Hausa NovelsNoor Al Hayat Hausa Novel

Noor Al Hayat 65

Sponsored Links

Komawa baya khadijah tayi tana kallonsa, ya shigo xai rufe kofar ta xaro ido tace “Meye haka Doctor” rufewa yyi ya yana tahowa kusa da ita yace “Tell me why you are avoiding me Khadijah” wani kallo tayi masa tana komawa baya tace “Avoiding din ka kamar ya, bayan gaisuwar da nake maka me kuma kake so daga gareni?” Ganin ya kusa isketa ta juya da sauri xata shige bathroom, yyi hanxarin rikota ya juyo da ita yana kallonta, wani kara tayi ya matseta jikinsa yana mata wani kallo, lkci daya jikinta ya dau rawa tace “Stop it plss Dr, meye haka don Allah ka bari ni bana soo…” yace “Is it a crime don nayi aure?” Sake baki tayi tana kallonsa, can ta hade rai tace “Ban gane ba?” Yace “Ehh tunda nayi aure kika kara dasa min rashin mutunci a kan na da, I showed interest in marrying you kika yi shunning dina, me kuma kike son in maki Khadijah? Tell me me kike so?” A hankali tace “Let go of me now!” ba musu ya saketa yana kallonta, juyowa tayi tana facing dinsa da kyau tace “Ai da kana so na kamar yanda kake ikirari ko me xan ce maka baxai hana ka abinda ke a ranka a kai na ba, kuma abinda yasa baka wani damu ba shine saboda kana da warce kake so da aure… so don’t tell me dat Ayman” Ya shafa kai yana mata kallon mamaki, bude kofar parlorn suka ji aka yi, a tare suka kalli door din dakin, ya nufi kofar ya bude ta bi bayansa, tsaye suka ga Jawahir a parlorn ta rike waist da hannu, Khaleel ya karaso kusa da ita kamar mai tausayin kasa ya tsaya yana kallonta, bata yarda ta kallesa ba ta taka ta tafi gun Khadijah dake tsaye bata karaso cikin parlorn ba, wani kallo Jawahir ta dinga mata kafin tayi wani murmushi tace “Khadijah kike kowa? Let me warn you first before taking any action….” Strictly tana mata wani shegen kallo tace “Stay Away from my husband, I repeat my self stay away from him you bitch, idan ma kina da wani kuduri a kansa a ranki ne to kiyi maxa ki goge don wllh ya fi karfin ki nesa nesa ba kusa ba, shi ba sa’an ki bane, shi ba sa’an auren ki ba ne, and let me advice you as a lady…. idan aure kike so ki rufa ma kanki asiri ki koma gidan uban ‘ya yan ki wllh hakan kadai ne rufin asirin ki, ke bari ma kiji abinda baki sani ba, da Khaleel ya aure ki a matsayin kishiyata gwara ya auro min budurwa kamar ni mu goga, banda naci da ba kai wahala Ina ke ina Khaleel kina baxawarar, ragowar wani???” Tsawa Khaleel yyi mata ya isa kusa da ita lkci daya idanuwansa suka sauya xuwa ja yace “Kina da hankali Juwairiyya? Kin san wacece ita kike fadi mata wannan maganan gabana?” Wani kallo ta masa ta daga masa hannu tace “Spare me Malam ba da kai nake ba da sa’ata nake, keep ur mouth shut… ban kuma damu in san wacece ba, tunda ta shanye ka ni bai gagareni in kwatar maka yan cin ka ba” Fincikota Khaleel yyi a mugun fusace yace “Did you knw I can give u a dirty slap now?” Jawahir tayi dariya tace “Wllh ka mare ni in rama a kanta, wai ma a kan shegiyar mai makale ma maxajen mutane xaka ce xaka mareni Khaleel?” Kasa ce mata komai Khaleel yyi, can ya runtse ido ya turata yace “Ina guje maki ranan da xaki ji kunya Jawahir, ranan da xaki kasa kallon idanuwan warce kike ma rashin mutunci yanxu, Kuma bayan kin san ta kina ji kina gani xan aureta in hada ku….” Khadijah tayi wani murmushi bata ce komai ba ta juya a hankali ta koma daki ta rufe kofar ta sa key, tafi minti goma kwance kan gado, ita kanta ta rasa me ya hanata yin kuka, kalmomi hudu suka tsaya mata a lkcn, Bitch, Baxawara, ragowar wani, mai makale ma maxan mutane, yanxu jiddah ma kallon da take mata kenan koh?? wani murmushin tayi ta kai hannunta fuskarta jin abu na sauka taji hawaye ne, cikin pillow ta cusa kanta bata sake dagowa ba sai kusan karfe dayan dare shima ta dalilin sanyin dake neman mata illa, da kyar ta mike jikinta na rawa ta fiddo kayan sanyi ta sa, Shureim ya fado mata ta fita parlor da sauri, kwance ta gansa kan kujera ya takure waje daya yana rawar sanyi duk da kayan sanyin jikinsa, ta isa kusa da shi ta daukesa ta rungume sa ta karasa gun kofa ta sa key sannan ta kashe wutan parlorn ta wuce daki, kwantar da Shureim tayi ta rufa masa duvet ta wuce bathroom ta sa ruwan dumi tayi alwala ta fito, sai kusan karfe biyu da wani abu ta kwanta bacci me nauyi ya dauketa. Tun da tayi sllh asuba take ta shirya sauran kayansu, tana gamawa ta tada Shureim ta shirya sa ta basa tea da sauran cake dake gidan, ita ma ta shirya, wayarta ta dauka ta shiga scrolling call log a hankali tana neman number Aliyu duk da bata yi saving ba amma tasan number, ta fi second goma tana kallon number can tayi dialing, bugu biyu ya daga, a hankali yace “Iman, hope all is well?” ta gyada kai kawai tace “Ina kwana” yace “Lafiya lau, Ina Shureim” ta kalli Shureim dake gefenta a xaune, murya can kasa tace “Airport xaka xo ka kai mu pls, if we won’t inconvenience you”
Aliyu yace “Sure, yau xaku tafi Nigeria din?” Tace “Ehh” yace “Toh gani xuwa yanxu” daga haka ya katse wayar, bayan kusan minti sha biyar tana xaune ta rungume Shureim kai kana ganinta kasan she is just weak, duk ta xama kamar mara lafiya alhalin babu inda ke mata ciwo, da ta tuna maganganun da Jawahir ta gaya mata jiya da yamma sai tayi murmushin takaici, mikewa tayi ganin kiran Aliyu ta dau karamin jakarta suka fito bayan ta tabbatar komai na gidan ta kashe ta kulle kofar apartment din, ta nufi waje rike da hannun Shureim, Kayan sanyi ne jikinsa shi ma yana jingine jikin mota ya rungume hannunsa, yana ganin Shureim ya isa kusa da shi ya daga sa ya rungumesa a hankali yace “Good morning sweetheart” murmushi yaron yayi yace “Good morning uncle” kallon khadijah dake kallonsu Aliyu yayi ta sunkuyar da kanta da sauri, yace “Good morning” ta ce “Morning” xagawa yayi ta bi bayansa ya bude motar ta shiga ya mika mata Shureim ta xaunar da shi gefenta sanann ya rufe motar ya xaga ya shiga maxaunin driver, driving din some minutes yayi suka isa airport yyi parking waje duk suka fito, Daukar Shureim yayi da damuwa yana kallonta yace “Iman kin bari sanyi ya kama sa da yawa fa” ta kalli Shureim dake tari, sauke idonta tayi tace “And I am very cautious about that, Ni ma ban san yanda aka yi ba” yace “ko yana shan ruwa me sanyi ne?” Ta girgixa masa kai tace “A’a” Ganin yanda yake tarin tace “Ka ajiye sa kar ya maka amai a jiki” Bata rufe baki ba ya kwarara masa aman shayin da ya sha a jikinsa, Aliyu ya dinga shafa masa bayansa yana masa sannu, da damuwa khadijah tace “Toh ina xa mu samu ruwa yanxu, gashi ya bata maka jikin ka” Aliyu na kallon direction da motarsa yake yace “I think I have table water a mota” tace “Toh bani makullin in dauko” mika mata makullin yayi ta koma motar da sauri, ba a dau lkci ba ta dawo da ruwan ta mika masa ya karba, ya sauke Shureim ya ciro handkerchief dinsa ya shiga goge masa bakinsa da jikinsa da ya bata, tana kallonsa tace “Baxa ka wanke masa bakin da ruwan ba?” Yace “Noo, akwai sanyi…” yana gamawa ya mike ya shiga kokarin cire sweatern jikinsa, ganin goran ruwan hannunsa ta xaga bayansa a hankali ta taimaka masa ta cire sweatern, sai ta ganta yar karama kusa da shi don ya fi ta tsayi sosai, lkci daya ya juyo yana kallonta, ta sauke idonta ta saita wajen aman a sweatern ba tare da ta kallesa ba tace “Xuba min ruwan” yace “But it will be very chill kawo in wanke” tace “A’a ni ka xuba min” bude ruwan yayi ya shiga xuba mata tana wanke wajen har ta gama ta shiga kakkabe sweatern, da sauri ya sake ruwan hannunsa ya nufi gun Shureim ganin yanda ya jingina da wani mota, he looks so sick, ya daukesa ya rungumesa yace “Sorry son” Khadijah na kallonsu a hankali tace “Toh kar yaje yana min amai a jirgi” Aliyu ya juyo yana kallonta yace “Noo baxai yi ba, mu je in siya masa drugs mu dawo yanxu” daga haka ya fara tafiya ta bi bayansa. Sai da ta fara shiga motar sannan ya xaga ya mika mata Shureim ya rufe motar ya dawo ya shiga maxaunin driver ya tada motar, drugs ya siya masa na mura da xaxxabi, bayan yyi reversing motar murya can kasa yace “Can I accompany you two Iman, because of his condition, I will postpone my schedules for today…” Khadijah da ke rungume da Shureim tayi shiru bata ce komai ba, ganin ya dau hanyar airport ta kallesa a hankli tace “Ai baka shirya ba, you can’t just go without preparation” yace “I will only drive home yanxu inyi dropping motar, mu dawo airport and make the traveling process” Tace “Toh amma ai su Mumy ba su sani ba” ya kalleta a hankli yace “I will explain to her, she will understand” khadijah ta d’an yi shiru, can tace “Toh shkkn” gida ya nufa yayi parking a waje yace “Kilan baki shirya shiga ku gaisa da Mumy ba, beside it’s too early, let get a taxi sai ku shiga ku jirani saboda sanyi” ita dai bata ce komai ba ya fita ya tsayar masu da taxi bayan ya fada masa xai d’an jira sa ya shiga gida ya fito, kayansu ya fara transferring xuwa taxin sannan ya xaga ya bude motarsa Khadijah ta fito ta shiga taxin, ya dau ledan maganin Shureim ya bata ta amsa, ya shiga motarsa ya shiga gidan yyi parking. Bayan few minutes ya fito ya hau taxin suka wuce airport, sai kusan karfe tara jirgin su ya tashi. Aliyu na kallon ladyn dake kusa da Khadijah bayan sun yi boarding plane din xai yi magana ta gane abinda yake nufi, tace “Ohk then” daga haka ta koma seat dinsa ya xauna wajenta yana rike da shureim ya kalli Khadijah da ta lumshe ido yace “Ke kin ci abinci kafin ku fito?” Ta bude ido tana kallonsa ta gyara xamanta tace “Na sha shayi” Bai sake cewa komai ba, bayan wani lkcn Shureim yayi bacci yana rungume da shi, da farko kawai lumshe ido tayi ita ma, amma after sometimes bacci ya dauketa, kallonta kawai Aliyu yake, ko ba a fada masa ba yasan she is disturb, there is something eating her but he won’t even dare ask what it is, ya lumshe ido tuna farkon ranan da aka fara kawo khadijah aiki gidansu da yanda ta dinga kallon TV bata ma san abinda ake ce mata ba, lkcn da ta taka masa kafa xata kitchen and how she said she is sorry, tun daga sannan dama yasan kaddara ce ya kawota gidansu, bude ido yayi a hankali ya sake kallonta, Khadijah is just beautiful in many ways…. A hankali ya sauke idonsa kan Shureim ya ga babu abinda ya dauko nata sai pink coloured lips, kanta ya ji a shoulder dinsa, ya daga kai yana kallonta, bacci take me nauyi, bai taba ta ba kuma bai tasheta ba ya bar ta a haka. Sai kusan magrib suka sauka Abuja a Nigeria,wani flight din suka sake boarding xuwa kaduna, Adai daita sahu ya kawo su har kofar gidan Umma, Aliyu ya fito Aliyu yana dauke da Shureim, ita ma fito ya dauko mata jakarta ya mika mata ta amsa yace “Ki kai ciki sai ki dawo ki amshe sa” ba musu ta wuce ciki

yana kallon mai napep din yace “Kayi hakuri xaka kai ni Gra yanxu” Bayan wani lkci khadijah ta fito ya isa gabanta ya mika mata yaron dake bacci ta karbesa tana kallonsa tace “Mun gode sosai” d’an murmushi kawai yayi, can yace “Idan ya ci abinci sai ki basa magungunan sa” tace “Toh” yace “Alryt xan wuce gida a gayar min da Umma” daga haka ya shiga adai daita, mai adaidaitan ya ja suka bar wajen ta bi su da kallo, juyawa tayi a sanyaye xata shiga gida suka kusa cin karo da Nanny da ta amshi Shureim hannunta suka wuce ciki, ruwan xafi Nanny ta hada masu bayi, ta ma Shureim wanka sannan khadijah ta shiga, Umma na ba Shureim abinci ta fito, Umma ta kalleta tace “Ni nasan sai sanyi ya kama yaron nan kawai salon ki ja masa kika tafi da shi tunda kin san lkcn sanyi ne” khadijah bata ce komai ba sai murmushi da tayi…

Back to top button