Hausa NovelsWaminal Hoob Hausa Novel

Waminal Hoob 5

Sponsored Links

Waminal Hoob*_ 5…..

_Asmy b Aliyu_

“Taya kakeso na fahimtar da Ammah duk bakai ka jawo mana wannan Rigimar ba .” yarinyya tamkar manyya kabi ka makale mata nima kana so ka sakani a rikicinku,nidai baxan iya hada fuskata da wannan bakar yarinyyar ba koda pics ayi mana .” kasan yarda xaka fahimtar da Ammah nagama magana.” Aliyu waxeer ya fada yana barin farhaan shagari a wajen tsaye,shidai Inhar Aliyu waxeer ya amince xai auri noory dinsa baida matsala.Ya tabbata koda shekara Goma nooriyah xatayi da Auren Aliyu ,Aliyu waxeer baxai taba cin Amanarsa ba Dan yasan kaunarsu mai girma ce,
Washe gari Aliyu da kawu balele suka gama tsara komai har daukarsa Aliyu yyi ya kaisa inda Kabir yake yaga yarda ake kula dashi,har haske yyi na kwana daya.matsalarsa Adama har yau taki amincewa akan maganar Auren Aliyu da nooriyah shima kawu balelen da yake Dan masifa ne, sai ya baiwa banxa ajiyarta ya cigaba da hidimomin gabansa.itama Adama anata bangare tana ta kiran layin Kabir amma a kashe gashi bai kwana a gida ba,shi ya kara daga hankalinta da safe har Marin nooriyah tayi .Haka ta shige daki taci kukanta ,ga kawu ya fada mata masu Neman Aurenta xasu xo ,
Ta dauka ko maganar Aurenta xaayi da Kabir duk tabi ta daga hankali ta ,tana ta kiran wayar Farhaan tun safe a kashe…………haka tayi taxama a daki,
Sai bayan La’asar kawu balele yasa yara suka rinka shigowa da buhuhuwan shinkafa da kayan Abinci da lemukka da suka cika Dan karamin tsakar gidan su ,Nooriyah ya shiga kwalawa kira da sauri ta fito tana durkusawa a gabansa ,dagota yayi yana fadin”tashi tsaye yar Albarka Leda baka ya bude ya fiddo rafar kudi yan dubu-dubu kwara biyu yace ga sadakin ki nooriyah Allah yay maki Albarka. nan da kwanakki kalilan xakiyi bankwana da Rayuwar talauci.”Gasu naira dubu Dari biyu ne, nayi alkawari xan baki kudinki ranar da xan kaiki gidan Aurenki.”da mugun sauri ta dago tana kallonsa gabanta na faduwa idonta na cika da hawaye lokaci daya ,cikin rawar murya take fadin Aure kuma kawu dawa??”daria kawu yayi yana fadin”ke kwantar da hankalinki ba siyar dake xaayi ba,wani yarone mai kirki xaaya aureki ae yace kin San sa,sunan sa Aliyu.”Kawu balele ya fada cike da jin ddi ,maimaita sunan ta shigayi juyawa tayi ta koma daki jikinta na rawa hawaye na xubar mata take kara gwada kiran farhaan .”karkayi min haka Dan Allah farhaan karka hadani da wannan mutunen kar mu fara wannan wasar da baxamu iya karasata ba.cikin sa’a wayar farhaan din ta shiga dama tana da naira talatin da biyar a waya tasan xasu isheta………..noory !”taji ya fada cikin sanyi murya ,tana jin yarda muryarsa ke narka mata xucia .cikin kuka take fadin”plz farhaan karkayi haka Dan Allah ,kaxo yanxu gida akwai matsala .”ta fada tana fashe masa da wani irin kuka mai cin rai,xubewa tayi a kasa tasa hannu tana toshe bakinta kar kukan Ya fita,
****
Tunani na a kullum ya xaayi watarana na wayi gari bbu kai atare dani ,shiyasa nake addu’a A kullum allah yasa na rigaka mutuwa Farhaan, ina sonka ina tsananin sonka son da ban taba yiwa wani a dunia ba,Kaine mutun na farko da ka nunamin gata da soyayya a dunia ,Dan Allah karkayi haka karka bari Aliyu waxeer ya aureni nayi alkawarin xan jiraka koda shekara nawane farhaan.”Ta fada hawaye na xubar mata ,harde hannu yayi a kirjinsa yana kallonta .nooriyah idan soyayya birni CE to ki tabbata ke kike mulki a wannan birnin,tana girgixa kai take fadin acikin soyayya son kan da kanuna shine bajintarka ,cikakken masoyi shi xai kauda kansa daga hawayen da kowa xaiyi Dan ya xauna da masoyinsa,pls nooriyah kidaina yimin gori wannan itace kawai mafitar mu.”Ae dole nayi maka gori karasa Wanda xaka hadani Aure dashi Sai Aliyu waxeer ,kasan xaman mu baxai yuyuba.idan ya nemi ya wulakanta ni baxan barsa ba wlhi.”daria Farhaan yayi ae baxai ma fara ba ,kema Dan Baku fahimci juna bane Aliyu yana da saukin kai ,saima kin xauna dashi keda kanki xaki bani labari shaye da toka da turo baki take fadin “Ae dama nasan kafi son wannan Jan kosan akaina,wara ido farhaan yyi yana daria sosai yake fadin” bbu ruwana idan yaji kina kiransa da wannan sunan,yaji mana nima bakaji yafi karfin ya kirani da sunana ba ,saboda girman kai”Bakar fata kuma ina Alfahari da sifar da Allah yayi ni”………..sun dde suna magana daga nan sukayi sallama tamkar karsu rabu koba komai cikin damuwarta kashi goma farhaan ya tafi da kashi shidda.shirye-shiryen Auren Aliyu waxeer Ammah ta shigayi dama a kwanakkin baya,ta fara hada lefensa ta dakatar sabida taga Aliyun kamar bai shirya Aure lokacin ba,,sai yawo yake yimata da hankali shiyasa ta dauki itama Al’amarin ta watsar,kayan da ta ajey xasu dauki saiti daya .Dan Haka ta kira kanwarta dake xaune a maley Dan Neman shawarata ,in saiti daya din yyi idan kuma karawa xaayi sai a kara.”Ammah a kara mana Aliyu waxeer ne fah.”ko Auren Khalil waxeer saiti biyu akayi ,mexai hana ynxu shi ayi masa saiti hudu,xaki kasheni da raina kenan Hannatu.”toh ki kira ango ya bada kudin hada saiti hudu ae yana da kudi,daria hannatu tayi haba Ammah kamar Aliyu ya xaayi ace saiti biyu ,xan mashi magana ae.”kamar Areefa mansoor wacce yake ji daita ae sai saiti hudu ,ammah ta sauke ajiyar xuciya tana fadin”Bafa Areefa bace ya canja,da mugun shock Hajia hannatu ke fadin”meyasa Ammah??fasawa yayi fada sukayi ne.”Lokaci daya hannatun ta jerowa Ammah tambayoyin ,
Nima ban sanni ba Hannatu haka na tsinci xancen har araina bana son wannan Yarinyyar Areefa ,sabida idonta ya gama budewa dayawa .burina A kullum Aliyu ya samu matar Aure marar son abun dunia haka Marar kyale-kyale Wanda wayewarta ya xama na addinin islama ne,,wannan lokacin ina ji ajikina Allah ya karbamin Addu’ata duk da banga matar Aliyun ba xuciyana ya natsu da Auren.”ajiyar xuciya hannatu ta sauke , kina ganin Aliyun xai iya Auren macce wacce bata wayeba marar kyale-kyale duba da yarda Aliyun yake.sun dde suna tattauna matsalar Aliyu ,sa’anan sukayi sallama………Bangaren Aliyu kuma komai bai fara shiryawa ba tamkar ba Auren sa xaayi ba ,farhaan ne gaba wajen komai ko dinkunan biki duka farhaan ne yyi da Aljihunsa ,Wanda sai da ya girgixa .Aliyu gefe ya koma yana kallon yarda farhaan ke rawar jiki da Auren…..
***
Ta cakumi kwalar rigarsa tana masa tsinannen kallo take fadin”Na rantse da Allah yau sai ka fadamin wurin da ka kaimin Yaro.”Adama ta fada cike da masifa,kawu balele ya hankadata yana fadin”Ashe bakida kirki har haka Adama ki kalli tsabar idona ki rika fadamin na fito maki da Yaro ni Aljani ne da xan boye maki Yaro.”waya sani ko kafi fiye da haka yau kwana biyar Kabir bai tako kafarsa a gidan nan ba.”Bai tabayin haka ba,duk lalacewarsa kuwa………Yarda naga baka wani maida hankali a batan nasa ba nasan da saka hannunka,toh wlhi baxan yarda ba polisawa xan dauko maka su tafi dakai,salati kawu balele ya shiga xabgawa yana fadin”Yanxu ni balele ni xaki daukowa polisawa akan batan Kabir wai adama na tambayeki ,ni Kabir ba Dana bane halama.”Yyi maganar so pissed up itama sounding so very harsh take fadin”Dan kane amma xaka iya kaisa wajen masu shan jini ,Dan kasamu kudi yarda na sanka tamkar yunwar cikina xaka iyayin komai akan kudi………”ni ban ma yarda da Wanda yaxo Neman yarka Aure ba wlhi wayasani koda shi ka hada baki kabasa Kabir Dan ya baka kudaden da ka fadamin haka ka dauki waccan bakar yarinyyar kabasa Auren ta ,baa dde ba sai ga motar polisawa har kofar gida dama Adama ta kira abokanin Kabir ta shaida masu,shahoo ne yyi sallama.da sauri adama ta sakesa tayi wurinsa tana fadin”shahoo kun taho da polisawa ,gasu a kofar gida Ummah.”kai Baba wuce muje.”…….gidan ubanwa xaku kaini “,idan mukaje xaka gani idan baka fitomana da oganmu ba wlhi tallahi sai Mun illataka mu illata banxa.!” Haka shahoo yaja rigar kawu balele har kofar gida,akwai wani kurtu tsaye awaje shi ya sankame hannayensa da sarqa akasa sa a mota.
“Shahoo da Adama suka bi motar polisawa a baya cikin adaidaita sawu.cike da tashin hankali nooriyah ta shiga Neman layin Farhaan,dama sunyi magana da kawu Kabir an kaisa makarantar gyara hali.hankalita ya kwanta sosai da hakan dama a kullum tana addu’a Allah ya kawo lokacin da Rayuwar Kabir xata canja duka.,,cikin rawar murya Nooriyah ta shigayi masa bayani yan sanda sun tafi da kawu balele.;bari na nemo Aliyu ya fada yana datse kiranta,
” Amma kasan yanxu shigana police station wata matasalar CE babba yan jarida xasu iya samuna a wajen,bara na kira commissioner a waya kafin nan ka kira kawu kaji a wane station ne,da sauri farhaan ya kira wayar kawu kusan kira ukku baa daga ba sai a na hudun wani officer ya daga,nan sukayi magana da farhaan cikin natsuwa ya fada masu a station din da case din yake,Farhaan yace yana xuwa nan da minti Talatin ,da yake wajen akwai nisa daga wajen da yake.
Cikin kankanin lokaci farhaan ya iso dama su Adama suna a reception kawune kawai aka tura cikin cell ,kai tsaye office din d.p.o.ya nufa ,kusan minti goma ya shafe ciki,
Sai ga wani officer ya leko ya kirasu Adama .Nan d.p.o.ya fada masu ba sace Kabir akayi ba,taimakonsa akayi.”wane arnen ne ya shimfida maka wannan karyar,yau ni Adama naga abunda ya isheni.”taimakon ubanwa kayi masa an fada maka yarona musakine da xaka taimakesa,ko kuma Jan duwawu yake.”Adama ta karasa xancen cike da masifa da balai,
Dakyar d.p.o.ya lankwasata ,Ya fada mata xasu dauketa su kaita inda yaronta yake ,
Amma da sharadi idan tayiwa mutane hayaniya na lahira sai ya fita jin ddi hannun sojoji yake ba yan sanda ba.”tun awurin shahoo ya sare, yana hada xufa yake fadin”Ummah ni na wuce dama innata na kwance gadon Asibiti yanxu hakama can na nufa,
Baki bude ta saki tana kallon shahoo ganin irin karyar da ya sharara………..Itada kawu Farhaan ya daukesu a motarsa ,haka cikin su bbu Wanda ya shaida fuskar farhaan din sabida toshewar basira ,
Yarda taga ana kula da Kabir sai taji jikinta yyi wani irin sanyi,amma duk da haka xuciyarta ko gixau baiyi ba.baxata bar kawu da nooriyyah ba har sai sun amsa mummunan hukunci a hannunta ,Kabir ya kamo hannun Adama yana fadin”Ya kk Ummah nayi kewarki ya nooriyah hop bakya dukanta bakya sakata debo Ruwa a bakin titi cikin maxa,kina Bata Abinci kuwa”kinga yarda Rayuwa ta juyani ko Ummah,Ashe ba karamin so Allah yake yimin da Rahamar sa ba.nagodewa duk Wanda ya canja min rayuwata har haka,ki kularmin da kanki da nooriyyah nasan idan na fito taga yarda na xama xatayi farin ciki da hakan…….”Adama xatayi magana akaja Kabir akace lokaci yyi sai wani lokacin kuma.duka jiki sanyaye adama ta dawo gida ta kasa koda kallon Kawu balele…
****
Janta ta shigayi Haka tana kai mata mari ta koina ,har tayi narasar fasa mata baki.kawu balele yana mata magana ko takansa bata biba. haka ta shiga janta tana fadin”wlhi tallahi !”xama na da yarinyyar nan cikin gidan nan ya kare tunda Kabir yabar gidan nan dolene itama tabar gidan nan,
“Idan tabar gidan nan ina kikeso ta tafi??Anya Adama kina da imani kuwa,wani banxa kallo
ta shiga watsa masa fadin take kai baka isa ka fadamin yarda xan tafiar da gidana ba,bbu ko kwandalar ka acikin siyen gidan nan kaima Xaman bulus kake acikinsa,Dan Haka ka rufemin baki .”xubewa nooriyah tayi akasa ta game hannayenta hawayen na xubar mata ta shiga Rokon Adama akan tayi hakuri ,wani hauri takai mata cike da jin haushin ta take fadin yau duk sanyi kalamanki baxasu narkar da wannan xuciyar tawa ba xo kifice min agida don ubanki tun kafin na hada maki jini da majina…………” Haka Adama ta shiga Jan nooriyya cike da toxarci kawu na bata hakuri ko kallo bai isheta ba ,tura nooriyah tayi da karfi taje xata fadi tajita a hannun mutum.kyawawan idonta ne suka sauka cikin nashi idon,sanye yake cikin farin yadi Fari kal”mai shara-shara har ana hango farar shimin dake jikinsa ,ta lura yana son manyan kaya kuma farare sabanin farhaan dinta da baya shiri da manyan kayan.da sauri ya saketa ,
Salati Ammah ta shigayi tana fadin”baiwar Allah lfy kuwa??wani kallon banxa Adama keyiwa Ammah taja tsaki gamida shigewarta gida ta kalli nooriyah tana rike da kofa take fadin”idan kika kara tako kafarki cikin gidan nan wlhi tallahi sai na maki illah sai na karawa shegiyar fuskar nan taki baki.”Adama ta fada tana buga kofar tabar Ammah tsaye da mugun mmkinta ,dama ita tace Aliyu ya kawota gidan su Nooriyah ta sanar da iyayen nooriyah yarda suke gudanar da bikinsu inhar Xaa auri yarinyya acikin xuri’ar waxeer ,uwar miji xata dauki amaryar na tsawon sati daya a bata kebantaccen daki na musamman ayi mata gyaran jiki haka idan anfara hidimar biki.Ranar salalle da amarya da ango lokaci daya xaa saka su lalle a gidan su Ango.wannan Al’adar xuri’ar waxeer CE………da sauri kawu balele ya nufi Aliyu waxeer sai hada xufa yake yana fadawa Aliyu abunda yasa Adama tayi haka,wani irin tausayi da son nooriyah suka shiga xuciyar Ammah lokaci daya,Bata taba ganin matar da tadace Da Aliyu waxeer a dunia ba irin Nooriyah.
Mami ta kama hannun Nooriyah ta dago fuskarta duka tana kare mata kallo,Nooriyah tana da wani irin sanyayyen kyau Wanda a boye yake.tana da cikakkar fuska mai dauke da cikar xati da kamala haka hancinta dogone sosai tana da matsakaitan labba,tana da manyyan idanu farere kyal.”sai dai nooriyyar bakace sosai ,Wanda harda wahala ya kara sakata baki.nan gaba idan ta goge bakinta mai kyau ne. “Wani irin murmushi Ammah ke saki,batareda Ammah tace komai ba ta juya ta nufi mota da nooriyah da kanta ta bude mata gaban motar tace ta xauna tana xuwa,a tsorace nooriyah take.nan Ammah ta dawo tana gabatar da kanta a wajen kawu balele,
Haka kawu balele ya shiga fara’a tamkar yayi mata sujada .wani irin haushinsa Aliyu waxeer keji.” Ina ganin na dauke nooriyah daga yanxu har xuwa lokacin da xaa daura Aure.”Ranar daurin Aure kaxo da waliyan nooriyya ,karka damu daga yanxu nan xan cigaba da kula da Rayuwar nooriyah har karshen Numfashi na bbu abunda xai kara samunta.”Ammah ta karasa maganar ta juya tana barin wurin ,cike da tausayin nooriyah din..
“Me Ammah keyi hakane??Aliyu waxeer ya fada yana hargitsa sumar kansa,xamuyi waya kawai ya iya fadawa kawu ya juya ya nufi motarsa cikin takunsa mai daukar hankali ,kallo kawu balele yabisu dashi sai yaji wani iri karo na farko acikin rayuwarsu da xaiyi nisa da nooriyah samun kansa yyi da daga mata hannu kwallah na cika idonsa,itama nooriyah daga masa hannu ta shigayi hawaye na xubar mata.tausayin yarinyyar ya kara dagula xuciyar Ammah.dukansu xaman shuru suka xauna a mota ,ganin Ammah har lokacin taki magana yasa Aliyu yaji duka bbu ddi,yasan xai sha tambayoyi awajenta duk farhaan shagari shiya saka sa a wannan halin yana xaman xaman sa.
daga kanta tayi tana kallon cikin unguwar ,Tamkar a kasar turai Dan kyau wasu irin tangama tangamen get ne awajen Wanda bata taba ganin kalar su ba,
Kusan gidaje hudu ne Jere a wajen masu kalar get iri daya,na karshen taga motar Aliyu ta nufa. Horn ya shiga dannawa da sauri aka wangale katoton get din ajikin get din anyi wani Rubutu akai( AHMAD WAXEER MANSION)wara ido nooriyah tayi tana kallon Aljannar dunia tsoki Aliyu waxeer ya buga karo na farko,yana wani bin nooriyah da harara Dan ya manta suna tare da Ammah,sauti kasa -kasa yake fadin ki kama kanki yar kauye kawai.”da sauri ya dauke kansa tamkar bashi yyi magana ba,maimakon Taji haushi sai ta saki murmushi gamida dauke kai,yana gama parking yyi saurin fitowa ya budewa Ammah motar ita kuma ta nufi side din nooriyah da Sauri ta bude mata.cike da jin kunya nooriyah ta sunkuyar da kanta haka kurum ta samu kanta da jin kunyar Ammah.tsaye Aliyu yayi yana kallonsu,hanyar Entrance din shiga gidan suka nufa,da sauri yabi bayansu yana son yin magana da nooriyah sai dai da alamar Ammah ta rufe kowace kofa.Dan gyaran murya yyi Ammah kawai CE ta ta juyo tana kallonsa ,shafa sumar kansa yyi yana fadin”ina son magana daita Ammah.”yyi maganar yana wani dauke kai,
Ammah ta girgixa kai tana fadin ba yanxu ba Aliyu waxeer xuwa da Yammah kadawo.”tana fadin Haka ta juya rike da hannu nooriyah samun kansa yyi dajin haushin Ammah kan wannan Ya’r bakar xatace ya tafi sai xuwa anjima tamkar wata sarauniya juyawa yyi ya nufi part dinsa.
Baki nooriyah ta saki tana kallon katon falon Ammah sai ta xama tamkar wata sakaryya sabida kallo,xama sukayi acikin Maroon din soofas din da sukayiwa falon kyau,ga fotunan su Aliyu nan jere a falon shidasu Ammah wani shi kadai,
“Jikin ki yana bukatar wanka Nooriyah ya kamata kiyi wanka kici abinci ki huta,anjima Aliyu xai iso kuyi magana.” Saukar da kanta kurum kasa tayi tana wasa da dogayen yatsun hannunta.waya Ammah ta dauka ta kira yar aikinta murja wacce xata kai kimanin shekaru talatin da biyar wandda duka yan aikin gidan suna xaune a boys Quartet’s sai idan suna aiki suke shigowa part din Ammah.murja itace Babbar yar aikin Ammah duka sauran a karkashinta suke ,Dan ita kadai ke shiga part din Ammah ta gyara mata.
Baa fi minti biyar ba sai ga murja da sauri ta xube agaban Asma’u waxeer ,
“Murja xaki tafi da bakuwar nan dakin baki a hada mata ruwan wanka .ki taimaka har kanta ta wanke ki bata abinci ki xauna tare daita anjima xan kiraki.” An gama Hajia xan sa batool tazo maki da kayan da xata saka.”da sauri murja ta mike tsaye Nooriyah na biye daita da kallo Ammah tabisu har suka bacewa ganinta.wani irin murmushi Ammah ke saki tana mamaki tana karawa ina kuma Aliyu ya samo wannan yarinyyar ,
Aliyunta ne xai Auri bakar macce kuma Yar tallakawa ??”yaushe tunanin Aliyun ya canja haka,tasan Aliyu tun yana Dan karami yake fadin”shi baya sha’awar bakar macce a tsarin Rayuwarsa fara yakeso kamar shi sabida kaf familyn waxeer farare ne koda yayi Rayuwa cikin yan uwansa babu bakar fata……har yau mmki yaki barin Ammah sai kai da kawo takeyi a tsakiyyar falonta ,Aliyu waxeer ne kawai xai amsa mata dukkanin tambayoyinta…….

****
Aliyu ya akayi haka??badai wannan itace matar da xaka Aura ba.”Ammah tayi maganar sounding so very confused………itace Ammah meya faru batayi bane.”Aliyu waxeer ya fada cike da dakewa ,Aliyu inhar tausayin wannan yarinyyar kakeyi karka cuceta Dan Allah .”Akwai hanyar taimako dayawa ,gaba daya ban yarda da wannan Auren ba.”Ammah ta fada cike da karaya.
Xufa yaji ya fara hadawa ganin Ammah na Neman ganosa,da sauri yace Ammah inason nooriyah ni ba tausayinta nake ba.”Yayi maganar cike da kwarin gwiwa.tsaresa da ido Ammah tayi tana juya ko wace magana tasa,Yaushe ka fara son bakar macce haka gidan tallakawa wacce bata waye ba.??’wannan karon sai da ya girgixa jin tambayar da Ammah tayi masa,xuciyarsa yaji tana tsalle lokaci daya,”I’m going to kill you Farhaan Shagari idan mun hadu ka sakani a matsala.” Yyi maganar duka acikin ransa ,wayarsa CE tayi kara da sauri ya Ciro wayar ganin farhaan ne ke kiransa ya mike tsaye yana fadin”Ammah zamu fita da farhaan yana jirana,har ya juya yaji Ammah na fadin”baka Amsa min tambayana ba Aliyu.”Jin yyi xuciyarsa na tsananin bugawa da sauri da sauri,
dauriyarsa ya tattaro yana fadin”Haka Allah ya nufa Ammah ,Nooriyah itace Allah yayi xan Aura ta xama uwar Ya’yana.da haka yabar falon har yana hadawa da gudu ,wata irin dariar farin ciki Ammah ke saki fadin Take .”Alhmdullhi na godewa Allah da ya cikamin burina Aliyu xai Auri irin matar da nakeso ,duk da bata xauna da Nooriyyah ba taji aranta tana da hali mai kyau haka xasu xauna da Aliyu lafia….
[9/15, 6:11 PM] Asmy Mom Aydah??: *_

Back to top button