin fada taci GABA dacewa “Tukunna ma kayi bincike ka tabbatar Aurenta yayi?” Alhaji sunusi yace “Eh tabbss nayi bincike hajiya, wlhi aurenta yayi….” Wani bakin ciki ya tokare hajiya mommy da na’eema wadda kejin kamar zata kashe nabeelah. “Tsintacciyar mage ai bata mage alhaji,,,Dan kudi ta Auresa kilama so take ta kashesa taci gado, da wuyama in cikin jikinta nasa ne, Alhaji kayi gaggawan sashi ya saketa Kuma ya mata korar kare zuwa kasarsu, shegiya ita kanta fa ta zina uwarta ta haifota…wannan abun ze taba maka martaba cikin abokanka Alhaji, … ” Hajiya mommy ta fadi cikin kissa da makirci. Alhaji sunusi ya jinjina Kai, shide yasan nabeelah ba Yar Zina bace. a zahiri yace mata “Za asan yadda za ayi, Nan Bada jimawa ba…” “Gaskiya Ayi gaggawan yin yadda za ayi. .Kuma ai yakamata ace shi Aeezad din yaxo ya bawa na’eema hakuri Nima ya bani hakuri kan cin mutumcin Daya mana a kan Wannan shegiyar yarinyar jinin karuwai Yar iskar yarinya! Yan kasar gadon asiri!” Alhaji sunusi yace “Dole zezo ya baku hakuri hajiya….” cikin sanyi yake mgna inde Yana gaban hajiya bashi da katafus. “Yayi gaggawar zuwa…” Cewar hajiya mommy. Alhajii sunusi yace “Toh yadda kikace haka za Ayi hajjajuna…” Murmushi hajiya mommy tayi a zuciyarta tace “Aiki na bugaka Alhajin Allah..” Alhaji sunusi ya kalli agogon dake manne a hannunsa kana yace “Zan fita YNzu Amma ba jimawa zan dawo…” Hajiya mommy ta hade Rai kana tace “Ina zakuje? Gaskiya ba yau ba sede gobe?” “Pls meeting zamuyi da Abokina
Bazan juma ba…” Cewar Alhaji sunusi, da yayi mgnr cikin magiya. Da kyar de hajiya ta barsa ya fita, dreva yajasa zuwa gidan Aeezad,. Alhaji sunusi na fita na’eema ta kalli mahaifiyarta tace “Mommy yadda daddy yake Miki Nima haka nakeso Aeezad ya dingamin, a maidaminshi se yadda nayi dashi Dan Allah mommy, ita Kuma Yar bura ubar Nan a haukatata, ita da Cikin a kaita can birnin seen ta karashe rayuwarta a can,ita da shegen cikin jikinta,…” hajiya mommy tayi murmushi tace “Me kikeci na bakinki na zuba? Fiye da haka na tanadar ma yarinyar Nan domin nafijin haushinta a kan Aeezad saboda na fahimci duk Dan ita ne ya mana wannan dibar Albarkar, Amma ki kwantar da hankalinki, yarinyar de dagani ta mori malami,,Ina me tabbatar Miki se tayi nadama ai ruwa ba sa’an kwand’o bane,ko kura ta rame ai tafi gaban raini ga Kar’e, sama Tayima yaro nisa sede ya tada Kai yayi kallo, yaro besan wuta ba seya taka, Wani ma yayi rawa balle d’an makid’a, sha ruwan sanyi y’ata kmr kin jika tsumma a ruwa…” Hajiya mommy ta karashe tana Jan kwafa, ko garwashi ta hada ta jefa nabeelah a ciki bata huce ba. “wlhi mommy hankalina baze kwanta ba Sam, bacci ma seda kyar nake yinsa har yanzu Ina San mijina, mommy wlhi bashi da lefi kawai Kiyi azabarki a kan nabeelah, duk asiri ne yasa idanuwansa ya kulle ya mana abinda ya mana, ni ko kashe yarinyar Nan akayi ban huce takaiba, mommy so nake Ayi mata DUk abinda zakiyi mata , ta d’and’ani azabar duniya taji, tinda harta aurar min miji ai dole in mata azaba mommy, gashi sanadinta mutumcinmu ya zube gaban masu mutunci, wlhi mommy kiyayyar da nakewa nabeelah bazata misaltuba..” hajiya mommy tayi murmushi mugunta kana tace “Ai duk kiyayyar da kike mata be Kai wadda nake mata ba naeema, Allah de ya kaimu gobe,in mukaje asibiti Kara duba jikinki, semu wuce gun boka kawai ba a bori da sanyin jiki…” na’eema ta amshe da Amin, kiyayyar nabeelah na Kuma ninkuwa a rayukansu ita da uwarta, sun rasa ma tayaya ta shammacesu.

Seda Alhaji sunusi ya tsaya Yama jikokinnsa shopping sosai na kayayyaki na Alfarma a babban boutique din da Ake saida kayayyakin jarirai Wanda Ake kawowa daga kasashen waje. Seda ya cika akwatina uku da kayayyaki na Alfarma dreva dinsa ya tayasa zaba da wata me Aiki a gurin. Ya biya akasa a booth. Suka sake tsayawa yawa mahaifiyarsa siyayyar kayyan makulashi. t kana Suka nufo gidan Aeezad,. Alhaji sunusi na shigowa falon yaga ga kugun Aeezad gana nabeelah se kara shishige mata yakeyi ga yara duka ukun a kan cinyarta, zaune take kan carpet Kuma ta daura pillow a kasanta, ta zuzzuba duka yara ukun a kan cinya, ta bawa wancan nono ta dawo ta bawa wannan nono, yaran nada lafiyar tsotso Suna tsotso sosai, danma ana hada musu da madara, saboda tsotsonsu yayi yawa, yau kimanin kwanansu takwas da haihuwa Amma sun kware a tsotso. Big hajiya na gefe tana Jira a gama shayar da yaran a batasu, ummih na can gefe itama,Aunty hafsat bata Nan tana gidanta,se wata laure itama tana zaune gefe me Aiki ce, big hajiya tasa aka kawota dazunnan daga gidan hajiya Maryam wato matar d’anta Alhaji abubakar, Se Yau big hajiya ta shaida mata komi Aiko itama ma ta shaidawa mijinta, Abu kmr almara kowa yaji dadin wannan hadin, Daman ita hajiya Maryam ta fara fahimta kwanciyar Aeezad a asibiti. Alhaji sunusi ya gaida mahaifiyarsa ta amsa fuska sake, ya bata kayayyakin ciye-ciyen daya siyo mata, se godiya take masa dasa Albarka, tinda aka haifo yarannan take ganin sauyi a gurin d’anta, gashima tanata ganinsa akai-akai gaskiya haihuwar yarannan yazo da Albarka, haka big hajiya Ke cewa motsi kadan. Ummih ta gaida Alhaji sunusi ya amsa fuska sake, besan meyasa ba inya kalleta se yaji gabansa na faduwa. Daman nabeelah tini ta gaisasa tin shigowarsa Aeezad ma ya gaidasa, ganin yadda daddy keta zuwa Yana duba yaran yasawa Aeezad jin dadih ba kadan ba. laure me Aiki ta gaida Alhaji sunusin cikin girmamawa. Ya amsa Yana kallanta Yace “Wannan fa?” yayi mgnar da Aeezad. Aeezad ya bashi amsa da “Big hajiya ce tasa aka kawota daga gidan Alhaji daddy,zata dinga taimakawa da Ayyuka…” Alhajii sunusi yace “Toh-toh…Amma an tabbatar ta iya wankan jarirai kou?” ya juya akalar tambayarsa ga big hajiya. Big hajiyar tayi murmushi tace “kar aje a jefa maka jikoki a ruwan zafi kou?” duk Yan falon sukayi murmushi ba karamin jin dadih sukayi ba musammanma Aeezad, dadih na nunawa yaran SO na tsakani da Allah Sam ma be iya boyewa. Alhaji sunusi ma murmushin yayi yace “Eh wallahi big hajiya, haka akayi da Yar Abokina ta haihu haihuwar fari aka dakko me wanka, garin gasa cibiya ta kona babyn, big hajiya satinsu uku a asibiti ana fama da babyn ba karamin kuna yayi ba,,, maganin Ayi ai kar a fara, kwara a bawa hajiya ta dinga musu wanka…” Ya karashe mmaganarsa Yana kallon ummih wadda kanta ke kasa. Aeezad yayi hanzarin cewa “Nima haka nace,Amma big hajiya taki, ita ke musu wanka daddy, da kyar take bari aunty hafsat ta musu wasu lokutan . ” Alhaji sunusi ya zaro idanuwa yace “gaskiya big hajiya dakin bari an dinga musu saboda naga ke ba Wani gani kike sosai ba…” Big hajiya ta amshe da “uban bana gani! A haka de na raineka, Shima Aeezad din Dan Anki bani shine Amma Dani zan rainesa… Dan haka ni zan dinga musu wankan da gashin cibi har Ayi arba’in banga me rabani da yarannan ba sede mutuwa…” “Toh ai shikenan Allah de ya tsare min…” Cewar Alhaji sunusi big hajiya ta rike Baki tana mamakin ganin yadda d’anta be kawaici a kan yaran Kuma duk kawaicinsa. Duk Yan falon suka amshe da Amin Banda nabeelah data kasa cewa komi se gyangyadi takeyi Ma ita bacci takeji, so takeyi ta gama bawa yaran nono taje ta kwanta. ” Hajiya me kula da jikokina, Jeki ce da dreva Dina ya bude Miki but ki kwaso kaya…” Alhaji sunusi yayi maganar da laure Cikin girmamawa bada raini ba wai Dan tana me AIKI. Laure tayi murmushi Hadi dacewa toh ta mike ta fice a falon, a kallah laure bazata wuce 45yrs ba. Ta kwaso akwatunan ta diresu a tsakiyar falon, Nan aketa kallon kayan arziki,. A haka hajiya Maryam da mijinta, da Saif da matarsa suka shigo falon, Daman big hajiya tasa aunty hafsat ta tura musu da address. Cikin murna suka karaso aka gaggaisa, duk hankalin kowa na kan baby’s,har rige rige sukeyi gun daukar babyn, se Masha Allahu kawai suke cewa Alhaji abubakar yace “Ashe haka ya kasance,,,Toh Allah yasa Albarka…” duk falon suka amsa da Amin nabeelah de a zuciya take ta Amsawa da Amin de. Nan de falo ya kicime se ganin babys akeyi da kayayyakin Arzikin da Alhaji ya siyoma babys din duk sunyi kyau kmr siyayyar mace. Big hajiya taji dadin ganin iyalansa a hade, anata nishadi,matar saif ta dauke babys ta rike sun bata shaawah sosai ta taba haihuwa Amma yaran sun rasu har Sau biyu,ji takeyi kmr a bata babys din ta tafi dasu. “Kowa de ya hallara, banda tsatson tsiya, Allah de wadaran hali irin na Rafi’ah…Sanusi bakayi sa’ar mata ba, Ubangiji de yasa da raina na ga ka auri mace ta arziki..” Big hajiya ta Sako wannan maganar ana cikin Hira. Alhaji sunusi yayi Shiru kawai shida kansa yasan macensa bata kirki bace Amma ba yadda zeyi ne. “Dafatan de baka sanar da ita an haihun ba?” tayi mgnr da Alhaji sunusi again. Ya daga mata Kai alamar Eh. “Toh kar inji kar in gani, domin kana sanar da ita wannan haihuwar,seta shiga ta fita ta kashesu, danma kullum se uwarsu ta musu Azkar An tofesu tako ina, bade mutum ba ko aljan be isa ba Insha Allahu, mun rike ubangijin da baya bacci, kema nabeelah ki dinga yawan askar din safe da rana da dare, koda Baki da tsarki, ki dinga zama da Alwala da”iman kinji kou?…” Nabeelah tace “Toh…” Daman kullum cikin Alwala take da Azkar, Kuma tana tofe yaranta da Addu’ah safe da yamma da dare, kullum se uwarta tace ta dafe kansu Daya bayan Daya duk safiya ta dinga ma yaranta Addu’ah. “Alhamdulillahi da zuwanki zuriahta nabeelah, kinada ibada ba abinda mugu zeyi dake…” Cewar big hajiya. Hajiya Maryam tace “Kwarai kuwa….insha Allahu ma zan amso musu maganin kariya Ayi musu wanka dashi itama uwar tayi wanka dashi gobennan, zanzo na kawo da safe zan aika kanwata ta amsa da safe se inzo in kawo insha Allahu…” big hajiya da ummih suka hada Baki gun mata godiya. Har karfe Shadaya na dare suna gidan nabeelah ta mike sbda bacci takeji sosai zata nufa dakin da Aeezad yace Nan ne nata, shi Kuma dakin da yayi first night dinsa da ita Nan ne nasa. Aeezad ya mike ze bita Hajiya Maryam tace “Kai Kuma Ina zaka?” ba kunya Aeezad yace “Bacci mukeji nida ita,…” hajiya Maryam ta bude baki tace “Au tare kuke kwana dame jego?” big hajiya ta amshe da ”Kadan kika gani, ai wannan yamafi babys din, danma bakiga Abu ba a asibiti, Kai wannan yaran jarababbe ne…” Nabeelah najin haka ta karashe shigewa dakin da sauri sbda kunya. “Toh Ina zan kwana fisabillahi big hajiya?” kowa ya zubu masa Ido Sam bashi data ido. Hajiya maryam tace “To ai haihuwa tayi ko jego taKeyi tana bukatar hutu? Sannan de Ai Doctor ta gaya maka ka’idojin CS kou? ” Ya daga Kai yace “Duk an gaya min gimbiya hajiya,Ai bance Wani Abu zan mata ba, wlhi ki kyale sharrin big hajiya…” Alhaji sunusi yayi kasa da kansa jin abinda d’ansa ke fadi,, se kawai ma ya mike ya musu Sallahma yayi kissing jikokinsa dake hannun big hajiya kana ya fice a gidan, a ransa bega lefin d’ansa ba domin be Yar a kasa ba inde jarabar bukatar macece, Amma su sunada kawaici akasin shi Aeezad,. Duk yadda aka tasosa da Baki seda ya shiga dakin da nabeelah take harta fara bacci taji an rungemeta, zatayi mgna ya kame bakinta ya tsotsa, ya tura mata hannu cikin nono kmr shine babyn, gashi yaki sakar mata Baki tayi magana. Soyayyarta na kuma ratsasa, a haka bacci ya kwashesa seda yayi bacci ta kwace bakinta cikin nasa ta cire hannunsa a cikin nonon,sbda tasan dole big hajiya zata shigo ta kawo mata yaran. Ta matsa nesa dashi, bacci ya dauketa. Se shabiyu hajiya Maryam suka bar gidan,big hajiya ta nuf dakin da Aeezad da nabeelah suke da babys a hannunta, tana fadin Dani suke zancen. Itama Nan daKin ta kwanta tsakiyar Aeezad da nabeelah, danma gadon uban fadi be dashi se mutun biyar su kwanta basu matsu ba,babys Kuma Daman an riga an shirya musu gadonsu Nan ta kwantar dasu, Aeezad Yana farkawa yaga big Hajiya a tsakiyarsu, Allah yaso be Kai mata raruma a nono ba, girgiza Kai kawai yayi a zuciyarsa yace “Nida matata…” Kawai ya tashi ya bar dakin ya koma dakinsa, big hajiya ta masa kora da hali Wanda yafi kora da sanda, ya saba kwana yana tattaba nono yanzu Kuma se a hnkli besan yaze kasance ba. ummih Daman an bata dakinta can ta kwana, Daman ita ba Wani bacci take ba, ibada take tayi tanawa yarta da jikokinta Addu’ah,toh ynzu ta Kuma kara zage dantsi gun musu Adduah,.

Washe gari tin da duku-duku Hajiya mommy da na’eema suka bar gidan ko asibitin Basu fara Zuwa ba, suka nufa gurin boka can cikin daura. Bokan na ganinsu ya kyalkyake da dariya irin ta wad’anda aka Cirewa Imani gabaki daya yace “wato magana ta fito Kenan…tinda na ganki da yarki asiri ya bayyana,,,,hahahahahaaaaaaa..” se yanzu naeema ta Kuma tunawa da abinda bokan yace Ashe tin lokacin ma da auren Aeezad da nabeelah, da ynzu Wani labaarin akeyi ba wannan ba Amma tunaninsu ya bace, in Abu ze faru de baka da tsumi baka da dabara. Hajiya mommy ta bude baki zatayi mgna bokan ya dakatar da ita dacewa “Aita haifa wannan Cikin yau ma yaran kwanakinsu tara….hahahaha duk Ina biye da taurarinku, a taurarinki nake ganin meke faruwa, Aiki aka mata aka cire mata yara Yan Uku!!!” ya kwashe da dariya dajin ya amsa. Dukkaninsu hantar cikinsu ta kad’a suka kalli juna, Hajiya mommy seda ta tsugunna sbda tashin hankalin tace “Yanzu shikenan inya mutu komi na yaran ne Kou boka mu Kuma se abinda Muka gani?” Bokan yayi dariya yace “Da wuya ma kugani ..” a wannan karan itama na’eema seda ta tsugunna, dukda ita bayan kudin da takeso tanasan mijinta ma, . Hajiya mommy ta daura hannu a ka tace ” Nashiga uku ni rafi’atu! Wace iriyar matsifa ce ta tinkaroni nida diyyata …ynzu yaza ayi boka? ka temakeni boka ka kashemin yaran first ita uwar a haukatata, irin haukan dazata dinga yawo tsirara, sannan asa mata warin tamkar warin sabon ZAWOOO, inda hali ma asa mata Fiye da haka… A fara Dasu Daga baya Ayi ta uban gayyar… ” Bokan ya kyalkyale da dariya yace an gama. Se yayi Shiru na wasu dakiku, kana ya kuma fashewa da dariya yace “Zeyi wahala wannan aikin domin kullum Cikin Azkar suke da yaran, dadin dad’awa dukkaninsu suna wanka da Wani magani Wanda bamu Isa muje kusa dasu ba,, sede ku bari in an samu damarsu a aiwatar da wannan aikin….” Na’eema ta fashe da kuka kawai, tana rokon boka ya temaka mata, ko kashe nabeelah ne yayi ita da yaran. Hajiya rafi’ah itama ji take uwa ta fashe da kukan Amma ta dake tasan aikin babba ne tinda har boka yace aikin ze wahala. “ka temakamin boka, bani dame temakona sekai boka, ka dubeni boka, ka rufamin asiri boka, karka bari suka karshena, banasan wannan yaran da uwarsu duka, gabaki daya komi nawa na neman kalacewa…” (hajiya rafi’ah ta mance da duk duniya bame taimakonmu se Allah) Boka ya kyalkyale da dariya yace “duk karki damu hajiya, ke zakiga bayansu, kin taba ganin nasa Abu a gaba banyi galaba ba? Zanta bibiyarsu harse nayi galaba a kanku ki kwantar da hankalinki….kuje gida kuyi bacci kawai..harshi uban gayyar bazan barsa ba, sena dawo dashi ga yarki tamkar yaro mara wayau… .” Ya Karashe Yana kwashewa da dariya. Nande hajiya da na’eema suka dinga magiya boka yace karsu damu, suka ajiye masa uban kudi suka koma gida na’eema ke driving motar, Amma hankalinta tashi yake, dukkaninsu bame mgna kowacce tashin hankali ya shafe tunaninta. Ranar ko asibitin Basu jeba, dukkaninsu ji suke damn mutuwa sukayi da wannan Labarin. Ranar haka suka wuni jugum jugum kamar an Aiko musu da sakon Mutuwarsu yanzu-yanzu. Alhaji Sunusi ya kula da yadda suke kmr marasa lafiya ko abinci basuci ba. Ya tambayi Hajiya mommy lafiya de ko tace masa lafiya Lau kawai Amma inside Abu na nukurkusarta, ta kula alwalar safe na Neman kaita la’asar, ta raina d’an hakki gashi ya shiga idonta ya addabeta da yawo Tako Ina. Ta tambayi Alhaji Sunusi nabeelah ta haihu Ashe? Nan Alhaji yayi mamakin yadda akayi taji Amma seya Waske yace shi be sani ba, ya nuna mata ma besan mgnr gudun kada Allura ta tono garma. Ranar de bacci gagarar Idanuwan Hajiya mommy da na’eema yayi, Abun har ya fara basu tsoro da mamaki, wai me Aiki tazo har gida ta Aure ma yarta miji, tsohuwar mace, kuma ya juyawa yarta baya ita da take sabon jini ya komawa tsohuwar mace. wannan abun a duba ne, ko yanzu nabeelah ta gushe tasama na’eema da Hajiya mommy bakin Cikin da baze gushe ba har abadan, Kai Wani abun fa dole sede insun kwanta Dama, basuga abinda zasuyima nabeelah ba su samu sassauci..

 

Karku manta Muna saida kayan gyaran Aure akwai pridal package manyan mata Kuma ba a barku a baya ba kuzo ku gyara jikinku a sabanta jiki. 08101626484

This book is 1k 08101626484

NAMIJIN ZUMA

Back to top button