Hausa NovelsSakayyah Complete Hausa Novel

Sakayyah 47

Sponsored Links

 

SAKAYAH

 

47

 

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

 

 

 

Assalamu alaikum mutanan arziki masoya kamshi ma abota kamshi Amaren kamshi masu jargon kamshi Yammata wadanda sukasan darajar kamshi ni Aysha Aliyu Garkuwa na kawo muku tallan wasu Amintattun turarukana masu matukar kamshi da Kama jiki

Masu saukin farashi sannan ga biyan bukata

Yarhjya_incense_and_more

Ta shirya tsaf domin ta gwangwajeku da Turaruka na alfarma

Farar khumrah

Bakar khumrah

Turaren Wanka

Oil 6ml 1

Oil 12ml 1

Turaren fesawa 100ml 24 hours guda 1

Duka Akan 8k kacal

Sannan kayanta suna tafiyane da guarantee duk wacce tasiya taji babu kamshin nan na alfarma ko kuma basuda lasting to tayi alkawarin mayar muku da kudinku

Wannan garabasar zata kare on 5th September insha Allah

Ku hanzarta ku mallaki naku domin kayan yarhjya babu Danasani a cikinsa saidai kuyi alfahri da siyan kayanta

Account number 1419787445 Amina Umar usman access bank

Kitura evidence of payment to

08092664954

Kuyi saving number TA domin ci gaba da ganin Turaruka Kala Kala

Normal price

Bakar khumrah 1500

Farar khumrah 2k

Turaren Wanka 1500

Oils 6ml 800

Oils 12ml 1500

Turaren fesawa 100ml 3500

Turaren fesawa 50ml 2k

Kayanmu available ne a koda Yaushe

Akwai turarukan wuta na jiki na Kaya Dana daki duka sai Wanda kika zaba

 

 

“Kazo mu koma ciki Maghriba tayi muje muyi alwala mu tafi masallaci”.

Cikin gamsuwa ya gyaɗa kai,

Ibraahim kuwa hannun Moddibo ya riƙe tare da faɗin.

“Yah Aleey daga yanzu zaka riƙa zuwa jam’i yanda kake buri da fata da marari”.

Sanyayyan numfashi Moddibo ya fesar kana yace.

“Alhamdulillah, dan babu abinda nafi bege kamar zuwa sallah jam’i da kuma Innayi na”.

Ya ida maganar tare da bin bayan Ibraahim suka fara tafiya.

Tuni ƴan Uwa sun fiffita falon ya rage babu mutane sai ɗaɗ-ɗaya.

Innayi dake riƙe da hannu Khausar ta nufi wajensu Ummi tare da faɗin.

“Kuzo mu koma masauƙinmu sai kuma gobe idan Allah ya kaimu, za’a cigaba da hidima”.

 

Sheikh Jabeer kuwa da kansa ya nufi inda su Abban Jameel ke zaune yace.

“Kuzo mu tafi Maghriba ta ƙara to”.

Kai suka gyaɗa kana suka miƙe suka bi ta ɗaya ƙofar suka tafi.

Moddibo da su Ibraahim kuwa a hankali suke tafiya cikin nitsuwa auka shiga Corridor da zai sada su da falon Side da suke.

 

Su Khausar kuwa sun fara haurawa kan steps din.

Asma’u ta juya da sauri ta kalli Ummi tare da faɗin.

“Ayyah Ummi bari inje na gaida Yah Moddibo in faɗa masa saƙon Bashir”.

Ƴar dariya Ummi tayi kana tace.

“Bismillah keda ɗan Uwanki”.

 

Kai ta gyaɗa cikin sauri ta juya ta nufi wajensu Moddibo tana faɗin.

“Yah Moddibo! Yah Modibbo”.

Moddibo kuwa Already sun riga sun shiga falon da Dr Jameel ke ciki.

 

Shi kuwa Dr Jameel jiyo motsinsu ne yasa ya sassauta murya cikin wani irin yanayi da yake ciki bisa ga duk kan alamu hirar batsa suke awayar cikin lumshe idanu yace.

“Please Baby kiyi haƙuri muna cikin wani Uzuri ne fa na Fada”.

Murmushi tayi tare da cewa.

“Ok bye bye Amma please kazo Ina jiranka, kasan cewa kwana biyu bamu haɗu ba ina kewarka”.

Ta ida maganar tare da katse kiran.

Dr Jameel na miƙewa su Moddibo na shiga….

 

Cikin yanayin takaicin halayyarsa Zakariyya ya maka masa harara tare da cewa.

“Wallahi kai dai kam Jameel kayi asara,  komai aka shirya da kai da zaran mace tashiga ciki saita ware ka cikin mu, musamman wannan shegiyar Baby na rasa yanda zanyi in raba ka da ita”.

Moddibo dake jinsu ne ya girgiza kai kana yace.

“Alhamdulillahi kaima kenan abin na damunka Zakariyya?”.

Kai Zakariyya ya gyaɗa yana mai cigaba da hararan Dr Jameel dake murmushi yace.

“Sosai ma kaga an tsara fitan nan dashi amma dayake shi Mamajone mayen mata, ni wlh ban na lura da lokacin daya zame ya dawo ciki ba, sai da muka shiga na gane baya tare damu”.

 

Sai kuma Moddibo yayi saurin juyawa jin muryan Asma’u na cewa.

“Yah Moddibo”.

Da murmushi afuskarsa yace.

“A’a Asma’u”.

Asma’u kuwa idanunta ta zare tare da ɗaura hannunta ɗaya akai kana ta buga ɗaya hannunta a ƙirjinta tare da faɗin.

“Yah Jameel”.

Tayi maganar idanunta na kan Dr Jameel dashi ma ita yake kallo.

Cikin sauri Moddibo ya juya ya kalli Asma’u sai kuma ya juya ya kalli Dr Jameel.

 

Cikin yanayin kaɗuwa, mamaki, Al’ajabi ta fara takowa har ta isa gaban Dr Jameel ta tsaya cikin sarkewar murya ta furta.

“Yah Jameel”.

Kallonta Moddibo yayi tare da girgiza kai yace.

“A’a Asma’u”.

Cikin ficewar hayyaci ta ɗaura hannunta akai tare da faɗin.

“Ummiiii kizo ga Yah Jameel”.

Sai kuma tayi baya luuu idanunta sukayi sama.

Cikin wani irin sauri Dr Jameel da tun time data kira sunansa ya zuba mata idanu yana kallon ƙiranta da kuma yanda Ubangji ya ƙawata surarta, lokaci ɗaya yaji wani irin yanayi da bai taɓa jin makamancin sa ba akan ko wacce irin mace da yake mu’amala da ita karon farko yaji wani irin tsarkakekken soyayyar ta ya mamaye masa zuciya.

Azabure ya nufe ta ganin saura kaɗan takai ƙasa ya tallafota jikinsa ta faɗa kan ƙirjinsa asume.

Faɗawa jikinsa da tayi yasa ya koma baya ya faɗa kan kushin ya zauna, hannunsa yasa ya tallafo fuskarta sai kuma ya ɗaga kansa ya kalli Moddibo kana yace.

“Suma fa tayi”.

 

Cikin Sauri Moddibo ya riƙe tsintsiyar hannunta cikin yanayin damuwa yake faɗin.

“Asma’u”.

Ina tuni ta samu kallon Ibraahim yayi kana yace.

“Ibraahim ka miƙo min ruwa”.

Dr Jameel kuwa kallon Moddibo yayi cikin wata kasalalliyar murya gami da shauƙi yace.

“Ya dai kake shiga hurumin daba naka ba, ya ina matsayin Dr sannan ta suma ajikina kake cewa amiƙo maka ruwa”.

Wani kallo Moddibo ya mata tare da watsa masa harara kana ya buga masa tsawa da faɗin.

“Kai Mahaukacin ina ne ya yarinya zata suma sannan ka tsaya kana maganar sai huruminka wani irin hurumi kake dashi a kanta, idan zakayi abinda zata farfaɗo kayi ka wani maƙale yarinya atsakanin cinya haukane akan ka”.

Kallon Moddibo yayi tare da juya idanunsa kana yace.

“Kamar ya kake cewa haukane akaina Ni naga matar Aure”.

Cikin tsawa da hararansa Moddibo yace.

“Koma yayane yanzu kayi abunda yarinya zata farfaɗo”.

Ahankali Zakariyya ya tsugunna kansa tare da bubbuga kumatunta yana kiran sunan da yaji Moddibo na kiranta da.

“Asma’u³”.

Hannunsa Dr Jameel ya janye kana ya ture gefe tare da cewa.

“Dakata Zakariyya nasan kai Likita ne amma wannan ba hurumin ka bane Saboda wannan hiruminane”.

 

Alalace Zakariyya ya banka masa harara tare da faɗin.

“Mayen banza mayen wofi, wato daga ganin Yarinya itama ka ɗaura ƙolafacinka da kwadayin ka akanta”.

Araunane ya ɗago kansa ya kallesu baki ɗaya cikin yanayin gaskiya da gaskiya yace.

“Wallahi ban kalleta da idanun da nake kallon sauran ƴan matan da nake mu’amala dasu ba, na kalleta ne da wasu irin idanu masu matuƙar daraja domin ita mai darace da mutunci”.

 

Tsaki Moddibo yayi cikin hasala da abinda Dr Jameel keyi ya karɓi goran ruwan da Ibraahim ke miƙa masa ya watsa mata afuska amma bata farfaɗo ba.

Langwaɓar da kai Dr Jameel yayi tare da faɗin.

“Dan Allah kar ka jiƙamu Ni nasan yanda zanyi in farfaɗo da abuna”.

Moddibo kuwa cikin mamaki ya zubawa Dr Jameel idanu yana kallon ikon Allah da karfin hali.

 

Cikin lumshe idanu Dr Jameel da har zuwa lokacin yake rungume da Asma’u ya sunkuyo da kanta.

Da wani irin azabebben sauri Moddibo ya riƙe ka sa fuskarsa babu walwala yace.

“Wallahi kada ka kuskura, Idan ka yarda ka kuskura Ni nasan abinda zanyi maka hauka ne akan ka? Ko kuma kayi tunanin itama irin ƴan matan da kake rayuwa dasu ne da zakayi ƙoƙarin kai bakinka kan nata?”

 

Hannunsa biyu ya haɗa kana yace.

“Dan Allah kayi haƙuri Moddibo na rantse da Ubangijin daya busa min numfashi bana kallon wannan Baiwar Allah Asma’u amatsayin matar da zanyi lalata da ita”.

Sai kuma ya furzar da iska mai zafi daga bakinsa kana ya cigaba da cewa.

“Idanuna suna kallonta ne amatsayin matar Aurena, kuma uwar ƴaƴana wallahi bawai kissing ɗin ta zanyi ba ya kuke maidani kamar Bunsurune zanyi ƙoƙarin dawo mata da numfashinta nefa”.

Still babu walwala atare da Moddibo ya gyaɗa kai kana yace.

“Ok”.

Dr Jameel kuwa cikin lumshe idanu ya sunkuyar da kansa kanta kana ya ɗaura bakinsa kan hancinta yana hura mata numfashi.

Asma’u kuwa ahankali taja wani dogon numfashi tare da faɗin.

“Ummi wallahi Yah Jameel ɗin mu bai rasuba ga Yah Jameel ɗin mu na ganshi da rabshi”.

Sai kuma ta buɗe Idanunta  ganinta kwance acinyar Dr Jameel cikin sauri ta yunƙura ta zauna tare da faɗa wa kansa ta rungumesa yayin da take kuka mai tsuma zuciya kana tace.

“Yanzu dama Yah Jameel baka mutu ba, aka kawo mana gawar wani akace ka mutu?”.

Kasa ƙara sa Maganar tayi saboda yanda kuka yaci ƙarfinta kana kallo zaka san daga ainihin zuciyarta maganar ke fitowa.

 

Lokaci ɗaya tausayin ta ya mamaye baki ɗaya ilahirin zuciyar Dr Jameel hannu ya ɗago da niyyar rungumeta.

Da sauri Moddibo ya buge hannunsa.

Shi kuwa Dr Jameel zafin bugun da Moddibo ya masane yasa shi saurin mayar da hannunsa yana yarfawa sai kuma ya kalli fuskar Asma’u dake cigaba da kuka yace.

“Asma’u Wayyo Allana Yayanki zai kashe Ni kafin komai ya kankama”.

Moddibo kuwa ahankali ya kira sunanta cikin girma da kamalada da zame mata matsayin babban wanta kana jagoro kuma uba yace.

“Asma’u”.

Ahankali ta juya ta kalli Moddibo sai kuma ta maida kallonta kan Dr Jameel ta sake rungumesa.

 

Ganin haka yasa Moddibo saurin fin cikota daga jikin Dr Jameel ya tsaidata  sai kuma yace.

“Zo ki zauna anan”.

Ya faɗa tare da zaunar da ita akan Kujeran cikin yanayin nutsuwarsa da tuno yadda J ɗinsa ke killacesu da basu kariya akan kamilallun mazama bare irin Dr Jameel a hankali yace.

“Asma’u ki buɗe ido ki kalleni da kyau”.

Idanunta ta buɗe da tuni hawaye suka kwaranya ta kalli Moddibo.

Cikin fesar da numfashi ya gyara zamansa tare da cewa.

“Wanene Ni awajenki?”.

Cikin raunin murya tace.

“Yah Moddibo Yah Jameel”.

Kai ya gyaɗa tare da faɗin.

“Menene matsayina awajenki?”.

Still idanunta na zubar da hawaye tace.

“Tamkar uba kuma tamkar Yaya Jameel”.

Zazzafan Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da faɗin.

“Toh kiyi haƙuri da abinda zan faɗa miki, Dr Jameel ba J ɗina bane mai kama dashi ne kawai, nima nashiga irin yanayin da kika shiga lokacin dana fara ganinsa”.

Kai Asma’u ke girgiza wa tare da cewa.

“Wallahi Yah Moddibo   ban yarda ba Yah Jameel ne”.

Cikin rauni ya kira sunanta da faɗin.

“Asma’u”.

Ahankali ta ɗaga ido ta kallesa cikin sanyi Murya yace.

“Na taɓa yi miki ƙarya ne?”.

Cikin wata raunatacciyar murya ta girgiza masa kai tare da cewa.

“Yah Moddibo baka taɓa yimin ƙarya ba, amma wallahi bazan yarda da abinda kake faɗa ba”.

Ta ida maganar tare da miƙewa ta nufi Corridor data shigo tana gudu tana cewa.

“Ummi Ummi”.

 

Ahankali Moddibo ya koma ya zauna tare da ɗaura hannunsa duka biyu ya dafe kansa.

Ya tabbar kafin Asma’u ta yarda cewa wannan ba ɗan uwanta bane za’a ɗauki lokaci.

Sai kuma ya ɗaga kansa tare da kallon Dr Jameel dake ƙoƙarin binta yana kiran Asma’u asanyaye yace.

“Ka dawo ka zauna saboda bazata saurareka ba.

Wallahi Ni kaina zuciyata bata gama yarda min cewa ba J ɗina bane kai.

Kawai jikina da zuciyata tana gamsuwa da cewa Kai ba J ɗina bane”.

Sai kuma ya lumshe idanunsa da yake jin ruwan hawaye na tsats-tsafowa kana ya cigaba da cewa.

“Saboda yanayin lalacacciyar ɗabi’ar da kake yi na tabbatar kuma babu abinda zaisa Ummi, Asma’u,da Bashir su yarda cewa ba kai bane J sai In har sun fuskanci mummunan ɗabi’unka da halayyar ka da yanayin ka na neman mata shine kaɗai zaisa su yadda”.

Sai kuma ya sanya bayan hannunsa tare da goge hawayen da suka saƙƙo asaman kuncinsa kana ya cigaba da faɗin.

“Saboda J ɗina Amintaccene mai Aminci mai kamala ne mai mutunci ne, kuma tsarkakekkene bai kasance yanayin makamancin ɗabi’unka ba”.

 

Tunda Moddibo ya fara magana jikin Dr Jameel yayi bala’in sanyi, ganin maganar da Moddibo keyi daga ainihin zuciyarsa ke fitowa kana yana jin magan-ganunsa nada muhimmanci da kuma ƙarfi kana yana ganin yana da yaƙini da gamsuwa.

Cikin mutuwar jiki ya koma ya zauna karo na farko arayuwarsa daya fara jin tsananin ƙyamar kansa da kansa akan ɗabi’unsa na neman mata.

Lokaci ɗaya ya riski kansa da wani mummunan tsinkewar zuciya saboda har ƙasan ransa Allah ya jarabcesa da son wannan yarinya daya gani wacce ake kira da Asma’u.

Wacce ita kuma take masa kallon ɗan uwanta wanda zuwa yanzu ya fahimci komai nasa yana mata kama da ɗan Uwanta ne daya rasu.

Hakanan ne yasa zuciyarsa ya cika da tsoro da taraddadi anya Moddibo zai lamunce abashi Auren Asma’u ayanda yake nuna tsananin ƙyamarsa akan halayyarsa na zina…

 

Kansa ya riƙe da hannunsa duka biyu kana ya furta.

_“Astagfirullah wa’atubu ilaik”_.

 

Moddibo kuwa cikin sanyi jiki ya juya ya kalli Zakariyya dake cewa.

“Moddibo muyi alwala muyi sallah ana kiran Sallah”.

Kai suka gyaɗa kana suka miƙe sukayi al’wala kana  nufi masallaci alayi ɗaya sukayi jam’i koda suka idar da Maghriba basu dawo gida ba saida akayi Isha’i kana suka dawo.

Suna dawowa suka samu an shirya musu komai na a binci dining….

 

 

Acan falon da aka sauƙe su Khausar kuwa cikin gigita Asma’u ta shiga falon tare da faɗawa kan Ummi dake zaune cikin ficewar hayyaci take faɗin.

“Wallahi Ummi naga Yah Jameel”.

Da sauri Ummi ta zaro ido kana tace.

“Me kike faɗa Asma’u”.

Cikin zubda hawaye da rauni Asma’u ta gyaɗa kai tare da cewa.

“Wallahi Ummi naga Yah Jameel tare da Yah Moddibo”.

Yanayin da take magana cikin alamun kiɗima da gigita yasa Ummi saurin janyota ta riƙe ta.

Innayi ma matsowa kanta tayi kana ta riƙe hannunta tare da cewa.

“Asma’u wanda ya rasu yana dawowa ne?”.

Kallon Innayi tayi da jiƙaƙkun idanunta kana tace.

“Innayi wallahi Yah Jameelu na gani naga Yah Jameel Wallahi na ganshi”.

Cikin fesar da numfashi Ummi tace.

“Asma’u ki nutsu mana, In dai Jameelu ne da gaske ai zai iso mu”.

Ummi kam kallonta kawai take aranta tasani cewa tabbas Jameelunta ya rasu ya barta tasan cewa babu wani Jameelu sai dai in gezo yake wa Asma’u ta.

Aunty Ruƙayya dake zaune can gefe ta miƙe ta matso gefen Asma’u ta zauna tare da riƙe hannunta tace.

“Asma’u ya za’a yi wanda ya mutu ya  dawo? Shi wanda ya mutu baya dawowa ai shi mutuwa ɗayace idan mutum yayi ta yayi ta har abada”.

Cikin matsanancin kuka Asma’u ke girgiza kai kana tace.

“Wallahi Allah Aunty Ruƙayya na gansa”.

Ƙiran Sallar Maghriba da akayi ne yasa Ummi kallon Asma’u cikin tsawa ta haɗe fuska kana tace.

“Maza tashi Kije kiyi a”wala kizo kiyi Sallah”.

Da sauri tace.

“Wallahi! Wallahi!! Ummi Yah Jameel na gani, ki yarda dani”.

Cikin haɗe fuska Ummi tace.

“Zakije kiyi salla ko zaki tsaya hauka”.

Jiki asanyaye ta miƙe taje tayi al’wala kana tazo ta shimfiɗa Sallah kana tayi Sallah koda suka idar da sallar Maghriba Azkhar sukayi har aka kira Isha’i kana sukayi …

 

Bayan sun idar da Isha’i Asma’u ta koma gaban Ummi ta zauna cikin muryan kuka tace.

“Wallahi Ummi Yah Jameel na gani Ummi ki yarda dani ku nemi Yah Moddibo wallahi Yah Jameel na gani fa Ummi”.

Ganin yanda ta rikice yasa Ummi sauke zazzafan ajiyar zuciya tare da kallon Innayi da tazo gabansu kana tace.

“Innayi ane momin Moddibo al’amarin Asma’u yayi yawa fa, gaba ɗaya agigice take kinga Sallar nan har aka idar da Maghriba kuka take har aka zauna Azkhar still kuka take har muka jira Isha’i kuka Asma’u keyi”.

Kai Innayi ta jinjina tare da faɗin.

“Toh shikenan”.

Ta faɗa tare da miƙewa ta nufi side ɗin Didi.

Tana shiga Side ɗin Didi suka sake gaisawa kana ta yiwa Didi bayanin abinda ke faruwa.

Cikin sauƙe numfashi Didi tace.

“Tabbas ai shima kanshi Aleeyu sanadin shigowar sa Masarautar nan haɗuwar sa da Dr Jameel ne”.

Cikin yanayin mamaki Innayi ta tallafe kuncinta tare da faɗin.

“Toh waye Dr Jameel ɗin?”.

Ahankali Didi ta shiga bata Labarin da Dr Jameel ya bata.

Ajiyar zuciya Innayi ta sauƙe kana tace.

“Toh dan Allah ayi min iso zuwa Side ɗin dasu Moddibo suke dan bansan inda suke ba”.

Ƴar dariya Didi tayi tare da cewa.

“Ai suna kusa daku suna ƙasa,  kuna sama bari nayiwa Jakadiya magana ta rakaki”.

Nan Didi ta umarci Jakadiya kana ta yiwa Innayi jagora zuwa sashen dasu Moddibo suke…

 

Innayi na shiga ta samu Zakariyya Dr Jameel Ibraahim suna Kan dining yayin da ta haɗu da Moddibo gab bakin ƙofa da alamun zai tafi wajensu ne, dan ya duba halin da Asma’u ta tafi.

Yana ganin Innayi sai yayi saurin komawa baya.

Innayi kuwa tana ganinsa tayi murmushi.

Shi kam hannunta ya riƙe suka ƙarasa cikin falon kana suka zauna kan kujera suna zama kan kujera yace.

“Innayi nayi kewarki”

Cikin jin daɗin ganinsa ta gyara zama tare da faɗin.

“Nima nayi kewarka, amman dama ai nasan cikin danginka za taho nasan ka dawo cikin ƴan uwanka muhallinka”.

Kai ya jinjina kana yace.

“Innayi wani irin tarin abubuwa kikayi ta ɓoye min a iya tsawon rayuwata?”.

Numfashi ta fesar da cewa.

“Sai ahankali yanzu dai farko waye Asma’u ta gani ta koma tana ihu tana ce mana Jameel ne”.

Kai ya jinjina tare da lumshe idanunsa kana yace.

“Gashi can Innayi juya ki kallesa baiyi miki kama da Jameel ba?”.

Da ƙarfi Innayi ta tashi kana ta buga hannunta akan ƙirjinta cikin tsananin ruɗu tace.

“Kamar yaya kama?,Aliyu kace min Jameel dai Ashe gaskiyan Asma’u Jameelu ta gani”.

Ta ida Maganar tare da juyawa ta nufi dining area cikin sassarfa.

 

Tana zuwa ta kamo hannun Dr Jameel tare da riƙewa tace.

“Jameelu”

Kallonta yayi tare da yin murmushi shima kansa yanda suke zuzuta tsananin kamansa da Jameelu ya fara bashi tsoro da mamaki.

Innayi kuwa batare data jira komai ba ta kama hannunsa tana ja.

Shi kuwa Dr Jameel tsintar kansa da bin bayanta yayi.

Shima Moddibo cikin sauri yabi bayansu yana cewa.

“Innayi ba Jameelu bane  wallahi tsananin kama ne”.

Ina tuni Innayi ta fice batare data sauraresa ba ta fara haurawa step ɗin tana cewa.

“Ummin Jameel”.

Zakariyya da Ibraahim ma na biye dasu suna shiga Falon da Ummu ke zaune Innayi na cigaba da cewa.

“Ummin Jameel Wallahi gaskiyar Asma’u ne Jameelun kine”.

Akuma dai-dai lokacin Ummi ta juya da sauri idanunta suka sauƙa akan Fuskar dake tsananin kama da Jameelunta komai na Jameelunta a fili.

cikin wata raunatacciyar murya tace.

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”.

Sai kuma ta koma ta faɗa kan kujera idanunta na zubda hawaye shar-shar-shar.

Itama Asma’u cikin sauri ta riƙe hannun Ummi tare da faɗin.

“Ummi ba kin gani ba na faɗa miki Yah Jameel ne”.

Sai kuma ta saki hannun Ummi ta koma ta riƙe hannun Dr Jameel na dama Innayi kuma na riƙe da hannunsa na hagu suka zo gaban Ummi suka durƙusa sai shima ya tsinci kansa da durƙusawa agabanta, haka nan yaji kima da martaban matar sun cika masa idanu.

Da sauri Moddibo ya ƙarasa shiga wa falon tare da zama gefen Ummi wacce ke kan 3sitter kana cikin raunin murya yace.

“Ummi”.

Cikin zubda hawaye ta juya ta kallesa cikin rauni ya cigaba da cewa.

“Ummi ki kalli duk komai na Jameel ne muryansa, Tafiyarsa, Gangar jikinsa, Har fa asakin da Jameel keyi shi yake yi amma wallahi Ummi ba Jameelunki bane kamannin ne yayi yawa Wallahi!³ Ummi ba Jameelunki bane”.

Juyawa Ummi tayi ta kallesa cikin jinjina masa  take cigaba da gyaɗa kanta jikinta yana bata ba Jameelu bane domin jikinta ba amsheshi a matsayin Jameel ba wannan bawai ɗan ta bane agabanta amma zuciyarta taƙi yarda.

Kai ta girgiza still hawaye na bin fuskarta ta juya ta kalli Dr Jameel da yake durƙushe agabanta.

Ganin yanda take zubar da hawaye yasa shima yake zubar da hawaye.

Murmushi tayi tare da cewa.

“Toh meyesa ka kuma?”.

Ahankali ya ɗago kai ya kalleta cikin tarin tausayinta da kuma rauni yace.

“Saboda kukan da naga kunayi shiyasani kuka, nasan ko waye Jameel awajenku mutum ne mai daraja, mai kima wanda shine jigo acikin rayuwarku”.

Kallonsa kawai Ummi keyi hawaye na cigaba da zuba daga idanunta sabida yadda muryasa ma sai ta Jameel ɗinta.

 

Shi kuwa  Dr Jameel kuwa cikin rauni da zubda hawaye ya cigaba da faɗin.

“Na fahimci kuna jin ƙuna na rashinsa amma Ummi nayi miki al’ƙawari in dai kin amince kun bani dama in sha Allah zan maye muku gurbinsa”….

 

 

 

*Dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn, masu cewa wai sun goda suga number’n nayine, ko kuma a’a bari dai in na shirya zan sake miki mgn, ko kuma yanzu dai kuɗin bai cikaba tukun sai sun cika, ko kuma a wanne gari kike, kai munyi nisa, toh in ba iyayiba ai duk nisan state da kike ba ruwan mota ba inda bazai kai mikiba, nake turawa ƴan ƙasashen wajema. Kuyiwa Allah da Manzonsa in dai in kinsan Baki shirya sayan kaya ba ku daina min mgnar ku bari sai kun shirya,kada kizo ki ɓata min lokaci a banza, wlh ni na tsani harkar karanta, duk bayani na gamayi in dai saya zakiyi ga kuɗin kaya ga account no ga numberta ai sai ki biya kawai kafin kimin mgn. Tunda dai ga alamominshi da duk illar da yakeyi na faɗi in kina dashi faƙat in babu kada ki wani zo kice min bayani dan ko kinzo iya bayanin da zan miki kenan*

Alamomin infection sune kamar haka. Rashin sha’awa. Ƙaiƙayin gaba Kiji idan ya fara miki ƙaiƙayi kamar zakiyi hauka. Warin ko ƙarnin wurin. Fitar farin Ruwa mai fatsi-fatsi. Ƙurajen su ɗan fetso ƙananan ko ƴan manya, melewar fatar wurin, Tusan gaba. Bushewar gaba, Rashin ni’ima. Buɗewar gaba, domin har budurwa infection na iya buɗata. Ciwon mara ko ciki mai tsanani yayi al’ada, rashin haihuwa, domin har baƙin mahaifa take toshewa. Ko kirinƙajin wani abu na miki yawo ƙasan mara, ko jin zafi yayin yin fitsari, da kuma saduwa, da dai sauran abubudann ban  lissafa. Sune manyan alamomin infection.

Shin kin kuwa san illar da infection keyi miki, amman kinajin ɗaya daga cikin alamominta kinyi bulum buƙui da ita a jikinki. To bari kiji illolin infection wato cutar sanyi.

Rashin haihuwa, ƙyara da hantara a wurin miji domin muddin kina tare da ita baki da wata daraja a idanu nai, sabida ƙyamas kike ba damshi bare wata ni’ima mai Taste, Kinga kenan shinfida ta lalace, in kuwa shinfiɗa ta lalace dole kiga sauyin fuska, domin su maza dole sunason wurin da kwaranya, zaki kasance baki da wani daɗi da ɗumin da mai gida ke buƙata. Kinga duk tsabtarki da kyanki da iya girkinki shinfidarki ta zama lami. Kiyiwa Allah ki nemawa kanki lafiya ki samawa mijinki da ke kanki nitsuwa.

KADA KUJI IYA WANNAN DOMIN AKWAI MUGUN INFECTION WANDA BAYA BAYYANA KANSA. Wanda kawai sai dai kijiki, kamar kwalta kin bushe ƙyamas ya dauke miki dukkan sinadaran ni’imomin ki, da sha’awarki, duk kayan matan da zakisha a wofi zadai kiji ƴan uwa da abokan arziƙi da ƙawayenki na yaba miki magunguna GARKUWAR MA’AURATA, amman ke in kinsha jiya I yau,  duk nacin oga da yi miki wasannin bazaki ji sha’awa ba, toh wlh muguwar infection ce, wacce bata bayyana kanta har sai ta gama yi miki rugu-rugu. Ta lalata miki zaman aure. Lokacin da zata bayyana sai kiji Doctor’s suna kira miki, ovarian cyst, ko kuma fibrod duk a cikin chronic infection ne yar uwa.

INFECTION set ɗinmu na kowa da kowane Mata, Maza, Bazawara, Budurwa, Maijego, Yara, Ke yar uwa Wlh har maiciki zatasha, bashi da matsalar komai Maganin na Gargajiya ne mai rakake INFECTION ya fito miki dashi, wlh duk nacin infection koda na cikin mahaifane bi’izinillahi ta’ala zaki rabu dashi, cutar infection cutace mai masifar naci, so yar uwa kana dole ki nace masa da maganin set ɗin na 10k ne kuma maganin kala biyarne nasha da kala uku na tsarki ɗaya na shafawa ɗaya. Yar uwa idan har kin saya to kiyi ƙoƙarin kisha da mijinki, in akwai abokiyar zama, kisa miji ya saya mata, domin ko kin rabu da shin dai ita tana dashi tofa kin kashe macijine baki cire kaiba, ma’ana zai sake dawo miki, idan kuna da yara suma a saya musu, domin tsoron kada ya riƙa a jikinsu musamman ya’ya mata ya buɗa miki ƴa tun tana ƙaramarta, ki aurar da ita miji na muku kallon lalatattun iyaye da baku iya bada tarbiyaba. Saboda yamayin garin yasa ina raba rabin set ɗin in sa miki komai rabi-rabi 5k amman set ɗin 10k ne. Idan kin san a shirye kike ga account number na nan 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA, ki turo kuɗinki kafin kiyi min mgn ta WHATSAPP NUMBER’N na 09097853276 sai ki turo min shaidar biyanki, domin akwaishi Available ko yau kika tura kuɗinki, gobe kayanki zai taho, ina bada sari ko sayan ɗaɗɗaya. Farashin Sari da sauƙi daga kan mutum 3 ko 6 ko 12. Kai ko na mutum 24 kikeso in Sha Allah zaki samu. Please dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn ki bari sai kin shirya. Taku ce dai GARKUWAR MA’AURATA.

 

 

By

*GARKUWAR MARUBUTA*

Leave a Reply

Back to top button