Hausa NovelsNoor Al Hayat Hausa Novel

Noor Al Hayat 71

Sponsored Links

Umma kasa kwakkwaran motsi tayi bayan ta gama jin bayanin Sudais ta kasa daina kallonsa, jikinta yayi sanyi sosai, tsoronta daya a lkcn khadijah, ko ya xata dau batun nan, Wai Aliyu? Kallon Khaleel dake xaune shi ma tayi, ya d’an yi murmushi ganin damuwar dake fuskarta yace “Umma you need not to worry, I know you might be thinking of how khadijah will take this, but I think ba lallai sai an fadi mata ba she will see for her eyes, and surely nasan she have a very soft spot for Aliyu, the problem is that she is confuse, sannan one thing about her is that bata mance abun sharri da aka mata ko ya yake which is wrong, she need counseling Umma….” Murmushi Sudais yyi a hankali yace “Sure, gaskiya doctor ya fada Umma, fatan Allah yasa ke dai kin fahimce ni, nayi abinda naye ne saboda future, I really don’t want anything that will hurt her again in life, she have had enough… duk Allah ne mai tsara komai” a sanyaye Umma tace “I am really proud of u both, irin ku basu da yawa a duniya Allah ya biya ku da mafificin alkhairinsa, ko wannen ku ya taka rawar gani matuka a rayuwar khadijah, Kun mata abinda dangin ubanta da ni kaina na kasa yi mata, Allah ya saka da alkhairi, and one more thing Sudais ka maida matar ka don Allah…” Sudais ya girgixa kai a hankali yace “Umma I don’t think xan maida jiddah, na hakura da ita, Allah ya musanya min ita da mafi alkhairi, may be abubuwan da nayi mata years back kan khadijah ne Allah ya saka mata ta samu damar yi min abinda ta so, tun da na aure ta take wahal da ni, I have had enough…” Umma tace “A’a ba ayi haka ba, kayi hakuri don Allah, ko albarkacin yarinyar nan dake tsakanin ku” Dai dai nan Baby ta fito ta kawo masu abinci kamar yanda Umma ta umarce ta kafin ta taho gun su, ajiye abincin tayi ta kasa kallon Sudais don ba karamin kunyar abinda tayi masa a waya taji ba daxu barin da ta ga bashi da laifi, Kallon Khaleel tayi daga karshe tace “Ina yini” yace “How are you” ta mike tace “Alhmdllh” daga haka ta juya ta wuce Sudais ya bi ta da kallo ganin bata gaishesa ba, Khaleel na kallon Umma yace “And lastly Umma, I think I’ve found out dangin mahaifiyar khadijah if I am not mistaken in sha Allah” daga Umma har Sudais kallonsa suka dinga yi ko kiftawa babu, ya sauke kansa kasa a hankali yace “But I won’t reveal that to her sai tayi settling gidan mijinta, ta kwantar da hankalinta, still xa mu je can gidan dake Umma duk da su ma ban ce masu komai ba tukun, but babu tantama they are her mother’s family in sha Allah” Mumy ba karamin sanyi jikinta yayi ba jin sadaukarwar da Barrister yayi ma Aliyu, she couldn’t even utter a word, abun ya mugun daure mata kai, Abbansa shi ma ya jinjina lamarin sai dai abinda bai ji dadi ba shine yin gaban kansu da suka yi babu shawara da kowa, and a whole daurin auren 1st son dinsa baya gun, but all the same he is happy for his son cos he is always after his happiness kuma ya bukaci number Barrister Sudais, Mumy na ta kallon Aliyu da har sannan mood dinsa isn’t encouraging da damuwa tace “What’s it again Abuturrab, ain’t you happy” ya dago ya kalleta da kyar yace “Mumy bata sani ba fa, and I don’t know how she will take this, ba so na take yi ba, tana kulani ne kawai saboda kids din, albarkacin su nake ci” A hankali Mumy tace “Then you will teach her to love you son…” Bai iya yace komai ba, bayan few seconds ya mike ya dawo kusa da ita ya xauna yana facing dinta, har lkcn idanuwansa basu dawo dai dai ba, cikin sanyin yace “Mumy me xan yi in biya su?” Shiru Mumy tayi tana kallonsa don tasan su wa yake nufi, ta d’an yi murmushi tace “Zumunci mai karfi da su is enough son” Aliyu ya sauke idonsa kasa a hankali yana tunanin xumunci yayi kadan ya biya both Dr Ayman and Barrister Aliyu, dafa sa Mumy tayi tace “That’s just it Abuturrab, mutanen nan biyu ka rike su a rayuwa, kaga riban hakuri… Da ka ci gaba a yanda ka fara da farko kana tunanin Barrister xai ga cancantar bar maka ita? Of course no, shi sa nake yawan ce maka you just have to be patient in everything in life” Bai dai ce komai ba, tace “Do what you are suppose to now, na kira su Siyama xa su je can gidan naka su yi abinda ya kamata, don xuwa anjima xa su kai ta can gidan, mun yi waya da Ummarta yanxu” Har sannan Kamar yanda khadijah bata san da wanda aka daura mata aure ba haka baby ma bata sani ba, gashi dai ana ta shirin tafiya da amarya wajajen karfe biyar, Umma duk ta kasa samun nutsuwa da ta tuna khadijah fa bata san da Aliyu aka daura auren ba sai taji gabanta ya fadi, tsoronta ma kada ciwonta ya kara tashi, daga karshe ta sa aka kira mata Baby bedroom dinta, Baby na kallonta tace “Gani Umma” cikin sanyi Umma tace “Khadijah kin san da wanda aka daura auren nan kuwa?” Girgixa kai Baby tayi da confusion tana kallonta, a sanyaye Umma tace “Yayan ki” still khadijah tayi tana kallon Umma baki bude ta kuma kasa cewa komai, a hankali Umma tace “Ban san yanda khadijah xata dau batun nan ba, am afraid….” A hankali baby ta dauke kanta tana sake nanata sunan yayanta a xuciyarta, to how comes??? Da kyar ta kalli Umma tace “Barristern fah?” Umma tace “Shi ya bar masa… For some concrete reasons which I found out to be nothing but the truth, Aliyu shi ne kadai rufin asirin khadijah da yaron nan, toh amma ba lallai ta gane hakan ba, ban san ta ina xan fara sanar mata ba” Baby ta sauke ajiyar xuciya, lkci daya jikinta yyi sanyi tace “Umma kar a gaya mata, she shud just see for her self, xasu sasanta kansu can din” Umma tace “I thought as much… Haka yawanci kowa ke ce min” Tagumi baby tayi ta rasa wanne xata yi a ciki, farin ciki ko bakin ciki, Umma tace “Tashi ki je ku gama shiryawa lkci na wucewa khadijah, har an gama kai kaya can gidan” Baby ta mike jiki ba kwari ta fita, tana komawa daki ta ci gaba da shirya ma khadijah few abubuwan da tace mata, Shureim ne ya shigo dakin da shadda irin wanda Sudais yasa ranan da hularsa, sai sheki kayan suke sun masa kyau sosai, tun wayewar gari sai sannan khadijah ta gansa, ta xaunar da shi kusa da ita tana kallonsa a hankali tace “Where have you being today?” ya wara mata ido yace “Uncle ne ya tafi dani since, mun dawo yanxu, Anty daxu Umma tace min baki da lafiya, me ya same ki” Shiru tayi bata ce komai ba, Ganin yanda yake kallonta ta rungumosa a hankali tace “Ae na samu lafiya yanxu” yace “Anty kinyi kyau sosai” Murmushi tayi ta ja hancin sa tace “Kai ma kayi kyau sosai, wa ya kawo maka kayan nan” Yace “Uncle, shi ma ya sa irin nawa, na tambayesa Ina na Sudais yace ya ajiye masa nasa” Shiru khadijah tayi tana kallonsa, ya kamo hannunta yace “Anty what are they celebrating today?” Baby dake gefe sai kallonsu take ta dauke kanta a hankali, sai a sannan tayi mugun ganin dacewar abinda Barrister Sudais yyi, shkkn sai su hadu su rungumi d’an su, khadijah ta sunkuyar da kanta tuna irin xagin da Jiddah tayi ma yaron daxu ta kirasa da shege mara uba, hawaye ne ya kawo idonta sai dai bata bari ya gani ba, Jikin baby yayi sanyi don duk tana lura da ita, ta juya ta ci gaba da abinda take, Shureim ya taho gunta yana gaisheta, ta rungume sa murmushi dauke fuskarta tace “Har kun dawo boy” ya gyada mata kai, shidda saura motocin tafiya da amarya suka iso gidan, nasiha sosai Mum din sadeeq da wata frnd din Umma suka yi mata, Kanta a kasa take saurarensu hawaye na sakko mata, ita kam bata samu gatar nasihar Uba ba, kalma daya Umma ta iya yi mata a lokacin bayan su Umman sadeeq sun gama “Allah maki albarka” hakan yasa khadijah taji dadi sosai, Shaheedah ta daga ta suka nufi kofa baby da wata kawarta na biye da su a baya, banda kuka babu abinda khadijah take duk jikinta yayi sanyi, duk aka bi ta da kallo cike da tausayinta, Baby da frnd dinta Hafsat sai mahaifiyar Shaheedah wato aminiyar Umma suka shiga mota daya da khadijah, sauran yan rakiyar Amarya suka shiga sauran motocin, Jikin baby bai gama sanyi ba sai da taga sun iso gidan yayanta, duk tausayin khadijah ya cikata a xuciyarta ta dinga addu’ar Allah yasa shock din ganin Aliyu as mijinta baxai yi affecting dinta sosai ba, dad’d’adan kamshin turaren wuta ke tashi ta ko wani angle a gidan, ga sanyin ac, parlorn so chill, har lkcn kuma su Siyama da kawayensu da frnd din Mumy suna gidan suna jiran Amarya, Su Hajiya Sajeedah suka wuce da khadijah well furnished bedroom dinta, ita dai har sannan fuskarta a rufe yake bata san kalan gidan ba gashi tun shigowar su gabanta ke faduwa ga hawaye ya ki tsaya mata duk jikinta yayi sanyi, ana xaunar da ita gefen gado ta riko baby cikin rawar murya tace “Stay beside me plss don’t leave me” a sanyaye baby ta xauna kusa da ita tana rike da hannunta, khadijah ta rike ta gam ta kwanta jikinta. Sai kusan bayan isha duk aka watse gidan har su Siyama suka wuce, sai da su Hajiya Sajeedah suka kara mata nasiha kan xamantakewar aure kafin su wuce su ma, gidan ya rage daga ita sai baby da Hafsat, kuka kawai khadijah take don tana ganin ko wani lkci jiddah xata iya shigowa gidan, Baby har ta gaji da lallashi tayi tagumi tana kallonta, yau kam tasan yayanta xai sha lallashi, d’an murmushi tayi dai dai lkcn da wayarta ya fara ring, Hafsat ta mika mata taga Aliyu ke kiranta, kallon khadijah tayi kafin ta daga ta kai kunne hade da sallama, shiru ya d’an yi kafin yace “Ku fito sai a ajiye ku gida yanxu” Tace “Toh” kamar khadijah taji abinda aka ce ma Baby tana kallonta a tsorace tace “Waye ya kira ki?” Baby ta sauke idonta tace “Mijin ki, mu xa mu wuce yanxu Iman, Allah ya bada xaman lafiya” khadijah ta fashe da matsanancin kuka tace “Na shiga uku, me yasa baxa ku kwana ba don Allah kar ku tafi, ki bani wayar xan masa magana” dariya ta ba baby amma bata yi ba tace “Gobe fa da safe xan xo Iman” cikin kuka sosai Khadijah tace “Don Allah ki rufa min asiri ki kwana” Baby tace “In dai gidan nan ne wllh baxan kwana ba, gwara ki hakura gobe in dawo, idan kuma kika ban haushi in ki xuwa goben ma, ko a kauye an daina haka kina abu kamar wata yarinya…” Dariya kawai Hafsa take don khadijah ta bata dariyan, Baby ta mike ta hade rai tace “Mu je Hafsah, ji wani abu da take fa kamar yar yarinya, ko yara sun daina haka, balle ita wayayya” Da haka baby ta samu fa fita Hafsat na biye da ita, Ban da kuka babu abinda khadijah take tana kallon kofar har suka fita suka rufe, Baby ta ji tausayin ta har ranta, amma tasan idan ba haka ta yi mata ba sai ta iya ma biyosu, A waje ta tadda Aliyu tare da Sudais a tsaye jikin motar sudais din, da alama su suke jira, Baby tayi kasa da kanta tace “Ina yini yayanmu” yace “Lafiya lau” Hafsat ta gaida Sudais sannan ta gaida Aliyu tayi masa fatan alkhairi a aurensa, murmushi kawai yyi bai iya yace mata komai ba, Sudais yace “Alryt, sai da safe Dr” Aliyu ya kallesa a hankali yace “Baxa ka shiga ba?” Ya bude motarsa yana d’an murmushi yace “Gobe xan xo in sha Allah” Aliyu bai iya yace masa komai ba, can ya kalli Baby yace “Ku shiga xai yi dropping din ku gida” Ta d’an buda ido, Aliyu ya matso kusa da ita da damuwa yace “Did she know….” Baby ta girgixa masa kai a hankali, sauke idonsa kasa yyi, Hafsat ta bude back seat ta shiga, Bayan few seconds ya kalli baby yace “Don’t keep him waiting, ki shiga motar ku wuce, sai da safe” A hankali baby tace “Yayanmu wllh kunyarsa nake, daxu da safe na gama tsigale shi a waya I never knew makirci matarsa ta hada masa” Aliyu ya bude ido yana kallonta, ta marairaice tana kallonsa, yace “Ki basa hakuri idan kin shiga motar” shiru tayi, ya gyada mata kai yace “Yea, do that” a hankali tace “Toh sai da safe yayanmu” daga haka ta xaga ta shiga front seat ganin Hafsat baya ta shiga Aliyu ya bi ta da kallo, Tana shiga motar ta rufe ta kasa kallon Sudais, bayan ya tada mota ba tare da ya kalleta ba yace “Good evening” sai a sannan ta kallesa dai dai nan shi ma ya kalleta, Murmushi tayi cike da jin kunya tace “Ina yini” yace “Lafiya lau” a hankali tace “Am soo sorry for what I did daxu da safe don Allah kayi hakuri” kallonta yayi da kyau, sai kuma yyi murmushi yace “Wai dama ke kika kirani?” xaro ido tayi ganin ashe ita kadai ke ta haukanta shi bai ma san wa ya kirasa ba, wani murmushin ya kuma yi yana shafa kansa ya ja motar yace “I bet da muna kusa har duka sai kin kai min” sauke kanta kasa tayi bata ce komai ba. Tun da Aliyu ya shiga gidan gabansa ke faduwa, ya kashe wutan parlorn da kyar ya haura sama, ya fi minti daya tsaye kafin ya bude kofar bedroom din da khadijah ke ciki, tana xaune can karshen gado ta hade kanta da gwiwa tana shesshekar kuka, ya kasa karasawa cikin dakin, a hankali ya kai hannunsa kan switch dake jikin bango ya kashe wutan dakin, da sauri ta dago kanta, ya rufe kofar a hankali, cikin rawar murya tace “Barrister ka kunna plss…”

Back to top button