Hausa NovelsSakayyah Complete Hausa Novel

Sakayyah 44

Sponsored Links

 

SAKAYAH

 

44

 

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

 

 

 

*Dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn, masu cewa wai sun goda suga number’n nayine, ko kuma a’a bari dai in na shirya zan sake miki mgn, ko kuma yanzu dai kuɗin bai cikaba tukun sai sun cika, ko kuma a wanne gari kike, kai munyi nisa, toh in ba iyayiba ai duk nisan state da kike ba ruwan mota ba inda bazai kai mikiba, nake turawa ƴan ƙasashen wajema. Kuyiwa Allah da Manzonsa in dai in kinsan Baki shirya sayan kaya ba ku daina min mgnar ku bari sai kun shirya,kada kizo ki ɓata min lokaci a banza, wlh ni na tsani harkar karanta, duk bayani na gamayi in dai saya zakiyi ga kuɗin kaya ga account no ga numberta ai sai ki biya kawai kafin kimin mgn. Tunda dai ga alamominshi da duk illar da yakeyi na faɗi in kina dashi faƙat in babu kada ki wani zo kice min bayani dan ko kinzo iya bayanin da zan miki kenan*

Alamomin infection sune kamar haka. Rashin sha’awa. Ƙaiƙayin gaba Kiji idan ya fara miki ƙaiƙayi kamar zakiyi hauka. Warin ko ƙarnin wurin. Fitar farin Ruwa mai fatsi-fatsi. Ƙurajen su ɗan fetso ƙananan ko ƴan manya, melewar fatar wurin, Tusan gaba. Bushewar gaba, Rashin ni’ima. Buɗewar gaba, domin har budurwa infection na iya buɗata. Ciwon mara ko ciki mai tsanani yayi al’ada, rashin haihuwa, domin har baƙin mahaifa take toshewa. Ko kirinƙajin wani abu na miki yawo ƙasan mara, ko jin zafi yayin yin fitsari, da kuma saduwa, da dai sauran abubudann ban  lissafa. Sune manyan alamomin infection.

Shin kin kuwa san illar da infection keyi miki, amman kinajin ɗaya daga cikin alamominta kinyi bulum buƙui da ita a jikinki. To bari kiji illolin infection wato cutar sanyi.

Rashin haihuwa, ƙyara da hantara a wurin miji domin muddin kina tare da ita baki da wata daraja a idanu nai, sabida ƙyamas kike ba damshi bare wata ni’ima mai Taste, Kinga kenan shinfida ta lalace, in kuwa shinfiɗa ta lalace dole kiga sauyin fuska, domin su maza dole sunason wurin da kwaranya, zaki kasance baki da wani daɗi da ɗumin da mai gida ke buƙata. Kinga duk tsabtarki da kyanki da iya girkinki shinfidarki ta zama lami. Kiyiwa Allah ki nemawa kanki lafiya ki samawa mijinki da ke kanki nitsuwa.

KADA KUJI IYA WANNAN DOMIN AKWAI MUGUN INFECTION WANDA BAYA BAYYANA KANSA. Wanda kawai sai dai kijiki, kamar kwalta kin bushe ƙyamas ya dauke miki dukkan sinadaran ni’imomin ki, da sha’awarki, duk kayan matan da zakisha a wofi zadai kiji ƴan uwa da abokan arziƙi da ƙawayenki na yaba miki magunguna GARKUWAR MA’AURATA, amman ke in kinsha jiya I yau,  duk nacin oga da yi miki wasannin bazaki ji sha’awa ba, toh wlh muguwar infection ce, wacce bata bayyana kanta har sai ta gama yi miki rugu-rugu. Ta lalata miki zaman aure. Lokacin da zata bayyana sai kiji Doctor’s suna kira miki, ovarian cyst, ko kuma fibrod duk a cikin chronic infection ne yar uwa.

INFECTION set ɗinmu na kowa da kowane Mata, Maza, Bazawara, Budurwa, Maijego, Yara, Ke yar uwa Wlh har maiciki zatasha, bashi da matsalar komai Maganin na Gargajiya ne mai rakake INFECTION ya fito miki dashi, wlh duk nacin infection koda na cikin mahaifane bi’izinillahi ta’ala zaki rabu dashi, cutar infection cutace mai masifar naci, so yar uwa kana dole ki nace masa da maganin set ɗin na 10k ne kuma maganin kala biyarne nasha da kala uku na tsarki ɗaya na shafawa ɗaya. Yar uwa idan har kin saya to kiyi ƙoƙarin kisha da mijinki, in akwai abokiyar zama, kisa miji ya saya mata, domin ko kin rabu da shin dai ita tana dashi tofa kin kashe macijine baki cire kaiba, ma’ana zai sake dawo miki, idan kuna da yara suma a saya musu, domin tsoron kada ya riƙa a jikinsu musamman ya’ya mata ya buɗa miki ƴa tun tana ƙaramarta, ki aurar da ita miji na muku kallon lalatattun iyaye da baku iya bada tarbiyaba. Saboda yamayin garin yasa ina raba rabin set ɗin in sa miki komai rabi-rabi 5k amman set ɗin 10k ne. Idan kin san a shirye kike ga account number na nan 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA, ki turo kuɗinki kafin kiyi min mgn ta WHATSAPP NUMBER’N na 09097853276 sai ki turo min shaidar biyanki, domin akwaishi Available ko yau kika tura kuɗinki, gobe kayanki zai taho, ina bada sari ko sayan ɗaɗɗaya. Farashin Sari da sauƙi daga kan mutum 3 ko 6 ko 12. Kai ko na mutum 24 kikeso in Sha Allah zaki samu. Please dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn ki bari sai kin shirya. Taku ce dai GARKUWAR MA’AURATA.

 

Da sauri Hajia Bunayyah ta zubawa Didi, idanu sabida a zatonta, lamarin zai zo da gardama ne, ta yadda zasu koma Nigeria da Khausar, ga mamakinta sai taga Didi ta gaza ƙarasa kalmar bakinta, sai juyawa tayi ta fuskanci alƙibla, tare da yin sujudul Shukur cike da yalwataccen farin ciki da yasa hawaye fara zubomata.

Wani irin malolon bakinci ne, ya takari ƙahon zuciyarta, sai kuma tayi ƙasa da kanta, jin Didi na cewa.

“Alhamdulillah wannan mgnar itace mafi daɗi a cikin dukkan bayanan da kikayi mana Innayi kin gama min komai a rayuwata”.

Lamiɗo kuwa sassayyan numfashi ya fesar hakama Bappa Jimeta da kuma Abban Jameel. Hajja Nana kuwa ajiyan zuciya mai nauyi ta sauƙe tare da gyara zamanta cikin jin daɗin nagartar ahlin Modibbo, yanzu matsalarta ɗayace, ta yaya Modibbo zai karɓi Khausar wacce irin tarba zaiyi mata a matsayinta na matar da aminshi ne yayi mishi zaɓinta, bawai dan ita ɗin zaɓin rashi bane, gouron numfashi ta kuma fesarwa tare dayi mgnar zuci.

“Dole in sa ido kafin komawarmu inga irin tarɓa da kuma yanadin da yaron nan zai amshi Khausar a matsayin mata, muddin naga abinda bai minba, ko alamu. Tozarci ko cin fuska, Allah shine shaida wlh bazan bar jikata a wulaƙanta min ita a ƙasar da bata da kowa nata ba.”

Sai kuma  ta juyo kanta ta kali Niyna kakar Modibbo kenan mahaifiyar Abualeey, cikin kamala kawaici mutuntaka gami da aminci tace.

“Ku shirya idan Allah ya kaimu gobe da yamma akwai taro na musamman, wanda dama an shiryashi tun kwana uku baya, don zamu gabatar da Aleey a gaban family’nsa, tuni Fada take amsar bakunar ƴaƴanta da jikokinta na nesa dana kusa, domin wannan shine buri da fatan dukkan ahlinmu. Toh Alhamdulillah gabatarwa ta ƙara armashi tunda da matar Aleey ta aure ta sunnan ma’aki S.A.W. za’ayi taro”.

Sai kuma ta kalli Jakadiya tare da cewa.

“Jakadiya a sanarwa sarki shiri a shirya gangamin gabatarwar da na aure. Kana ki gayawa Gimbiyya Lailai ta tanadi kayan amarya dana ango, a kuma fidda ƙoren al’ada”.

Cikin biyayya da girmamawa Jakadiya ke amsawa da.

“An gabama Gimbiya Shatu”.

Sai kuma ta kalli Sarki Youseep Mouleey tare da cewa.

“A sanarwar faɗa gobe babu zama, kana taron na family ne, idan Allah ya kaimu jibi kuwa za’a gabatar da Aleey a Fada, da kuma bayyanenne matsayinss”.

Yah Salam Didi kam sai wasu hawayen farin cikin ne ke zuba mata wani ba korar wani.

Galadima kuwa da Waziri kawai murmushi sukeyi kai kace anyi musu bushara da al’jannane.

 

Sheykh Jabeer kuwa a  gyaran murya yayi tare da kallon matar amininsa Marigayi Sarki Muhammad Mouley, da ɗan murmushi a fuska yace.

“Da dai kada a yawanta bidi’a a lamarin, kuma da an sirranta shi ko”.

Cikin sauri Galadima yace.

“Yah Sheykh ai Aleey ya sirrantu tsawon shekaru talatin ai yanzu kam lokacin bayyanar sa ce tayi, dole ya fito ko domin girgiza zuƙatan sauran  ɗan burbushi magauta duk da dama suna zaton haka tunda kowa yasan labarin wasiƙar da Innayi ta bari kafin tafiyar kuma a san shi ba a tsinci gawarsa ba kamar yadda ake tsinta na yayunshi da suka gabata, masu fariyar dole sarauta ta bar hannun ahlin Aliyu Mouley, su san cewafa ga wani Aleey mazan”.

Murmushi mai ɗan sauti Sheykh Jabeer yayi dan shi kansa al’amarin yana tsumashi yana tuna mishi irin magautan da suka fuskanta a masarautar Joɗo, shida har tsuntsuwa aka meda mahaifiyarsa. *A Littafin GARKUWA sai gashi kuma ƴar shima ta faɗa irin gidan*

Innayi kuwa cikin yaƙini tace.

“Da izinin Allah su da Aliyu na sai dai kallo basu da zarrar iya cutar dashi”.

Cikin gamsuwa Sarki Youseep Mouleey ya gyara zamansa tare da fuskatarsu kana yace.

“Aje a fara shiri”. Daga nan aka watse taro cike da jin daɗi.

 

Didi ce zaune a bakin gadon ta na alfarma yayinda

Lalla Khadijah da Hafsat dake zaune a gabanta cikin tsananin happy tace.

“Didi kin ko tuna cewa gobene birthday ɗin Aliyu”.

Kai ta jinjina tare da kallon Rahama da ta miƙe zaune tana mai danna wayarta tace.

“Didi kice inyi gayyata ta mu samman”.

Ta ƙare mgnar tana shiga group ensu na  Mouley family.

Didi kuwa cikin jin daɗi tace.

“Ai kuwa Rahama ki gayyata ta musamman domin bikine na musamman.

Sai kuma ta kalli Hafsat tare da cewa.

“Ki kira ƙawarki Islam kuje  Ryad square shopping mall. Ku ɗebo dukkan abinda ya dace, kama daga na amarya da shi Aleey.

Daga nan in kun taso ku biya Marocco Mall ki ku zaɓo dukkan abin buƙata na al’adun amaren masarautar Mouley, Hafsat so nake komai ya zama na musamman ne”.

Cikin sanin manufar mahaifiyar tasu ta ce yanzuma kuwa Didi.

 

Khadija kuwa da sauri tace.

Amman sai munje munga amaryar kafin mu tafi”.

Gyaɗa musu kai Didi tayi tare da cewa.

Nima yanzu zan tafi sashin Niyna dan ance min su Goggonku Salma da Zakariyya sun iso”.

Daga nan ta miƙe ta fita.

Rahama kuma tana gama fesa labarin hidimar da za’ayi a masarautar tasu gobe misalin ƙarfe huɗu na yamma.

Ta kuma shiga group ɗin na ƙawayenta.

Nan ta fesa musu.

 

A masauƙinsu Khausar kuwa bayan su Ummin da Innayi sun dawo cikin farin ciki Ummu ta zauna kusa da Khausar dake riƙe da kwanon ƙasaitacciyar mace da Ummin ta dama mata tun kafin su tafi.

Ƙwaffa tayi tare da cewa.

“Wai Khausar har yanzu baki shanye damun nan ba?”.

Fuska ta ɗan kwanɓe tare da cewa.

“Allah ko Ummi abun babu daɗin”.

Da sauri Asma’u tace.

“Ni dai Wlh yayi min daɗi gaba ɗaya gumbunan da da garukan ɗaɗine dasu, wani garɗi kamar na dabino da aya da kwakwa harda ɗanɗannon zumafa a ciki, Ummi gashi da zaƙin su ƙungiyar alewa da kuma mazarƙwaila”.

Da sauri Ummu tace.

“Toh sha zumami kice mana wanda aka ɗan sha ɗin ma kece kika shanye. da kike koro jawabi haka”.

Yar dariya tayi tare da rufe idonta kana tace.

“Sai daifa gsky kuma duk da kayan dadin akwai itatuwa da jijiyoyi dan naji ƙamshi jijiyar ilanwaddihi ma da ma kwaranyi wanda kike yawan aikena in amso miki wurin Innayi”.

Harara Ummi ta cilla wa Asma’u tare da cewa.

“Dama ai mgni kam bazai yi ɗaɗiba, maza Khausar kafa kai ki shaye”.

Cikin rumtse idanun ta kafa kanta ta fara sha.

Saida tasha kusan rabi kana ta janye kwanon tare da kwaɓe fuska tace.

“Wlh Ummi ni dama can kayan zaƙi bai cika dakuna ba, nafi son abun yaji-yaji kiga mana kazar nan da kika dafa min duk da babu daɗi  amman dana zumbuɗa yaji na cinyeshi fes. Kuma Kinga Wanda Aunty Hajara ma ta kawo min na cinyeshi. Shi kam ma yafi rashin daɗi dan da ƙyar naci tanata zagina wai dubu ashirin da takwas ta biya AYSHA ALIYU GARKUWA ta dafa minshi wai zuciyar farin ragone”.

Haɗe fuska Ummi tayi tare da cewa.

“Kuma wannan ɗinma sai kin shanyeba”.

Jin haka yasa ta kafa kai ta shanye, tare da ajiye kwanon kana tace. “Alhamdulillah na gama”.

Cikin sauƙe numfashi Ummi tace.

“Yanzu muka dawo daga sashin kiran da akayi mana, munje bisa jagorancin innayi”.

 

Da sauri Asma’u tace.

“Ummi kunga Yah Modibbo?”.

Kai ta jujjuya mata tare da cewa.

“Bamu ganshiba, baima san munzoba, innayi ma sunce ta bari sai gobe zata ganshi”.

Taɓe baki Khausar tayi tare da cewa.

“Uhmm me ake ta ɓoyeshi sai kace kuɗine shi ko zinari”.

Zura mata ido Asma’u tayi tare cewa.

“Yoh ba doleba, sun san akwai mai ƙar mishi kallo har gashin ƙeyarsa ta iso”.

Harara ta cillawa Asma’u tare da cewa.

“Waya ma damu da dashi”.

Murmushi Ummi tayi  tare da faɗin.

“Yanzu dai tashi kiyi Wonka, tunda dilken ya kai awa biyu a jikinki”.

Da sauri tace to, tare da miƙewa ta nufi bathroom din.

 

Asma’u kuwa falo ta nufa jin innayi na kiranta.

 

Zaune ta sameta dasu Hajia Bunayyah da kuma su Aunty Hauwa duk dai waɗanda suka zo tasu.

Gyara zama tayi tare da kallon su ɗaya bayan ɗaya kana tace.

“Idan Allah ya kaimu gobe za’a fara hidimar bikin Khausar da Modibbo kamar yadda al’adar masarautar Mouley takeyi.

Dan haka ku shirya karfe huɗu na yamma ne za’a fara.

Zuwa Maggarib an gama na gobe sai kuma zuwa jibi.

Cikin tsinkewa da lamarin cigaban da Khausar ta samu Hajia Bunayyah tace.

“Uhmm Allah ya kaimu”.

Sai kuma ta yunƙura zata tashi.

A hankali ta koma zaune jin muryar Hajja Nana na cewa.

“Bisa alamu dai Khausar taci ribar ƙin auren ɗan mayu, abu ya haɗu, sunna ta haɗu da farilka, sakekke ya haɗu da sakekkiya, wato bazawari ya samu bazawara ɗan maye da ƴar Mayu, jikar tsarki da jikan sarki”.

Cikin takaici Hajia Bunayyah tace.

“Kamar yaya kuma Sunan ta hadu da farilla?”.

Kai Hajja Nana ta jinjina cikin isa kasaitar data motsomata yau tace.

“Eh ɗan babban Sarkin Mouley na kasar Marocco ya auri jikar babban Sarkin Gombawa na ƙasar Nigeria jihar Gombe, kin san su dama su Khausar kirarinsu Gombawa ɗiban fari ba’a kwana dasu ba a tashi dasu, Gombe doma hamadar sarki lahirar sulaimanu”.

Da sauri Innayi ta kalleta cikin rashin fahimta ita kuwa Hajja Nana cikin ƙasaita tace.

“Yoh da ji kikeyi ku kadaine keda masarauta, to idan baki saniba, Sarki  Buba Yero shine tsohon mijina kuma kakansu Khausar,  barina  Gombe da mahaifin Khausar da bappanta Muhammad, ne yasa masarautar ta koma hannun kaninsu ɗan abokiyar zamata, kuma shi har yanzu jira yake Yayanshi bappan Khausar yaje ya karɓi ragamar mulki dan su masarautarsu sunada imani da ƙaunar juna babu wani tsaface-tsaface, nice na hana sabida ni kwanciyar hankali ƙannena yafi min”.

A hankali Ummi dake jiyo Hajja Nana ta fesar da numfashi tare da cewa.

“Haba sai haka mana ƙasaita da isar Hajja Nana tayi yawa, ita kanta Khausar ƙasaitarta da kwarjinin ba irin na normal mutane bani, kwarjinin ta yawa gareshi.

 

Sai kuma ta kalli Khausar da fitowar ta kenan daga Bathroom.

“Masha Allah”. Shine abinda Ummi ta faɗa sabida ganin wani irin sheƙi da ƙellin da fatar Khausar keyi kai kace tarwaɗace, tsabar farin da tayi kace balarabiyace.

 

Gashin kanta dake tubke ta zubawa ido.

Sai kuma ta kalli Khausar ɗin dake tsane jikinta tare da miƙa mata.

Man shafawa, da dauko handdryer kana ta dawo ta bayanta.

Tare da fara busar mata da gashin dan ya ɗan jike. yaje mata tayi tare shafa mata mai.

Ita kuwa Khausar mai take shafawa a jikinta kusan a tare suka gama.

Ajiye handdryer ɗin Ummi tayi tare da juyowa gefen gadon inda akwatuna set ke jere,  ɗaya pink ɗaya blue, wanda Ummi ce ta bada aka haɗawa Khausar ɗin Kayan lefe, kana kuma shine aka kai gidansu dangi da abokan arziƙi suka gani.

Wanda suma Hajia Bunayyah dai bata samu abin kushewa ba.

 

Na forkon ta buɗe wanda tun a gida Asma’u ta haɗa dukkan abin buƙata da kuma kayan da Khausar ɗin zata saka har gama bikin.

Wata Dubai Abaya Ummi ta zaro mata, Black color sai kuma zare golding color da aka yiwa rigar aiki zuɓi na musamman mai masifar kyau da ratsin fari kaɗan  rigar irin mai ɗan faɗin nanne musamman daga sama. sai kuma ta zaro mata wani tattausan mondo Wanda bazai wuce iya guiwarta ba, sai bra su duka fararare, turare ta zaro kusan kala uku ta feshesu dashi. Kana ta ɗauko Kulaccar sirri wacce ta saya wurin AYSHA ALIYU GARKUWA, miƙa mata tayi tare da cewa.

Gashi ki shafa wannan.

Amsa Khausar ɗin tayi tare da cewa.

“Ayyah Ummi a tubke min gashin nan”.

To Ummin tace tare da fara tubke mata shin.

Tana gama ta nufi falo tare da cewa.

In kin gama kizo, kai kawai Khausar ɗin ta gyaɗa mata.

 

A can Falo kuwa Hajia Bunayyah ce ta miƙe jiki a salube ta shige ɗakin da nanne masauƙinsa inta da Aunty Hajara da kuma Aunty Ruƙayya.

Da sauri ta maida ƙofar ɗakin ta rufe tare da dannawa Hajia Lami kira a wayarta.

Bugu ɗaya ana biyu Hajia Lami ta ɗauka tare da cewa.

“Mutanen Marocco yaya akayi?”.

Cikin fesar da numfashi mai zafi Hajia Bunayyah tayi kwafa tare da cewa.

“Wllhi Allah Hajia Lami munyi babbar asara daba Samira wannan yaron ya auraba. Na rantse miki da Allah munyi asarar samun daular duniya.

Wannan shegiyar yarinya  mai idanu kamar na mujiya ko yaushe suna lunshe kamar mai jin bacci anya ma kuwa ba idanun dunane da ita ba.

Kinga tayi nisa ta barmu da Naseer ɗin da ubansa ko Sarkin tasha bai taɓa samuba, ke kuwa ta bar miki ƴa da wari da yoyon ƙazanta”.

Nannauyan numfashi Hajia Lami ta fesar tare da cewa.

“Toh yanzu me abinyi?”.

Cikin tsananin hasada Hajia Bunayyah ta buga hannunta da jikin gini tare da cewa.

“Wallahi Allah ni dai na rantse da Allah, sai na kashe auren nan, koda zan tafi tsirarane sai na watsa aurenan, muddin ina raye wlh Khausar bazata ji daɗin rayuwarta a gidan nan ba, idan zaki zo mu haɗa hannun da ƙarfe mu tumɓuke auren nan, mu shiga da Samira gidan to ki fara shiri, domin ina dawowa zamu bazama”.

Cikin ƙeƙashewae zuciya Hajia Lami tace.

“Ai ke dai Allah ya dawo dake lafiya, Ƙawata na sama mana labarin wani ƙasurgumin boka a ƙasar Niger cikin dajin Damagaran ance min aikinshi kamar yankan wuƙane, babu haufi shi bazama ka biyaba sai buƙatar ka ta biya”.

Cikin yaƙini tace.

“Ke dai ki shirya ina dawowa zamu tafi”.

Daga nan suka katse kiran kana ta fito.

 

A falon kuwa da sauri su Ummi suka ƙali ƙofar falon jin sallamar Jakadiya da kuma su Lalla Khadijah da Hafsat.

Cikin sakin fuska Ummi da Innayi suka amsa tare da nuna musu wurin zama.

Zama sukayi cikin sakin fuska da cikekken fulatancinsu da suka iya ta sanadin Didi suka kalli su gaisa cikin mutumtaka.

Jakadiyace ta kalli Lalla Hafsat tare da juyowa ta kalli innayi kana tace.

“Dama yayun Aliyu ne suka zo ganin ƙanwar tasu tare da marabtanta.

Cikin jin dadi Ummi tace.

“Ayyah to babu laifi barin in kirawota”.

Sai kuma ta mike ta nufi dakin da Khausar take.

“Masha Allah diyata kinga yadda kikayi kyau kuwa”. Murmushi tayi tare da rufe fuskarta da tafukan hannunta.

Ita kuwa Ummi kamo hannunta tayi ta ajiyeta tare da cewa.

Zo mu je ki gaisa da yayun Modibbo.

Da sauri ta sunkuyar da kai ganin yadda Ummi ke gyara mata tarhan da tayi da gyalen abayar sosai tayi masifar kyau ta fito cas da ita a matashiyar budurwar yar kimanin shekaru 19 zuwa 20. Duk da rigar nada faɗi bai hana kyan surar jikinta bayyana ba.

 

A hankali suka fito falon.

Khausar kam kanta a ƙasa take wani irin amintaccen taku mai cike da nitsuwa.

 

Da sauri Lalla Khadijah ta miƙe tsaye lokacin da suka iso tsakiyar falon.

Hannunta ta buɗewa Khausar tare da faɗin.

“Wow  Masha Allah, Didi dai ta samu ƙarin diya wannan ai in an ganta da Rahama kai kace tagwayene”. Murmushi mai yelwa Lalla Hafsat ma tayi tare da miƙawa Khausar hannun a hankali Khausar ta ɗan janye jikinta dan jikin Lalla Khadijah ta ɗan saketa.

 

Ruggumeta Hafsat tayi tare da cewa.

“Masha Allah,  Khausar muna farin ciki da shigarki Mouley family. Allah ya baki hikima da basirar zama tsakiyar wannan Fada”.

Kusan a tare suka amsa da Amin ita kuwa Khausar yatsun hannunta take ɗan murza tare da ɗan rusunawa kana ta gaidasu.

Amsawa sukayi suna mai ƙare mata kallo. Cikin ɗan sakin fuska Hafsat tace.

“Ai wannan  komai nata kamar na Rahama zaiyi mata dai-dai”.

Cikin girmamawa Jakadiyarsu tace.

“Sosai ma kuwa”. Ita kuwa Hafsat hannun Khausar ta kamo tare da cewa.

“Takalmi sise nawa kike sawa”.

Cikin sanyin murya tace.

“37”. Da sauri Khadijah tace.

“uhm jinjina sise ɗin Rahama kenan”.

Sai kuma ita Khadijah ta kamo hannun Khausar tare da ajiyeta gefen Innayi kana tace.

“Zauna abinki. Didi da Niyna sunyi miki Barka da zuwa, masarautar Mouley. Yanzu mu zamu fita ne.”

A hankali tace.

“Allah ya kiyaye hanya.”

Amin sukace a tare sai kuma suka ɗan kalli Asma’u tare dayi mata murmushi suke.

“Ke me sunanki?”.

“Asma’u”.

Murmushi Khadijah tayi kana tace.

“Yauwa toh in ba matsala innayi zamu tafi da ita, ai kin san sise ɗin Khausar da kalanta ko?”.

Cikin fara’a Asma’u tace.

“Sosai ma kuwa, Nama fita sanin abinda yake mata kyau”.

Dariya sukayi ganin hararar da Khausar ta cilla mata..

Ummi kuwa murmushi kawai tayi.

 

Daga nan suka fita da Asma’u.

 

Sune basu dawoba sai gab da Maggarib.

 

Acan Side din da Modibbo yake kuwa.

Zaune yake shi da Ibrahim da Dr Jameel.

Cikin tsuke fuska ya kalli Dr Jameel dake zoro wayarsa daga aljihu.

“Baby”. Ya faɗa a saman lips enshi.

Sai kuma ya tsaida idonsa kan Modibbo da ya wani irin tsaresa da idanu.

A hankali yace.

“Yah dai Malam kallon nan fa?”.

Fuska Modibbo ya kuma tsukewa tare da cewa.

“Kaji tsoron Allah, Dr J kasani. Abinda kakeyi kana tafiya cikin fushin Ubangiji ne, kuma masifar zunubinka zaiyi ta bibiyarka tun anan gidan duniya, kasan cewa abinda kayiwa ƴaƴan wasu za’ayiwa ƴaƴan ka, shin me ribarka a cikin in har ka jazawa ahlinka. Ka tuna shifa zina tsananin muninsa yasa Allah baice kada kuyi zinaba,  cewa yayi kadama ku kusaceshi fa. Shifa mazinaci baya zina har sai an zare mishi imaninshi. Kasan kuwa abinda Allah ya tanadarwa mazinata abinsha a cikin jahannama?”.

Cikin tsananin sanyin jiki Dr Jameel ya rumtse idanunsu tare da cewa.

“Nifa shiyasa badon Abualeey da kansa yace min dole in kasance kusa da kaina wlh bazanzoba sabida na lura kai mutumne mai tsaraɓe-tsaraɓen halal da haram”.

Cikin takaici Modibbo yace.

“Koda baka zo inda nakeba kasa a ranka in dai ina cikin ƙasarnan, sai na kasance tare da kai, na kuma yi al’ƙawari zan ƴaƙi shsiɗanin dake tare da kai, in Sha Allah sai ka dawo managarci tamkar J na”.

Murmushi Dr Jameel yayi tare da kallon hadimai guda huku da suka shigo da manyan jakukkuna guda biyar  masu ɗauke da tambarin Anfaplace mall Marocco.

Da sauri Ibraahim ya miƙe tare da cewa.

“Ku shigo dasu cikin bedroom kada ku barsu a nan”.

Jin hakane yasa suka bishi a baya.

Kusan a tare suka shirya kayan cikin wodurob.

 

Daga bisani suka fito falon, a tsaye ya samu Dr Jameel.

“Mujeko  Ibraahim”. Cewar Dr Jameel.

Kai Ibraahim ya gyaɗa tare da bin bayanshi sai kuma ya juyo ya kalli.

Moddibo dake cewa.

“Wai dan Allah Ibraahim sai yaushe za’a buɗeni in samu zuwa jam’in salla, wlh abinfa yana damuna.

Sassan numfashi Ibraahim ya fesar kana a hankali ya juyo ya dawo gaban Modibbo tare da cewa.

“Kayi haƙuri Yah Aleey in Sha Allah gobe dai a jam’i zakayi sallan magarib. Akwai babban dalilin ne da yasa ba’a barka ka fitoba.

Ƙwaffa Modibbo yayi tare da lumshe idonsa Allah ya sani suna ƙona mishi rai da batun hanashi jam’i da wotoyinsa.

 

Shi kuwa Ibraahim juyawa yayi yabi bayan Dr Jameel suka tafi.

 

Washe gari tun safe Dr Jameel da Jabeer bin Jabeer da kuma Ibrahim suka shigo wurin Modibbo.

Tare da wani Kekkyawan matashi wanda bazai wuce sa’an Modibbo ba.

Cikin sakin fuska matashin ya bawa Modibbo hannu tare da cewa.

“Sunana Zakariyya Khallin”.

Cikin ɗan sakin fuska Modibbo yace.

“Masha Allah”.

Ibrahim ne ya amshi mgnr da cewa.

“Yah Aleey Wannan ɗan Goggo Salma ne  ƙanwar Abualeey. Shi a India yake shima likitane, taron gabatar da kaine ya kawoshi.”

Murmushi Modibbo yayi tare sake bashi hannun, shi kuwa Zakariyya ruggume Modibbo yayi tare da faɗin.

“Duk da zumuɗin Mami na rigata ganin ɗan yayanta”.

Shi kuwa Modibbo Ibraahim ya kalla jin yana cewa.

“Dr Jameel ma ɗan Goggonmu ne Aunty Sahrah itake bin Goggo Salam, kuma babanshi Aminin Abualeey ne ɗan ƙasar Turkey, duk dangin babanshi suna can”.

Dr Jameel kuwa numfashi ya ɗan fesar kana yace.

“Ni ya labarin Yusuf ne, kwana biyu bamuci wayaba”.

Da sauri Zakariyya yace.

“Ya tafi Mexico kasanshi ya nacewa Zeeyada yar Lalla Hafsat”.

Sai kuma ya kalli Modibbo tare da cewa.

“Yusuf ɗan Unclee Haroon Mouley ne, ƙanin Unlee Youseep Mouleey”.

Cikin fahimta Modibbo yace.

“Na fahimta, toh amman kuma tunda nazo banga Unclee Haroon ɗinba”.

Cikin sanyi Dr Jameel yace.

“Dashi da Mamina, da Abbana duk rana daya sukayi haɗari, su sun rasu shi kuwa har yau baida lfy tsawon shekaru ashirin da biyar kenan”.

Cikin sanyin jiki da tsananin tausayi Modibbo yace.

“Allah sarki Jameel Allah ya jiƙansu da rahama yasa sun huta shi kuma Unclee Haroon Allah ya ya bashi lfy”.

Da Amin suka amsa baki ɗayan su.

Shi kuwa Modibbo cikin sanyi ya kalli Dr Jameel tare da cewa.

“Dan J kabar abinda kakeyi ka zamewa Aunty Sahra da Abba al’waladussaliha ko dan basa raya ka zame musu sanadin samun lada”.

Cikin sanyi jiki Dr Jameel yayi ƙasa da kansa yana mai taunan lips inshi na ƙasa.

Shi kuwa Modibbo a raunace yace.

“Mu kuwa zamuci gaba dayi maka Addu’o’i Allah ya shiryeka”.

Amin suka amsa a tare.

Sai kuma Ibrahim yace.

“Yauwa mu shiga daga ciki masu gyara zasu shigo gyara nan ɗin”.

Toh sukace kana suka shiga Corridor nan tare suka shiga ƙofar nan ta dama inda Modibbo yake, a falon suka zauna.

Zamansu ba jimawa Rahman ta shigo da hadimai da sunka kawo musu breakfast.

 

Acan Side ɗin dasu Khausar suke kuwa, suma tuni an kawo musu breakfast, dama dukkan abin buƙata.

 

A nan wannan falon kuwa, zuwa bayan an isar da sallam la’asar  duk an gama ƙawatashi da shiryashi irin shirin nan na al’farmar da kamala.

Kujerun gaba ɗaya an mannasu da ginin duk da girman falon wai dan a samu ya ƙara girma.

Wata kujera mai zaman mutum biyu aka ajiye daka san tsakiyar falon. Sai kuma wasu datsa-datsan Turkiy Carpet masu masifar kyau da taushi. Da aka shimfiɗa a gaban kujerar, wacce duk ta inda ka shigo zaka kalli waɗanda ke ka kujerar. Sai kuma wasu tukwanen kasa masu zanen ɗawisu da aka jere gefe da gefen kujerar yayinda daga sama tukwanen kuwa, gashin gezan ɗawisunne a cikin mai cikekken launi daban-daban, sai kuma wani tim-tim da aka ajiye a guda biyu a gaban kujerar wanda da bisa alamun anan waɗanda zasu zauna kan kujerar zasu daura sawunsu.

Sai kuma hadimai guda uku ɗaya na bayan kujerar ɗaya na gefen dama ɗaya na gefen hagu.

Kana duk inda ka wulga idanunka a falan kaskon turaren wutane mai fasar da sassayan kanshi.

Sai kuma sanyin ac dake ratsa ko ina, an sassake labulayen, tare da kuna wutan falon baki ɗaya a ƙalla falon zai iya ɗaukan mutun settun zuwa tamanin.

 

A nan sashin dasu Khausar suke kuwa.

Wasu matane guda biyu, aka kawo dan shirya kausar, Kasancewarsu ƙwararrun masu shirya amare, wanda suke zaune acikin masarautar musamman domin gyara da kuma ƙyale amare.

Wata Haɗaddiyar rigar Caftan and Takchitas suka sanyawa Khausar din, wacce ta kasance farace ƙal, mai ɗauke da ratsin adon gold da kuma sky blue wato kalan sararin samaniya.

Rigace me tsananin kyau da takasance traditional wedding dress wanda ƴan masarautar Mouley morocco ke sawa lokacin biki, sosai rigar ta zauna ajikin kausar, tayi mata ɗas tare da k’ara bayyana tsantsar kyaunta, musamman da suka ɗaura mata tsadadden sarƙan gold da kuma ƴan kunne haɗi da awarwaro da kuma zobunan gold, wanda suka ƙara cika adon nata, babban mayafin daya kasance fari ƙal, wanda aka kewaye bakinsa da tsararren ado me kalan sky blue, suka sanya mata akanta, wanda ya sauko har yakai ga ya rufe kyakkyawar fuskarta.

Masha Allah da wannan tsananin kyaun da kausar tayi, wanda kallo ɗaya zakayi mata kasan ta cika mace har mace, saboda tsananin kyaun da traditional wedding dress din yayi mata, a kyawawan ƙafafunta kuwa wani haɗadɗen takalmi irin nasu na sarauta me kalan sararin samaniya suka sanya mata, daya sake k’awata shigan nata. Duk da kafafun nata ba lalle dan innayi ta hana a saka mata.

 

Su kansu sun yaba da kyaun yarinyar domin tunda suke shirya amare basu taɓa shirya amaryar da tayi kyau sosai kamar wannan ba, kai kace asalinta balarabiyar Morocco’n ce, musamman yanda jikinta ke fitar da sihirtaccen k’amshi kulaccar sirri da me matuk’ar ratsa zuciya haɗi da daɗin shaƙa.

 

“Masha Allah, tsarki ya tabbata ga Ubangiji me tsara kyawawan halittun da yayi wannan halittar da ta kasance tamkar farin fure acikin tarin jajayen furanni, Allahumma Barik.”

 

Cewar Lalla Khadija da shigowarta kenan, cikin shigar ƙasaita.

 

“Masha Allah.”

Ta kuma faɗa tana me miƙawa su Asma’u, Dija da kuma Asiya kayan dake hannunta, wanda suna ɗaya daga cikin kayan da aka kawowa kausar jiya, dogayen riguna ne guda uku masu matukar kyau.

“Ga wannan kuma ku sanya, domin naga kaman kune ƙawayen amarya.”

Amsa sukayi suna godiya..

 

 

*Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa ki biya ki karanta abinki cikin Salamah 1k nefa kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP NUMBER’N 09097853276, in tura miki littafin ki karanta abinki cikin salama kana in saki a Group ɗin*

 

 

 

By

*GARKUWAR MARUBUTA*

Leave a Reply

Back to top button