Gidan Aunty Book 1Hausa NovelsHausa Novels

Gidan Aunty Book 1 Page 37-38

Sponsored Links

BOOK 1📕

Page 37-38 💖

Maso da fuskarsa yayi Daidai kunnanta kafun ya furta “banda rashin ji” da sauri ta gyada masa kai ,dago da ita yayi daga jikinsa kafun yayi mata kallo d’aya ya dauke kansa,Jan hannunta yayi ya zaunar da ita kan kujera kafun ya dakko magungunan ta, tana ganin magungunan ta fara kunkuni duk yana kallanta,Ballan magungunan yayi ya bata, kamar zatai kuka haka ta sha magungunan Sabida kallan da yayi mata, allura ya fara hadawa ,tana ganin alluran ta fara bunburi idanuwanta duk sun cika da kwalla, kallanta yayi kafin yayi magana tayi saurin cewa “ni bana san Allura”,be ce mata komai ya rike hannunta , da sauri ta mike zata gudu ya rike hannun nata kafun ya hade ransa , narai narai tayi masa da ido har kwallar data tara sun fara sauka, ce mata komai ba har yanxu ya dakko allurar,kuka kawai tahee ta fashe masa dashi, duk da Hakan be kyaleta ba sai da yayi mata allurar.Ta dade tana kuka be ce mata komai ba har sai da tagaji dan kanta ta fara ajiyar zuciya a hankali ,kofa ya nuna mata kafun ya furta “jeki wanke fuskanki”, cikin turo baki ta mike tare da barin wajan , ba’a dau dogon lokaci ba ta dawo idanuwanta har sun fara canzawa zuwa red colour . Har yanxu be kulataba sai ma nufar kofar fita da yayi,itama cikin sauri ta biyo bayansa sai faman kunburi take.
Direct part din dada suka nufa ,koda suka shiga ba kowa a falon sai su ihsan da basu dade da shigowa ba, ko wannan su shiga taitayinsu yayi musamman su amrah da ke binsa da mayataccen kallo kamar su hadi yeshi,har yar rige rigen gaishesa suke ,ba gaisuwar Wanda ya amsa acikinsu sai ma tanbayar da ya jefo musu cikin hade rai “ina da dada”har saurin hada baki suke wajan furta “sunje gaisuwa ne”, be kara cewa komai ba sai tahee da ya dan kalla ta kasan ido, har yanxu sai faman kunbure kunbure take , Taki yadda ta kalli kowa na cikin falon “ I will be back “ ya fada cikin kasa kasa da murya ,ko su da ke cikin falon babu Wanda ya jisa sai tahee data kara cuno baki, be kalli kowa na cikin falon ba ya fita ,ihsan ce ta kalli tahee tare da sakar mata murmushi,”kin tsaya a tsaye ,toh kizo ki zauna mana “ ko kallanta tahee batayi ba bare ta sa ran amsawa,kara maimaita maganar ihsan tayi, yanxun ma tahee bata kalleta ba sannan bata amsa mata maganar ba, cikin tsakanin jin haushi da tsantsan kishi amrah ta ja tsaki” aikin banza , kece ma kika tsaya kula wannan kaskantarciyar da bata da maraba da kazamar bola, ni naso ace ba iya kwakwalwar ce ta juyeba naso ace ta haukace shegiya dan gin mayu da alama ba haka kika bar muba,kuma wallahi ko ina so ko ba kyaso sea kin rabu da king danshi mallakinane,bata kammala zancan nata ba sumayya ta kalleta cikin jin haushin karshen zan centa wai malla kinta,dogon tsaki sumayya taja kafun ta furta “iska na wahalar da me kayan kara” tana kammala zancan ta tabar part din tana bin tahee da kallan tsana,ita dai har yanxu tahee tana tsaye kamar wacce aka dasa ,itama firdausi tashi tayi tabar part din batare da tace da kowa Uffan ba, falon yayi saura daga ihsan sai amrah da tahee ,tabe baki ihsan tayi kafun ta soma magana “ni bansan me ke damun ku ba wallahi tunda aure dai anriga an daura ai..” bata kammala zancan nata ba amrah ta zabura tana katseta cikin sauri,”tsaya tsaya, idan bazaki goyan mana baya ba ,bama bukatar bakinki a ciki” bude baki ihsan tayi da niyar yin magana taji wayarta na ringing , sunan mamy ne ya fito cikin wayar ,daga wa tayi tare da kara wayar a kunnanta,toh kawai tace kafun ta mike tsaye “zan dawo mamy na kira na “ tana gama fadar hakan ta bar wajan. Sosai wani farin ciki ya lullube amrah, ganin daga ita sai tahee,”dogon tsaki taja tare da mikewa tana bin tahee da wani matsiyacin kallo,kafun ta fara zagayeta tana tafa hannaye,TAHEE kuwa na tsayen ta har yanxu bata zauna ba sannan batayi wa kowa magana ba, bata ankaraba sai jin saukan mari tayi a fuskarta , da sauri ta dafe wajan da aka mare tan tare da dago fuskarta,amrah ce ta mare tan ,ta daga hannu da niyar kara marin nata tahee ta daddage ta tsinka mata marin itama, kara amrah ta saki sabida sosai taji zafin marin” ni kika Mara”,shareta tahee tayi tare da juyawa da niyar barin wajan , saurin fincuko tahee tayi baya,sosai kafarta daya ta bugu, itama taheen karar azaba ta saki cikin fitar hayyaci ta shake amrah,tare da gantsara mata cizo,sosai suka fara fada musamman tahee da idanuwanta suka rine,sosai take jibgar amrah kamar wacce aka aiko,suna cikin wannan rigimar king ya shigo falon ,da sauri ya daka musu tsawa,rabuwa sukai ko wannansu yana sauke nunfashi sabanin amrah dake sauke nunfashin wahala,”me ya faru” ya tanbayesu cikin daka tsawa,”mari na tayi” tahee ta furta tana nuna ban garan fuskar da amrah ta mareta ,cikin rawar murya amrah ta furta “karya take mun,rashin kunya ta zo tana mun dan nace ta zauna”, ganin irin kallan da king ya jefa mata,bude baki tahee ta yi da niyar magana ya daka mata tsawa,”bata hakuri” da sauri ta dago idanuwanta ,cikin rawan murya ta furta” mari na tayi fa”, Kallan da ya jefa mata ne yasa tayi shiru tana sauke idanuwanta, “kiyi hakuri” ta furta kawai tare da juyawa , hawayen da suka zubo mata ta share tare da soma tafiya cikin din gishi, dan kallanta yayi ganin tana dingishi har ta fice da ga falan kafun ya mayar da kallan sa yayi kan amrah dake faman sakin murmushin jin dadi,tana cikin dogon tunanin da ta fada taji saukar mari a fuskarta , sosai marin ya shigeta ,bata gama dawowa ba ya shako wuyan ta ,ganin hakan be masa ba yasa ya murde mata hannu da karfin gaske kamar me shirin karya hannun kafun ,kara amrah ta saki cikin azaba ta soma bashi hakuri,guntun tsaki yaja kafun yayi wulli da ita yana binta da kallan tsana kafun ya soma magana cikin kausashshiyar murya “daga yau ,idan kika kuskura hannunki ya kara taba ko gashinta ne ,hmm” ya karasa tare da jinjina kai kadan yana taunar lips, ko inda take be kalla ba yayi hanyar barin falon, amrah kuwa sabida azabar da takeji da bakin ciki yasa kukan da take ma ya dauke duka sai kukan zuciya da ta fara tana faman tsinewa tahee .

Yana fita daga part din yaci karo dasu dadan suna kokarin shiga part din,TAHEE na rike da hannunta,sai hawayen da take sharewa, ganin king ya fito daga part dinta yasa tayi saurin kallansa “Yawwa kwanda da Allah yasa na ganka,ga tanan sai faman kuka take mun na mata tanbayar duniya tace mun faduwa tayi sai ka lallashi kayarka,dan bazan iya ba ,ka dauketa ku tafi”, ta kasan ido ya dan kalli taheen gefen fuskarta har ya danyi ja,kafun yace komai tahee tayi saurin cewa “ ni zan zauna a wajan ki” ba dada ba hatta king sai da ya dago idanuwansa ya kalleta ganin yadda ta hade ranta lokaci d’aya,”kikace me” dada ta tanbaya cikin mamaki ,sau da dama in dada tace tazauna bata zama shiyasa abun yayi mugun bata mamaki” zan zauna a wajanki” ta kara fada har yanxu bata kalli inda dadyn nata yake ba,washe baki dada tayi cikin farin ciki” oh Allah na ,yau de tahura zata yini dani ,Allah na gode ma “,ta karasa tana kamo hannun tahee sai faman zabga mata murmushi take, dan tabe baki king yayi ba tare da ya ce musu komai ba ya soma tafiya,kallansa dada tayi “Kai de bakin halinka yayi yawa,yanxu matar taka ma bazaka ce mata ka tafi ba tunda ni ka rainani “, dan tabe bakinsa yayi kadan kafun ya kalli yadda taheen take danyin dingishin kadan kadan,harta shige part din dada,har yanxu kuma bata kalli dadyn nata ba, mai da kallansa king yayi kan dada kafun yace “toh matata sai na dawo “ ya na kammala zancan nasa ya bar wajan, rike baki dada tayi tana bin bayansa da kallo kafun ta furta” shi wannan Auran dan iska ma ya Mayar dashi ,wacece matar tasa” ganin ba me bata amsa yasa tabi bayan tahuran itama.

A kofar shiga taci karo da amrah, tana ganin ta ,ta kara hade ranta ,tare da shigewa cikin falon,itama amrah binta tayi da kallan tsana kafun ta wuce tana cizon yasa.kan doguwar 3sitter tahee ta kwanta tana buye fuskar tata kafun ta fashe da kuka kasa kasa, a haka dada ta shigo ta sameta, ganin yadda ta rufe fuskar tata yasa dada tayi tunanin bacci ne ya dauke ta”ke kuma tahura haka ake ai da kin wuce daki kinyi baccinki” tana kammala zan can ta tayi hanyar zuwa dakinta. Har yanxun tana kwancan tana kukanta har bacci ya dauketa a hakan .

🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧

YOLA
Sosai ya jigata in ba kallan kurinla kayi masa ba ,ba Lalle ne ka gane saba, jikinsa duk ya saki sabida azabar wahalar da yasha, tsaki daya daga cikin mutanan ya saki kafun ya kalli Wanda ya dago da fuskar taheen,fatan dai kullum kuna basu hotan da ya kamata, cikin wata murmuya Mara dadi ya amsa mata,jinjina kai sukayi alamar gamsuwa kafun daya daga cikinsu ta furta ,a kara ninka musu hotan kamar yadda aka saba, ka tabbatar kana da ido a kansu ,duk Wanda yayi kokarin guduwa kuma ka harbe mun kansa ka ciro mun kwakwalwarsa,sosai matasan suka firgita da jin kalamanta, ko karfin motsa jikin su basu dashi balantana su rokesu,saukar bulala suka fara ji ,tun basa kokwarin guda har suka mike cikin a baza ,kafun a mayar dasu cikin kurkukun, kyalkyalewa da dariya mutanan sukai daya daga cikin mutanan ce ta furta “amma ni yarancan ya tayar mu da jikina ,dole na biya biyan bukatata kafun ya bar nan wajan,kara sakin wata yar iskar dariya sukai gaba ki dayan su , ta kusa da Itace ta kalleta ,”ni kuma ya zakiyi dani ,kinsan ke tawa ce ko” shafa mata fuska tayi kafun ta sakar mata kiss agaban mutanan,saurin rungume juna sukai kafun su bar wajan, haka ko wannan su ya rike hannun partner dinsa suka bar wajan.

Cikin dakin da aka maidasu,cike yake da maza sosai aciki kowa ka kallesa a galabaice yake ,gashi ba daman yiwa juna magana, shima taheer yana rabe daga can gefe duk an tuttureshi,a boye yake share hawayan da yake zubo masa ,zuciyar sa fal tunanin oumman sa da tahee,kullum tunanin sa a Wana hali suke ciki yanxu..

➰➰➰➰➰➰➰➰➰

KANO
A cikin dan lokacin nan da tayi da mutanan gidan sosai suka saba musamman Khaleed da zahra, alhaji kabeer ne kawai bata haduwa dashi,har mamakin yadda su zahra suka sake da oumman yake amma har yanxu be ce mata komai ba akanta ko yayanta da suka bata .

Bayan idar da sallanta sosai take yiwa yayanta addua musamman taheer da batasan halin da yake ciki ba , tana adduar tana share hawayen da suke zubo mata,sosai tunanin taheer dinta yake mata yawo a zuci ko a Wana hali d’anta yake ciki, ya zama dole ta koma bunkure ko ya dawo yana nemanta itama , wannan tunanin yasa ta mike sanye da hijab dinta duk da kasancewar bata da kudin motar da zata koma haka tafito falan , da sauri zahra ta mike tare da nufota “oumma sannu da fitowa, yanxu nake shirin zuwa wajanki, ga waje ki zauna kinji”dan girgiza Mata kai oumma tayi “zan koma bunkure ko zanga taheer “da Sauri zahra ta rike hannunta “To zan biki oumma “ girgiza mata kai oumma tayi , hawayene suka fara taruwa a idanuwan zahra “toh oumma ki zauna tare da mu dan Allah”, share mata hawayen da ta fara oumma tayi kafun ta furta “kiyi hakuri zahra” sosai zahra ta fashe mata da kuka gwanin ban tausayi dan ganin oumma take tamkar oummanta data rasa ,ganin yadda zahran take kuka yasa oumma kwata kwata bataji dadin abunda tace matan ba, suna tsaye a wajan shima Khaleed ya shigo falon, ganin yadda zahra tke kuka yasa ya karaso wajan ta yana tanbayarta ,fadawa jikinsa tayi sosai ta kara fashewa da kuka “yaya!! zata tafi ta barmu kace ta tafi dani kaji” ta karashe zancen nata da fashewa da wani saban kukan.shima kallonta Khaleed yayi” oumma dan Allah ki zauna damu, muna jinki kamar momma din mu da muka rasa” ga baki d’ayan su sun sakar wa oumma lakar jikinta,sosai tausayinsu ya kamata amma tasan ya zaman mata dole tunda ba a halinsu bace.”Assalamu Alaikum “ sallamar alhaji kabeer ta karade kunnuwansu, da gudu kuwa zahra ta nufeshi tana sakar masa kuka shima ,cikin matsanan damuwa ya kalleta ,”auta me akai miki” abunda ta fadawa Khaleed shi ta fadawa dadyn nata, share mata hawayen fuskarta yayi “shikenan dena kuka auta ,zomu karasa ciki”, murmushin jin dadi ta saki jin abinda yace mata,kama hannunta yayi suka shigo falan kafun ya kalli oumma shima,” oumma dan Allah ki zauna damu” ya furta yana kallan fuskarta ,ba zahra ba hatta Khaleed sai da ya murmusa ganin yadda dadyn nasu yayi,suma hade hannayensu sukayi kamar yadda dadyn nasu yayi, sun kuyar da Kai oumma tayi duk tana jinta a takure , fahimtar hakan yasa dady yace duk su zauna, samun waje sukai gabaki dayan su, cikin serous Tone dady ya soma magana,”na da anbincika mun garin naku kamar yadda kika bamu labari, har yanxu ba a ga taheer ba amma jami’ai suna kan bincikensu har yanxu”cikin sauri oumma ta share kwallar dataji tana kokarin zubo mata, cigaba da magana dady yayi”ko wana dan Adam da tashi kaddarar, sannan kisani Allah yana jarabtan salihan bayinsane domin ya duba imaninsu, tabbas duk musulmin Kwarai anaso ya yarda da kaddarar sa me kyau da mara kyau”sosai dady yayi musu Nasiha gabaki dayan su ,har yanxu kan oumma a sunkuye taye, kafun daga karshe ya dora da “muna neman Alfarmar ki zauna damu nida yarana kafun abinciko inda taheer yake ,gamu da kokan baranmu”,saurin buda baki zahra tayi harda tsugunnawa” Dan Allah kuma ko dan sabo dani” ta furta har ynxu muryanta na rawa,bude baki oumma tayi daniyar yi masa Godiya ya dakatar da ita”mudai ba godiyarki muke soba abincewarki muke jira” duk zuba mata ido sukai kowa yana jiran jin amsar ta,yadda suka zuba mata idanune yasa ta jinta duk a takure ,gashi ba damar tayi musu , musu”Dan Allah oumma” zahra kara fada ,gyada mata kai oumma tayi, da wani irin speed ta karaso wajan oumma tare da rungumeta ,lokaci d’aya tana sakin kuka da dariya, ganin yadda suka shiga farin cikine yasa zuciyar oumma raunana tabbas sunyi rashin uwa,shima dadyn sosai yaji tausayin yaransa ganin irin farin cikin da suka nuna,be kuma cewa komai ba ya tashi ya bar falon.

🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧
➰➰➰➰➰➰➰➰➰

Tunda yashiga office dinsa time to time yake duba wayar hannunsa kamar me jiran abu,yadda take din gishine ya fado masa arai da lokacin da take furta”zan zauna a wajanki”tuno wa da hakan yasa ya dan taki tsaki sabida jin hau shin tunanin da ya fado masa, aikin gabansa ya cigaba dayi,lokaci zuwa lokaci ya na kara kallan time.

7:00pm bayan sun idar da sallahn magrib,sosai kafar tahee ta rike ga idanuwanta da suka kara ja kadan sabida kukan da Tasha, kallanta dada tayi “yanxu ke Sabida sakarci kafarki da wannan ciwon shine kikai shiru baki bari an duba miki ba” ita de tahee sai faman kuka take kasa kasa ganin yadda kafarta ke mata zafi,suna cikin haka abeey yashigo part din bayansa kuma ammi ce , ganin halin da tahee take cikine yasashi dubansu”dada ya akai haka ,da ansani tun lokacin da ta samu wannan ciwan an duba matashi,ciwo irin haka ai ba dadi” girgiza kai dada tayi”kaide kasan wannan ,Nima da muke tare da ita bansan da wannan ciwan ba ,nasan de tace mun ta fadi,mijinta kuma be fada mun ba” kamar ammi zatace wani abu sai tayi shiru kawai tana bin taheen da kallo, sallamar ummey ce ta katse musu zan canai, kara soma tayi ciki ganin yadda ko wannan su yayi cirko cirko, dai dai lokacin da su uncle salim suke shigowa falon, “Yawwa “ dada ta furta ,”yanxu kawai abunda za ai Akira likita ya duba ta,Kai saleem kirawo likita yanxu”, tsayar da ita abeey yayi ta hanyar furta”bari na kira mujinta yazo ya dubata dai “, kowa sai faman sannu yake mata, ganin lokacin sallah yayi ne yasa dada umartar kowa da yaje yayi sallah sai su dawo,itama taheen da kyar take tsayar da kafar tata sabida dan kunburin da tayi a hakan tayi sallahr tata cikin natsuwa kamar asalin tahee dinta, tana idar da sallan ta kwanta a wajan, anan bacci ya kara daukarta. Shigowa dada tayi hannunta dauke da fura ganin yadda take baccinta cikin kwanciyar hankali yasa dada kura Mata ido” ko dai cikine da ita” ta furta a ranta, kafun kuma ta kawar da zancan ta hanyar ajje mata furan a gefe tare da fita daga dakin.

🫧🫧🫧🫧🫧

9:30 motocin king suka danno kai cikin gidan , part dinshi yayi niyar zuwa sabida yanda ya gaji, tuno kiran da abeey ya masa ne yasa ya nufi part din dada, a hankali ya zuro da kafarsa kafun ya fito da gangan jikinsa gabaki d’aya tare da nufar part din, dada da abeey ya tarar a falan sai su uncle musaddiq da suke dan hira kasa kasa, dada na ganinsa ta jefa masa harara “ shanyar da ka shanya sun bushe saura babbaka” dauke idanuwansa yayi kanta tare da kallan abeey ,ganin yaki kallansa ne yasa jikinsa yin sanyi kadan kafun ya karaso cikin falon,ba tare da abeey ya kallesa ba ya furta “kaje ka duba lapiyar matarka”,cikin kasa kasa da murya ya furta “am sorry abeey” ko su uncle musaddiq basuji me yace ba se shi abeey din ,dago da idanuwansa yayi cikin dan rauni ya furta “ka kula da ita” jinjinawa abeey kai yayi cikin kwantar da murya ya furta “insha Allah” ,nauyayyar ajiyar zuciya abeey ya saki tare da sakin gun tun murmushi, king kai tsaye dakin dada ya shiga, kwance ya tarar da ita kan sallaya sai faman baccinta take hankali kwance, karasowa yayi cikin dakin tare da durkusowa kadan,sosai ya ke kallan fuskarta musamman dan wajan da yayi ja kadan,yadda ta turo bakinta ya kalla “cikin barcin ma” ya furta tare da dauke kansa,hannayensa yasa tare da daukarta kamar wata baby yana shirin fita daga dakin,dada ta shigo” iskancin kuma anan zaka fara” hade ransa yayi kafun ya kalleta” ko mu zauna anan dakin zefi “sakin baki dada tayi tana kallansa jin kalaman sa,”Nide babu ruwana, furar ta hura nazo dakko mata daman tunda yau taki cin abinci, yar hirar ma yau batayi ba”ta karara zan can nata tana dauko wata sabuwar furar cikin fridge ne dan girma,tana mika wa king ko dago da fuska ta kallesa takiyi wai ya fi karfinta, ta na mika masa tashi toilet shi kuma dan kallan taheen yayi jin ko abinci bataci ba kafun ya bar dakin, a falo ya tarar da oummey da ammey, kowa kallan mamaki ya bishi dashi ganin yadda ya dakko taheer,abeey kuwa sosai hakan yayi masa dadi,gaishe da su oummey Kwarai yayi tare da barin part din gabaki d’aya .

****** Direct wani daki ya shiga da ita dake kasan stairs komai nacikin dakin fari ne kal dashi ,sosai dakin ya hadu iya haduwa,kan lallausan gadan ya nufa tare da kwantar da ita ,sannan shima ya bar dakin,kusan tsawan lokaci kadan ya dawo sanye da wasu fararan phyjamas fari tas dashi me shegen laushi da san tsi , da alama Wanka yayi, kamshin imperial majesty ta ko ina ya cika dakin, inda take ya nufa hannunsa dauke da wani dan kwalbar dan karami,a hankali yake bin kyakkyawar fuskarta da kallo ganin yadda take ya mutsa ta,kafar data dan kunbura ya fara bi da kallo,kafun ya kai hannunsa a hankali kan kafar,kamar wacce aka sanarwa ta farka arazane tana sakin kara, Wanda ta gani ne yasa ta dan turo bakinta, tare da dauke idanuwanta tana share hawayan idanuwan,guduwa zatai akan gadon kafarta ta kara rikewa ,kallan ta danyi Ganin har yanxu taki kallansa,rike kafar tata da ta kumbura yayi gagam batare da yace komai ba, kara tahee ta saki,tana rike hannunsa da ya rike mata kafar,”da zafi ,ni banaso”ta karasa zancan nata da sakin wani marayan kuka, be ce mata komai sai hade ransa da ya karayi,kafar da ta kunbura yake matsawa a hankali tare da shafa man da ya dauko,duk da haka sosai take jin zafin,fuskarta duk ta baci da hawaye,”Banasan ka dady, I hate you” shine abunda take faman fada ganin ta kasa kwace kafarta da yake matsa mata,har dodan kunnansa yajiyo sautin I hate din you din data fada, be kyaleta ba sai da ya gama matsa kafarnan sosai,lokacin har kukan ya dauke sai sheshshekar da take faman saukewa,bece mata komai ba ya mike ya fita, be dade da dawowa ba ya shigo da wata kwarya ,mika mata furar dake ciki yayi,karba tayi idanuwanta na zubar da hawaye ta shanye furar daman yunwa take ji, magungunan ta ya mika mata,yanxun ma bata dago ba ta karbi maganin tasha,bayan ya hada allura yayi mata shima,da mamaki ya ke kallanta”fushi” ya furta kasan zuciyarsa , ganin yadda taki kulasane yasa shi dauke kansa cikin hade rai shima” wanka”yanxun ma batace komai ba ta mike tana dan gisawa kadan kadan,duk da ta gane ba wancan dakin bane haka ta nufa wata kofa ta shiga, kamar yadda wancan dakin yake haka wannan yake shiyasa batayi wahalar gane toilet ba, Wanka tayi cikin sabulan wankan toilet din masu shegen kamshi, kafin ta fito tana din gisawa a hankali,turo bakin ta tayi kadan tana bin wajan da kallo , cikin karanbani ta danna wani button,a hankali kuwa wajan ya fara budewa,wasu budaddun wardrobe suka bayyana , dan murmushi ta saki tana bin kayan wajan da kallo,wata white t-shirt ta dauka,sosai rigar tayi mata burgujeje har wajan qwiwarta,pant kawai ta saka tare da feshe jikinta da turare, sai wata hula da ta saka haryanxu gashin ta be shige jiki ba sai faman zamewa take, rigar data saka kuwa sosai yayi mata kyau kamar dan ita aka fita, juyawar da zatayi ne idanuwansu ya fada na juna, da Sauri ta d’auke idanuwanta tana juyawa,be ce mata komai ba ya fito daga dakin,kin fitowa tahee tayi daga wajan kusan tsawan lokaci saida ta ga hasken wajan ya d’auke duka kafun ta fito cikin sauri tana furta “dady” karo da tayi da abune yasa cikin tsoro ta fara shafa sa tana furta “dady”,uhmm kawai yace mata ,sosai ta damki rigar jikinsa kamar wacce akacewa za a kwace mata shi,soma taku yayi a hankali ganin duk taku dayan dazai yi sai tayi itama har suka karasa kan gadon, tana jin ta akan gadon ta kara lafewa a jikinsa, magana yake san furtawa amma bakinsa ya masa nauyi, ya dau dogon lokaci yana juya maganar tasa,”bai san lokacin da bakinsa ya furta “fushi kike “kara lafewa tayi ajikinsa ba tare da tace masa komai ba sai dan bakinta da ta turo masa,kamar wacce aka sa dole cikin muryar kuka ta furta”Itace ta mareni” kinaso na rama miki ya tanbayeta , da sauri ta daga masa kai kafun ta kara cewa “kuma taji mun ciwo” shima zamu rama,”kuma ka kara tabamun kafata, a hankali ya kai bakinsa Daidai kunnanta ka fun ya furta “yanxu Lefi nane ko” Kai ga jinjina masa,saman goshinta ya dan summata kadan kafun ya furta “shi yasa kikace kin tsaneni”turo masa dan karamin bakin ta sakeyi ,cikin wauta ta furta “ai yanxu ina sanka” tana karshen maganarta ya hade bakinsu waje d’aya……

 

********
KUYI HAKURI DA RASHIN JINA KWANA BIYU DA BAKUYI BA.

MSS LEE 💖

💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖
💖💖GIDAN AUNTY💖💖
(a heart touching love story)

Story & written
By
Mss Lee 💖

PAID BOOK

MAI BUKATAR COMPLETE DIN GIDAN AUNTY YAYI MUN MAGANA TA WANNAN NUMBER 07041879581

Leave a Reply

Back to top button