Duk Karfin Izzata Book 1Hausa NovelsHausa Novels

Duk karfin Izzata Book 1 Page 31

Sponsored Links

 

Episode 3️⃣1️⃣*

Aunty Amarya che zaune a bakin gadon ta tana waya da hajj sadiya

“To yanzu hajj sadiya ya ki kayi dashi ne nifa wlh na matsu, banson ganin yaran nan a gidan nan, daga ɗayan bangaren hajj sadiya tace “haba hajj hajara sai kace yau muka fara aiki da gagarabadau, ki kwantar da hankalin mana yanzu zan miki bayani ai tun da ki kaga na kiraki kam kema kinsan akoi bayani “to hajj sadiya ki faɗamin da wuri mana dan na matsune naji ai

“Jiya naje wajen sa, yana faɗamin chewa Aiki na tafiya yadda ya kamata, dan yache ma akoi wani shu umin malamin da basu san daga ina yake ba yana taimaka musu sosai, shima yana bibiyar rayuwar yaran ne, ahalin da akechiki yanzu yama kusa kunche tsarin dake jikin yaran saura kaɗan, amma fa yace ita babban wlh ba wanda ya isa ya mata wani abu asiri ba zai kamata ba, aljanu ma bazasu iya shiga jikin taba, dan tana karatun qur’ani tana askar, bata wasa da sallah kuma tana sallan dare gashi bata shiga harkan kowa, yaso shiga jikin ta last month da tana period ma amma sai dai kas bai yi nasara ba, domin duk da tana period, tana askar, kuma tana zama da alwala,ba ta yadda zaiyi ya shiga jikinta, su kuma sauran nan da two weeks, malin Chan in ya gama kunche tsarin jikin nasu, yana gama kunchewa shikuma gagarabadau zai ɗaura nashi aikin a kansu
Dogon numfashi Aunty Amarya taja kafin tace “to shikenan Allah ya kaimu “amin Hajj Hajara karki damu ke dai ki kara hakuri saura kaɗan yauwa baki bani lbr sabon sarkin ku ba ya ake chiki? ” Hmmm ke dai hajj sadiya bari wani sarki wlh ranan da ya fara hawa kujerar mulkin nan tun ranar ya fara rashin lfy baya magana baya motsi, sai dai numfashin sa kawai da zakiji shine zai tabbatar miki da bai mutuba abun gwanin ban tausayi,
Wani shewa hajj sadiya tayi ta chikin wayar kafin tace “ai albishir ya kamata kimin hajj Hajara kiche aikin gagarabadau yayi kyau,
zubur Aunty amarya ta mike muryar ta har rawa yake wajen faɗin “hajj sadiya kenan ke kikayi wa Ahmad wan nan abun? ke nan daman ba chiwon Allah da annabi bane ya kamashi? tsaki Hajj sadiya taja kafin tace.

Kamar ya ni na masa, ke dai kika masa ba niba, dafe kirji Aunty amarya tayi ta zaro ido tana faɗin “ni kuma hajj sadiya a yaushe na masa hakan, “Hajj Hajara wai lfy ki?, watoma kin manta aikin da kika sani naje na sa gagarabadau ya miki akan, idan ba mijin ki ko ƴaƴan ki ba, ba wanda zai karɓi mulkin nan duk kuma wan da yayi kuskuren hawa mulkin tofa mutuwa zakiyi

Girgiza kai Aunty amarya ta shigayi tana faɗin “aa hajj sadiya ni dai gaskiya banche a kashe kowa ba ni dai to a kunche aikin nan dan wlh bakiga yadda Ahmad ya koma bane Allah ko ke kika ganshi sai kin masa kwalla,ni su Ahmad basumin komai ba,su diyana ne bana so, su nakesan a haukata min, amma ban da su Ahmad
Wani dogon tsaki Hajj sadiya ta kuma ja kafin tace “amma hajj Hajara bansan baki da wayau ba sai yau wlh ki na tunanin idan da uwar su che ta samu damar da ki ka samu a kan ƴaƴan ki, zata raga musu ne? wlh bazata ragawa kowa ba, ke kowa da kika gani aduniyar nan kanshi kawai ya sani wlh sai dai in bai samu dama bane sai ya rinƙa nuna chewa shi na Allah ne, da zarar ya samu dama to a nan zaki gane asalin mugun halinsa, ki tsaya ke dai kiche kinajin tausayin su kina ji kina gani, Aisha zata mamaye komai na gidan in bakiyi Sa’a bama wlh sarki na mutuwa yar wanke wanke Aisha zaki zama, dan haka zaɓi yarage gareki.

Dogon numfashi Aunty amarya taja tare da sauƙe ajiyar zuchiya kafin tafara magana “eh hajj sadiya kina da gaskiya wlh,dan yanzu ma mai martaba yafi jin maganar Aisha fiye da na kowa a duniyar nan, da Zarar Aisha tace ga abun da takeso wlh zakiga jikin sa har rawa yake wajen biya mata bukatun ta, kin dai san halinsa idan yayi magana baya chanzawa to wlh Aisha tana sa shi ya sauya magana.

“Yauwa hajj Hajara kin gane abun da nakeson ki gane kenan yanzu dai bari mugana dasu diyana sai mu koma kan farida muna gamawa da ita sai muyi maganin Aisha itama, wani murmushi Aunty amarya tasaki kafin tafara magana “yauwa kawata shiyasa nake son ki ai, amma yanzu ya zamuyi da maganar zulaihat? tunda kinga ita ya kamata Safras ya aura
“Eh karki damu yanzu zulaihat ɗin ma bata nan wlh wai tabi saurayin ta party a Dubai, zasu dawo nan da tsakiyar wata mai shiga, inaga abun da za’ayi, idan ta dawo kasar sai ta dawo wajenki da zama har musamu shi Safras ɗin ya fara Son ta ni kuma zanyi nawa kokarin wajen malamai na dan naga an chusa masa Son ta sosai

“Haba hajj sadiya ya za’ayi ki barta tabi saurayi, yanzu tana zuwa yawon nan ne kuma kike tunanin Safras zai sota to wlh tun wuri ki hanata in ba haka ba tofa duk in da zaki shiga Safras dai ba zai sota tana yawon banza ba “Karki damu hajj Hajara idan ta dawo ai shike nan zata dawo wajen kine da zama, gashi kinga gidan ku ba’a fita sai masu zuwa school, suma kai su ake, a dawo dasu, kinga ba halinta fita taje yawon ko ?

“Eh hakane kam to shike nan sai munyi waya zan turomiki 500k ki karawa malamai ɗin naki amin aiki masu kyau da zafi, “to kawai hajj sadiya tace daga haka sukayi sallama, Aunty amarya ta ajiye wayar sama drawer gefen gadonta ta karisa hayewa gadon gaba ɗaya ta kwanta, ta lunshe ido

Aryan

Zaune yake a bakin katafaren gadon sa sanye da kayan barchi riga da dogon wando masu laushi farare tas,yan shara shara marasa nauyi, ya dukar da kan sa kasa, gaba ɗaya gashin kan nan nashi a hargitse ya kwanto masa har kan fuska, ya zuba uban ta gumi, sai wani irn huchi yake kamar wadda aka batawa rai wayar sa dake kan gadon ya ɗauko ya kunna hasken screen ɗin, ya duba time 10:30pm chire password na wayar yayi ya shiga chikin contact nashi, yayi dealling num ɗin Zahra, wayar tana ta ringing har ta kusa katsewa san nan Zahra ta ɗaga.
Chikin muryan barchi tace “hello yaya Aryan, ina wuni
Bai amsa mata gaisuwar sai yace “ki chewa yarinyar nan ta kawomin coffee
“Yaya Aryan ai bata nan, “what? Bata nan ina kuma taje a daren nan? yayi maganar chikin tsawa
“Ammi ta mai da ta kauye, zubur ya miƙe yana faɗin “what? kauye kuma to da izinin wa za’a fita da ita gidan nan, nache a kai min ita wani waje ne?
Ita dai Zahra tsoro ne ya kamata jin yadda yaya Aryan ke magana chikin tsawa, muryar ta har rawa yake tace, “kayi hakuri yaya Aryan,

a fusache ya nufi kofar fita batare da ya sake che da zahra komai ba, kuma bai katse kiran ba,dan yama manta waya yake, idon sa ya rufe,
har ya kai bakin ƙofa zai fita sai kuma ya dakata ya ɗago wayar sa dake hannunsa, ya katse kiran Zahra san nan ya duba time 10:38 ” dare yayi bai kamata naje part na Ammi yanzu ba,
Chike da ɓachin rai ya juya ya koma kan katafaren gadon sa ya kwmata ya lumshe ido kamar mai barchi, Almost 5mnt

Sai kuma ya miƙe zubur ya zauna chikin tsawa yace “kauye kuma aa ina hakan ba zai yuwuba wlh, wai shin nama bada izinin ta fita gidan nan ne? wlh duk ma wanda ya fita da ita daga gidan nan sai na hukun tashi, akan wani dalili?

Zuro kafarsa kasa yayi kafin ya miƙe gaba ɗaya yanufi hanya fita yana faɗin “wlh Ammi dole na tasheki a daren nan, dan in ji ina kika kai yarinyar nan ba zan iya hakuri gari ya waye ba,
Taku yake irin na jaraman maza ji kake dif dif dif idan yana taka kasa, sauri yake sosai kamar zai tashi sama,

Da sallama ya shigo babban palon Ammi na kasa, chikin sauri ya haye sama, kai tsaye betroom na Ammi ya nufa, a bakin kofa ya tsaya tare da ɗan buga kofar yana faɗin Assalamu alaikum.

Ammi dake kwanche kan katafaren gadon jin muryan Aryan yasa ta miƙe zaune da mamaki a face nata, ta amsa masa sallamar

San nan ta sauko daga gadon ta nufi drawer kayan ta ta ɗauko hijabi ta sanya a jikinta, ta dawo bakin gadon ta ta zauna tana faɗin “shigo mana Aryan.

A hankali ya turo kofar ya shigo, tsayuwa yayi a bakin kofar ya ɗan jingina da jikin kofar, yana kallon Ammi dan ya kasa ko magana saboda azaban raɗaɗin da zuchiyar sa ke masa

“Aryan lfy baka yi barchi ba? Da kyar ya iya buɗe baki ya fara magana “Ammi pls tell me ina kika kai yarinyar nan
Ɗaure fuska sosai Ammi tayi kafin tace “kauyen su mana na mai data
“Kauye kuma Ammi to akan me? Akan wani dalili? Kuma taya zaki mai data kauye ba tare da izinina ba, tirkashi Ammi dai baki ta sake tana ganin ikon Allah, ganin Ammi tayi shiru bata bashi Amsa ba yasa yace “wai ma tayaya zaki ɗauke ta bada izinina ba? Kuma wani driver nema ya fita da ita daga gidan nan wlh yau sai ya karɓi hukunchi, in a serious matter yayi maganar,
“Kaga Aryan wlh ka fita min a ɗaki bansan iya shege fa, kai da kanka kazo nan da safe kache baka son ganin yarinyar nan a gidan nan yanzu kuma na mai data gidan baban ta san nan kache, ya za’ayi a mai data ba da izinin ka ba to sannu,nache sannu,

Waro ash eyes nashi yayi waje sosai kafin yace ” Ammi yaushe nache bana son ganin ta kuma, ni fa aa inaga dai mantuwa ki kayi Ammi,

cheke da jin haushi Ammi tace
“Karya dai zakache na maka ba mantuwa ba, girgiza kai ya shigayi yana faɗin “nashiga uku karya kuma Ammi aa wlh ban haka Ni nake nufiba kawai abunne yake bani mamaki da ki kache, Ni nache bana son ganinta.

“To idan ka gama mamakin naka sai katafi ɗaki ka kwanta ai dan dare yayi,

shiru yayi kamar mai tunani almost 10 mnt yana tsaye ya kasa koda motsi,
sosai ya bawa Ammi tausayi dan bata taɓa ganin Aryan a irin wan nan yanayi ba sausauta murya tayi tace “Aryan kaje ka kwanta kaji dare yayi, ɗan firgigit yayi alamar tunani yaƙe, ɗago ash eyes nashi yayi ya sauƙe su kan Ammi, bakaramin tsorata Ammi tayiba ganin yadda idon sa suka sauya sukayi jaaa sosai, ya kasa magana ma a hankali ya juya ya fice daga ɗakin

Dafe kai Ammi tayi tana faɗin “wai duk wannan abun na menene mai yasa mai martaba zai wa yaran nan haka ni ai tunani na burin shi kenan yaga sun fara son mace har ya samu ya musu aure to Amma me yasa yanzu kuma zai wa Aryan haka, ni gaskiya bazan iya ganin Aryan a chikin irin wan nan halinba dole musan abunyi, yau kawai da bai ganta ba jibi yadda ya dawo, hmm

jiki ba kwari ta chire hijabin jikin ta ta mai da drawer san nan ta dawo ta kashe wutar ɗakin ta haye gadonta ta takwanta

Aryan kuwa saboda bakin chiki da ɓachin rai dakyar ya iya kai kanshi ɗaki, dan gaba ɗaya idon sa sun rufe baya gani, addu’a kawai yake Allah ya gaimu gobe, yayi wa garin Yola diran asuba yana shiga ɗaki ya haye katafaren gadon sa ya kwanta, sai juyi yake ya kasa barchi
sai ya lumshe ido kamar mai barchi idan ya tuna diyana na kauye kuma wata kilama yanzu tana tare da wanchan wawan Bello sai ya sake ware manya manyan ashe eyes nashi, da suka sauya yanzu suka koma jaaa sosai saboda tsananin kishi da ɓachin rai,

Da kyar ya iya laluɓo wayar sa ya kunna hasken screen ɗin, ya shiga Kga App yayi playing na hoto nan diyana ya fara binsu ɗaya bayan ɗaya yana kallo, nan take murnushin ta bayyana a kan kyakkyawar fuskar sa, abu ɗaya kawai yake tunawa kuma yake jin sautin a kunnensa wan nan zazzakar muryar tata idan tana faɗin Yaya Aryan, wow gaskiya yau nayi missed sexy voice naki sis, sosai yake ta kallon hotunan yana murnushin har ya kai kan video da ya musu shekaran jiya da zai saka mata sarƙa,

playing na video yayi ya fara kallo yana murnushin, zuba mata ido yayi sosai yana kallon yadda ta zura hannu a riga tana kokarin chiro sarkan, bai ankaraba kawai sai yaka boobs nasa a waje daman shekaran jiya ya kawar da kansa bai san taya ta fitar da sarkan ba, ashe wayar sa ta ɗau komai, a sukwane ya chire video ya fita daga App ɗin san nan ya kashe wayar ma gaba ɗaya, ya ajiyeta a saman drawer gefen gadon, shiru yayi kamar mai tunani har barchi ɓarawo ta ɗauke sa batare da ya saniba.

Maiduguri

Aunty farida che kwamche kan katafaren gadonta ta tada kai da chikin yar dadyn junior, suna yar hirarsu yana shafa kyakkyawa kuma lallausan bakin gashin kanta
My farida magana mai muhimmanci nake son muyi dake fa amma kinzauna kinata zubamin shagoɓa

Aunty farida tace “Kai baby Allah kana da neman rigima to yanzu kafaɗi maganar mana ina jinka ae,
“Watoma nine nake da rigima ko? “Eh mana Allah my baby kafini iya rigima,
Kwafa dady’n junior yayi yana faɗin zamu haɗune yanzu dai magana mai muhimmanci nake son muyi bari mugama maganar zakiyi bayani “to shike nan na ji yanzu dai faɗamin me ka ke so muyi magana a kai
“Yauwa my farida to bani hankalin ki nan, nitsuwa Aunty farida tayi ta zuba masa ido tana kallonsa

“Wan nan yarinyar da kika zo da ita wlh ta shiga raina sosai dan Allah idan ba damuwa ki faɗawa Abba, ya taimaka ya bawa Auta bakura Auren ta,

zubur Aunty farida ta miƙe zaune,tana kallon face ɗin shi taga dai da gaske yake “aa my farida lfy kika miƙe haka ko dai yarinyar matar Aure che? To ai ko matar Aure chema bai kamata kiyi irin wan nan miƙewarba,
“Dady’n junior diyana fa Abba ya riga da ya mata miji wlh, dan da zamu taho har mun shiga mota zamu tafi, Abba yasake bina har chikin motar yamin kashedin kada na kuskura na bar diyana ta kula wani namijin, domin ya mata miji a ɗaya daga chikin kanne na Amma bansan wanene daga chikin su ba, dan Abba’n bai faɗamin wanene ya bawa diyanar ba

Dogon numfashi dady’n junior yaja kafin yace “to shike nan, nima dai kafin na tambaya nayi tunanin hakan domin abun da mamaki ache yarinya kyakkyawa kamar wannan tafito daga gidan ku, dake chike da zaratan samarin nan, ache ba’a mata miji a chikin su ba abun, abun dubawa ne,
Aunty farida zatayi magana sai sukaji alamar motsi a palon kasa, kallon dady’n junior tayi shima ita yake kallo, a tare suka sauko daga gadon da sauri suka nufi waje

Suna saukowa palon kasa turus suka tsaya, suna kallonta da mamaki, Aunty farida tace “my diyana me kikeyi a nan ? Meyasa kika fito daga ɗakin? Shiru diyana bata basu amsa ba tana zaune saman sofa tana kallon kasa ta buga uban tagumi,
juyowa Aunty farida tayi ta kalli dady’n junior, shima ita yake kallo, sake dawo da kallonta tayi kan diyana dake zaune ko motsi batayi, a hankali Aunty farida ta taka zuwa kusa da diyana tasa hannu ta ɗan taɓata tare da kiran sunan ta a hankali,
Firgigit diyana tayi tare da miƙewa, zuba mata ido Aunty farida tayi kafin tace “my diyana lfy kike zaune a nan? Tunanin me kikeyi haka kuma?
Tsuke fuska diyana tayi ta turo baki ta fara magana

“Aunty farida wlh na kasa barchine, kuma ina jin ajikina kamar yaya Aryan bai da lfy san nan kuma Allah idan na rufe idona sai in rinƙa ganin yaya Aryan yana faɗin, bakin ki kawomin coffee ba yau to munɓata, Allah Aunty farida ina son ganin yaya Aryan, kewar shi nake

Tirkashi turus Aunty farida tayi tama rasa me zatachewa Diyana, domin iya gaskiya diyana tafaɗa dan bata karya, amma bansan meyasa Abba zai yankewa yaran nan irin wan nan ɗanyen hukunchin ba gashi diyana ta kasa barchi, kuma ina da tabbachin shima Aryan ɗin yana chikin damuwa.

ganin Aunty farida tayi shiru alamar ta tafi duniyar tunani ne yasa dady’n junior ya dubi diyana yace
“jeki ɗaki ki kwanta ko da safe da kaina zan kai ki wajen yaya Aryan kuma ki daina tunanin ko bai da lfy, lafiyan sa kalau sharrin sheɗan ne yasa kike ganin kamar bai da lfy, kije kiyi addu’a ki kwanta kinji, to kawai diyana tace san nan ta nufi ɗakin ta,

Hannun Aunty farida dady’n junior ya kama suka nufi stair ɗin suka koma ɗaki,
“My farida wai meke faruwane?, ko dai Aryan shine mijin da Abba yayi wa diyana
“Dady’n junior wlh nima abun yafara ɗauremin kai, nan dai Aunty farida ta shiga bashi lbr duk wani abun da ta sani dan gane da yaya Aryan da diyana, ta karisa maganar dai dai lokachin da suƙe hawa kan gadon su,

“Kinsan me my farida, batare daya jira amsar taba ya chigaba da chewe “Abba yana da gaskiya domin kinga dukkan kannen namu basu taɓa soyayya ba hasalima basu ɗauki mace da daraja ba, ganin ta suke kamar abun banza, wlh a irin wan nan yanayin da suke chiki idan aka ɗauki mace aka basu to ta shiga uku domin basusan darajar taba zasu wahalar da ita sosai, yanzu dai ki dubi yadda Aryan ke masifar son yarinyar nan batare da yasan Son nata yake ba amma duk dahaka daga ɗan magana dasu Umar sukayi, ya fusata har yaje ya samu Ammi ido da ido yace bayason ganin diyana kinga a nan ma rashin sanin darajar mace ya bayyana karara, a tare dashi, wlh gwara da Abba ya masa hakan, kuma ku barshi sai ya gasu sosai sai yasan mace fa halittace mai daraja wadda kowani ɗa namiji ke son kasan chewa da ita, ku kyalesa sai ya furata da bakin sa chewar yana Son ta, in ba hakaba ko an musu aure ran da su Umar suka sake mai maita abun da sukayi shima sake mai maita abun da yayi zai yi. da katawa yayi da maganar yana mai da numfashi,

“Kana da gaskiya dady’n junior wlh rashin sanin darajar macece har yasa Aryan ya iya tinkarar Ammi ya faɗa mata hakan, to amma abun tausayin a nan shine ita diyana yanzu dai da kunnen ka kaji halin da take chiki, tana son Aryan sosai Amma itama batasan chewa Son nashi takeba, saboda kaga ita yarinya che kuma gashi ba wani ilimin ke gareta ba ita ko kallon film batayi sai dai buga game kawai, ta iya

“Hakane my farida dolene diyana ta zama abun tausayi amma ke zaki jata a jiki domin ki rinƙa rage mata, kewar nashi kada ki bari ta rinƙa zama ita kaɗan, gobe idan Allah ya kaimu zan saya mata sabuwar waya mai kyau sai kisa Sim naki a chiki, ki mata download game’s dayawa, idan kin gama ki chire Sim ɗin, san nan kema kiyi taka tsantsan da wayar ki dan kinsan gaba ɗaya kannen ki basa iya yin wuni ɗaya batare da sun kira ki ba, kada ki kuskura ki sakawa diyana Sim card a wayar ta, domin a yadda kika bani lbr na fahimci yariyar akoi kwakwalwa sosai, dan haka sai kinyi taka tsantsan da ita sosai

“To shike nan dady’n junior zanyi duk yadda kace Saboda nima ina kaunar diyana sosai kamar yadda nake kaunar Aryan, bazan so taje gidan mijin da bai san darajar ta ba, zanyi iya bakin kokarina wajen ganin, na bata kulawa na chanza mata abubuwa da dama

“Good my farida hakan yayi to yanzu dai mu kwanta muyi barchi kinga dare yayi ma karisa maganar gobe idan Allah ya kaimu,

atare suka kwanta ta shige chikin kirjin sa ta lafe shi kuma yana shafa bayan ta har barchi ya ɗauke su.

Kano

Tun misalin karfe 6 su hiyana suka gama shirin zuwa school, yaya Khalid kawai suke jira yazo ya ɗauke su.

sai misalin karfe 7:30 yaya Khalid yazo ya tasa su a gaba suka fito harabar gidan suka nufi parking space, yau da kanshi ya tuƙa su a family car,

Gudu yake shararawa da motar sosai akan shin fiɗaɗɗiyar hanyar school nasun, chikin kan kanin lokaci suka isa makarantar,kai tsaye parking space na ya nufa yana kashe motar, ya fito a gurguje ya yana faɗin “kufito ku tafi class dan kun kusa makara, yana gama faɗin hakan ya nufi office na HM na makarantar, domin naje ya biya musu kuɗin makaranra.

Abangaren su hiyana kuwa yaya Khalid na tafiya suma ko wace ta kama hanyar class nasu, amma kallo ɗaya zaka yiwa hiyana kasan tana cikin matsanan chiyar damuwa ga blue eyes natan nan duk sun kunbura da alama tasha kuka, dan dai ita ba mai yawan kallon mutane bane kullun kanta na kasa shiyasa mutun ba zai gane kunburin da idon nata sukayiba, tazo dai dai zata shiga class nasu, taji daga bayan ta an che “ke zonan chikin tsiwa, da sauri ta juyo, ganin….✍️✍️

More comments an share

 

 

💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER’💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(Star Lady)

*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat….love)

*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)

 

 

More comments an like pls

*💫STAR LADY💫*32

💖The Talent Troupe Writer’s 💖

*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

 

*

Leave a Reply

Back to top button